Littafan Hausa Novels

Gidan Bature Hausa Novel Complete

Gidan Bature Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

GIDAN BATURE

(Romantic love story & Family Saga)

 

Ummu Subay’a

 

dedicated to

RUFAIDA OMAR

(GWANATA)

 

Wattpad UmmuSubaya

 

Ina mai bawa SOYAYYA CE fans hakurin rashin ci gaba da banyiba a dalilai na tsaro

 

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR

Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA

Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN

Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

 

0⃣1⃣

 

“MA’U MA’U MA’U pls xo kiban littafina ai bani na hanaki yin assignment dinba, kuma ai kinsan ina baki ki copy idan har ba’a mana gargadin kada a kawo iri dayaba”

Wata yarinya ce da baxata wuce shekara 15 ba takebin wadda ta kira da MA’U itama baxata wuce 15 years dinba, tanata mata magiya

 

 

Amma ko a jikin Ma’u sai tafiarta take kamar ba da ita akeyiba hadda guntun dariarta

 

Palon Amminta ta nufa kai tsaye anan ta taradda Anty Jidda tana bawa diyarta Amal nono, tunda taga Ma’u ta shigo da sauri tasan akwai magana

 

” wa kuma kika tabo Anty Masifa” bata gama rufe bakinta ba Sukrah ta shigo kamar xatayi kuka

Sanadin Boko Hausa Novel Complete

Murmushi Anty Jidda tayi tace

 

“Nasan xa’a Rina ai, Shukrah me tayi miki?”

 

Hawayena suka fara ambaliya a fuskar Shukrah

 

“Assignment nawa ta kwace wai xata kwafe kuma.tacewa Uncle namu nice na kwafe nata baicin kuma yace bayason copy copy”

 

Kallon bbu wasa Anty Jidda tama Ma’u wadda take tsaye ta kama kumkuminta kamar wata babbar mata

 

” maxa bata littafinta”

 

Bani Ma’u ta tura tace

 

” wlh baxan bataba don ban yiba kuma ban iyaba, da a dake ni daya gwara an dakemu mu biyu”

 

” xaki bata ko sai na tashi na babbalaki a wajen”

 

Ganin sarai Anty Jidda xata aikata abunda tace don tasan ba’a kawo mata wargi yasa ta fara kwadawa Amminta kira

 

Ai kuwa bbu bata lokaci sai ga Ammi ta bayyano

 

” keda wayene? Sam ba’a barin kuruwarki ya huta sai an dinga daga miki hankali”

 

Ssai Anty Jidda ta bata rai tasan sarai yanxu Ammi xata goyi bayan Ma’u

 

“Wlh Ammi kekike goyawa Ma’u baya take duk fitsarar dake, har ta isa na bata umarnin tace baxatayi ba, wlh kada kiga idon Ammi idan bakiyi maxa ki bata littafinta ba bbu Uban da xai hanani farfasa miki jiki da duka”

 

” uwar ubankine xata hanaki fasa mata jiki da duka kinji ko nace ni nan Asma’u uwar Ahmad ubanki ni xan hanaki fasa mata jiki da duka, littafi kuma baxata bayarba, ke kuma munafuka kinyi fuska kamar wata munina kina jira a amsa miki littafinki to baxata bayarba maxa bacemin daga part

 

Da gudu Shukrah ta fice tana kuka mai ban tausayi don ta tabbatar littafinta ya tafi kenan forever

 

A balcony Shukrah taci karo da Zahra, har xata wuceta Zahra ta kamo ta

 

” keda waye? Waya dakeki”

 

Cikin kuka Shukrah ta mayarwa Zahra abunda ya faru, ssai ran Zahra ya baci kama Shukrah tayi suka koma Palon Ammi

 

Nan ma sun sami Jidda nata mitan abunda Ammi tayi

 

Saura kiris fitsari ya kufce a marar Ma’u ganin Zahra Dodonta, bbu shiri ta koma bayan Ammi

 

Ita kanta Ammi tasha jinin jikinta ganin Zahra don tasan bbu abunda xai hanata karbar littafin

 

” to algumguma kinje kin dauko Anty fitsara taxo karba miki, to bari kiji ko uban Zahra’un kika kawo baxa’a bada littafinba”

 

Inji Ammi tana kara kare Ma’u dake bayanta

 

Ganin.tsayawa magana ma bata lokaci ne yasa Zahra nufo bayan Ammi gadan gadan don amsar littafin

 

Cikin karfin hali Ma’u tayi hanxari ta raba littafin gida uku ta xubar a kasa ta juya ta nufi bedroom na Ammi kamar walkiya ta shige ta rufe kofar hadda sa ki don sam bata gigin barin kofar Ammi baki saboda rana irin wannan

 

Marayan kuka Shukrah ta saka ta fice tabar falon gwanin ban tausayi

 

Takaicine yasa Jidda sabar diyarta a kafada itama ta fice

 

Zahra kam tsayawa tayi kamar mutum mutumi don tsabar bakin ciki, dakyar itama ta ja kafarta ta fice daga falon xuciarta na tafasa

 

Ita kanta Ammi jikinta yayi sanyi kujera ta samu ta xauna tana kuma godia ga Allah dayasa hakan ya faru BATURE baya gari da yau na lahira sai yafi Ma’u jin dadi

 

“Assalamu Alaikum”

 

Kamar daga sama Ammi taji Muryan BATURE ya rangada Sallama

 

A firgice ta juyo tana kallon bakin.kofar falon don.tabbatarda abunda kunnenta ya ji

 

Ba karamin raxana tayiba dataga BATURE tsaye a bakin kofar falon yana jiran amsa sallamarta

 

Adan kidime ta amsa tace

 

” jabbama Gorko amm”

 

Cikin takunsa na katsaita ya shigo cikin falon yana karantar yanayinta, daria ma ta basa don sarai yasan meya wakana

 

A bakin kofa sukaci karo da Zahra ta sanardashi abinda ya wakana

 

Amma ya batsar kamar baisan komai ba, xama yayi kusa da ita

 

” saukar yaushe BATURE”

 

Wayarshi ya fito dashi daga aljihun gabar rigarsa ya hau latsawa kan yace

 

” saukar safe, bandai shigo cikin gida bane ina can company tareda Balarabe”

 

Murmushi Ammi tayi tace” wato kace nina fara tokali dakai a gidan nan kenan”

 

Ssai ta kara bashi daria wai a nata xata buga cikinsa kenan

 

Kamar baxai amsaba yace ” eh dake na fara haduwa”

 

Dadi ssai Ammi taji tana ganin yau Ma’unta ta kubuta daga ukubar BATURE sai kuma gobe wani lamarin ya bullo

 

Gyara xamanta tayi tace” in kawo maka furane”

 

Murmushi yayi a xuciarshi yace

 

” kin kama kanki da kanki ”

 

A xahiri kuma yace

 

” yanxu kam bana jin yunwa amma kan na kwanta xanso nasha”

 

Mikewa yayi ya gyara wuyar rigarsa

” xan.shiga cikin gida na gaida su Umma, Ma’u ta dau furar ta kaimin part na tasa a fridge”

 

Bai jira cewar Ammi ba yasa kai ya fice yana murmushin mugunta

 

Sanin tsananin wayon Ma’u ne yasashi wucewa part din Ummi duk da bai jima da barin part dinba

 

 

 

Koda Ammi ta fadawa Ma’u sakon BATURE kuka tasa

 

” wlh Ammi an fada mishine shi yasa yace na kai mishi Allah bani kaiwa”

 

Rarrashinta Ammi ta shigayi

” bbu wadda ya fadamishi ai da an fada mishi xuwa xaiyi ya balla kofar ya dakaki yau ya fara balla kofarne”

 

Baki Ma’u ta tura don ita har yanxu bata amince da BATURE bai san da abunda ya faru ba

 

” to ki kai masa da kanki mana ai baxai gane ke kika kaiba tunda baya dakin”

 

Da mamaki Ammi take kallon Ma’u tace

 

“Kinci ubanki ja’ira wato fitsarar taki takai a aikeki ki aikeni”

 

Kara tura baki Ma’u tayi tace

 

“To to basai ki bawa matarsa takai masaba”

 

Mikewa Ammi tayi tace

 

” kinga rabani fa bala’in BATURE ki mike ki dau furar nan ki kai masa, ko idan ya shigo ya Tara miki jini da majina bbu ruwana”

 

Bbu yadda Ma’u ta iya taje ta dau furan tana mita

 

“Shi Ya BATURE kam ubankune da yakeyin duk abunda yaso bbu mai taka mishi birki kodon yaci sunan kakanmune? Ai cin suna ba cin girman mai sunan bane, gani nida naci sunan Ammi amma Sam bbu mai daga min kafa komai nayi sai an takamin burki”

 

Murmushi tayi

 

” koda shike nima ina kwatar yancina don bbu mai cemin kule bance ass ba”

 

Kamar yadda BATURE ya hasaso haka kuwa ya faru sanda Ma’u tabi part nasu Ummi ta leka don tabbatar da BATURE na wajen

 

Ai kuwa ddi taji data ganshi tare da Zahrarsa suna soyewa a falon Ummi, kwafa tayi ta wuce part dinsa tana cewa

 

” mutane sai karuwanci ido da ido ko kunyar manya ma basaji, ji inda ta kwanta a jikinsa kamar suna palonsu, suyi su koma inda suka fito ma na sheke ayata bbu kasalanda”

 

 

Janye Zahra yayi daga jikinshi ya manna mata peck a check dinta yace

 

” Habibty bari inje kada ka kufce min kin santa kamar walkiya take”

 

Daria Zahra tasa tace”

 

Ok Baby idan kungama dramar Ku ta tom and jerryn sai na kirani don baxan iya tsayawa Ku cikamin ciki da daria ba na kasa nuna maka yadda nayi missing dinka”

 

Hararar wasa ya watsa mata

 

” ji kamar xatayi wani abun kirki, yau dai ki shirya 7 hours service na jiranki”

 

Murmushi kawai tayi shi kuma ya fice son matarsa na kara shiga jikinsa

 

Cikin hanxari Ma’u ta shiga falon BATURE ta bude fridge taxa Furan data kawo ta juya da Saudi xata fita kawai sai taga kofa a karkabe

 

A raxane ta fara kewaye falon da kallon, karaf idonta ya sauka akan BATURE yana xaune kan kujera yana latsa wayarsa fuskarsa bbu alamun wasa balle tausayi ya jade cif kamar hadari

 

Batayi mamakiba dajin dumin fitsari yana bin cinyarta don ban yau aka fara ba

 

Jin abu na diga ne yasa BATURE dago Blue eyes dinsa ya xuba akan tiles yana ganin yadda fitsarin Ma’u ki diga kamar wata diyar goye

 

Tirkashi……………..

 

 

Your

Votes

Comment

Are needed

 

Ummu Subay’

[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: GIDAN BATURE

(Romantic love story& family Saga)

 

Ummu Subay’a

 

dedicated to

RUFAIDA OMAR

(GWANATA)

 

 

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR

Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA

Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN

Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

 

0⃣2⃣

 

” xo ki xauna anan ki fadamin laifinki da bakinki”

 

Bature ne yayi maganar cike da umarni

 

Jikin Ma’u har rawa yake ta tako a hankali hawaye sai ambaliya yake a fuskarta, ga kuka nacinta amma bbu hali ta fitar don muddin muryarta ya bayyana na lahira sai yafita jin dadi

 

Xama tayi a gabanshi cikin rawar murya ta fara koro bayani

 

“Chemistry assignment book na Shukrah na dauka, da Anty Zahra tare da Anty Jidda suka matsa na bata sai na yaga littafin”

 

Murmushin mugunta yayi

 

” bari mu fara da favorite dinki Oyo mike kimin frog jump”

 

Hawayen Ma’u ne ya kara yawa wajen kwaranyowa, daga gani kasan batason frog jump din amma bbu yadda ta iya ta hau xagaye dakin kamar yadda ta saba, tana kuka mara sauti tana sauke ma Bature Allah ya isa kwando kwando

 

Mikewa Bature yayi ya nufi bedroom dinshi don kimtsawa kota kanta ma baibi ba

 

Bbu wani sassauci da barin falon Bature ya kawo mata don tasan akwai security camera a falon

 

Hawaye, Majina da gumin axaba su suka wankewa Ma’u jiki sai haki take kamar ranta xai fita, tasha wahala iya wahala

 

1hour later

 

Bature ya fito cikin shigar jallabiya daga gani shiga yayi ya kintsa kansa sai xabga kamshi yake kamar sabon Ango

 

Daya daga cushion dake falon ya xauna, ya dau wayarsa ya turawa Zahrarsa short text

 

” Baby turomin Shukrah”

 

Knocking da’ake a bakin.kofar falon ne yasa Bature mikewa yaje ya bude kofar

 

Da sallama Shukrah ta shigo ta xauna akan center carpet dake sakiyar falon tana duban Ma’u wadda anan wannan lokacin mala’ikar mutuwa kawai take jira yaxo ya dau ranta don tsabagen jikatar datayi

 

Bature daya dawo ya xauna a inda ya tashi

 

” jeki daukomin dorina a bedroom”

 

Ya umarci Shukrah bbu musu Shukrah ta mike ta nufi bedroom dinshi

 

Da rarrafe Ma’u ta iso gaban Bature ta fara rokonsa

 

” don girman Allah Ya Bature kayi hakuri wlh baxan sakeba, na tuba ka yafemin Allah baxan kumaba”

 

Shureta yayi da kafa ya watsa mata mugun harara

 

Bata damu da buguwar da tayi da center table ta kuma dawowa ta rike kafarsa tasa kuka mai ban tausayi

 

Cikin muryanta daya dishashe ta kuma yi masa magiya

 

Amma koya kulata ci gaba da latsa wayarsa yayi

 

A ladabce Shukrah ta mika masa dorinar data dauko

 

Bbu xato bbu sammani Ma’u taji saukar dorina a bayanta

 

Wani raxanennen ihu ta sake don tsananin axaba

 

Bbu tausayi balle imani Bature ya shiga dukar Ma’u kamar aikosa akayi

 

Tun tana iya ihu har ihun ya gagareta, Shukrah dake gefe toshe kunnenta tayi tana xubda hawayen tausayi

 

Sanda Bature ya daki Ma’u son ransa kan ya kyaleta ya mikawa Shukrah dorinar

 

” ki mata bulala goma”

 

A raxane Shukrah ta dubi Ma’u dake kwance kamar gawa tana fidda numfashi.sama sama

 

Kai Shukrah ta fara girgixawa tace” don Allah Ya Bature kayi hakuri wlh baxan iya ba”

 

” ke! Ni joke mate dinkine daxan saki abu kece baxakiyiba oya do as I said”

 

Shukrah sarkin tsoro jiki na rawa ta amshi dorinar ta daga a hankali ta xane Ma’u

 

Warce dorinar Bature yayi a hannun Shukrah ya watsa mata

Ihu ta sa tana tsotsa wajen tana kuka

 

Mika mata dorinar yayi da mugun kallo

 

Bbu yadda Shukrah tayi illah watsawa Ma’u dorinar kamar yadda Bature ya mata tanayi tana kuka

 

” kan na bude idona banason ganin ko inuwarku”

 

Bature ya fada a tsawace bayan Shukrah ta gama xane Ma’u

 

Da taimakon Shukrah Ma’u ta mike suka fice Ma’u kuka Shukrah kuka

 

Da sallama Jidda ta shiga falon Alhaji Ahmad Bature (Abba), tare ta sameshi da kaninsa Alhaji Mahmud Bature (Abbu) suna tattaunawa

 

Da murmushi suka amsa sallamarta, a kasa ta xauna ta kwashi gaisuwa

 

Shiru falon yayi nadan lokaci kan Abbu yace

 

” ince dai lfy Hauwa”

 

Cikin natsuwa Jidda ta fara koro bayani

 

“Daman wata shawarace naxo da ita”

 

Sai kuma tayi shiru saboda batasan yadda xasu dau maganarta ba

 

Abba ne ya katse shirun nata

 

” muna jinki Jidda ”

 

Gyara xama tayi

 

” daman akan Ma’u, mexai hana idan Ya Bature xasu koma su dauketa taje can ta xauna a wajensu ko xata samu cikekken natsuwa da kuma tarbiya, am sorry to say a gaskia xamanta a wajen Ammi bbu wani alfanu sai kara ruguxa mata tarbiya datake, Ya Bature da Zahra ne kadai take shakka a gidan nan kuma tunda suka bar gidan ta barjin maganar kowa ta bar shakkan kowa kuma duk sanadin daurin gindi data samu gun Ammine, ina roko don Allah a duba maganata a kira family meeting don a tattauna akai”

 

Kai Abbu ya jinjina yace

 

“Tabbas Jidda maganarki dutse kuma yadda kike bukata haka xa’ayi”

 

Murmushin manya Abba yayi yace”

 

 

Wani hanxari ba guduba ya xamuyi da Ammi don kunsan baxata taba yadda a tafi da Ma’unta ba”

 

“Tun kan naxo nan nasan yadda xa’ayi da ita Abba, upper week su Ma’u xasu fara exam xan jira har su gama sai na tafi da ita a xummar xatamin Hutu, kunsan Ma’u da son yawo xata amince inyaso daga Kadunar sai na wuce da ita Abuja na danka musu ita, ita kuwa Ammi sai dai taji a slow nasan tana shakka Ya Bature baxata je ta dauko ta ba”

 

 

Harara Abba ya hurgawa Jidda yace

 

“Tsabagen kin rainamin uwa har xama kikayi ka tsaro yadda xa’ayi da ita ”

 

Daria Jidda tasa ta mike tana cewa

 

“Abba Ammin ne sai da haka”

 

Abbu yace

 

“Sai.ki sanarwa yan uwanki, mukuma xamu sanarwa iyayenku game da meeting din sa’annan ki tabbatar Ammin Ma’u bataji ba”

 

 

Duk daria suka saka Jidda ta fice farin ciki fal ranta

 

 

 

Duk halin tsananin da Ma’u ke ciki bai hanata balbale Shukrah da masifa ba lokacinda taga shukrah tayi hanya part din Ammi da ita

 

” Uban me xanyi a wajen Ammi baicin yau da ita aka hada baki MUGU ya dakeni, ni ki kaini part din Mami”

 

Babu musu Shukrah tayi hanyar part din Mami da Ma’u

 

Mami na xaune tana kallon Sunnah TV sai ga Ma’u da Shukrah kamar daga sama, tunda ta kalli yanayinsu tasan inda xancen yake

 

” yau kuma meya hada tom and jerryn aka kawomin jinya”

 

Mami tayi tambayar tana kallon Shukrah

 

“Nima ban saniba”

 

Shukrah ta fada tana gudun bala’in Ma’u

 

A jikin Mami Ma’u ta xube tana kuka mai tsuma rai

 

Fita Shukrah tayi daga dakin tana tuna arangamar daxa’a sha kan Ma’u.ta fara mata magana don tasan gaba mai tsanani Ma’u xata shigayi da ita

 

 

” Mamana Sam bakyajin magana, kin tsan halin Bature Sam baya miki ta wasa idan kikayi laifi ai sai ki dinga kiyayewa, yanxu dubi irin lahanin daya miki kamar wadda aka turawa dan ta’adda ya hukunta”

 

Cewar Mami tana dudduba yadda farar fatar Ma’u tayi ja dakuma layi layin duka

 

“Ai wannan tafi Dan ta’adda ma Mami, yanxu idan kin bincika mugun abu tayo aka hadata da Ya Baturen”

 

Cewar Batool tana dake xaune kan dinning tana dinner

 

Mugun Harara Ma’u ta aika mata tace

” abunda kukeso kenan yayita dukata kamar jaka, to wlh baxan natsuba sai abunda ya karu, nasan kowa yanxu ya tsaneni a gidan nan Mamita ce kawai take sona”

 

Baki Mami ta kama tace”

 

Yau kuma ni Balkisu kesonki Mamata, ina Ammi kuma”

 

Baki Ma’u ta tabe tace” mun bata da ita don ta ita aka hada baki akamin TARKO”

 

Daria Batool tasa hadda shewa tace

 

“Yau kuma Ma’un Ammin ta bata da Ammin”

 

Kira Mami ta kwadawa yar aikinta Lami, ta umarceta ta kawo mata ruwan dumi a cikin roba

 

Daga Ma’u Mami tayi ta shigarda ita bedroom Batool kuma sai tsokanarta take don ta samu dama idan da da kafarta baxata samu irin wannan damar ba

 

Ruwan dumi Mami ta hadawa Ma’u ta kaita toilet tayi wanka

 

Ruwan duminda Lami ta kawo Mami ta daddanewa Ma’u jikinta tana mitan irin Muguntar da Bature ke mata

 

Sanda Mami ta tabbatar Ma’u tadan ware taja mata blanket nan da nan kuma baccin wahala ya dauki Ma’u

 

Idan da sabo Mami ta saba da jinyar nan don duk randa Bature ya samu xarafin dukan Ma’u wajen Ammi to tabbas ita take jinyar

 

Shiga toilet din Mami tayi ta kintsa kanta tajawa Ma’u kofa ta wuce turakar mijinta

 

 

 

Daria Zahra tasa lokacinda ta shigo falon Bature taga sai feshe falon yake da Room freshner, rumgumeshi tayi ta bayanshi tace

 

” hala ta aikata maka abunda ta saba”

 

Takaitacen Murmushi Bature yayi ya dawo da ita gabanshi yayi hugging nata dakyau yace

 

” ni lamarin Ma’u har ya fara bani tsoro gata da shegen tsoro ga taurin kai, baki ga yadda ya hada mata jini da majina ba kamar baxatayi rai ba amma nasan bbu abunda xai hana gobe ta sake aikata fiye da hakan”

 

Yana gama maganar ya dauketa kamar yat tsana ya wuce da ita bedroom dinsa

 

A kan bed ya mata masauki ya fara kissing dinta ta ko’ina

 

Dakatar dashi tayi tace

 

” kada na mantar dani Sweety, gobe insha Allah akwai morning meeting”

 

Tsaki Bature yaja yace

 

” bai wuce maganar dukan Ma’u bane, Ammi ko Mami suka hada meeting”

 

Hannunta Zahra ta sakala a wuyarsa tace

 

” bana tunanin haka don Jidda tacemin kada Ammi ta sani don xata dagula waje”

 

Baki kawai Bature ya tabe yaci gaba da nemawa kansa natsuwa

 

 

For live update follow me at Wattpad Ummusubaya

 

Ur

Votes

Comments

Are needed

[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: GIDAN BATURE

(Romantic love story& family Saga)

 

Ummu Subay’a

 

dedicated to

RUFAIDA OMAR

(GWANATA)

 

 

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR

Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA

Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN

Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

 

0⃣3⃣

 

Tushen Labarin Gidan Bature

 

 

Dr Lingard haifeffen London ne, Blue eyes dinshi shi xai tabbatar maka cikekken Baturene gaba da baya

 

Yaxo Nigeria ne cikin volunteers Doctors da ake dibowa daga England xuwa Nigeria a Congola aka turashi

 

Bbu xato bbu sammani ya fada soyayya da Asma’u diyar Sarkin Yola

 

Ba’a samu wani tangarda ko tashin hankali ba Mai martaba Sarkin Yola ya aurawa Dr Lingard aure da Asma’u bayan ya karbi Kalmar shahada

 

Saboda Mai Martaba ya yaba da kyawawan halayensa

 

Ta bangaren iyayen Lingard da labari yaje musu nan take suka sallamashi duk da shi kadai suka Haifa

 

Cikin shekara 10 Allah ya albarkaci Dr Lingard (wadda ‘yan uwan Asma’u da jama’a suka lakaba masa Dr BATURE) da Asma’u da yara uku

Ahmad

Mahmud

Muhammad

 

Bayan Dr Bature yayi retire daga aiki sai ya shiga cikin business gadan gadan inada ya mallaki company da dama kuma ta ko’ina kudade nashigowa

 

Ba’a jimaba sunanshi yayi shura a Nigeria

 

Kaduna yaje ya buga tamfatsetsen estate na alfarma xubin gidan turawa wadda a bakin gate akasa BATURE ESTATE

 

tattara iyalansa yayi suka koma Kaduna da xama

 

Dukkan yaran kammanin Asma’u (Ammi) suka dauka xubin Fulanin asali ko farar fatarshi fat basu daukaba amma kam fararene farin Nigeria

 

Rana daya Ahmad da Mahmoud sukai aure kasantuwar sun tashi kansu daya

 

Ahmad ya auri Fateema diyar kawunshi wan Ammi

 

Mahmud kuwa Hauwa ya aura diyar Governor Kaduna na lokaci

 

Fateema macece mai kirki bbu ruwanta, tanada sanyin hali tanada fara’a dason mutane, yadda take kal haka xuciarta ma kal

 

Hauwa itama bbu yabo bbu fallasa tanada son mutane ga kirki masalarta dayane son abun dunia da kuma son ace ita wacece ta xama ko’ina anaji da ita ssai

 

Ranar farin ciki da bakin ciki

 

Fateema ta haihu lfy ta haifo santalelen danta mai kama da Dr BATURE kamar an saga kara an karya, ya dau daga Blue eyes dinshi hadda farar fatarsa

 

A daren ranar ne kuma Allah ya amshi ran Dr BATURE

 

Ranar bakwai aka sawa yaron Muhammad don shine favorite sunanda Dr BATURE keso nan take aka fara kiransa da BATURE

 

Bayan sati biyu itama Hauwa ta haifo da namiki, ranar suna aka sa masa Ahmad ana kiransa da Balarabe

 

Duk da jimamin mutuwa bai hana Hauwa da danginta shirya gagarumar bikin suna ba

 

 

Bayan shekara 12

 

Fateema (Mami) nada yara hudu

Muhammad (Bature)

Hisham

Hauwa (Jidda)

Batool

 

 

Hauwa (Ummi) itama tanada yara hudu

Ahmad (Balarabe)

Abdullah

Fateema (Zahra)

Shukrah

 

Muhammad autan Ammi kuma shalelen Ammi ma yayi aure, ya auri kanwar Mami Asma’u kuma takwarar Ammi

 

Ga dan lele ga takwara sai Ammi ta dau son dunia ta dora musu komai Asma’u da Muhammad, hakan ba karamin haushi ke bawa Ummi ba hadda cewa wai tana daddaga mata kai

 

Wata Ranar Bakin cikin

 

Labari mara dadine yaxowa Gidan Bature na rasuwar Muhammad sakamakon accident dayayi a hanyarsa ta dawowa daga Abuja yaje meeting

 

Tsayawa fadan tashin sense dasuka shiga bata lokaci musamman ma Ammi saura kiris ta xauce

 

A lokacin Asma’u nada ciki Wata 9 dole ma ka xubda kwalla idan ka ga yadda ta dawo

 

Kwana hudu da rasuwar Muhammad, Asma’u ta haihu ta, ta haifi santaleliyar diyarta mai kama da Ammi sak, kyaun Ammi duk ta kwashe

 

A rana ta biyar da haihuwar, Asma’u ta rasu bayan ciwon ciki mai tsanani

 

Tun a ranar Ammi.tasawa yarinyar suna Asma’u kuma take kiranta da Ma’u

 

Bbu yadda ba’ayi Ammi ta bawa Ummi Ma’u ta shayar da itaba kasantuwar bata jima da haihuwar Shukrah ba, amma Sam Ammi taki haka ta dau Ma’u take bata madara, kuma bbu wadda ya isa ya dauki Ma’u kana daukarta xata amsheta

 

Bature da Balarabe tare suka tashi kamar mahaifansu idan gansu kamar tagwaye sai banbanci hali kalar data da yanayi

 

Bature mutum ne da bayason wasa sam komanshi a manyance yakeson yinshi gashi mugun karshen xamanine baya murmushi sai ta baci ga miskilanci da wuya kajishi yana hira halanshi a murde yake ssai shiyasa sam baya shira da Mami sunfi dasawa da Ummi don haka tafison yaro one in town

 

Balarabe ko so simple yanason wasa ga surutu yanada saukin hali yaran Gidan kowa Ya Balarabe shiko yafi dasawa da Mami

 

Muddi akacewa yaran Gidan Bature ga Ya Bature duk wani ta’asan da suke xasu daina tunba Ma’u data xama customer ba ko batayi komai ba yana kallonshi jikinta xai fara rawa

 

Ba karamin ddi sukajiba lokacinda su Bature xasu fita abroad karatu

 

Tafiarsu ce tasa Ma’u kara taurarewa da kuma bijirewa mai dan taka mata birkin Xahra ce tunda tanada xafin rai, takan iya xuwa har gaban Ammi ta bubbugeta

 

Bayansu Bature sun dawo daga Abroad ne yasa kafar wando daya da Ma’u duk ranar dunia sai sun sha dramar duk wadda tama laifi can yake kai kararta, shiko Bature ya mata hunkuci na fitan rai

 

Amma duk baxai hanata gobe ta kara wani laifin ba, sai suka xama kaman Tom and jerry alkhairi baya hadasu

 

Bature ya samu aikin soja inda ya fara aiki a nan Kaduna

 

Shi kuma Balarabe Companynsu yake aiki daga baya kuma ya koma companynsu na Lagos

 

Soyayya Balarabe ya fara da Jidda har kowa ya sani, manya suka xauna aka tattauna inda Ummi ta kawo xancen Bature da Zahra wadda Sam bbu so a tsakaninsu

 

Nsuyin Ummi Bature yaji ya amince da auren Zahra

 

Biki akayi naxo a gani a fada don Ummi ce ta tsara komai ita da ‘yan uwanta iyayen son a shina

 

Auren bai jimaba akama Bature transfer xuwa Abuja

 

Bayan shekara daya da watanni da auren Jidda ta haihu ta sami diya mace aka sa mata sunan Ummi ana kiranta da Amal

 

Yanxu ta dawo goyon gida Balarabe ma ya dawo sai ta gama su koma

 

Shiko Bature yaxo wani aiki Zaria ne yasa Zahra biyosa ta wuce Kaduna

 

 

Cigaban Labari

 

Washegari duk manyan Gidan Bature sun hallara a palon Abba, Bature na kawai baya nan kuma shi ake jira

 

Da sallama ya shigo kowa ya amsa masa banda Mami data bishi da harara

 

Gaisuwa ya kwasa ya samu waje kusa da Balarabe ya xauna

 

Kasa-kasa cikin xolaya Balarabe yace

 

” da banga Zahra ba anan da sai nace network ne ya rikeka”

 

Harara Bature ya watsa masa yace

 

” ce maka akayi ni kaine Angon karni”

 

Har Balarabe ya bude baki xaiyi raddi sallamar da Abba yayine ya hanasa

 

Cikin natsuwa Abba ya bayyana masu shawarar da Jidda ta kawo

 

Abba na iddawa Mami tayi sauri tace

 

” kinci gidanku Jidda wannan wani irin banxan shawarace, sai yau na gane bakida digon tausayi, anan dake Muke ganin yadda Bature ke lahanta Ma’u kamar wata ‘yar ta’adda Sam baya raga mata, don so kike yaje ya kasheta sai kice a bashi ita yaje ya karasata koh, to nikam ban yarda da gurguwar shawarar nan ba, dama dama da kune yawwa”

 

Ummi datayi na’am da shawarar Jidda tace

 

” tab ai Ma’u tafi karfinsu, daidainta su Baturene, kawai suje can ya dinga sauke mata allurar sojoji ko xata natsu”

 

” wlh gaskiar Ummi ce Ma’u tafi karfinmu sai su Ya Bature”

 

Cewar Jidda tana marairaice fuska

 

Kara hasala Mami tayi

 

” to bbu inda xata uwar son a shina, Balarabe kai tattari matarka Ku koma ta barmu inda ta samemu”

 

Mami ta karashe maganar tana duban Balarabe

 

Murya Abbu ya gyara yace

 

” Nidai banason fada akan rashin gaskia in-law, duk nan bbu wadda yaki shawarar nan sai ke, hakuri kawai xakiyi Bature ya tafi da Ma’u don sama mata ingancecciyar rayuwa”

 

Ganin kowa ya amince da tafia da Ma’un yasa Mami ba don tasoba ta sallama

 

Zahra ce ta rufe taro da addu’a

 

Mami ta riga kowa tashi ta fice tana mitar an hade mata kai

 

 

 

Batool da Shukrah tareda da driver ke tsaye a parking space

Sunata mishi magiya ya kaisu makaranta xasuyi Latin don Ma’u tace baxataje ba kafarta na ciwo

 

” don Allah Ku taimaka kuje ku jawota sai mu tafi, ranar ai a idonku oga Bature yamin gargadin duk ranarda na kaiku makaranta ba tareda Ma’u ba to na sallami kaina da kaina”

 

Cewar Isa drive yana kokarin xama kan mota

 

Kamar Shukrah xatayi kuka tace” don Allah ka taimaka mana, ai baxai San bataje ba tunda yanxu xai koma Zaria ma”

 

Kai idi ya girgixa yace

 

“Ina sam baxai yiyu ba wannan kasada ne, idan kuma bai komaba fah? Kinga tawa ta kare”

 

Xama Batool tayi kan resting chairs wajen ta tabe baki tace

 

” shikenan sai mu dawwama anan amma bbu inda xani wai kiran wata Ma’u ”

 

Kuka Shukrah tasa ya nufi cikin.gida

 

Karaf ta hadu da Bature tareda Balarabe a hanya

 

Saura kiris tayi fitsari ganinsu a gabanta duk da batada laifi tasan sai ta sami rabonta gun Bature

 

Aikuwa wani mahaukacin tsawa ya daka mata, sanda Balarabe ya toshe kunnenshi

 

” Uban me kike a wannan lokacin baki tafi school ba

 

Shukrah uwar tsoro take jikinta ya dau rawa cikin rawar baki tace

 

“Ma….Ma…..Ma…..” Sam tsoro ya hanata karasawa

 

Balarabe ya janyota jikinshi yace

 

” cool ur heart, ki fada masa meya faru ko yanxu ya tattaka ki”

 

Add Comment

Click here to post a comment