Nazlah Hausa Novel Complete
NAZLAH
*DAGA ALƘALAMIN*
SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️
*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHENSHI, SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF), WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YARDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI’ARKI, YA KUMA KARA RUFA MIKI ASIRI, DUNIYA DA LAHEERA*
ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
(DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI,YAH RAB YARDA NA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA, ALLAH KASA NA KARESHI LAFIYA, ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR’ANI)
*PAGE 1-2*
Tafe nake cikin wata Unguwa mai suna Barhim Wanda Unguwar Qauters ce,hakan yasa Unguwar bata da wata hayani ko ina tsiiit kasantuwarta na Unguwar masu kuɗi, duk in da zaka jiyo sauti to sautin karene, cikin natsuwata nake tafiya, har na ƙaraso gurin wani katafaran gida mai kyau da fasali, hayani yaji, hakan yasa na karasa jikin gidan, tura kofar nayi, jin babu wani abunda ya tokare kofar alamar gidan ba kulle yake ba yasa na tura na shiga, kofar palon da na gani bude na tunkara gadan-gadan, hayaniya najiyo hakan yasa na dan kara tsawon tafiyata,………
.
Hamshakiyar Uwa Hausa Novel Complete
ina shiga naji ana burutun, da gudu duf-duf-duf, da sauri nabi inda nakejin sautin gudun,saman benen gidan na hau, kai tsaye dakin na nufa , cikin daga sauti naji tana cewa “Wallahi Hamid baka isa ka kusance ni ba, sai ka bani kuɗin da na fada maka, in ba haka ba kuwa sai dai kayi hakuri da buƙatar ka”, ta fada tana tulla mishi harara…………….
Dara-daran idanunwanshi farare tas-tas masu kyan fasali da girma, ya kara buɗewa tare da cewa “yanzu ke Sadiyya dan zan anshi haƙƙina shine zaki ce sai na biyaki kuɗi, mai yasa ke kwata-kwata baki da tsoron Allah, Sadaki fa na biya aka Auramin ke bawai zaman Dadiro mukeyi da ke ba da zakice sai na biya kuɗi zan kusanceki,” ya fada yana kara daura mata rinannun idanunshi akan fuskarta………….
Jijjiga jikinta tayi, tare da cewa “Ai Wallahi bari na fada maka ka gama kusantata ba tare da ka biya kuɗi ba, kama daina yimin wani wa’azi domin tanan yake shiga yana fita tanan”, ta fada tana nuna kunnuwanta………….
Mararshi da take mishi Azababban ciwon ya dafe, tare da cewa “yanzu haka kika zaɓarwa kanki, tunda hakane, nawa kike bukata yanzun ?”, ya fada idanunshi na tara hawaye ……………
Wani murnushi ta saki tare da cewa, “Nairah Dubu dari biyar kachal nake bukata”, ta fada tana wani ƙas-ƙas da Chewing-gum din da yake bakinta, wayarshi ya dauka, ya fara latsawa kallonshi ya yi tare da cewa “Na tura miki”, yatsina fuska tayu tare da cewa “Ni banji Alert ba”, ta fada tana tura dan kwalinta gaban goshinta…………….
“Ai kinsan bazance na tura miki ba Alhalin ban tura ba”, ya fada ranshi na dan ɓaci, ƙas tayi tare da cewa “na sani ko karya zaka fara min”, ta fada tana wani yatsina, a harzuƙe ya mike ya nufota, ganin ya nufota gadan-gadan yasa ta zura da gudu ta fita a bedroom din, wani bedroom na kusa da wannan ta shige tare da sanya key, dukan kofar ya farayi, muryarshi a dishe yake cewa “ki sani zaki kwana a cikin fushin Allah da Mala’ikunsa, kin hanani Haƙƙina sai da na baki kuɗi, na baki kuɗin kuma zaki gujeni, ki sani haƙƙina bazai barki ba, ki bude Sadiyya, ko kinfi son naje na fadawa halaka”, ya fada yana kara dukan ƙofar………
Daga chan cikin ɗakin taɓe baki tayi tare da cewa “Sai fa kayi ta yi, dan Wallahi bazan bude ba, kuma kuɗi ma yanzu na fara ƙarɓa”, ta fada tana daukar wayarta, latsawa ta fara yi, tana ji yana dukan kofar amma tayi burus dashi……………
Sai da ya gaji da dukan Kofar , kafin ya koma bedroom din da ya fito, yana jaan ƙafafunshi, yana shiga mata kofa ya nufa, budewa ya yi, haɗaɗan bathroom ne ya bayyana, fadawa ciki ya yi, tare da sakarwa kanshi ruwan sanyi, dukan kashin ruwan ya ci gaba dayi, yana tsaye ko motsi baiyi ba, ya dade sosai a haka,kafin ya fito jikinshi na ɗigar da ruwa, bai damu da ya goge ruwan ba, ya fada kan gado, yana sauke wani numfashi mai zafin gaske, cike da ƙunar rai………………
Dayan Ɗakin kuwa, gyara kwanciyarta tayi, jin ya daina buga kofar yasa, tayi kiran waya minutes kaɗan aka dauka, shewa tayi tare da cewa “Ahaayeeeee Naanaye, “murmushi akayi daga chan kafin wata muryar daban ta dakin dodon kunnena, cikin dariya tace “Duniya taki Kawata bani nasha yau kuma da wace kikazo”, ta fada cikin sigar Ƙawaye masu kai mutum ga halaka……………..
dariya tayi tare da cewa, “Ahhaf in da nake sonki kennan , ke da na kiraki kinsan da wata siga nazo miki da ita”, “Uhmmm ai sai dai na fadawa wani halinki amma badai a fada min ba, yanzu dai bani nasha” ,,dariya ta kara saki tare da cewa “ai ban baki labari ba yanzun nan mutuminki ya turamin #5000k kuma na gudu na kyaleshi da abunshi, ai daga yanzu na gama yarda ya kusance ni sai ya bani cash, cash dib ma in naga dama ko ya bani na gudu”, ta fada tana wani juya kwanciya daga in da take……………
Dariya ta sheƙe da ita tare da cewa “Kai wannan abun yamin Suga, kici gaba da gasa mishi aya a hannu, bamce ki bashi ba sai kin gama lale dan Iska, ke ko dattin Aljihu bance ki barshi dashi ba”,ta fada cikin maganar mata yan duniya,wanda suka san takan tsiya, dariya tayi tare da cewa “ai dadina dake kina da man kai, yo dama ta ina zan yarda ai ko zan yarda sai na tabbatar da ba samu rabona”, haka suka ci gaba da surutansu wanda basu da kai balle gindi, sai shawarwarin banza take bata, ita kuwa sai dariya take tana kara hawa kan motar ƙaiƙai……………..
Cikin mugun yanayin nan ya kwana, yana murkususu, sai yanzu yake nadamar Auren Sadiyya da ya yi, gashi bata mishi komai,,ko bakutarshi in yazo da ita bata sauke mishi, gashi a rayuwarshi bashi da tsarin yin Aure-Aure balle saki……………
*WASHE GARI*
Tun Asuba bai koma bacci ba, dan yana dawowa daga Masallaci gurin motsa jiki ya nufa, motsa jikinshi ya fara yi, kusan 2 hours yana abu daya, kafin ya nufi cikin gidan tana share zufar da take yanko mishi, zaune ya tarar da ita a palo, ta chaɓa Ado cikin wani tsantsareran lass mai kyan gaske, ba wata babba bace dan ba zata wuce 19 to 20 years ba, ba laifi tana da dan kyanta dai-dai gargwado……………
kallonshi nayi shima din dai ba zai wuce 27 to 28 ba sai dai yana da garin jiki sosai, dan in ba fada maka akayi ba bazaka taɓa dauka Asalin shekarunshi ba kennan, saboda yana da babban jiki, yana da tsawo sosai gashi da ƙiba sai dai ba irin ƙiba ba sosai dai-dai misali dan ba za’a kirashi mai ƙiba sosai ba sannan ba za’a kirashi ramamme ba, tsaka tsakiya ne, sai dai Allah ya zuba kyau ,dan kallo daya zaka mishi kasan cewa shi cikakken Bafulatani ne, dan fari ne tas yana da matsakaicin baki mai dauke da ƙananan lips masu dan kauri kaɗan , dogon hancinshi har baka, idanunshi dara-dara fsrare tar sai golden Eyes ball da yake da shi, gashin girarshi da na idanunshi gazar-gazar gwanin kyau , Fatabaraqallahu Ahsanun qalikin ,Masha Allah , na furta dan ya haɗu iya haduwa yakai karshe a gurin kyau…………..
yana karasowa cikin palon tace “Good morning My Solder”, ta fada tana dan mishi murmushi, wani kill smile ya saki tare da cewa “Morning how are you ?”, “Alhamdulillah”, jinjina kanshi ya yi tare da cewa “Good”, yana fadar haka ya hayewarshi sama……………
Tana mugun Mamaki da shi duk abinda zata mishi vaya yin fushi, ko ya yi ina saurin saukowa da wuri, wayarta ta dauka da sauri ta danna kira , ring biyu aka dauka , daga chan ɓangaten aka ce “Ya akayi ne Ƙawata”, dariya tayi tare da cewa, da dauri ta dakatar da ita tare da cewa “Yanzu My Solder ya dawo daga motsa jiki”, dariya tayi tare da cewa, “ya akayi kikasan haka zan fada ?”,,dariya tayi tare da cewa “Sharw kawai yanzu ya akayi, mai kika girka na aiko na Ansa”,,dariya tayi tare da cewa, “Wallahi Doya da kwai kawai ba soya, ganinan ma zuwa gidan baasai kin aiko ba”, ta fada tana kike…………….
Mayafinta kawai taja , sai da ta shiga kitchen ta haɗo kan komai kafin ta fice , abunta dan ko tambayarshi batayi ba………..
Yana shiga Wanka ya fads bathroom ya yi, yana fitowa yaji wayarshi na ringa, da sauri ya matsa gurin Wayar *Hajiya* ya gani rubuce akan screen din wayarshi, kashe kiran ya yi, tare da kira back, sai da ya ɗuƙar da kanshi Ƙasa kafin yace “Ina Kwana Hajiyata” murmushi tayi tare da cewa, “Alhamdulillahi Auta , wai nace kayi sauri kar dare ya mana a hanya, dan kasan bana son dare a hanya ko kaɗan”, ta fada cikin so da kaunar Ɗan nata……………
Jinjina kanshi ya yi tare da cewa “To insha Allahu Hajiyata ganinan a hanya”, “To sai kazo”, suna fadar hakan ya kashe wayar, cikim sauri-sauri ya shirya cikin Shadda mai kyau sai maiko take taji aikin surfani wanda kana kallonshi zakasan kuɗi ya yi kuka gurin aikin , takalminshi da Agogonshi Gucci sai bakar Zanna da ya kafa a kanshi,baƙin gashin kanshi da ya kwanto bayan wayanshi, ya yi kyau sosai, turaruka ya fara fesawa sai da ya yi wanka dasu kafin, ya fara takawa cikin takun isa ya fito daga bedroom din, dayan bedroom din ya leqa tun da ya ga wayam yasan ta fice, gefen bed ya karasa raper na 1k ya ajiye mata kan bed din tare da fice abinshi……..
Rantsatsiyar Motarshi mai kyau da tsari ya nufa, sai yanzu ma ni naga Sojojin da suke shawagi a gidan da Alama ma sune masu gadin gidan, nayi mamaki sosai dan lokacin da na shigo jiya banga wannan tulin mutanan ba, suna ganinshi suka fara sara mishi, wasu ukku ne suka rugo da gudu suja bude mishi bayan mota, daya ne ya shiga cikin motar, sauran kuwa suka shiga cikin wasu motoci guda biyu suka mara mishi ba, tsula gudu suke kan hanyar , duk wanda ya gansu gefe yake dan yau manya ne akan hanyar da jiniyarsu suke tafiya………….
**************
Wani daki na shiga da babu wani haske sosai cikin ɗaki, ina shiga na hangi Wata mata Durƙushi take akan guyayinta, tana jujjuya kai ga wata uwar zufa da take karyo mata, sai kace wadda ta haɗiyi kunama, murkususu take tana cije lips dinta, a hankali ta fara nishi mai sauti irin na wanda yake cikin fitar hayyaci, ta dade sosai tana cikin wannan halin, a hankali ta fara rarrafe har ta isa gadon bononta da yake cikin ɗakin…………..
A hankali ta fara dan dukan gadon, tana nishi, a hankali ta fara furta “Mai gida! Mai gida!! Mai gida!!!”, ta fada tana daura kanta jikin gadon bonon , wani wawan tsaki akaja kafin wata murya ta daki dodon kunnena, cikin faɗa yace “so nawa zan fada miki in ina bacci ki daina tashina mai yasa ke gaba daya, bakya da tunani ne, kamar Dabba haka kike Al-amuranki , Wai ya akayi ne ma,” ya fada cikin fada-fada…………..
Hawayen da suke maƙale a idanunta ne suka zubo, cikin rawar murya tace “Dan Allah kayi hakuri”, tsaki ya kara jaa tare da cewa “to! da hakurin ya mutu Sadakar nawa kika bada Ke! Maryam Wallahi ki kiyaye ni, dan zanyi mugun saɓa miki Shashasha kawai”, cije lips dinta tayi tare da cewa, “dan Allah ka taimakamin ina jin naƙuda ce nake”, dariya ya sheƙe da ita tare da cewa “Au haba naƙudar ce, Uhmmmm lokacin da kikazo kikaji dadin ki wa ya hanaki , sai yanzu ne kike cewa kina wata naƙuda, to ki haife mutanen duniya ma mana ni ina ruwa, dan haka karki kara tashina ko kuma Wallahi ki gane kuranki “, ya fada yana juyawa……………
rasa yarda zatayi tayi, ga wani azababban ciwon baya da na mara da ƙafafu da ya sauko mata gaba daya, a hankali take rarrafawa har ta isa bakin kofar ɗakinta da ko siminti bata samu arzikinshi ba, kanta ta leqa tare da cewa “Haleem! Haleem!! Haleem!!!”, ta fada cikin rashin fitar murya…………
Wani Yaro da bazai wuce Shekara 9 zuwa 11 ba ya fito daga wani ɗaki da gudu tare da cewa, “Ummu gani”, rike hannunshi tayi tana sauke numfarfashi tace , “Haleeem jeka ka kiramin Iya yi sauri”, ta fada tana dafe mararta, “Ummu baki da lafiya ne ?”, ya fada cikin muryar tsoro, jnjina kanta tayi , tare da cewa “yi sauri kaje”, ta fada tana sakin hannunshi…………..
da gudu ya fita daga gidan, minutes kaɗan sai gashi sun shigo da wata Yar Tsohuwar mata sai dai ba tsohuwa bace chan ta dai manyanta, da sauri ta karasa gareta, tare da dafa kanta da tan jinginar a jikin ginin ɗakin tana hawaye ga wani kyarma da jikinta yakeyi, naman jikinta har wani rawa-rawa yake, cikin tausayawa tace “Maryama! Maryama Assha naƙudar ce, sannu tashi mu shiga ciki”, ta fada tana riketa, dakyar ta yunƙura, da taimakon Iya suka shiga cikin ɗakin………………
tsakiyar dakin suka tsaya, kallon kan gadon da Lawan ke kwance tayi, cikin fada tace “Kai Amma Lawan anyi ɗan iskan Yaro ashe dama haka kake, yanzu matarka tana naƙuda amma kana nan kwance, amma kayi Asara wallahi, k……” dafata tayi tare da cewa “Iya bai sani bane, kuma…”, ɗaga mata hannu tayi tare da cewa “…………..
*Wannan littafin na kuɗi ne #200 ne kuɗinshi, ki daure ki biya kisha karatunki cikin kwanciyar hankali*
~DAGA TASKAR SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE~
[…] Nazlah Hausa Novel Complete […]