Rariya Hausa Labaran Duniya
Rariya Hausa Labaran Duniya
Wannan shafi yana kawo muku sabbin labaran rariya hausa ku kasance da mu koda yaushe.
Bbc Hausa Labaran Duniya da Dumi Dumin su
NAZARI: Jinkirin Shigar Rarara Tafiyar Gawuna/Garo Ne Ya Kayar Da APC A Jihar Kano
Daga Haruna Sardauna
Tun ranar 6 ga watan Maris na watan da za a yi zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, jiki na ya ba ni za mu iya faduwa a zaben gwamnan jihar Kano, har ma na yi tsokaci akan dalilai da zai sa mu fadi amma wasu ba su fahimci hakan ba, saboda Rarara Mawaki ne, al’umma sun raina baiwar fikira da Allah ya ba shi na sandar kiwon juya hankalin al’umma kan hanyar da yake so musamman ma ta fuskar siyasa.
Duk da cewa Rarawa Mawakin ne, ban taba raina baiwar da Allah ya ba shi ba, duk da cewa yawanci masu cin albarkacin Baiwar Rarara, sun raina baiwar da Allah ya masa, basa karamta shi yarda ya dace, kuma nayi imani da Allah duk yan APC jihar Kano daga Ganduje ban ware kowa ba a Kano daga 2019 zuwa 2023 albarkacin Baiwar Rarara yake ci, domin kuwa shine kaso 70% na kashin bayan nasarar jam’iyyar APC a zaben jihar Kano na shakarar 2019.
Inda jam’iyyar APC a Kano ta baiwa Rarara daman daya dace tin farko, bana kokonto akan APC zata kara kafa gwamnati a Kano, a siyasar Kano Farfagandace akan gaba, kuma yan Kwankwasiyya suna da karfin farfaganda, a siyasance Rarara ne kawai tauraron shi yake danne na yan kwankwasiyya saboda shi Mawakin ne Sananne kuma yasan lagon Siyasar janyo Mawaka da yan socia media a jiki domin tallata hajar yadda za’a kiwaci hankalin al’ummah.
Ni Haruna Sardauna marubuci ne, a bangaren Media ina daga cikin marubutan arewacin Nijeriya da suka jagoranci ceto kujerar Ganduje a maimaicin Za6en Kano na 2019, na karanci Siyasar Kano ta fuskoki da dama, Marubuta sun bada gudummawa sosai amma gwamnati bata musu sakayya ba, haka shi kanshi Rarara gwamatin jihar Kano tayi Masa riqon sakanyar Kashi.
Rarara yana da wasu Qualities a Siyasa wanda asalin yan Siyasar ma, basu da shi wannan qualities na Siyasar da Rarara yake da ita, kasancewar shi Mawaki sai ake kuskuren daukar shi a matsayin mawaki kadai, inaso ku lura ko kyautar Mota daya Rarara zai bada sai Labarin ya ratsa arewacin Najeriya fiye da wanda ya bada kyautar Mota 100, inde zaiyi kyauta sai ya duba mutum sananne mai tauraro, sai ya bashi Mota, daga karshe shida yayi kyautar, shine da riba kuma haka kyautar Siyasa take Bukata.
Inda Rarara ya samu dama tin farko a zaben 2023 da APC jihar Kano ta yi nasarar da ba a yi zato ba, saboda inda Rarara yana tafiyar da yawancin Yan TikTok ba su bar jam’iyyar APC ba saboda ko challenges na wakokin shi da yake sakawa zai rike su da kyautar motaoci da yake, tinda na hau Tiktok na auna Siyasar Kano a mizani na gano cewar jinkirin shigar Rarara tafiyar Gawuna/Garo zai yi kai APC ga rashin nasara a jihar Kano.
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Gwamna Masari Ya Baiwa Rarara Kyautar Katafaren Gida A Jihar Katsina
Daga Comr Nura Siniya
Gwamna Aminu Bello Masari, na jahar Katsina ya gwangwaje mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, da kyautar katafaren gida na miliyoyin Nairori a cikin birnin Katsina, Bayan Kona mashi gida da wasu matasa batagari Sukayi a jihar Kano.
“A wani bangare Kuma Rarara ya samu kyautar mota kusan guda 7 daga ƙone mashi zuwa yanzu wanda ciki har da “Land Cruiser wacce batajin alburushi.
Wane fata kuke yi mashi.
Ni Da Amaryarta Sakina, Yar Shekara 21 Da Haihuwa, Wadda Ita Da Kanta Ta Zaɓe Ni A Matsayin Miji Kuma Ina Son Abuna, Don Haka Masu Yada Jita-Jita Ku Ganewa Idonku, Cewar Aminu Ɗan Maliki
WAIWAYE: Yadda Kwankwaso Ya Rungumi Kaddara Bayan Ya Fadi A Zaben Gwamnan Kano A 2003, Inda Kuma Ya Yi Kira Ga Magoya Bayansa Da Kada Su Tada Rikici
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Bada Sanarwar Ganin Watan Ramadan A Najeriya.
Daga Comr Nura Siniya
Majalisar ƙoli mai kula da harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin mai Alfarma sarkin musulmi Sultan Abubakar Saad III ta bada Sanarwar tabbacin ganin watan Azumin Ramadan a Najeriya.
Jahohin da aka tabbatar da ganin jaririn watan na Ramadan a Najeriya sune:
•Katsina
•Kaduna
•Sokoto
•Jigawa
•Niger
•Yobe
•Kebbi
•Osun
•Adamawa
•Bauchi
•Rivers
•Taraba
•Kogi
A gobe Alhamis 23, ga watan March 2023, wanda shi ne zai kama 1, ga watan Ramadana na shekarar 1444, za a tashi da azumi a Najeriya.
Allah Yasa muna daga cikin waɗanda zasu zama ƴantattun bayi a wannan wata mai Alfarma..
DA DUMI-DUMINSA: Za A Soke Zabukan Wasu Kananan Hukumomi A Taraba, Bayan INEC Ta Tabbatar Da An Yi Aringizon Kuri’u Sama Da Dubu Dari A Zaben Jihar
Daga Comr Abba Sani Pantami
Bayan binciken da hukumar INEC take yi na tsawon sati guda game da zaben jihar Taraba, yanzu haka IREV PORTAL ya nuna cewa adadin mutanen da aka tantance su domin su gudanar da zabe a jihar Taraba ya nuna mutane 555,358 ne dai-dai, amma yawan kuri’un da aka kada wanda aka kawowa INEC ya nuna mutane 663,358. A takaice dai sunyi magudin kuri’u 108,640.
Dama mun fada muku Hukumar INEC ta jihar tace zasuje suyi bincike na tsawon sati guda akan Portal din BVAS domin tabbatar da sahihancin zaben da akayi a jihar.
Bayan kammala binciken matukar aka samu tabbacin Magudi kamar yadda aka samu a yanzu haka, to tabbas za’a kashe zabukan dukkannin kananan hukumomin da aka samu magudin a sake sabon zabe a iya kananan hukumomin.
Dama an sanar da cewa PDP ce ta lashe zabe a jihar da tazarar kuri’un da basu wuce dubu 55 ba, wanda hakan yake tabbatar mana da cewa tabbas dan takarar Gwamna na karkashin jam’iyyar NNPP Farfesa Muhammad Sani Yahaya ne ya lashe zaben.
Idan kuka duba hoton dake kasa, za kuga yadda jadawalin lissafin yake na kowace karamar hukuma a jihar.
Don Allah ‘yan uwa mu cigaba da Addu’a Insha’Allahu za’a tabbatar mana da Farfesa Muhammad Sani Yahaya a matsayin zababben Gwamnan jihar Taraba da yardar Ubangiji.
Add Comment