Ashe Dana Ne Hausa Novel Complete
ASHE ƊA NA NE
PAID BOOK
LABARI DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(SARAUNIYAR KANAWA)
*GODIYA*
Godiya da jinjina ta tabbata ga ubangijin sammai da ƙasai wanda bashi da abokin tarayya, gareka muke bauta gareka muke naiman taimako, ina godiya ga Allah da ya bani ikon dawowa domin nishaɗantar da ku da wannan littafi mai cike da darussa.
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin tun daga farkon shi har ƙarshe wa Kakan nina Hajiya Zainab Aliyu Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, da Malama Raliyatu Hussaini Allah ya kai haske kabarinki ya miki rahma halinki na gari ya biki.
Ramuwar Gayya Hausa Novel Complete
Littafin nan na kuɗi ne akan Naira ɗari biyu 200, vip group kuma ɗari biyar ne 500 posting sau biyu safe da yamma, ga mai buƙata zai biya kuɗin shi kafin free page ya ƙare, masu biya ta katin waya ku turo katin wayar ku ta wannan number 08037420816 ga masu turawa ta Account kuma zasu turo ta wannan number 6019964818 zainab Salihu yarima keeystone bank, sai kiyi screen short ki turomun shaidar biyar ki ta wannan number 08037420816.
PREE PAGE 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM
*************************
BIRNIN ZARIA
LOW-COST
Yara biyu ne mace da namiji wanda ba zasu wuce shekara bakwai-bakwai ba a harabar makeken gidan da yake ɗauke da manyan motoci da shuke-shuken fulawa wanda suka ƙara ƙawata gidan, in da gefe guda kuma in kin zaga ta bayan gidan swiming fool ne da gurin hutawa da kuma gurin wasan yara duk a haɗe, kallo ɗaya zaka ma gidan kasan cewar lallai kuɗi sun zauna a gidan, yaran biyu mace da namiji wsan su sukeyi hankali kwance a gurin da aka tanada don wasan yara,abun da zai burgeka kuma ya baka mamaki shine yaran irin su ɗaya tamkar ƴan biyu farare ne tas da su suna da manyan idanuwa da zagayayyen fuska mai kwance da kwantaccen saje ga yalwar gashin kai, dukan su duk da cewa shi ɗayan namiji ne bai hana bayyanar kwantaccen baƙin suman shi da yake ta walkiya ba bayyana saboda rana da ya hasko su, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewa Allah yayi hallita mai ƙyau, sai dai yanayin shigar su ba ɗaya ba domin ita macen sanye take da lafiyayyen doguwar rigar ƴar kanti wanda kallo ɗaya zaka mai kasan cewa kuɗi yayi kuka a gurin siyar rigar, kafafuwanta kuma sanye da wani takalmi mai matuƙar ƙyau, kan ta kuma an kama mata gashin ta da wani pink ribon tayi matuƙar ƙyau saɓanin namijin da yake sanye da wasu koɗaɗɗun t-shirt da wando wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewar sun ji jiki, duk da cewar sun tsufa amma fes fes suke, ƙafar shi sanye da wata koɗaɗɗiyar silifas, namijin ne ya dubi macen ya ce mata, “Zeeyterh ki bani keken nima in ɗana kinga ke kike ta hawa tun ɗazu.” ya ƙarisa maganar yana juya shanyayyun idanun shi tamkar mai jin barci, turo ƙaramin bakinta tayi haɗi da murguɗa shi ta fara magana, “ni Mu’ayyid ka ƙyaleni yau ba zan baka kekena ba kai ma ka ce Abban ka ya siyama mana kullum sai ka zo kai ta ɗana mun keke.”
Tayi maganar cike da shagwaɓa da sangarta.
“Ke ni kike kiran sunana baki ce mun Yaya ba, bacin Jaddi ta ce na girmeki.” Mu’ayyid ya faɗa a fusace yana mai nufan in da Zeeyterh take tsaye, ai da gudu ta saki keken ta ranta a na kare domin tasan kaɗan daga cikin aikin Mu’ayyid ne ya bubbugeta, dai dai lokacin Hajiya Uwani ta fito daga sashinta tana kwala ma Zeeyterh kira, suka ci karo da ita Mu’ayyid ya biyo ta ai tana ganin Mahaifiyar tata taje da gudu ta ɓoye a bayanta tana ma Mu’ayyid gwalo, wani irin kallon tsana Hajiya Uwani ta bi Mu’ayyid da shi cikin tsawa ta fara magana tana cewa, “Uban me ya shigo da kai gidan nan, ban hanaka shigowa ba shegen yaro irin maita irin tsiya, kul ka fitamun harkan yarinya, ɓace mun da gani kafin in makeka a dunga ma magana kana ƙure mutane da shegen idon ka irin na mayu!”
Juyawa ta yi gurin Zeeyterh da ta cika tayi fam tamkar ita ake ma wannan hayaniyar, “ke kuma mara jin magana ban hanaki kula shi ba.?
Ta ƙarisa maganar ta wurga ma Zeeyterh harara, ai ko gama rufe baki mahaifiyar bata yi ba ta wani fashe da ihu haɗi da juyawa ta shige sashin na su da gudu tana bubbuga ƙafa, shi ko Mu’ayyid juyawa yayi ya fice daga gida, yana fita ya nufi wani ɗan madai-daicin gida mai ɗauke da dakali da faranda wanda kaf layin nan shine gidan da yafi kowani gida rashin ƙyau, yana shiga ya ci karo da wata tsohuwa fara tas da ita ƙyaƙƙyawa wanda da ka kalleta kasan cewa tsufan jin daɗine ba wahala a tare da ita, ɗaga kai tayi ta bishi da kallo kan ta kwala mai kira tana faɗin, “kai Mu’ayyidu zo nan daga ina kake.?
Ƙarisowa kusa da tsohuwar yayi ya zauna a tabarman da ta shinfiɗa kofar ɗakin na ta sannan ya ce mata, “Jaddi daga gidansu Zeeyterh nake, wai don ta tsokaneni zan bigeta shine Momynta ta dunga zagina har da ce min maye,” ya ƙarisa maganar yana ɓata fuska, murmushi Jaddi tayi haɗi da shafa kan shi ta ce mai, “haba Mu’ayyidu jarumin maza karka damu ya kamata a ce zuwa yanzu ka fahimci halin uwar ta ku, maza je ka ga Umman ka can tana neman ka dama.”
Cikin sauri ya miƙe ya nufi ɗakin mahaifiyar ta shi, sallama ɗauke a bakin shi.
*************************
ASALIN SU
Alhaji Ahmad Sambo shahararren mai kuɗi ne kuma cikakken ɗan boko, sunyi soyayya da Asma’u tun soyayyar ƙuruciya sai Allah yayi nufin ba shi zai fara auran ta ba, kasancewar an tura shi yin wani course a ƙasar india in da kafin ya dawo tayi aure duk da cewar tayi iya ƙoƙarinta na taga ta jira shi hakan bai yuwu ba, ta auri wani mutum wanda ba kowa ya san asalin shi ko dangin shi ba amma yana da arziƙi sosai hakan yasa iyayen Asma’u aura mai shi ba tare da wani bincike ba, bayan wasu shekaru Asma’u ta haifi ɗan ta namiji ƙyaƙƙyawa wanda aka sa ma suna Tahir, bayan haihuwar Asma’u da shekara biyu aka nemi Alhaji Hamza aka rasa sai wasiƙa da ya bar ma Asma’u cewar ya saketa saki uku sannan ya bar mata rabin dukiyar shi ita da yaron shi sannan ta mance da shi a rayuwar ta, sosai abun ya girgiza Ahalin Asma’u bayan wasu shekaru sai Ahmad ya dawo ya tarar da labarin cewar Asma’u tayi aure har da ɗa sannan ga tarin dukiya da take da shi hakan yasa Ahmad jajircewar sai da ya Auri Asma’u saboda son da take ma Ahmad Sambo yasa duk ta miƙa mai ragamar dukiyar Tahir gaba ɗaya ya fara jujjuyawa nan da nan dukiya ta haɓaka Alhaji Sambo ya sahara a cikin birnin zaria da kewaye har da maƙotan jahohi, gefe guda kuma ya tsani ya buɗe ido ya ga Tahir ya tsani yaron nuna mai ƙiyayya yake a fili har uwar yaron da yaron suka fahimci haka, amma kasancewar soyayyar Alhaji Ahmad Sambo ya rufe ma Hajiya Asma’u ido kwata-kwata ta kasa ma Alhaji Ahmad magana, haka Tahir ya ta so a gidan a wahale a haka yayi karatu tamkar agola har Hajiya Asma’u ta zo ta ƙara samun ciki ta haifi santalelen ɗan ta namiji lokacin Tahir shekarar shi sha bakwai ya kusa gama secondry school, sosai Tahir yayi farin cikin haihuwar Muhammad yana matuƙar son Muhammad, sai dai kash a hankali a hankali iyayen suka cusa ƙiyayya a tsakanin yaran domin yadda suka fifita soyayyar Muhammad akan Tahir komai Muhammad ne a haka suka taso duk da yaran a haka suna son junan su sai dai in har Daddy ya gansu tare ya dunga ma Hajja tsiya kenan akan me zata bar ɗan da bai da Asali da ɗan shi ɗan asali kuma a gaban yaran yake faɗan haka sosai abun ke ɓatama Tahir rai, a haka dai har suka girma sosai Tahir yake samun ɗaukaka a duk al’amuran shi tamkar mahaifin shi, bai dogara da dukiyar mahaifiyar shi da Alhaji Sambo ya kankane ba, sosai abun ya fara ba Alhaji Ahmad Sambo haushi ganin ƙaramin yaro yana so ya kamo shi dukiya.
BAYAN WASU SHEKARU
Abubuwa da dama sun faru ciki har da ƙarayar arziki da ya samu Alhaji Ahmad sambo wanda hakan yasa ya kasa tawakkali har ya kamu da ciwon ɓarin jiki, in da tuni Tahir ya bar gidan ya gina na shi tankasheshen gida kuma yayi aure bai damu da zuwa gidan mahaifiyar ta shi ba, gefe guda kuma Muhammad ya ta so a sangarce ban da yaje makaranta ya dawo ya kwanta yayi barci in yana buƙatar kuɗi yaje gurin Daddyn shi ko Yaya Tahir su bashi a haka ya gama makarantar shi bai iya sana’ar komai ba ya fara neman aiki duk aikin da ya samu ya ce ya mai kaɗan yafi ƙarfin yin wannan aikin, ga mahaifin shi yanzu bai da komai gidan da suke ma ya siyar ƙarshe Tahir ne ya basu wani ƙaramin gida kusa da gidan shi, a nan Alhaji Ahmad Sambo ya rasu bai kuma nemi gafarar Tahir ba, sosai rayuwa ta yi ma Muhammad zafi domin ya ta so cikin gata da sangarta ga shi yanzu babu, har kunyar shiga abokai yakeyi yanzu, Tahir ya kirashi ya ce ya zo ya bashi aiki a companyn shi ya ce mai shi in har ba manager zai bashi ba bai so, haka rayuwa ta cigaba da juyawa a haka har yau kuma Alhaji Tahir basu samu haihuwa ba shi da matar shi Uwani, har ƙasashen waje sunje don check up kuma an faɗa musu lafiyar su lau lokacine kawai, Hajja Asma ta matsama Tahir yayi ma Muhammad aure, hakan yasa Muhammad ya ɗan kara natsuwa da hankali, har ya samu koyarwa a makarantar primary yana kuma yi haka, bayan Auren su da wata biyu matar Tahir ta samu ciki lokaci guda da matar Muhammad, farin ciki a gurin Hajjah Asma bai misiltuwa haka ya zama bata gidan Tahir ba ta gidan Muhammad, sosai take basu kulawa rana ɗaya suka fara naƙuda Hajja Asmee da kanta ta kai su asibiti ko faɗa ma mazajen su bata yi ba, basu wani ɗauki dogon lokaci ba suka haihu tare matar Muhammad ta fara haihuwar ɗan ta namiji sai matar Tahir ta haifi ƴar ta mace, haka suka dawo gida ranar suna aka sama yara suna kamar haka Namijin Sunan shi Ahmad Mu’ayyid wato yaci sunan kakan shi shiyasa suke kiran shi da Mu’ayyid, ita kuma mace ta ci sunan kakar ta ta gurin uwa Zainab ana ce mata Zeeyterh, sosai yara suka ta so cikin kulawar kakan su in da ya kasance duk duniya ba wanda Hajiya Uwani ta tsana irin Muhammad da iyalin shi hakan yasa ta fara ma mijin huɗubar tsiya tun bai ɗauka har ya fara ɗauka ga Asiri da Hajiya Uwani ta keyi tuni ɗan taimakon da yake ma ƙanin na shi ya fara ragewa, duk da uwar ta su na iya ƙoƙarinta gurin ganin ta haɗa kan ƴaƴan na ta sai dai ta bar shiri tun rani, domin hajiya Uwani ita ma a tsaye take, makaranta ɗaya aka sa Mu’ayyid da Zeeyterh gashi yaran sun ta so suna son junan su duk da ƙoƙari uwar Zeeyterh na ganin ta rabasu amma abun ya ci tura gashi kullum ƙara jin tsanar yaron ta ke duk in ta ganshi sai gabanta ya faɗi wannan kenan.
*************************
CIGABAN LABARI
“Umma ni na tsani Momyn Zeeyterh ban son ta.”
“Kul Mu’ayyid kar in kuma ji domin ita ma momynka ce ka ji ta shi kaje ka kaimun markaɗe.”.
“Tom Umma ba zan ƙara ba kiyi haƙuri.”
WASHE GARI
Hajiya Uwani ce zaune gaban wani malami da ya tara uban gashi a fuskar shi gashi baƙinƙirin fuska ba rahma ya tasa katakon ƙasa a gaban shi ya fara magana kamar haka, “karki cika matsawa akan yaron nan domin in ya lalace tamkar ƴar ki ce ta lalace saboda haka ki bi komai a hankali, maganar uwar mijin ki kuma gaskiya a yanzu ba zan iya mata komai ba domin macece ita mai matuƙar ruƙo da addini da addu’oi, sabida haka ki ta shi ki je zamu san abin yi.!✍️
Labari ne mai cike da tsantsan tausayi sadaukarwa rashin tausayi, tsantsar soyayya, da dana sani da tsantsar ilmantarwa sannan zan kawo muku abubuwan ƙaruwa sosai,ku dai kawai karku bari a baku labari ko da kuɗinka sai da rabonka siyan na gari maida kuɗi gida ɗari biyu ne 200 kachal ba tsada VIP group ɗari biyar masu so ta private 700 ku nuna mun one love.
Zeey yar mutan zazzau ce
Add Comment