Littafan Hausa Novels

Zain Abeed Hausa Novel Complete

Zain Abeed Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ZAIN_ABEED

 

 

 

_By Nimcyluv Sarauta_

 

page 1

 

 

 

 

 

_Allahamdulillah! Thanks to Almighty ALLAH (swt). For giving me opportunity to start this book. *ZAIN_ABEED*_

_Finally, I just want to say that this would never been possible without all of you and I am so, So grateful for everything You have done for me. You guys have seriously made my dream come true and you’re the reason Gaslight even made it this far. I hope that You Will continue to support my Journey as an Author And I can’t wait for You to read the published version_

_just follow my pen, For i assure You, You Are going to fall in love with_

_Seriously Love guy’s! Lot’s of Love NIMCYLUV._

 

Sadaukar ne ga ADDAH RAMLA #Mai dambu ko bayan babu ni wannan shine zaki tuna dani Much luv.

 

I’m just wanted to say Duk wanda labarin bai masa ba, Wallahi ya faɗi duk abinda yay niyy Nice dai Marubuciyar *Moon, Tsintacciya, Abu Maleek, Sirrin mu, Kwaila ce, Uncle ne e.t.c*

 

 

 

 

 

Hazon da ake yi, a ƙasar Moscow bai hana jirgin Aeroflot-Plus sauka a Sheremetyevo Airport dake nan ƙasar Moscow ba. The weather is too high pilot ɗin da ƙyar yake iya ganin, mai bashi direction ɗin sauka ƙasa. Banda Snow babu abinda yake zuba. Mai asthma kam sanyin babbar illa zai iya yi masa, zai iya sashi cikin critical condition. A hankali jirgin keyin parking har ya samu wajan tsayawa. Daga can cikin jirgin kowa passengers ne suke ƙoƙarin zame belet ɗin jikinsu domin sauka daga ciki. A hankali yaja numfashi mai ɗan ƙarfi yana matse hannayensa suna bada wani, sauti na gajiya.

 

1000+ Free Hausa Novel Books Download, Littafan Hausa Novels

 

Wrist ɗin hannunsa ya duba yaga 1:15Am na dare. Gently ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun suit ɗinsa, walking slowly ya ƙarasa Vip side. He’s just thinking why har yanzu biyuninsa bai fito ba? Is he alright or what? If sanyin nan ya yi effecting health nasa? A fili yace “Ya rabb, ga bawanka” buɗe ƙofar vip ɗin yay a hankali yana mai tura kansa ciki. Cak ya tsaya saboda ganinsa da yay a kwance saman duguwar kujera.

 

 

 

Infact bai da alamar tashi, saboda ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa a ƙirji Numfashinsa na sauka a hankali. He’s sleeping peacefully yay kyau sosai a baccin, domin gaba ɗaya sumar dake goshinsa ya ɗan zuba fuskarsa kamar wata mace. Ƙuri ZAIN yaywa ABEED da idanunsa wanda suke cike da Zallar so da ƙaunar abokin haihuwar tasa (Twins).

 

 

 

Ƙarasa shiga yayi har zuwa inda Abeed ke kwance, yana zuwa ya saka hannunsa ya ware masa hannayensa da suke ƙirji. Shiru Zain yay ganin ƙirjin Abeed na ɗagawa, kafin a hankali ya ɗura kansa a ƙirjin na Abeed domin gano what wrong with him yake jan numfashi haka? Something is fishy Abeed baya bacci cikin airplane. Kansa ya janye kafin a hankali yace “I don’t know what wrong with my Biyuni, bai san me yake ɓoyewa ba,is he hiding something for me? No! Abeed bai zai ɓoyan komai ba, shine rayuwata nine rayuwarsa, he can’t do that…. seriously” ya faɗa yana ɗaukan iphone ɗin Abeed, sosai Zain yay mmkin ganin 20miss call na RIYA tun suna 9ja take kira Abeed, ba kira ɗayan da ya yi, respond. Cike da damuwa Zain yace “sorry Riya, In sha Allah zan shige maki gaba” wayar Abeed ɗin ya saka cikin Aljihu, yana faɗin “I love You Biyunina” motsi Zain ya ji, ya juya da sauri haɗa ido sukai da Abeed, yaga duk yadda ƙwayar idanunsa take blue amma yanzu tayi wani mugun jaa. Shiru yay yana noticing ɗin sa, amma bai gane komai ba. Cikin sakin fuska yace “Yaushe ka tashi?” Kamar Abeed ba zai magana ba sai kuma ya ɗan buɗe baki da ƙyar yana yatsuna fuska, cikin slow voice yace “from i love You Said” ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye, tare da unlock na suit nasa. Murmushi kawai Zain yay yana girmama, nauyin bakin Abeed hatta shi da aka haifesu rana ɗaya, lokaci guda,wata guda, shekara guda wani time ɗin banza yake masa. Da mutum uku Abeed yake rayuwa yaji daɗi na farko, abokin haihuwar sa Zain, na biyu Mai martaba sai kuma Naila.

 

Zain nada tsayi, fari ne shi idanunsa ma fara re ne, fuskarsa a sake bashi da wata damuwa, damuwarsa ɗaya akan Biyuninsa. Baya ɓoye komai yana da sauƙin kai. Abeed kuma yana da zuciya baya ƙaunar kallo ko kaɗan idan ba wajan show yaje yana gabatar da waƙarsa ba, baya ƙarya sam bai san yadda ake ba, Idan yace Yes of course yana nufin Yes ɗin. Ko waye kai baka isa yay maka ƙarya ba, fari ne tass, yana da manyan idanu wanda ƙwayar idanun ta kasance blue, ga suma mai kyau har gaban goshi take sakkowa, sumar goshin kuma ita ta banbanta tsakaninsa da Zain, da ita ake iya gane waye Abeed waye Zain. Amma har gobe akwai abinda Abeed yake ɓoyewa Zain, Meye shi?. Toilet ɗin dake cikin jirgin Abeed ya shiga yana tafiya a hankali hannunsa zube cikin Aljihu, yana shiga cikin toilet ɗin ya maida ƙofar ya rufe, kana ya jingina da jikin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar, bai damu dan ya rasa ransa ba, amma idan ya rasa ransa wanne hali Zain zai shiga? Wannan tunanin shine yake ƙara damun Abeed yake ya hanashi barci, domin abincike ya nuna cewa saura wata biyar ciff wa’adin rayuwarsa a duniya zai ƙare. Zain jin Abeed shiru ya sanya ɗan yi knocking ƙofar, tare da faɗin “Hey my frnd is everything okay?” Shiru Abeed yay saboda Aman da yazo masa, cikin sauri ya ƙarasa wajan sink ya fara amai wanda rabin aman duk jini ne….. Bakinsa ya wanke tas tare da wanke fuskarsa kana ya buɗe ƙofa ya fito, yana fitowa cikin sauri yay gaba abinsa ba tare daya tsaya Zain ba, yay hakan ne kuma saboda baya son ya fahimci wani abu. Da idanu kawai Zain yabi Abeed dashi. Har zai fita sai yaga inhaler ɗin Abeed girgiza kai kawai yay tare da ɗauka yabi bayansa. A strains ɗin jirgi yaga Abeed tsaye kansa a sunkuye fuskar nan a haɗe tayi jajir, juyawa yawa yay nesa dashi yaga ashe wata baturiya ce ta kafe Abeed ɗin da kallo, murmushi yay yace “Can i call her?” Still Abeed shiru yay, Zain yace “shall we..?” Sai a lokacin Abeed ya ɗaga fararen idanunsa da suka fara dawo wa daidai, ya tsorawa Zain idanu, alamar akwai Abinda yake buƙata wajansa. Dafe kai Zain yay yana faɗin “Ya rabb, i almost frgt wlh” hannu ya sanya a cikin Aljihu ya ɗauko wani mars mai kyau, kana ya matsa kusa dashi suna farcing juna yana sanya ma Abeed mars ɗin tare da faɗin. “How was your body? Sanyin bai dame ka ba ko?” Abeed idanunsa ya lumshe, kana ya buɗe har ya buɗe baki zai Mgna, yaga Wannan baturiyar tana ƙara kallonsa. Hannuna ya ɗura a shoulder ɗin Zain kana ya juyo dashi gabansa hakan yasa ya rufe fuskarsa da jikin Biyunin nasa, fararen idanunsa ya wara kana ya ciro wani ring na Daimond a hannunsu ya kama hannun Zain ya zura masa, yana sakin wani cute smile murya can ƙasa kamar mai tsoro yace “Zakai replacing nawa” ya faɗa yana kama hannun Zain ɗin zuwa wajan wata hadaddiyar mota da tayi parking gabansu, gaba ɗaya a baya suka zauna, driver ya kwashi kayansu, shima ya shiga motar kana ya jasu suka bar airport.

 

About Azimut Hotel Tulskaya Moscow Motar tasu ta tsaya, Zain ne ya fara fitowa sai Abeed, har lokacin mars ne a fuskarsa, sai wani glass daya saka a idanunsa, kasancewar zuwan sirri sukai yasa, Zain shima ya saka mars cikin nutsuwa ya kama hannun Abeed suka fara shiga cikin reception na hotel alrdy an gama musu komai, key kawai Zain ya amsar musu suka haura sama, room 120 suka tsaya, Zain ya buɗe musu suka shiga, Kallon Abeed Zain yay yace “So what about your show? A wanne hall ne?” Abeed yana cire rigar jikinsa yace “Ba zani ba” da mmki Zain yace “pardon?” Abeed ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle murfin gorar zai kai bakinsa,Zain yay saurin kwacewa babu alamar wasa yace “Are You at of your sense? Kalli yadda bakinka ke hayaƙi saboda tsananin sanyi, shine zaka sha that stupid water?” Ka faɗa Abeed ya ɗaga irin he doesn’t care ɗin nan, kana ya ƙara ɗaukan wani ruwan zai sha, again Zain ya ƙara kwacewa cikin ɓacin rai tare da ɗaga murya yace “Wai baka tuna cewa lafiya bata isheka ba? Ka manta issues ɗinka na Asthma?” Baya Abeed yay tare da zama kan kujera yana jan numfashi ya jima a haka kafin ya ɗago kansa ya kalli Biyunin nasa, gently ya miƙe tsaye har zuwa inda Zain yake murya a sanyaye yace. “Mutuwa kake tsoro? To….” Cikin faɗa Zain yace “Kada ka sake yi min mgnar mutuwa a nan, kuma mutuwar ta rasa wa zata ɗauka sai kai? Wlh duk sanda aka wayi gari babu kai Tabbas a rana nima zan rasa raina..” taɓe baki Abeed ya yi kawai, yana ju yawa ba tare da yace komai ba, ganin yadda jikin Abeed ɗin ya yi sanyi ne ya sanya Zain saurin shan gabansa, Cak Abeed ya tsaya da tafiyar da yake, kafin ya ɗaga idanunsa suka haɗa idanu da Zain, ganin yadda idanun Zain ya cika da ƙwalla yasa Abeed ɗan zare ido yace “what again?” Kasa mgn Zain yay sai kawai ya rungome Abeed tare da faɗin. “Stay with me Biyuni na, stay with me ABEDDEEN” Murmushi mai ciwo Abeed yay yasan cewa, ɗan uwansa bai san meke damunsa ba, ciwon Asthmar da yake damunsa shi kawai ya sani, a ransa yace “Dole na tafi na barka, I think my mother is calling me” a fili kuma yace “Love u” A sanyaye shima Zain yace “To the rest of my life” da ga nan duk freshen up sukai na jikinsu. Kana suka kwanta bacci, Zain yay bacci cike da damuwa inda ya ɗauki al’ƙawarin zai samu tattauanawa Da Babban likita akan ciwon Abeed.

 

Alarm ɗin dake jikin wayar Abeed shine ya fara ƙara, wanda ya sanya Abeed ɗin motsawa kaɗan, slowly kuma ya shiga ware idanunsa saboda nauyin da sukai masa, sam bai yi bacci daran jiya ba, idan ya tuna mgnar Dr Siya yay masa, komai nasa tsayawa yake. He can’t even think mene yake daidai, mene ba daidai ba. Juya ya yi bakinsa ɗauke da addu’a ya ƙarasa buɗe idanunsa, kafin a hankali ya janye duvet ɗin daya rufe jikinsa dashi, miƙewa tsaye ya yi har zai shige toilet sai ya juya ya kalli Zain da har yanzu yake bacci, baya ya koma ya ɗan ja yatsun ƙafar Zain kamar yadda ya saba, ganin ya yi motsi yasa Abeed shigewa toilet. Miƙewa Zain ya yi kai tsaye shima ya shiga wani toilet ɗin. Kusan a tare suka shirya cikin wasu farar Arabian jallabiya mai taushi, Masjid ɗin dake cikin hotel ɗin suka shiga, ana idar da sallar suka dawo gida. Zain ne ya zauna kan kujera cikin sauri yake danna keyboard ɗin system, wani babba case ne dashi wanda zai ja ragamar shari’ar, criminal case domin zargi ne na fashi, har da kisan kai, the case was super bai taɓa samun case mai haɗarin wannan ba, Idanunsa ya ɗaga yana kallon Abeed dake tsaye yana tsiyaya madara a glass cup yace. “Ina confused wani abu” shiru Abeed yay, haka nan yaji baya mood ɗin na Magana, jin shirun yay yawa ya sa Zain yace “Arrogant…” Taɓe baki Abeed ya yi, kana a hankali ya dawo baya ya zauna kan kujera cikin nutsuwa yake shan Madarar, sai da ya shanye tass kana gently ya kalli Zain yana mai shafa gemunsa yace “Me kace?” Ɓata fuska Zain yay yace “Shafa kaji” Cije baki Abeed ya ɗanyi yace “Sorry” Juyawa Abeed system ɗin Zain yay yace “Look, already nayi searching all na abinda nake buƙata but…” Abeed yace “But wat?” Zain yace “firstly wanda nake zargi da akaita fashin, babban mutum ne, secondly yadda akai amfani da mace wajan gudanar da aikin, Lastly bayan fashin da mutumin yake akwai wani abu da yake da ƴan mata, wanda har yanzu shine abinda ban gane masa ba” taɓe baki Abeed ya yi yana Miƙewa tsaye yace “U hve to drop this criminal case ɗin” tunda suka zo sai yanzu Abeed ya yi mgn mai ɗan tsayi, da Mmki Zain yace “Kasan me kace?” Abeed na lumshe idanunsa yace “ka taɓa ji nai hauka ne?” Murmushi Zain yay yace “how can i knw, ina mgnar serious kana wani magana” shiru kawai Abeed ya yi, for some minutes kana ya miƙe ya kalli Zain kamar zai Mgna sai kuma ya yi shiru, gane cewa akwai abinda Abeed ɗin ke son faɗa yasa Zain yace “Speak up my friend, what’s in ur mind?” Abeed ya buɗe baki murya can ƙasa yace “Zakai replacing nawa wajan show”… “Why? Bayan ka amshi kuɗin jama’a, then ta yaya zan iya waƙa nida ba aiki na ba?” Cewar Zain, gaba Abeed ya yi abinsa yana mai faɗin “Be ready, zaka je matsayin ni” yana ƙoƙarin shigewa cikin wani bedroom Zain yace “Oh! Hello idan aka gane cewa bani ne Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ba fa?” Kai tsaye Abeed yace “No one knows” Ya faɗa yana shigewa bedroom ɗin. Da yamma Zain na zaune watching TV, Abeed ya fito cikin dark blue ɗin floral jacquard one button suit. Zain na ganinsa ya miƙe tare da ƙarasa wajansa, hannun Abeed ɗin ya kama ya ɗaura masa wrist kana ya tsuguna ya sanya Leather shoe yana faɗin “Ina zaka?” Murya can ƙasa Abeed yace “I have a meeting” “meeting?” Zain ya faɗa da mmki, tare da sake faɗin “Yaushe ka tsara?” Shiru ya yi bai magana ba, ganin yadda ya ɗaure fuska yasa Zain yace “it’s okay, kaga weather garin is not good, so take good care of yourself ok?” Abeed na barin room ɗin yace “I’ll..”

 

*****

A wani yanki dake kudancin garin Katsina. Cikin Wata haɗaɗɗiyar prvt school ta maza da mata. Da sauri class teacher ɗin Yake tafiya it’s already late, amma har yanzu basu fito daga cikin class ba, bayan dukkan student na makarantar sun tafi, kowa ya watse what wrong with them su kullum basa ganewa, they didn’t understand what is good and what’s wrong. ”lazy babies” ya faɗa a Zuciyarsa, cikin class ya shiga shiru babu ƙarar komai, idanunsa ya shiga rarraba wa can ya hango su a zaune ɗaya na drowning a mac nata, ɗaya kuma ta ɗura kanta akan kujera, da mamaki Teacher ɗin yace “SAIRAH” Wacce aka kira da Sairah ɗin ta ajjiye color ɗin hannunta tare da kallon Teacher ɗin, farar yarinya ce ƙyakkyawa, kana kallon ta kasan bafulatana ce ko kuma wani yanki na Fulani, kai tsaye ba zaka fasallata kayanta ba, yanayinta kamar na Kajol😌tana da tawadar Allah a saman hancinta. Ƙuri tayi masa da ido ganin hakan yasa Teacher yace “Haba twins yau kuma me akai maku?” Shiru tayi masa sai kawai yace “Ok tashi ƴar uwar taki” juyawa tayi har lokacin kanta a ƙasa a hankali Sairah ta shiga tashin ta “SARA! SARA!SARA!!” ganin ta motsa yasa ta zame hannunta. Wacce aka kira da Sara ta buɗe idanunta Subuhanallahi, wallahi babu wanda ya isa ya iya bambance wace Sairah wace Sara komai nasu iri guda ne, tawadar Allah ce kawai ta banbanta ta Sairah a saman hanci ta Sara a ƙasa. Ikon Allah buwayi gagara Misali Cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda yake halittar Mutane a mahaifa ɗaya, hukumcin sa da buwayarsa ta sanya su zo duniya a tare wanda akewa laƙani da TAGWAYEN ASALI. lumshe idanun Sara tayi kana ta ɗan murguɗa baki, kasancewar ita bata barin ko ta kwana, saɓanin Sairah da take da mugun haƙuri. Teacher yace “Twins ɗin Dady mai akai maku ne yau?” Wata uwar harara Sara ta watsa masa cikin siririyar muryarta mai tsiwar gaske tace “Heyyy! Shut up… And leave” cikin sauri Teacher yace “Ok daman Dadynku yazo ɗaukan ku” da wani sauri suka haɗa baki wajan faɗin “what? Daddy?” Sara ce ta fara yin gaba Sairah kuma ta ɗaukar masu bags nasu. Yana tsaye a kusa da motarsa cikin shiga ta ilhama gaba ɗaya ya naɗa fuskarsa idanunsa ne kawai a waje, yana ganinsu ya saki Murmushi mai sauti tare da buɗe musu hannunsa, gaba ɗaya suka shige jikinsa suna faɗin “We miss you alot Daddy” shiru kawai yay musu Sairah ta shiga gaban mota, Sara a baya kana ya jasu suka bar sclh ɗin. Bayan sunyi nisa sosai ya ɗauke hanyar zuwa gida ya nufi wata hanyar, Sara da bakinta baya shiru tace “Daddy ina zamu?” A taƙaice yace “Unguwa” tun suna Shira sukai shiru bacci ya ɗauke su har suka sake farkawa, wani baccin ya ƙara ɗaukan su.. cikin wani jeji ya shiga mai tsananin duhu da ban tsoro, kana ya kashe motar ya fito, da ɗan sauri ya shiga tashin su “Sara, Sairah” kusan a tare suka farka da mmki suka ce “Daddy area nan is not good, mu koma gida” shiru yayi kawai sai ya jasu jikinsa ya rungume, sun jima a haka kafin yace “Waye ni a wajan ku?” Sara dake tafi surutu tace “Kai ka haife mu Daddy,kai ne babban mu farin cikin mu” da sauri yace “I’m not your father, ban taɓa haihuwa ba, bare na samu albarkar tagwaye kamar ku, Sara ki kula da ƴar uwarki twins ɗinki, Biyuninki, ki kula da ita a nan zan barku” da ƙarfi Sairah tace “Daddy a nan fa? Idan abu ya cinye mu fa?” Yace “Ba abinda zai same ku, rayuwarku cikin jejin nan tafi fiye da wacce za kuyi a waje na, ni ba mahaifinku bane, Zan barku a nan Ubangiji ya ƙaddara saduwar mu” yana faɗin hakan ya shafa kawunansu, ya shige mota, tuni Sairah ta fashe da kuka tana ƙanƙame ƴar uwarta, Sara dake tana dakakkiyar zuciya ajjiyar zuciya kawai take saukewa, idanunta sunyi wani masifar jaa. Daddy da gudu yaja motar yana tafe a motar wani abu mai zafi ya shiga bin fuskarsa, parking ya yi kawai sai ya fashe da wani Irin kuka tare da faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un i lose my own children….

 

 

Yaya kuka ji? Idan yay muku kawai kuyi share Sarautar marubuta na shirya tsaf wannan salon da ban yake da sauran….

 

 

08119237616

ZAIN_ABEED

 

 

_By Nimcyluv Sarauta_

 

Page 2

 

 

 

“I lose my own children, which kind of father is these? Ni ne na haife su, na raine su tun suna jarirai, amma akan wani ƙaramin dalili zan kawo yarana cikin wata uwa duniya cikin jejin da yake da mugwayen Animals na zube? What exactly wrong with me? Wallahi ina jin na haukace, i can’t live without my children in sha Allah I’ll bring them back to my house, ko mene zai samu su ya same mu tare” Ya faɗa yana share hawayen dake cikin idanuna, kafin a hankali yaywa motar key tare da reves ya juya baya zuwa cikin jejin. Almost 20mints yana driving cikin jejin inda yake effecting ganinsu, amma babu su babu alamar su, tsananin tashin hankali ya wanzu kan kamilalliyar fuskarsa wanda zuwa yanzu ya zame hiramin da ya yi covering face nasa dashi.. he was shock ganin baya iya gane ko inda ya zube su, balle ya gansu a wajan, yana matsanancin tausayin yaransa, Sairah nada hqr, ko ina taje za taci ribar zama da hqrin ta, Sara asalin mara kirki ce, ga baƙar zuciya, amma duk abinda da take sai an taɓa ƴar uwarta Sairah ne, idan ita kayiwa ko kallonka ba Zatai ba, amma kana taɓa Sairah za kaga ruwan bala’i.. parking ya yi cikin jejin tare da fitowa waje yana ƙara sakin wani irin raunataccen kuka mai tsuma zuciyar dukkan mai sauraran sa, bai taɓa zubar da hawaye ba tunda yake sai yanzu, yana da rauni akan Twins ɗin sa. Juyawa ya dinga yi yana kiran sunansa “Sara! Sairah! Sara! Sairah!” Shiru no respond, kamar daga sama ya hanki hijibin dake jikin Sara a yashe a ƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata sa, cikin tashin hankali ya zube a wajan tare da faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un shi ke nan, na kashe yarana da kai na, Wata dabbar ta cinye min Twins” ya faɗa yana sakin kuka, kafin kuma ya fara sakin wasu surutai alamar ya fara samun matsala a ƙwaƙwalwarsa, haka ya ƙanƙame hijibin yana kuka tamkar ransa zai fita, dama Uba na gari na iya wufintar da yaran daya haifa da ƙwayayan haihuwar da Ubangiji ya dasa masa?….

 

A ƙasan wata bishiya suke a zaune, gaba ɗaya Sara bata hayyacinta wani irin tari take jini na zuba daga bakinta, duk yadda tasu ta samu kwari ta nunawa Sairah ba komai, amma hakan ya gagara, cikin tashin hankali Sairah ta riƙe Sara tace “mene yake maki ciwo twin na?” Numfashi Sara taja da ƙyar tace “Ba komai, kawai naji ƙirji na ya yi min nauyi ne, stop cry twin noting will happen to me, kukan ki shine damuwa ta” ta faɗa tana kama hannun Sairah, tare da share mata hawayen dake bin fuskarta… Girgiza kai Sairah tayi tace “Haba twin, taya hankali ne zai kwanta, bana mance time ɗin da muna primary school na nemi na rasa kuma a lokacin baki da lafiya, kina fama da ciwon ƙoda daga ni har Daddy babu wanda kika faɗawa, a kiɗime muka je hospital ɗin, muna zuwa Dr yace mana an ƙodar gaba ɗaya biyun sun lalace, amma wani saurayi ya bada tasa an cira an saka maki, munce masa waye amma Dr yace shima bai san shi ba, Yanzu haka silarsa yasa kike raye a duniya da kuma taimakon Ubangiji, duk da hakan kike tunanin hankalina zai kwanta? Ko kuma kina tunanin ke kaɗai kike so na? Sara a mahaifa guda aka haife mu, dole Soyayyar junanmu da kasance abu nada ban, ina Sonki ba zan iya bari na rasa ki ba” Sairah ta ƙare zan can tana sakin kuka, ganin yadda hankalin Sairah yay masifar tashi, yasa Sara ta saki wani Murmushin ƙarfin hali, tana danne wani tarin da yazo mata, tace “Haba twin akan wannan kike kuka? Haɓo nayi fa” Sairah tace “No Sara, stop laying baki ƙarya kada ki fara yanzu, Meke damunki, saboda Daddy ya barmu a nan? Kasan dole zai dawo ba zai iya rayuwa babu mu ba, ƙilan yana da wata manufa daya sanya ya yi hakan” shiru kawai Sara tayi domin muguwar zuciya ce da ita, a halin da take yanzu bata ƙaunar ma, a kira mata sunan Daddy, wanda yake son su da ƙaunar su yau shine ya juya musu baya, akwai kidnappers, Arms robber, bad Animals duk a ciki jejin duk da haka ya tsallake ya tafi ya barsu…. Kallon Sairah tayi da tayi lamo a jikinta tana sauke ajjiyar zuciya, a hankali tace “Twin da gaske ba Daddy ya haife mu ba” da sauri Sairah tace “A’a shine Daddynmu shine ya haife mu” gyara zama sosai Sara tayi tace “Look twin kin san bana ƙarya ko?” Slowly Sairah ta ɗaga kanta, Sara tace “Good, as frm today zamu daina amfani da sunan Daddy, na maki Al’ƙawari, zan zame maki fiye da Daddy, da kuma uwar da muka rasa, tun muna ciki, zan baki farin ciki ko da zan rasa nawa, ki daina kuka kinji babu abinda zai same mu sai abinda Ubangiji ya tsara” Sairah tace “Twin to me zamu na cewa sunanmu?” A hankali Sara tace “I’ll think about that…. sleep” ta faɗa tana ɗura kan Sairah a cinyarta, kwaɓe fuska Sairah tayi tace “I luv u twin” Sara tace “Luv u too…” Sanyin safiyar daya shiga kaɗawa shine ya farkar da Sara daga baccin da take, tana farkawa idanunta ya sauka akan Sairah wacce take zaune ta zabga tagumi tana kallon ƴar uwarta, da mmki Sara tace “Mene?” Girgiza Sairah tayi tace “naga baki tashi ba, ina tsoro ne” Sara tace “yanzu fa” Murmushi Sairah tayi tace “Naji daɗi” Miƙewa duk sukai, suka fara tunanin inda zasu samu ruwan alwala, hannun juna suka riƙe suka shiga tafiya cikin jejin cike da tsoro ƙarar ƙwari da dabbobi sun cika ko’ina, a haka suka isa wata gaɓar ruwa nan sukai alwala, Sairah ta kunce ɗan kwalinta ta shimfiɗa, kana ta yi sallah tana idarwa ta bawa Sara hijib tunda nata ya Faɗi.. shiru duk sukai banda yunwa babu abinda suke ji, juyawa Sara tayi jin cikin Sairah na ƙara, a hankali ta miƙe tsaye tace “twin tsaya a nan ina zuwa” tana faɗin hakan ta bar wajan, wajan ruwan ta koma tayiwa ruwan ƙuri da idanu can ta hangi wani ɗan ƙaramin kifi a gefen ruwan yana tsalle, da sauri ta ƙarasa ba wani tsoro ta kama kifin ta ajjiye can nesa har ya mutu, tana da tsaye ko zata ƙara ganin wani kifin amma babu, juyawa tayi ta hada itace kamar yadda taga anayi a film, ta samu fararen duwatsu nan take wuta ya tashi, a nan ta fasa kifin sai farin ciki take Sairah zata samu abinda za taci…. Kifin ta ɗauka har zuwa wajan Sairah ta same ta kwance riƙe da ciki, da sauri tace “Twin come and eat fish” ta faɗa tana ɗura kifin akan wani leaf mai faɗi, jikin Sairah har rawa yake saboda yunwa, tace “Sara na kema kici to” girgiza kai Sara tayi tace “Ai naci, nawa ma yafi naki yawa” ta faɗi hakan ne domin tasan kifin ko Sairah ba zai isa ba, balle su biyun duk da cewa itama tana jin matsanancin yunwa, da kallo kawai tafi Sairah yawunta na tsinkewa, ganin yunwa zata kashe ta, yasa ta miƙe tayi baya can, wani kuren ganye ga gani mai kyau ga ruwa duk a jikinsa, da sauri ta tsinka ta shiga ci kamar mayunwaciya, sai da taci gayen da yawa Sannan ta goge bakinta, ta koma wajan Sairah lokacin harta gama cinye kifin, Murmushi tayi tace “Taso mu tafi” Sairah tace “where?” Sara tace “muje ko zamu samu wani garin a gaba” tafiya suka fara hannunsu riƙe dana juna…

 

A can Mascow Abeed ne zaune, a gaban Dr siya, yana sauraran abinda yake faɗa, gaba ɗaya a tsorace Dr Siya yake, domin gani yake kamar Zain ne ba Abeed ba, duba da cewa komai nasu iri guda ne, babu wani bambanci, shigarsu, magana everything… Taɓe fuska Abeed ya yi, kafin a hankali ya ɗan ja numfashi, kamar wanda akaiwa dole yace “Uhm all ears” Dr Siya yace “Har kawo yanzu babu wani magani da aka samu na ciwonka, kuma binciken ya ƙara tabbatarwa Tabbas ba zaka shige wata biyar ba a raye,but…” Hannu Abeed ya ɗaga masa alamar ya isa haka, Miƙewa kawai ya yi tare da gyara zaman mars ɗinsa ya fita daga office ɗin, ko maganin da Dr Siya ya bashi bai amsa ba, a ganinsa shi da yake dab da mutuwa wanne magani kuma zai sha?. A hankali yake tafiya cike da nutsuwa he was so weak and sick, mota ya shiga ya yi mata key ya koma cikin hotel ɗin…Zain ne zaune da wani three gauther sai Red ɗin Armless, yana vedio call da Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, Murmushi Zain yay yace “Gashi ya dawo” A hankali Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake zaune kan wata tattausar ladduma gabansa cike da kayan marmari, yana tsaye da wata farar jallabiya mai kyau wacce tasha aiki irin ta sarakai, ga wata jar hula a kansa mai ɗan tsayi, wani ƙawataccen Murmushi Ya saki yace “Nuna min fuskarsa” Cikin e Sauri Zain ya saka hannu ya jawo Abeed dake tsaye yana sauraran abinda suke faɗa, zama yay kusa da Zain ya ɗan ɗura kansa a kafaɗar Zain ɗin, wani irin marairaicewa Abeed ya yi tare da ɗan kwaɓe fuska cikin Muryar shagwaɓa yace “Abba” wata mummunar faɗuwar gaba ce ta saukarwa Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas wacce bai san ko tame bace, addu’a ya yi kafin yace “Are You alright?” Shiru Abeed ya yi sai kallon mahaifinsa yake, can yace “Ina Naila?” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace “gata” ya faɗa yana hasko fuskar Naila da sauri tace “Muhammadur Rasulullah s.a.w, Jama’ar Annabi yau ga gantalallun yara masu son cutata, a’a wlh Ubangiji yay min tsari daku, maza ku bambance min kanku” Dry Zain yay kafin yace “Nine Abeed, wan can kuma Zain” washe baki tayi tace “Yau koda naji, ai tunda naga wan can yana zare ido kamar na gafiya nasan billahi ba shine Abidin ɗin ba” Murmushi kawai Abeed ya yi ganin yadda har yanzu ta kasa gane su, Zain yace “Naila ya tsofa?” Da sauri tace “A’a wallahi mugun nufinka ya ƙare a kanka, wani garin ne kuma tsofa? Kai dan kaji wallahi sai dai ka mutu ka barni a raye” dry sosai Zain yay yace “Ai ke yanzu kina tunanin kaiwa wani lokaci mai tsayi haka? To ai bana jin ko wata biyar zaki kai a raye?” Da sauri Abeed ya kalli Zain gabansa na ƙara faɗuwa, mene ya sanya suke maganar mutuwa ne? Ko dai ya tabbata cewa zai mutu ne? Haɗe fuska Naila tayi tace “Wlh ba zan mutu ba, idan na mutu Allah ya tsine..” da sauri Abeed ya miƙe tare da barin wajan ya shige cikin bedroom zuciyarsa na tsananin harbawa, Meke faruwa ne? Yanzu ne lokacin daya dace ya bawa kansa farin ciki tunda ya tabbatar Ubangiji bai ƙaddara zai yi rayuwa mai tsayi ba, yanzu wacce hanya zai bi ya samu farin ciki? Wata zuciyar tace masa kawai kayi rayuwa mai ƴan a hankali ya buɗe baki yace “Club…..

 

Add Comment

Click here to post a comment