Nahuce Part 4 Hausa Novel Complete
Nahuce Part 4 Hausa Novel Complete
Ga dai kiran ya shiga, ga wayar tana ta ruri, amma sai ta nemi dukkan karfin gwuiwar da ta tattara take tinkaho da shi na jin cewa zata iya tarar sa gaba da gaba ta rasa, ta nemi kalaman data harhada a fatar bakin ta don yin magana da Nahuche ta rasa, ta nemi boldness din da jajirtacciyar ego din ta suma ta rasa…. A lokacin da ta ji calm, cool muryan nan ta Habibu Nahuche cikin kunnuwan ta tana kwarara mata sallama, kamar wanda dama ya ke jiran kiran nata ya amsa impatiently,
“Hello, Ma’am, ina kan layin!”.
Duk sai ta kara daburcewa ta rikice gabadaya.
Ya ya san cewa ita ce ta kira shi?
A ka’idar sa bai amsa kiran da bai san ko na waye ba, amma already ya san Rahinah zata kira, psyche din sa ya dade da bashi zata kira din, da wacce fuskar zata kira ne bai sani ba; da tsiya ko da arziki.
Don haka tuntuni Habibu yana jiran kiran nata ne, shi ya sa yaki yin barci, yayi mamaki ma da ta kai har sha biyun dare bata kira ba, a yadda ya san ta da wutar ciki a kan Dan ta, ya san yadda ya kasa barci itama yau bazata iya ba, watakila har gara shi, tunda yana makale da dan sa rabin ran sa a gefe abin debe masa kewa (apple of his eyes), ya fi kyautata zaton kiran nata bana arziki zai kasance ba, kuma ya shirya mata da duk irin wacce ta zo masa.
Zakisan Koni Waye Hausa Novel Complete
Shi yasa koda ya ga bakuwar lambar da aka nuna daga cikin Kaduna kiran yake ya san cewa; ita ce. Dr. Rahinah Omar Girei. Don haka bai yi nawa ba wajen dagawa a ginshire, ya amsa a kagauce. Yana magana a kasaice.
He is expecting her rigimammen call a daidai wannan lokacin orbefore. Jin dadin sa daya Junior ya yi barci. Zai ji dadin caccaba mata Magana yadda yake so.
Bayan ya sha jerin tambayoyi masu dimbin yawa daga wayayyen yaron nasa mai kaifin basira da wayayyen kai, da kalaman da suka bashi mamaki, akan BAKUWAR FUSKAR da ya gani ta gidan Mummy Badiya a yau, wadda ta biyo su har gurin mota.
Abdallah ya ce da Habib bayan ya fito daga wankan da ya sa shi dazu, yana goge sumar kan sa da karamin tawul.
“I just like her Daddy, and i don’t know why I admire her from the first glance….. (Kawai na ji ina son ta, ban san kuma me yasa nake son nata ba, daga sanda na fara ganin ta, ta kwanta min a rai Daddy).
Wacece ita? A ina take? She’s beautiful. Ina so in koma gidan Mummy don in kara ganin ta”.
A wannan lokacin Habibu rasa amsar da zai baiwa Abdallah yayi, sabida ya san howsmart yaron nasa is, sai ya yi taka-tsan-tsan kwarai wajen gaya masa ko wacece Rahinah gare shi, dole ya bashi gamsashshen bayani, son samu ya gaya masa abinda zai dakusar da tasirin data samu haka nan da nan a ran sa, don kalaman da yaron ya yi amfani da su a kan ta sun bashi mamaki matuka, kasancewar sa wanda bai son bakin fuska bai kuma sakin jiki da su sam.
Sai ya shiga shafa kan yaron cikin wani hali na tausayin kai, tare da da tasowar wata irin KEWAR Rahinah Omar, ya samu kan sa cikin wani hali na kaka-ni-kayin SO mai wahalar da zuciya, da kuma bakuntar wadannan tsofaffin feelings dinnan da yake dasu tuntuni a kan ta, a dalilin ganin da yayi mata yau; (she’s more beautiful and looking more ravishing than ever before).
A baya ya dauka ya dade da rasa sha’awar sa ta Da namiji a kan mace, tun daga kan ta, ya dade da rasa mazantakar sa a kan rashin Rahinah Omar, kudi kawai yake nema sune kadai bukatar sa a rayuwa. Har sai yau da ya ga RahinahOmardin ganin idon sa…Ya ji muryar ta jin kunnen sa…. Ya gan ta more mature, more ravishing and more sexy than before.
Sai komai ya dawo masa sabo fil, ya ji shi ya koma yaro matashi danye mai tashen balaga da tashen kuruciyar nan, wannan Habibun dan kimanin shekaru ashirin da tara ba arba’in din da yake da su a yanzu ba, wato lokacin da ya fara ganin Rahinah a Jamus. Wani abu mai kama da tsoro kuma ya zo ya darsu a ran sa a dalilin maganganun yaron a kan Uwar sa.
Daga bisani ya ga bashi da mafita, domin Abdallah ya tsatstsare shi da Almondshapedidanun nan nasa irin na uwar sa, wadanda ke tado masa da tsofaffin abubuwa da ya riga ya manta da su, suka shude tun wani karni can da ya shude, amsar sa kawai Abdallah yake son ji. Sai yalumshe ido na tsayin lokaci kafin ya bude su a kan Abdallah ya ce.
“Ka yi hakuri sai gobe Abdallah, zan gaya maka ko wacece ita, amma in ka yi min alkawarin duk runtsi; ni zaka zaba a kan ta!”.
Cikin mamaki yaron ya kalli mahaifin nasa da kyawawan idanun sa sak na Rahinah, in da abinda Abdallah ya dauko a jikin ta guda daya kwakkwara, to kwantattun idanun ta ne masu gazar-gazar eye-lashes, har sai da Habibu ya ji wani irin abu ya tsirga a zuciyar sa da ruhin sa a dalilin kallon da Abdallah ya yi masa, domin exactly irin kallon da Rahinah Omar ta yi masa dazu ne yaron yayi yanzu. Wato kallon tuhuma, amma na Abdallah mai cakudeda kauna irin ta Da da mahaifi.
Sai ya tuna idanun ta dake kallon su dazun,a bakin kofar shiga falon gidan Uncle Usman,cikin ragaita da rashin sanin abin yi….. gani ya ke kamar Abdallah zai zabi Rahinah ya bar shi in ya ji ko wacece ita a gare shi, shine abinda ya ke tsoro, to gashi ya ce yana son ta (from the first glance) ba tare da ya san ko wacece ita ba, ina ga ya ce masa ita ce ta yi nakudar sa?
Shi kuma yaron sai ya russunar da kwayar idon sa kasa, bai ce komai ba.
Bai ce komi bane saboda bai fahimci dalilin Baban sa na cewa hakan ba. Amma duk da kasancewar sa yaro to fa ya digawa maganar Baban sa a kan bakuwar matar nan katotuwar ayar tambaya….cewa da Baban nasa ya yi,
”….in ka yi alkawarin ni za ka zaba ba ita ba!”.
A haka Habibu ya samu yayi barci, ya karanta addu’ar barci ya shafe shi sosai, lokacin ne kiran Rahinah ya shigo masa.
“Hello!”
Habibu ya sake fada, wannan karon da kwantar da murya, jin tana numfarfashi kawai cikin bala’i ta kasa cewa komai. Ta rasa ta ina za ta fara. A yadda ya san ta da ego da boldness, bai zaci zata kasa voicingout maganarda ke cike a bakin ta ba. Wata irin mace ce mai tsayayyar zuciya.
“In ba kira bane please zan ajiye in kwanta, ina da sammako gobe da safe” ya fada da harshenGerman. Maimakon Hausa ko Ingilishi. (German Language) shine harshena biyu da ya san Rahinah ta fi sabawa da shi. Wannan ya tada tsigogin jikin Rahinah, wani abu yamm! Kamar tashin tsigar jiki ya soma bin tafin kafar ta, sakamakon tuna baya. (The way he kept on…. raping her daily a tsayin KWANAKI BAKWAI kamar ya samu kuyanga) ya dawo sharr! A zuciyar ta da yayi magana da harshen German. A wancan lokacin duk sanda ya kusance ta da harshen Jamusanci yake mata sambatu. Zuciyar ta ta tuna mata ko waye Habibu, don haka kada ta bari kwantar da muryar sa ya kassara ta ta fasa kudirin ta na kwatar Dan ta, zaluncin sa ya fi da haka.
Ba’a kidnapping Da kawai ya kware ba, har da kidnapping zuciya da ruhin diya macen duk da ta yi hadarin fadawa hanyar sa.
Da wannan tunanin, Rahinah Omar ta kwarara kan ta, ta hanyar tattaro dukkan kuzarin ta da karfin zuciyar da ya rage mata. Hankalin ta da nutsuwar ta ta hada su wuri guda ta dunkule su cikin tafin hannun ta, ta sani kwarai cewa da babban mutum take magana a yanzu, mai amsa taken (Young Nigerian Hotelier) wanda ya kama kasa, ya ajiye Naira da kwalayen boko, ba dan saurayin dalibin nan na ‘Cologne University’ da ta sani ba. Don haka dole ta yi taka tsan-tsan. Ta kuma iya takunta.
“Kana magana da Rahinah Omar!”.
“I’m aware”. (Wato ya sani)
In ji Habib kamar cikin rada, muryar sa na nuna halin ko in kula.
A ran sa ya ce “the happiness destroyer, the cruel lady in action, and also a heart breaker (mai tarwatsa farin ciki, muguwar mace mara tausayi ma’abociyar karya zuciya)!”. Rahinah ta hadiye bacin ran ta, tana kara baiwa zuciyar ta hakuri. Ita ke nema a wajen sa dole ya wulakanta ta yadda ya ga dama.
Zata shanye komai in dai eventually zai bata Dan ta, gudan ran ta Abdallah ta tafi da shi gidan ta a Abuja. Ta sanya shi makaranta, su kwana gado daya suna hira, tana koya masa karatun Alqur’ani daga kwance. Me zai fi wannan moment din dadi a zuciyar uwa? Ba abinda zai kara gama su ko a hanya (bayan ta karbe Abdallah) balle yayi mata wulakancin sa da ya gada nau’i-nau’i.
“Ba Hotel nake so a bani in sauka ba Yallabai, balle a zaci bara ce ko maula suka kawo ni. I don’t care ka gane mai magana ko a’ah?
Da na, Abdallah, wanda na haifa a kasar Jamus ba tare da taimakon kowa ba, wanda aka bi dare aka dauke mini, nake so a bani yanzu, kamar yadda Shari’ah ta bani, cikin aminci da salama, ba tare da mun taba mutuncin juna ba ko wani thirdparty ya shiga.
In ya so idan ya balaga sai ya zabi wanda zai zauna da shi tsakanin ni da kai din, tunda haka shari’ah ta tanadar mana”.
“Allah ko?”
Habibu ya tambaya cikin izgili da shagube. Kai har da tsagwaron raini. Kafin ya ce.
“Baki san hanyar kotu bane da zaki neme ni da salamar in baki Dan ki? Na dauka komai bisa doka da doron shari’ahr yafi bada ma’ana? Ai Dr. Rahane kike ko wa? Ba Otorlaryngologist ba ko shugabar likitocin Najeriya da Jamus aka baki kin yi kadan ki karbi yaron nan daga hannun Uban sa. Muguwa kawai, azzaluma!!!”.
Yana fadin haka ya kashe wayar sa. Ya cusa kan sa a karkashin filon da yake kwance a kai, zuciyar sa na hankoro a cikin kirjin sa kamar zata fito ta bakin sa.
Sabuwar soyayya ta zo ta lullube shi, tamkar numfashin sa zai bar gangar jikin sa. Tamkar ruhin sa zai bar cikin numfashin sa.
Ko me ya tuna? Sai ya dago kan sa daga karkashin filon, idanun sa sun kada sun rine, gara a ce hawaye yake da launin da suka koma. Ya dauki wayar sa ya rubuta sako (text) ya turawa lambar data kira shi yanzu.
“Delete my number from your phone Rahinah, don’t ever attempt to call me again, daga ni har Abdallah we don’t need you in our lives anymore!”.
(Ki goge lambata daga wayar ki Rahinah, kada ki kara kokarin kira na, daga ni har Abdallah bama bukatar ki cikin rayuwar mu ko kadan).
Yana tura sakon ya goge lambar da sakon bakidaya.
(Saidai ashe ya goge lambar ne a kan fuskar wayar sa kadai, amma tuni kakkaifar kwakwalwar sa ta haddace lambar Rahinah Omar ba tareda yin shawara da shi ba, kamar yadda ya haddace karatun sallah a cikin kwanyar sa).
Da asubahin washegari ta gan shi at a smart pace (afujajan) babu ko wankan safe ta san wani muhimmin al’amari ya taba zuciya da ruhin Habibullahin ta. Tabawar da aka dade ba’a yi masa irin ta ba. Habibullahin ta dan gayu da kwalisa yau babu ko wanka ya kamo hanya. Idanun sa sun yi luhu-luhu na rashin barcin daren jiya, sun kada sun yi jajir dasu.
Ilai kuwa suna gaisawa abin da Habibu ya fara fadi shi ne.
“Hajiya, ga Abdallah nan na kawo miki shi ya yi miki sallama, zan kai shi makarantar kwana a duk garin da Allah ya nufa”.
Da jin haka Abdallah ya dago da sauri, nan da nan ya soma turjiya yana shura kafa irin na ‘ya’yan gata shagwababbu “…ni gaskiya Daddy ban yarda ba, bana son boardingschool, wallahi bana so, ni wajen Mummy zan koma gun su Yaya Musaddiq, kuma na ce maka zan koma in ga wannan balarabiyar matar baka maida ni ba”.
Bai san sanda ya kai ma Abdallah duka ba, ji kake gab! Ya gabje masa baki, dama zuciyar a kusa take. Hajiya ta yi maza ta tare dukan don ya sauka a nata hannun amma tuni ya samu Abdallah, bakin sa saura kadan ya fashe. Habibu ya hau fada kamar ba shi ba, ta inda yak e shiga ba ta nna yake cfita ba.
Hajiya ta manta yaushe rabon da ta ji Habibu ya daga muryar sa irin haka, (he is always calm, cool and smart) amma yau ya ma manta da Hajiyar sa yake magana.
“daga yau kada a kara kai shi gidan Yaya Badiya, na hana daga yau, in dai don makaranta ne zan nemi boardingschool da ta dace da shi in kai shi goben nan, amma ya gama zuwa Kaduna, yagama har abada ba zai kuma zuwa ba”.
Hajiya da sakakken baki ta ke kallon sa.
“Kan ka daya kuwa Habibullahi? Me Badiyar ta yi maka haka da zafi? Allah dai ya sa ba shaye-shayen zamani kuma ka fara ba”
Mikewa ya yi yana balle links din hannun rigar sa yadda zai ji dadin yin alwala yayi sallahn nafila ko zuciyar sa ta lafa daga tafarfasar da take yi masa, wanda ba kowa ya janyo ba sai RAHEENAH OMAR, haka kawai -kawai yana rayuwar sa lafiya ta dawo ta hargitsa shi, ba tare da ya baiwa Hajiya Kaltume amsa ba, ya sa kai ya fita daga dakin.
Duk wanda ya yi wa Habibu Nahuche farin sani kamar Badiyya da Hajiyar sa, kallo daya za su yi masa su gane daga jiya zuwa yau har wata ‘yar kwarya-kwaryar rama ya yi, sabida damuwa da azabar tasowar soyayyah, ramar da ganin Rahinah Omar ce ta haifar, ya kuma tada tsohon tsumi da tsohon miki wadanda suka dade da warkewa don haka a yanzu bai san ya ya zai yi da su ba.
Haka Hajiya Kaltume ta rabu da shi ya yi alwala shi ma Abdallah ya yi, don ya tsorata sosai da dukan da Daddyn ya kai masa, wanda wani abu ne da bai taba faruwa ba sai yau, don haka sosai ya shiga taitayin sa, suka tafi masallacin gidan tare (wanda shi ya gina wa al’ummar unguwar) don samun jam’i.
Kuma har suka je masallaci suka dawo suka zauna shi da Hajiya suna sallama bai gaya mata maqasudin dalilin sa na rabo dan sa da gidan Badiya ba, Badiyar da ta zame wa yaron UWA a lokacin da yake tsananin bukatar kulawar Uwa. Hajiya Kaltume ta dube shi sosai, alal hakika a matsayin ta na uwar sa, ba ta taba ganin Habibullahin cikin kwatankwacin irin wannan birkitaccen yanayin ba.
“Ka ki gaya min me ya faru? Laifin me Badiyar ta yi muku da za ka ce haka? In duniya da amana har kana iya nuna wa Badiya iko a kan Abdallahi? In da alkawari ruwa ba zai dafa kifi ba”.
Hajiya ta fada da sanyin murya.
Habibu ya yi kasa da ido, cikin kasalalliyar murya ya ce, “In tana son ganin shi ta zo nan ko ta je Lagos ta gan shi, amma na raba shi da gidan ta daga yau. Ra’ayi na ne kawai hakan Hajiyar mu, ba don sun mana wani laifi ba, ita ko maigidan ta alkhairi ne kawai tsakani na da su. Allah ne kuma zai biya su alkhairin su ga Abdallah ba ni ba”.
Hajiya ta yi masa kallon, ”to ba ka isa ba”, sannan ta gyada kai ta ci gaba da jan carbin ta. Daga haka ba ta kara ce masa komai ba, don ita duk abin da zai raba kan ‘ya’yan ta biyun nan (Badiya da Habibu) da Allah ya ba ta tana neman tsari da shi.
Ba ta fatan ‘ya’ya su raba wannan kyakkyawan zumuncin na Habibu da Yayar sa Badiya har bayan ran ta. So take su rungume juna ’ya’yan su su dunkule su zama abu guda. Allah SWA ya yi gaskiya da ya ce (’ya’ya da dukiya fitina ne).
Bazata zuba ido ’ya’ya su yi sanadin wannan zumuncin ba.
Washegari suka wuce Lagos a jirgin sama da zummar zai je ya yi masa cuku-cukun samun gurbi a (British International School) da ke Lagos. Gara shima ya hakura da ganin Abdallahn, da dai RAHINAHOMAR ta samu access din sake ganin sa!
******
DR. RAHEENAH OMAR
A
can Kaduna kuma ko kafin jama’ar gidan su tashi daga barci Rahinah ta kama hanyar Abuja a washegari. Ita kadai cikin motar ta kiapicanto, sai sharara gudu take yi kamar zata tashi sama, don tsabar rashin nutsuwa a can ta baro Baba Sahura ta manta ma tare suke. Hukuncin Allah ne kawai da kiyayewar sa ya kawo ta Abuja lafiya amma ba nutsuwar tuki ba.
Tana shiga Abuja gidan ta ta nufa, cikin gidajen likitoci na ’National Hospital’, ta shige ta kulle kan ta. Ta kuma kashe dukkan wayoyin ta.
Nutsuwa ta ke so ta samu ko ya ya ne, kafin ta yanke shawarar abun yi, amma nutsuwar ta ki zuwar mata sama ko kasa.
Ta kwanta rigingine tsakiyar lallausar gadon ta da niyyar ta yi barci, ko ta samu rangwame, amma barcin ya ki zuwa shima. Gabadaya jin kanta ta ke wani irin a birkice, upset, kuma upside-down. Ko ta ki ko ta so, kuma hakan na da nasaba ne da muggan kalaman dan mutanen Nahuche a wayar da suka yi jiya, bayan wucewar shekaru goma.
To dama ita soyayya tana rikidewa ne farat daya ta koma kiyayya? A sanin ta har suka rabu bin ta yake da kokon barar SO. Yaushe wsannan son ya rikide zuwa kiyayya? Itace dai bata da tabbaci akan tata zuciyar, amma kalaman sa sun sa ta gano da gaske ba ya bukatar tata, amma ita tana da bukatar tasu (Uban da Dan sa) in su basa bukatar ta (kamar yadda yace).
Sai dai kuma ko da bukatarta ta dawowar su cikin rayuwar ta ita ce zata yi ajalin ta… a haka zasu kare wutsiya a zage. This self-esteem da yayi takingfor granted a baya, yanzu ta fara maintaining din sa.
Ta tuno sunan da Habibu Nahuche ya kira ta da su a karshe,
“…..Muguwa-Azzaluma!!!”.
Rahinah kamar tayi hauka, kalaman sun rikita ta, ita kadai a uwardaki sai kai da komo take kamarf zararriya tana tambayar kan ta,
“da gaske ni muguwa ce? Azzaluma ce ni? Me na yi masa na zalunci? Me na yi masa na mugun ta? Ni ban kira shi da duka wadannnan sunayen ba sai shi zai kira ni da su?
A wurin ta mata suna sarayar da ESTEEM din su akan ’ya’ya da SOYAYYAH su bari maza su taka su son rai, su keta alfarmar su. Su danne ’yancin su da hakkokin su da addini ya basu. Hujjar su da taqamar su shine zasu zauna sabida ’ya’yan su. Annabi SAW mai girmama matan sa ne da mutunta bukatun su, mai nuna musu soyayya ne, ya yi umarni ga mazan aure kada su zowa matan su ba tare da dan aike ba, kada su aure su bisa tursasawa, ya yi umarni da fahimtar juna kafin aure.
Wadannan su ne hujjojin ta na kin barin soyayyar Habibu ta yi galaba a kan ta, amma ba don bata son shi ko ba ta son Dan su ba. Ta fara son shi immediately bayan rabuwar su, ta yadda har ta dinga bibiyar al’amarin shi, amma sai bata dauki soyayyar matsayin priority ba sama da goalattainment.
A yanzu all her dreams have come true. The goals are well achieved and properly actualized. Abu biyu ya rage mata yanzu a rayuwa; soyayyar miji da soyayyar Dan ta (family life).
“Dole in yi amfani da kuduri na na biyu, da na ki da na so, in ba haka ba HABIB NAHUCHE zai sha ni basillah! Bazai bani Dana ba, sannan na cigaba da bin sa ta lalama zai cigaba ne da wulakanta ni ne da bata min lokaci.
Rahinah ta shigo garin Abuja ne daga Kaduna absent-minded don haka ta manta cewa ita ma’aikaciya ce da za a iya nema a kowanne lokaci, amma ta kulle kanta ta kulle wayoyi. Ta manta tana zuwa aiki kullum. Halin da ta ke ciki ya danne komai. Ita kadai ta ke suffering a zuciya da ruhi, ba tare da Habibu Nahuce ya san tana yi ba.
A lokacin shi da Abdallah suna gidan sa dake Ikoyi. Har ya fara registration din makarantar Abdallah.
Daga wannan ranar, daga wannan lokacin daga Habibu har Rahinah babu wanda ya kara nutsuwa, babu wanda ya kara samun sukunin zuciyar sa, (they are internally suffering with concurrent love, hatred, and emotional torture). Habibu ya shiga tafka shirme a wajen aiki bisa rashin sani, haka a takardu muhimmai sai ya yi ta kuskure ana ankarar da shi.
Wannan ne yasa PA din sa na Lagos, Rasak, wanda bayerabe ne ya karbi komai daga hannun sa ya dauki hutu na tsayin sati uku.
Maimakon ya zauna a gidan sa na Ikoyi bayan ya kai yaron makaranta sai ya tafi NAHUCHE HOTEL, LAGOS, ya kama (Excutive VIP room). Ita kuma daga baya Dr. Irshad ya ba tahutudon ta gaya masa bazata iya aiki ba awannan dan tsakanin tunda ta san rayukan mutane ne hannun ta a NIZAMIYE kasancewar shi da kan sa yafahimci ba daidai ta ke ba a satin nan. Ta gaya masa tana neman wanda zai shige mata gaba on a legal issue zata maka wani kotu!
Dr. Irshad ya dauka wasa take yi sai ranar da ta kira shi a waya ta roki alfarmar ya zo ya dauke ta a ‘Federal High Court’ baza ta iya tuki ba, tana fama da ciwon kan barin kai guda (migraine).
Dr. Irshad ya dauko ta daga kotu zuwa asibiti ba tare da ya san abinda ta je ta yi ba, a hanyar su ta dawowa Rahinah tace ta bashi dama idan har yanzu yana son auren ta ya turo wajen iyayen ta.
Dr. Irshad dai ya san Dr. Rahina ba daidai take ba a satin gabadaya, wannan amsawar da ta yi masa ma ta farat daya bai gane mata ba, tana magana idon ta a rufe kamar mai ciwon baki, butkoma dai menene matsalar ta he will not miss this golden chance (wannan kyakkyawar damar data bashi wadda ya dade yana jira), yace insha Allah cikin satin nan zai turo magabatan sa daga Yemen.
Ita kadai cikin gida kamar sabon kamu, gabadaya ta birkice. Gashi dai ta ce da Irshad ya turo, amma duk da haka ta kasa nutsuwa, Habibu Nahuche ya kusa haukatata da mere kalaman bakin sa, wadanda basu fi kalma biyu ba.
“Muguwa-kawai-azzaluma!”, sune kalaman da ke haunting din ta.
Gashi ta baro Sahura a Kaduna. Da ta ga za ta mutu ita kadai a cikin gida don ko abinci ba ta iya girkawa sai dai ta sha madara, da dan abin da yake cikin firjin gefen gadon ta, sai ta tattara inata-inata ta nufi gidan su Nene.
Don ma kada kadaici ya sake tambayar ta wane ne Habibu Nahuche? Ko ya tuna mata kalaman bakin sa. Sai ta ki sauka a dakin ta na gidan kamar yadda ta saba, ta sauka a dakin Yafendo. Ta tabbata duk runtsi tsohuwa Yafendo ba za ta barta da damuwa da kadaici ba.
Ai kuwa Yafendo ta shiga hidima da kawar ta likita Rahin (yadda ta ke kiran ta) ta tashi musamman ta yi mata burabuskon shinkafa da miyar taushe tana cewa,
“Mutumiyar Rama, ko a jika rama ne?”
Ta yi dan murmushi ta ce, “Komai ma na samu zan ci Yafendo, kwana na hudu kenan ban ci dafaffen abinci ba”.
Yafendo ta kama haba, ta ce.
“Kwana hudu? To a dalilin me? Haba, ni fa na ga duk kin yi wani zuru-zuru, firgai-firgai da ke”.
Ba ta bai wa Yafendo amsa ba ta mike tana rage nauyin kayan jikin ta. Laffaya koriya sharr da ta ji adon pinkflowers. Amma da zata iya da ta gayawa Yafendo cewa; A dalilin HABEEBUN su, a dalilin dan mutanen NAHUCHE, ba zuru-zuru firgai-firgai ba har dan karamin hauka ta tabbata ta san ya same ta a tsayin satin nan bakidayan sa, tunda kuwa an dakatar da ita daga ayyukan ta na fidar kunne, hanci da makogaro wanda tafi kowa kwarewa a kai a garin Abuja don shugaban ta ya gane ta fara zautuwa.
*******
[10/08, 4:37 pm] Ummah Salisu: SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870
*HABIBU NAHUCHE*
Ya bai wa kan sa hutu ne domin ya gama fahimtar a hargitse yake, ci gaba da ayyukan sa a wannan halin da ya ke ciki ba abin da zai haifar sai tarin nakasu da koma baya cikin harkokin kasuwancin sa. Domin hatta lissafi kowa da ke tare da shi ya san ya daina yin sa daidai.
Ya dauka komai nata ya tafi, tafiyar da babu dawowa, ya dauka ya riga ya binne ta a zuciyar sa ba don ta mutu ba, sai don ta gama taka rawar ta a rayuwar sa, ya dauka komai nata ya zama bygone? Tunda bai hana shi progressing ba. Amma ashe likimo ta yi wa zuciyar sa mai kama da kwanton Bauna!
Daga lokacin da idanun sa suka shiga cikin those innocent fulani eyes din na Rahinah Omar, komai ya dawo masa sabo fil. Wai kunama ta harbi gyambo.
In ma ya ce har da kari ba zai yi karya ba. Yanzu ya gan ta ne a matsayin cikakkiyar mace (matured young lady in her late twenties fiye da yadda ta ke a baya. Yanzu ne ta ke amsa sunan mace sosai, ta ke amsa sunan (Dr. Rahinah Omar Girei Otorhinolaryngologist) ba ‘yar yarinya budurwa mai tsananin kyau da ya sani a Jamus, mai amsa sunan Rahinah Omar ba.
Wannan kyan na yanzu hade yake da sanin ciwon kai, matured mind, contentment of life.
A halin yanzu ka ganta tsammani za ka yi balarabiyar kasar Oman ce sabida yadda fatar jikinta ke glittering.
Dr. Irshad bai iya boye hakan a ran sa, a duk lokacin da ya ga Rahinah ko wani aiki ya kawo ta ofishin sa sai ya fada kasa-kasa cewa, ‘Looking Ravishing’.
A duk sanda ya fadi hakan ita kuma za ta yi kicin-kicin da fuska, don duk namijin da ya yabe ta haushi yake ba ta.
Habibu Nahuche has never praised her beauty, watakila bai ma san ya ake gaya wa mace abin da zai dadada mata rai ba. Yet shi kadai yake burge ta, shi kadai ta ke so ta ji ya yabi wani abu nata. Unfortunately bai taba ba, sunan ta “muguwa-azzaluma” a bakin sa.
Watakila wadannan muggan kalaman nasa da suka haukata ta a kwanakin nan, su za su cigaba da birkitata suna farautar farin cikin ta da nutsuwar ta har zuwa ranar da ta daina numfashi.
*******
Duk da bai san wace irin alaka ce tsakanin ta da su Uncle Usman ba, ya fahimci alaka ce ta kusa ba ta nesa ba.
Maimakon ya samu hutu kamar yadda yake bukata cikin ’Nahuche Hotel’ na garin Ikko, tun bayan da ya sada Abdallah da ‘Boarding School’ don ma kada Rahinah ta samu access din sake ganin sa, sai kadaicin ya bankado wa zuciyar sa tsohon kundi da tsohon miki na rayuwar KWANAKI BAKWAI a birnin Cologne din JAMUS.
Rayuwar da har yau bai kara maimaitawa ba, bai kara samun kwatankwacin ta a gardi ba, bai kara attemptingdin ta da kowacce ’ya mace ba tsayin shekaru goma, wato rayuwar auratayyah! For she left no space in him. Ta mamaye ko’ina na zuciyar sa.
Ya rike kan sa ta duk hanyar da addini yayi umarni, ta hanyar maida kan sa busy kullum, da neman kudi da azumin tadawwu’i don kada ya tuna ta. Don kada ya nemi mata. Ya sani ba irin mummunan zargin da duniya bata yi masa akan rashin aure.
Idan ya ce yana sufferinginternally a cikin wannan dan tsakanin, ya yi kadan ya bayyana irin halin da ya samu kan sa. Ganin ta ya tuna masa cewa shima NAMIJI ne mai lafiyar bukatar aure, don a baya ya dauka ya dade da komawa mace. Sabida kowacce macen kallon mata-maza yake mata sai ko yau da ya ga RahinahOmar ganin idanun sa, ya kuma ji muryar ta jin kunnen sa…
******
*ASHE RAHINAH BAKI SAN GATSE BA?*
Mr. Atiku wato PA din sa na Abuja ne ya kira shi, da bai same shi ba, sai ya kira PA din Lagos. Rasak. Cikin tashin hankali yake gaya masa ya hada shi da Oga, itisurgent. Shi kuma yace masa Oga fa ba ya amsa waya currently, yana hutu a Hotel, ajiyar zuciya PA din Abuja ya yi, yace.
“Sai ka gaya masa hutu bai gan shi ba, an turo masa da SAMMACI daga Federal High Court, Abuja, kuma zance har ya bullawa media.
He has to be in Abuja today or tomorrow a kashe zancen nan kafin ‘Daily Trust’ su shigar da jaridar da zasu fitar jibi zuwa yanar gizon su, ko su fara sayar da ita a kan takarda.
Ban san wa ya kai musu zancen ba kuma ban san wa ya yi karar sa ba. Amma hakika a kan yaron sa ne, Abdallah. Har suna questioninglegitimacy din sa dalilin hakan. Ana neman sa nan da kwana uku a kotu!”.
Jeremy da ke kula da abincin sa shi ya shigo masa da jaridar yau da ya sayo tare da lunch din sa. PA dinsa ne ya ce ya kai masa jaridar tare da abincin rana, tunda sun yi-sun yi da shi akan ya daga waya don su gaya masa yayi wani abu kafin ’Daily Trust’ su saki labarin, amma ko damar ganin sa bai basu ba balle ya san abinda ke faruwa.
Headline na jaridar Sabuwar Najeriya (NEW NIGERIA) dauke ya ke da kanun labaru kamar haka…..
“NAHUCHE’S EX-WIFE DRAGS HIM TO COURT, ACCUSES HIM OF INJUSTICE ON THEIR CHILD’S CUSTODY….DR. RAHINAH OMAR OF NIZAMIYE APPEALS THE COURT FOR JUSTICE…
Yayin da Headline na ‘Daily Trust’ ya ce.
“IS ABDALLAH NAHUCHE A LEGITIMATE CHILD???”
A cikin kanun labaran kuma an yi bayanin zuwan sa Germany karatu, tare da dawowa da yayi tare da karamin yaron, ba tareda kowa nasa ya shaida auren sa ba.
“No one knows how, and where Habibu Nahuche got his beautiful son Abdallah in GERMANY…..not even his Mother….”.
Ba da niyyar cin abinci ya fito falon ba, ya fito ne domin ya dauki wayar sa da ya bari akan diningtable din. Babban abinda ya fizgi hankalin sa kan jaridar da ke ajiye shine hoton Abdallah a fuskar jarida, sai na shi dana Rahinah, a kagauce ya bi headlines din. Wadanda suka sa wani irin gumi tsatstsafo masa.
“Ita kenan bata san gatse ba?! Ashe Rahinah bata da hankali da hangen nesa har yanzu tana nan yadda take da kafiya da taurin kan ta? Nauyin shekaru ba su kara mata komai ba daga sanin da ya yi mata a baya, basu canza ta ba haka basu ishe ta yin hankali ba?
Har yanzu tana nan a sha yanzu magani yanzun ta! (not giving things a second thought)”.
Ya tambayi kan sa cikin tasowar wani matsanancin bacin rai, da bai taba ji a rayuwar sa ba, ba don yana shayin kotu zata kwace masa Abdallah ta bata ba, sai tunanin wannan tereren da ta ja musu, da Dan sa da ya ji ana kokarin sheganta masa!”
A take ya yi waya yayi booking jirgi mai zuwa Abuja, da zummar zai je yau ya fuskanci Dr. Rahinah Omar da duk abinda take taqama da shi a duniya, sai ta gwammace bata yi karar nan ba…sai ta gwammace bata san shi ba, sai ta gwammace wata alaqa bata taba hada su ba. Yau za ta san ko waye “REAL Habibu Nahuche” domin zai fiddo mata truecolour din sa.
Abdallah kuma sai dai ta daukaka kara zuwa SupremeCourt, (Federal High Court) ta yi tsararo ta kwatar mata shi, kai duk duniya bai ga kotun data isa kwatar Abdallah ba a kasar nan da wajen ta daga hannun sa……
(Babban bacin ran Habibu Nahuche ba karar sa da Rahinah tayi gaban Alkali bane, kamar shegan ta masa Abdallah da ta janyo ake kokarin yi a kafafen yada labarai babu gaira babu dalili, sai don neman magana da neman suna irin na ’yan jarida).
******
*ABUJA*
Kafin ka ce meye wannan labarin ya bazu kamar wutar daji a media, musamman cikin birnin tarayyah, kowace jarida tun daga ta cikin gida wato LEADERSHIP har Daily Tribune da Sahara Reporters ta maida shi headline din ta na wannnan satin. FACEBOOK, TWITTER, WHATSAPP groups kuwa sun maida shi ’topic of discussion’ hotunan Habibu da Rahinah da kyakkyawan dan su Abdullahi ya baibaye wayoyin al’ummah. Kowa yana fadin albarkacin bakin sa mai dadi da marar dadi.
Duk wanda ya kwana da sanin Habibu Nahuche (Lucky), Hotelier, ya ji labarin tsohuwar matar sa ta maka shi a kotu kan ya bata dan ta, dan da ba’a da tabbacin na halaal ne don a kasar Germany suka haife shi ba da sanin kowa nasu ba.
Washegari Aunty da Uncle suka bi bayan su zuwa wajen Hajiya, Aunty ta tabbatar wa Uncle babu inda Habibu zai je da Abdallah sai Zamfara, don ba zai iya yawon jihohin Najeriya da yake yi da yaron ba, don ba ya so jama’a suna tanka wa a kan tsananin kamannin da ke tsakanin sa da yaron.
A cewar sa don kada baki ya kama shi. Yana guje masa kambun baka. Don haka Aunty ba ta raba dayan biyun tabbas Zamfara suka nufa.
Ilai kuwa Hajiya Kaltume sai ganin Aunty da maigidanta ta yi sun yi sallama suna shigowa.
Suka zazzauna suna gaggaisawa da Hajiya cikin tsananin girmamawa. Hajiya ta ce,
“Ni laifin me kuka yi wa Baban Abdallah ne?”
Dariya Aunty da Daddy suka yi a tare, Aunty ta ce,
“Babu laifin fa da muka yi masa. Laifin mu daya kasancewar mu iyayen mahaifiyar Abdallah”.
Hajiya ta dan zamo jikin ta daga cikin kujerar ta, ta tattara hankalin ta kan babbar diyar ta, cikin rashin fahimta ta ce.
“Wace mahaifiyar Abdallahn?”
Aunty ba ta bata lokaci ba, ta ce, “Dr. Rahinah, mahaifiyar sa wadda ta haife shi, matar Habibu a Jamus, wadda ta guje shi.
Diya ta ke ta halali ga Baban su Musaddiq shi da mahaifin ta mai rasuwa ciki daya suka fito”.
Hajiyar Nahuche ba ta san sanda ta ce, “Allahu Akbar!” ba, “Allah da iko Yake, to ya aka yi da can ba mu sani ba?”
Aunty ta ce, “Muna tare da Rahinah tsayin shekaru masu yawa, tana karatun likita a Jamus, sai dai ta zo ta kwana biyu ta koma. Yanzu ne ta dawo gida gabadaya ta fara aiki a Abuja. Circumstances ne ya sa muka gane cewa ita ce, ba don wani cikin su (ita ko Habibu) ya gaya mana ba.
Hajiya gudun juna suke yi, bayan kuma a fili yake dayan su bai iya sake aure ba da dan uwan sa ba.
Laifin da muka yi masa har ya kwace Abdallah shi ne, mun yi plan din da ya ga Rahinar sa a gidan mu. Ba don haka ba sun zabi har su tsufa ba su kara neman juna, while dukkannin su sun san inda junan su ke rayuwa. Alaqar da ke tsakanin mu ce basu sani ba.
Hajiya, Habibu da Rahinah suna bukatar interference na iyaye da masu iko da su, domin su taimaka wajen gyara rayuwar su, su kuma ci gaba da rainon dan da Allah ya ba su a tsakiyar su”.
Hajiya ta nisa cikin al’ajabi,
“Ke nan ‘yar family din Sarkin Fulanin Girei Habibu ya aura?”
Daddy ya ba ta wannan tabbacin, sannan ya kara da cewa, “Uban ta shi ya sha nono ya saki na kama. Abin da dukkanin mu ba mu sani ba, kuma muke son sani shi ne, laifin da Rahinah ta yi wa Habibu, da laifin da Habibu ya yi wa Rahina suka gwammace su rayu a tagayyare cikin soyayyar juna shekara goma ba tare da juna ba”.
Hajiya ta ce, “Sha’ani na miji da mata ai babu yiwuwar sai an san abin da ya hada su. Hanyar gyara kawai za a nema a sulhunta su. Oh ni Kaltume Ya Allah ka nuna min wannan ranar… da Habibullahi zai sake aure a rayuwar sa ta duniya, duniya kuma ta shaida”.
Sai kawai ta soma matsar kwallah. Kwallan da ba ta komi ba ce face ta farin ciki, a dalilin sunsuno cewa lokacin auren Habibu ya zo. In dai da gaske ‘yar su Aunty ita ce mahaifiyar Abdallah, ita shaida ce kan cewa babu wadda Habibu yake jira sai ita, ko da za ya soma furfura ba aure.
Uncle Usman ya ce, “Ai sulhu ba zai yiwu ba tare da an san rootcause na matsalar ma’aurata ba. Ta hanyar sanin mene ne hakikanin matsalar su ne za a san hanyar magance ta da hana ta sake faruwa a gaba.
Don haka Hajiya komai yana hannun ki yanzu. Ke kadai za ki iya tankwara Habibu ya nemi sulhu da matar sa.
Hajiya ta girgiza kai ta ce, “Wani irin lallashi ne ban yi masa ba a kan aure? Wane irin nasiha ne ban yi masa ba? Wace irin addu’a ce ban yi masa ba? Don haka tunda dai wannan din ita ce uwar Abdallah kuma mu duka shaida ne a kan cewa ita kadai yake so, sannan kai ne madaurin auren ta, to mu taru mu gyara sunnah, in ba su shirya don Allah ba sa shirya albarkacin dan su. Ku tashi yanzun nan komin dare mu wuce Nahuche in gaya wa madaura auren sa”.
Ba karamin jin dadin shawarar Hajiya Daddy Usman da maidakin sa suka yi ba. A take ya kira Ambasada Shehu ya gaya masa duk abin da yake faruwa da hukuncin da Hajiya Kaltume ta yanke.
Ambasada sabida sanin da ya yi wa Habibu da Rahinah sai ya ga cewa shawarar su ba mai billewa ba ce idan har ba Rahinah da kan ta ta amince za ta koma wa Habibu ba, to fa baza’a haifi da mai ido ba, don haka ya ce su ci gaba da abin da suka tsara, shi kuma zai zauna da Dr. Rahinah formally ya tattashe ta a kan komen ta gidan Habibu don ita ce mai babbar matsala ba Habibu ba. Duk suka yi na’am da shawarar Ambasada.
*******
A Nahuche, baffanin Habibu sun ji dadin batun da Uncle da Hajiya Kaltume suka zo da shi. To kowa a kan gwiwa yake da damuwar rashin auren Habibun. Dadin dadawa an ce uwar dan sa Abdallah. Don haka kowa ya yi na’am da a maida auren.
Amma zasu jira Ambasada tukunna kamar yadda yace sai ya zauna da Rahinah officially akan maganar komen nata, matsayin ta na bazawara wadda addini ya baiwa damar zaben mijin aure.
Suna kan hanyar dawowa Zamfara daga garin Nahuche wayar Ambasada ta shigowa Uncle Usman, da sauri ya amsa cikin fara’a yana gaya masa nasarar tafiyar su Nahuche da matsayar da aka cimma idan Ambasada ya gama Magana da ita Rahinah. Ambasada Shehu sai ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan yace da Usman,
“kunna data ka duba WhatsApp, na turo maka wani abu yanzun nan da ‘Daily Trust’ suka fitar cikin makon nan”.
Da sauri Uncle ya hau duba dayar wayar sa.
Salatin da ya yi ba Aunty kadai ya firgita ba har Hajiya Kaltume. Sai ya kasa Magana kuma, sabida kunyar Hajiya Kaltume, a lokaci guda yana kissima irin yadda zai saka kafar wando guda da Rahinah, ana ganin ta mai ilmi ashe bata da hankali ko kankani? Kuruciya bata bar ta ba a shekaru 29?
Kasa fada musu ya yi, yayi shiru, duk da tambayar sa ko lafiya da suke ta yi yake jera salati? Sai ya ga gara su ji a bakin sa akan su ji a media. Ya gaya musu Rahinah ce ta yi karar Habibu a kotu, gobe zasu shiga Federal High Court ita da shi su fara Shari’ah akan dan su, amma su kwantar da hankalin su (he will never let this happen) insha Allah in dai yana raye kuma shine uban ta, zai yi maganin Rahinah.
Jikin su duka sai yayi sanyi, a lokaci guda kowacce ta soma tunanin ko dai a hakura ne? Allah kadai ya san abinda ya boye a karkashin wannan takun-sakar na Habibu da Rahinahr sa, sai kuma su da suka aiwatar da rayuwar su ta dan lokaci tare a Jamus.
Har suka iso gida jikkunan su a sanyaye suke. Aunty Badiya bata kai Uncle Usman jin ciwon abinda Rahinah ta yi ba, domin ya nuna bacin ran sa a fili, fada ya ke ta yi kamar Rahinar na ganin sa har suka isa Zamfara.
Hajiya kam ta fi kowa jin babu dadi, Habibullahi a Kotu! Wani abu ne da bai taba faruwa da shi ba, kuma wai da uwar Dan ka wannan terere da bankada da me ya yi kama. In Rahinah na son karbar dan ta ta bi ta maslaha mana ko ta zo ta same ta ta gaya mata sai kawai ta sa su a bakin duniya?
Dama can Hajiya Kaltume tana jin haushin Rahinah, a bisa ganin cewa, sabida ita Habibu ya ki aure, balle yanzu da ta yi wannan danyen aikin, ana cikin kokarin gyara aure.
Sai Hajiya ta ji Rahinah ta kara sire mata, amma zata ci albarkar Usman don miji ne har miji ga ‘yar ta, wanda ba’a taba jin kan su da Badiya ba shekaru ashirin da doriya, sannan zata ci albarkacin dan ta. A yadda ta san Habibullahi, da son da ya ke wa Abdallah, to ba kotu ba, ko ina Rahinah zata je zata gaji ta bari babu mai iya raba shi da Abdallah.
Uncle Usman yayi kwafa “banda hauka irin na Rahinah? Wa ya gaya mata ana jayayya a kan Da? Da, na kowa ne kuma ajiyar Ubangiji ne ga iyayen sa, zamu gamu da ita, sai ta gwammace bata taba sanin Usman Girei ba”.
Ko da suka isa Zamfara, anan ya bar Aunty Badiya. A daren ya dawo Kaduna, washegari ya nufi ‘airport’ ya bi jirgin ‘Max Air’ zuwa Abuja don hanyar Abuja ta kazanta a wannan dan tsukin, ba’a fiya bi da mota ba, balle shi da yake a kagauce da yin tozali da Rahinah, ko a waya bai kira ta ba, burin sa ya bude ido ya gan ta gaban sa, yana kuli-kulin kubra da ita. A sanin da ya yi wa Habibu ko kadan bai son tashin hankali balle abinda zai taba mutuncin sa.
******
*RAHINAH*
Abinci ta ke ci a dakin Yafendo, abinci mai rai da motsi da Nene Balki ta dafa mata na musamman, tana ci suna hira ita da Yafendo hankalin ta kwance ya tsumma a randa. Tana fadi cikin ran ta jibi I yanzu suna gaban alkali ita da dan Nahuche. Har Lawyer ta dauka mai zaman kan ta daga Chambar Lauyoyi masu zaman kan su na garin Abuja.
Sai ganin Daddy Ambassada ta yi tsaye a kan ta rike da jarida, tsabar bacin rai ko sallama bai yi musu ba. Ya ce
“Rahinatu, me na ke gani haka?”
Ashe baki da hankali baki da tunanin dana ke ganin kina da shi?”
Ya jefa mata jaridar ‘Daily Trust’ akan cinyar ta sannan ya ce “maza-maza ki je ki janye karar nan, kafin in kifta ido na, wa ya ce miki ana jayayya a kan yaro? Kina so Ubangiji ya yi hukuncin sa a kan sa? Kina son ku rasa shi gabadaya ko? In kina son rayuwa da yaron da gaske, me zai hana ki koma gidan uban sa?”
Rahinah ta sunkuyar da kai, bata ce komai ba, ganin yadda Ambasada ke tafarfasa, ko wa ya kai wa ‘yan jarida labarin kuma? Bata yi don ta bata ran iyayen ta ba da masu kaunar ta, ko don a yayata su a mediasai don kwatarwa kan ta ‘yancin ta da Habibu ya bi ya danne ya ke kuma kan dannewa, domin so ya ke har ta mutu ba ita babu dan ta.
Ita ba don a sa a media ta kai Habibu kara ba, ta kai shi ne don shari’ah ta kwatar mata dan ta, tunda ta bi shi ta lalama ba wanda ya ji ba wanda ya gani amma ya bi ta da gatse da bakar Magana. Ya raina mata hankali.
“Maza-maza ina umartar ki da ki tashi ki je ki janye karar nan, yanzu yanzun nan kafin isowar Usman, ya gaya min ya taso a jirgi, zai saba miki yadda ba kya zato. Don ta ni kin sani mai sauki ne, har kullum Uba nake mai fahimtar ki da bin ra’ayin ki, mai yawan yi miki uzuri, hadi da baki damar da Allah ya ce a baki. Amma a wanan karon bana bayan ki Rahinah.
Akwai muhimmiyar Magana da dama nake so mu yi a yau, kawai na ci karo da wannan shirmen naki ana sayarwa a hanyar motoci, tashi maza-maza ki je ki janye ki dawo kafin isowar Usman don ya gaya min kan azahar zai sauka a garin nan.
Rahinah ta dan tsuke baki da fuska cikin alamun gardama, karo na farko da zata yi wa Ambasada musu, Yafendo da bata gane akan me ya ke ta fadan ba ta ce.
“Me ke faruwa ne Jakada?”
Nan Daddy yayi mata bayani a takaice “Rahinah ta kai Habibu kara kotu, a kan ya bata dan ta!”.
Sai ga Nene Balki ma ta shigo, ta tsinkayi karshen maganar da yake fadawa Yafendo, salati suka hau yi a tare, Nene na fadin “Rahinah kan ki daya?” Yafendo ta ce “ko kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? Don an ce min yanzu a kasar nan mata sun koyi shaye-shaye, kuma kika kunshe baki kika yi shiru kina sabgogin gaban ki hankalin ki kwance kamar kin kashe rai, sai zabga lomar abinci kike, Allah ya raba mu da kotu, ko makiyin mu kada Allah ya kai kotu balle Baban Abdullahi, ‘yar nema, ja’ira.”
Nene kuma ta ce “Rahinah ki komawa uban sa mana! In kin san kina son yaron ki da gaske? Ki rayu da su har abada cikin salaama da aminci, wannan taurin kan da girman kan ba naki bane a matsayin ki na ‘ya mace, na rasa ina kika koyo su, ita ‘ya mace da rauni aka san ta da yafiya ga mijin auren ta, ki tashi maza ki bi umarnin Abba Jakada, kin ga shi bai iya fada ba, kada ki sa yau a kan ki ya koya”.
Cikin bacin rai Ambasada ya ce “ai ni bata dauke ni Uba ba shi yasa ina ta Magana tana ji na ta yi kunnen uwar shegu da ni, ku bari uban ta na halali ya zo, shi in ya sa ta za ta yi, ya ce min har da dorina sai ya buge ta wallahi”.
Kalaman Ambasada Shehu na “bata dauke ni Uba ba, ku bari uban ta na halali ya zo” sun taba zuciyar Rahinah sun kuma karya ta. Ta mike tana hawaye ta isa gaban Ambasada ta durkusa, cikin rawar murya take magana.
“Ba ni da uban da ya fi ka Daddy, ka yi min abinda kowanne uban halali yake yi wa ’yar sa. Ka yi hakuri zan je in janye yanzun nan. Saboda kai!”.
Ambasada ya juya ya fita sakamakon kiran sa da ake ta yi a waya duk akan maganar, wadda ke kara yaduwa kamar wutar daji a garin Abuja. Ita kuma ta dauki Jilbaab din ta da mukullin mota jikin ta na rawa ta fita.
Lawyer data dauka wato Barr. Hanifa Suraj Kumo (AMANATA) ta fara kira tana hawaye tana tuki, ta gaya mata Baban ta ya ce ta janye karar, so ta janye, amma kudin da ta riga ta bata ta bar su. Barr. Hanifa ta ce baza’ayi haka ba, zata maido mata da ko rabi ne. Sannan ta karasa kotun, cikin dan lokaci ta janye karar.
Al’amarin da bai yi wa ‘yan jarida dadi ba, don sun so samun kudi sosai da issue din Nahuche da ex-wife din sa. Kasancewar Habibu Nahuche wani matashin miloniya mai farin jini a kasar Najeriya. Tana hanyar dawowa gida, Uncle Usman ya iso, Ambasada ya tura direban sa ya dauko shi daga filin jirgi, suna falon saukar bakin sa suna kara tattaunawa akan al’amarin.
“Na tura ta yanzu kan ta je ta janye” inji Abba Jakada.
Sai ga wayar Habibu ta shigowa Uncle Usman, inda ya gaya masa “ga shi ya sauka daga Lagos shima yanzu, an aika masa SAMMACI, wai wata mahaukaciyar Likita ta kai karar sa, zai halarci zaman kotu jibi tare da ita”.
Uncle ya kasa gane halin da muryar Habibu ke ciki a wannan lokacin. Sai ya ji sunan da ya kira Rahinah da shi ya ba shi dariya, ya kuma dace da ita ya ce masa,
“ina gidan Ambasada yanzu haka, nima ban dade da shigowa garin ba, ka bar duk abinda ka ke, ka zo ka same ni a can. Maitama ne”.
Habibu ya juya yayi wa PA din sa na Abuja Magana wanda shi ya dauko shi, ya bashi umarnin su fara zuwa gidan Ambasada Shehu kafin ya kai shi gidan sa na Abuja da ke a ‘Life-Camp’.
A dai-dai wani shatale-tale (roundabout) na kan titin da zasu bi su dauki hanyar unguwar Maitama, danja ta tsayar da su.
Kusan a tare suka tsaya da motar da ke barin daman su kirar KiaPicanto fara sol, kamar an ce da shi ya kalli matukin motar, sai ya dan janye jaridar ‘daily trust’ da ke hannun sa yana dubawa, wadda ke dauke da kanun labarun kai shi kotu. A gefen nasu mace ce fara sol ke jan motar, sanye da (Egyptian Jilbaab) ruwan kasa-kasa, hannayen ta biyu da ke dafe da sityari sun sha zobban zinare guda uku-uku, bai dauki ‘yan sakanni ba kwakwalwar sa da kyawawan idanun sa suka gane ta; Dr. Rahinah Omar Girei.
Itama jin alamun idanu a kan ta, sai ta waiwaya kadan, motar su kirar bakar ‘Chevrolet-Volt’ wadda bata da yawa ko a cikin Abuja ba itace ta dauki hankalin ta ba, kamar HandsomeMan din, mai wani irin sassanyan kyau da aji na musamman, wanda ke kwance cikin lallausar farar shaddah Wagambari a bayan motar.
Ko mutuwa ta yi ta dawo wannan fuskar bazata taba bace mata ba, lumsassun idanun nan masu son shigewa cikin nata a yawancin lokuta, har yanzu suna nan yadda suke farare kal, a lumshe, cikin farin glasses tar-tar da shi kamar ba glass ne a idon sa ba sabida garai-garai din sa; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche, shi ke kallon ta cike da wata irin lumsassar ‘tsana’ kwance cikin kyawawan kwayan idanun sa.
Yatsun ta masu dauke da zobban zinare ta kai tana danna maballin dake jikin motar ta, glassai bakake suka maye gurbin masu haske su ka yi sama zuuu! Kamar yadda ta kautar da kai itama, cikin tsananin faduwar gaba marar misaltuwa.
Dai-dai lokacin danja ta basu hannu, ta wani irin zugi motar da gudu ta tsere musu. Ashe an yi ba’a yi ba, an gudu ba’a tsira ba.
Domin kuwa kusan a tare su duka suka isa gidan Ambasada Shehu Bichi da ke unguwar Maitama, ta riga su shiga, har ta adana motar ta a ma’adanar motoci kafin su iso, akan idon ta mai gadi ya bude musu kofa suka sulalo cikin gidan kamar ita kan ta motar tasu tafiyar takama take yi tamkar Ba-Rumen ubangidan nata (dan kabilar Rumawa).
Kafin PA Mr. Atiku ya gama parking ya fito don ya bude masa, ya bude da kan sa ya fito.
Rahinah bata tsaya ba, kusan da gudu-gudu ta karasa shigewa cikin gida, bata sani ba ko da ace ta tsaya din sun jera, ko alfarmar kallo ba zata samu daga Habibu ba.
Dakin Nene Balki ta fada ta shige toilet ta rufe, don ta san nan ne kadai waje na karshe da za’ayi tunanin neman ta cikin gidan. Addu’ar ta daya kada ya kasance wani ya ga dawowar ta, balle a neme ta.
Sai dai kuma tana shiga toilet din Nene na shigowa dakin, ta kuma ga rufo kofar toilet din data yi, sannan kamshin turaren ta ‘Nina Ricci’ shi ke fallasa ta a duk inda ta s higa.
Nane bata kawo komai ba a ran ta, ta dauka ta shiga ne don yin alwallar sallahr azuhur.
******
Is not for free. It’s 1000 via
3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank
[11/08, 12:22 pm] Ummah Salisu: *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
*BAKO DAGA IKKO*
“Karaso daga ciki Habibullah”.
Ambasada ya fada cikin kulawa. Ya taka a hankali zuwa cikin kayataccen falon na tsohon Ambasadan, kyawawan kafafun sa na nitsewa cikin lallausar kilishin falon, har kasa ya tsugunna yana gaishe su, Uncle Usman ya nuna masa kujerar da ke fuskantar su, amma sai bai hau ba, ya zauna akan kafafun sa daga nesa da su.
Sun dauki dan lokaci su duka ukun babu wanda yayi magana a falon bayan gaisuwar data gudana. Zuwa can Ambasada ya ce “ya hanya? Kuma ya kokari? Ya a ka ji da jama’a?”
Uncle Usman bai bari ya amsa ba ya yi kwafa, sannan ya ce.
“Kayi hakuri Habib, wannan mahaukaciyar ta taso ka daga wajen neman abincin ka, amma yanzu Ambasada yake gaya min ya sa ta taje ta janye karar.
Na zo da zummar zane ta da dorina kan wannan rashin kan gadon nata, sai shi Baban nata ya bani hakuri ya ce yanzu haka ta tafi ne ta janye karar”.
Shi dai bai ce komai ba, amma a cikin ran sa cewa yake “Kash! Ai da kun bar ta, an goge rainin da ke tsakani na da ita a kan idanun duniya, watakila da ta fi hankalta, in ta gane ni ba sa’an yin ta bane. Ambasada ya kira sunan sa a hankali,
“Habibu!”
Bai amsa ba amma ya dago ya dubi Abba Jakadan. “Har yanzu kuna nan a kan bakan ku na cewa bazaku sulhunta ba ko saboda yaron nan? Wa ya gaya muku ana jayayya a kan yaro?”
Uncle Usman ya ce “ai su duka ya kamata su zauna yau a gaban mu, mu yi magana ta gemu kuma ta karshe mu da su, babu yaro cikin mu, kuma babu sa’an ku, wasa da hankalin da kuke yi mana ya isa haka”.
Ambasada ya dauki wayar sa yana kiran layin Rahinah, tana kallon wayar na ringing kamar yadda hantar ta da hanjin cikin ta ke kadawa suma, bata iya ta daga ba har ta katse. Sai ya kira Nene Balki.
“Ki zo min da Rahinah falon saukar baki yanzu”.
Nene ta hau kwankwasa mata kofa, ai kuwa Rahinah ta kara tsurewa. Bata son fuskantar kowa a cikin su sabida kallon da Habibu ya yi mata dazu a danja ya lalata dukkan karfin zuciyar da ta ke ji da shi. Ga shi bata san kiran me aka yi masa gidan ba.
Nene kawai sai ta murda kofar toilet din don ta fahimci ba wani abu take yi a ciki ba, ta ce “Rahinah lafiya? Buya ne kuma a toilet? To ki wuce Abba Jakada na kira”.
Koda ta dago ido yau Nene sai ta ga rauni a cikin idon ta, kafin a yi haka she’s always bold akan duk wani al’amarin ta da Habibu Nahuche.
Nene sai ta kamo hannun ta, ganin idanun ta sun cika da kwallah, ita kuma sai ta bi ta tamkar Rakumi da akala.
Shigowar su falon tare da Nene bai sa Habibu ya dago ido daga sunkuyawar da yayi ya dube su ba, but her presence overwhelmed him (ya ji kasantuwar ta a wurin acikin jikin sa). Amma hakan bai sa ya nuna ya san da shigowar su ba.
Gefen Habibu Uncle Usman ya nuna mata ya ce ta je ta zauna, zaman ta daura da inda ya ke zaune, da dan motsawar da yayi kamar ya kara zakudawa (ja baya) ya sa ta shako sassanyar kamshin ‘Carolina Herrera’ wanda ya tuna mata haduwar su ta farko a cikin jirgi, ranar da ta fara mannuwa da shi ta shaki wannan kamshin. Sannantheir second encounter at Cologne Public Library (haduwar su ta biyu a labiraren jami’ar Cologne) ranar da ta barar masa da littatafai ta shaki the same perfume, the subsequent encounters (sauran haduwarwakin da suka biyo baya har zuwa firstnight din su (ranar daren farkon su na aure).
A take ta ji dukkan karfin zuciyar ta ya dawo, kwanan nan ya kira ta muguwa, azzaluma. Shin tsakanin ita da Habibu idan aka dora a sikeli wanene mugu kuma azzalumi?
He took away her pride by force, sannan a arha, with no love nor affection. Wannan duk bai ishe shi ba, ya mayar da ita bazawarar shekara goma (ta manta ita ta nemi sakin by all means) ya kuma dauke dan ta kwalli daya da Allah ya bata tun yana zanin goyo ta hanyar sacewa.
Don haka wannan mutumin ba abun tausayi bane, selfishness and rudeness din sa are in style, sun barranta (banbanta) da kamannin sa na zahiri na kamili kuma salihin mutum.
Uncle Usman ya soma Magana cikin bacin rai. Bacin rai irin wanda daga Habibu har Rahinah, babu wanda ya taba ganin sa cikin kwatankwacin sa.
“Yau na ke fatan komai ya kare a tsakanin mu da ku. Ya kuma kare a tsakanin ku. Kodayake tsakanin ku ba zai taba karewa ba tunda zuri’a ta hada, amma bazamu zuba ido ku zubar da mutuncin junan ku a idon duniya ba, shi kuma yaro ku sa bakin duniya ya lalata shi.
Wannan shine zama na karshe da zai guda na, mun baku dama kowa ya fadi abinda ya sa ya kasa yafewa dan uwan sa da abinda yasa kuka zabi zama shekara goma babu aure”.
Dukkan su kan su na kasa, amma Rahinah gumi ta ke kashirban. Habibu ya dago a hankali ya dubi Ambasada idanun sa sun kada, sannan ya dubi uban Rahinah, kuma ubangidan sa sannan surukin sa Alh. Usman Girei. Murya babu karsashi yace,
“Ni ba abunda ta yi mun, ni ne ma na yi mata laifi kan laifi, na kuma roki afuwar ta tun a wancan lokacin. I’m not sure (bani da tabbas) ta yafe din ko bata yafe ba.
Rashin aure na shekara goma kuwa mai yuwuwa ne wannan ce kalar kaddarar mu. Amma ni ba don ita na ki aure ba, sabida ba ita ce autar mata ba.
A bayan haihuwar ta da kafin haihuwar ta an haifi dubunnan mata wadanda suka fi ta duk abinda ta ke takama da shi. Kawai bana ra’ayi ne. Don na san zan iya rike kaina. Amma yanzu na baku wuka da nama, ni Habibu Mustapha Nahuche, na amince ku aura min kowacce ‘ya kuke da ita, tsohuwa ko yarinya, budurwa ko bazawara, ko daga ina ta ke, komai munin ta, akan dai ku mayar min da wannan…..”. Ya nuna Rahinah da bakin sa cikin izgili, disgustingly da son tura haushi.
Ta dago a tsanake, idanun ta sun kada, domin sosai kalaman nasa sun buge ta, sun tura mata haushin har fiye da yadda yake so su tura. Maimakon ta dube shi ta maida masa martani, sai ta dubi Baban ta Usman Girei.
“Uncle, ba ka dade kana min maganar CMD ba? (Chief Medical Director) na Nizamiye, ina cewa ya dakace ni? Ai tuni na bashi damar fitowa kuma ya ce cikin satin nan zai je Yemen ya zo da Baffannin sa, su karbi auren. Ni wannan mutumin (ta nuna Habibu da baki) ba abinda ya yi min. Dan da ya shiga tsakanin mu kadddara ne. Amma ba don shi na ki aure ba.
Ban samu wanda ya kwanta min bane tuntuni sai yanzu, ina so ne in yi settling sosai da ayyukana kafin na yi aure. Kuma alhamdulillahi lokaci ya yi yanzu, na baiwa Dr. Irshad damar fitowa already”.
Ta kare da sunkuyar da kai sabida hawayen da ke son bada ita. Daga Uncle Usman har tsohon Ambasada sakin baki suka yi galala! Suna kallon su, sun rasa mai ya kamata su ce kuma, ko ta ina kuma za su bullo musu?
Sai Uncle Usman ya ce “toh-toh, yanzu kin yarda da auren bakon hauren kenan duk da baki ko san al’adun kasar shi ba balle irin mutanen da yake tare da su? Nasaba, halayya da dabi’a duk baki sani ba?”
Rahinah ta runtse ido ta ce “Uncle shi na zaba, na dade da sanin wasu daga cikin halayen sa musamman neman mata, amma wallahi ya fi min wannan sau dubu….” (ta sake nuna Habibu da baki). Kuma tunda kun hana ni kai shi kotu sharia’ah ta kwatar mun Da na, to ku karba ku bani……”.
Kawai sai ta fashe da kuka, ta jingina kai a jikin kujerar da Habibu ke jingine tana ta yi riiii-riii-riiiii”.
Ambasada ya ce “ai na sha gaya miki muddin ina raye Rahinah, babu mai yi miki auren dole, not evenyour father (ya nuna Uncle Usman). Na tsaya miki Rahinah, and I will foreverstand by you (kuma har abada zan cigaba da tsaya miki a matsayin ki na marainiya”.
Sai dai kuma Rahinatu bana son yadda kuke ta jayayya akan yaron nan, Allah da ya halicce shi ya fi ku son sa, kada ku tabo fushin sa. Yau da iyayen da suka haife ki suna raye, na tabbata zasu maida ke gidan uban dan ki ne ko ba tare da yardar ki ba.
Mu da mu ke matsayin iyayen ki a yanzu muna neman “ALFARMA”. Ki yi mana alfarma ki koma gidan mijin ki, zai je har GIREI ya nemi auren ki cikin mutunci, adalci da girmamawa yadda duk ya kamata a hannun iyayen ki, sadaki kuwa sai abinda kika yanke.
Bayan auren kuma, za mu cigaba da bibiya mu tsaya mu ga cewa ya rike ki da amana, adalci, soyayya, daraja da mutumtawa.
For our sake! For Abdallah’s sake, for your late Daada’s sake, for the sake of the love you have for your son……(sabida mu, sabida Abdallah, sabida marigayiya Dadan ki, sabida kaunar ki ga dan ki) ki manta komai, ki komawa Baban sa. In na ce komai ina nufin KOMAI”.
Ya hada hannayen sa biyu cikin alamun roko. Kafin Ambasada ya kai karshen maganar sa kukan Rahinah ya cika falon, ya nunka na baya. Ta rasa inda zata saka kanta. Habibu ban da jibi (zufa) ba abinda yake yi.
A wannan lokacin ya rasa takamaimai a matsugunin da zuciyar sa take, wani irin duka zuciyar sa ke yi tana lugulgude a tsakiyar kirjin sa. Addu’a yake Allah yasa kada Rahinah ta amince da rokon Ambasada Shehu, don bashi da gurbin da zai saka ta cikin rayuwar sa yanzu.
Ya riga ya gama binne ta daga zuciyar sa ba don ta mutu ba! Yana jin dadin rayuwar sa a haka, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba.
Ita kuwa Rahinah nata tunanin daban yake, Abba Jakada, wato Ambasada Shehu ya fi karfin ya nemi kowacce irin alfarma daga gareta. A irin kalaman da ya yi mata amfani da su, babu tursasawa, a irin lallashin da ya yi mata babu bada umarni, face tsagwaron bata hakkin ta da addini ya ce a bata.
Sannan Ambasada ya ce za’a je neman auren ta ne cikin mutunci hannun iyayen ta karkashin tushen ta da asalin ta, babban abinda ya sa ta kullaci auren Habibu na baya kenan; auren ta da ya yi ba a hannun kowa nata ba, wannan kadai ya rankwafar da zuciyar Rahinah, amma ba don matsayin da ta aje Habibu ya canza ko kankani daga zuciyar ta ba.
Ba don feelings din ta a kan sa ya canza ba, har gobe yana nan a Habibun sa, dan mutanen Nahuche da har abada bazata yafewa ba. Aure ne a je a yi ta mayarwa tunda ta yarda ta amincewa ran ta tana son ABDALLAH, baza kuma ta iya rayuwa ta nutsuwa yanzu ba tare da shi ba, daga lokacin da ta dora ido a kan sa bayan wucewar shekaru goma. Bata kuma da wata hanya ta rayuwa tare da Abdallah yanzu, bayan komawa gidan su.
“’Ya ta Rahinatu kin min alfarmar? Kin amince a mayar da auren ku ki koma zama gida daya da dan ki Abdullahi karkashin inuwar auren mahaifin sa?”
Sai ta gyada kai sama cikin hawaye, wasu na korar wasu. A fili Ambasada ya jero Hamdala, Uncle Usman kuma a zuciyar sa yake yi, don shi ya so ba’a tsaya yi wa Rahinah wannan irin lallashin ba, kawai a maida auren in ya so ta kashe Habibu don kiyayya. Ya amince Habibu ba ya kin Rahinah, tata kiyayyar ta fi yawa.
Amma a yanzu ko shi ya fi jin dadin hakan, da bai zama cewa auren tursasawa ne zai kara gudana a tsakanin su ba, a zo a koma ‘yar gidan jiya.
Duk da haka Uncle Usman na tsoron Rahinah. Ya fahimci ba wai ta amince bane 100%. Ta amince ne kan ba yadda zata yi albarkacin Ambasada, albarkacin ya fi karfin kowacce alfarma daga gareta.
Sai a lokacin ya magantu, “in ma akwai abinda kika kudurta a ran ki ki sani Allah yana kallon ki, in ma ba don Allah kika amince ba duka ya rage naki, da hannu na dai bazan dauki ‘ya ta in baiwa bakon haure ba.
Mu za mu dan fita, ku yi amfani da wannan damar ku yi maganin matsalolin ku domin insha Allahu rabbi, sati mai zuwa za’a maida auren ku. Saura kuma ya rage naku. Duk wanda ya zalinci dan uwan sa ko da da kalaman fatar baki ne shi da Allah. Ubangiji SWA ya ce “Was-sulhu khair!”.
Da fadin haka, suka mike shi da Ambasada suka bar falon. Motsin kirki wannan babu wanda ya yi tsakanin Habib da Rahinah.
Kowanne zuciyar sa ta yi nauyi da sabon al’amarin da ke shirin samun sa, wato sake zama da juna a karo na biyu.
Rahinah ji tayi bazata iya cigaba da jurewa zama a inda Habibu yake ba. Gara ta tashi ta bar wurin kafin zuciyar ta ta yi bindiga da bakin cikin da ke cin ran ta. Ta san yanzu bakin alkalami ya riga ya bushe bata da sauran abun yi, bata isa ta dawo ta ce da dattijan nan ta janye alfarmar da ta yin ba. Amma cigaba da zaman ta a falon nan zai iya sawa ta yi hakan (tace ta janye din).
Gara mata zama waje daya da bakin maciji a kan zama kusa da Habibu Nahuche. Don haka ta mike cikin azama ba tare da ta dube shi ko ta ce da shi kanzil ba ta nufi kofa.
Da zuzzurfar muryar shi ya dago idanun shi da suka canza launi ya dubi bayan ta tana ficewa. Ya daga murya yadda za ta ji shi sosai.
“Gara miki ki koma ki warware musu fake yardar taki, na gaya maki, ina kara gaya miki we don’t need you in our lives anymore daga ni har Abdallah.
Bar ganin na yi shiru, ki dauka nima na amince ne, a’ah, su biyun nan suna da wata irin kima ne a idanu na da bazan iya yi musu musu ba. Amma wallahi gara duk matan duniya da ke Rahinah! Gara a aura min kowace ce da in kara hada rayuwa ta da ke”.
Wani lalataccen murmushi ne ya subuce a siririyar fatar bakin ta. Ta juyo gaba-gadi ta fuskanci Habibu.
“Ni da nace na amince, ce maka na yi har zuciyata ne? I just want to be with my son and nothing more, sabida bana so in kara jayayya a kan sa. Ka kwana da sanin Rahinar da ka sani da, ba ita ce yanzu ba, wadda ka ke raping a duk sanda ka so,wannan sai dai ku yi wrestling, ka shirya zama da sabuwar Rahinah mai ‘yanci, mai gata, tsayayya a kan kafafun ta. Auren ka ko rashin sa, ba zai kare ni da komai ba, banda Da na da zai dawo kusa da ni”.
Habibu ya yi murmushi wanda Kalmar ta ta wrestling ce sanadin sa, wasu irinbeautiful serene smiles, ko kadan kalaman ta basu yi masa ciwo ba, (as he expects words like these from her) domin ya tsammaci kalamai kamar su, ko ma fiye da su daga bakin ta, a duk ranar da suka sake haduwa. Don ta huce haushin ta.
Yace cikin ginshira.
“Rahane kike ko wa? Ki tuna yaron nan bai san ki ba, ni ya sani matsayin uwa da uban sa, don haka zuwan ki gidan su wai saboda shi, ba abinda zai sa, ba abinda zai hana.
Zan tabbata na gaya masa Uwar sa muguwa ce, azzaluma ce akan Uban sa, wadda bata cancanci yafiya da soyayya daga gareshi ba. Bata taba waiwayar sa ba tsayin shekara goma sai don ta gan shi a akan hanya.
My boy is smart, kuma da wayon sa da hankalin sa, ba kowacce karabiti ce zata zo ta ce da shi ita ta haife shi ba ya yarda….”.
Yatsunta biyu ta sa ta toshe kunnuwan ta, sannan ta karasa ficewa da ga falon da dan banzan sauri. Har tana cin uban tuntube tare da sa hannu ta toshe bakin ta daga azababben kukan da ke son kubuce mata.
*******
*ME YE ABIN YI?*
Dakin Yafendo ta nufa tana kuka wiwi, ta soma hada komai nata da zummar komawa gidan ta. Yafendo, bata ce mata ko uffan ba domin cike take da farin cikin maida auren da Abba Jakada ya ce mata za’a yi ranar Juma’ah mai zuwa.
Nene ce ta shigo dakin ganin Rahinah ta sunkuto Jakar ta tace “Rahinah, babu inda zaki koma fa, daga nan gidan sai gidan mijin ki, za’a je a kwaso komai na gidan gobe da safe insha Allahu”.
Ta fada jikin Nene tana kuka “Nene wallahi har gobe ba ya so na, nima bana son shi, Da na kawai nake so”.
Nene abin sai ya koma bata dariya Yafendo kuwa haushi ne ya kama ta, tace “shi SON ya ci uwatar, ya ci Uba nai, mu da iyayen mu suka yi mana aure bamu taba ganin mijin ba fa sai a gidan sa? Ba gashi mun haifi wadanda suka haife ku ba babu soyayyar? Aka bar duniya ana begen juna, ku kuka dauki soyayya wata tsiya, ba kya son shi kika hada shimfida da shi har kuka haifi Da?
Ina ce karewar so kenan ka hada shimfida miji?”
Nene na ta dariya ta ce Yafendo wannan ai ba sai da so ba, kaddara ne, umarnin Ubangiji ne, amma ni in zata dau lasifika ta hau duro tana yekuwar bata son Habibu ba zan taba yarda ba, domin na sha kamata tana searching (browsing) din sa a yanar gizo, har da saving hotunan sa cikin wayar ta da kwamfutar ta, in babu so me ya kawo wannnan? Wanda ba ka so meye naka na bin kwakkwafin sa?”
Rahinah ta rasa inda zata sa kanta don bakin cikin abinda Nene ke fada, kamar ta dora hannu aka ta saka ihu, Nene ta cigaba da baiwa Yafendo labarin ranar data kama ta da hoton sa cikin kwamfuta tun suna Frankfurt.
Yafendo ta ce “ahap! Ai shi munafurci dodo ne mai shi yake ci, aure kuma an mayar an gama da iznin Allah”.
A fusace Rahinah ta bar dakin zuwa nata dakin da ke gidan, ta shige ta rufe har da key. Nene da Yafendo basu kara bi ta kan ta ba a gidan. A take Nene ta kira Aunty Badiya.
Suka gaisa, suka taya juna murna na maida auren da za’a yi, amma jikin Aunty Badiya a sanyaye yake, don a lokacin tana can tana fama da Hajiyar Nahuche wadda ta ce gara Habibu ya hakura da Rahinah, don bata hango masa kwanciyar hankali a sake zama da ita ba. Matar da zata kai ka gaban Alkali tabbas bata son ka, Aunty ta ce,
“Hajiya ki rabu da Rahinah ba halin ta bane, bacin rai ne ya kai ta ga hakan. Amma ba don bata son Habibu ba”.
Don haka da Nene ta bugo yanzu suka yi wa juna murna sai ta ke yi wa Hajiya Haj. Kaltume bayanin marikiyar Rahinan ce ta bugo, komai ya daidaita ta bangaren su sai jiran ranar daurin aure.
Kuma dama Uncle Usman ya kira su ya gaya musu sati mai zuwa za’a je Girei a maida auren don Hajiya ta sanar da iyayen sa maza da zasu je su karba masa auren daga garin Nahuche, Hajiya dai kadaran-kadahan ta amsa don Rahinah ta gama sire mata, da ta yi wannan danyen aikin, kamar wadda bata da mafadi ko mashawarci.
Don ta ita a hakura da Rahinah a nemawa Habibu wata, abu daya take tunawa ta hakura wato Abdallah. Tana matukar son ya cigaba da girma karkashin kulawar iyayen sa biyu, ya daina walagigi tasakanin Zamfara da Kaduna.
Amma maganar soyayya irin ta uwar miji da surukar ta tsakanin ta da Rahinah Omar babu ita. Kamar yadda at the same time babu kiyayya. Watau bata kin ta haka bata son ta. A yadda ta ke son Habibullahi, kamata yayi a ce matar sa ta fari ta zame mata ‘yar gaban goshi, wadda zasu kashe su rufe tare, amma banda wannan Rahinar mai jin kan ta kamar wani dutsen yaqutu.
Washegari suka je suka kai goron tambaya da kudin aure. Aka sa ranar daurin aure Juma’ah bayan masallaci, tun ranar Alhamis Ambasada da ‘ya’yan sa maza Abbas da kanin sa wadanda suka dawo karatu daga Frankfurt, Uncle Usman da nasa samarin ‘ya’yan hudu wato su Musaddiq suka kama hanyar Adamawa.
Sun dauki hanya tun da sanyin safiya daga Abuja amma basu isa Girei ba sai dare. Kai tsaye gidan Sarkin Fulani suka sauka bayan sun je sun kama Guest Inn din da zasu kwana anan cikin garin Girei.
Kafin isowar su mutanen Nahuche sun riga su isa, kannen mahaifin Habibu ne da wasu dattijai daga family din su har da Baban Ex budurwar sa Shafa’atu wanda shine madaurin auren sa duk sun isa Girei kamar yadda aka tsara. Alh. Usman shi yayi musu masauki a inda suma suka sauka (Girei Motel).
Washegari misalin karfe uku na rana bayan an sakko masallaci duk suna zaune zauren Sarkin Fulani, manyan ‘ya’yan sa su Ilyasu, Dagacin garin Girei, makwabta da dattijai abokanan arzikin Sarkin Fulani, abokan mahaifin Rahinah na kuruciya da abokan Uncle Usman na garin Girei da duk wani mai fada a ji a garin Girei, jama’ar gari ‘yan gayyar sodi ma ba’a bar su a baya ba.
Iyayen Habibu (Baffannin sa) suka mika sadakin su mai daraja wanda ya fito ne daga aljihun su da aljihun Hajiyar sa da suka yi karo-karo suka hada ba tareda sun bi ta kan sa ba, kasancewar kowannen su a kage yake kan yayi auren kawai koma da wacece, to balle da aka ce uwar dan sa Abdallah.
Don haka kowannen su cikin farin-ciki yake yin komai, ba bata lokaci aka daura auren HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE da DR. RAHINAH OMAR GIREI. Wani aure da ya bar tarihi cike da farin cikin kowanne bangare. Ana yi ana raha da annashuwa. Limamin masallacin Juma’a na garin Girei ya bi auren da addu’o’I na musanman, tare da rokawa ma’auratan zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada a tsakanin su.
Washegri Asabar kowa ya kama hanyar komawa garin da ya fito, tarewa sai Habibu ya zo da kansa inji Sarkin Fulani. Ya ce Usman ya kawo masa Rahinah nan gidan sa, daga nan Girei za’a dauke ta zuwa gidan mijin ta bayan sun yi biki irin na al’adar garin Girei. Usman ya gaya masa tana gidan Ambasada yanzu haka, amma Nene Balki da Yafendo zasu dauko ta su kawo ta, in ya so, su rankaya daga nan Girei zuwa duk inda Habibu ya zaba mata ta zauna.
Kwanaki biyu kenan da daurin auren, ba tare da Habibu ko Rahinah wani ya kara neman dan uwan sa ba ko a waya, amma suna sane da cewa an daura din. Ita tana dakin ta na gidan su Nene a kwance kawai, ba abinda ke tada ta sai sallah.
Ta kashe wayoyin ta bakidaya tana wani irin jinyar zuciyar ta, da jinyar matacciyar gangar jikin ta kamar wadda ke fama da cutar paralysis, sabida yadda ta bi ta rafke akan gado, kokwakkwaran motsi bata yi, sallahr ma bata sanin lokaci yayi har sai Nene ta leko ta shaida mata cewa an yi kiran sallah.
Tun daga ranar da aka kara daura musu aure uffan bata kara cewa ba, domin kalaman Habibu na ranar da ya zo, sun yi wa zuciyar ta lahani da barna mai yawa.
Idan ta yi tunanin wai yanzu ya kara zama mijin ta na sunnah, sai duk wani kyakkyawan tunani ya subuce mata. Ta rasa wanda za ta kama.
Bata da tsumi ba ta da dabara a halin yanzu, sai na irin zaman da za ta fuskanta nan ba da jimawa ba a gidan Nahuche, a karo na biyu!
Ita dai ta san trial din ta da Habibu bai kare ba, akwai sauran manyan kalubale da ya tanadar mata, wadanda suka fi na baya. Domin ya rama abinda ya ke ganin ta yi masa. Abinda za ta rike a matsayin makamin ta yanzu shine kadai (maintaining self-esteem) din ta, na cewa ta fi gaban duk wani wargin sa a halin yanzu, za ta nuna masa cewa wata fuskar yanzu ta fi gaban mari. In Rahinah ya sani, wannan Rahinatu ce, warki daidai kugun kowanne da namiji.
Daga ita har shi sun kasa kulla komai sai tunani, wanda ya kasa basu mafita ga tarin damuwoyin su da tarin kalubalen da suke hangowa sake zama da juna, tunda dai har yanzu basu kai ga cimma matsaya kwakkwara wadda za ta yi maganin matsalolin su da rashin fahimtar da ke tsakanin su ba.
A nasa bangaren, Habib Nahuche, ya kudurce a ran sa ko kadan ba zai dauki rabin abinda ya dauka a baya daga Rahinah da sunan rashin SO ba, tunda dai yanzun ita ta amsawa kanta ba wani ya tursasata ba, don haka babu hannun sa a ciki. Nan kusa ma bai shirya mata tarewa ba ko inda zata zauna, don kamar yadda yace din ne da gaske bashi da bukatar ta cikin rayuwar sa ta yanzu.
Da dai Uncle da Ambasada sun sani da sun bar bygone a muhallin ta, don basu gama sanin ko wacece ‘yar su Rahinah ba har gobe, shiyasa suke tsammanin da zuciya daya ta amsa, shi kam ya dade da sanin cewa ya riga ya bata baya. Ya manta da ya taba auren ta, ya dade da karbar rayuwa a yadda ya same ta, kuma yana jin dadin ta a hakan. Da Rahinah, da babu ita, ba zai kasa rayuwa ba, insha Allahu.
Me jiya ta yi bare yau? Abin nufi me rashin ta na shekaru goma ya kara musu ko ya hana musu shi da Abdallahn?
Da wannan jinyar zuciyar kowannen su ke jibge akan gadon sa, ya dakatar da kowanne ayyuka na cigaban rayuwar sa da dailyactivities din sa.
Amma ga iyayen su da masoyan su abin ba haka yake ba, aunty Badiya, a ranar don farin cikin an daura wa Habibu aure da Rahinah, sai da ta kai goshin ta kasa ta yi sujjadar shukr, ta kuma dafa abinci mai rai da motsi ta rabawa mabukata sadaqah.
Hajiya Kaltume kuwa, ko da bata maraba da Rahinah, farin cikin yau Habibullahi yayi aure da azumi ta tashi a bakin ta.
Itama ta sa an dafa abincin sadaqa an raba a Kofar Jange har gidajen makwabtan ta, ko dama duk Juma’ah tana bada sadaqar naman saniya, da ake kayarwa a rabawa mabuqata na Kofar Jange, ranar da Uncle Usman ya tabbatar mata sun dauro auren suna kan hanyar dawowa Shanu uku ta sa aka kayar don yin sadaqah.
Nene Balki da Yafendo kuwa suna can suna yi wa Rahinah kyakkyawan shiri irin na iyayen kwarai masu shirin kai ‘yar fari daki, Nene tayi ordern kayan gyaran mata ‘yan gaske tafiyayyu tun daga Nijar. Ta kuma yi Magana da Yagana ‘yar Maiduguri mai yi mata gyaran jiki kan ta zo a washegari ta fara gyara Rahinah.
Sahura mai aikin Rahinah tana Kaduna, da Anty Badiya ta yi mata waya ta ce su fara shirin tarewa har rawa sai da ta taka. Don haka duk wani masoyin su cikin farin ciki yake, ya kuma ci wa auren nan alwashi da buri sabanin ma’auratan, wadanda ke ganin tamkar Alkiyamar su ta matso.
Kowanne gani yake an katse masa rayuwa an kuma hada shi da alaqaqai, tunda kar ce ta san kar, kowanne da irin alwashin da yake ci wa zuciyar sa a kan dan uwan sa.
Shi dai Habibu alwashi ya ci ba zai bari Rahinah ta shiga tsakanin sa da dan sa ba, tunda tare ta gan su, ta sake kutsowa cikin rayuwar su don ta kara tarwatsa ta.
Ita kuwa Rahinah abu daya ne yake sassauta zuciyar ta in ta tuna yanzu zata samu kusanci da Abdallah. Za ta maida hankalin ta ne kacokam kan cike wawakeken gibin da Habibu ya samar a tsakanin su wanda ta san ba zai yiwu a lokaci guda ba, sai ta yi da gaske wajen kwatowa kan ta soyayyar dan ta, ta cike ratar da Habibu ya janyo a tsakanin su.
Wannan shi ne kadai abin da zai zaunar da ita a gidan Habibu Nahuche amma ba Habibu ba; soyayyar dan ta Abdullahi!
Uwa uba farin cikin iyayen ta da kwanciyar hankalin su wato Ambasada da Uncle Usman. Ita kan ta Aunty Badiya Rahinah tana darajja ta, bata jin Habibu ya isa ya farraqa tsakanin su.
Domin Badiya ta kaunace ta kauna ta hakika tun kafin ta san alaqar da ke tsakanin su. A lokacin da ta ke neman dangin da za su rungume ta. Don haka ko wanene Habibu ga Badiya alaqar su mai kyau tana nan bazata taba canzawa ba saboda shi.
******
*Na huce* is not free.
It’s 1000 via 3094856450
Sumayyah Kabara Firstbank
Shaidar biya
07030137870
[13/08, 10:20 am] Ummah Salisu: *SUMAYYAH ABDULKADIR* 07030137870
*NA HUCE*
*ZAMFARA*
Dr. Badiya ta isa Zamfara yamma lis, domin su hadu ita da Hajiya da sauran ‘yan uwa su shirya yadda tarewar Rahinah za ta kasance. Ta sha kiran Habibu a waya tun daga ranar da aka daura aure, ba don ta yi masa albishir din komai ba sai don ta ji lafiyar sa. Duk da ta san fushi ya ke da su daga ita har Daddyn Musaddiq tunda su ne silar komai, silar sake kulla masa Rahinah Omar a matsayin matar sa, amma duk sanda ta kira sai ta samu duka wayoyin sa a kashe suke.
A karshe ta kira PA din sa na Lagos wato Mr. Rasak, shi yake gaya mata Ogan sa ya dauki hutu baya ganin kowa kuma baya amsa wayoyi, tace ya kai masa wayar, ya ce daga gida Zamfara ne. Amma sai ya ce mata “I’m sorry Ma, bani da hurumin yin hakan, bai bani damar zuwa inda yake ba, in ba shi da kan sa ya neme ni ba.
Amma ki kwantar da hankalin ki lafiyar sa kalau, don Cook din sa ya tabbatar min yana dan cin abincin da yake kai masa”.
Aunty Badiya ta yi a jiyar zuciya, a zuciyar ta ta yi alkawarin sai ta ji abinda ya hada wannnan gabar tsakanin Habibu da uwar dan sa Rahinah daga bakin ita Rahinah, don ta tabbata Habibu ba zai taba gaya mata ba.
Abinda Badiya bata sani ba shine har gara Habibu wani lokacin akan Rahinah wajen taurin kai da zurfin ciki irin na Fulani.
Badiya ta lura yau annurin da ke tare da Hajiyar su ma daban yake, alamu ne masu kyau na ta fara sakin ran ta a kan auren. Bayan sun gaisa ta ce “me yasa bata zo mata da Zarah ba ta debe mata kewar Abdallah, tunda Juniour din uban sa ya dauke shi? Don ya gwada musu shi ke da iko da dan sa?” Badiya ta bata hakuri tace “Zarah na da (common entrance exams) shi ya sa basu taho tare ba”.
Hajiya ta ce “me kika tsara game da tarewar ‘yar taki? Ta wani fannin kanwar taki? Kuma yaushe zaku je ku dauko ta?”
Badiya ta langabar da kai cikin damuwa ta ce “Hajiya ina naga Habibun balle mu tsara tarewa? Ko waya ya daina amsawa tun daga ranar da aka daura aure”.
Hajiya ta jinjina kai ta ce “shin wai ni menene hakikanin matsalar su ne? Sama da shekara goma kullum magana daya yake yi a kan ta “ba ta son shi” ku kuma kun dage sai ita, tunda ‘yar ku ce. Amma ai gara ka auri wanda ke son ka, a kan ka auri wanda kake so, ba ya son ka”.
Badiya ta ce “ai ki bar maganar rashin so a tsakanin su Hajiya, tsabar iya shege ne kawai. Sabida son junan su suka kasa aure kowa ya shaida wannan. Manema ba irin wadanda Allah bai baiwa Rahina ba, har da ‘yan asalin kasasshen larabawa, shikuma Habibu wadanne irin mata ne ba’a kawo masa ba? Ko bai gani a duniya ba?
Don haka ni bana regretting maida auren nan da su Daddy suka yi kuma har abada ba zan yi nadamar hakan ba. Sannan Daddy ya gaya min da amincewar ta suka maida auren, ba tursasa ta suka yi ba.
Sanda suka hada kan su a can wata uwa duniya suka yi aure har suka haifi da ai bamu sani ba, basu yi shawara da mu ba, to haka yanzu ma, sanda zasu daidaita kan su, su yi wa kan su maganin matsalar da suke da ita baza mu sani ba Hajiya. Ko labari ba zamu ji ba. Tunda dukkan su ba yara bane.
Abinda yake hakkin mu shine mu tabbatar Habibu ya zama cikakken mutum ta hanyar cika sunnar Manzo SAW, haka itama Rahinah, abinda ya ragewa Baban ta kenan, ya sada ta da dakin aure don cika amanar dan uwan sa marigayi.
Don haka ta fannin mu mun sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu. A dai wadannan shekarun na Habibu da ya dace ace yana da ‘ya ‘ya hudu ko biyar.
Don haka Hajiya ki daina fargaba kan duk wani nunkufurci da zai nuna, ina mai tabbatar miki a zuciyar sa farin ciki ne zallah, jin zafi ne kawai akan abinda ta yi masa wanda su kadai suka san shi, kuma a hankali bacin rai mai gushewa ne. Amma soyayya ba mai gushewa bace, da sannu zan binciki ko ma wace irin matsala ce a tsakanin su don a magance ta”.
Hajiya Kaltume ta ji dadin bayanan babbar ‘yar ta Badiya, hankalin ta ya kara kwantawa. Domin hakika a baya ta shiga rudani akan auren, sabida yadda Rahina ta fita fit! Daga ranta, yanzu kuwa Anty ta dan kankaro mata mutunci tunda ta ce da ita tana son Habibullahi itama, bacin rai ne ya sa ta kai shi kotu, sannan ba shi kadai yake koshin wahala ba, itama kuma ta dandana rashin auren na shekara goma a kan sa ba don ba ta da manema ba.
“To yanzu ta yaya kike ganin tariyar zata kasance tunda kin ce ko waya ba ya dagawa? Nima bai kira ni ba. Bana so iyayen ta su gane baya murna da komen auren”.
Hajiya ta fada cikin damuwa, Badiya ta ce “tattaki zamu yi har Lagos din mu same shi, ni da ke da Baban Musaddiq, sai dai kawai ya gan mu a gidan shi, in ya so ayi wacce za’a yi ya fadi duk inda yake son ta tare. In gidan shi na Abuja ne? In kuma Lagos din za’a bi shi da matar shi to duk ya fada, ba zai mai da mu kananan mutane a idon surukai na ba.
Habibu yayi kadan ya dinga juya mu, wanda yayyi a baya ma ya isa. Hajiya sanyin ki yayi yawa a kan Habibu shi yassa yakke yin yadda yagga dama”. Murmushi Hajiya Kaltume ta yi ta ce,
“to Badiya in ban tausasa masa ba wa zai tausasa masa shi ba mata a gida ba? Mu bi komai ta nutsuwa. Kuma a hankali, abinda lallashi bai bayar ba tursasawa ba zata bayar ba.
Ni babu Ikkon da zan iya zuwa, kafafun nan bazasu jure hawa jirgi ba don kwanannan ba dadin su nake ji ba, ku dai je ke da mijin ki amma don Allah ku lallabashi ku lallashe shi”.
Dariya Aunty Badiya ta yi, “Habibullahi autan Hajiya!” Hajiya tace “na ji din”.
A haka suka tsayar da maganar, cewa a gobe, kwanaki hudu da daurin auren, Uncle da Aunty zasu bi jirgi zuwa Lagos domin su tadda Habibu a gidan sa.
******
Rahinah na kwance rigingine a dakin ta bisa gado, cikin dakin ta na gidan Ambasada Shehu, ita ba barci ba ita ba ido biyu ba, Allah kadai ya san abinda ta ke sakawa tana warwarewa a zuciyar nan tata. Wadda ke cunkushe taf da al’amura daban daban duk a kan komen ta gidan Uban dan ta Habibu Nahuche.
Nene ta yi sallama a dakin, biye da ita wata bakar babarbariyar mace ce, ta yunkura kadan ta tashi zaune tana amsa musu da kyar, kallo daya Nene ta yi mata ta gane tun safe bata yi wanka ba. Ta ce “anya Rahinah? Wannnan wace irin amarya ce? To tashi maza in hada miki ruwan dumi ki yi wanka, ga Yagana ta zo zata fara miki gyaran jiki yanzun nan”.
Kamar mai fama da ciwon baki ta motsa bakin ta kadan tana tambayar Nene “wane irin gyaran jiki Nene?”
“irin wanda ake yi wa amare ‘yan gata mana! Wadanda ake so mijin ya so su, ya gigice a kan su, balle mazan duniya irin Habib Nahuche wadanda ba irin matan da basa gani suna zarya a hotel”.
Murmushi ta yi mai ciwo, ta ji ta kara tsanar auren bakidaya, har gara mata sanda yake dalibi akan yanzu da ya zama mai budadden ido, tace,
“Nene ki yi hakuri ki sallami Haj. Yagana domin bana bukata, bazan yi ba”.
Nene ta ce, “wannan ne kuma baki isa ba, in kika yi min musu in kira Yafendo yanzu ta wanke min ke tas. Wawuya kawai ana nuna mata abinda ya dace tana shirme”.
Ala dole ta mike cikin dacin rai ta zuro fararen kafafun ta kasa, sumul sumul da su tamkar bata taka kasa. Suka nufi toilet tare da Nene.
Nene Balki ta hada mata ruwa mai zafi a kwami ta yi wanka da kyau sannan ta fito, hatta cikin ruwan wankan ta saida Yagana ta zuba turarukan humra wadanda take tafe dasu.
Lokacin da Rahinah ta fito daga wanka sai mai gyaran jikin ta hau aikin ta a kan ta, ta yi mata Dilke da Halawah ai kuwa ta ci kwakwa kasancewar ta mai yawan sumar jiki, a zuciyar Yagana mamakin kyawun jiki da kyawun fata irin na Rahinah take yi tana tazbihi ga Sarkin halitta. “Rahinah matar manya ce, Allah SWA ya kyautata halittar ta. Tana ta tsokanar ta da cewa
“Amma Anti Rahinah angon ki ya more!”.
Bata san bakanta mata ta ke da wadannan kalaman ba. Wai angon ta! Don haka ta zabga mata harara kasa-kasa.
A daren ranar Ambasada ya kira Rahinah falon sa, ga Nene a zaune, yayi mata nasiha mai ratsa jiki da bargo irin wadda ta dace kowanne uban kwarai ya yiwa diyar sa da zai kai gidan miji, don ko Safeenah iyaka abinda ya gaya mata kenan da zai kaita gidan nata mijin shekaru biyar a baya (da jimawa an yi wa Safeenah aure a Jos, ta auri wani Navy Officer Suhail Sajoh a can amma bata haihu ba har yanzu). Sannan ya kawo mukullin sabuwar mota irin tata ta baya ya bata, yace ta barwa Musaddiq tata.
Rahinah sai da ta yi hawaye, a zamanin nan samun mutanen kirki irin Ambasada da iyalan sa masu halin maida dan kowa na su zai yi wuya. Mutane yanzu kowa dan sa ya sani bale wanda baku hada alaqar jini da shi ba sai ta mutunci. A karshen nasihun sa Ambasada ya ce.
“Ina fatan matsalolin ku da kuka kunshe cikin cikin ku, ku kawo karshen su yanzu da kyakkyawar fahimtar juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci dan ku da sauran kannen sa masu zuwa a gaba”.
Ta rasa ina zata sa kanta yau, don yanzu ta gama saddaqarwa ta tabbata matar Habibu Nahuche a karo na biyu.
Washegari suka kama hanyar Adamawa duk gidan, har da Safeenah wadda ta zo tun jiya daga Bukuru, tafiya ce su ke yi mai dadi yau, domin hatta ruwn da zasu sha a hanya da abincin da zasu ci sun tanade shi tun daga gida sun zuba a kuloli sun tafi dasu domin tafiyar wuni guda ce curr. Raha kawai suke suna tsokanar Rahinah wadda bata iya tankawa kowa.
Safeenah ta ce “sai ni babbar kawar amarya, amara kirjin biki” bayan a baya sam bata shiga harkar Rahinah har zuwa sanda aka yi mata aure, amma yau kam ta ware sai tsokanar ta take yi don ta fahimci bata son komen.
Sai bayan isha suka isa Girei, a dakin Uwargida Dudu su Yafendo suka sauka, Rahinah da Safeenah suna dakin Surbajo amaryar Sarkin Fulani.
Duk ‘ya’yan Sarkin Fulani da da ke gidan aure a washegari suka zo gidan tun da safe suka taya iyayen su dora tukwane. Sarkin Fulani yasa aka kada shanu har biyu don a yi hidimar abincin biki dasu. Ya kuma gayawa Usman ya gayawa matar sa cewa duk hidimar aure da ake yi na al’ada a garin Girei bai yarda ba sai an yi wa Rahinah, don haka yana umartar sa da ya gayawa angon da iyayen sa.
Uncle Usman ya gayawa Badiya sakon Sarkin Fulani, ya kara da cewa ya ce ba zai basu Rahinah su tafi da ita ba sai sun sauke duka wannan nauyin na al’adar su.
Na farko tunda an daura aure gabanin kawo wadannan kayayyaki na al’ada to sun zama bashi dole ango da iyayen sa su kawo.
Kayan aure wato ‘lefe’ shi ne na farko, sannan zasu kawo ‘suddaje’ ga dangin amarya, wato turamen Atampha guda dari, sai akwatin Uwa da na Uba duka za’a hada a kawo mana su tare da kayan aure.
Mu kuma zamu yi wa dangin ango ‘paute’ kwatankwacin yawan kayan auren d suka kawo mana (Paute shine kaiwa dangin miji kwanukan samiru, kuloli, gado da katifa da kayan abinci kamar ‘gara’ a harshen Hausa amma ya banbanta dana Hausawa) domin su rarraba a tsakanin su. Ana yin paute ne iya yawan kayan aure da dangin ango suka kawo.
Bamu sani ba ko a taku al’adar ta Zamfarawa kuna yin ‘Fansar Ido’ wato (budar kai) a hausance, wanda shi dangin ango ne su ke shiryawa washegarin kai amarya gidan ta, a family house din su inda dangin sa da nata za su tara musu kudi daidai karfin su da iyawar su. Mu anan har yanzu muna yin shi madadin ‘zaman Ajo’ da ake yi a baya, in kuma baku yi a can Zamfara to ya rage naku.
Mu dai ‘yar mu yanzu ne muka san zamu yi mata aure ba ruwan mu da wancan gantalallen auren da suka yi, don haka duka binda ake yi wa budurwa shi zamu yi mata. Bamu dauke muku komai ba”.
Ai jin haka a wuni guda Aunty Badiya ta hada lefe na gani na fada, ko dama can tana da niyyar lefen, ta bari ne sai bayan tarewar Rahinah lokacin ta nutsu, amma tunda ga abinda Kakanta ya ce ai bata ga ta zama ba.
Ta kuma gayawa Hajiyar su komai, a take suka fidda makudan kudi don gudanar da komai ko ta kan Habibu basu bi ba, har ninkin abinda sarkin Fulani ya lissafo suka yi. Daga Nahuche suka hadu suka wuce kai tsaye zuwa garin Girei ita da kafatanin matan family din su, cikin su har da kanwar Habibu da ya ki aure wato Shafa’atu wadda ta taho tun daga Talata-mafara ta tadda su a Nahuche bisa umarnin mahifin ta, don dai a gyara zumuncin da ya samu tangarda na shekaru masu yawa.
Kasancewar mahaifin Habibu baya raye, Baban Shafa’atu da ke bin sa shine matsayin mahaifin sa a yanzu kuma madaurin auren sa.
Ai kuwa sun ga karba ta girma wajen iyalin sarkin fulanin Girei, fura da nono kindirmo sabuwar tatsa, soyayyun zabbi da kaji, faten achcha da yaji ganyen rama, gudun kurna da miyar taushe sune abinciccikan da aka sauke su da su. Uncle Usman kuma ya kama musu gidan saukar baki na Girei Motel inda zasu sauka har a gama biki. Baza su wuce ba sai tare da amarya.
An yi biki na al’ada cikin karamci, karramawa da mutumta juna, sarkin Fulani da rigima, ya ce shi fa bai gane ba, har yanzu bai ga ango ya zo ba, to bai basu amarya (su Aunty Badiya) sai angon ya tako da kafafun sa ya zo duk mukamin sa.
Duk da uzurin ayyuka da Uncle Usman da Aunty Badiya suke ta bayarwa a kan Habibun don basa son bada wata kafa da mata zasu san somethingisfishy tsakanin Habibu da Rahinah. Daga nasu dangin na Nahuche da dama suke kullace da shi tun a kan Shafa’atu har dangin ita Rahinah.
Amma sarkin Fulani ya san komai, duk shawarwarin da ya baiwa Usman da Ambasada na kada a turasasa su da su suka yi amfani, sun bi shawarwarin daya bayan daya, sun basu dama don su yi sulhu kafin su maida musu auren, sun kuma nemi yarda da amincewar Rahinah.
Duk da Uncle Usman da Ambasada sun san ba wai tsugunne ta kare bane tunda ba wai sun daidaita bane baka da zuci, amma a hakan ma suna masu farin ciki matuka, Ambasada ya san with time, a irin son da ya san su duka suna yi wa dan nasu, zasu yarda su manta komai su kuma manta baya su hada kai su raine shi.
Tun kafin a kammala bikin Uncle Usman da Aunty Badiya suka zare jiki don tafiya Ikko su tadda Habibu, don sun san Sarkin Fulani da gaske yake, ba zai bada Rahinah ba sai ya zo da kan sa. Duk da cewa cikin raha ya fadi umarnin nasa, bafillace ne mai Magana guda daya a duk yadda ya fade ta.
Cousins da Nieces din Rahinah da ‘ya’yan Inna Dudu su biyu ana kiran su Kubra da Ladi su suka yi mata kwalliya ranar yini da fararen kayan saki, murjani da sauran duwatsun da Fulani ke ado da su, kada ki so ki ga yadda Rahinah ta bada wata irin kala a yau, ita ba balarabiya ba ita ba bafullatana ba haka ita ba ba’indiya ba.
Safeenah sai daukar ta a hoto ta ke da digital camera da wayoyin ta, tana fadin “da inada lambar wayar Uncle Habeeb, da yau ya sha kallo, don da duka sai na tura masa” Ladi ta ce “ba an ce kanin Aunty Badiya bane matar Baba Usmanu?” nan Ladi ta ce zata karbo lambar sa wajen Maman Musaddiq a tura masa wadanan hotunan. Rahinah ta galla mata wata muguwar harara ba tare da ta kula ba.
Amma Ladi ta nemi Badiya sama da kasa a gidan ta rasa, da ta tambayi mahaifiyar ta Inna Dudu sai ta ce ta tafi unguwa, itama bata san inda ta tafi ba. Dole zancen turawa Habibu hoto ya sha ruwa. A lokacin Uncle da Aunty suna cikin (Arik-Air) mai zuwa Lagos.
*******
*LAGOS, NIGERIA*
Uncle Usman Girei da mai dakin sa Aunty Badiya Nahuche, sun sauka a garin Lagos da yammaci, da taimakon waya da suke ta yi da PA din sa na Lagos watau Mr. Rasak. Shi ya zo da daya daga cikin motocin daukar baki na *NAHUCHE HOTEL (LAGOS)* ya dauke su kai tsaye zuwa gidan Habibu da ke Ikoyi. Don daga baya ya baro hotel din ya koma gidan sa.
“Pls Uncle, don’t mention my name”.
Mr. Rasak ya roki Uncle Usman, wato kada ya sa da shi kan taimakon da yayi musu na kai su gidan sa. Don kuwa bai basu damar gayawa kowa yana gida ko yana hotel ba, shi kuma yayi duba ne da cewa Aunty Badiya ce, da mijin ta Uncle Usman wadanda matsayin iyaye na halali suke ga maigidan nasa.
“Kada ka damu Rasak, ka koma bakin aikin ka”, inji Uncle. Yayi musu sallama ya juya bayan ya nuna musu kofar falon da Habibu ke ciki, wadda dakin barcin sa ma yana ciki.
Ginin gidan Habibu na Ikoyi ya burge su ba kadan ba, domin yafi gidan sa na Abuja kyau da tsari nesa ba kusa ba. Sosai Badiya ke bugun kofar babu sassauci da hannayen ta biyu, Uncle kuma ya hau rafka saallama. A lokacin Habibu na kwance rigingine bisa makeken gadon bedroom din sa. Shi ba barci ba shi ba ido biyu ba.
A hannun sa carbi ne dan karami yana ja, don bai dade da idar da sallahr maghriba ba.
Bugun kofar da ya ji ana masa ya bashi mamaki, don ya san ma’aikatan sa baza su yi masa wannan rashin hankalin ba. Sai kawai ya mike ya kunna CCTV camera din sa don dai ya ga ko wanene, ya tabbata dai ba kukun sa bane don lokacin cin abincin daren sa bai yi ba ko mai yi masa share-share. Mr. Rasak bai zo ma a ran sa ba don ba lokacin zuwan sa bane kuma ba ya zuwa sai ya neme shi.
Wadanda ya gani a bakin kofar ya sa shi saurin sauya sutturar jikin shi daga pjs zuwa jallabiyya ruwan madara mai santsi, ya tako cikin nutsuwa irin tasa zuwa falon, daga nan ya bude kofar da Badiya ke neman ballawa.
“Easy mana Maman Musaddiq, kin san bana son hayaniya” ya fada yana bude kofar yana yamutsa fuska, Aunty ta balla mai harara, a lokaci guda tana mai bin sa da kallo daga sama zuwa kasa.
Sai ta ji duk jikin ta yayi sanyi kuma, a lokacin da ta ga irin ramar da kanin nata yayi, Habib Nahuche, wanda yake healthy and energetic a kullum, yau tamkar wanda ya kwanta jinyar sati biyu.
SO, a harshen hausa, LOVE a harshen turanci, HUBB a luggar larabci ba karya bane, it’s human nature, wato halittar ubangiji ne a zukatan ‘yan adam da babu dan adam din da ya isa yayi yadda ya ga dama da shi ya kuma zauna lafiya.
To Habibu da Rahinah sun ce zasu iya yin yadda suka ga dama da SO. Ko shiyasa dukkannin su suka kasa zama lafiya?
Uncle Usman ya ce “Ango ne haka!” Sai ya basu hanya suka wuce zuwa ciki, yana yi musu sannu da zuwa cikin girmamawa, fuskar shi babu murmushi he looks moody, babu far’a ko kankani haka babu alamun yayi maraba da zuwan su a lokacin da ba abinda yake bukata fiye da kadaicewa.
Suka zazzauna kujerun alfarmar da ke falon har da shi, Aunty na karewa kayataccen falon kallo daga sama har kasa, sai ya dauki wayar land-line wadda iyakacin ta cikin gidan, yayi wa kukun sa Lawrence Magana kan ya shirya wa su Uncle abinci da gaggawa.
“Ba abinda ya kawo mu ba kenan ka bar abincin ka, mun zo ne takanas don ka gaya mana inda Rahinah zata tare, Abuja ko Lagos ko kuwa Port Harcourt? Ka kuma bamu mukullan inda ka zaba mata a hannun mu, sannan mu tasa ka a gaba zuwa Girei, ka je ka amshi auren ka da kan ka”.
Inji Aunty Badiya, Uncle Usman kuma ya ce
“ina Abdallah da ka dauke mana??”
Sai ya rasa wa zai fara amsawa cikin su, don kowannen su a kage yake da son jin amsar tambayar sa, tunani daya ne ya zo wa Habibu a wannan lokacin kuma kyakkyawan tunani ne;
Cikin abubuwan da Rahinah ke kullatar sa a kai, har da rashin zuwa neman auren ta hannun iyayen ta cikin daraja da mutunci sai wasu banzaye can, for the second time, sai ya ji ba ya son maimaita wannan kuskuren kamar yadda Aunty ta ce ne ya kamata ya je GIREI, yayi duk abinda ya kamata mai neman aure na hakika yayi wajen iyayen Rahinah, sannan ya nemi gafarar su a kan auren ta da yayi a baya a urunce, ba da yawun su da cikakkiyar yardar su ba.
Ko meye ke kwance tsakanin sa da Rahinah Omar (this one is a compulsory duty) da yake tamkar nauyi a kan sa da dole ya sauke. Maganar ya ce baya son Rahinah, ko ya daina son ta, ko ya cire ta bakidaya daga ran nasa is a fable. Wani abu ne da yafi kama da yaudararkai. Abinda yake zahiri inreality shine ya na jin zafin ta, ya hakura da ita ne sabida wulakancin ta, rashin afuwa da kafiyar ta. Da kuma tursasa shi da ta yi ya sake ta ba da son ran sa ba.
Ya hakura da ita ne sakamakon ta kasa yi masa adalci shi da dan sa Abdallah, ta zauna da su ta yafe masa, maimakon hakan sai ta dubi maslahar kanta kadai ta ki karbar kaddarar da ta fada musu su duka.
Shima bai je Jamus don yayi aure ba, ya je ne don yayi karatu kamar yadda ta je yi, amma bai isa ya kori kaddarar sa ba da kuma rabon da ya rantse a tsakanin su.
Da wadannan laifuffukan zai cigaba da challenging Rahinah Omar daga nan har karshen rayuwar su. A wurin sa ta zalunce su shi da Abdallah zalunci na deprivation. Idan har ba ita ta san yadda ta yi ta wanke kanta daga cikin su ba (laifuffukan da yake tuhumar ta a kan su) ta hanyar da kowacce macen kwarai ke yi wa mijin ta da dan da ta Haifa.
Wanda ya san ba abu ne mai yiwuwa ba daga Rahinah Omar, a irin girman kan ta da izzar ta, taurin kan ta da ji da kan ta. Sannan da kafiya da tsayuwa a kan ra’ayin ta.
Bakin alkalami ya riga ya bushe a tsakanin su, don haka ya san ta inda zai bullo mata da wadannan baudaddun halayen da dabi’un nata.
Da wannan tunanin ya yankewa zuciyar sa zai je Girei, ya karbi auren Rahinah, kamar yadda kowanne mijin kwarai ke zuwa gun surukan sa ya yi duk abinda ya kamata tunda ya amince, ya yardarwa kan sa har gobe YES! Yana son Rahinah a duk yadda Allah ya halicce ta.
Ita kadai yake so, ita kadai yake bege. Daga kan ta ya rufe so, daga kan ta ya dade da jingine so a muhallin sa.
Rahinah Omar. Za ta ci albarkaci mai yawa a yanzu; albarkacin dan su, da albarkacin iyayen ta. Da gaske iyaye da dangi martaba ne kuma sutura ne, domin a baya da tana da su ya san da bai samu damar da ya samu a kan ta ba.
Sai ya ji duk jikin sa ya yi sanyi da tunanin sa ya zo nan.
******
NA HUCE is not for free. It’s 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank.
SHAIDAR BIYA
07030137870
[13/08, 10:26 pm] Ummah Salisu: A hankali ya sunkuyar da kai, kafin ya dago ya dubi Yayar sa da mijin ta.“Ku yi min alfarma ku ci abinci ku yi sallah ku natsa” yace da su finallycikin muryar sanyi, bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, daga Aunty har Uncle basu katse masa hanzari ba sun bashi dama yayi tunanin sa positively.
“Ba zan iya cin wani abinci ba sai ka tabbatar min zaka bi mu zuwa Girei Habibu”. Inji Badiya.
A hankali ya gyada mata kai alamar zai bi sun. Uncle ya ce, “to alhamdulillahi, ina Abdallah? Cikin kunkuni ya ce.
“Ba zan gaya muku inda yake yanzu ba don ban shirya ba da shi ga uwar shi ba”.
Dariya Aunty ta yi, sabida farin cikin ya yarda zai bi su zuwa Girei kadai ya karbi auren sa da kan sa ya wadatar da ran ta.
“Can ta matse muku, a bamu masauki mu je mu huta”. Inji Aunty.
Waya yayi wa mai kula da share-sharen gidan ya zo ya tafi dasu sassan baki, Kuku kuma tuni ya shirya musu abinci ya kai, ya san ba wanda zai yi masa wannnan karambanin na kawo su Anty Ikoyi sai Mr. Rasak.
Amma bai ce masa komai ba don shima yanzu ya ji dadin zuwan nasu, domin ya yaye masa damuwar da yake ciki kaso tamanin cikin dari 80%. Kuma shine babbar maslaha ga mutuncin sa aidanun iyayen Rahinah, dama ita Rahinar kan ta.
Ba wai sulhu yake nema da ita ba, illa shi mutum ne mai yawan submissiveness, wanda idan yayi laifi ya kuma gane daga baya yayi laifin, ko aka nusar da shi, yake gaggawar mika wuya nan da nan ga gyara wannan laifin.
Sun tattauna sosai a daren shi da ‘yar uwar sa. Duk abinda suka kashe ita da Hajiya da Uncle da su Baban Nahuche wajen hidimar auren sai da ta kwashe ta labarta masa, don ya san ba a banza ya samu Rahinah ba wannan karon.
Tace atampopin ‘suddaje’ kawai daga Super sai Holland muka zuba, sauran da suke kanana ‘yan uwa ne suka baka gudummuwar su har da Shafa’atu”.
He felt loved! Sabida ko kana da shi, idan ‘yan uwan ka da iyayen ka suka yi maka aikin zumunci da kara irin wannan dadi ka ke ji. Ya ce da Anty zai maida mata kudin kayan suddaje din da na lefe cikin account din ta, Aunty ta harare shi nan ta hau shi da fada, inda ta ce,
“ka ji min yaro, lefe ai gudummuwata ne dama, suddaje gudumuwar Hajiya, Paute gudummuwa ne daga gare mu zuwa ga zuri’an amarya, sauran hidimdimun kuwa duk daga ‘yan uwa na Nahuche suka fito, fatan mu Habibu kada ka bamu kunya, ka zauna lafiya da uwar dan ka, domin dukkan ku kuna bukatar juna”.
Bai ce komai ba, domin duk jikin sa ya yi sanyi, sai ya samu kan sa yana mai tambayar kan sa da gaske yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa ta yanzu ko kuwa Anty ta dai fada ne don ta ji dadin bakin ta???
Daga can kasan ransa sai ya ji wani sako na amsawa da cewa “YES! Har gobe yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Irin bukatar da nisan shekaru ko tsufa ba ya taba canza ta.
Iyayen sa da ‘yan uwan sa basa bukatar komai daga gare shi duk da Allah ya bashi wadata, burin su kadai ya zama cikakken mutum ta hanyar yin aure da wadda suka tabbatar ita kadai yake so.
Ko don albarkacin Hajiya, Yayar sa Badiya da Uncle Usman zai sassautawa zuciyar shi, zai karbi Rahinah da duk irin fuskar da ta zo masa; da tsiya ko da arziki. Wato duk irin rayuwar da ta zaba musu ita za su gudanar.
Aunty ce ta katse masa tunani da cewa “in aka zaba mata ta zauna?”
Ya dan zakuda kafada yace “I have no idea. The choice is her’s (wato zabin nata ne). Tunda ni ba mazauni bane na wuri guda ba”, Aunty ta ce,
“na san ma Abuja za ta zaba, ko don saboda ayyukan ta”.
Dan kyabe baki yayi irin na ba matsalar sa bane wannan.
A daren yayi musu booking din jirgin da zai juya da su Adamawa a washegari har da Mr. Rasak wanda ya nemi alfarmar halartar auren Ogan su, don Aunty ta gaya masa tun jiya da ya dauko su.
“Halan bai gaya muku cewa shi ango bane ko? Maman Abdallah za ta dawo!”.
“Congratulations Oga, congratulations Boss!”
Inji duka ma’aikatan gidan.
“May yours be among the best!”.
Kowa sai da ya fadi irin fatan alkhairin sa, domin hakika sun yi farin ciki.
Washegari tun sassafe gabadayan su suka biyo Arik-Airdaga Ikko zuwa Adamawa.
******
Add Comment