Abokin Mijina Hausa Novel Complete
ABOKIN MIJINA
*PAGE 1~5*
“Wai kai sai wani d’oki kake kamar wanda yau aka kai maka matar.”
“Abokina bazaka gane bane Wallahi tunda na auri Husna ban ta6a kusan tantaba kai baka tunanin zan shiga hakk’inta?” Ya k’arasa maganar fuska d’auke da damuwa.
Wani dad’i ne ya lullu6e Yusuf sannan yace
“To ai sai kayi hak’uri tunda kasan tsoro take ji kuma idan kayi bata cire wannan tsoron ba Wallahi ciwo zaka ji mata kaca-kaca.”
Fansa 2022 Hausa Novel Complete
Gaban Farooq ne yayi mummunar fad’uwa sannan yace
“To Abokina menene mafita?” Ya tambaye shi.
“To mafita dai d’aya ce kawai ka hak’ura har sai ranan da Husna ta bude baki tace ka kusanceta.”
Waro ido yayi yace
“Kai Wallahi Husna bazata iya cewa na kusanceta ba koda kowa zamu shekara ne sai dai kawai na cire tausayinta nayi abinda yake raina dan kuwa Wallahi yana damuna kasan dai abinda Doctor yace mun.”
Wani kallon tsana Yusuf yayiwa Farooq sannan yace
“Kenan kayarda ka kashe ‘yar mutane ko?
Dan kuwa nasan kai bazaka sausauta mata ba.”
“No Yusuf yanzu nazo wajen kane dan kabani shawara saboda kai ka dade da mata kuma kaine aminina dan haka nazo gunka please Abokina ka taimaka mun.”
Murmushi mugunta Yusuf yayi sannan yace
“To shawara ta d’aya ce kajira ta nan da sati d’aya idan kaga babu halamun buk’ata a tattare da sai kawai kayi abinda kayi niya.”
“Hmm to Allah yakaimu nan da satin amman Wallahi nikam a matse nake.”
Haka dai suka tayi a tsakanin su sannan suka yanke akan sai nan da sati.
Yusuf ne ya rak’oshi har gida a lokacin da suka shigo gidan wani wawan k’amshi ne ya daki hancin su Wanda sai da gaba d’ayan su suka shiga wani hali.
Zaune take akan d’aya daga cikin kujerun da suka zagaye parlour.
Swiss lace ne a jikin ta Wanda ya amsheta kamar dan ita akayi.
Farooq ne yayi sallama wanda Yusuf ya kasayin Sa.
Amsa musu tayi cikin zazzak’ar muryan ta sannan ta tashi tana musu sannu da zuwa.
Yusuf sake rikicewa yayi da ya kalli halitattar Husna Wanda bai ta6a tsammanin tana da shi ba.
Farooq ne ya d’an bigeshi yace
“Kai kuwa sai kace Wanda baka Santa ba sai wani kallon ta kake” ya k’arasa maganar cikin zolaya.
D’auke idon shi yayi a kanta sannan yace
“Wallahi abokina sai naga kamar Yau ta chanza mu…..”
“Sannun Ku da zuwa”
Yusuf yayi saurin amsawa da cewa
“Yauwa sannu amarya ya kike?”
Murmushi tayi tace “Lafiya k’alau Ya Yusuf, ya Anty Hafsat?” Ta tambaye shi.
“Lafiya ta k’alau gobe insha Allahu zan kawota ku wuni saboda Ku fara sabawa tun yanzu.”
“Kai amman naji dad’i Wallahi ya Yusuf Allah yakaimu.”
Shikuwa Farooq yana zaune yana kallon amaryar Sa wacce duk kallon da zai mata sai yaji wani abu a jikin shi.
Juyowa tayi tace
“Sannu da zuwa ya Farooq.”
“Yauwa sannu uwar gidana uwar ‘ya ‘ya na ya kike?
Ya kuma kad’aici.”
“Alhamdulillah
Ya office?”
“Alhamdulillah My Angle.”
Wannan kalamai na Farooq ne ya fara 6atawa Yusuf rai hakan ne yasa shi katseshi da cewa
“Abokina nifa yunwa nake ji muci na gudu nima gida na.”
Murmushi Farooq yayi yace
“To ai ga abinci a dining muje mana.”
Haka kuwa suka tashi suka nufi dining dan cin abinci amman ina Husna Sam ta kasa sakewa dan wani kallo Yusuf yake mata hakan ne yasata tashi tabar abinci.
Bayan sun kammala sun koma parlour in zauna Yusuf yace da Farooq
“To Abokina ni zan gudu amman dan Allah kar ka kusanci yarinyar nan Wallahi yanda na fahimceta har yanzu tsoro ne a ranta kagani dai ko abinci ta kasa ci.”
“Eh nima dai hakan nagani amman kasan bazai yu na zuba mata ido ina kallon ta ba, dole sai nayi abinda yake rai na.”
Mugun kallo ya masa sannan yace
“To naji ka k’irata kuzo Ku rakani zan wuce.”
Haka kuwa ya tashi yaje ya kirata suka rakashi bakin motar shi sannan suka dawo cikin gida.
Bai tsaya a ko inaba sai gidan shi,
ba laifi yau tayi wanka tayi kwalliya har da turare ta saka a gidan ta abinda rabonta da shi har ya manta.
Sallama yayi ya shiga kamar yanda yayi tsammanin a parlour ya sameta kwance akan three siter.
Amsa mishi tayi ya shiga
“Sannu uwar ‘yan jin dad’i ai daman nasan kina nan kwance.”
Turo mishi baki tayi tace
“Sai yanzu kadawo kasan inajin yunwa.”
Kallon ta yayi yace
“Wai ni bawan kine da zan dinga dafa miki kina ci to Wallahi Yau bazan dafa ba sai dai ki kwana da yunwa.”
Mik’ewa tayi da k’yar ta zauna tace
“Haba ya Yusuf kaima kasan bazan iya fad’awa ba kuma ko na daga bazan iya ci ba ko naci ma amarwa nake.”
“To Allah yasa kar ki iya ki zauna nikam bazan dafa ba” ya k’arasa maganar yana hayewa sama d’akin shi.
Ita kuwa cewa tayi
“Oho dai idan baka dafa ba zan iya badawa a siyomun.”
Haka kuwa tabawa Isyaku mai wanki da guga kud’i ya siyo mata tsire kasan cewar tanada yogurt a friez.
B’angaren Farooq kuwa hankalin shi gaba d’aya baya jikin shi yanda yau yaga Husna……..
ABOKIN MIJINA
*Page 6~10*
Yanda yaga Husna tana mishi wasu irin salo Wanda bai ta6a tsammanin ta iya irin su ba haka kuwa shima ya biye mata suka ci gaba da jin dad’in su.
Ringing d’in wayan shine ya dawo da su daga duniyar da suka tafi.
Ganin Number Yusuf ne yasashi d’auka da sauri ya kara a kunnen Sa.
“Hello Abokina bakayi barci ba” Yusuf ne ya tambaye Farooq.
“Eh Wallahi banyi ba amman dai lafiya ka k’irani cikin wannan daren?”
“Lafiya k’alau kawai dai na kiraka muyi hira idan amarya tayi barci.”
“Hira kuma nida inada mata kaima kanada me zaisa muyi hira bayan ga matan mu.”
“To sarkin iyayi ai cewa nayi idan sunyi barci ko kai naka har yanzu batayi ba?”
“Eh batayi ba sai nan gaba.”
“Kai dai kawai bakason muyi amman me zaisa Husna zama har yanzu batayi barci ba.”
“To shikenan tunda baka yarda ba to gatanan kaji muryan ta” ya k’arasa maganar yana mik’a mata wayar.
Wani dad’i ne ya lullu6e Yusuf daman abinda yake nema kenan gashi kuma ya samu.
Kar6an wayar tayi ta saka a kunnen ta badan ta so ba.
“Hello Yaya Yusuf baka yarda cewa banyi barci ba?” Ta tambaye shi.
Murmushi jin dad’i yayi yace
“Ina kuwa zan yarda bakiyi barci ba dan nasan wannan lokacin ba abinda zakiyi.”
“To shikenan sai da safe.” Ta kashe wayan.
Ba dan yasoba saboda yanzu a rayuwar shi ba abinda yake so kamar yaji muryan Husna.
Shi kuwa Farooq tsaki yaja yace
“Wallahi Yusuf ya cika matsala war yanzu zai kira mutum a waya kawai ya katsemun jin dad’i na” ya k’arasa maganar yana rungumo Husna.
“Husna dan Allah inason na miki tambaya ina fatan zaki bani amsa.”
Gyara kanta tayi wanda yake k’irjin Farooq sannan tace
“Ina jinka ya Farooq.”
“Husna meyesa kike tsoro na? Kike tsoron bani hakk’ina?”
Juyowa tayi ta kalli fuskan shi sannan tace
“Wanne irin tsoro Yaya?”
“Husna nasan tunda aka kawoki gidan nan kike tsoron had’a shinfid’a da ni shiyasa nima na barki har sai wannan tsoron ya fita amman kuma naga har yanzu banga kina buk’ata naba.”
Rufe fuskan ta tayi Alamun jin kunya sannan tace
“Aa Yaya kar kasa mala’ikun Allah su tsine mun.”
“Amman har yanzu baki bani amsa na ba.”
“Yaya Wallahi ba wani tsoron ka da nakeji ba, sai dai kasan duk wata mace dole sai tayi far gaban first night d’in ta.”
Murmushi yayi sannan yace
“To yanzu kin yarda da nayi abinda naga dama?”
Wani irin kunya ne ya lullu6e ta wanda ya sata tusa kanta tsakanin pilo.
To yanzu tashi muje muyi alwala mu gabatar da sallah raka’a biyu.
Bata amsa mishi ba sai ma kara danna kanta take ganin zata 6ata mishi lokaci ne ya d’auke ta zuwa bathroom.
Alwala sukayi sukazo suka gabatar da sallah sannan ya musu addu’a sosai tukun suka nufi gado.
Sai Yau Farooq yasan cewa yayi Aure sun faran tawa junan su sosai sai misalin k’arfe d’aya na dare Farooq ya barta.
Farooq ji yake kamar zai mayar da Husna ciki tsabar yanda yake jin k’aunarta yana k’ara shiga cikin zuciyar shi.
Yau Husna ta shayar da shi madarar soyayyar ta.
Ita kuwa Husna taji maza Wanda haka yasata narkewa sai faman kuke-kuke take na shagwa6a.
Toilet ya shiga ya had’a mata ruwa mai d’umi sannan ya dawo yace mata
“Heartbeat tashi na d’aukeki muje na miki wanka.”
Turo bikin ta tayi gaba tace
“Aa Yaya nima zan iya kabar shi kawai nayi.”
“Aa Heartbeat nasan kin wahala bazaki iyayi ba kibari kawai na miki.”
Kuka tasa mishi tace
“Yaya nace zan iya Wallahi zan iya kayi hak’uri nayi”……
” Aa Baby kar kiyi kuka dan Allah tashi ki shiga ina jiranki.”
Tashi tayi ta shiga
Tana shiga shi kuwa ya cire beshit d’in ya chanza wani sannan ya cire mata wasu sleeping dress masu d’an nauyi.
Fitowa tayi d’aure da towel da sauri ya k’araso inda take yana mata sannu yace mata
“Sannu Babyna zo muje na saka miki sleeping dress.”
Sake narkewa tayi tace mishi
“Ya Farooq jikina yana mun ciwo.”
“Ayya sorry Heartbeat ko zan kaiki hospital ne?”
“Aa basai munje hospital ba.”
“To ko nasake had’a miki ruwan zafin ne?
Shiyasa nace ni zan miki amman kika k’i.”
Bata mishi magana ba ta wuce.
A hankalin ta k’arasa bakin gadon ta zauna.
D’auko kayan yayi yasa mata ya kwantar da ita sai da ya tabbatar tayi barci sannan shima ya shiga toilet.
B’angaren Yusuf kuwa dad’i yake ji sosai dan kuwa ya tsorata Farooq ko ba komai burin shi zai cika.
Tashi yayi yaje d’akin Hafsat a zaune ya sameta tana chart hakan ne yabashi daman k’arasawa.
“Bakiyi barci bane?”
” Eh amman yanzu zan kwanta.”
“Daman in son na fad’a miki gobe insha Allah zamu tafi gidan Farooq zamuje mu wuni.”
“Gaskiya kuma fa ya kamata mu tafi gidan shi.”
“To sai ki shirya gobe 8:30 zamu tafi.”
“To Allah yakaimu goben.”
Washe gari Farroq shida kanshi ya shiga kitchen dan had’a musu breakfast.
Dankali ya soya musu da eggs sai kuma tea.
Bayan ya gama da yadawo d’akin se ya same zaune tasha kwalliya sai k’amshi take sha ga kuma kayan da ta saka sun bayyana suranta.
K’arasowa wajan ta yayi yana murmushi yace
“Heartbeat har kin warke kinsha irin wannan kwallayar gaskiya ya miki kyau.”
Wani irin fari da ido tayi wanda yake k’ara mata kyau sannan tace
“Na warke mana ya Farooq ko bakason na warke ne?” Ta tambaye shi.
“Aa na isa ai ni nafiki damuwa,
Yanzu ba wannan BA tashi muje dining muyi breakfast.”
Tashi sukayi suka nufi dining amman suna zama sukaji………..
“`Masoya littafin BARRISTER JANNART ina mai baku hakuri da jina shiru nayi niyan yimuku shi Yau amman kuma zazzabi ya hanani plz ina mai neman addu’ar ku“`
ABOKIN MIJINA*
*Page 11~15*
Sallaman su Yusuf sukaji daga k’ofar parlour dan su ko bude k’ofa basuyi ba.
Farooq ne yaje ya bud’e musu, ganin abokin shi da matar shine yasashi yin murmushi sannan yace
“Aa Abokina kaine da sassafan nan?”
“Eh nine ko bakason zuwan mu ne?”
“Aa bai kai ga haka Ku shigo sannun ku da zuwa.” Ya k’arasa maganar yana nuna musu hanya.
Hafsat ce ta kalli Farooq sannan tace
“Abokinka kad’ai Ka sani ko?”
“Aa k’anwata kiyi hak’uri ai dole na gaida ki.”
Gaba d’ayan su a parlour suka zaune itadai Husna badan ranta yaso ba saboda kwana biyun nan ta kasa gane me Yusuf yake nufi.
Farooq da Hafsat ne suka gaisa cikin mutun ci da girmama juna saboda it a Hafsat ta d’auki Farooq tamkar yayan ta.
Shikuwa Yusuf sai faman zuba ido yake nason yaga Husna amman ina bai ganta ba hakan ne yasa yace da Farooq
“Wai kai ina Amaryan ne ko har yanzu bata tashi a barci ba?”
“Aa ta tashi tana dining ko breakfast bamuyi ba.”
Ita kuwa Husna yanayin kayan jikin ta ne yahanata tashi hakan yasa ta koma gefe ta zauna.
Yusuf ne yace
“Yauwa nima haka yunwa nake ji kutashi muje mu karya.”
Haka kuwa suka tashi suka nufi dining.
Tsayawa yayi cak ko motsawa ya kasa sai faman lashe le6e yake kamar sabon maye ya zuba mata ido musamman yanda yaga na shanun ta sun kunburo a cikin k’aramin riganda ta saka.
Farooq ne yace
“Ya katsaya ne bazaka zauna ba.”
Sai a lokacin ya d’an motsa sannan yace
“Zan zauna Amarya me ta girka mana?”
“kai yau ba nata girkin bane nawa ne.”
“Kana nufin kaine kayi girki?”
“Eh nine wani abune?”
“Aa ba komai kawai dai naga ga Amarya ne.”
“Kai kabari kawai yau Heartbeat d’ina batajin dad’i.”
Wani wawan juyowa yayi ya kalli Farooq sannan tace
“Me yake damunta.”
“Zan fad’a maka amman ba yanzu ba muci abincin mu kawai.”
Ita dai Husna batada bakin magana saboda duk wani iri take jinta.
“Ya Farooq” ta furta a hankali.
Matsowa yayi kusa da ita yace
“Na’am my Angle.”
“Dan Allah kabani hijabi na a d’aki.”
Sai a lokacin shima ya gane abinda yasa taki sakin jiki bare tayi magana.
Da sauri ya mik’e ya shiga d’aki ya d’auko mata k’aton hijabi har kasa ya bata ta saka.
Sai a.lokacin tace
“Sannun ku da zuwa Anty Hafsat.”
“Yauwa sannu Amarya ya kike?
Ya Amarci?”
Cikin jin kunya tace
“Lafiya k’alau
Alhamdulillah.”
“To ni kuma baza’a gaidani ba?”Yusuf ne yayi magana.
Murmushi tayi tace
“Aa wallahi Ya Yusuf zan gaida Ka
Ina kwana.”
“Sai da na rok’a za’a gaidani banaso.”
Farooq ne yace “to yanzu dai muci abinci ba wai surutu ba.”
Haka kuwa sukaci abincin su duk da Husna ba dad’in cin abincin take ba saboda Yusuf ya zuba mata ido duk motsin da zatayi.
Bayan sun kammala parlour suka koma suka zauna shi kuwa Farooq zan Husna yayi tace suje ya chanza mata kaya.
Kusan 30 minutes sukayi wajen chanza kaya wanda duk ya dami Yusuf ji yake kamar ya bisu yaga me sukeyi.
Sanye take da wata atamfa me d’an green a jiki Wanda ya mata kyau sosai duk da ba wani kwalliya tayi ba,
Rike suke da hannun junan su kana ganin su sai sun baka sha’awa.
Farooq kenan da matar shi Husna.
Wani bak’in kishi ne ya bige Yusuf wanda yasa zuciyar shi bugawa da k’arfi amman sai ya danne yace
“Wai kai Farooq bakajin kunya ne dan Allah?
Kana gani a gaban mu zaka rik’e mata hannu kuna tafiya.”
Cikin mamaki Farooq yace
“Haba Abokina wannan fa Matata ce ko kamanta lokacin da Ka auri Hafsat a gabana kake d’aukanta dan ni na rik’e hannun ta shine rashin kunya.”
“To naji kayi hak’uri kazo Ka zauna muyi hira.”
“To tashi muje parlour na yau akwai labari.”
Wani kallo ya mishi sannan yace
“Dan meye sa bakason mu zauna anan tare da matan mu?”
“Kai dalla cewa nayi zan baka labari kuma banson suji.”
“To shikenan muje.”
Haka kuwa suka tashi suka wuce parlour Farooq.
“To inajin Ka menene labarin?”
“Abokina jiya na kusanci Husna nasan wacece ita kuma nima na samu lafiya Alhamdulillah.”
Tunda Farooq ya fara magana YusufYa shiga cikin wani hali wanda shi kanshi baisan dalili ba.
Sai kuma yace
“Haba Farooq dan meyesa Ka kusanci yarinyar nan a yanzu?”
Cikin mamaki Farooq yace “kamar yah ban gane ba?”
“Ina nufin ai dakabari sai zuwa wani lokaci.”
Add Comment