Littafan Hausa Novels

Rayuwata Ce Hausa Novel Complete

Rayuwata Ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAYUWATA CE

 

 

 

*Story & writing by*

*QUEEN AMEERAH*

 

 

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

 

 

*A NEW HEART TOUCHING, LOVE AND SELFISHNESS STORY, FROM YOURS HABIBIYA QUEEN AMEERAH*

 

 

 

 

PAGE 1➡️2

____________”Ochhee” ya fada ya na lumshe ido, da sauri ta juyo ta na ce wa “Hilal lafiya” ciza lips ya yi ya na ce wa “babu komai” harararsa ta yi sannan ta gyara towel dinta ta shiga toilet, ya bita da kallo ya na sauke numfashi.

 

Leelah ce ta bude kofar dakin ta shigo ta kama kugu tana kallon Hilal, cikin fada ta ce “ina Moofeey” ba tare daya kalleta ba ya nuna mata toilet, ta daga murya ta na ce wa “wallahi Moofeey na gaji da jiranki tafiya zanyi na barku” daga cikin toilet din ta bata amsa da ce wa “please Leelah karki tafi” Leelah taja tsaki ta ce “na baki ten minutes ko ki sameni a can” ta juya ta fita ta na mita, Hilal ya bita da harara ya na ce wa “uwar fada”

Cikin sauri2 ta fito daga toilet din, ta kalli Hilal da ya ke mike saman gado, ta ce “yanzu Hilal baka fito min da kayan da zan saka ba?” Mikewa ya yi ya na ce wa “ay ke ce kika tafi kika barni da shock” murmushi ta yi ta ce “in dai ni ce ka hadu da shock” ta zauna gaban dressing mirror ta na shafawa shining skin dinta lotion, shi kuma ya bude wardrobe ya na fito mata da kaya.

 

A cikin sauri take gyara dogon gashinta saboda Leelah, Hilal ya matso ya karbi comb din hannunta ya na ce wa “Besty ki yi komai a hankali in dai saboda wannan uwar fadan ce ay mun san hanya” murmushi ta yi ta ce “Besty ay Leelah is my chewing gum” Hilal ya bata rai ya ce “ni kuma fa?” “You are my chocolatey” ta fada ta na bashi kiss ta mirror.

Hilal ya yi mata style mai kyau da gashinta ya yi dropping dinshi a tsakiya kasancewar gashin mai santsi ne sai ya yi squeezing a gefen fuskarta, ya saka white gel ya kwantar dashi.

Hakan yasa ya yi mutukar kyau. Moofeey ta yi murmushi ta ce “thanks my besty,” shi ma murmushi ya yi ya na kallon yanda ta yi masifar kyau mussamman cute lips dinta da suke shining din lip gloss, ya matso daf da ita ya bata light kiss akan lips, ta daki kafadarsa ta na tashi daga gaban mirror ta nufi inda ya ajiye mata kayan da zata saka, inner wears din ta fara dubawa ta kalli Hilal daya tsareta da ido ta juya masa baya, tana cikin saka hock din Brezier taji shi a daf da ita, ba tare data juyo ba ta ce “what’s” ya ce tayaki fa zanyi, no need” ta fada cikin golden voice dinta, Sai data gama saka komai ta juya ta kalleshi ya na tsaye ya na kallonta, harararsa ta yi ta cigaba da shiryawa,

Sosai ta yi kyau cikin crazy trouser, onion colour wanda kadan ya wuce gwuiwar ta ya kamata sosai ya fito da shape bom dinta, sai riga t-shirt cotton a gabanta an rubuta HAPPY BIRTHDAY SAUBAN,

ta saka silly gold din sarka doguwa har kirjinta, kafarta sanye leg race da takalmi hill, ta sanya p cap an rubuta MOOFEEY a jiki.

ta yi wani shegen kyau sai tashin kamshi take mai dadi duk in da ta juya boos dinta ne suke juyawa,

A’indo Tantagaryar Yar Aiki Hausa Novel Complete

Ta yi wani fari da ido ta kalli Hilal ta ce “idan ka gama kallona sai ka same ni a falo ina jiranka” ta bude kofa ta fita ta barshi tsaye ya na binta da kallo.

 

A falo ta sami Leelah zaune akan kujera ta na danna I phone, ita ma ta yi kyau sosai ta na sanye da riga irinta moofeey da trouser baki ita ma a jikin p cap dinta an rubuta LEELAH, Moofeey ta yi hugging dinta ta na ce wa “my chewing gum” Leelah ta yi dariya ta ce “kin yi kyau my chocolatey”.

 

Hilal ya fito daga dakin ya na rike da karamar jakar Moofeey, shi ma ya na sanye da rigar birthday din sai dai bai sanya p cap ba sai wani shegen aski da ya ke kansa.

 

“Ohh besty ka fito min da phone’s dina” Moofeey ta fada ta na kallonsa, ba tare da ya yi magana ba ya mika mata jakarta, Leelah ta hararashi ta ce ya na abu kamar wani king, ita ma bai kula taba ya yi hanyar fita daga falon suma suka bi bayan sa, kana kallon su kaga stubborn children😁.

 

Suka fito parking space suka zabi motar da zasu fita da ita mai shegen kyau da tsada.

Leelah ce take driving, Hilal yana kusa da ita sai Moofeey a baya, a over speed ta figi motar suka fice gidan.

 

Basu tsaya ko ina ba sai cikin hotel din, ba tare da bata lokaci ba suka nufi hall din birthday tun kan su karasa Leelah ta fara rawa sa bo da irin kidan da yake tashi, Hilal ya kalleta ya ce “please karki zubar mana class ko kallonsa ba ta yi ba ta cigaba da rawarta, suna shiga ciki wurin ya kaure da ihun ganinsu, Sauban birthday boy ya taso ya yi hugging dinsu ya na ce wa “welcome my guys” ya yi wata shegiyar shiga gashin kansa ya koma kalar blue, sannan suka karasa high table wurin zamansu, suna zama Moofeey ta dauki shisha ta fara busawa cikin nishadi.______

 

Your comments is my confidence

 

SHARE

 

 

*WRITING BY.

*QUEEN AMEERAH*

RAYUWATA CE

 

 

 

 

 

BY

*QUEEN AMEERAH*

 

 

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION

{R.S.W.A}

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

 

*A NEW HEART TOUCHING, LOVE AND SELFISHNESS STORY, FROM YOURS HABIBIYAQUEEN AMEERAH*

 

 

PAGE 3➡️4

____________Hilal ya zubawa Moofeey ido ya na kallon yadda take busa shisha ta na lumshe ido, murmushi ta yi wanda ya nuna beauty point dinta ta shafa fuskar Hilal ta ce “Besty kallon fa?” ya ja mumfashi ya ce “karfa kisha abun nan da yawa ki kasa tafiya” dariya Moofeey ta yi ta dauki glass cup din gabanta wanda ya ke dauke da juice ta yi mixing dinshi da syrup kurba ta yi kadan sannan ta mikawa Hilal, karba ya yi ya na kallon kyakkyawar fuskarta sannan ya shanye duka ya mika mata cup din, haka ta ringa zuba masa ya na shanyewa sai da ya gaji ya rike hannunta ya ce “ki barni haka please” 6ata rai ta yi ta na turo lips, murmushi ya saki ya yi kissing din lips din nata, ita ma murmushin ta yi tana juya masa sexy eyes dinta.

Leelah kuwa ta na tsakiyar hall tana rawa idan kaga yadda ta ke juya jikinta sai ka ce “yar” Naira Marley, friends kuwa sai zuba mata kudi suke kamar abin banza.

 

Wata classy girl ce fara doguwa mai kyau ta karaso wajen Moofeey da fara’arta ta zauna kusa da ita ta na ce wa, “sunana Zully tunda na zo wurin nan naga kin burgeni, dan Allah ina so ki zama kawata” wani murmushi Moofeey ta yi ta na lumshe sexy eyes dinta da suka fara buguwa, ta ce “karki damu sunana Moofeey, wannan shi ne babban abokina sunanshi Hilal,” Hilal ya dago ya hararari Moofeey. Ita kuwa Zully zuba masa ido ta yi ta na ce wa “woow shi ma ya na da kyau kamar kee gaskiya naji dadin haduwa daku”, murmushi Moofeey ta yi ta na mika mata cup din mix juice ta karba ta fara sha ta na ce wa “ni ina garin Kaduna ne Babana shi ne mataimakin Commissioner of police ina fatan ke ma a Kaduna ki ke?, shegen murmushi Moofeey ta yi ta ce “ay ni ina ko ina ma” da mamaki Zully ta kalleta ta ce “ban gane me ki ke nufi?” Moofeey ta yi dariya ta na kallon Hilal da shi ma ita yake kallo sannan ta ce “zaki gane idan kina tare dani,” murmushi Zully ta yi ta ce “na fuskanci tafiyarmu dake za ta yi dadi na yi farin cikin haduwa dake,” Moofeey ta ciza lips ta ce “gaskiya ne kanki ya na kawo wuta” Hilal ya mike ya na ce wa “Besty ina zuwa” Moofeey ta ce “okay dear” hira sosai Zully take yi wa Moofeey, ita kuwa sai da ta bata amsa a dunkule ko ta yi murmushi, Zully ta kusanci Lpy qalau Moofeey irin mutanan ne da ba’a gane kansu, hakan ya sa ta yi shiru kawai ta na kallon yadda take busa hayaki cikin kwarewa.

BIRTHDAY BOY ne ya zo wurinsu ya na ce wa “Moofeey biggirl kina enjoying” murmushi ta yi ta na juya eyes, Sauban ya ce “ya kamata ki taso mu yi pictures gasu Mubeen suna ta cigiyarki” ta ce “okay” ta na kallon Zully suka mike a tare.

 

Sosai suka ringa zuba pics da video, friends kowa ya na so ya yi hoto da Moofeey, after that Sauban ya yanka cake nan take wurin ya kara cika da music, lady’s and mens are busy romancing.

Sai a lakocin Moofeey ta tuna da Hilal dan ta lura baya wurin, duk da ta na cikin maye don da kyar take iya bude ido, Leelah ta fara nema tana can tsakiyar friends dinsu Moofeey ta ja hannunta ta na ce wa “ina Hilal?” Leelah ta ce “ba kuna tare dashi ba?” tsaki Moofeey ta yi sannan ta nufi hanyar fita daga hall din.

Tafiya ta ke a hankali idanuwanta a rufe da kyar take ganin gabanta a haka ta nufi garden din hotel din duk da dare ne akwai wadataccen haske a ko ina, ji ta yi an janyo hannunta ta fada jikin mutum, ajiyar zuciya ta sauke a hankali furta “Hilal” sa bo da kamshinsa da taji, ya kalli fuskarta ya ce “me ki ka fito yi?” ta bude idonta da kyar ta kalleshi ta ce “kai na ke nema” ta janye jikinta daga nashi ya yi murmushi ya na kokarin boye bottle din hannunsa karaf idonta yakai kai, kallonsa ta yi tana hade fuska, ya sunkuyar da kansa kasa, cikin fada ta ce “Hilal bana hanaka sha ba?” besty kiyi haƙuri ya fada yana kamo hannunta, ta fizge hannunta tana kokarin barin wajen, ya yi sauri ya rumgume ta yayi kasa da murya yana fadin Besty kar kiyi fushi dani, ta kalli cikin idonsa ta ce “Hilal na hanaka shan alcohol is haram” shi ma tsakiyar idonta yake kallo ya na mamakin halayyarta ita tana aikata laifi amma tana kokarin ganin ta hana wani sabawa Ubangiji, Besty inshaallh bazan kara ba ya fada kamar xaiyi mata kuka, murmushi ta yi, ta ce “promise”, ya mayar mata da murmushin yana kallon lips dinta, sai a lokacin ta raba jikinta da nashi tana harararsa, hannunta ya ruko yana ce wa ya kamata mu tafi gida Besty barci nake ji tunda kin hanani abinda nake so, murmushi ta yi ta daki kafadarsa tace kwana fa zamu yi, ya zaro ido yace please muje mu janyo Leelah mu tafi don kema yau kin jiku da yawa, lumshe ido tayi tace hakanma ban koshi ba, suna rike da hannun juna suka koma cikin hall din da kyar hilal ya janyo Leelah wacce take tikar uban rawa, haka ya cillata cikin mota ta na yi masa bala’i, ita ma Moofeey sai dauko ta ya yi don tafiyar ma ta kasa yi duk jikinta ya saki, wannan karon Hilal ne ya yi driving dinsu zuwa gida.

Ya na parking ya bude ya fito ya cillawa Leelah key din ya dauko moofeey kamar wata baby ya nufi cikin gida Leelah ta biyo bayansa tana zuba masa masifa, bai kulata ba direct dakin Moofeey ya yi ya kwantar da ita saman bed idonta yana rufe sai motsa baki take tana magana kasa kasa, yaja blanket ya rufe ta sannan ya bata kiss a koshi, ya fito daga dakin ya janyo mata kofa, ya na fitowa falo suka ci karo da Affan ya na shigowa da trolley dinsa, suka rumgume juna cikin farin ciki, Hilal ya ce dama yau zaka dawo, Affan yace na gaji duk na yi missing dinku, Hilal ya ce mu ma yanzu muka dawo daga BIRTHDAY

Leelah ce ta fito daga dakinta da gudu ta rumgume Affan, dariya Affan yayi ya na ce wa ina Moofeey, Hilal ya yi saurin ce wa ta yi barci, Leelah ta harareshi taja hannun Affan suka shiga dakin Moofeey, ta na kwance yanda Hilal ya barta tana ta motsa baki, Affan yayi murmushi ya ce Moofeey ta yi over ke nan, Leelah tace hmmmmmn kasan halin ay, please ku barta ta huta Hilal ya fada ya na tsaye jikin kofa, Affan yaja hannun Leelah suka fito ya na ce wa “sorry Besty” Hilal ya rufo mata kofa.

Suna fitowa Affan ya yi dakinsa don ya samu ya huta, ita ma Leelah ta yi nata dakin, Hilal ya rage shi kadai zaune a falo ya na tunanin abinda ya ke kasan zuciyarsa ya na tsoron ya bayyana shi._________

 

 

*YOUR COMMENTS IS MY CONFIDENCE❤️❤️*

 

 

*SHARE🙏🏻*

 

 

*WRITING BY…

*QUEEN AMEERAH*

RAYUWATAH CE

 

*BY*

*QUEEN AMEERAH*

 

 

 

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

*Ina jin dadin comments dinku fans Allah ya bar qauna*

 

 

 

 

PAGE 5➡️6

____________sosai yayi nisa cikin dogon tunani, tabbas ya dade da gasgata cewa zuciyarsa ta dade kamuwa da matsananciyar soyayyar moofeey Kullum kaunarta kara ratsa jiki da jijiyoyin sa take, a kowanne numfashi da yake shaka soyayyar tace take kara mamaye zuciyarsa , Kullum fargabarsa daya ce “moofeey zata yarda da soyayyarsa”, yafi kowa sanin halayyar moofeey bata da alkibla guda daya bazaka taba gane inda ta nufa ba, tana gudanar da alamuranta ne lullebe ta yanda ita kadaice tasan mai take nufi, yarinyace ita mai mugun wayo da kaifin basira, wannan abu shine yake damun zuciyar hilal gashi Kullum kara nisa yake a cikin soyayyarta.

Haka hilal ya ringa tunani bai bar falon ba sai wajen karfe daya na dare sannan ya nufi bedroom din shi ya kwanta.

 

Bangaren moofeey kuwa tana cikin maye haka barci ya dauke ta, bata samu ta farka ba sai chan tsakiyar dare, duk jikin ta yayi weak haka ta tashi da kyar ta nufi toilet, wanka ta farayi sannan ta dauro alwala ta fito ta zuro doguwar riga da hijab, ta hau kan clean praymat dinta cikin nutsuwa kamar ba ita ba ta gabatar da Sallahr magrib da isha’i, da bata yisu ba, sannan ta fara nafila ta dau lokaci tana sallar kafin ta zauna ta fara tasbihi, bata koma barchi ba har akai sallar asuba rakatanul fajhr ta fara yi sannan sallar asuba tayi addu`ointa data saba,

Sannan ta tashi tana mika ta cire hijab din,ta nufi frige ta dauki fresh milk mai sanyi ta zauna akan stool tana sha a hankali tana lumshe ido, bata wani sha mai yawa ba ta ajiye, side drower ta bude ta dauko wasu tablet ta balli guda biyu tasha, sannan ta haye saman bed few minutes wani mugun barci ya dauke ta.

Karfe 9:30am Affan ya fito falo yayi kyau cikin kananan kaya Kasancewar sa black beauty ga kuma hutu da jin dadi da suka ratsa shi, falon yayi shiru babu motsin komai sai kamshin airfreshner koina kal kal dashi, ya zauna a kan daya daga cikin kujerun falon yana latsa waya,number da yayiwa saving da ihsaan ya kira video call, kiran bai dade yana ringing ba aka dauka, daga chan bangaren wata kyaukkyawar budurwa ce tayi murmushi tana kallon Affan, shima murmushin yayi yace baby ihsaan ya kike, ina lafiya amma nayi missing dinku ta fada tana dariya, Affan yayi murmushi yana kallonta, tace ina patners da sweet hilal fatan duk kuna lafiya, Affan yace duk muna lafiya nima jiya na dawo daga canada naje duba dadd dina, ihsaan tace okay nima gobe ko jibi nake so na dawo duk na gaji wallahi, wasu kudi nake jira ne, Affan yace money hunger, tayi dariya tace kowa ma yana son kudi, yace amma ke naki na dabanne.

Dai dai lokacin Leelah ta fito daga bedroom dinta cikin short gown tana gyara gashinta tayi kyau sosai, ta nufi Affan tana cewa dawa kake wayene kake ta dariya, ya dago da kansa ya kalleta yace ihsaan ce, da sauri ta karasa kusa dashi ta zauna ta karbi wayar, dariya suka saki a tare da ihsaan, Leelah tace patner naga kinyi kumatu, ihsaan ta shafa fuskarta tace ba dole kiga na chanja ba Kullum ina wanka da fresh milk, Leelah tayi murmushi tace Ohh ihsan harka babu wasa, ihsan tayi dariya tace ina sweet hilal, Leelah taja tsaki tace ay kina da number sa, ihsaan tace please kuna kulawa dashi, Leelah ta harareta tace wannan sai dai moofeey, murmushi ihsaan tayi tace karki damu ay na kusa dawowa,

Hira suka cigaba dayi sosai har sanda Affan ya karbi wayarsa sannan suka yi sallama,

Leelah ta kalli Affan tace ka tura min 50k a account dina anjima zamu je saloon da chewing gum, Affan yace 50k kawai ya isa, it’s okay ta fada ta tashi ta nufi dining area Affan yabi bayanta, suka zauna Leelah tayi serving dinsu da tosted salad Irish da hot milky coffee, suna cikin breakfast hilal ya fito yayi wani mugun kyau cikin short niker da armless kirar jikinsa ta fito as cikakken jarumin namiji and handsome he’s, duk da shegen askin da yake kansa hakan ya bayyana kyakkyawar oval face dinshi, purewhite din eyes dinshi masu kyan kallo zuwa dogon hancinsa ga kuma shape lips masu taushi da kalar brown akan skin dinshi mai dan haske, hilal first class ne a kyawawan maza, ya hadu over,

Ya karasa dining area Affan ya mike yayi hugging dinsa sukayi shaking hand kowa yana murmushi sannan ya zauna kusa da Leelah, ta dago ta kalleshi suka hada ido ya daga mata gira yana hada rai, ta dan harareshi tace you looks beauty, thanks yace ya dauki tea din gabanta ya kurba , zata fara masifa Affan ya roko hannunta ya mika mata nashi, karba tayi tana harararsa.

Affan yace aboki how’s your night,murmushi hilal yayi yace fine ya gajiyar ka, gajiya ay ta wuce Affan ya fada yana kokarin hada wani tea din.

Hilal ya mike da cup din tea din a hannunsa ya nufi dakin moofeey,carefully ya bude kofar ya shiga ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yayi tozali kyakkyawar fuskarta tana barchi, zama yayi a gefenta yana shakar kamshinta mai dadi ya zubawa fuskarta ido yana kallon yadda take barchi cikin kwanciyar hankali, lips dinsa yakai saman koshinta ya bata light kiss a hankali ya furta love you more, yana jin wani irin sonta yana fisgar zuciyarsa.

Haka ya zauna yana kallon duk wani motsi nata har sanda lokacin tashinta yayi wato karfe 12:00pm, tana bude idonta suka sauka kan fuskarsa yana kallonta, wani perfect smile ta sakar masa, lumshe idonsa yayi ya bude su still akan fuskarta, cikin golden voice dinta ta furta “hilal” yanda ta kira sunansa har cikin jininsa yaji, janyo ta yayi jikinsa yana sauke numfashi lips dinsa yakai saman nata ya fara kissing dinta, hannu biyu tasa a saman faffadan kirjinsa ta ture shi gefe, kwantar da kansa yayi saman pillow yana maida numfashi, ita kuma mikewa tayi daga kan gadon tana harararsa, rigar jikinta ta fara cirewa tana fadin ka daina yunkurin rage filings dinka a kaina hilal, yana jinta yayi shiru don bazai iya magana ba, ita kuwa towel ta daura ta shige toilet tana tunanin wane mataki zata dauka akan bestyn nata.

Koda ta fito yana kwance yanda ta barshi kamar mea barci, ta dauke kanta daga kallon shi ta fara gyara jikinta, ta shirya cikin wando 3quater da half cotton shirt, ta daure gashinta a tsakiya, tayi wani fitinannen kyau,

Zama tayi saman sofa ta dauko jakarta ta fito wayoyinta tana dubawa tana almost 30 missedcalls, data ta bude nan ma tana da sakonni kala kala a both chats din da take yi, babu wanda tayi wa reply ta zuro wayoyin cikin pocket dinta, tana dago kai suka hada ido da hilal ya lumshe nashi idon yana ciza lips, ita kuwa kallonsa kawai takeyi ta dade da sanin hilal yana matukar sonta amma yanzu abin nashi ya fara nisa dole tasan abin yi, don soyayyarta a gareshi zata iya cutar dashi, wani shegen murmushi tayi tana jin tausayin hilal don zuciyarsa bata masa adalci ba.

Tashi tayi ta dawo kusa dashi ta kwantar da kanta a kirjin shi tana jin yadda zuciyarsa take bugawa, murmushi tayi cikin golden voice dinta tace my besty, uhmmmmmn ya furta chan kasan makoshi, besty muje muyi breakfast yunwa nake ji nasan kaima baka ci komai ba ta fada cikin shagwaba, hilal ko motsi ma kasawa yayi, moofeey ta dada shigewa jikinsa tana murza tafin hannunsa, tana kiran sunansa a hankali, da kyar ya bude idonsa da suka chanja launi ya kalleta, itama kallonsa tayi tana juya sexy eyes dinta cikin salo mai rikita zuciya, ya shafi fuskarta yana matso da lips dinsa kan nata, zamewa tayi daga jikinsa tana dariya ta fice daga dakin tana juya masa hips cikin salon mugunta,

Dafe kansa hilal yayi yana sauke numfashi ya gane moofeey tana sane take masa abubuwa yana fatan itama ta kamu da irin son da yake mata,

Moofeey na fitowa falo taga Affan tare Leelah suna kallon series, cikin murna tayi hugging din Affan tana cewa Yaushe ka dawo, shima cikin farin ciki yace jiya na dawo lokacin kinyi over kina flight a sama, murmushi tayi tace welcome Affan munyi missing dinka, missing you too ya fada yana dariya,

My chewing gum Leelah ta fada, moofeey ta juya gareta ta bata side hug suka sakarwa juna murmushi,

Dining area ta nufa tana kiran hilal zama tayi ta janyo pleate ta fara zuba musu abinci, hilal ya karaso ya zauna kusa da ita,haka suka yi nasu breakfast din.

 

Leelah tare da moofeey suka fito harabar gidan ta daura top a jikinta, sai ta kara kyau, Leelah kam still gown ne a jikinta, moofeey itace take driving dinsu zuwa saloon gallery din, bayan sunyi parking suka fito dai dai lokacin wani hadadden guy ya fito daga motarsa ya nufe su yana kallon moofeey, yace please lady’s na dade ina binku ki bani ten minutes to introduce my self, ko kallonsa moofeey bata yi ba suka wuce suka barshi tsaye,

Akwai sanayya tsakaninsu da salooner din cikin girmamawa aka karbe su,

Sosai suka kara kyau bayan an gama musu musammam moofeey ta kara zama classy dama ko bata yi hairstyles ba gashinta mai kyau ne,

Wata messenger ta kawo wa moofeey sako a envelope tace wani ne yace a bata, karba tayi kawai ba tare data duba ba,

Sai a hanyarsu ta komawa gida Leelah tana driving moofeey tana kusa da ita ta bude envelope din tana budewa kudi a ciki 1million naira da short note kamar haka “you refused to give me chance beauty, manage this for your saloon bill” sai kuma compliments card dinsa, tabe baki moofeey tayi bayan ta gama dubawa ta saka kudin cikin jakarta, note din da card kuma ta yaga su ta watsar ta window.

Leelah ta bita da kallo tana mamaki halin moofeey._________

 

 

*YOUR COMMENTS IS MY CONFIDENCE*

 

 

*SHARE*

 

 

 

 

 

*WRITING BY*

*QUEEN AMEERAH*

Add Comment

Click here to post a comment