Malamai Ne Sila Hausa Novels Complete
MALAMAI NE SILA
By
Usaina Adamu Usman
*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER’S ASSOCIATION* (A.Y.T.W.A)
Page 1
Wata Ƴar budurwa ce da shekarunta Bazasu wuce goma sha shida ba, a duniya, sanye take da kayan makaranta, tafiya take cikin nutsuwa da kamala, da alama makaranta zataje, jitayi anrufe mata idanu ta baya da hannu, “Khadija” shine abunda yafito daga bakinta,
Wani irin shewa khadija tayi, “ƴar gari yanzu na biya miki goggo tace kin tafi” ta fada tana murmushi, “ayya ai bansan zaki zoba, dana jiraki, kinga yau Monday muyi sauri kafin a fara assembly” wata uwar harara Khadija ta watsa mata a fakaice, “toh sarkin bin doka, ai dai ƙya bari mu fara zuwa gidan su Habiba ko, sai mu wuce tare da ita”
Halin Girma Hausa Novel Complete
“Aa gaskiya mu tafi, kar mujawa kanmu duka, kinsan yanzu haka ko tashi batayi ba”,”kee! dallah to saime idan munyi lattin, kinsan bamu da matsala dan ba shegiya ko shegen daya isa ya tabamu muddin akwai Vice da Uncle Abba” tsaki taja “ni dalla mushiga gashima har mun karaso” haka suka shiga gidan badan Zainab taso ba, saidan Khadijah ta matsa,
Ilai kuwa kaman yadda Zainab ta fadan ne, domin kuwa samunta su kayi tana brush, kallon su tayi tana buga uban tsalle, “yaya dai ƙawayen arziki, yanzu nake tunanin ku” matsawa Khadijah tayi kusa da ita, tana rada mata wani abu a kunne, tsalle ta kumayi a karo na biyu, “kice yau akwai chasu, bari nayi sauri na shirya” ta fada suna tafawa, ” bakwai da arba’in da takwas fa, dan Allah kiyi sauri ki shirya” Zainab ta fada tana kunbura fuska, “dan Allah Malama ki sauraramin, waima Khadijah ya akayi kuka hadu ne, dan nasan haka kawai bazata biyo min ba, hala a hanya kuka hadu da ita” ta fada tana jan tsakai, turata daki Khadijah tayi, “nide jiki ki shirya na baki labari a hanya” ta fada tana dariya,
Basu suka fito daga gidan su Habiba ba, sai takwas da ashirin, hankalin Zaynab idan yayi dubu toh ya tashi, su kuwa ko ajikin su domin kuwa dariya ma suke mata, a hanya ma haka suka tsaya a shagon chajin waya, wai zasu karba wayan khadija, sanan sukayi turin abubuwa, ita dai Zaynab binsu kawai take yanzu, dan kuwa bata da zabin daya wuce hakan, dan tasan idan taje makaranta yanzu zataci na jaki ne kawai, amman idan ta tsaya suka tafi taren ba mai tabata, saidai tayi missing darrusa da yawa,
Saida suka gama abubuwan da zasuyi kasan tara da rabi, sannan suka isa zuwa makarantar, suna zuwa makarantan Habiba ta ciro waya daga cikin jakar makarantar ta, Vice ta kira ringing daya ya dauka, babu jimawa sai gashi ya fito, ya shigar damu, sign yayi musu da ido, suma sukayi mashi, nide ba ganewa nakeyi ba, nan mukayi class dinma, nide na rigasu shiga Malamin yana kallon allo, nayi shiru, na samu waje na zauna,
Sukuwa su Khadija da Habiba da hayaniya suka shigo, jiyiwa Malam Sabitu yayi, yana kallon su, “yanzo kuka zo?” babu kunya ko tsoro suka ce masa, “eh” bai kuma bai ta kansu ba, ya juya ya cigaba da rubutun sa, baice su shigo ba, haka zalika baice karsu shigo ba, sukuwa da yake sun saba, ba tare da ladama ba suka koma wani class din da ba mutane a ciki, wayarta ta ciro ta kunna musu abinda ta turo wato blue film, Subhanallah, Allah ubangiji ta shiye mu, Allah ka shiya mana zuri’a, da yaran mu baki daya,
Comments
Like
Share
MALAMAI NE SILA
By
USAINA ADAMU USMAN
*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER’S ASSOCIATION* (A.Y.T.W.A)
Page 2
****
Gaba daya hankalin su yana kan abinda suke kallo a cikin wayar, fizge wayar da akayi ne yasa suka dago da kawunansu daga kan abinda suke kallo, a razane suke kallonsa saboda basuyi sammanin shine ba, idonsa ya dauke daga kansu ya mayar kan wayar shima yana kallon abinda suke kallo,
Harara Habiba ta dalla masa kamar idonta zai fado kasa saboda gaskiya ya tsorata su, cikin shagwaba tace “Uncle miye haka dan Allah kasan kuwa yadda ka firgita mu” murmushi yayi yana sosa keya, “haba Beauty mene abin tsoro kuma, wannan abinfa ba bokon mu bane ba nima anjima zaki tura min naje nasha kallo” ya karasa maganar yana kashe musu ido, “unlce ai kai bamuda matsala dakai, mun dauka ko wani ne daban” Khadijah ta fada tana binsa da wani mayatacchan kallo.
“To wai maima kukeyi anan?” cike da takaici Habiba tace, “wanchan dan rainin hankalin ne ya hanamu shiga saboda mun makara”,”Sabitu ne koh?”,”Ehh mana”,”Shine kuma kukazo nan kuka zauna, to kuzo na ai keku ku siyomin fura a bakin titi” batare da wata damuwa ba suka amsa da to suna mikewa, gaba yayi suna binsa a baya har staff room duk kusan malaman makarantar suna nan, hira malaman suka fara jansu dashi, suna wasa suna dariya, kudin furar ya miko musu suka karba suka fito, koda mai gadin makarantar ya tmby su inda zasuje, “Uncle Abba ne ya aike mu ko zaka hana ne?”,”aa mai gadin yace yana basu hanya saboda yasan halin Uncle Abba da rashin mutunci yanzo inya hanasu fita saiya iya zuwa yayi masa wankin babban bargo.
————Koda Malam Sabitu ya fita Zainab karbar note din da akayi tayi a wajan kawarta Safiya, note din ta Fara kwafa tana yin tsaki, break aka fita amma ita bata fita ba ta cigaba da rubutun ta dama ba fita takeyi ba, harta gama rubutun kota kan su Habiba bata kara bi ba.
Su kuwa cikin tasha suka shiga wajan yan fulanin da suke kawo fura da nono, siyawa Uncle Abba sukayi, sannan sukaje wajan mai taliya da kosai suka siya suka zauna a wajan sunaci babu kunya babu tsoran Allah, dubbin nan alumma suna wucewa suna kallon su saboda tsabar rashin kamun kai, saida sukayi nak sannan suka dawo makaranta sakon Uncle Abba suka kai masa, nan fa Malamai suka fara aiken su, siyo musu dan wake sai masu ruwa pure water, a haka sika wuni a gantale ba tare da sun shiga aji ba har lokacin tashi daga makaranta yayi,
Komawa aji sukayi dan su kira Zainab, samunta sukayi tana tattara littattafanta, “sarkin abi doka ai saikizo mu tafi ko?” ko kallonsu batayi ba ta cigaba da abinda takeyi, Khadija taja tsaki, “dan Allah kinga ki gyaleta kizo mu tafi”,”ki tsaya mana inma bazata bimu ba niga wayata nan ki bawa Sani ya sakamin chaji kafin mu dawo, “batanan zanbi ba” Zainab ta fada tana kokarin fita daga ajin, “haba ke kuwa kawata mai yasa baki ganewa sai kace ba yar gari ba” Khadija ta fada tana rike ta, “Zamuje raka Uncle Abba dubiya ne kinsan Maryam batada lfy”,”kunga Dan Allah ku rabu dani”,”shknn Khadija saketa” Habiba ta fada a fusace, Fitowa Zainab tayi suka biyota a baya motar Uncle Abba suka shiga ita kuma ta wuce gida.
Like
Comments
Share
MALAMAI NE SILA
By
USAINA ADAMU USMAN
*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER’S ASSOCIATION* (A.Y.T.W.A)
Page 3
GA MASU BUKATAR SHIGA KUNGIYAR MU TO GA DAMA TA SAMU, WADANDA SUKESON SUYI RUBUTU AMMA BASUSAN TA INA ZASU FARA BA TO GA DAMA TAZO MUKU, DOMIN KARIN BAYANI ZASU IYA TUNTUBAR MU TA WANNAN NUMBER 07048614405.
*****
Ganin haka yasa Uncle Abba yaja hannun Habiba suka tafi dakin vice haka dai suka aikata alfashar su sannan suka fito babu zanchan wankan sarki haka suka zura kayan su, lokacin har magariba ta kawo kai dan wasu masallacan sun fara kiran salla, “to mu zamu tafi” Khadija ta fada tana saka hijabinta, “to ku bari nayi wanka nayi salla sai muje na sauke ku” ta inda ya fisu kenn shi yana sallah, “Aa gaskiya baza mu iya jiranka ba, ka bamu kudi kawai mu hau napep” dari biyar ya zaro ya basu, a wulakance Habiba ta kalli kudin, “nifa matsalata dakai kenn yanzo duk wannan abin dari biyar kadai zaka bamu”,” in bakuso ku bani abata, ta ishaini gobe da safe na karya” ya fada yana kokarin karbe kudin daga hannunta, tura kudin tayi a cikin bireziya tana galla masa harara, “gobe ma rana ce” ta fada tana jan hannun Khadija suka fice daga gidan kamar zasu tashi sama saboda bacin rai, “dama na fada maka yaran nan fa yan akuya ne, shiyasa ma kaga ko fitowa banyi ba daga daki” Vice ya fada a dai dai lokacin da yake fitowa daga dakinsa, “naso mu rabu dasu mu fita sabgar su amma na kasa haka nan zamu cigaba da hakuri dasu” Uncle Abba ya fada yana daukar ruwan wankan sa ya shige makewayi, da kallo Vice ya bisa yana shigewa dakin kafin Uncle Abba ya fito shima ya shiga.
Add Comment