Garkuwa Hausa Novel Complete
GARKUWA
PAGE 1
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Littafi na ɗaya. Shafi na forko!*
Free page
*Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya min labarin LITTAFINA tako wacce sigar bana so ban bada damaba in kana buƙata akwai number ta a jiki ki\ka nemi izinina a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Kuma hanyar lafiya a bita da shera yafi, wannan littafin haƙin mallakarsa nawane Aysha Aliyu Garkuwa!.*
Bismillahirahamanirahim
Ina mai farawa da sunan Allah mai rahama mai jinƙai mai komi mai komai.
Ina gode Allah daya bani aron rai da lafiya da nitsuwa da konciyar hankali ya bani damar fara wannan littafinawa mai suna GARKUWA. Ya Allah ina roƙonka ka tsare min tunanina da hannuna ka tsare min al’ƙalamina daga rubuta shari da duk wani abu da zai zamo guba ko masifa a rayuwar al’ummar Annabi, ya Allah ka bani ikon rubuta al’khairi da abinda zai zamewa al’ummar Annabi dan al’farma Annabi da Alqur’ani mai tsarki, ya Allah ka bani rai da lafiya dani da masu karatu ka nuna mana ƙarshen littafin nan lafiya kamar yadda ka nuna mana forkonsa lafiya, Amin ya rabbil izzati…
Yar Gidan Yaddiko Hausa Novel Complete
*LITTAFINA NA KUƊI NE, BIYA ƊARINKI UKU KACAL DOMIN SAMUN DAMAR KARANTASHI BA TARE DA HAƘƘIN KOWA A KANKIBA, AKWAI SP GROUP SHI KUWA 1K PASTING NASU YAFI NA ƳAN 300 YAWA, TURO ƊARI UKU TA ASUSUNA 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA, SAI KI TURO SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER TAWA 09097853276, ƳAN SPECIAL GROUP BANA SON KATI, GA POS BURJIK A GARI, KUMA YAN 300 IN DAI KINADA DAMA DAN ALLAH YIMIN TRANSFER TA AC YAFI, AMMAN IN YA ZAMA DOLE BA MATSALA TURO KATIN MTN NA ƊARI UKUN, KANA BA HOTON KATIN ZAKIYI KI TURO MINBA, A A NUMBERS ƊIN ZAKI RUBUCE KU TURO MIN*
Dan girman Allah da Manzonsa.
masu tambayata tsoffin littatafaina ku daina bana so.
Ku nema a cikin groups zaku samu, in dai ba Hukuncin Allah ko NAKASA BA KASAWA BACE, da GARKUWA kada ku tambayeni in kuna ƙaunar Allah, in kuwa bakya ƙaunar Allah to tambayeni.
*YAHUNDE! Babban birnin ƙasar Cameroon.*
Cikin wani kekyawan rugar FULANI mai tarin al’barkatun duniya.
Kota wani sashi Allah yayiwa Rugar Arɗo Babayo, ni’imomi na musamman, makiyaye ne cikakkun Fulanin ƙasar Cameroon.
Ranar wata jumma da yammaci la’asar sakaliya, makiyaya nata dawowa gida yayinda kota ina. Shanu tumaki raƙuma awaki zabbi keta kai komo ko wanne na nufar garken ma-mallakinshi domin ko dabba tasan uban gijiyinta,
Garken Arɗo Babayo yana ɗaya daga cikin garken da babu kamarsa a nahiyar Afirka baki ɗaya,
Yanada MAKIYAYA a ƙala mutun arba’in.
Garin ya fara duhuwar sanire alamun yanayin sanyin damina da ake ciki ko ina yayi kore shar ga tarin tsirrai kana ga igiyar ruwa da yayiwa rugar Babayo ƙawanya,
Wasu dattawane a zaune bisa ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake ƙofar gidan Arɗo babayo Farin dottijon ne mai cikar zarra da mutun taka ke zaune a tsakiyarsu, kana sai wasu manyan mutane dake zagaye dashi.
A gefen damanshi kuwa wani Babban mutun ne mai cikar zarra da wadatar zuciya ga tarin alamomin mutuntaka da cikar imani da haiba, bisa dukkan alamu tattaunawa sukeyi kan abinda ya shafi rayuwarsu.
Da sauri Arɗo Babayo ya ɗago kanshi ido ya zubawa sashin damanshi, inda ya hango wasu ƴan saffa-saffan samari guda huɗu suna biye da ƙatuwar suntsuwar Boleru babban cikinsu ne a gaba wanda zai kai shekaru 15 sa mai binsa wanda zai kai shekaru 13 sai mai bin masa da zai kai shekaru 11 kana sai ƙaramin cikinsu da bazai gaza shara 9 ba, gudu sukeyi sosai da iya ƙarfinsu sun tasa tsuntsuwar Boleru nan a gaba wacce ta kasa firewa sai gudu takeyi da sawunta biyu, bisa dukkan alamu tsuntsuwar tanada tsohon ciki mai girma.
Gudun da takeyi gudune na ceton rai.
Arɗon Babayo daya buɗe baki kenan da nufin zaiyi magana sai kuma ya juyo ya kalli kekyawar yarinya ƴar kimanin shekaru 8 a duniya wacce take kan cinyar mutumin nan dake gefen damanshi.
Ta miƙe da sauri cikin tsananin azama da harshen fillanci da ƙarfi tace.
(“Acce mo) Ku barta”. Sai kuma ta juyo ta fuskanci mutumin da take zaune kan cinyarshi cikin kaɗuwa da firgici da alamun tsananin tausayawa tace.
(“Appa a vi’a ɓe acca tokkugomo nɓe naunanmo) Appa kace su dena binta zasuji mata ciwofa”.
Murmushi Arɗo Babayo yayi tare da cewa.
“Kai Gainako ku barta zaku kamata a hankali ai”.
Da sauri wanda aka kira da Gainako yace.
“Baffa Giɗaɗo ne yace mu kama mishi ita mu yanka mishi”.
Da sauri suka juyo kan ƴarinyar jin wani irin ihu da tai tare da cewa.
“Ku yankata kuma, Appa kajifa wai zasu yankata, wayyo Appa kace musu kar su yankata, gashifa tanata kuka gashi sun sa taji ciwo a hannunta yanata zunda jini”.
Da mamaki suke kallon ƴarinyar sabida furucinta na wai hannunta yaji ciwo yana zubda jini, ina tsunstsuwar Boleru ina hannu?.
Wanda ta kira da Appa ne ya jawota gabanshi tare da cewa.
“Parvina tsuntsu kuma tanada hannune?.”
Da sauri ta miƙe tare da ɗaga murya tace.
“Ba tsuntsu bane Appa wlh mutunce gata nan da ciki gashi ma tana kuka tana-ta kare cikin jikinta”.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Boleru ido su dai Allah ya gani gaba ɗayansu tsuntsuwa suke gani tana guduwa da kyar wanda kuma kowa ya ganta yasan tanada tsohon cikine.
Giɗaɗo ne wanda shine ƙarami yaron ɗan shakara 9 kuka yasa tare da cewa.
“Wayyo ya Gainako kayi sauri ka kamo min ita karta gudu”.
jin haka yasa ƴarinyar nan da aka kira da Parvina ta miƙe da gudu tabi bayansu tana gudu tana kuka wanda har ga Allah daga cikin zuciyarta yake fitowa kuma ita ba tsunstsuwar Boleru take ganiba a zahiri a fili da kuma baɗinin Allah ya nuna mata mutum take gani kekyawar mace mai cikar sura da kamala kana ga ƙaton cikin dake jikinta wanda haihuwa yau ko gobe.
Ihu takeyi tana binsu tana cewa.
“Dan Allah ku barta zataji ciwo Wayyo Appa kazo mu ceceta zasu kasheta.”
Ihu tasa da dukkanin ƙarfinta tana yarfa hannu cikin gigita take kurma ihu lokacin da su Gainako suka isa kan tsuntsuwar Boleru suka danne fikafikinta suka kama suka medata baya.
Ihun da tayine yasa gaba ɗaya dattawan nan suka miƙe tsaye suka biyosu a guje dan ihun nata ya cika illahirin rugar babu wanda zaice baiji ƙaranta ba dan saida tsaunuka da kogin da suke gaɓarsu ya amsa da sautinda da take cewa.
“Wayyoooooooo! Appaaaaaa! zasu kasheta, sun karya mata hannu”.
A gigice suka ƙaraso wurin wanda ganin yadda take a gigice yasa Appa kamata da sauri, yayinda ita kuwa taketa son zillewa tana fiffizgewa daga hannunshi, Arɗo Babayo kuwa tsawa ya dannawa Gainako tare da cewa.
“Kai! Kai!! Kai!!! Gainako sake tsunstsuwar nan saketa”.
cikin sanyi Gainako ya sake tsunstsuwar, daga tsaye ta faɗi ƙasa hakan yasa,
Parvina sake saka ihu da ƙarfi ta fizge ta nufi kan tsuntsuwar da ita mace take gani kuma sanadin saketa da akayi daga sama ta faɗi ƙasa a kife yasa cikinta buguwa wanda yayi sanadin a take naƙuda ya fara murɗarta kana ga jini daya fara bin sawunta.
Tana isa gaban tsuntsuwar tasa hannunta ta kamo hannun baiwar Allah nan da ita kadai Allah ya bawa damar ganin a mutun ba tsunstsuwar Boleru ba, hannunta data riƙo su kuma kab mutanen wurin gani suke fiffigen tsunstsuwar ta riƙo.
Cikin kuka take shafa kan kurciya a ganinsu yayinda ita kuwa hawayen fuskar matar da take ganin take sharewa cikin muryar kuka tace.
“Sannu sunji miki ciwoko, kice musu ke ba tsunstsuwa bace ki gaya musu ke mutunce kamarsu ki gaya musu kema bani adam ce karsu yankaki”.
Kuka ta kuma fashewa dashi ganin matar nan bata magana sai dai hannunta data riƙo ɗin ta ganshi tamkar robo wato alamun hannun a karye yake, cikin sauri ta sake hannun tare da cewa.
“Appa mu tafi da ita mu kaita wurin masu gyaran ƙashi”.
To al’amarin parvina fa ya fara zarta zaton mai zato ya fara shallake tunanin mai tunani abin ya girmi shekarun Dattijannan.
Shi kuwa Giɗaɗo kuka ya fashe dashi tare da nufarta yana mai cewa.
“Ki bani tsunstsuwata ai tawace nine nayi ta renonta kullum tare muke cin abinci tare komai duk abinda naci sai na barmata dan tayi ƙatuwa, kuma yanzu kice baza a yanka min itaba”.
faɗawa tayi jikin matar wanda su a ganinsu ruggume tsuntsuwar tayi ita kuwa parvina cikin kuka ta juyo ta kalli Giɗaɗo tare da cewa.
“Kai mayene ko? To Wlh bazan baku itaba in dai ina raye a duniya bazan bari a cutar da itaba, babu wanda zai kasheta a gabana sai dai in bana raye ku bar ce mata tsuntsuwa wallahi tallahi mutunce kamar kowa”.
Kiran sallan magriba da akayine yasa ɗaya daga cikin dottijon mai suna Yayari yace.
“Arɗon Babayo lokacin salla yayi”.
Sai ya kuma kalli Giɗaɗo da Gainako da Seyoji da Ja’eh yace.
“Maza kuje kuyi al’wala kuzo muyi salla, kai Giɗaɗo ka bar mata tsuntsuwar kurciyar kaji ko gobe da safe zabbi za’a yanka muku ku gasa kuci”.
Cikin kuka Giɗaɗo yace.
“Wallahi Ni dai ta bani tsunstsuwata, bana son zabuwar ni ko ɗawisu zaku yanka min bana so kurciyata nake so a bani abuna”.
(Giɗaɗo sabo da kaza baya hana a yankata kenan)
Cikin tsawa Arɗo Babayo yace.
“Kai tafi daga nan ba kaine babba ba kaci girma ka bar mata tsuntsuwar kaji ko Giɗaɗona”.
Tura baki yayi yabi bayan yayun nashi yana cewa.
“Ni a dena cemin Giɗaɗo ai dani Giɗaɗone da komai nakeso zaku bani”.
Basubi ta kanshi ba duk suka meda hankalinsu kan Parvina da tsuntsuwar dan ganin ƙasan tsuntsuwar Bolerun yana zubda jini, wannan abun ya sasu cikin nazari to, amman sai mgnar Parvina ta katse musu nazarin da cewa.
“Allah sarki gashi sunji mata ciwo har sun fidda mata jini”.
Jin haka yasa suka sa a ransu yess jinin ne daya fita sanadin jin ciwo,
cikin kula Arɗo Babayo ya matso parvina da taketa shafa kan tsuntsuwar da suke gani a idanunsu a hankali ya kamo hannunta cikin lallashi yace.
“Parvina muje cikin gida ko, kinga dare yayi kiyi salla kici abinci, tsuntsuwar taki kuma ki saketa zata fire ta hau makwancinta”.
Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na zuba tace.
“Baffa Arɗo ta fire kuma? Bata da fiffigefa mutunce fa,tare zamu kwana da ita wallahi ba tsunstsuwar bace, mutunce ku daina ce mata tsuntsuwa, karmu barta ta kwana a woje”.
Sai ta kuma kama fiffigen tsunstsuwar tace.
“Ga hannunta nan sun karya mata”.
Sai ta kuma kama ƙafafun tsuntsuwar tace.
“Baffa Arɗo kaga ga sawunta ga idonta tanata zubda hawaye ga cikinta ga kunnenta ga bakinta ga gashin kanta har bayanta”.
Kallon-kallon suka tsaya sunayiwa junansu,
domin kafiyar parvina kan cewa Wannan tsuntsuwar Boleru mutun ce bani Adam ce ya fara basu tsoro to ko dai ƴarinyar tayi gamone? Koko tsuntsuwar iskace?.
cikin tsoron daya fara rufe Appa baki na rawa ya kamo hannun ɗiyar tashi da yake masifar so tamkar ƙoƙon ranshi cikin kaɗuwa da muryar fillanci kasan cewar sam fulanin ƙasar Cameroon basa jin hausa koda kawo min wuƙa in kashekane shiyasa cikin fillanci yace.
“(Parvina tsonɗu on fa na ɗum innu adamajo, ko waɗi a vi’ata neɗɗo on) parvina tsuntsuwace fa ba mutun bace meyasa kicewa mutunce?”.
Kuka ta kuma fashewa dashi harda shessheƙan gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi ganin yadda jikin matar ke karkarwa. Ruggume tsuntsuwar kurciyar tayi a ganinsu yayinda ita kuwa cikekkiyar kamilar mace take gani hannunta matar ta kama ta juya ta nufi cikin gidansu dansu da Gainako suka shiga tana kukan shur-shur da hawayenta.
Zurui sukayi suka rakata da ido har ta ɓacewa ganinsu.
A mashigar gidan sukayi kiciɓis dasu Giɗaɗo da sauri ta koma gefe.
Shi kuwa Giɗaɗo wani irin dundu ya kima mata a tsakiyar bayanta tare watsa mata harare cikin fillanci yace.
“Hegiya muguwa wallahi sai na yanka tsuntsuwata muna fuka”. da sauri tasa jikinta ta kare tsuntsuwar, tare dayin sauri tayi cikin gida.
Seyoji ta samu tsaye gefen mamansu yana bata labarin tsuntsuwar da duk gidansu babu wanda bai san Giɗaɗo da itaba dan yanzu kimanin watanni takwas kenan kullum babu dare babu rana a nan gidan nasu tsuntsuwar take rayuwa kullum in Giɗaɗo yaci abinci ya rage inta kuma sai tazo tayi ta tsastsaga har sai tacinye duk abincin daya bari kana ya ajiye mata madarar shanu nanma tazo tasha,
idan tasha ta ƙoshine sai ta juya da tafiya take barin cikin gidan ta koma bakin kogi.
Da sauri Mamansu Giɗaɗo ta kalli Parvina tare da cewa.
“Parvina na zo nan zo keda tsuntsuwar ki kada ki damu babu mai yankata”.
Da sauri ta iso gaban matar tare da cewa.
“Inna ki hanasu yankata Allah kuwa ba tsunstsuwa bace mutunce”.
Cikin kula matar tace.
“To parvina kada ki damu babu mai yankata daga yau ta zama taki, yanzu ajiyeta kije kiyi al’wala kizo kiyi sallah”.
Da sauri tace.
“To”.
A jiye matar tayi bisa taburmar dake tsakiyar gidan, kana taje tayi al’wala tazo ta shimfiɗa sallaya a gefenta, itama Inna gefenta ta shimfiɗa suka sa baiwar Allah’n nan a tsakiya…
Kamar da wasa da abin ya girmama domin koda sukayi salla isha’i fir parvina taƙi ta rabu da tsuntsuwar nan.
Su kuwa su Arɗo Babayo sun mance batun tsuntsuwar ma, tunda sukayi sallan isha sukaci abinci.
Suketa lissafin kan dabobbinsu kama daga kan Raƙuma, Dawakai, shanu, tumaki, raguna, awaki, ɗawisu, tolo-tolo, zabbi, tattabaru, saida suka waresu baki ɗaya dan sanin adadin zakkar da zasu fitar sannan suka gama fayace na zakkar kowanne daga ciki da shariya ta umarci a bada zakkanshi.
Hira sukaci gaba dayi kan abinda ya shafi kiwon nasu.
A can cikin gida kuwa, tunda Inna ta gama yiwa su Arɗo Babayo gashin zabbi ta haɗa da madarar shanu aka kai musu taketa fama da Parvina kan yadda ta tasa tsuntsuwar nan a gaba tana mata magiya kan tasa hannunta taci abinci,
ganin bazata iya ci da hannun nata bane yasa iya tasa hannun tana bata abinci har baki tana amsa tanaci yayinda hawaye keta kwaranya a fuskarta babu ƙaƙƙautawa.
Koda taci ya isheta sai ta mirgina alamun zata konta.
Ganin hakan yasa parvina kallon inna cikin sanyinta da nitsuwarta tace.
“Inna tare zamu kwana da ita”.
Kai inna ta jinjina mata kana ta miƙe tace muje cikin ɗakin kinga gari yayi sanyi Giɗaɗo da kike tsoron kada kiyi bacci yazo ya ɗauke tsuntsuwar ma yayi bacci”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe suka shiga cikin ɗakin,
bisa katifar gado huts ɗinnan ta zauna tare da tsuntsuwar a gefenta, yayinda ga hasken wutan da aka kunna janareta ya gauraye ko ina na gidan da kuma ɗakin.
Inna kuwa kan gadonta take,
suna ɗan hira,
yayinda sam hankali parvina kan tsuntsuwar nan yake.
Tashi zaune tayi lokacin da taga gaba ɗaya jikin matar nan yana ta karkarwan ga hannunta dasu Gainako suka karya ya kumbura simtin, hannunta mai lafiyan kuma ta ɗaurashi kan tirtsetsen cikinta, gaba ɗaya jikinta zufane keta tsastsafowa tako ina,
cikin tausayawa parvina tace.
“Sannu hannunkin ke ciwo ko? Kiyi haƙuri gobe da safe zamu kaiki gidan mai magani”.
Inna ce ta zubawa Parvina ido cikin yanayin tsoro tace.
“(Parvina ɗun sonɗufa) Parvina tsuntsuwace fa. ki dena magana da ita ba jinki takeyi ba”.
Da sauri ta jujjuya kanta hawaye na zubo mata tace.
“Inna Wallahi tallahi mutunce ku dena ce mata tsuntsuwa inna ki ganifa bata da lfy, jikinta duk rawa yakeyi”.
Kai Inna ta gyaɗa kana tace.
“To na yarda yanzu dai ki kwanta kiyi bacci sai gobe da safe zamu kaita gidan mai gyaran karaya da targade”.
Jin hakane yasa ta konta tare da lumshe idonta. Sai bacci ya fara saceta sai kuma tayi firgigit ta farka,
ta kuma tada Inna sabida, suntsuwar nan ta kasa nutsuwa, yayinda ita kuwa Parvina take ganin baiwar Allah’n cikin mawuyacin halinda ya rintane yasa bata gane cewa matarnan naƙuda takeyi ba.
A haka suka kwana, har garin Allah ya waye basuyi bacciba, sabida ita kanta inna yanzu tsoron tsuntsuwar ta fara haka kuma take tsoron parvina, ita kuwa baiwar Allah’n nan zafin ciwon naƙudane ya hanata bacci ita kuwa parvina tausayin matar da mutanen garin da gidan ke cewa tsuntsuwar Boleru ne ya hanata bacci.
Asuban fari suka tayi sukayi salla,
daga nan suka fito tsakiyar gida, kai tsaye sashin Arɗo Babayo suka nufa ita da Inna,
shiru sashin nashi alamun basu dawo masallaci ba, cikin alhini da tsoro Inna ta kalli Parvina cikin daburtacciyar murya tace.
“Ajiye tsuntsuwar nan haka kina rike da ita kamar kin samu uwarki maza ajiyeta”.
Cikin zubda hawaye ta tsuguna ta ajiye tsuntsuwar kan buzun Arɗo Babayo,
Wanda dai-dai lokacin ne kuma Arɗo Babayo da Appa, Gainako, Seyoji, Buba, Giɗaɗo, Ja’eh suka shigo kamar yadda suka saba.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Kurciyar nan ido ganin yadda taketa birgima a kan buzun tana wasu irin cure-cure tamkar ranta zai bar jikinta.
Ita kuwa Parvina kuka ta farayi bil haƙƙi da gskya tanayi tana yarfa hannu,
Buba ne yayi maza ya nufi kan tsuntsuwar kurciyar tare da cewa.
“Haukan banza a kan buzun salan Arɗo zaku ajiye tsuntsuwar.
Ihu mai ƙarfi parvina tasa ganin Buba ya ɗaga kafarshi da ƙarfin bala’i zai kaiwa tsuntsuwar harbi da naushin ƙafarsa,
Kamar a mafarki kamar gilmawar walƙiya tamkar daga sama.
Sukaga tsuntsuwar Kurciyar nan tayi wani irin ɗagowa ta karkaɗa fikafikinta cikin ƙudurar Ubangiji da hikimarsa da buwayarsa sai gata-ta d…!
Salon na dabanne labarine mai cike da sarƙaƙiya, biya 300 ko 1k ki karance badaƙalar cikin salama.
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 2
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*LITTAFINA na kuɗine, akwai na 300 wanda a wata ɗaya za’a gama Part 1, akwai kuma na 1k wanda a mako biyu kacal za’a gama Part 1 da izinin Allah. Yimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1ooo ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar BIYANKI ta number 09097853276 Ayyah ƴan SP Group banda kati, in baki da ac bada a POS. Kuna ƴan 300 in dai da hali turamin ta ac yafi, in babu kuma to turo katin mtn na ɗari uku ta layin 09097853276. Na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san niyarki ki saya ki fiddamin littafina, dan daraja da girman Allah da tsarkin al’ƙur’ani kada ki saya Please kuwa darajar iyayenki kada ki saya, ba don niba sai ɗan Allah da manzonsa da iyayen da suka haifeki/ka*
~AKWAI KAYAN GYARA HAƊIN AMARE DA MASU JEGO, DA MASU SABUNTA AMARCI, IN KINASO KI TUNTUƁI WANNAN NUMBER 09097853276~
Ta juye ta dawo mutun *bani Adam* mace fara ƙal mai tsananin kyau da cikar sura da haiba.
Wani irin zabura sukayi cikin tsananin tsoro da firgici da tashin hankali suka zaburi gaba ɗayansu, Giɗaɗo kuwa da azaban ƙarfi ya afka jikin Arɗo Babayo,
Inna kuwa gaba ɗaya jikinta rawa da karkarwa yakeyi tamkar mazari wata iriyar fitinenneyar zufa mai azabar ƙarfice taketa tsastsafo mata tako wani sashi na jikinta.
Seyoji, Gainako, da Ja’eh, gaba ɗaya jikinsu karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Giɗaɗo kuwa wani irin juyawa yayi a firgice ya yunƙura zai gudu, Arɗo Babayo ne yayi hamzarin kamo hannunshi ya rikeshi gam.
Zabura sukayi.
Gaba ɗayansu sabida wata iriyar fitinenneyar iska mai azabebben sanyi daya fara kaɗawa yana rausaya ganyayyaki da dukkan tsirran dake yakin surururururu haka iskar ke kaɗawa a hankali tana ratsa jikinsu.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun. Hasbunallahiwani’imanwakil”.
Shine abinda suketa maimaitawa gaba ɗayansu cikin tsananin kaɗuwa, ruɗani, firgici, tashin hankali da tarin tsoro, da nitsuwar ganin ikon Allah.
Iskar dake karkaɗawa ce tasa gaba ɗaya suka hautsine.
Parvina kuwa da sauri ta faɗa jikin baiwar Allah’n tare da ruggumeta.
Baki na rawa ta fara addu’a.
“Allahumma inni as’aluka khairaha wa’azubika min sharri ha”.
Da ƙarfi take fidda sautinta tana maimaita addu’ar.
Wanda sanadin haka suma kab suka fara bin bakinta.
Allah cikin ikonsa da ƙudurarsa sai ga iskar nan ta fara lafawa a hankali.
Cikin al’ajibi da tsoron ƙudurar Allah suka ware idanunsu baki ɗaya a kan baiwar Allah’n nan, da
shigar suturar dake jikinta ne yayi masifar sasu ruɗani.
Cikin dakiya da ƙarfin zuciya Arɗo Babayo ya kalli Buba a hankali yace.
“Buba ɗauki su Giɗaɗo ku tafi garke kuje kuyi tatsa”.
Kai ya gyaɗa mishi domin baki da jarumar Buba sun tafi,
Dan a iya tsawon tarihin rayuwarsa ko a films ko a books story bai taba ji da katari da makamancin abinda ya yagini a zahiriyaba, tsuntsuwar Kurciyar ta zama mutun mace a gabanshi ba labari aka bashiba ra’anul ayni.
Cikin yanayin tarin kaɗuwa da rawan jiki yasa hannu ya jawo hannun Giɗaɗo daya kifa kanshi jikin babanshi.
Cikin fillanci yace.
“Zo Giɗaɗo zomu tafi”.
Da sauri ya miƙa hannunshi ya kama na Buba kana suka juya suka fita.
Appa kuwa kanshi ya kauda daga kallon wannan kekyawar halittar dake gabanshi a cikin ransa yace.
“Anya kuwa, wannan mutunce ba iskaba”.
Inna kuwa gefe ta ɗan matsa cikin rawan murya na tsoro da hausar da sai ka dage zaka gane me take cewa tace.
“Ra ga Allah bewar Allah mutun ko al’jan?”.
Ido suka tsurawa matar a zatonsu ko zata basu amsa.
Sai dai ganin yanayin da take cikine ya sasu cire tsammanin samun amsarta.
Domin gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, tamkar mazari.
Kana sai zufa dake tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta,
ta rumtse idanunta da azaban ƙarfi, tasa haƙoranta ta datse lip ɗinta na ƙasa,
duk mace data taɓa haihuwa in ta ganta tasan naƙudace ke azazzabarta.
Tausayin ta ne ya cika zuƙa tansu baki ɗaya.
Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace.
“Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al’jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al’amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace”.
Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa.
Appa ne ya kalleta tare da gyaɗa mata kai, alamun eh ta taimaketa,
Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace.
“Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata”.
Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace.
“Zo nan Parvina za’a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta,
kinga ki dena danne mata hannun da cikinta”.
kai ta gyaɗa kana ta kalli matar cikin sanyi tace.
“Sannu!”. Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu,
haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba.
cikin sanyi tace.
“Taso muje daga ciki”.
ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji,
hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye.
Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas.
Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin ɗakinta ta kaita,
a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta,
da sauri ta koma woje wuta ta hura ta ɗaura ruwan zafi.
Kana ta dawo ciki.
Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta.
Gefenta ta zauna ta zuba mata ido.
Jin an zauna gefen tanne yasa ta buɗe kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace.
“Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?”.
Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji,
murmushi inna tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana”.
Kanta ta jujjuya mata alamun.
“Bazan iyaba”.
Jin muryarsu Arɗo Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito,
Ganin Arɗo Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa.
“Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa”.
Taburma ta shimfaɗa musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa.
“A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?”.
“Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne”.
Inna ta faɗa cikin alhini.
Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
“Ina son ganinta”.
Arɗo Babayo ne yace.
“To bisimilla, shigo daga ciki”.
Ɗakin suka nufa Inna na gaba Arɗo Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya.
Suna shiga suka sameta zaune ta haɗe jikinta wuri ɗaya,
jin motsin shigowar mutanene yasa ta ɗago kanta,
da sauri ta kauda idanunta.
Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al’hini yake cewa.
“Mutun ce ba al’janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki.”
Sai kuma ya kalli Arɗo Babayo cikin sauri yace.
“Maza a bani madarar shanu mai ɗumi wanda aka tatsa yanzu”.
To Arɗo Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono,
da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin.
Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan,
yana amsar ƙoryar,
ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar,
saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace.
“A bani zuma da zam-zam”.
Da sauri tace.
“To”. Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,’.
Kana ya bawa Malam Liman da Arɗo Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar.
Inna ya miƙawa kwaryar yace.
“Gashi bata tasha”.
Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta.
Tare da cewa. “Bismillah ki Sha”.
A hankali ta buɗe bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haɗe da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa.
Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta.
Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna.
Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar.
Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin ɗakin ta wuce.
Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa.
Bayan sun yanke cibiya sun gyara,
komai na wurin.
Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka,
ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haɗeta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle.
Koda suka fito daga wonka,
konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da ƴar a gabanta.
Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa,
Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al’ƙur’ani mai girma da tarin addu’o’in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma.
Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje.
Sashin Arɗo Babayo suka nufa,
suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy.
Shiru sukayi baki ɗayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana.
“To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah”.
Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa.
“Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka.
Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaɗanne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana”.
Arɗo Babayo ne yace.
“Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al’ajabi”.
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
“Ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi ɗan adam dare”.
Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa.
“Yanzu tayi magana ne?”.
Da sauri Inna tace.
“A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa”.
Kai ya rausayar tare da cewa.
“Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace zan bata magunguna kuma,
sannan kada kuji tsoronta ko kaɗan in sha Allah ba mai cutarwa bace”.
Malam Liman ne ya gyara babbar rigarshi tare da cewa.
“To wannan baiwar Allah’n ko daga ina ta fito? Ko ta yaya zamu gano yan uwanta danginta ahlinta ko wani nata a duniya?”.
Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
“In sha Allah ita in ta dawo haiyacinta, zatayi mana bayanin komai zata faɗa mana sunanta sunan garinsu sunan iyayenta sunan mijinta da anguwarsu sai mu mikata garesu”.
Appa ne ya ɗanyi ajiyan zuciya tare da cewa.
“Allah ya bata lfy ya kuma dawo da ita cikin haiyacinta, kuma in sha Allah duk wani abu daya kamata ayimata a duniya zan mata har sai munga ta samu’ lafiya ta koma ga iyayenta”.
Da haka sukayi ta tattauna duk abinda ya dace ayi mata.
Anan kuma sarkin baka yaje da kanshi ya ɗaure mata karayar hannunta yayinda Parvina kuwa ke like da ita…!
Haka Inna da iya laure sukayi ta kula da ita a cikin wannan satin sunan…!
************
…Bayan shekaru Goma sha biyu…
Cikin Ƙasar Kautal A Jihar Ɓadamaya state.
A wani yanki na Ɓadamaya state, cikin Shikan local Government area a wata rugar FULANI mai suna.
*RUGAR BANI*
Garin Shikan wani yankine daga yankunan Ɓadamaya yankine mai tarin ƙabilu ma banbanta addinai da al’adu wanda duk yankun Ɓadamaya shida Bimu sune sukafi tarin ƙabilun sai dai babbancin mafiya yawan kabilun Bimu musulmaine saɓanin mafiya yawan ƙabilun Shikan kafurine maƙiya Allah da Manzonsa.
Shikan shine sashin da yafi tara ƙabilu mafiya yawa, masu baƙaƙen zuciya ƙabulun da hasken addini bai cimmusuba.
Ƙabila mafi rinjaye a yankin Shikan itace ƙabilar ɓachama. Mafi akasari Ɓachamawa mutanene kafurai ne marasa ɗigon imani a zuƙatansu marasa son zaman lfya, mugunta da kisa shine abinda ke sasu farin ciki, abinda kawo ya sanine duk sanda akaji jihar Ɓadamaya cikin wani tashin hankali to daga ƙabilar ɓachama ne.
Duda yawan ƙabilu na garin Shikan hakan baisa fulani sun sakar musu garinba, domin tushen garin na fulanine, sabida kowa yasan makiyayi basa nesa da wurin damshi da ruwa, domin rayar da ababen kiwonsu.
Haka yasa akwai musulmai Hausawanmu da tarin yawa cikin garin Shikan, wanda duk rintsi da wahala sunƙi barin garin, koda yake hakan baya rasa nasaba da irin al’barkatu da ni’imomin da Allah yayiwa garin.
Daga gefen. Garin Shikan akwai babban kogin da yakeda ruwa biyu wanda ko wucewa zakayi ta kan babban gadan da titin da zai kaika cikin Ɓadamaya zaka hangi ruwane kala biyu a kogi ɗaya basu kuma taɓa haɗewa wuri ɗaya ba da izinin ubangiji.
Gefen kogin ta dama wata babbar *Rugar fulani mai suna Rugar Bani* ce mai tarin tarihi, rugace mai girma wacce Ubangiji ya ƙawatata da ababen buƙatar yau da kullum, wannan Ruga itace yanki mafi sanyi a yanki Ɓadamaya state rugace damu fulani muke ce musu *JOTTAN MA’EN* Bi ma’ana fuli mazauna wuri ɗaya, ba ire-iren fulani makiyaya masu tafiye-tafiye bin rugageba, fulanin Rugar Bani fulanine makiyaya masu tarin dabobi masu tarin yawa, Rugar Bani Rugace da aƙalla fulaninmu sunyi sama da shekaru dari da ashirin awannan Rugar, shiyasa harda gini zamani da kyawawan gidaje fulanin sukayi, yayinda kuma akwai bokkokinma a cikin Rugar tasu wanda kuma suka sayi filin da kuɗinsu zufansu a hannun sarkin Shikan na wancan zamanin ya sayar musu yankin wurin gaba ɗaya sun biya kuɗinsu ya kuma basu takardu su, suna zaune a nan suna noma suna kiwo.
Rugar Bani na zagaye da ƙauyukan ƙabilun Ɓachamawa da tarin yawa, wanda nan gefensu ƙauyen Bonon yake wanda nanne dodon tsafin ƙabilar ɓachamawan take wanda sunan dodon tsafin nasune suka sawa suna ƙauyen suna Bonon. Kauyen Bonon shine zuciya da karfin kafuran nan, sunyi imani dashi, fiye da zaton mai zato, koda laifi wani yayi bonon ake kaiwa ƙara kuma muddin bonon ya tsinewa mai laifinsun to zai lalace ya ɗai-ɗaice dashi da zuriyarsa baki ɗaya, da yake sunyi imani da hakan kuma yana faruwa suna gani shiyasa bonon yake tamkar zuƙatansu, kamar dai yadda in jikin ɗan adam idan zuciya ta ɓaci gagganji na ɓaci to haka bonon take a wurinsu… Wannan kenan
Rugar fulanin Bani yafi ko wani yanki na Ɓadamaya sanyi mai ɗan karen daɗi.
Koda yake hakan ya samune sanadin ƙawanya da wani babban dutse mai fesar da numfashin sanyi yayi musu, wanda ya kasance musu tamkar rufar garin.
Gefen hagun Rugar Bani kuwa wani babban fadama ne mai cike da lamɓu mai ɗauke da ababen more rayuwa wanda ya kasance mallakinmu Fulanin Rugar Bani, lambun yana da duk wasu kayan marmari kamarsu.
Lemu, mangoro, gwaiba, ayaba, dabino,kwakwa, kashu, kankana, abarba, da jefi-jefin tuppa da inabi.
Wanda wannan fili yake mallakin Fulanin Rugar Bini’nne, kana bayan filin kuma akwai wani rafin da ya kasance masarrafin noman shinkafawa ne wanda suke yinshi noman rani da damina, kuma shina mallakin Fulanin Rugar Bani ne, wanda komawa yasan iya filinshi,
Daga gaban Rugar Bani kuwa kogin Shikan ne malale a gabansu iya ganin mai hange da ido biyu gefen hagunsu kuwa nan garken shanunsu ke shimfiɗe bila adadin.
Rayuwar Fulanin wannan Rugar rayuwace mai cike da aminci da amana da hakuri da kauda kai duk da tarin zalunci da kafurai ƙabulun Ɓachamawa keyi musu.
“Kamar yadda duk kowa ya sani duk duniya anyi ittifaƙin ba fulatani ko ba fulatana basa neman tsokana ko tada husuma bare tada zaune tsaye. Akan cutar da bafulatani yayi kamar bai san an cutar dashi ba ko bai ganeba, wannan dalilin yasa duk ƙabilun ƙasar Afirka sukeyiwa ƙabilarmu kallon wawaye ne ko basu san abinda sukeyiba ko sokayene, masu ƙarancin wayewa Gidadawa.
Mu kuwa a namu sashin fulani mun kasance masu kauda ido kan cutarwar forko data biyu, sai dai a haƙiƙinin gsky bama lamunta ko jurar cutarwa ta uku! Domin rama cuta ga macuci ibadace. Kuma Ba’a sarar mumini a rami ɗaya sau uku”.
Wannan shine jawabin da wani farin dottijon bafulatanin dake zaune tsakiyar al’ummar wannan rugar bayan sun dawo daga jana’izar mutun ɗaya da ƙabilun ɓachama suka kashe musu cikin sunkuru, a daren jiya wanda ya kasance ɗane ga Arɗon Yabani shugaban Rugar tasu kenan.
Hannu yasa ya share zafafan hawayenshi dake kwaranya daga ida nunshi cikin ɗaga sauti yaci gaba da cewa.
“Fulani basa ɗaukar mataki domin yaƙi ko zalumci sai dai dan kare kawunansu. Kuma kun sani duniya duk ta sani FULANI BA ƳAN TA’ADDA BANE! Ba ƴan bindiga daɗi bane, makiyayene masu ƙare rayuwarsu dan samawa mazauna cikin birane jin daɗin rayuwa, muyi kiwo mu kai musu suci naman susha madarar shanu kana muyi noma mu ciyar dasu.
Meyasa su mutanen birane basa ɗaukar matsalarmu tasu matsalar ana kashemu tamkar kiyashi kuma babu masu kulawa”.
Tsagaitawa ya ɗanyi tare da shashsheƙa cikin bada umarni a matsayinsa na shugaban Rugar uban wanda aka kashe kuma yace.
“Na roƙeku da Allah kada wanda ya ɗauki makami domin ramuwa duk da munga yankan rago akayiwa Hashimu amman bamu san wayeba kuma bamu da hujja, dan haka kada wanda yace zai ɗauki makami.
Muyi rubutu mu aikawa maimartaba sarkin Ɓadamaya, domin Al’ƙalami yafi tokobi, mu kai kukanmu gareshi, tunda shi sarkin wannan yanki na Shikan mun kai mishi kukanmu a karo na barka tai bai kulaba, kuyi hakuri mu miƙa lamarinmu ga sarakuna mu, inada yaƙinin zasuyi mana adalci”.
Shiru mutanen da aƙala sun kai ɗari da ashirin sukayi.
Yayinda kowa ya keta zubda hawaye.
Sai ɗaya daga cikine da ya kasance baƙin jakada Ɓachama ruwa biyu uwarshi ƙabilar ɓachama, wacce ubanshi bakura babarbaren borno wanda shike saida kanwa a rugartasu ya auro Uwar Ba’ana. yana naɗa komai a wayarshi,
domin miƙawa shugaban mayaƙan ƙabilar ɓachama, komai ya gani, domin shi ɗin ya kasance, makashinsu ne kuma taburmarsu ne, domin dama bahaushe yace sai da ɗan gari akanci gari da yaƙi!…
A cikin babban birnin Ɓadamaya kuwa. *Land of beauty* Garin Modibbo Joɗa,
Mai tutar fulɓe garinda duk arawacin ƙasar Kautal mune kaɗai muka rage da tutar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo.
Wanda ya dasashi ya kafashi da hannunshi masarautar fulbe mai ƙarfi Masarautar Joɗa…
Cikin birnin matsarautar Joɗa.
A cikin babban birnin Ɓadamaya.
Wasu irin tsala-tsalan motocine wanda a ƙalla sun kai Goma suke jere suna fitowa daga harabar shaharerriyar makarantar Jami’a ta dake cikin babban birnin Ɓadamaya wato J.U.B Joɗa University Ɓadamaya
Yayinda suke tafiya a jere a jere cikin tsananin gudu tamkar zasu tashi sama kana ga jiniya daya karaɗe illahirin sashin wurin wanda dole yaja hankali duk wanda ke wurin gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama da titin.
Motoci huɗune a gaba, wanda suka kasance masu kyau.
Sai wata Rolls Royce, mai kuɗi kimanin naira million 4, 959,630. Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai sheƙi da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine ƙal sai glass ɗinta daya kasance tin tek mai duhu.
Wani kekyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa.
Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin Super Nour a jikinsa wanda a ƙalla zai kai tamanin ɗ kuɗinshi, ya ɗaura baƙar al’kebbarsa ta jinin larabawan saudia Al’kebbar baƙace mai faɗi, kana yasa farin hirami a kanshi da zagayen baƙin saman hiramin.
Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido, wani irin tsabtaceccen gemune da bazai wuce kamu ɗaya ba ne yayi lib a haɓarsa.
Zaune yake cikin motar ya jingina bayanshi da sit ɗin, ya lumshe fararen idanunshi,
A hankali yake motsa tattausan jajayen laɓɓansa yana tasbihi.
“Subahanallahi wal’hamdulillah wa la’ilahaillah Allah Akbar, Astagafillaha wa’atubu ilaik”.
Yanaji a jikinshi kudun da akeyi yayi yawa, to amman dolene ayi irin wannan gudun domin lokaci na gab da ƙurewa, dan sosai sallan jumma’ar ya gabato, yasan yanzu masallacin ya fara cika, wannan dalilin yasa bai hana drevernshi gudunba, kuma bai hana fadawanshi sakin jiniyarba, dan ta hanyar jiniyarce zaisa a basu hanya su samu su isa kan lokacin daya dace.
Bawai ya bari ayi jiniyar da gudun dan nuna isa da ɗagawa bane, sai dan son isa masallacin Masarautar Joɗa da yake limanci kuma yake gabatar da Hudubar jummar matuƙar yana ƙasar tiyatar da yayiwa watace ya sa lokaci yaso ƙure mishi.
Motoci, biyar kuma na bayanshi wanda uku daga ciki na ɗaliban J U B da ya fitone, wanda yana aiki cikin Hospital ɗin makarantar, bayan kuma asibitinshi da kuma Genaral Hospital Ɓadawaya da yake zuwa sau ɗaya cikin ko wanne sati.
motoci biyun bayanshin kuma, Jalal ne da abokanshi.
Shiyasa motocin suka taho a jere-a jere dan shi bai fiye yarda ya fita da mota sama da biyarba, suma ba kullum ba, wani lokacinma yakan fita shi ɗaya.
A haka dai har suka fara ratsowa cikin Ɓadamaya, a dai-dai mashigar laleko ne,
Cunkoson ababen hawan ya yawaita, yayinda suka danno kai wurin yasa da yawa suka fara komawa gefen titi suna kauce musu dan basu hanya dan jiniyar dake musu nunin akwai uzurin gaggawa ga kuma fadawa a motocin.
Wani mai keke Napep ne ya gangara gefen titi har kusa da wani mai saida su Oranges Banana da dai sauransu.
Dogon tsaki mai Napep ɗin yaja tare da cewa.
“Wannan ai mulkin mallaka ne da izza duk an tsaidamu sabida wani can zai wuce ai duk nan muma saurin mukeyi munada babban uzuri, saurin da duk mutanen wurin nan keyi duk an katse mana hamzarinmu na son isa masallaci kan lokaci muji huɗubar jumman wannan rana”.
Mazan dake cike a bayan napep ɗin ne suka haɗa baki wurin cewa.
“Wallahi kuwa, gashi motocin nasu nada yawa.
zasu sa mu rasa jin hudubar wannan fasihin Malamin”.
Wani mai motane dayake gefensu ya amshi zancen da cewa.
“Kuma gaba ɗaya mutanen nan wurin masalacin zasu tafi, sabida duk mai son jin huɗuba mai ratsa jiki da zuciya baya ƙaunar ko furuci ɗaya na wannan malamin ya wuce shi domin Allah ya rigada ya mishi baiwar lafazi mai shiga zuciya”.
Wanda ke gefensu ne ya amshi zancen da cewa.
“Gaskiya ne wannan sabida shi Allah yayi mushi baiwar lafazi da iya tabsiri mai nusar da gafalelle”.
Mai saida kayan yayan itatuwan dake gefen sunne yayi ɗan murmushi kana ya miƙawa ƴan matan daketa kallon motocin da ido, lemun da suka saya ya miƙa musu.
Kana ya kalli dan-dan zo matasa daketa wuce da kafa,
mutanen daketa maganar Malamin ya kalla tare da cewa.
“Eh kam gsky duk malaman ƙasar nan babu yashi a lafazi, cikin second ɗaya zai yi maka lafazin da zai gamsar da kai tsawon shekaru Talatin,
koda yake hakan baya rasa nasaba da tsatson mahaifiyarshi, da ta kasance balarabiya kuma alarabawanma a cikin ƙabilar da tafi dukkan ƙabilun duniya a baiwar lafazi da iya sarrafa harshe”.
Cikin mamaki suka kalleshi,
Alhajin dake cikin zazzafar motar shin nanne yace.
“Haba sai haka mana ashe Balarabe ne wani yanki na tsatsonshi Allah yayi mishi rahamomi masu tarin yawa.
Gashi wannan zai hanamu muje muji Kuɗubar”.
Murmushi mai Appul ɗin yayi tare da kallon gefen baya yadda ya hango dandazon motoci da keke Napep dama masu tafiya da sawu ma.
Wasu na meda motocinsu gefe sukayi suna fitowa da sallayoyinsu a hannu suna takowa da ƙafa,
kanshi ya ɗan rausayar ya kalli mutanen dake gaban nashi tare da cewa.
“Kasan su wayene a cikin motocin nan da kuketa zagin kuwa?”.
Da sauri suka jujjuya kai tare da cewa.
“A a waye ne?”.
Tsala-tsalan motocin ya zubawa idanu zazzafar farar mota kirar Rolls Royce ɗince ya zubawa ido a hankali ya maida kallonshi garesu tare da cewa.
“Shine Sheykh J….!
Uhummmm wasa farin girgi.
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 3
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*FREE PAGE*
*LITTAFINA NA KUƊI NE. TURO 300 DOMIN samun damar KARANTASHI. Ko ki turo 1k domin shiga SP Group, inda zaku samu posting fiye da na 300. Ayyah Ƴan SPG bana son katin, turo dubu ɗayan ta asusuna na, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta layina na 09097853276. Kuma masu 300 in dai kinada damar turawa ta ac tura,in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari ukun ta layina na 09097853276, ba hoton katin zaki turoba, numbers ɗin zaki kofa ki turon*
“`ALHAMDULILLAH MASU NEMAN TSOFFIN LITTATAFAINA, NA SAMESU GABA ƊAYA, SAI RIGAR KOWA NE BAN SAMUBA. IN KINASO KIZO DA KATIN MTN NA ƊARI UKU kacal IN BAKI DUK LITTAFIN ƊAYA DA KIKESO, A CINSU.ƳAR FULANI, MU’WASMITI, NAMIJI BAYA KAƊAN, A TAUSAYAWA JUNA, BANDIRAWO, RUBUTACCEN AL’AMARI, HUKUNCIN ALLAH, NAKASA BA KASAWA BACE, DA KUMA GARKUWA.“`
“Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa ne.
Doctor Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kenan. Ina nufin GARKUWAN FULANI”.
Da mamaki a fuskokin su sukace.
“Astagafirullaha. Bawan Allah ashe sauri yake ya rigamu kada muje muyi ta jira”.
Kai mutumin ya jinjina musu tare da nuna motoci biyu wanda Jalal da abokanshi ke ciki, wanda kiɗan dake tashi cikin motocin ya cika ko ina, a hankali yace.
“Wannan kuma Jalaluddin kenan ƙanin Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero”.
Dai-dai lokacin kuma motocin su Jalal keta gilmawa suna bin bayan nasu Sheykh da azaban gudu har kamar zasubi ta kan motocin gaban nasu, cikin mamaki mutanen sukace
“Ikon Allah to wannan saurin duka na menene? shi kuma”.
Kai ya jinjina musu lokacin da yake rurrufe kayayyakin shi dan shima shirin tafiya masallacin yakeyi cikin yin ƙasa da murya yace.
“Kuyi a hankali kada ya jimu domin takadirinin yarone, saurin da yakeyi kuma, yasan muddin Sheykh bai gansu a masallaci ba ranshi zai ɓaci”.
Cikin nisawa mai Napep ɗin yace.
“Kai masu saida kaya a titi iyayen gulma, dasa ido to kai ina kasan su haka?”.
Da
Murmushi mai lemun ya ɗanyi tare da cewa.
“Wallahi sam ba gulma bace, akwai ƙaninshi Jamil abokin tagwaicin Jalal ɗin mutumi nane yakan tsaya a nan in zai shiga gari, kuma yanada ɗan karen surutu da fara’a shiyasa na sansu, akwai randa yana tsaye a nan yaga Jalal ɗin ya wuce a guje shine yayi dariya yace.
“Hege mai komaɗeɗɗiyar fuska bosawa Sheykh ne ke nemanshi shine yake gudu kamar zai tashi sama”.
to nan ya ɗan bani labarinshi. Kuma Sheykh ɗin da kanshi akwai shekarar da yayi azumi a garin nan yakan sayi kaya wurina, wani lokacin
Shiru sukayi tare da zubawa motocin idanu.
ganin sunata gilmawa, saida suka wuce gaba ɗayansu.
Sannan sauran al’ummar gari suka fara biyo bayansu.
Mafi akasari ababen hawan dama mutanen dake tafiya a ƙafa kab masallacin Masarautar Joɗa ba fadan jihar suka nufa wanda tuni Sheykh ya isa har yanata gabatar da Hudubar jummar sa mai taken, mu tsaida salla a lokacin ta.
A can cikin masallacin Masarautar Joɗa kuwa tuni al’ummar Annabi sun cika sunyi maƙil tako wacce kusurwa jama’a ne saffan-saffan suke shigowa,
yayinda cikin masallaci yayi maƙil har harabar masallacin ma ya cika tab da muminai salihan bayin Allah.
Kusan a guje wasu ke shigowa sabida lokaci na gab da ƙure musu domin bisa dukkan alamu an kusa ƙare Huɗubar.
Duk da tarin mutane manya da yara, amman sabida ladabi irin na addinin musulunci addinin mafi karamci da tsari, shiyasa baka jin motsi ko sautin kowa.
Sai wata iriyar zazzaƙar murya mai tsanani daɗin ji da sauraro da iya sarrafa harshe, cikin nitsuwa da iya laffazi muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ke tashi yayinda yake ratsa zuciya da jiki da Kunnuwan dukkan muminin dake sashin da sautin muryarsa ke kaiwa.
A can cikin masallacin yake a fili na musamman wurin da aka ware domin Limami,
Yana tsayene bisa sawunshi ya fuskanci tarin bani Adam dake cike maƙil a wurin.
Kekyawan matashine mai tarin kwarjinin da haiba mai firgita magautanshi,
Sanye yake cikin shiga ta al’farma shigar dake nuna nasabarsa ta wanne sashi,
Wani datsetstsen yadin Getzner ne fari ƙal-ƙal wanda yasa riga da wondo,
Kana sai wata hamshaƙiyar al’kebba dake nuni da nasabarsa mai tarin ilimin addini da kuma alaƙantuwa da jinin sarauta,
Wani irin rawani ne ke murze a kanshi wanda jelanshi ke kwance a gadon bayanshi.
Farar fuskarsa dake zagaye da tattausan saje baƙi ƙirin mai fitinenne sheƙi da ɗaukar ido,
Ne yayi matuƙar kara mishi ƙwarjini sai tsabtataccen gemunshi da bazai gaza kamu ɗaya ba.
Cikin rahama da nimar da ubangiji yayiwa laraba ta baiwar iya sarrafa harshe da tausasan laffuza, yake gabatar da Hudubar jummar da yakeyi.
Wanda yana bayayi ne da jan hankali kan girma da darajar salla da tsaida ita a kan lokacin ta.
Shiru mutane nen ya ƙara tsananta ne a lokacin daya fara tsorotarwa a kan illloli da masifun dake bibiyar mai wasa da salla.
Shiru masallacin da farfajiyar sukayi baki ɗayanshi sai sautin A/C da kuma sauƙar numfarfashi mutane da shessheƙan kukan da wasu salihan bayin Allah sukeyi sabida yadda wa’azin ke ratsa jiki da zuciyar mai imani.
A hankali yasa hannunshin ya gyara zaman al’kebbar jikinshi tare da gyara abin sautin maganar dake saƙale a wuyan al’kyabbar jikinshi.
A hankali ya lumshe idanunshi kana yayi ƙasa da kanshi cikin yanayin nitsuwarsa ya buɗe jajayen laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yaci gaba da cewa.
“Ya ƴan uwana musulmai muji tsoron Allah mu tsaida salla, domin itace forkon, abin bincika a cikin aiyukanmu.
Kada muyi wasa da salla a cikin dukkan halin da muke ciki.
Domin hukuncin mai wasa da salla hukuncine mai girgiza zuciyar dukkan mai mutuwa”.
Kanshi ya ƙara rusunarwa sabida tarin manyan mutane daddatawa dake gabanshi waɗanda da yawa sunyi jika dashi wasu kuwa sun haifeshi, cikin tausasa lafazi yaci gaba da cewa.
“Hukumcin mai wasa da salla lokuta biyar ɗin nan.
Duk mai wasa da salla, za’a ɗebe al’barka a rayuwarsa.
Ƴa yan uwana mene amfanin rayuwar da babu al’barkan Allah a cikinta, babu.
Kana duk mai wasa da salla za’a ɗauke kamala ta mutanen kirki a fuskarsa, ya zamana baka da kamala da daraja a idanun al’ummar duniya.
Sannan muddin baka tsaida sallaba dukkan wani aikin da zaka aikata Allah bazai baka ladaba.
Kana dukkan addu’o’in da zakayi baza’a ɗaukakasu zuwa samaba.
Kana bazaka kasance daga cikin addu’o’ina salihan bayiba matuƙar kana wasa da salla”.
Sassauta muryarsa yayi cikin yanayinshi na tarin kamala ya ɗan nago kanshi wanda dai-dai lokacin kuma ya hango ƙaninsa Jalal yana shigowa cikin harabar masallacin.
Kanshi ya kauda kana yaci gaba da cewa.
“Akwai uƙuba uku lokacin mutuwar dukkan mai wasa da salla.
Na ɗaya duk mai wasa da sallah zai mutu a matsayin matsiyaci gafalelle.
Na biyu
Zai mutu yana jin yunwa.
Kana na uku
Dukkan mai wasa da salla zai mutu yana tsananin jin ƙishi.
Ƙishinda koda za’a bashi ruwan ƙoraman duniyar nan baki ɗaya bazai gusar masa da wannan ƙishinba.
Kana duk mai wasa da salla akwai uƙuba uku dake jiransa a ƙabarinsa.
Za’a ƙuntata masa ƙabarinsa ya tsuƙe ya matse har sai ta kai matsayin da haƙarƙarinsa na dama ya haɗe dana hagu.
sannan kuma. Za’a saka masa garwashin wuta a cikin ƙabarinsa yayi ta juyawa a cikinsa ba dare ba rana.
Na uku. Za’a saka masa wata macijiya mai suna Shuja ul Qara,u wacce ta kasance ne ɗaya daga cikin macizan wuta.
Ida nunta na wutane. Farshenta kuma na baƙin ƙarfene.
Tsawon ko wani farcenta ɗaya tsawon tafiyar wuni ɗaya ne.
Zatayiwa mamaci magana, da muryarta mai tsawa da amo mai firgitarwa, zatacewa mamaci mai wasa da salla yayin rayuwarsa cewa.
(Ubangijina ya umarceni inyi ta saranka tun lokacin sallan asuba har zuwa azahar, daga azahar har suwa la’asar daga la’asar har zuwa magriba daga mangriba har zuwa isha’i daga sallan isha’i har zuwa wayen gari asuba.
Duk sara ɗaya da zaiyima mai wasa da salla har ya mutu bai canzaba zai nitse cikin ƙasa anayi mishi azaba, bazai gusheba anai mishi azaba har tashin al’ƙiyama.
Allah ya tsaremu.
Uƙuba uku lokacin fitowarsa daga ƙabarinsa itace.
Na ɗaya hisabi mai tsanani.
Na biyu. Fushin Ubangiji.
Na uku. Shiga wuta. Allah ya tsaremu ya bamu ikon kiyaye salla da tsaidashi a kan lokacinsa, yaku taron matasa kune shagala tafi auranku, mu dage mu tsare salla duk rintsi”.
Ya ƙarishe maganar cikin rauni da kushu’i.
Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi la’asar musamman matasa masu wasa da salla,
Jin ya juya yayi gyaran murya ne.
Yasa gaba ɗaya kowa ya mike ya fuskanci gabas masamar lada.
Cikin nitsuwa da tattausan harshe yake rare karatun al’ƙur’ani mai girma.
Lokacin da yake limancin sallan jumma’ar da a ƙalla yana samu halartan mutun sama da Dubu biyu.
Bayan anyi salla raka’a biyu kamar yadda yazo a nafsi, akayi addu’a aka shafa kana, mutane suka fara firfita daki-daki.
Bayan 30 minute shal cikin masallacin.
Dan gaba ɗaya kowa ya nufi wurin lamuran yau da kullum ɗinshi sai mutanen da ba’a rasaba wanda su sai dare zasu bar cikin masallacin.
Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, ne tafe a hankali cikin irin takunsu na sarakai,
Yayinda Jikinsa mafi soyuwa a garesa ke gefen damanshi,
fadawane ke biye dasu a baya, sun zagayesu,
Sai kuma bayansu can kuma Ayarin fadawan Jalal da Jamil ne wanda suke tagwaye ƙannen Sheykh Jabeer.
shi kuwa Malam Jabeer taku yakeyi a hankali cikin rashin nuna ɗagawa a kan doron ƙasa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar yayinda mutane kuwa ke kallon hakan a matsayin ƙasaitace da jinin sarauta dake yawo a sasan jikinshi.
Suna tafene a tare yayinda bakin Sheykh Jabeer ke motsawa a hankali hankali, wanda sai ka lura kake gane, tasbihi yakeyi a zuciyarshi wanda hakan ya zame mishi abin ci da sha a rayuwarshi.
“Astagafirullaha wa’atubu ilaik, Astagafirullaha! Astagafirullaha!! Subahanallahi! Walhamdilillah wa lailaha’illalahu Allaahu akbar. Astagafirullaha”.
Waɗannan sune kalamen da basa rabuwa da bakinsa, dama wasu masu tarin yawa.
Ta ƙofar dake shiga masarautar daga jikin masallacin sukabi.
Masarautar Joɗa babbar masarautace mai tarin girma tarihi.
Ginin Masarautar ginine mai masifar kyau da ɗaukan hankali.
Kana shiga daga asalin babban gate ɗin fadar, zaka samu wata shimfiɗeɗɗiyar hanya mai girma irin mai guda biyun nan, gefe da gefen hanyar duk wasu irin dogin fulawowi na mijin kwanda ne masu tsawo da kyan gani,
sai kuma tsakanin titunan, shima jerin dogayen bishiyoyin ne.
Tafiya mai ɗan tsawo, zakayi kafin, ka isa wani babban Round about mai masifar kyau, wanda cikinsa ke ɗauke da babban kwarya a ƙasa, sai kuma ƙananan kware, guda uku, sai kuma ginin mutum-mutumi na kekyawar saniya fara mai ɗigo-ɗigon baƙi, wanda mace ke tsugune a gefe kamar tana tatsan nono sai kuma ɗan saurayi matashi na riƙe da sanda ya coge da ƙafa ɗaya.
Sai kuma korayen ciyawi masu masifar kyau da sanyi wanda akayi alamun manomi na ciki.
Daga nan ne hanyoyin cikin masarautar suka rabu huɗu, ɗaya yayi gefen dama ɗaya yayi gefen hagu ɗaya yayi gabas ɗaya yayi yamma wanda ta nanne ake shigowa.
In ka miƙe ta yamma daret itace titin da zai sadaka da asalin sashin Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda nan sashin matanshi da hadimanshi yake da sashinshi dama faɗar duk nan take.
In kayi gefen dama kuwa wasu irin tsala-tsalan gine gine-gine masu tsananin kyau da ɗaukar hankalin wanda suna nan part-part ne masu girma da tsaruwa, an ƙawata tsakiyarsu da wani sassanyan Garden mai girman gaske.
Inda part ɗin sun kai goma, mafi kusa da sashin mai martaba sarkin Nuruddeen Aliyu Bubayero, shine sashin GARKUWAN FULANI, wato Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Sai kuma na gefen daman Sheykh Jabeer shi kuma na Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero ne, da matarsa Juwairiyya.
Sai na gefen hagunshi kuma na Jalal, ne na kusa da Jalal da kuma na Jamil ne sai dai Jamil yafi zama a sashin Jalal duk da korarshi da yakeyi wasu lokutan kuma lokacin kuma yana sashin Sheykh.
Sai sashin baya kuma sashin Affan.
Daga gefen hagun Masarautar kuwa wasu tamfatsa-tamfatsan plat ne masu girma har guda huɗu, sai kuma wani babban bene dake tsakiyarsu mai tarin girma wanda nanne sashin babban ɗan sarki Habibullah da matanshi.
Sai ta gefenshi can kuma wasu manyan part- part ne kimanin guda biyar wanda duk ƙanne shi ne da iyalansu da ƙananan yaransu a ciki.
Yayinda duk manyan yaransu kuwa kowa nada part ɗin shi a gefen da part ɗin Sheykh yake a ƙalla dai Part ɗin cikin masarautar Joɗa sun kai hamsin da biyar.
Can wurin mashigar kuma wasu ƴan saffan-saffan part-part ne wanda bisa dukkan alamu duka na bayine da hadimai da matansu.
Tsayuwa fasalta cikin ko wanne sashi na masarautar bazai yiwuba, sai a hankali.
Sai dai ko wanne part yanada Garden mai ɗan girma, wannane yasa gaba ɗaya masarautar ke zagaye da korayen fulawowi da bishiyoyi masu kyau.
Fentin masarautar gaba ɗaya iri ɗaya ne, Sky blue and white, mai ɗan karen kyau, a mahaɗar sashukan kuwa wani irin tamfatsetsen sweeminpool mai girma wanda ruwansa ke sky blue.
Can bayan sashin Mai martaba da Sheykh kuwa wani ƙaton filine mai cike da dawakai, da sashin mai rainonsu, gefe ɗaya kuma raƙuma da shanaye ne da makiyaya su, kana ga tumaki, a gefen Sheykh Jabeer ne kuwa akayi wani ɗan madai-daicin gidan zu ta bayan ɗakunan shi wanda yake da tarin tsuntsaye kamarsu, Ɗawisu, jimina, mikiya, agwagin ruwa, tolo-tolo, tattabaru, kana sai Aku. Da sauran tsuntsaye carki, kurciya, hasbiya, caccagi da-dai sauransu, shiyasa sashinsa ya kasance namusamman, don Garden Park ɗin ciki yafi na sauran part ɗin duka girma da kyau, sabida shine asalin Garden ɗin tarihin masarautar Joɗa.
Daga nan mashigar masarautar kuwa akwai wani babban filin sukuwa mai girma.
Daga masallacin Masarautar kuwa akwai miƙeƙƙiyar hanya har cikin masarautar wanda za’a iso gab da fada sannan kowa zai samu hanyar sashinsa.
A tsakiyar cikin masarautar ma kuwa akwai wani masallaci mai girma.
Wannan kenan sai a hankali zaku san mutanen masarautar da sunayensu halayensu dama nasabarsa da danƙantarsu da manufarsu.
A hankali Sarki Nuruddeen da Sheykh Jabeer suke takawa.
Suna shiga cikin gidan waɗannan fadawan suka tsaya a bakin Gate ɗin.
Kana wanda suka samu a wurin suka miƙe da azama wani dogon carpet mai azabar kyau da taushi, ɗaya daga cikin fadawan ya zo ya ajiye gabansu kana ya rinƙa yin baya-baya yana worwore musu carpet ɗin.
A hankali Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa yasa hannunshi ya kamo hannun kekyawan matashin jikan nashi da kab cikin jikokinshi ya fita da ban, hannunshi yake murzawa cikin nasa hannun a hankali a hankali.
kana suna tafiya a hankali, cikin takun sarauta,
Gefen mai martaba Nuruddee bayine da dogarai a ƙallah sun kai Ashirin da biyar, gefen Sheyk Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kuwa,
Ƴan saffan-saffan fadawane da basu kaishi shekaruba, a ƙalla sun kai goma.
Wanda wannan tsarinsa ne yace bazai iya ganin sa’an mahaifinshi ba ko sa’an Ya Jafar ɗinshi ba suna mishi bauta Babban Yayansu Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero suke kira Yah Jafar.
Kanshi ya ɗan murza ya juya a hankali da gefen ido ya kalli Kakan nashi dake magana cikin yin ƙasa da murya dan ko sarkin dogaren dake gefenshi baiji me yake cewa ba.
“Sheykh yaushe ne tafiyar taku?”.
Siraran kyawan Idonshi ya lumshi a hankali ya kuma buɗesu tare da rausayar da kanshi.
Maimartaba bai damu da jiran amsar tasaba yaci gaba da cewa.
“Munyi Magana da Aminina Sarki Jalaluddin yace min Kakarka UmmuKulsum tace tafiyar taku ta ƙara toko?”.
Shiru ya ɗanyi har saida sukayi taku uku zuwa biyar kana ya gyaɗa mishi kanshi kai a hankali irin gyaɗa kai na kamala”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso dab ƙofar mashigar sashin Maimartaba, wanda dama duk ran jumma’a daga shabiyu yake tashi zaman fada,
sanin hutawa yake a irin wannan lokacin ne ya sashi ɗan sake hannun Sheykh Jabeer tare da cewa.
“Sirranta komai a rai yanada wuya, amman kai baya maka wuya, ya zama kamar jininki, akwai tauraro na musamman a goshinka, wanda nake fatan watan wata rana ya haska zuƙatan ahlinka dama talakawan da zaka mulka”.
Jin kakan nashi ya sake hannunshi da kalaman da yake jero mishine yasa ya ɗan kalleshi a hankali ya kuma sunkuyar da kanshi.
Sai ya kuma ɗan kalli Sarkin tare dayin mgna.
“Mulki yana da nauyi mai girmi Ni kuwa baya cikin tsarin jadawalin ababen buƙata ko sha’awa a rayuwata,”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Ba sai lallai abinda mutun keso ke samu ba, bakuma dole ka rasa abinda baka soba”.
Ganin kakan nashi yaci gaba da tafiya ne yasa shima ya yaci gaba da tafiya.
Inda fadawanshi ke biye dashi a baya.
Yayinda fadawan Maimartaba kuwa suka tsaya a bakin sashin sa.
Sunyi tafiya mai nisa kaɗan kafin suka ratso ta gaban sashinsu mai azabar girma da kyau sashine mai ɗauke da part-part masu tarin yawa da girma wanda tsakanin ko wannensu da ƴar tazara sosaima.
A hankali ya ɗago hannunshi daga cikin babbar rigarsa da zazzafar al’kebbarsa ta rufe,
ɗan ɗaga musu hannunshi yayi alamun su tsaya daga nan.
Cikin abinda bai gaza 18 second ba duk suka rusuna ba tare da sun ƙara koda taku ɗaɗɗaya ba, kusan a tare suke cewa.
“Takarwarka lafiya ɗan Baban yaya Habibullah jikin Sarki Nuruddeen, jika ga sarki musulmai Jalaluddin”.
A hankali ya kuma ɗaga musu hannunshi alamun ya isa haka, dan shi dai Allah ya sani har ranshi baya jin daɗi da son wannan kirare-kiraren dan yayi imani da Allah zasu iya sawa ɗan adam ɗagawa da jin kanshi shi wani abune, zasu iya sa mutun yaji kansa a matsayin wani sarki mai iko bayan kuma babu wani Sarki sai Allah.
Yana tsoron ɗagawa ta samu mazauni a zuciyarshi, sam baya son wannan kirare-kiraren na zamanin jahiliyya ina dalili kana mutum ɗan Adam mai daraja azo ana wani ce maka toron giwa ko tozon raƙumi ko dokin ƙarfe yaya Allah ya karramaka yayika ɗan Adam ka bari na ƙasa da kai suna suffantaka da dabbobi.
A hankali yace.
“Ya isa, duk kuje kowa yayi uzurin gabansa in inada buƙatar ku zan nemeku”.
Shiru sukayi tare da baje manyan rigunansu suka zauna a inda ya dakatar da suɗin.
Kana sukace.
“An gama”.
Shi kuwa a hankali yake taku cikin shigarsa da tafi kama data limamen harami.
A hankali yake taku, har ya iso bakin ƙofar shiga side ɗinsa inda a nan dogari mai tsare mashigar sashinsa sarkin ƙofarsa ke tsaye.
Tuni Sarkin ƙofa ya miƙe yasa hannu zai buɗe mishi ƙofar kenan sai ya kuma ɗan rusunar da kanshi,
Ganin Jamil ya rigashi kai hannunshi ya buɗe ƙofar cikin salonsa na raha ya nunawa Hamman nashi ƙofar tare da cewa.
“Sheykh Dr Malam Hamma Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa GARKUWA barka da yamma”.
Kanshi ya kauda daga kallon ƙanni nashi, sannan ya kutsa kai ciki,
da sauri shima Jamil ya mara mishi baya,
Cikin wani haɗeɗɗen corridor mai fitinenne ƙamshi da azabebben sanyi suke tafiya a hankali.
Tafiya kaɗan sukayi sai gasu cikin wani tamfatsen falo na al’farma da more rayuwa,
ɗaya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun kilisai na manyan sarakunan dake falon ya zauna a hankali.
Ido ya ɗago ya watsa ƙanin nashi su, cikin sauri Jamil yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
“Na tuba Hamma kayi magana ina tsoron hukunci da idanunka gwara kamin duka kon ka haɗani da wannan saggamemen na bakin ƙofar kan nan ya dakani kawai in huta”.
Kanshi ya kawar Cikin harshen larabci yace.
“Ban gankaba a masallaci”.
Da sauri ya durƙuso gaban Hamman nashi cikin yin wuƙi-wuƙi da idanu cikin sanyi yace.
“Ana Aspet ya Akhi, a matsallacin ƙofar gidansu, Khadija nai sallan jumma’ar”.
Kanshi ya gyaɗa kana ya kauda kanshi ya fuskanci wani katon majigi dake liƙe a jikin ginin yana fuskarta kujerar da yake zaune a kai.
Majigine dake ɗauke da full Qura’an, a hankali yake karatun cikin sassanyan murya.
Ganin hakane yasa Jamil ɗan rusuna duk da yasan ba amsa zai samuba cikin sanyi yace.
“Hajia Mama tana son ganinka”.
Kanshi kawai ya gyaɗa yaci gaba da karatun shi.
Ganin hakan yasa Jamil ya juya ya fita. Shikuwa Sheykh yaci gaba da karatunshi, kusan awa ɗaya kana ya shiga Bedroom.
Shine bai fitoba sai lokacin da sallan la’asar ta gabato, jin an kira sallane, yasa ya shiga ya sabunta al’wala kana ya fito ba kowa a wurin sun watse kemar yadda ya umsrcesu.
Sai can bakin mafita ya samu mutun huɗu, yana tafe fadawanshi na biye dashi wanda suma sunyi al’walan.
Jamil kuwa daga sashin Hajia Mama ya fito da nufin zaije side ɗinsu yayi al’wala.
A harabar gidan yayi kiciɓis da abokin tagwaicinsa wato Jalal, cikin sanyi ya kalli yadda Jalal ke zagaye da fadawa yana tafiya da yanayinsa da muddin zaka yanke mishi hukunci da ganin zahiri zakace cikekken ɗan iskane, sai dai a baɗinin ba haka abin yakeba.
Kekyawa ne shima dan shi yana ɗibin kamanni da Hamma Jabeer ɗin nasu sosai saɓanin Jamil da yafi kama da Babban yayansu, Barrister Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Tafiya yake cikin shigar tsamari zamani, wondon a saɓule har kana iya hango boxes ɗinshi, kana ga wani irin kafirin aski da yayi mai ɗaukar hankali.
sam a rayuwarsa shi baya ta’ammali da manyan kaya,
Baya tsoro ko shayin ko shakkar kowa a duniya sai Hammansun kaɗai.
tafe yake bayinshi na biye dashi a baya, da wasu kolabe a hannunsu, cikin tsare fuska Jamil yace.
“Kai ku tsaya, kolaben menene wannan a hannunku?”.
Juyowa yayi a zafafe cikin halin faɗa yace.
“Kwalaben Giyane ko kanada maganne Akukkuturu?.”
Da azaban ƙarfi da tsoro Jamil ya zazzaro ido cikin ɗaga murya yace.
“Kwala ben giya a gidannan Jalal kasan abinda kake cewa kuwa? Kwalaben giya a Masarautar Joɗa”.
Ya juyo da masifa kenan yayi arba da Hamman nasu,
shiru yayi tare da yin ƙasa da kanshi, jiki a mace.
Shi kuwa Sheykh Jabeer idanu ya zuba mishi na wasu yan daƙiƙu kana ya juya ya nufi hanyar da zata sadashi da ƙofar tafiya masallacin Masarautar tasu ba tare fitar nan bisa dressing mirror suka ajiyesu kana suka juya suka fita.
Shi kuwa al’wala yayi ya nufi masallacin.
Ƙarfe tara dai-dai na dare. Sheykh Jabeer, ne zaune a bisa wani tattausan carpet mai azabar taushi,
Wata Hamshaƙiyar Gimbiyace mai cikan iko da muƙami, mulki, iko, cikin wani irin kallo mai cike da kulawa tasa hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin nonon inabi dake cikin wani kekyawan tray dake gabanta miƙa mishi tayi tare da cewa
“Jabeer Yaushene tafiyar taku?.”
Tankwashe kanshi yayi bisa kafaɗunshi kana a hankali ya ɗan kalleta tare da motsa laɓɓanshi a hankali yace.
“jibi”.
ya faɗi mgnar a gajarce, gyara kishingiɗarta tayi bisa kilisan tum-tum dake gefenta,
Cikin kulawa tace.
“Da Umaymah zakuje ne?”.
Kanshi ya jujjuya mata alamun a a.
Kanta ta rausayar cikin ƙasaita tace.
“Naga kamar bacci kakeji Saida safe”.
Kanshi ya gyaɗa kana cikin girmamawa yace.
“Allah ya bamu al’khairi”.
Amin tace, shi kuwa daga nan ya fita ya tafi.
Koda ya koma sashinsa. A falo bakin ƙofar ya samu Jakadiya, tana ganinshi ta ɗan rusuna duk da tasan yana hanata hakan a hankali tace.
“Akarmakallahu, Umaymah ce take biɗar mgna da kai, ta kirayi layinka ba’a ɗagawa, shine tace in kawo maka wayar”.
Kanshi ya ɗan sunkiyar a hankali yace.
“Ummi kice mata tayi hakuri saida safe”.
Cikin mamaki jakadiya tace.
“Lafiya dai ko Sheykh?”.
Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh lfy.
“To ba laifi zan gaya mata”.
Daga nan ta juya ta koma sashinta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, daga bakin ƙofa ya dakatar da bayinshi.
Kana cikin nitsuwa ya kallesu tare da cewa.
“Sarkin ƙofar ka janye bayin dake bina da bin Jalal da Jamil, kaima ka koma can sashunku, ba’a buƙatar bibikon nan, in inada buƙatar ku Ummi zata sanar muku.”
Ciki girmamawa sukace.
“To Sheykh”. daga nan ya juya ya nufi ciki.
Su kuma suka juya.
Koda ya shiga ɗakinshi kai tsaye bathroom ya wuce wonka yayi tare da al’wala a cikin bathroom nashi da yafi makoncin wani kyau.
Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower’n glass wanda yake cike da ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets boxes and pants kana towels da rigunan wonka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma 3 qtr da kuma turaruka dasu brosh da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske pravet part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai.
Bayan ya fitone, yayi shirin baccinsa cikin wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da tsada,
A bakin gadonshi na sarakuna ya zauna,
idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower’ Woyoyin sun kai biyar,
a hankali yasa hannunshin ya ɗauki ɗaya daga cikinsu data kawo haske, alamun ana kiranshi,
Karawa yayi a kunnenshi tare da yin shiru.
A can ɗaya sashin kuma kekyawar tsohuwar balarabiyace keta mishi faɗan ina ya shiga tana kiranshi bai amsawa.
A hankali ya lumshe idanunshi tare da mirginawa ya konta tattausan gadonsa da shimfiɗar sa, wanda Jamil ke gyara mishi a koda yaushe, cikin harshen larabci yace.
“Sitti raja’an!”.
shiru sukayi baki ɗayansu, can kuma sai yaci gaba da magana cikin larabcin,
sawon 32 second yana maga kafin ya katse kiran,
kana yayi laduban konciya bacci ya konta.
Washe gari da safe da misalin karfe sha ɗaya na rana.
Dawawonshi kenan daga fada,
Yana shiga falonshi asalin falon dake gab da makoncinsa kiran Umaymah na shiga wayarsa.
Ganin video call ne ya sashi, amsa kiran kana ya ajiye wayar kan Glass Stull dake gaban kujerar da yake zaune.
Fuskar wata kekyawar Matace ya bayyana a fuskar wayar tashi, cikin sanyi ta zuba mishi idanu ganin yadda ya tonƙoshe wuyanshi bisa kafaɗunshi a hankali tace.
“Jazlaan”. Kanshi ya ɗan mirgina cikin wani yanayi ya jujjuya mata kai a hankali yace.
“Jazlaan, Umaymah sai yaushe zan zama Jazlaan? Sai yaushe, Jazlaan zai wadaci rayuwarmu?”.
Murmushi mai ciwo a zuciya tayi tare da cewa.
“In sha Allah nan kusa”.
A hankali ya lumshe idanunshi cikin sanyi yace.
“Umaymah, kizo kafin mu tafi, ina so mu haɗu”.
Cikin tarin kulawa da tsananin ƙauna tace.
“Menene matsalarka?”.
A hankali yace.
“Ya Jafar…!
Add Comment