Littafan Hausa Novels

Waye Mijina Hausa Novel Complete

Waye Mijina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

WAYE MIJINA ???*

 

 

By Yasmeen Ahmad

 

 

Autar alheri

 

 

*ALHERI WRITERS ASSO*

 

 

A*W.A

 

 

 

 

 

 

 

*ALHERI SED’AN ALHERI, ALHERI GADON BACCI KUNGIYA D’AYA TAMKAR DUBU, KUNGIYA MASU AIKIDA ILIMIN ADDINI DA ZAMANI DANWAYAR DA KAN AL,UMMA*

 

 

 

*Gargad’i*

 

 

Wannan novel na matan aurene kawai anyishine domin fahimtardasu zaman takewar aure da matsalar da mace ke fuskanta da Kuma yanda zatayi maganin ta insha Allah

 

*KARKIBARI YARA SUKARANTA*

 

Dayawa ana kirana ko,aturomin sak’o danneman shawara to kitsaya kikaranta wannan novel zewarware Miki komai insha Allah.

 

 

 

Free page

 

 

Page 1 & 2

 

 

Jos

 

___wani katafaren State nahango Wanda fad’in girmansa B’ata lokacine. State d’in malakar wasu bayin Allah ne su biyu *gali da Sami* Kuma Y’an uwane na jini uwarsu d’aya ubansu d’aya Amma yanzu basa raye se iyalansu kawai. Gali yamutu yabar matan aure ukku y’ay’a 9. Salmu, itace uwar gida se ego itace tabiyu se Kuma laure. Salmu y’arta d’aya mace wato bintu salmu mace,ce matsana,nin hak’uri da kauda Kai ga duk wani abunda akayimata ko y’arta.. sab’anin ego datakasance masi faffiyar mace da mita.yaranta biyar ak’ilu,sule,Hamza,saude,sahiya..

Yar aikina Hausa Novel Complete

Laure itace k’arama itako halin ko inkula ne da ita ammafa Muna fukace tabugawa ajarida.y’ay’anta ukku Amina,sadiya,bala

 

Sami kuwa yabar Mata biyu y’ay’a 6. kulu itace uwar gida Kuma itama Kamar salmo take mace,ce mehakuri da kawaici da San mutane. y’ay’anta 4 jafaru,gambo,idi,se autarsu zenabu,

 

Hari itace tabiyu mace,ce dazakarasa gane Ina tadosa domin komai nata adukunce takeyinshi. Yaranta biyu suwaiba..uwani

 

Ayanzu dukkansu suna rayuwane acikin State din daga su har iyayensu bayan rasuwar mahai fansu maza wato gali da Sami…rayuwa sukeyi cikin duhun jahilcinnan namaguzawan farko abun sedai ace Allah ya kyauta.

 

 

Bintu kyakkyawar yayince wadda gabaki d’aya family su tafisu kyau.kasancewar mahaifiyarta salmu bafulatanar dajice. Acan gali ya,aurota.

 

Duka yaransu auren gida akamusu wato auren had’i..jafaru shiya auri bintu..Buhari ya,auri sahiya..gambo ya,auri saude..sule ya,auri zenabu..hamza ya auri suwaiba..buhari..ya,auri uwani..dukkaninsu anan suke zaune Kuma har sun Tara iyali.

 

Iyayensu kuwa yanzu tsufa yazo Amma duka yaransu Mata bawadda Bata d’auko halin mahai fiyartaba..bintu da jafaru yaransu ukku salmanu aliyu faruku..hakama duka sauran kowa nada nashi Yara.

 

Aduk cikin wannan family jafaru da buhari Sufi kowa tsanar rayuwar dasukeyi cikin duhun jahilci Amma basusan yazasuyiba.

 

Dukansu basajin komai aransu Dan wannan yarungumi matar wannan ko yarik’a hannuta ko sutab’a in,anafira Dade makamancin hakan sallah ba,adamu ayi cikin lokaciba.baruwansu da rabawa yaransu maza da Mata wurin kwanciya..yaya ze iya k’anciya da k’awarsa ko yarungumeta ko suyi bacci a makwanci daya Kuma dukansu baliggai duk Wannan badamuwarsu bace.

 

 

Jafaru yanada wani amini Wanda ba Dan garinba awurin kasuwancinsa suka had’u..yakoka Masa Yana so yaranshi suyi karatun islamiyya Dana zamani..shiyabashi shawarar yakaisu KD suyi karatu acan zehadasu da yaranshi surink’a Yi tare..yaji dad’in hakan sosai.nantake yahada yaranshi yaturasu KD

 

Sunfara karatu cikin sa,a domin duk abunda akekoyardasu baya gagararsu..yayinda mahaifinsu yasaki kud’i sosai.amininshi alh.Musa nakula Masa dasu..har Allah yatemakesu suka Gama lpy..sunfito da saka mako mekyau..abbansu yy murna sosai har farincikinshi baya,iya boyuwa..yayinda aketa zaginshi acikin State din anafadar yatura y’ay’a yawon duniya..Amma yasharesu domin shi bayada burin dayawuce yarabasu da irin dabi,un dangin nasu.aliyu duk yafi k’ok’ari aciki domin takardunsa sunfi kyau.dashi da D’an alh.musa atiku..shiyasa alh.musa yace suhada k’arfi suturasu saudiya karatu..hakako,akayi

 

Antura aliyu da atiku Jami,ar madina.kuma sunfara karatunsu cikin nasara..salmanu da faruku sukawuce A.B.U Zaria Suma suka Kama karatu gadan2.

 

 

Masha Allah rayuwa mesauyi lokaci zuwa lokaci Inda ayanzu watanni sunshud’e shekaru sunja..ahalin alh. jafar wato jafaru ada.sunkammala karatunsu cikin nasara harsunzama manyan mutane..aliyu yazama babban likita.kuma saudiya tadaukeshi aiki acan haryayi aurenshi dawata balarabiya.

 

Suma k’annen shi duka sunkammala karatunsu.inda furuk yafito soja Salman ko lauya. Kuma Suma sunyi sure anan cikin State din.dasu da sauran Yan uwansu..Kuma ayanzu alh.ali da k’anen shi faruk da Y’ay’an shi Salman suke kulada y’ay’a Yan uwansu sundage akan se y’ay’an su Dana Yan uwansu sunyi karatu. Bayanda iyayensu suka iya Dole sukabarsu..Amma fa hassada fal zukatansu.

 

Ayanzu Salman Wanda sukekira da abbah yanada Yara hud’u.jafar Wanda yaci sunan mahaifinsu,se jabir, Usman,se Jalila.domin shi alh.jafar yafara yiwa aure saka makon Yana fama da matsanan ciyar sha,awa wadda idan tataso Masa harsuma yakeyi.wannan dalinne yasa yake tab’a Al,adarsu Yana matsar k’annen su mata danyasami sauk’in abunda kedamunsa to da alh.jafar yafahimci hakan se ya aura Masa diyar Dan uwansa buhari wadda akekira adwiyya.

 

Daga baya yayiwa faruk Ida shi yanzu y’ay’an shi ukku ne harun,Kamal,se haidar Wanda yaci sunan yayan mahaifinshi wato alh.ali Wanda shima yanzu Yana can saudiya da iyalanshi.

 

*Wannan shine takai taccen tarihi wannan family mekaratu katsaya kanutsu afahimci tarihinsu hakan zesa kafahimci sakon da labarin kisan isarwa cikin sauk’a*

 

 

Saudiya

 

Hakeem,Hakeem,waibazaka fitobane kuyi breakfast d’in kutafi kabarsu se jiranka sukeyi ah,ah

 

Naji wata kyakkyawar dattijuwa balarabiya Dake tsaye bakin k’ofar bedroom din tana fad’a.ganin ba,ayimaganaba Kuma ba,abud’eba yasa tabude k’ofar tashiga..hango shitayi duk’unk’une acikin blanket serawar sanyi yakeyi.nashiga ukku mikedamunkane Hakeem?dama bakada lpy ne duk acikin larabci take maganar.

 

Tana yaye blanket d’in dayarufa dashi.hannu takai tadafa jikinshi taji zafi rau “innalillahi Hakeem miye yakedamunka kayi magana mana uhnm..Bude dara,daran Ida nuwansa yayi dasuke alumshe kamar nad’an maye yawatsa matasu..salati tasake,saki ganin yadda ida nuwansa sukayi jajir.sakamakun azabar ciwon dayakeji.

 

Tashi yy zaune dakyar Yana cizon leb’enshi nak’asa yad’ago fuskarsa.masha Allah nafurta araina sakamakon tozali da wannan kyakkyawan matashin balaraben.

 

Yaro matashi Wanda baze wuce shekaru 18 ba Amma haibarsa tazarta tad’an shekara 25.yanada manyan Ida nuwa masu shek’i da walwali suna Tara ruwa acikin kamar k’wallah.bakinsa kuwa Kamar bakin asusu zaka iya rantsewa spoon baze shigaba.sumar kansa da girar idanuwansa abun ba,acewa komai.sabida bak’in ta da shek’i.hancinsa kuwa dogo ne medan fad’i kadan Wanda yadace da kyakkyawar fuskarsa.befitadda saje ko gemo ba Amma duk wanigu daze fitarda Suma ajikinshi tafidda alama.abin gwanin Sha,awa.

 

“Mom bakomaifa naji sauk’i..ah,ah Kam Hakeem dubi yanda kk hada gumi kace bakomai tashi muje hospital gasu dadyn ku cannajiranka kufita se mufara zuwa hospital kajiko..no mom naji sauk’i fa karki damu bara nayiwanka muje shopping Moll din kawai.

 

Shikenan inbazakajeba bara nagayawa dadyn ku yadobaka idan kafito..tashi yy cikin k’arfin halin yashiga bathroom d’in.bataredayace komaiba..da ido tabishi tana karantar yanayinshi har yashige bathroom d’in.kana tamik’e tafita..shiko wankan yayi adaddafe yafito daure da towel ak’ugunsa.komai beshafaba yasaka Kaya marasa nauyi yafito.

 

A dining yasamesu su hud’u zaune mom dady da wani natashi Wanda baze wuce sa,ar Hakeem ba se baby girl Dake zaune saman ciyar dady.

 

K’arasowa yayi yazauna yanafar “good morning Mom & dady.had’a Baki sukayi wurin fad’in morning my son ya jikin naka? Dasauk’i dady..okk Yi breakfast se muje hospital adubakako..okk kawai yace Dan baya iya yiwa dady shi musu.

 

Sannu bro y jikin..juyawa nayi inda naji wannan maganar mekamada ta Hakeem kutttt nace Ina tasbihi ga ubangijin talikkai daya halicci way’an,nan bayi nasa masu matsanan ciyar kama.dumin bashida banbanci da Hakeem komai nasu iri daya hatta tabon da Hakeem yakedashi adamtsen hannu wannan saurayin nadashi.

 

“Naji sauk’i bro.okk Allah yabaka lpy.ameen yace atak’aice.

 

“Ya hafees miyake damun ya Hakeem ne? Cewar wannan yarinyar mekama dasu.murmushi Wanda takira da Hafees yayi kana yace”Nima bansaniba lil kitambeshi Mana inyagayamiki muma muji.

 

Harara Hakeem yadallahmasa kana yad’oki cup yahad’a coffee.yadauko danufin Kai bakinsa kenan….

 

 

 

 

Tofa kobiyoni domin jin yaza,ayi wannan mird’ad’d’iyar rayuwar a cikin wannan family.

 

 

 

 

 

 

Autar alheri.

*WAYE MIJINA

 

 

*ALHERI WRITERS ASSO*

 

A*W.A

 

 

 

 

 

 

Free page

 

Page 3 & 4

 

 

__danufin Kai bakinsa kenan sekuma yayi saurin ajiye cup d’in Yana had’agumi jikinshi kuwa ko Ina rawa yakeyi.dady da Hafees ne sukamik’e tare suna fadar subhanallah miyafarune? Ciwonne? Duk atare sukemasa tambayar..Amma ba,Baki yadunk’ule wuri d’aya se taunar leb’enshi nak’asa yakeyi.. sahibi kukaishi hospital kagafa Suma zeyi..kamashi sukayi aka kwantardashi perlon saman 3ster..alhj.ali nafadar no sahiba baranadubashi anan kamin muje hospital ze,iya suman..yana gamafad’ar hakan yashiga bashi temakon gaggawa.. dakyar ya samu lumfashi sa yadedeta kana yayi Masa allurar bacci.duk suna tsaye jugum2 suna kallansa mom kuwa se kuku takeyi itada haseenat.

 

Hafees kuwa Ida nuwansa suyi jajir sabida tausayin Dan,uwan,nasa.domin ko ciwon Kai d’ayansu yayi se d’ayan yayi Amma Banda wannan jarababben ciwon dashi besan komineneba.

 

“Miyake damunsane sahibi? Muryar mom takatse Musu tunani domin ko alhj.ali tunanin yakeyi ba Hafees kad’aiba.

 

Nisawa yayi kana yace Nima abun yad’au remin Kai sahiba.inaga yagad’o Yaya Salman ne domin shiyakeda wannan jarababbiyar sha,awar to Amma abunda keban tsoro anan shene shifa Hakeem ko 19 yers beyiba Amma itace kewaha lardashi.

 

Kuku sosai mom keyi tana jimamin wannan abun daya Sami gudan jinin nasu.

 

Magana tafarayi cikin kuka”yanzu meye mafita ?

 

“Mafita d’aya ce sahiba sedai badamar yinta ayanzu sedai kawai mudage dayimasa addu,a..too shikenan Allah yakawo Masa mafita.ameen ya Allah suka amsa Mata atare..tashi sukayi sukabar perlon yayinda akabar Hafees zaune Yana tunanin wannan abun.

 

 

Jos

 

Zaune take bisa abunzaman,Nan nadori namanyan Mata wato kilisa.takishin gida.yayinda y’ay’an ta jikokinta da tattab’akunne kezagaye da ita. *Mebabban d’aki kenan kulu* uwargida wa Sami. Ayanzu dahaka suke kiranta.. dattijuwar tsofuwa medattako kenan.

 

Tashi tayi zaune Dede danjin abunda babban dannata kefad’a wato alhj.jafar

 

“Bansan miyasa sukeyin hakanba Koda Ace wani gunne suke auren hakan zasuyi sub’ata Mana sunan zuria, Yan ace haka,kawai safiya zatasa isham yasaki matarsa gayaransu nakallan ta kokunyarsu batajiba wannan wane irin abune?

 

Imatama saudatu haka tayiwa gambo rashin mutunci,sabida yahana mansura kwanciya d’akin su mubeen

 

Kuma Wannan aiduk lefin iyayensu ne dasuka barsu nangidan. Kowanne datashi fitnar.

 

 

Kuna jiya buhuri yasameni akan zancen yarannan misbahu da jalija Y’ar wajen Salman

 

 

Amma uwane Tak’i bayadda goyon bayanta akai duk uban yaron yazo musu dazance setashareshi…

 

Gayan murya tayi kana tace”to yanzu wanne mataki zaku d’auka akansu? Eh to muyi magana da buhari Amma yace hajje tace Wai baruwan kowa akyalemata jikokinta suhuta. Ego itasukekira da hajje tsofa yazo Amma masifarta na,nan…to kyalesun zakuyi? Ah,ah zamuyi abunda yadace ne shiyasama nake Neman izini awurinki..to shikenan kuyi abunda yadace nabaku dama Allah yashige maku gaba.

 

Ameen ya Allah suka amsa Baki d’aya.kana alhj.salman yace. Inada magana mebabban d’aki..too sarkin surutu inajinka.dariya sukayi kana yace “Dan Allah kisaka baki babu yasaka aliyu yadawo kasarsa tahaihuwa. Nayi2 yasakashi yadawo Amma yak’i ko faruk ma yayimasa magana Amma yasharemu. Kidubafa yaransa kaf family Nan bawanda yasansu se a hoto kawai.suma hakan basusan kowaba.miye amfanin hakan fisabilillah.

 

Nisawa tayi kana tace”tokai miyasa bazakace D’an ka yadawo cikin y’an uwansaba? Murmushi alhj.jafar yayi kana yace to ainibanhanasa dawowaba shine betashi dawowarba yace acan saudia basaso yadena aiki dasu Kama yafiso kozedawo seyaranshi sunkammala karatunsu..shiyasa nabarshi.

 

Kuma Salman dakake wannan k’orafin Taya zance yadawo yabar Yara sukadai acan tunda su Kamal ma gobe zasutafi.

 

Hakane babu Amma ni ,a gaskiy naso ganin k’ane na.. dariya sukayi atare suna fad’ar tokaje kasameshi acan Mana..kaga se incigaba da kulama da tsofaffinan. Lewar faruk..abe kabishi kawai aikoni zankula maka dasu.cewar jafar k’arami. Yana nunin alhj.jafar.

 

Duka aben nasu yakaime yanafadar ja,iri tsoho na saudiya Yana fama da tsofaffin larabawa.

 

Tashi yy dagudu yabar wurin Yana dariya Suma k’annen nasa dariya sukayi kana akacigaba dafira..

 

********

 

 

Unguwar gurum unguwace ta yarbawa acikin garin Jos

 

Wata yarinya nagani wadda bazata wuce shekaru 6 ba tafe take tana y’anwak’e wak’ensu na yarbawa da tsalle.daga ita se y’ar K’aramar riga iya guywa..tsayawa tayi tana kallan wasu yara dasukayi gun,gu wuri d’aya suna tik’arrawa irin tayarbawa.wurin tadumfara gadan2 tana murna samtamanta da Aiken da origo tayimata..tanazuwa akafara ihu anafar se mebo,se mebo,se mebo.aitanajin anfara yimata kirari tafara botse mazaune tana rawar yarbawa setakai k’asa tadawo sama.idan mutun yagani ze dauka y’ar shekaru 14 ce sabida yanda Allah yayimata baiwar manyan mazaunai da iya rawar tasu.ihu kawai Yara keyi dama wasu manya Dake wurin..tanacikin rawar taji anfisge Hannuta anfiddata cikin filin rawar.tirjewa takeyi ahaka Kuma Tak’i Dena rawar.yara kuwa se kana,nan maganganu sukeyi Dan anfidda musu tarraruwarsu.

 

 

Seda sukayi nisa kana wadda kejanta yatsaya yad’au keta cak yad’orata akafad’ar shi bedireta ko,inaba se madedecin tsakar gidansu.saukowa tayi cikin tsiwa danufin sauke Masa rashin kunya.setaga Ashe yayanta ne ola shiru tayi tana mazurai.origo ce tafito da buta ahannuta zatayi alwala.kutt nace araina dama musulmaine? Tambayar daba me amsamin ita.

 

Muryarta naji tana fad’ar maza jekid’auko buta muyi sallah.wucewa tayi tana juya mazaunai sekace babbar mace.ola ma masallahcin gefen gidansu yanufa domin yin sallar.shine kawai masallahci dasukedashi a,unguwar.

 

Bayan sun idar da sallah ne yadawo gidan yajawo mebo datake kwance saman cinyar kakar Tata origo.tsuma giya yasamu yafara lafta mata yanafad’ar bana hanaki yin rawa acinkin unguwar nanba Amma bakyajiko toko zakiga yanda zanyi Dake muddin kikace bazaki denaba.itako ihu kawai takeyi tana fisge2 Kamar kamun jinnu. Seda yayi Mata lilis tukunna ya kyaleta origo nagefe tana kallansu batace komaiba haryagaji yadena dukanta yafita.

 

Abunci origo tabata ammafir tak’itaci sabida zuciyar har yanzu Bata saukaba.”inba zakiciba bani Aiken Dana miki.nanma shiru batace komaiba.

 

Itama shareta tayi taci gaba da aikinta domin tasan inzasu kwana anan bazata tankaba tunda zuciyar taboro dama haka take dabak’ar zuciya.

 

Bebo yarinya ce k’arama y’ar kimanin shekaru 6 Farace ita Amma basosaiba tanada manyan idanuwa masu d’aukar hankali tuntana jinjira wasu Dan,aga,ida nuwanta kawai akezuwa gidan.tanada hanci Dede gwargwado.tanada Dan k’aramin Baki Wanda iba katsura Mata idoba ayanzu datake k’arama zakadauka bakin baze bud’uba. Inkuwa tabud’eshi wowoww hak’oranta harkashin Ido sekeyi sabida haske gasu ajere reras tubarakallah.dudda zamanta bayarbiya Amma tanada sumar Kai baka wulik sabida mahaifiyarta bafulatanar daji ce mahaifinsu ne bayarbe.

 

Subiyu ne agun iyayensu daga ita se yayanta ola iyyensu sun rasu ahannu kakarsu suke.origo mmn mahaifinsu.Dan gin mmn su sunso sukarb’esu Amma fir origo da danginta sukak’i amincewa domin Allah yasaka musu San yaran bakad’anba.

 

Mebo rarinyace me illimi sosai dudda rashinjinta behanata karatuba sedaifa na boko kawai sukeyi basa zuwa islamiyya.

 

Kuma dangi mmn sune ked’auke da nautin karatunsu.

 

 

Cigaban lbr

 

Zaune take tunda yagama dukanta Bata tashiba yanzu kusan awa 4 kenan tun k’arfe 2:00 haryanzu 6:00 ko sallar la,asar batayiba origo tayi2 tatashi Amma tak’i haka tasaka Mata Ido domin intamatsa kuku zata sake sakamata.

 

Ola ne yashigo jikinshi bid’i 2 dak’urar ball ruwa yazuba a bokiti zeyi wanka seyafarayin alwala danufin iyadawo yayi wankan domin lokaci yak’ure.kallan mebo yayi dake zaune inda yabar.yadaka Mata tsawa.keeee maza tashi zuwa sallah Kona tattakaki anan.yana gamafad’ar hakan yafita jin anfara tada sallah.

 

Koda yadawo daga masallahcin begantaba tatashi..d’aukar ruwansa yayi yashiga wanka..wankan yakeyi Amma zafi yakeji ajikinshi bedamuba yacigabada wankansa Amma yanajin zafin nak’aruwa.seda yazo wankin fuska Yana zubawa suskarsa ruwa seko ya……

 

 

 

___________

 

 

Wannan novel nakud’ine duk,wanda yakesan spc group Wanda yabiya IZZAR MULKI to #300 zebiya vip Kuma #200

 

Inkuma bakibiya IZZAR MULKI ba to spc #500 vip #300 zakibiya

 

Inkuma complete kakeso lokaci d’aya to #500 zaka biya

 

Kuma gabaki d’aya tawannan nomber *08062979421*

 

 

 

 

 

 

 

Autar alheri..

*WAYE MIJINA ???*

 

 

By Yasmeen Ahmad

 

 

Autar alheri

 

 

 

*ALHERI WRITERS ASSO*

 

A*W.A

 

 

 

 

 

Free page

 

Page 5 & 6

 

 

___yana zubawa fuskarsa ruwan yashigarmasa idanuwa Aiko yaji rau cikin idon kamar zasu tsage sabida azaba..yadauka yajin sabulu ne yashigar Masa seko yakoma zuba ruwan Amma sedad’a karuwa yajin keyi.

 

Mek’ewa yayi gigice Yana dokawa origo Kira cikin azabar da idanuwansa kemasa yashiga lalaben towel Yana rik’oshi yadauro yafito dabin gini..origo na d’akinta tak’are sallar magarib taji Yana doka Mata Kira cikin hanzari tafito danufin Isa bayin.setaganshi yafito yanabin gini se murzar idanuwa yakeyi Yana Kuma kiranta ga idanuwansa sunyi suntun sunkumbura.

 

K’arasowa tayi tana fad’in lpy miyafarune?

 

Baniruwa3 kawai yake fad’a cikin fitar hayyaci..dasauri origo tad’ebo ruwa tabashi yarink’a wanke jikinshi da idanuwanshi Amma zafin yak’i yatafiya seyaji yarage dazarar yadena zuba ruwan seyak’aru..haryagaji dazuba ruwan origo natayashi dayimasa tambayar miyazubawa kansa haka amma Sam hankalinshi baya raredashi.. ganin zafi yak’i tafiyane yasa origo cewa mebo tadauko mai vasilin yashafa ko abun zeragu.

 

To kawai tace tashiga d’akin domin tunfitowarsa take zaune tanacin abuncinta da origo takawomata d’azu.

 

Robar vasilin d’in tad’auko tajuye vasilin din cikin wata robar tad’auko Loko tasaka cikin robar vasilin..takawo masa

 

Karb’a origo tayi tabashi yafara shafawa tana tayashi.fuskarsa yafara shafawa kafin jikinsa..Amma ko,idarwa beyiba yawulgarda man Yana ihun azaba.

 

Domin jiyakeyi kamar anatsaga jikinshi ana zubamasa barkono.hankalin origo yatashi sosai tarasa yazata yimasa yadena ihun da birgiman dayakeyi ak’asa.

 

Kiran uncle d’insu tayi adebo tagaya Masa yazoda Dr aduba ola ba lpy.aiko cikin kan,kanin lokaci ya,iso tareda Dr akashiga dubashi.

 

Bayan Dr yagama dubashi yarubuta Masa magani yayi Masa allura.

 

Miyake damunsane Dr ?cewar uncle adebo..ruwan barkono ko attarugu ne yayi wanka dashi haryashigar Masa ido yazo Kuma daga baya yashafawa jikinshi Loko shiya haifarmasa da Wannan zafin. Sabida haka yakiyaye yin amfani dawad’an’nan abubuwan domin zasu iya illatamasa fata.

 

To sukace cikin mmki sukayiwa Dr godiya yatafi.anan uncle adebo yazauna harseda yafalka bawani zafi dayakeji yanzu se ciwon jiki kawai da Dan abunda ba,arasaba.abunci aka,kawomasa yaci sosai seda yak’oshi.kana suka shiga tambayarsa aina yahad’u da barkono yayi wanka dashi.nan yakebasu lbr yanda yayi shibesan ya,akayi yasami barkonoba.

 

Wata tambayar uncle adebo yasakeyi domin bayaso abunda zetab’a lpyr y’ay’an yayan nasa.”to Aina kasami Loko kashafa? Wannan Kam kaganta Nan itatakawo Masa shi Nima hankalina yatashi ban kula daminene takawo masaba. Cewar origo.

 

“Mebona miyasa Kika kawowa yayanki Loko unmm bakisan zafine dashiba? Yatambayeta cikin lallashi Yana rungumota jikinshi

 

Baki tatura gaba kana tace to Uncle bashibane ya dakeniba d’azu.salati origo tasaka tanafad’ar kadde harbarkono kekika zubamasashi aruwa.

 

Sake tura Baki tayi gaba tana k’uk’unai k’asa2.duka origo takawomata uncle yatareta yanabata hak’uri.

 

Barni da,ita adebo ayi yarinya k’ank’anuwa se masifar tsiya eyee.origo Yafasan halinta Kuma yake dukanta yarigada yasani komi zakayiwa mebo setarama Bata barin bashi kokad’an.miyasa bazaki yimasa fad’a yadena dukantaba..to ai yanzu inbedenaba zasurik’a yinjinya tare.

 

Yanakaiwa Nan yamek’e rataye da mebo akafad’arsa yabargidan..ola kuwa tunda yaji mebo ce silar wannan azabar dayasha zuciyarsa ketafasa jiyakeyi kamar ya kakkaryata gunduwa2.

 

Hummm ola kenan ka,karyata ko kukarya juna domindai mebo babarinka zatayiba😂😂

 

 

Saudiya

 

Hakeem tunda yafalka ciwon yasakesa Kamar beyiba.tashi sukayi suka Koma sashensu. kowannesu bedroom d’inshi yanufa danyin wanka.bayan sufito daga wankanne suka shirya cikin Kaya iri d’aya Kamar kowanne yasan abunda wani zesaka.

 

Fitowa sukayi gwanin Sha,awa ajere suka nufi farfajiyar gidan.

 

Dama haka suke basa saka Kaya daban,daban komi zasu,saka iri d’aya suke sakawa domin kowace sutura da ranar dasuke sakata.hatta tabarau da agogo da zobe iri d’aya suke sakawa. Ko iyayensu basa iya ban,bantasu domin zaka,iyarantsuwa mutun d’aya ne ba biyu ba.

 

Inda Allah yaban,bantasu kuwa b’oyayen wurine Wanda kosanda suna Yara ananne kawai iyayensu keganesu. Wato mazan takarsu ta ban,banta kowanne da kalar tasa hallitar. Hakeem abunshi nada girma kosanda Yana yaro Kuma tunyana yaro yakeda suturar jiki wato gargasa.

 

Hafees kuwa beyi girman Hakeem ba Amma shima bak’arami bane Kuma shi bayada gargasa seda lokacin yinshi yayi.

 

Hanya tabiyu kuwa in abun fad’a yasamu domin dukansu miskilayene nak’arshe basa shiga Sha,anin kowa basada yawan dariya bakinsu murmushi

 

To ammafa in antab’asu Hakeem bashida sauk’i akwai bak’ar zuciya yayinda Hafees yakasance mehak’uri bayaso rigima Amma in,an tab’a Dan uwansa Yanayi sedai bashida rok’o

 

 

Zuwa sukayi sukatadda iyayensu azaune wurin Shan iska gaidasu sukayi.amma ba,atareba Hafees ne yafara cewa barka darana mom & dad.

 

Yawwa barka Hakeem yajikin naka? Kallan juna sukayi suka saki murmushi atare kana yace dasauk’i sosai..to Allah yabaka lpy. ameen suka amsa Baki d’aya.

 

Kana Hakeem d’in yagaidasu shima suka amsa suna fad’ar “Hafees kakula da D’an uwanka pls kaga bashida lpy sosai karkujima kunjiko.

 

To sukace atare sukabar wurin.iyayen nasu suka rakasu da addu,a.

 

shiga mota sukayi suka nufi shopping Moll Hafees ke driving Hakeem nazaune gefinshi.

 

“Bro Wai baka mmkin yanda su mom kekasa ganemu? Ni,abun naban mmki wlh wani lokacin Kuma yaban dariya to Wai inbasu ganemuba waye zeganemu?

 

D’agowa Hakeem yayi Yana murmushi yace”to bamuda ban,banci dazasu ganemu ne shiyasa..No munadashi Mana bro.

 

“To nidai banganshiba.haba gashi kuwa yafad’a Yana nunamasa setin joystick dinshi Yana murmushi kasa2.harara ya zabga Masa kana yace toyanzu tayazasu ban,bantamu anan?kodama dasukr iya ganewa ai Dan bakada wannan abunne yanzu Kuma kanadashi to kaga ko anan bazasu ganeba kenan.

 

A,a fa zasu iya dubawa idan sunso ai koyanzu da ban,banci.ganin yau surutu Dan uwan nasa keso yasa yashareshi.shima shareshin yayi harsukaje suka dawo.

 

 

Jos

 

Alhj.jagar ne da y’an uwansa suka tasa k’annen su gaba suna saura,rar bayaninsu.”agaskiya Yaya bawani abunda takemin Amma shimijin nata Bata ganin girmansa bata Masa uzuri kokad’an akan yarannan ba,abunda batayi eyee haka akeyin rayuwa sabida Allah zata sakamin yaro damuwa abanza shiyasa nace yasaketa taje cangidansu akoya Mata tarbiya.cewar gwaggo safiya

 

 

“Nisawa alhj.buhari yayi kana yace”yanzu ke safiya wayagayamiki duk wad’annan abubuwan dakika fad’a? nasanine ai waye besan zamanda isham keyi da zulaiha ba.

 

Shikenan tunda bawanda yagayamiki to Amma kisani kifitadda hannuki acikin maganar auren isham domin koshidai yanzu bayaro bane yadace yasan ciwonkansa ya,iya seta gidansa base,kinshigaba.

 

Kuma kidena biyewa hajje domin yanzu kome zatayi aikin tsufane domin yanzu koke dakike y’arta shekarunki sunja balantana ita Dole semuna masu uzuri.Kuma kiyi gaggawar sakashi yamayarda matarsa wlh koranki yayi mummunan baci inagayamiki.

 

Hakane gaskiya Kuma karnasake jin bakinki acikin Wannan maganar kinjiko.cewar alhj.jafar..eh naji Yaya Amma itama kujamata kunne dan bazanyarda tasalwantarmin da yaro ba.waye yaro? Alhj.buhari ne yakarb’e zancen dacewa Shi isham shine yaro Zaki rufemin Baki kosena tattakaki anan mutuniyar kawai.shiru tayi Bata sake maganaba.

 

 

Kekuma saudatu munji duk abunda kikayi kisani wannan abun kuskurene gambo yafiki gaskiya kisani danine kikayiwa rashin kunyar dakikamasa wlh Allah dukan tsiya zammiki agaban y’ay’an naki da jikoki tunda ke bakisan mutinciba koba darajar aure gambo ba yayanki bane dazayimasa hakan abunda kikeyi tunyarinta Ashe haryanzu Baki denashiba tokisani wannan yazan nak’arshe bazamu sake lamuntar rashin mutunci daga garekuba amatsayinku na iyaye mata.kokugyara komusaka kafar wando d’aya daku mutanen banza mutanen wofi.

 

Kuma nayiwa gazali magana yazo yad’au ke yaranshi tunda kansune kike tujarar.

 

Nan desuka yimasu fad’a sosai kana suka sallamesu.sukatafi

 

Sunrage dagasu sesu mazan.tattauna yanda yadace subullowa lamarin family nasu sukayi.kuma alhj.jafar yacewa alhj.buhari yafitadda hannusa cikin lamarin aurenda jikokinsu kesanyi wato misbahu da jalilah

 

Jalilah dai kusan yace ga alhj.salman shiko misbahu D’a ne ga alhj.hamisu D’an baba buhari da uwane nafari.

 

 

Abunda yasa nace kafitarda hannuka shine mukyale iyayen Yara suyi hukuncin dasukaga yadace dayaransu mude kawai shawara ce tamu da addu,a..hakane shiyasa tunfari bance komaiba sabida naji faruk nazance shiga gazali.shikenan to Allah yashige Mana gaba..ameen duk suka amsa atare kana akayi addu,a kowa yakama gabansa.

 

Alhj.gazali kuwa D’a nega saudatu da gambo.

 

 

*Mekaratu sefa kabi labarin,nan tiriyan2 sa,annan zaka fahimta karkuga inabayyana muku wasu sunaye daga baya kuyi tunanin zandabirtakune a,a nayihakanne dankugane sosai domin inbayya namuku subaki d’aya zaku mantasu kamin akai gamatakin dazasu taka tasu rawar shiyasa se lokacin amfanin mutun yayi zanbayyanashi Inna baku labarinsa Sena bayyana muku koshi waye inafatar kunfahimta*

 

 

Alhj.Isham ne kejaune perlon kakarsa wato hajje shida mahai fiyarsa da kanwarta. tanacika tana batsewa.magana tafarayi cikinfushi

 

“Kanaji kamayar da,ita d’in Amma banyarda kasaurara mataba dededa kwayar zarrane karka yadda tasake acikin gidannan.tunda subasada mutunci Wai hadda Yaya buhari fa hardafad’an Wai hajje batada tunani yanzu tatsufa.ko ubanwaye yagaya Masa batada tunani oho.

 

 

Car ubannan nicema banida tunani aikozezo yasameni mutumin banza mutumin wofi Wanda besan Ina kemasa zafiba yafiso yahad’a Kai dasu ayita cusguna muku zanyi maganinsu ai tunda bani nahaifeshiba Kuma yayunku sunfi shi laifima tunda dukkan abunda sukace shida wacan daya tsufa besan yatsufaba yatura yaro saudiya dasunan karatu Amma Allah kad’ai yasan abunda yake aikatawa acan d’in Amma yazo yasaka muku Yara agaba duk abunda yashimfida bame tsallakawa.

 

Ikon Allah kuji dattijuwar tsofuwa waida zagi🤔🤔

 

Sema naje nasami uwar tasa naji ko wani asirin sukamuku suyi gaggar karyashi Dan bazan yardaba

 

 

Gwaggo saudatu ceta karb’e zancen dacewa “kyalesu kawai hajje Nima aizanyi maganinsu Dan bazanbi umurninsuba dansuga Allah bebani Yara dayawaba shiyasa sukeso Yan jikokin surabani dasu yadda sunka kwace mahaifinsu seyadda sukace yakeyi dudda zamansa shikad’ai besa suka Bari naji sanyinsaba.

 

Danhaka Niko senaga merabani da jikokina dasuke cewa arabamusu makwanci dagamu harsu har yaran namu damukayi kwanci wuri d’aya miyafaru damu balesu Kuma Yara uwa, d’aya,uba d’aya Dan mugun sharri garsubarsu naji sanyi bara su bullo da wanna.

 

“Hakane saudatu aizamu nuna musu Basu isaba Kuma karki soma raba musu wurin kwanciya tunda aihakan bawani abubane shinwaima tsaya da Aina suke ne? Adaki d’aya kikabasu kokuwa?

 

A,a wlh kowama da dakinsa wani lokacinne in mansura taje yafad’a Mata karatu indare yayi setayi kwanciyarta acan shinefa abun rigimar.

 

Humm tobarakiji yanzu Basu bedroom d’aya Kinga basetaje koyon karatuba sesuyi abunsu anan insuka Gama se suyi kwanciyarsu koya Kika gani?

 

Hakane yar uwa hakan za,ayi wlh Senaga karshen Isa da felek’e cewa yad’auke yaranshi.tafawa sukayi suna shewa uwarsu namara masu baya yayinda suke k’ara zuga isham akan matarsa.

 

Semuce Allah yakyauta

 

 

Komawa gida isham yayi da,abubuwa dayawa aransa.koda yashigo gidan zulaihat na zaune parlo itada yaranta Y’an kimanin shekaru 18 & 15 siddik’a da nabila se nabil d’an shekara 24

 

 

Dama tunlokacin da safiyya tace seya saketa tanan gidan ba,inda taje acewarta anan zatayi idda

 

Shigowa yayi pelon Yana shuri da tubalanye Dake ajiye aperlon domin da,akawai kwanuka kowani Abu shizeyi shuri dashi shine sallah marsa

 

Jiyowa sukayi Baki d’ayansu suna dubansa Amma Banda nabil dayayi Kamar besan da zamansaba.tafiya yafarayi zuwa pert d’in shi shiyasa duk sukacigaba da kallan dasukeyi na tashar BBC Hausa.suna cikin kallan sukaji abu rassss,rass, guffff,gigigif.agigice yukajiyo Aiko sukazabura sunafad’an…..

 

 

Add Comment

Click here to post a comment