Littafan Hausa Novels

Ramuwar Gayya Hausa Novel Complete

Ramuwar Gayya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

..

 

RAMUWAR GAYYA

PAID BOOK 300

 

 

LABARI DA RUBUTAWA

ZAINAB SALIHU YARIMA

 

 

Godiya ga Ubangijin da ya bani iko fara wannan littafi, ina muku albishir masoyana cewa Insha Allah in da na fara sai na kai ƙarshe ku dai kawai ku nuna mun one love gurin siyan littafin nan, na muku alƙawarin zai faɗakar kuma ya ilmantar kuma ya nishaɗantar da ku Insha Allah.

 

 

Zaku iya samuna

FACEBOOK: ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU

YOUTUBE CHANEL:SARAUNIYAR KANAWA YOUTUBE CHANEL

WHATSAAP: XAYYEERSHERTOUL HUMAEEERETH

 

FREE PAGE 1

 

 

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM

 

 

 

Zugunne ta ke gaban gawar iyayen nata tana gurshiƙan kuka tamkar ranta zai fita, ta ma kasa yi musu Addu’an ga shi ana so a ɗauki gawar ta riƙe makaran ƙam-ƙam da hannun ta, wata dattijuwa ta ta so ta riƙe ta tana jan ta da kyar aka ɓanɓareta, daga jikin makaran tana ihu tana komai, duk mutanen da ke gurin sai da suka tausaya mata.

Allah Wadai Hausa Novel Complete

“Haba Safnah wanda ya mutu ya riga ya mutu, ba abun da suka fi buƙata yanzu agareki in ba addu’a ba.”

“Shikenan Mama Habi Dady da Momy sun mutu, ban da kowa yanzu a duniyar nan sai ke sai Allah.! Ta ƙarisa maganar cikin gunjin kuka, haka dai aka dunga lallashin Safnah da nasiha mai matuƙar ratsa jiki, duk wanda ya shigo gaisuwa sai ya jimanta wannan al’amari a ce cikin dare ɗaya a wayi gari an ma mata da miji kisan gilla.

Sallama aka dunga rafkawa wanda ya ja hankalin matan da suke zaune a falon, bayan sun amsa sallama kowa ya zura ido yaga wanda zai shigo.

Wata macece sanye da baƙar abaya ta shigo fuskar ta ɗauke da fara’a ta fara gaida mutanen da ke falon tayi musu ya ƙarin gaisuwa, sannan ta fara magana kamar haka, “sunana Dsp Fatima, na zo ne in ƙara jajanta muku bisa abun da ya faru na rashi sannan kuma mu gabatar da bincike game da mutuwar marigayi Alhaji Sulaiman da mai ɗakin shi, duk da kafin mu ƙariso nan abokan aiki na sun zo kuma likitocin sunyi na su gwaje-gwaje kuma Insha Allah yau za’a kammala zamu karɓi sakamako tunda wuƙar da akayi kisan da shi tana hannun mu, sannan muna buƙatar zamu tafi da Safna ofishinmu don ta amsa mana wasu tanbayoyi.?

“Haba ranki ya daɗe taya zaki ce zaku tafi da Safna da me zata ji da rashin Iyayen ta ko da damun ku.”

Cewar Mama Habi cikin ƙuluwa da al’amarin ƴan sandan da suke ta musu zarya tun jiya, wanda hakan yasa ba a kai gawar ba sai washegari.

Suna ji suna gani Dsp Zuhra ta tasa Safnerh a gaba suka fita nan gida ya rikice kowa na faɗan albarkacin bakinshi wasu suna faɗin ai dole ta zama abun tuhuma domin daga ita sai Iyayen ta a gida a ce an kashesu amma ban da ita, wasu kuma suna faɗin Safnerh yarinyar kirkice mai sanyi hali a iya sanin su bata da abokiyar faɗa amma taya za’ayi a ce ita ta kashe iyayen ta to akan me, wasu suna faɗin tayi ƙanƙantar da za’a ce tayi kisa kwata kwata shekararta sha takwas ne fa kuma Safnerh irin yaran nan ne masu ƙaramin jiki, haka dai kowa ke faɗin albarkacin bakin shi yayin da Mama Habi ta rungume ƴarta sa’ar Safnerh tana kukan mai tsuma zuciya, wanan Bala’i da mai yayi kama da Mutuwar ɗan uwan ta zataji ko da tafiya da ƴar shi.

 

Fitowar Dsp Fatima da Safnerh bakin gate ɗin gidan shi ya jawo hankalin mazan da ke haraban gidan suna zaune suna karɓan gaisuwa miƙewa, Alhaji Musa Mijin Mama Habi har yana tuntuɓe gurin ƙarisawa gurin su, “Dsp Lafiya naga kin ta so Safnerh gaba.?

“No karka damu Alhaji akwai ƴan wasu tambayoyi ne da zata amsa mana Insha Allah da zaran mun gama zata dawo karku damu.”

“To to yanzu na ji batu ko in biyo kune dai in an gama sai mu dawo tare saboda kar a barta ita kaɗai saboda halin da take ciki na rashin nan.?

“Karka damu zan dawo da ita da kaina Insha Allah.

 

 

*******************

 

 

“Hello Ƙaura kana jina ko ka tabbatar kai da yaran ka kun bar garin nan har sai komai ya lafa sai ku dawo, sannan na tura muku miliyan ɗaya a cikin Account ɗin ku wannan ɗin so min taɓi ne kafin komai ya kankama kunji ko, “an gama Alhaji yanzun nan ku zamu tattara mu yi na Lagos, har sai ƙura ya lafa,”

“Yauwa ɗan gari shiyasa nake son aiki da kai, sai munyi waya.

 

 

*******************

 

OFISHIN ƳAN SANDA

 

 

“Safnerh ki saki jikin ki da ni, ki ɗaukeni tamkar ƴar uwarki kuma ƙawarki Aminiyarki, ki faɗa mun duk abun da kika sani game da Mutuwar Iyayen ki kinji.”

Gyaɗa kai Safnerh tayi fuskar ta fall hawaye.

“Yauwa kina jina ranar da daddare me ya faru.?

 

“Ina kwance da daddare a ɗakina kawai sai na jiyo ihun Mahaifina, da gudu na fito na nufo ɗakin shi, kafin in shiga naji suna magana da mahaifin nawa amma banji me suke cewa ba, kuma banga fuskar su ba da yake sun juya baya, mahaifiyata na gani sun kwantar itama sun ɗora mata wuƙa a wuyarta fit suka yankata ban san lokacin da na kwalla ƙara ba na juya aguje tuni suka biyoni……!

Kasa ƙarisa maganar tayi saboda kukan da ya ci ƙarfinta, sosai take kuka tamkar ran ta zai fice, “Aunty a gabana suka kashe mun iyayena yankan rago, sannan suka dunga nemana a cikin gidan basu ganni ba saboda na shiga store na ɓoye, bayan sun fita na koma ɗakin da iyayena suke na samesu male male cikin jini….!

“To amma taya aka samu shedar hannun ki a jikin wuƙar da aka samu a ɗakin.?

” Bayan na shiga ɗakin ne naga wuƙar makale wuyar Mahaifiyata shine na je zare mata daga nan ta cika, mahaifiyata a hannuna ta cika Aunty….!

Tasowa dsp Fatima tayi ta zo ta rungume Safnerh tana bubbuga mata baya a hankali alaman rarrashi, “Insha Allah Safnerh na miki alkawarin sai na binciko miki duk wanda ke da hannu cikin mutuwar Iyayenki, ta shi muje in rakaki gida.”

 

“Sagent Mardeeya.”

“Yes ma”

“Ki maida Safnerh gida.”

“Ok Ma”

 

*******************

 

 

Bayan kwana uku da Rasuwar Alhaji Sulaiman da mai ɗakin shi.

Zazzaune suke a ƙayataccen falon Gidan Alhaji Musa ne a zaune sai Alhaji Dabo, sai Mama Habi, sai Barrister Umar, sai Safnerh da ke zaune a gefen ƙafar Mama Habin Sai wani Malami, bayan an buɗe taro da Addu’a sai Barrister Umar ya fara magana kamar haka, “da farko da Sunana Barrister Umar faruq lawal nine Lauyan marigayi Alhaji Sulaiman, kamar yadda aka Umarceni cewa in tattaro dukkan wasu kadarori da Alhaji ya mallaka da kuma abun da ya shafi asusun shi na ijiya da sauransu to Alhamdulillah gashi na tattaro, Marigayi dai ya mutu ya bar kamfanoni guda Ashirin a nan gida Nigeria, in da kuma a ƙasashen waje irin su Dubai, Cameron America, Egypt yana kamfanoni guda bibbiyu a waɗan na kasashe da na lissafa, sannan yana da hannu jari a manya kamfanoni na ƙasashen duniya, sannan kuma a asusun bankin shi yana da kuɗi kimani naira trilion ɗari, duk ga takardun su da komai da komai, sannan wannan takardun wasu kadarori ne da gidaje da hannun jari da ya bani ya ce na ƴar uwar shi ne Hajiya Habiba da iyayenta suka damka mai Amana yake ta juya mata har suka kawo haka.”

Bayan Barrister ya gama maganar shi ne ya tattara takardun gaba ɗaya ya miƙa ma Alhaji Musa, bayan Alhaji Musa ya karɓa ne ya fara magana kamar haka, “to Allah ya gafarta malam kaji bayanin da Barrister ya mana yanzu kai muke saurare, “to Alhamdulillahi Barrister sannun da ƙoƙari, yanzu ana buƙatar aji a cikin ku tun da kune shaƙiƙan Alhaji shin akwai wanda kuka sani yana binshi bashi.?

Caraf Mama Habi ta amshe da cewa, “ni dai a iya sanina yayana ba mai cin bashi bane.

“kina yawo da shi ne Habiba da zaki sani wannan ai mu zaki bari muyi magana domin mune shaƙiƙan shi da barci kawai ke rabamu.!

Cewar Alhaji Dabo, “to da farko dai akwai bashin da muke binshi da muka haɗa hannu zamu gina masana’antan shi da ke Lagos to bayan an gama ginawa sai ya ce mu bar mai zai mayarmana da duk abun da muka kashe to ana kan maganar hakan ne ya mutu saboda haka mu yanzu ba kuɗin muke buƙata ba Masana’antar za’a bar mana a madadin kuɗin mu.”

“Amma ranka ya daɗe ni ba muyi wannan maganar da marigayi ba a iya sanina ba wani masana’anta nashi da ya taɓa faɗamin cewa kun haɗa kuɗi gurin ginashi.?

“Kaga dakata Barrister ka tsaya a matsayinka na Barrister wannan sirrinmu ne tsakanin mu da Aminin mu, gudun haka yasa sai da mukayi takardu a rubuce.”

Alhaji Musa ya ƙarisa maganar yana ɗauko takardun ya miƙa ma Barrister, tabbass wannan sa hannun Alhaji ne da komai amma yaushe akayi haka baida labari.

 

Bayan gama gabatar da komai ƙarshe dai malam ya kammala raba gadon an bama kowa haƙƙin shi in da dai Safnerh ce mai gadon kaɗai sai wasu ƴan basissika da su Alhaji Dabo suka ce ana bi duk an cire in da aka yanke cewa Mama Habi zata cigaba da riƙe Safnerh ita da mijinta Alhaji Musa, in da kuma Alhaji Musa zai cigaba da kula ma Safnerh da kadarorinta, ita dai Safnerh tun da aka fara maganar ba ta ce komai ba, bayan an kammala ne kuma aka yanke shawarar cewa su Mama Habi zasu dawo nan gidan Su Safnerh da zama don ɗebe mata kewa.

 

 

 

*******************

 

“Ina Magana dsp Fatima Zahra ce ko.”

“Eh ni ce da wa nake magana.?

“Ba damuwar ki ba ce da sai kin san ko wacece take magana ina so in gargaɗeki akan cewa ki cire hannunki akan case ɗin kisar Alhaji Sulaiman in kuma ba haka ba tabbass kema zan aikaki in da yaje….!

“Hello! hello oh god Sajent kabeer yi maza kayi mun tracking wannan Number don Allah…

 

 

Yanzu aka fara wasan kuyi hanzari ku fara biyqn payment na ku ɗari uku ne ba tsada 300 show me one love

Add Comment

Click here to post a comment