Sanadin Boko Hausa Novel Complete
Sanadin Boko 1 01
Posted by ANaM Dorayi on 09:25 AM, 10-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na
Maryam Abdullah K.Mashi
Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta
kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu
kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma
suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce
poly wasu Jami’a, wasu Nursing school.
Sa’adatu da ke kusa da ni ta ce, “Hafsy don Allah kema
ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana.” Nayi dan
murmushin takaici.
“Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda
in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni.”
Ta zaro ido. “Kada kice min kina cikin wadanda za’a
dakile a kai gidan miji?
Na sake ajiyar zuciya.
“Ke dai Sa’a taya ni da addu’a, Allah Yasa ina da rabo,
Rayuwata Ce Hausa Novel Complete
dan kuwa ina son in ga karshen boko.” Jamila ta dube ni,
“Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki
ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen
ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne?
Na ce, “To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke
ba kince aure ba?” Jamila ta ce, “Aure kuwa insha Allahu
ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna.
Sa’a ta ce, “Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki
za ki watsar da batun karatu. Na ce, “Dubu nawa akayi?
Ai ni boko yanzu muka sa dan ba.”
Ta ce, “Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta
aikhairi”. Na ce, “Ga magana da za ki yi kawai, Amin”.
Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam
fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba,
da wuya naje wata Makarantar.
An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka
nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita
ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana
da makarantar wato mun kammala.
Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna “Ga Hafsat
ga Hafsat”. Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta
dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na
ce, “Innarmu ba su hamsin”. Ta kwance habar zani ta
mika musu.
Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan
gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa.
Inna ta aje min kwano tare da cewa, “Alalar har ta
huce”. Ta dire min kofin ruwa na ce, “Har yanzu bata
kare ba ne?” Ta ce, “Ta kare mana, ai tun kwanaki da
Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku
kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga
magariba tayi ne sannan in ba yara.
Nayi dariya tare da cewa, “Innarmu kenan! Ina Yaya
Ummar?” Ta ce, “Tun safe bai dawo ba, kin san nasai
mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako
na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan
yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan
ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina
fama da shi.
Na ce, “Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa
asiri”. Ta ce “Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da
ni, na ce “Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna
ta ce, “Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?”
Na rungumota a jikina ina cewa, “Gani na dawo”. Ta rufe
fuskarta, ita dole taji kunya.
Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce “Kin
zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa”. Na rike
baki, “Inna har da Sakina?”
Ta ce, “Eh! Na ce, “Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da
karatuna ma”. Innarmu ta ce, “Malam ne matsala, amma
ko Nas din nan da ‘ya’yan Kawunki suke yi ai zan so
kiyi.” Na ce, “Wane Nurse? Ni fa Jami’a nake so, burina
in zama ‘yar Media”.
Ta ce, “Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka,
sannan na ajiye tare da cewa, ” ‘yar jarida mana! Sai dai
matsalar kudi ne”. Kai lomar alala da nayi baki, ta zo
daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar
na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa,
tare da shimfida mishi tabarma.
Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau
fuskar shi sake ya amsa, har da ce min “An dawo lafiya?”
Na ce, “Lafiya lau”. Innarmu ta ce, “Allah cikin ikonSa
Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya
kammala.”
Ya ce, “To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa
magana ya fito in hada su da Sakina in huta”. Inna ta ce,
“Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi
makarantar gaba da…”
Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike
tsaye ransa a bace.
“Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya
ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya
shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata
tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon
zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin
wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun
gidan duniya ne?”
Inna ta kufulo itama, ta ce, “To dama ka saba ka min
tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu
sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, “To zan ga
wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke”. Ya fita.
Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena
basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce
masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin
nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina
ba.
Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai
mita take, na ce “Innarmu ki bar batun haka, kinsan
gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana
sauraro”. Ta ce, “Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka
dai mace tayi da ni naji mu kwashi ‘yan kallo ni da ita”.
Na idar da sallar isha’i, ina zaune a gurin ina istigfari,
wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce
“Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje”. Ta ce, “To”.
Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter
cewa na dawo.
Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan
na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo
kamshin turarensa.
Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka
wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin
farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da
kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa.
“Babyna”. Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na’am”.
Ya diro “Zo muje cikin mota.” Na ce, “A’a mu zauna
can”. Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu.
Ya dan gyara tsaiwa, “Kin ce fa baki son Baba ya dinga
ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai
ganni dole ko?”
Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa
Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga
suturar da yake sakawa.
Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba
jikina.. Ya katsemin tunani da cewa.
“Zo muje, na zo da muhimmiyar magana”. Na ce masa,
“Nima ina da nawa muhimmin zancen”. Baya ya bude ya
shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya
ce “Rufo kofar mana”. Na ce, “Ka barshi haka ma ya yi.
Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka
kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin
wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina.
Ya ce, “Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki
ba.” Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya
na ce, “Don Allah Munnir ka daina son taba jikina,
haramunne fa”. Ya ce, “Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne
fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki
yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta
ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki
ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki
ba.
Na bata rai, ya shafi kumatuna.
“Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin
daure fuska”. Shikenan, ban san lokacin da murmushin
ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya
ce, “To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in
kinji saikin bani goron albishir.
Na ce, “To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace
yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na
gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka
dai sani”. Ya ce, “Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin
manta alkawarin da muka yi ni da ke?”
Na ce, “Ban manta ba”. Ya ce, “To ki kyale fadan Baba
kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on
aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne
saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je
kasuwa musai kayan sawa?
Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake
matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai
rungume ni. Da sauri na ce, “Duk lokacin da ka shirya”.
Ya ce, “Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din.”
Na ce, “Um”. Ya ce, “Wai ba ki murna ne angel dina?
Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin
zama *yar media insha Allah.
Na dube shi, “Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?” Ya
ce, “Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada
master dina, before time din kin zama *yar media ko?
Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin
juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, “Kin san ina son
aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki.
Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya
ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni.
Na ce, “To sai yanda Innarmu ta ce”. Ya ce, “Bana jin
Inna, zata yarda”. Ya sake yin kasa da murya “In dan yi
kissing din kunnenki?” Naja baya tare da cwa, “A’a”. Ya
ce, “To bari na tafi”. Yana magana yana kallon agogon
hannunshi, “Zan kalli wasan Arsenal yau.” Na ce, “Kai
kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan.”
Ya ce, “Kema za ki koya in kinzo gidanmu”. Nayi dan
murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi,
amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin
mata masu bukata…. Ya katse tunanina da cewa, “Ko
kada in tafi ne?” na ce, “A’a kaje sai gobe”. Ya ce,
“Shikenan.” Ya miko min wata farar leda.
“”Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk.” Na ce na
gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan
dawainiyar.
Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har
da kayan tea. Ta ce, “Kai yaron nan baya gajiya da
dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon
karatun kyayi can a dakin shi.
“Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara
hakuri.” Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe,
sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana
son abinda nike so.
Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar
Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata
mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu
shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa
nake son in ganni a dakin kaina.
Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da
Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana
cewa, “Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira
ki ba, nasan gurin ki ya zo.
Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na
atamfar (Java), gyale na sura na ce “Inna Munnir na
kirana.”
Ta ce, “To.” Na nufi waje kai tsaye.
Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa
ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya
shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na
ce, “Muyi sauri ban ce zamu fita ba.” Ya ce, “To”.
Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a
gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga
wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai
tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, “To zabi wanda
ki ke so.”
Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da
*yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar
zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi.
“Duk ba su yi min ba”. Ya bata rai sosai, “Tashi muje”.
Na kafa mishi ido. Ya ce, “Tashi mana”. Cikin daga
sauti na ce, “To, to naji zan amsa, amma ni na gane
kamar zasu yimin kadan.” Ya dan sassauto “Muje
gidanmu ki gwada.” Da sauri nace, “A’a zasu yi min.”
Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga
motarshi. Ya ce, “Muje mu dan sha Ice cream”. Na ce,
“A’a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma
nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min”. Ya ce,
“To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada
na cinye ki.”
Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a
dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana,
ya ce “To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi
yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura
mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da
muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last
kudin shi don muyi karatu.
Na ce, “Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba,
amma ka fito ku gaisa.
Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi
cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce,
“Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga
lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, “Um asibiti muka je
dubo kanwarshi”. Ta ce, “Shi ne ba za ki fada ba? Kin
san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja
min surutu sanadin bokon nan.”
Na ce, “Kiyi hakuri Inna.” Ina rufe baki Babanmu yana
shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana
cewa.
“Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min
manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan
wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to
ban laminci wannan ba.”
Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni,
ya ce “Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta
ce, “A’a Malam asibiti fa suka je.” Ya zaburo tamkar
zai kai ma Inna duka, ya ce, “In ji wa? Wa ya fada
miki?”
Inna ta ce, “Ga ta nan.” Ya ce, “Makaryaciya, to shi
abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk
ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?” Inna
ta tsare ni da ido, “Kasuwa Hafsa?” Nace, “Kuyi hakuri,
ba zan kara zuwa ba.” Tayi kwafa tare da ci gaba da
yin aikinta. Baba ya ce “To wallahi ba zan yarda da
gantali ba, wai ku *yan boko.”
Inna ta dube ni, “Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni
na jajirce ki samu karatun boko.” Na ce, “Don Allah
Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba”. Ta ce, “To
me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min
karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?” Na ce,
“Na sani.
Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta
sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi
saurayi wani guri.
Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane
ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na
ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi
shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore
shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin
wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure
shi. Shi kadai nake jin sha’awa. Na rasa yanda zan yi
ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina
cikin damuwa, ta ce “Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce,
“Ciwon kai ne yake damuna.” Ta bayar da Naira goma
a amsomin panadol.”
Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar
makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, “Kar ki
zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?” Na ce, “Ai
dazun ciwon kai ke damuna.” Ban yi wata kwalliya ba,
kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari
mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu
saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su
kuma suna Makarfi Road.
Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga
motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri.
Daidai ya bude motar zai shiga na ce, “Munnir” Ya juyo
da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana
ciki, ya ce, “Beby lafiya?” Na jingina da motar, sannan
na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma
lokacin ne naga rashin hankalina.
Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo
biko? Ya sake cewa, “Me ya faru Baby? Na ce, “Ai ba
ka ma sani ba?” Dabara tazo min, na ce “Dama nazo ne
na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko
zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba.”
Ya ce, “Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya
rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni”
Kafin nayi magana ya ce, “Ina zuwa.” Ya leka motar
yayi magana, sannan ya ce, “Zo muje ciki kiji.” Na ce,
“A’a. Ya bata rai, “Bana son yawan gaddamar nan, ki
daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala.
Na ce, “Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, “Ba
za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate
din gidan, muka shiga.
Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga
haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, “A’a, ka fasa fita
dinne? Ya ce, “A’a Baba, yanzun zan fita.
Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin
gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, “Yau kin zo
gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su
Nana.
Na ce, “Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni
cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce,
“Shikenan.
Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai
kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna.
Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin,
jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi
ya zauna hannun kujerar da nike
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 1 02
Posted by ANaM Dorayi on 09:42 AM, 10-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na
Maryam Abdullahi K/Mashi
Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai
kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina
kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim
kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya
zauna hannun kujerar da nike.
Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika
min, na girgiza kai tare da cewa, “Na gode. Ya ce, “Wasa
ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki.
Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya.
Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da
mikewa.
“Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, “Dama ni banyi fushi
ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin
idonshi daya, nayi saurin kauda idona saboda yarr din da
tsigar jikina tayi.
Na ce, “Yaushe zaka zo? Ya ce, “Zauna to mu tsara in da
zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba
su zo ba kada ya sake ganina.
Na ce, “Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya
dan yi shiru, “To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan
hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke
ba ki da irin ‘yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a
silent.
Na ce, “Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na
marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura
yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba
Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji.
Ya tsare ni da manyan idanunsa.
“Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba “Ban san me yasa
gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da
Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya
musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku.
Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye.
Na ce “Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake
son ya yi ma ‘ya’yanshi. Ya ce “Shikenan dai, mu bar
maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke
ce dai ba ki ga dama ba.
Wani friend dina yarinyarshi itama ‘yar Geto ce, amma ta
jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali,
amma ke kin kasa.
Na ce, “Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin
yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai
kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa.
Cikin rawar murya na ce, “Munnir la..la….lafiyarka? Don
Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza,
da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi
da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, “A’a don
na tsorata, dole suka bar ni.
Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min,
dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun
shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni
na bar shi.
Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na
fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana
shi zuwa nan.
Inna ta ce, “Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da
Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani
abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki.
Na ce, “To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir
ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba.
Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani
ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa
Baba zai sani.
Na zama cikin sa’a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya
tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano,
sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta
ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda
gobe za ku je yin rijista.
Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu
nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana
sanar da Babanmu komai.
Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, “To bokon nan
ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura
tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko
duniya?
Inna ta ce, “Duka. Ya ce, “Karya ne, duniya ku ke nema,
kuma ga ku gata nan. Jami’ar da aka ce ‘ya’ya suna
lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru
amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai
hudu ba.
Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba
ruwana, zai shafe ki ne da ita.
Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba,
matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da
Allah Ya dora min.
Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki,
duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO.
Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba
kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa
dani ta zauna.
Tasa hannu ta dan dake ni, “Tashi Hafsatu.
Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce “Nasan kin ji
duk zancen da Malam yake yi ko?
Na ce, “Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, “Insha
Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da
kai gaba daya.
Ya ce “Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana.
Babah ta ce, ” Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki
ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi
miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama
ki.
Na ce, “Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu
zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri
mara ilimi ba.
Babah ta ce, “Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma
sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan
Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son
Munnir?
Na dube ta, “Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake
yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba.
Ta ce, “To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba
na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba.
Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi.
Anya auranki zai yi? Na ce, “Allah Babah aurena zai yi, ki
dubi dadewar mu da hidimar da yake min.
Ta ce, “Ba ta a nan, amma fa shawara ce.” Na koma na
kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta.
Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da
ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi
guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni
ba zai aure ni ba?
Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata
Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da
safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa
sha, Innarmu ma sukuku take.
Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan
alalarta manja, na ce “Inna ko dai zamu hakura da batun
bokon nan ne?
Ta dube ni, “Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, “Naji
duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce,
“Abu daya zuwa biyu nike so ki min.
Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da
mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin
da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata
ya zama sanadin alkhairi.
Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi
wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin
kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba
ba yana jin haushi.
Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki
da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni,
na ce, “Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki
kunya, SANADIN
BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni.
Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami’ar
Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata
daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba.
Nan na tafi na barta da surutun ‘yan gidanmu, da ‘yan
unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi
yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi
cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko.
Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe
kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita,
sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta.
Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su
bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi
hakuri suka ce wai karatun yana da amfani.
Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a’a tayi shi can
gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka
ce ya yi hakuri ‘yan kwanaki ne zata gama, don haka sai
ya dawo ya zura mana ido
******* ********** ********** *********** *********
Jami’a wata rayuwa ce da ta sha bamban da
secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya
kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina,
don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da
Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala
Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati
biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu
hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji
dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba
mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin
rubuta labari na “SANADIN BOKO” .
Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata
dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba,
ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji
muryarshi zan boye.
Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha
mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce, Munnir
ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na
fadawa Inna, ta ce, “Yana asibiti ne?” Duk da ban sani
ba sai na ce mata, “Eh.” A zatona yana asibiti ne, sai
da yaja mota sannan nace, “Wane asibiti ne.” Sai ya
ce, “Ai yana gida.” Har gefen su Munnir Bello ya raka
ni, ina shiga sai yace mun, “Toh yana ciki ni na wuce ki
fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce,
“Toh!” Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar
falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga
Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da
vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way)
yana sha. Na ce, “Ah! Ka samu sauki ne?” Ya ce, “Eh,
A’a.” Ya nuna min kujera, “Zauna.” Na zauna ina kallon
shi tare da son jin karin bayani, “Ban gane eh, a’a ba?”
Ya tsugunna a gabana, “Ciwon ya dade yana ci na, ga
shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba
tare da na samu maganin ba.” Na ce, “Wane irin ciwo
ne?” Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, “Ciwon
sha’awarki…..”
Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike,
“Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da
sha’awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki.” Na ce,
“Munnir ka san ina son ka.” Ya ce, “To ki nuna min.”
Na ce, “Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka?
Ka sani.” Ya ja tsaki, “Kin dai gane nufi na, ina son yau
daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni.” Na ce, “A’a
ba zan iya ba, domin haramun ne.” Ya ce, “Ni fa zan
aure ki!” Na soma tafiya don fita ina cewa, “Sai ka jira
sai ka…..” Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar
da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi
ya ce, “Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan
iya biyan bukata ta.” Jikina ya soma bari na ce,
“Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa.” Ya
zauna, “Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata
nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila
suna Makaranta.” Na zube gwiwoyina biyu a rude ina
cewa, “Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don
Allah.” Na soma kuka. Ya ce, “Nima ki taimake ni na
gaji, wanene za ya gane me muka yi?” Na ce, “Allah ya
sani, na tabbata zai kama mu.” Amma da yake Shaidan
ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina.
Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai
kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala’i dashi
kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a
kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta,
fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir
dina ba.
Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin
zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, “Duk kin
sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada
ba?” Na ce, “Bude min kofa kawai ni dai na tafi.” Ya
nufo ni, “Come on kiyi wanka sai na kai ki.” Ban san
lokacin dana daka mishi tsawa ba, “Budeni mana”
Sabon kuka ya kwace min na ce, “Allah ya isa tsakani
na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min.” Ya tashi
ya bude tare da cewa, “Sai na zo.” Ban kulashi ba na
fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na
fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo
daya Inna ta min tace, “Lafiya?” Jikina ya soma bari, ta
ce, “Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a
kumbure.” Na ce, “Umm jikin ne.” Ta ce, “To shine na
kuka? ki masa addu’a.” Na ce, “To.” Na nufi ciki. Ta ce,
“Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?”mummunar
faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto
min, amma sai na yi saurin cewa, “Fashin Sallah ne.”
Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin
zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce,
“Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan
wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye
jikinki.”
Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika
zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah
ya isa Munnir.
Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo
bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman
safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, “Ke da
naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa
tashi?” Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da
daman in tona asirina…
Yaron gidanmu ya shigo ya ce, “Hafsa wai in kin shirya
wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi.” Na
ja tsaki, “Ka ce masa ya tafi na san hanya.” Innarmu ta
ce ma yaron, “Kai zo, je kace tana zuwa.” Yana fita ta
fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai
kirani in ‘ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu
ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli
Innarmu a zuciya na ce, “Da kin san abinda ya min sai
kin fini tsanar shi.” Ban ce komai ba na ci gaba da
shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine ‘yan hamsin
hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin
robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji
Baabarki….. Na ce, “Ki bar kudinki.” Ta ce, “A’a na dai
baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne.
Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min
aurenku.” Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro,
“Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi
doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki.” Ban
tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga
but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya
bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi.
Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban
tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, “Ga
wayarki.” Sai lokacin na yi magana, “Bana so.” Ya
daurata kan cinyarshi, “Dole ki so ta Hafsat don in na
tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki,
abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan
aureki…” Na zabga mishi harara tare da cewa, “A
ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka
aure ni kayi ZINA dani ba.” Ya katseni, “Ki daina cewa
Zina.” Na daga murya na ce, “Ka biya sadaki na ne?
Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko
jama’a sun shaida.” Ya ce, “Ba daya.” Na ja tsaki ban
kara tanka shi ba har muka kai.
A dakinmu ba yadda bai yi ba na’ki tankashi, ya aje
mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi
na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya
sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma
mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in
dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni.
-Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na
hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da
wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake
ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin
Imani.
Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga
al’adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya
tilastamin shiga rudani.
Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta
ce, “Hafsy yaya ne?” Na ce, “Ciwon kai ne.” Ta bani
panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo.
Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba
cikin ‘yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana
dagawa na soma kuka, ya ce, “Mai ya faru?” Na ce,
“Banga period dina ba yau kwana uku.” Ga mamaki na
sai na ji bai damu ba ya ce, “Zan shigo wannan ba
wani abun damuwa ba ne.”
Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa
na soma kuka nan take ya bata rai, “Kukan nan ya
soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun
kuka ba.” Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba
har da cewa, “Daga sau daya sai ciki?” Munnir ya ce,
“Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in
anyi bikin mu juya Mahaifarta za’ayi don bana son yara
su wuce biyu tsanani uku.” Tsabar bakin ciki ya hana ni
tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya
kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo
suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je
asibiti.
Mun shiga office din Likita mace ‘yar kimanin shekara
arba’in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido
bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, “Me ke tafe da
ku?” Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya
ce, “Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna
so a gwada ta.” Ta tsareshi da ido, “Kanwarka ce?” Ya
ce, “Budurwa ta ce.” Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar
da kai ina hawaye, “To ku dan bamu wuri.” Suka fita.
Ta zabga min harara, “Kin bashi kan ki ko?” Murya ta a
sarke na ce, “Wallahi…
Zaharaddeen Shomar
what’s app 08168575100
Sanadin Boko 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 09:47 AM, 10-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
NA
Maryam Abdullahi K/Mashi
To ku dan bamu wuri.” Suka fita. Ta zabga min harara,
“Kin bashi kan ki ko?” Murya ta a sarke na ce, “Wallahi
Anty fyade yayi mun.” Ta ce, “Tun yaushe?” Na ce,
“Za’a kai wata daya.” Ta bani wata ‘yar roba ta nuna
min wata kofa, “Shiga toilet ki bani fitsarinki.” Ina
fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, “Don Allah sister
ina son result yanzun nan.” Ba jimawa ta shigo, Likitar
tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, “Kina da
cikin wata daya da kwanaki.” Nan da nan na soma
zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin
tsananin kuka da kunan rai na ce, “Ya cuce ni. Mai
zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.” Kuka na ya shigo da
su, ta mika mishi result ya duba sannan ya kalle ta, “To
yanzu doctor ya za’a yi tunda gaskiya ni da ita karatu
muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba.” Na dube
shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya
aikata abin arziki. Ta ce, “Baka shirya tarban Baby ba
mai ya kaiku aikata haka?” Ya ce, “Tsautsayi ne.” Ta
ce, “A’a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da
ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai
kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya
sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira
(S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki
sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye
da aure.” Ta nuna shi da biron hannunta, “Musamman
irinku ‘ya’yan ‘yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai
kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku
shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya
turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako
lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba
bare kusan illar ZINA.”munir yace to doctor, yanzu
menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a
cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki
iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana
nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi
ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan
da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma
nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka
wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya.
Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan-
gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na
koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a
turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba,
itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode
Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin
saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita
ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni.
Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida
kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna
kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki
daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta
fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta
shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da
kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne
ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace
a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na
sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace
asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki?
Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da
Asabe.Mu ‘yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar
kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata
mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana
diban yara ‘yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da
Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan
samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi
son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai
Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai
yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya,
kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka
dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da
Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba
wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala
in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne
dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne
don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta,
amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba,
don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina
kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar
komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi
in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta
so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi
dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na
dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire
kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na
cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya
hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe
ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun
daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar
matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai
lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata ‘yar
uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir
cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana.
Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn
da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai
amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya
gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari
dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta
shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata
wanda ya min, na ce Yasir ne.
Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara
ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo
ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min
kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce
mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi
masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara,
kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka
cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada
naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati
biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido,
sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa.
Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole
na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don
ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk
ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya
son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana
tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun.
Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya
zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO.” Na jinjina
kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni,
kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce
Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child
abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi.
Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru
da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido,
hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in
taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan
cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire
miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na
share hawaye,sannan na ce da ita. “Sunana Hafsatu,
Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida
tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan
yake ‘yar sana”arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can
lkcn tazo gidn yarta a Na’ibawa. Babana Shi ne ta
tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma’aru
me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana
sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina,
unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don
yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo
magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu
Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban
dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa
auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa
kaduna, ya fara sana’ar saida lemo da Ayaba,daga
bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da
Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar.
Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf
ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce
mana. Mata goma sha ne, kowace da ‘ya’yanta wasu
hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro
wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki
kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa,
shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata
biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun
Babah ‘ya’yanta 6, Innarmu 8. Ni ce ‘ya ta 2, masu bina
3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su ‘yan
boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don
haka tana da burin mu ‘ya’yanta muyi boko, shi ko
Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi
ra’ayin nayi saukar Alkur’ani mai girma ya min aure.
Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don
haka ni da yayana mun taso muna son karatun
boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani.
Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai
cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin
haka ne yasa Innarmu ta kama sana’a. Gyada take
soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta
dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin
haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga
Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai
lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a
Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta
ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba
da primary balle ‘yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa
makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba
yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba
ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka
kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka kara
yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa
yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma
yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna
ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi?
Na ce A’a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na
ce “Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna
ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da
safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce
Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi
ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a
saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba
kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga,
na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi
alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka
ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa’a kin ji, kan lkcn
Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don
na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani
har na gama primary duk report card dina ba wanda ba
a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake
karatuna.
a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla
na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na
tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti,
tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake.
Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in
yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai
har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka
zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har
da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda
naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi
ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na
tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar
carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso
nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko
ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta
kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa
innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar.
Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare
don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina
wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa
(government college) wata rana ina zaune kan duntsen
da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena
hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan
barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani
ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na
dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, “Sa min
daya a leda sarkin wasa.” Na ce, “Zaba.” Ya ce, “Zabar
min.” Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido
saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi,
kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro
wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya
zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a
raina ina cewa, “Dama ‘yan gayu suna cin gyada?” Ya
dube ni, “Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware.” Na
dauke idona daga bisani na tashi, na soma ‘yar gala-
gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa
banda ni, da ya mi’ke zaya tafi ya ce, “To sarkin wasa
ga kudinki.” Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a
rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na
ce, “Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba.”
Ya ce, “Mai zaki yi da ita?” Na ce, “Ajiyewa zanyi ba
zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta.”
Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi
ya ci rabi ya bar saura, na ce, “Ji fa baka cinye ba.” Ya
ce, “Na koshi.” Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira
goma wai in bashi canji na ce, “Wai don Allah kai kuwa
a ina kake samun sababbin kudi?” Bai amsa ba yana ta
kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya
girgiza kai, “Ba na amfani da Tsohon kudi.” Na ce,
“Saboda mene?” Bai amsa ba ya ce, “Gobe zan amshi
gyada.” Na ce, “Toh”Ku san kwana 2 ban ga mu2min
ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta ‘yan gayu kamar
kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar
10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka
ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida
su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko?
Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce “Mu ne ai muke kera
su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk
“Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai
kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana
da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro
sabababn dal ‘yan naira ashirin da goma-goma na zaro
idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji
dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce
na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga
sai mana kayan dadi da su nama da mota, su
mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe
shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na
siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa
gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje?
Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi
ina ta kallon shi. Sa’a da Zaituna wadanda muke tafiya
tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce
ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to
in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi
ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun
yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai
yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin
kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa’a suka yu cewa
ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce
min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan
na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su
Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu
mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi,
nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa
gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan
masa tambayoyin da zai gamsar da su.
washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana
sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar
amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada
ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina
ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke
kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya
sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi
da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da
manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi
ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na
kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa
cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai
ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin
ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina
haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa,
dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me?
Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi
dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da
takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda
mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga
kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi
maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda
kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da
in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son
tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to
shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan
kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya?
Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki
nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin
ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin
tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe
ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi
karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na
gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka
fada,yanzun JS1 za ki shiga? “Eh tallar da nake ai kudin
rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina
talla, ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki.
Ya ce “Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son
ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce
musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce,
“Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko
Rediyo? Ya ce, ” Media ki ke so? na ce yawwa, haka
zan zama ‘yar media,yayi murmushi, to ni zan wuce, ina
kayanki? Sai lokacn na tuna da tirena da kudina cikin
ledar gwangwani, na ce to sai gobe. Na tafi ina
waiwayanshi, ina cewa kai,wannan mu2min dan gayu
ne,ga kamshin turare yana yi. Ranar Litinin tsawo naga
ta min,yau kam d murna na iso,na nutsu ban yi wasa
ba,saboda wata zuciyar da ke ce min in ya ki zuwa fa,
ga shi na zo da sabon littafina, ba karamin damuwa
nayi ba da na ga lkcn tafiyarmu yayi ban gan shi ba.
Ina kulle gwangwanaye sai gashi, na ce hr na cire rai,
ya ce ai zan zo, na ciro littafi na ba shi, tare da cewa
wannan takardar ta isa? Ya ce eh, na ce na gode, na
mika mishi gyada tare da cewa na rage mishi ne. Ya ce
ya gode ya tafi. kai, kuruci dangin hauka, nifa
tsakanina da Allah na yarda suke buga kudi. Daga
ranar ban kuma ganin shi ba, Kusan sati 2 hr na soma
tunanin ya gudune da kudina kun ji shirme. Wata ranar
Jumma’a ranar za a yi wa dalibai hutu hr cikin
Makaranta muka shiga muna ta ciniki,mun saida mun
fito sai na hango shi tsaye gurin zaman mu. Da sauri
na isa gurin shi, me bugakudi……
Zaharaddeen shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 1-04
Posted by ANaM Dorayi on 09:56 AM, 10-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
@* NA
Maryam Abdullahi K/Mashi
“Da sauri na isa gurin shi, me buga kudi ina ka tafi na
daina ganinka? Ya ce aikin kudin ki ne ya 6oye ni, na ce
Allahu! Har ina cewa ka gudu. Ya yi dry, na gudu da
kudin ki ki ke zato Na ce eh, nima ina dry. Ya ce kai kina
da bn dry, to ga kudinki,amma muje gidan ku na bawa
iyayenki kada wani ya bi ki ya kwace. Cikin murna na ce
to daga nan ma in sun gan ka sun fi yarda. Na kama
hanya a kafa ya ce ga mota can zo muje, in kin san
hanya direbn mu sai ya kai mu, ba tare da wata shakka
ba na ce to. Sam na manta da su Sa’a, sai da zamu
shiga motar naji muryarsu,suna cewa ke Hafsatu ki ka
sani ko dan yankan kai ne? Na dube shi, shima ya ji
amma sai yayi tamkar bai ji ba, na ce ba wani dan
yankan kai na shiga motar da dan tirena, shima ya shiga
ya ce kawarki fa,shawara suka baki nace tame? Yace
kin san ni ko dan yankan kai ne? Duk da gabana ya fadi
amma sai na dake nace, bakayi kama dasu ba yace suna
da kama ne? Nace oho amma kai bashi bane yace, dama
sunanki hafsatu? Nace eh abakin su sa‘a kaji ko da suka
kirani dazu ko? Yace eh nace yan bakin ciki ne, dan fa
nace masu kana buga kudi sai suka ce mun karya ne, kai
malamin makaran tane. Yace gaske ne ni malamin
makaranta ne, amma daga yau na gama nace, duk da
kudin da kuke bugawa basu ishe ka ba sai kayi koyarwa?
Yayi dariya yace bautar kasa aka turoni daga jahar mu.
Nace bautar kasa kuma? Yace kema watarana zakiyi in
dai kikayi karatun da kike fadi, gwamnati zakiyi wa aiki
na wata tara ko shekara.
Ban gane nufinshi ba amma nace Allah yasa naga
lokacin.
Da gudu na shiga cikin gidan mu ina cewa inna fito kiga
mai buga kudi ya bugo min inna ta saka hijab ta fito tana
cewa ni ban gane wanan shirmen naki ba, ina mai buga
kudin? Wannan yarinya da wautar tsiya kike inna tayi
turus lokacin da tayi arba da rantsatsiyar motar tace
hafsatu aina kika jajibo wadan nan…? Cak! Maganar ta
tsaya lokacin da saurayin ya bude motar ya fito
kyawunshi yasa inna tunain ko aljani na janyo, ta soma
karanta (ayatul kursiyu) zata juya gida na rike mata
hannu. Inna dan Allah ki tsaya mana zo muje gurin su
tace a a hafsatu muje ciki bana tsamanin wadannan
bil‘adama ne nifa nasan banda aljan ke ina kika isa kiga
mai buga kudi, sai dai in jabun kudi. Saurayin yatako har
gaban inna ya dan rusuna ya gaishe ta, ta amsa tana
dan dari dari, nace to wanan ce inna ta sai ka bata
kudina inna tayi ta maza tace samari daga ina? Ni fa ban
fahimci surkulen da yarinyar nan take yi min ba? Yayi
mur mushi ya dube ni jeki kawo min ruwa nasha, da gudu
nayi ciki ban saurari inna ba da takecewa in dibi na baba
yafi sanyi
ina tafiya ya dubi inna yace mama zolayarta nake yi, ni
dan bautar kasa ne an turo ni daga Adamawa state, ina
koyarwa a makaranantar da take zuwa talla. Yawan
wasanta ke burgeni har na shiga sabagarta, sai kuma na
fiskanci cewa tana son karatu amma rashin hali ya hana
hakan. Dan ta fada mun tana talla ne dan kawai ta tara
kudin makaranta. To ni nazo ne in ba damuwa zan
taimaka mata don ni daga yau in sha Allahu na bar
kaduna kenan, don na gama abin da ya kawo ni, dai dai
nan na taho da ruwa na ce masa gashi. Inna tace mika
mashi yace a a dama basha zanyi ba bakiga na sha ruwa
a mota ba? Nace eh yace to maida. Yaci gaba da cewa
dama nawa ne kudin nata? Tace ni ban tambayi nata ba
amma lokacin na wanta inaga dubu uku muka kashe? Ina
ga ba zai wuce hakan ba. Ya ciro yan daurin nera goma
gama guda uku sababbi fil ya mika mata ga wanan
mama dan Allah ku biya mata kudin makaranta, ku cika
burinta har tazama abin alfahari nan gaba. Allah ne kadai
ya san al‘ummar da zasu anfaneta. Innarmu jiki yana bari
ta amshi kudi tana ta zubo mashi godiya ma, sai daka
tsale nake tamkar yarinya karama, ina cewa shi kenan na
huta talla. Innarmu ta harareni tana cewa to kiyi mashi
godiya mana, nace na gode yayi murmushi ya tafi yana
daga mun hannu nima haka. Sai dai kash nayi mantuwa
ban tambayi sunan shi ba, a lokacin ban damu in san
sunan shi ba muka nufi cikin gida da murna innarmu bata
da rufi, don haka a tsakar gida ta fada musu cewa wani
bawan Allah ya taimaka min da kudin makaranta. Wasu
suka taya mu murna ciki harda babarmu, wasu kuwa sun
nuna bakin cikinsu a fili don Ade ina bayi naji tana cewa,
maman abba yau kinji matar nan mu zata rainamawa
hankali ta dai tura yarinyar ta maula. Maman abba tace
ai shegen son kudi irin na maman hafsatu ya isa, ace
mata sai rashin godiya Allah duk fa kokarin mujinta ta
raina. Daga can asabe ta sako baki shi wannan mujin
nata ai tuni ta gama dashi katsinawa kuma da shegen
asiri? Dubi fa fada irin na mutumin nan sai da tasha
karfin shi ga kishiya kuma sai yan da akayi da ita Ade ta
ce, ayi dai mu gani, kina nan yarinyar zata janyo mata
abin kunya, Maman Abba ta ce ta dage sai yarinya tayi
boko, za su ga boko ai. Na fito cikin takaici ina kallon su,
sai nan da nan suka canza mgn. Asabe ce suna ta zagin
ki,wai kina asiri ke Bakatsina,wai zan ja miki abin kunya.
Inna tana da fada, balle in an ta6o ta, ta fita da sauri
Yayana Umar ya hau ni da fada,wai don ubana ni
mahaukaciya ce da zan fada mata, na ce ka ji gulmar da
suke yi ne? Hayaniyarsu ce ta fito da mu, Umar ya je
yana cewa, Inna ta bari ta dawo daki, nan dai haka gidan
kan rikice wani lkcn. Musamman in ana fada kan yara, ko
gulma. Innarmu tana da fada kowa a gidan yana shakkar
ta6o ta. Bayan komai ya lafa, muna daki ta ce “Hafsatu
kin dai ji da kunanki, ina so ki baiwa mara da kunya, ki
kare min mutuncinki, kiyi karatunki ki zama abn sha’awa
da kwatance na ce to Inna. Cikin kwazo na soma
karatuna, kudin dan gayu mai buha kudi ya bugo min sun
taimaka min kwarai. Inna tayi musu kyakykyawan
adani,sun ishe ni har zuwa lkcn da na gama JS 3, lkcn
shekaruna 14 girma ya soma zuwa min ‘yan alamu sun
bayyana. Na kan ji mutane suna cewa, wai ban cika kyau
a fuska ba, sai dai jiki. Yawan fadin ina da diri shi ne ya
sani jin cewa ni mace ce musamman in nayi kwalliya.
Wata safiyar Jumma’ naje fitsari sai naga jini, cikin
fargaba nazo har da hawaye nake fada wa Inna. Ta ce,
Hafsatu girma ne ya kama ki yau nawa ga watan bature?
Na ce 7. Ta ce to duk 7 ga wata za ki ga wannan jinin.
Ta iya yiwuwa yazo kafin 7, ko bayan 7, amma duk wata
dai za ki gan shi. In kuma ba ki gan shi ba hakan na
nufin kina da ciki. “Na zaro ido ta ce ai ba a samun ciki
haka sai in kin kasance me wasan banza da MazaNa
sauke ajiyan zuciya,don nasan bana yi. Na ce ni dama
ba ruwana da maza, ta ce na sani, amma ki kara.sannan
ki kara sa tsoron Allahn ki cikin zcyrki. Daga yau din nan
an bude miki fayil dinki, duk aikin alkairi ki ko akasin
haka za a rubuta miki, don haka sai ki kula, ki kuma san
me ki ke ciki. Tun daga wannan lkcn nasa ma raina
tsoron maza, nake kuma duba duk wani aiki da zan yi
zunubi zai ja min ko lada.
Marubuciyar tace’Yan uwa mata zan dan mana wani tuni
nan gurin, mu nutsur da ‘ya’yanmu muyi musu bayani
mai kyau tare da nutsa tsoron Allah cikn zukatansu, lkcn
da suka samy kan su a irin wannan yanayin na
balaga…..Allah yayimana jagora
Ba zan manta da Jumma’ar ba, misalin 4 da mintina na
yamma gari yayi sanyi La’asar, nayi kwalliyata da riga
da wandon pakistan da Inna ta sai min a gurin wata
mai gwanjo. Kore ne kalar lemun tsami da gyalanshi,
Sakina kanwata yarinyar Baba kishiyar Innarmu ta ce ”
Yaya Hafsatu zan biki.” Na ce, zo muje gidan kanwar
Innarmu zan je Hayin Malam Bello na kai mata kudin
dashin sabulu da suke yi. Ko can gidan matan gidan
suna ta yaba yanda kayan suka yi min kyau.Dai-dai kan
layin Biliya wasu matasan samari suna tsaye jikin
mashin, kallo daya na musu na dauke kaina ban kuma
kawo komai a raina game da su ba. Sai naji takun
tafiya, ana cewa ‘yanmata ji mana,maza sun sha yi min
haka bana tsayawa, don Innarmu ta fada min karatu
basa haduwa da soyayya, kada na sake na kula kowa.
Ya zagayo ta gabana Beby saurare ni mana. Na’ kalli
fuskarshi,sai zcyta ta buga, ina son mu2m mai kyau,
daga ganin shi dan gidan ‘yan gayu ne. Na harde
hannuwana a kirjina, ya sake dubana daga sama kuwa
gsa kasa, “Wow! Ya sunanki?” na ce “Hafsatu.” Ya ce
“Nice name, Hafsy ina ne gidanku?” Kawai sai na samu
kaina da yi masa kwantance, can kasa muke Abuja
Road, layi na shida marar kwalta, kana zuwa layin ka
ce ina ne gidan yawa za a nuna maka. Ya dan yi shiru
don ya fahamice a geto take amma sai yace zan zo
anjima ko gobe zan samu ganinki? Nace eh yace to sai
kin ganni na tafi ina wai wayanshi sakina tace yaya
hafsat mijinki ne? Cikin yar dariya nace eh mijinane
wasa ne ya ruda ni na kasa sukuni, tare da boyiwa
innarmu don kada ta hanani fita, sai dai har tara banji
ance ana kiran hafsa ba,har fita nayi gurin bakin titi ina
tunanin wai ko yazo bai gane layin ba na dawo daf da
zan shiga gida na ganshi tsaye kofar gidan mu. Wani
sanyi naji acikin zuciyata, sai na soma tunanin zan jene
na ce mashi gani ko ko ce mashi zanyi ni kake nema?
Sai na yanke shawarar na bi ta gabanshi, har na daga
labulen buhun da yake kofar gidadanmu zan shiga, sai
naji yace hafsy sai na tsaya tare da sauke a jiyar
zuciya, sannan na wai wayo na tako cikin irin tafiyar da
ban taba sanin na iyata ba. Duk da yake dare ne a kwai
kwan lantarki a kofar gidan, yace nafi minti 5 ina jiranki
nace ina yini? Yace lfy da farko dai sunana munnir jafar
dalibi ne a (A B U) zariya ina shekara ta 2. Sanan
muna zaune ne a nan makarfi road son munnir ya kara
shiga ta, don a rayuwa ta inaso in auri miji dan boko
nace ni kuma na gama js3, yace me ya hanaki cigaba?
yanayin garin ne. Haka muka ta fira sam bansan dare
yayi ba har 10 ta gota ba sai da naji karan raidiyon
baban mu ya nufo gida. Ya tsaya tare da cewa wacece
nan? Ke hafsatu me kikeyi haryanzu? Na dubi munir
nace ga baba na. Ya cire hular kansa hana sallah yace
ina yini baba? Ya dubeshi lfy lau zo ki shige muje, nace
to sai anjuma yace zan zo gobe nace to. Tun kafin
mushiga daki baba yake min fada tare da tambayata
wanene wannan yaron ya dame kugu? Nace dazum ne
muka hadu dashi. Hayaniyar shi ne ta tashi inna daga
dan baccin da ta soma, tana tam bayarshi lfy malam
kake fada da tsohon daran? Yace amma dai ke
sakaryar uwace, 10 ta wuce yarinyarki tana can tana
zance da wani kato ke kuma kin hamgame baki kina
bacci Inna tace hafstu na can tayi baci tuni dakin
babarsu, ba ita kagani ba ita da bata fita zance ma
yace to ga tanan ma bare ki karyata ni. Inna tace hafsa
zance kika fita? Ya mukayi da ke? Baba yace ni dai
tashi ya turo mun iyayensa dama ni burina in aurar da
ita. Inma shi bayi zaiyi ba akwai mutane da dama sun
min magana. Inna tace je ki kwanta itama ta maida kai
ta kwanta alamun zancen baba bai shigeta ba. Da safe
ta tsareni da son jin wajen wa na fita? Nace inna wlh
jiya ne fa da kika aikeni ya ganni shine yazo. Tace
amma nace maki ki fita hanyar samari ko? Kin san
babanki matsawar zaki rinka tsayawa zance kina son
karatun nan zaki barshi ko nace inna naga shi wannan
yana son karatun, don su gidansu yan boko ne. Maman
shi da baban shi duka aikin gwamnati sukeyi yace min
jami‘a yake yi (A B U) zariya tace to ni dai banaso
kurinka tsayawa nace yama ce zai bani kudi nacigaba
da karatu na. Inna tace to indai ko haka ne sai dai
kitafi makarantar kwana, saboda kin san babanku sarai.
Koda munnir yazo washegari, haka na zauna na fada
mashi komai dangane da ma haifina game da kin boko.
Yace taf kice cutarki zaiyi? Tun kina karama zai
kasheki da aure ai gaskiyar innarki ne kada ki yarda.
Nace kudine matsalar mu sai dai in shiga ta kwana
yace haka ne, yace zan baki kudi bari dad dinmu zai
bani kudi in yadawo tafiya. Nayi ta masa godiya yace a
a shidai abinda zanyi mishi kada in saurari kowa kuma
na saki jikina dashi, nace kada yaji komai cikin sati 1
na gama yarda munir na sona, nima kara sonsa nake
duk zuwa yakan zo min da wani abu, turare ko dan
zobe ko dan wani abun kwalama. Bana manta ranar
lahadin da yazo min sallama zai koma makaranta ya
kuma bani kudi naira dubu 20 har kuka nayi mashi dan
bana so rabuwa dashi. Ranar shida abokin sa sukazo
wai shi faisal, kawai sai naji munnir ya rumgume ni,
wani abu naji tun daga tafin kafata har tsakiyar
kaina,shiko sai cewa yake inyi shuru in daina kuka
hannun shi kuma na zaga sassan jiki na, fadan inna ya
fado min cikin rai inda take cewa. In kula da kaina
wasan banza da namiji zai iya sawa in sami ciki, nayi
sauri na janye jiki na daga gareshi, yasa hannu yana
share min hawaye muka yi ban kwana na shiga gida.
Suna tafiya faisal yace munir dagaske kana son
yarinyar an? Munir yace da dai nazo na dan kwashi rabo
nane, sai kuma na gane yariyar ba yar hannu bace.
Sannan kuma nasamu kaina da sonta na gaske faisal
yace ka dai san dadinka ba zai barka ka auri yar geto
ba ko? Yace kai nif zan zaba da kaina ba zan yarda ace
min naje ga yar wani ba. Nikam ina shiga gida muka
soma murna da inna, nan muka shiga tsara yanda
zamuyi wa baba bayanin munir. Washegari inajin inna
tana cewa baba wai kananta da yayansu sunce ta kaini
zasu nemmar min makarantar kwana. Baba yace a a
shifa bai yarda ba, tace yayi hakuri kwana nawane zan
gama? Baba yace nifa ba kin karatun nake ba, nafiso
tayishi a can dakinta inaso kisani har in yarinya ta
soma tsayawa da saurayi mafi kyawu shine ayi mata
aure. Inna tace za ayimata malam, wannan yaro da ka
ganta dashi shene yake son auranta na lura itama tana
sonshi yace to ba sai ya turo magabatan shi ba muyi
zancen manya! Inna tace yo shima ai karatun yake sai
ya gama itama ta gama kafin nan. Shuru yayi bai sake
tankawa ba shurun ba yana nufin ya yarda bane,
shurunsa yana nufin mukarata can shi ba ruwansa.
Kwana 2 tsakani muka shirya ni da inna muka nufi
manunfashi kananta kawu sha‘iabu da kawu bashir
harda wanta kawu kabiru sun sunji dadi sun kuma tsaya
har saida nasamu shiga ss1. Haka baba ya hakura ya
zuba muna ido, na cigaba da karatu cikin nasara da
kwazo, yan gidanmu kam da makota sai gulma da
tsegumi, ba mu damu ba. Fatan inna shine inzama abin
kwatance nan gaba.
A duk lokacin da nazo hutu munnir nazuwa, haka duk
lokacin ziyarar dalibai in yana da sarari yakan zo.
Hidimar karatuna shi yake yinta haka nan duk wani
kaya na yan mata shi ne yake siyan min, wanan shine
yasa na kara sake wa dashi. Matsalata dashi son taba
jiki na, kawai lokacin da wani hawaye yayi min wai in
bishi muje dakin wani abokin shi, niko nace a a muji
tsoron Allah ba don son da nake yiwa munnir ba a tuni
na hakura dashi. Cikin haka na gama karatuna na
secondary. Na dubi likitar idanuna suna zubar da
hawaye nace, anty ko lokacin da na gama karatu na
baba ko gai suwa nayi baya amsawa, kannena yaran
kishiyar mama na guda 2 ya musu aure. Sannan
karatuna kafin na tahoshi sai da ta kai yace in har wani
abu ya biyo baya abakin auran innata, sannan in nemi
uba….. Kuka ya kwace min mai karfi, ina fadin na shiga
ukuna zan kashe auran iyaye da kaina. Munir ya cuceni
fyade yayi min anty ki taimaka ki cere cikin nan. Yan
gidanmu da yan unguwarmu duk dariya zasuyi mana.
Kalo kawai likitar keyi cikin tausayi har nayi kukana mai
isata na gama ba wanda ya bani hakuri. Daga ita har
asabe tace to, ke hafsat ki koma makaranta gobe kizo,
keko asabe ki kwana nan nace anty don Allah nima zan
kwana nan din, ko naje makarantar ba zan iya komai
ba, tace shikenan. Ta mike sannan ta nuna mana wani
daki, ku shiga nan kuyi sallah da komai a ciki. Ba tare
da ta jira amsa ba ta nufi dakin ta, kaiwa da kawowa
kurum take yi. Ta ina zata bullowa wayanan yara? Sam
bazata cire cikin ba, bazata kuma bari suje su cire su
zubar ba. Ta lura Asabe tafi saukin kai don haka da ita
zata fara. Yanda naga rana haka na ga dare, alwaula
kawai nayi na yi nafila. Daga bisani na koma istigifari,
washegari bayan ta lalabemu mun karya, sai ta bamu
wasu magun guna tace kada in damu in koma
makaranta insha, suna da karfi na sati 3 ne, ta tabata
cikin zai fita nayita godiya na komo. Sai da daktar
hindu ta sami shugabar kungiyar kare hakkin bil adama.
Tayi mata bayanin komai game da halin da asabe ke
ciki, Shugabar Hjy Adama ta ce, to za su samu Hjyr
Yasir su fara neman sulhu, in ta ki kuma to za a maka
Yasir a kotu. Doctor Hindu taji dadin haka, don haka ta
tambayi Asabe yaushe aka fi samun Hjy Mairo a gida?
Asabe ta ce Lahadi da rana, sauran ranakun sai dare
ake samunta. Sun same ta cikin Kasaitaccen falonta
tana shan kayan Marmari, suka sanar da ita dalilin
zuwansu. Ta ce, sam ita dai ba danta ba, ai ta ja mata
kunne, nan suka nuna mata cewa zata amsa kira a kotu
gobe Litinin. Yasir na dawowa ta hau shi da fada, ya ce
tayi hakuri sharrin shaidan ne, ta daka mishi tsawa ta
ce, yi min shiru,wawa kawai. Ta tausasa murya a bin
da nake so da kai, za su shigar da mu kara, saura in
mun je ka saki baki ka nuna kai ne, ina so ka bata rai
ka hade fuska ka nuna sam ba ka sam ba ka san
zancen ba. Ni kuma zan tsaya maka, Babanka zai tsaya
maka, domin duk Alkalin garin nan ba wanda zai ketare
bukata mahaifinka. Yasir cikin murna ya ce, “To Hjyta.
A daran ranar ta kira mahaifin Yasir ta shaida mishi
abn da ya faru, wai me aikinta tayo ciki tazo ta ce
Yasir ne, yanzun haka kungiyar kare hakkin dan adam
ta shigo cikin lamarin sun ce za su shigar da kara,Ni
kuma na ce su shigar, ya ce amma ba ki da hankali,
kina fa da masaniyar ina da burin tsayawa takara a
siyasa mai zuwa, ko kin manta? Kin san cewa abokan
gaba za su iya fakewa da wannan su ci zarafina har
suyi nasarar kada ni? Ta ce to yanzun yaya za’ayi? Ya
ce bani Yasir din a waya, ko ba ya kusa? ta ce ba ya
kusa, ka kira layinsa. Yasir ya daga kiran wayar
Mahaifinsa, ko gaisawa ba su yi ba ya jeho masa
tambaya, gaya min gaskiya kai ne kayi cikin? Yayi shiru,
fada min na ce kai ne ka min shiru? Uban ya fada cikin
daga murya. Yasir ya ce “Dad ba zan kara ba,
Mahaifina ya ce, Ok kai ne kenan? Ya ce Tsautsayi ne.
Alhjn yayi shiru yana nazarin abn yi. Can yaja tsaki, in
ka kuma ranka zai 6aci fiye da zatonka. Abn da zan
maka sha mmki, kila ma kayi zaton ko ba ni ne na haife
ka ba. Ya ci gaba da fada. In ma ba iskanci ba duk
nawa ka ke 25 years amma ka iya jarabar mata? Yasir
ya dinga ba wa Mahaifin shi hakuri, Alhjn ya ce shi
kenan, ya kira Hjy Mairo ya ce, kada su shiga kotu, su
nemi sulhu duk yanda aka yi su fada mishi. Washegari
da kanta taje ofishin shugabar kungiyar don neman
sulhu. An kira Dakta Hindu sun zo tare da Asabe,
sharadin 2 suka gindaya wa Hjy Mairo, aka c ta za6i
daya.Na farko ko dai dan nata ya auri yarinyar bayan ta
haihu, na 2 kuma in ba zai aure ta ba, to zai dauki
nauyin cikin tun daga yanzu hr zuwa lkcn da za a haife
shi a yaye shi. Daga bisani su dauke shi. Hjy Mairo ta
nemi saukin Asabe ta rike danta za su ci gaba da mishi
komai,amma shugaba ta ce a’a ba za su yarda ba,
domin Asabe in ta samu miji aure zata yi. Ba zai yiwu
ta tafi da dan wani gidn wani ba. Nan ta take ta kira
mijinta ta mishi bayanin komai, ya ce su dauki za6i na
biyun in yaso zasu yi shawara in ya dawo. Ta ce to.
Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa
hannu Daga nan ta tafi……..
Add Comment