Littafan Hausa Novels

Tawa Soyayyar Hausa Novel Complete

Tawa Soyayyar Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

TAWA SOYAYYAR*

 

_(love story 2023)_

 

~January 2023~

 

© Ouummey

 

*Wattpad @ouummey*

 

°°°From the experienced writer of SARAKI, BANI DA LAIFI & more, here comes wat a mind blowing story of ★★TAWA SOYAYYAR★★.°°°°

 

 

“”You can’t afford to miss…stay tuned”””.

 

 

%%*Dedicated to my patronizers, my lovers and my sweethearts, ANJANE PAID GROUP MEMBERS, love you dearly

 

 

 

 

°°01°°

 

 

_Gudu take yi a hankali a hankali tana share fuskan ta da kyakkyawan pink handkerchief, she’s totally exhausted sedai ba zata tsaya ba har se ta kai destination din ta, bata San yau wane irin kasala ke damun ta ba  domin seda kyar ma ta iya yaki da kanta kafin ta fito training ɗin nan.

 

Tsaya wa tayi dan kamba zata iya cigaba ba dole se ta huta, bottle water dake right hand din ta ta buɗe ta shiga sha, she almost drank all kafin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya, seda ta huta sosai sannan ta tashi ta cigaba, bata wani daɗe ba ta ratso cikin layin su.

Sadauki Omar Hausa Novel Complete

Daga ganin manya manyan kayatattun gidajen dake wajen kasan unguwar bata yamu bayi bace, unguwa ce ta manyan shegun duniya da suka ci suka tara suka kuma tada kai, gaba ɗaya layin ba wani medium gida balle ayi maganar kanana, gidaje ne wannan yana wane wancan wancan yana wane wannan, gaba ɗaya na daburce na kasa gane wanda ya fi wani kyau har seda na sauke ganina kan wani hamshakin gini da da ban lura dashi ba.

 

Nesa ba kusa ba ya kerewa dukkan gidajen da suke layin wajen kyan tsari, kyan zubi da kyan fasali.

Ko da ga iya fuskar gaban sa kasan gida ne da ya cinye biliyoyin kudade dan gate din kaɗai ya isa wasu bayin Allahn suyi rayuwar su su gama cikin rufin asiri da kwanciyar hankali.

 

Tsaye tayi bakin wannan wawakeken gate din, yatsan ta ta ɗora kan wani madanni da ba kowa ke lura dashi a jikin gate din ba, yana gama analysing finger din ta karamar ƙofar da ake shiga ta bude da kanta yayinda ita kuma ta shige kofar ta koma ta rufe.

 

“”Alhamdulillahil laziy biniimatihi tatimmus salihat””, na fada a raina ganin wani irin kayatacciyar compound da ban taɓa ganin irin shi ba kaf rayuwa na, lallai ko gidan wane ne wannan ba karamin hamshakin me kudi bane, ko a cikin masu kudin da alama shi ɗin daban ne.

 

Hannu ta sa ta zare band din da ta kama gashin kan ta dashi ta girgiza kanta hakan yasa gashin ya watse a kafadun ta ya kuma sauka a fuskar ta har yana rufe mata ido, tsananin ƙyalli da ɗaukar idon da gashin ke yi ze tabbatar maka lallai ba kananan kudade yake lashewa ba, taushi da santsin sa kuwa ko indiyawa albarka.

 

Gyara na gaban fuskar ta tayi ya koma baya sannan tayi heading entrance na main building din tana ƙwala kiran Anna.

 

“Anna, Anna, Anna”.

 

Haɗaɗɗen falo da yaji wasu shegun marbles, rug me tsananin taushi kamar jikin kuliya da har kafar mutum na nutsewa a cikin sa ta shiga, kwaɓe fuska tayi jin ko so daya Anna bata amsa mata ba.

 

Fuskar ta a kwaɓe ta shiga undressing kan ta cikin tsakiyar falon, sake nayi da baki ina kallon ta ganin wani sabon ikon Allah, budurwar da a kalla zata yi shekaru sha tara ce ke cire kaya a falo batare da wani kunya ki damuwa ba.

Legis iya gwiwa da half vest kaɗai yayi saura a jikin ta ta faɗa kan kujera tana zare sneakers din ƙafar ta da socks.

 

“Annnnaaaaa”.

 

Ta sake Kiran sunan cikin shagwababbiyar murya.

 

“Na’am daughter”.

 

Wata murya ta amsa daga cikin wani corridor kafin kuma mamallakiyar Muryar ta bayyana, dattijuwa ce dan a kalla zata yi shekaru sittin zuwa da uku haka, ita ɗin tsaka tsaki ce wato dai ba kyakkyawa ba haka kuma ba mummuna ba, kamar yadda fuskar ta take haka ma fatar jikin ta, ita ba fara ba ita ba baka ba, tana da tsayi sosai wanda ya bayyana kan sa duk da ƙibar dake gare ta.

 

Zama tayi kan kujerar da matashiyar take yayinda ita kuma ta kwanta kan laps din matar, hannu Anna ta sa kan gashin ta tana shafawa

 

“Har an dawo kenan”.

 

“Na dawo Anna, sedai am much very tired”.

 

“Then let’s go ki taking warm bath, you’ll feel better”.

 

“Zaki min da kan ki ko, Allah na gaji”.

 

Zare eyes Anna tayi kafin ta dungurewa yarinyar kai

 

“You so lazy daughter, maza tashi muje, amma baya kadai zan cuda miki”.

 

Da haka suka mike suka nufi bedroom, haɗaɗɗen royal king size bed ne me walwali da akai wa ado da gilasai hakan yasa yake reflecting ta ko ina, ita kan ta wardrobe din jikin ta duk glasses din ne, komai na dakin pink and blue ne, hatta ko da paint din, sedai pink din wani irin launi gare shi me matuƙar kyau da ɗaukar hankali haka ma blue ɗin ba wai normal blue bane.

 

Kan bed ta zauna ita kuma Anna ta wuce toilet haɗa mata ruwan wanka, seda ta haɗa komai sannan ta fito lokacin har yarinyar ta karasa cire kayan ta ta daura ƙaramin pink towel.

 

Toilet din suka shiga nima kuwa na bisu dan so nake kawai inga ta yadda za’a yiwa ƙatuwar budurwa me koshin lafiya wanka, lumshe ido tayi lokacin da kamshin turarukan wankan da Anna ta mata amfani dasu ya shige hancin ta.

 

Ba kaɗan ba take so da kaunar Anna dan tafi kowa sani da fahimtar ta, duk wani abu da take so Anna ta San shi haka ma duk abinda bata so Anna tafi kowa sani da kiyaye masa.

 

Hararar ta Anna tayi ganin tana neman bantare towel din wanda daga shi bata da sauran komai a jikin ta

 

“Get in the water kafin ki cire towel ɗin, kullum se na fada miki ba kyau yin naked a gaban mutane addini ya hana amma ba kya ji”.

 

“To Anna ai bubbles din ze bata towel din Kuma ba a gaban kowa nake yin naked fa se ke kadai”. Ta fada in a shagwaɓa manner

 

“Nima ai mutum ce, Islam be yadda kowa ya ga tsiraicin ki ba ko da kuwa maman ki ce se in ya zama da lalura, mijin ki kadai ke da privilege din ganin ki undressed, maza shiga ina da aikin yi kin sani surutu a bathroom”.

 

“Ina son ki Anna ta”. Ta faɗa tana shiga cikin jacuzzi tub din, seda ta shige ta yadda bubbles din bath soaps suka rufe mata jiki kafin Anna tace ta cire towel din.

 

Cuda mata baya tayi da wuya dan a cewar ta hannun ta baya kai wa wajen shiyasa bata iya wanke wa, ganin abin nata iya shege ne yasa Anna ficewa ta bar mata toilet din dan ƙirjin ta ta nuna wai su ma Anna ta wanke mata bata iya wanke su.

 

Dariya tayi da yasa kyan ta kara fitowa sosai, dimples din ta duka uku na fitowa, na both cheeks din ta se kuma na habar ta, a hankali ta lumshe hazel eyes din ta tana lafewa cikin ruwan ɗumin sa na ratsa ta haka kuma tana shaƙar ƙamshin sa, baccin da ya fara ƙoƙarin sace ta yasa ta ƙoƙarta ta karasa wankan tare da ɗauraye jikin ta ta fita daga bathroom din bayan ta saka blue bathrobe ta bar towel din a toilet dan tasan Anna zata shiga ta wanke mata.

 

A haka sanye da jikakkiyar bathrobe ta faɗa kan bed tare da rufe jikin ta da comforter, cikin kankanin lokaci bacci me daɗi yayi gaba da ita.

 

Ko da Anna ta shigo yi mata maganar breakfast haka ta tadda ta kwance tuni tayi watsi da comforter bathrobe din jikin ta ma duk ya bude gaba ɗaya kyawawan cinyoyin ta suna waje se pillows da tabi ta ƙanƙame kamar wasu ya’ya.

 

Girgiza kai kawai tayi ta fita zuwa dining, tun da ta doso wajen duk suka zuba mata ido cikin son Jin ina kuma take da basu taho tare ba.

 

“Anna Ina Afiyar take?”.

 

“Ai har tayi bacci Ammar, kawai kuci abincin ku kar ku makara office”.

 

Dan shiru saurayin da aka kira da Ammar yayi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan shi ɗin wa ne ga yarinyar ɗazu da Anna ta Kira da daughter sabida tsananin kamar da suke, shima kamar ita kyakkyawa ne sedai be kai ta kyau ba haka kuma fatar sa tafi tata haske

 

“Anna kin san bata iya cin abinci ita kadai, kawai a taso ta”.

 

Wannan karon magidanci da suke tare kan dining din ne yayi magana

 

“So kake tayi ciwon kai ne boy?, Anna abar ta har ta tashi dan kan ta Please, tunda kince zaki jira ta se kuci tare in Kuma da ni take so You can call me se in dawo”. A iya Muryar sa kaɗai mutum za iya sensing tsananin so da kaunar da yake wa ɗiyar sa wanda daga ita har Ammar shi suka kwaso a kamanni sedai ita ta hada da kamannin mahaifiyar ta shiyasa ta zarce Ammar a kyau.

 

“Ba damuwa Alh ƙarami, nasan ba ma se an kira ka ba, kudai ku karya kar ku makara”.

 

A hankali kowannen su ke cin breakfast din da tayi serving din su, ba wani da yawa suka ci ba suka tashi dan dukkan su ba su da ci sosai, sallama suka yi wa Anna ta musu addu’ar dawowa lafiya suka fice.

 

Dining din ta Kuma gyarawa yadda za dauki hankalin Afiya kamar yadda Ammar ya fadi sunan yarinyar, ta sani in dai Afiya ce tana iya cewa ma ta koshi ba zata ci komai ba, ita kam har yau da ta ke da kusan shekaru talatin tare da Alaji Karami ta kasa daina mamakin rashin cin abincin sa, gashi nan ya gadawa ya’yan sa dan Afiya se ta wuni bata kai abinci bakin ta ba sedai kayan kwalama da kwaɗayi, ita in an barta ma se tayi sati bata ci abinci me nauyi ba haka ma Ammar ze gama mata ihun yunwa yake ci amma in ta kawo abinci be fi yayi spoon hudu zuwa biyar ba ze ce ya koshi.

 

Seda ta tabbatar komai yayi yadda ta kamata sannan ta koma falo ta kishingiɗa tana azkhar tare da kallon zee world, a hakan da take itama bacci ya sace ta batare da ta ankara ba.

 

A hankali ta sake mika kafin ta miƙe zaune kan bed din, yamutsa fuska kawai take yi dan bata san sanda bacci ya ci ƙarfin ta da har ta kwanta ba, kamar wadda aka zabura haka ta kai duban ta ga agogo a ɗimauce, zare oily Hazel eyes din ta tayi tare da dafe kan ta

 

“Oh my God, quarter to twelve”.

 

See Kuma ta sauke hannun da sauri tana sauka daga gadon ta wuce gaban wardrobe din ta ta hau zubo da kayan ciki cikin son nemo wanda zata saka, yaya akayi tayi bacci da har ta makara irin haka,

 

“Wayyo Allah, Rabb see me through”.

 

Ganin ta kasa nemo daya da zata sa a jikin ta yasa ta hau kwalawa Anna Kira, cikin bacci Anna ta dinga jin siririyar muryar Afiya na ambato sunan ta, buɗe ido tayi tana miƙewa zaune se kuma taji wani kiran, yadda taji ta kamar cikin tashin hankali yasa ta miƙe da sauri zuwa dakin.

 

Turus tayi daga bakin ƙofa ganin yadda Afiya tayi watsi da kayan cikin wardrobe din gaba dayan su, kowanne ya dau matsaya a inda aka wullashi.

 

“Yauwa Anna ta, pls come and choose an outfit for me, gaba ɗaya na rasa wanda zan sa, but let it be Marron and milk in color dan har na fito da shoea and bag din da zan saka, Please Anna make it so fast, am already late, bari in maza in gyara fuskana kafin ki dauko min”. Ta faɗa tana ƙarasawa gaban standing mirror din ta da yake nan babba dan tun daga kasa har sama yake bayyana Mutun se drawers din sa a gefe da gefe se kuma ta wani Dan glass Shima da be fiya fadi ba wanda akan shi kayan makeups din ta suke, mayuka da turaruka.

 

“Can You please shut your silly mouth, sabida baki da kirki kalli yadda kika turning dakin nan upside down Afiya bayan jiyan nan ki na gama yimin promise din kin dena, and I always tell you me ƙarya alƙawari dan wuta ne ko”.

 

“Please Anna not now, Ni ba ƙarya alƙawari nayi ba, ita just that am in a hurry, na fada miki am late fa, pls choose the Kaya for me fast fast, ɗaki Kuma leave it a haka I’ll put everything in place when am back”.

 

Duk maganar da take hankalin ta Naga modelling powder da take yi a face ɗin ta, tana gamawa ta saka eyeliner and mascara, lips din ta kuwa ta wadata su da pink chapette me paint hakan yasa ya zauna das kan kananan lips ɗin kamar a haka aka halicce ta.

 

Doguwar rigar da Anna ta ɗauko mata ta daga, seda ta duba ta tabbatar tayi kafin ta shiga zura ta a jikin ta dan tuni ta saka bra and pant, ba damuwar Anna na ɗakin ta yar da bathrobe din ya ragu da ga ita se pant da bra ta saka rigar, ba ƙaramin kyau da haska ta rigar yayi ba gashi ya mata cif cif kamar a jikin ta aka kera ta.

 

English gown ce maroon Kamar yadda ta bukata, fish tail gown ce da aka yi wa tattara da milk din abu a gaban ta, duwatsu masu kyau aka yi pattern dasu yan kaɗan se abin ya bada kala sosai, milk veil tayi Rolling se takalmin ta maroon and milk haka ma purse din sa.

 

Gaba daya se ta fito kamar ba bahausa ba domin dai se tafi kama da Larabawan dubai ɗin nan da basu da haske sosai, turare ta ɗauka ta fara feshe jikin ta, ita dai Anna bata Kuma kula ta ba se bathrobe din da ta yar ta dauke ta kai toilet, ganin abin nata ya fara yawa yasa ta kwace perfume din hannun ta ta nuna mata ƙofa tana hararar ta.

 

Dariya tayi ta matso ta Rungume Anna tare da pecking din ta a kunci da goshi kana ta fice daga ɗakin da sauri, itama da sauri tabi bayan ta tana kiran tazo taci abinci sedai tuni ta nufi entrance tana faɗin

 

“Am full Anna, Will take launch when am back”.

 

Bata Hana ta ba dan tasan tun da tace haka ba ci ɗin zata yi ba.

Wata dunƙulalliyar milk din sport car ta buɗe ta shiga tare da bata wuta ta nufi gate, abin mamaki tun kan ta ƙaraso gate ɗin ya buɗe kan sa tana kuma ficewa ya koma ya rufe rufe…………………”.

 

 

 

.TAWA SOYAYYAR

 

 

“”You can’t afford to miss…stay tuned”””.

 

 

%%*Dedicated to my patronizers, my lovers and my sweethearts, ANJANE PAID GROUP MEMBERS, love you dearly

 

 

 

°°2°°

 

 

 

_Duk da tana fargabar kar taje ya riga ya tashi amma hakan be hana ta maming wakar da ta saki a motar ba, gudu kawai take falfalawa kan titin su har ta fice daga unguwar, sannu a hankali take murza staring tana yi tana duba bakin fashionable wrist watch din ta.

 

Minti talatin ya kai ta inda ta nufa, tun daga nesa ta ƙurawa wajen ido cikin son ganin yana nan ko kuwa, ajiyar zuciya ta saki haɗe da kyakkyawan murmushi tana kuma slowing motar har ta karasa junction din daidai lokacin da wani ɗan karota ya daga hannun sa alamun tsayarwa.

 

Itace ta gaba gaba a motocin da suka tsaya inda ta tsura masa ido tana kallo kamar wata sabuwar warkewar makanta yayinda farin ciki ya cika mata rai, ji take kamar ta dawwama a haka tana kallon kamilalliyar fuskar sa me cike da kwarjini.

 

Tun da take bata taɓa ganin ƊAN KAROTA fari ba se a kan shi, ta kan dai ga masu ɗan haske kaɗan, amma fari kamar shi bata taɓa gani ba.

 

Ba hasken sa ne ke ruɗar ta ba tunda itama dai fara ce, kamewa, kwarjini hadi da kirar sa ta jarumai su suka tafi da ita har yasa ta fola masa batare da ta sani ba, lokacin da yayi magana kuwa bata san sanda ta sake ware manyan idanun ta a kan sa ba, lion voice gare shi ba wai siririyar murya ba kamar wani mace, Muryar sa me amo ce wadda tun da ta shige mata kunnuwan ta sa ta dena jin dadin sautin kowane namiji in har ba shi ba.

 

Kayan jikin sa, yellow ɗin riga da bakin wando ba karamin kyau suke masa ba tun bare ma bakar hular kan sa da ta sake fito da hasken fatar sa, gashin girar sa na daga cikin abubuwan da tafi so a fuskar sa, wani irin shape ne da girar kamar wanda aka zauna aka jera gashin, cikar ta da kalar bakin ta me ƙyalli shike dada ƙawata fuskar nasa se ko low sajen sa da ba shi da cika an gyara shi ya yi kyau a fuskar.

 

“Ya Rabb ka mallaka min wannan bawa naka a matsayin mijina, ya Allah this is all I want and ask from you, ya hayyu ya qayyum fulfil my dream”.

 

Haka ta faɗa a bayyane idanun ta na cika da hawaye tsabar yadda son sa yayi mata kaka gida a rai.

 

Ƙwanƙwasa mata glass din da aka yi yasa ta farga har lokacin kan titi take, gashi tuni an sake hannu amma tayi blocking mutane ana ta horn amma bata ji ba, kallon sa ta sake yi har lokacin dai yana jingine jikin abin nan na tsayuwar yan karota dake tsakiyar titi, da kyar ta janye idanun ta daga kansa ta maida jikin window ɗin da har lokacin ake kan ƙwanƙwasa mata, jin dadin ta daya shine motar tinted windows gare ta so ba Wanda ze San me ta tsaya yi cikin motar.

 

Sauke glasses din tayi yayinda tayi arba da wani bakin dan karota (me irin kala ta kenan gashi tubarkallah mummuna dashi idanun nan jawur dasu kamar zasu zubda jini, ita wallahi firgita ma taso yi se Muryar sa ce tasa ta gane mutum ne ba dodo ba .

 

“Madam koma gefen titi ki kashe mota domin kinyi laifi”.

 

Kallon sa tayi jin rainin hankalin da yake kawo mata, kamar ita Afiya babyn Papah wani banzan dan karota ze cewa tayi laifi, ha ta buɗe baki zata masa tsiwa se kuma ta tuna ai DREAM MAN din ta na tsaye se kawai tayi as he said.

 

Tana parking ta kashe motar tare da buɗe side din ta ta zura ƙafar ta waje yayinda shima dan karotan ya zagaya bangaren ta cikin son blackmailing din ta ganin ta yarinya ga kuma ƙatuwar motar da ya ganta da ita.

 

“Madam kin karya mana doka kinyi parking a kan titi so zamu tafi dake office din mu dan se an ciki tara”.

 

Fitowa tayi gaba ɗaya ta tsaya jikin motar ta shiga bin dan karotan da kallon me kake nufi

 

“Excuse me malam, wane irin parking a tsakiyar titi kuma, ina ku kuka tsayar damu da hannu?”.

 

Cikin kwarewa da iya shirya makirci dan karotan ya haɗe rai

 

“Ko da muka tsayar da ku ai mun bada hannu amma fiye da minti goma baki motsa ba haka kuma ko da muka tsayar da ku ai kin riga kin haura layi dan haka ki buɗe mota in shiga muje headquarter din mu”.

 

Hararar sa tayi tana tsuke baki

 

“Wannan ne kuma baze yiwu ba ehe, kar ka ganni yarinya kace zaka min dabara malam”.

 

Kasa da murya yayi kamar ba shi ne yanzu ya gama daga murya ba

 

“Tun da baki son zuwa office to a sauƙaƙe ki kawo dubu biyar dan in muka je office se kin Kashe kusan dubu Ashirin wallahi”.

 

“Kai sisi da ba zan biya ba dan banga laifin da nayi ba, ni muje office din naku ma ɗin kawai”.

 

Gaba daya se taji ranta ya ɓaci, dama haka yan karotan suke da sharri da ƙirƙirar karya?, Kenan shima dream Man ɗin nata haka halin sa yake tun da ɗan karota ne kenan.

 

“Me kake yi ne a nan tun ɗazu Salihu?”.

 

Dan karotan da ya tare Afiya da aka kira da Salihu tuni ya shiga sosa kai yana ɗan yake cikin son basarwa

 

“Ah ba komai Oga kawai dama ina mata maganar ta dena tsaya wa tunani a kan titi shine…….”.

 

Da sauri Afiya ta katse shi jin abinda yake faɗa, da farko hankalin ta ya dauku ga kallon Man ɗin ta ne sedai kuma jin yadda salihun ke karya alamun baya so a san me yayi yasa ta dawo hankalin ta

 

“Karya yake yi, cewa yayi wai na yi laifi nayi crossing line Kuma nayi parking kan titi so wai in bada dubu biyar”.

 

Ta karasa faɗa tana hararar Salihu da yayi tsumu tsumu gaban Ogan nasa

 

“A wace dokar aka ce a kama wanda mota ta mutan masa a kan titi Salihu, wa ya baka umarnin karbar kudi a hannun me laifi, duk girman laifi ko kankantar sa Ina office ya kamata a kai shi?”.

 

Murya na rawa Salihu ya shiga bada haƙuri

 

“Ayi haƙuri Oga, insha Allah baza’a kuma ba”.

 

Cikin takun sa ya soma barin wajen yana faɗin

“Dole ka karɓi hukunci Salihu domin itama da laifin tayi ba hakuri zata bayar a kyale ta ba, barin irin ku kuma sake gurbata doka ne”.

 

Wani irin sabon shauƙi taji ya cika ta har kamar ya mata yawa, farin cikin kusan abu uku, shi ɗin ba gurbataccen jami’i bane, taji Muryar sa sosai , ga kuma farin cikin ganin sa dab da ita.

 

Da wannan farin cikin ta kai wajen aikin ta inda take aiki a Companyn Papah matsayin accountant dan accounting tayi degree din ta.

 

Yau kowa ya kalle ta yasan tana cikin farin ciki maɗaukaki domin dai fara’ar ta ma ta zarce ta kullum duk da dai dama ba wai miakila bace ita , ita ɗin me fara’a ce da haba haba da jama’a sedai akwai tsiya haka kuma bata san wulaƙanci.

 

Ƙarfe hudu ta tashi aiki ba dan lokacin tashin tayi ba sedan ta gaji a cewar ta, sanin bata iya jure zama ta wuni a waje ɗaya da sunan aiki yasa Papah ya dauki wani accountant daze dinga yin aikin duk sanda bata zo ba ko in tazo ta gaji se yayi substituting din t duk da cewa kusan accountants biyar gare su sedai ita ce chief accountant gaba ɗaya.

 

Tana gama daidaita motar ta fita hannun ta riƙe da purse ɗin ta, da gudu gudu ta nufi entrance din falon yanzu ma sunan Anna a bakin ta tana kira, kiciɓis tayi da Anna a kofar falo wadda jin yadda Afiyar ke kiran ta yasa ta nufi wajen tana faɗin

 

“Kai ni zainab na ga ta kai na, wannan ƴa in ba gani tayi suna na ya kare ba hankalin ta ba kwanciya ze yi ba”.

 

Fadawa jikin Annar tayi tana ƙyalkyale dariya tare da ƙanƙame ta

 

“Ke lafiyar ki kuwa, wannan irin dariya haka kamar wadda ta shaki laughing gas?”.

 

Zama suka yi kan kujera ta sake mannewa Annar

 

“Ina farin ciki ne Anna ta, am over joyous my Anna”.

 

Gyara zama Anna tayi tare da tallabe kunci

 

“Maza bani na sha ƴa tagari, faɗa wa Annar ki tun kafin curiosity ya Kar ta”.

 

Seda ta riƙo duka hannayen Anna guda biyu sannan ta faɗa mata

 

“Na gan shi yau ma Anna, har ma magana da yayi a kaina, kuma a kusa dani ya tsaya, Anna dadi, wayyo Allah na daɗiiiiiii”.

 

Ta faɗa tana sake fadawa Anna a jiki, zugum Anna tayi cikin damuwa, tun da suke rayuwar su kullum cikin farin ciki suke batare da wata damuwa ba, se gashi rana tsaka Afiya na neman sata cikin damuwa da tashin hankali.

 

Numfashi ta sauke tare da ɗago Afiyar daga jikin ta kana tayi magana cikin serious voice

 

“Zauna sosai muyi magana Afiya”.

 

Jin yadda Anna taci serious yasa itama ta zama serious din ta bata hankalin ta

 

“Tun da kika taso baki taɓa neman abu kin rasa ba Afiya, Papahn ki, Ammar da ni muna iya kokarin mu wajen ganin baki rasa komai ba, duk abinda kika nuna kina so hankalin mahaifin ki da na dan uwan ki baya taɓa kwanciya har se sun tabbatar sun baki shi haka nima, yanzu kuma haka kawai kwatsam se ki tashi ki jajibo abinda bana tunanin zaki taɓa samu, me yasa Afiya?”.

 

Jiki a sanyaye take kallon Anna dan bata gane me take son cewa ba

 

“Anna ban gane me kike son cewa ba, nayi wani abu ne da be dace ba?”.

 

“Ki fahimce ni yarinyar kirki, ba ina nufin wani abu bane a rayuwar ki, a kullum I want the very best of all things for you, haka ma your dad and brother, you know ba zan yi abu dan na bata miki ba ko na ganki cikin kunci ba”.

 

Gaba daya se Afiya ta daburce, me tayi da zafi haka da Anna ke irin wannan kalaman, ita kam tayi abinda ya bata musu rai ne ko kuwa tayi ba daidai bane, a rayuwa taki jinin abinda ze taɓa ran mutanen nan uku da duk duniya bata da wanda suka fisu, duk san da take yiwa abu zata iya haƙura dashi a kan su, ba abu ba hatta rayuwar ta zata iya bayar wa saboda tasu.

 

“Ina nufin ki bar batun wannan dan karotan Afiya, sam be dace dake ba, shi ɗin ba kalar ki bane ba kuma irin tsarin mazan ki bane, dan Allah ki manta dashi kinji daughter”.

 

Wani irin kallo ta shiga bin Anna dashi, akan me zata ce ta rabu dashi, meye dashi da yasa be zama kalar ta ba, ko kuwa dan shi ɗin talakane shine zata ce ba tsarin mazan ta bane, to ita kuma shi ta zaba, shi take so shi kuma zata aura at all cost.

 

“Dan yana talaka shiyasa ya zama ba kala ta ba Anna?, Ko kuwa dan shi dan karota ne yasa be zama cikin tsarin maza na ba?”.

 

Da sauri Anna ta shiga girgiza kai tare da matsowa kusa da ita sosai ta riko haɓar ta

 

“Nima talaka ce a baya Afiya, ni ma da ba kowa bace har seda kakannin ku suka tsamo ni daga ƙangin talauci, su suka inganta rayuwa ta suka rufa min asiri haka ma mahaifin ku ya dora bayan babu su dan haka in har ni din me hankali ce be kamata na zagi ko kyamaci talaka ba.

 

Ina batu ne akan rayuwar ki Afiya, ke ɗin yar gata ce da ta taso cikin jin daɗin rayuwa, ko me kike so shi ake miki, baki san babu ba, baki san wahala ba, ki kalla fa Afiya hatta gyaran gado ni nake miki, wankin toilet da yake ba wani aiki ba baki iya ba, banda dafa ruwan tea ba abinda kika iya Afiya, Papahn ki yace be yarda kiyi girki ba tunda Allah ya hore masa abinda ze ɗebo me miki, common gyaran wardrobe baki iya ba, ki kalli kan ki fa, hatta wanka se kince in cuda ki, uhm, Fito da kaya sometimes duk se na miki, a haka zaki yi wa kan ki fatan auran dan karota wanda yayi depending kan ɗan albashin da yake samu da be taka kara ya karya ba, wanda a cikin sa yake rayuwar yau da kullum yake kuma kula da iyayen sa dan nasan ba ze rasa ba, taya kike tunanin rayuwa zata yi miki kyau a tare dashi bayan bashi da karfin nemo me yi miki duk irin abinda kika saba, kinga kuwa ai babu zaman lafiya domin ko da ace ya zauna dake da sauran halin ki baze iya zama dake da rashin iya girki ba, domin bature kan sa yace the way to a man’s heart is through his stomach, to taya kike zaton zaki samu zaman lafiya da soyayya?.

 

Ki hakura ki manta da wannan yaron kinji, ga nan yaran abokan Alaji Karami dake masifar son ki banda ragowar samarin waje da suka isa gani suka tara ko aka tara musu, ki daure ki manta dashi ki zabi daya a cikin su don a nan ne kawai zaki samu irin rayuwar da kika saba ki ka kuma tashi a cikin ta, ina fatan kin fahimce ni”.

 

Duk wannan dogon sharhi da bayanin da Anna ta Gama yi ita ba abinda ta fahimta face sentence uku masu barazana ga rayuwar ta, ‘ki manta dashi’, ‘ki rabu dashi’, ‘be dace dake ba’.

 

Inaaaaa, sam baze yiwu ba, haka ta faɗa a ranta kafin ta watsawa Anna idanun ta da suka fara tara ruwan hawaye

 

“Kin fi kowa sanin wace Afiya Anna, I love with all my heart and life, I hate with my whole heart and soul, duk dayan da nayi a ciki bana iyawa da sauki, shine ma dalilin da yasa ban kula kowa dan bazan juri breakup ba, shine Kuma dalilin da yasa nake da yawan yiwa mutane uzuri dan bana son in tsane su, dan duk wanda na tsana kuma to na gama rufe babin sa a rayuwa ta, kiyi haƙuri amma iya gaskiya itace ina son sa, ina masa so da dukkan zuciya ta haka ina fatan kasancewa dashi, ki min addu’a kawai”.

 

Tana gama fadar haka ta zame hannayen ta daga na Annar ta shige bedroom din ta, da kallo ta bita har ta shige kafin ta daga hannu sama ta shiga addu’a

 

“Ya Rabb ka kawo mana lamarin nan da sauki kayi wa yarinyar nan zabi nagari, ameen ya Allah”……………….!

 

 

 

 

 

Ouummey

 

Guess what 😌, lack of Commenta will make me privitized this book, I know many will buy coz is not a mere book that you can remove an eye on and my account will add on heaviness 😁😋, the choice is yours🤷

 

Ouummey 003

^      ®••••°°°°••••®°°°°°°°°°^°°°°°°  °° °°.

°   ®°°°°°•••••°°°°®.             °° °°.

^             °.   °    ^     °   ^    °°°.          °° °°.

°.     ^  .   °.      °°°.   ^      °° °°.

°.             .    °°°.                °° °°.

^          °.         ^          .     . .                °° °°.

O.                                             °° °°.

 

ΩΩΩ**TAWA SOYAYYAR**ΩΩΩ

 

_(love story 2023)_9

 

~January 2023~

 

© Ouummey

 

*Wattpad @ouummey*

 

°°°From the experienced writer of SARAKI, BANI DA LAIFI & more, here comes wat a mind blowing story of ★★TAWA SOYAYYAR★★.°°°°

 

 

“”You can’t afford to miss…stay tuned”””.

 

 

%%*Dedicated to my patronizers, my lovers and my sweethearts, ANJANE PAID GROUP MEMBERS, love you dearly 💞💞 *%%.

 

♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣

 

°°03°°

 

_Harara ta watsawa kayan da ta ci karo dasu da shigar ta dakin, se lokacin ta tuna ta cewa Anna ta bar mata kayan zata gyara wanda ita ta faɗa ne kawai amma ba zata iya wani gyara wannan uban kayan ba.

 

Na jikin ta ta cire ta watsa su kan yan uwan su sannan ta shige toilet, wanka da alwala tayi ta fito ɗaure da guntun towel din da be gama sauka kan cinyoyin ta ba, gaban mirror ta zauna ta gyara jikin ta sannan ta saka wani guntun wando da riga kana ta zurma ƙaton hijab din ta ta tada sallar la’asar da tayi missing.

 

Tana idarwa ta cire hijab din Shima tayi watsi dashi gefe ta fita zuwa falo, zaune ta tadda Anna Kamar yadda ta bar ta tagumi hannu bibbiyu, da alama tayi zurfi cikin tunani dan bata ma lura da fitowar ta ba.

 

Fada wa kan ta tayi kamar wata yar baby tana kwaɓe fuska

 

“Anna custard plsss”.

 

Se lokacin Anna ta dawo daidai tare da sa hannu ta ɗago Afiya da ta kanannade ta, cikin yanayin damuwar da ta ke ciki ta mata magana

 

“Ba na koya miki yadda ake yi ba, maza je kiyi in gani in kin iya”.

 

“Amma na gaji fa Anna, nikawai kiyi min dan Allah”.

 

“Ashe kuwa ba zaki sha ba”. Anna ta fada tana kauda kan ta gefe bayan ta janye jikin ta daga danne tan da Afiya tayi, jikin ta a sanyaye ta sake riko hannun Anna dan ta tsani ganin ta cikin damuwa da rashin walwala

 

“Ki kwanar da hankalin ki kiyi min addu’a kinji Anna, insha Allah Alkhairi me tarayya ta dashi, ki koma normal kiyi watsi da duk wata damuwa pls, kin San bana son ganin ki moody ko”.

 

Ajiyar zuciya Anna ta sauke tana faking smile tare da riko kumatun Afiya duka biyu

 

“In Sha Allah zan taya ki da addu’a daughter, in da alkhairi Allah ya tabbatar ya kai mu lokaci musha biki in Kuma babu Allah ya watsa lamarin yayi miki zabi na gari, tukunna ma ya sunan jikan nawa?”.

 

“That’s my Anna, Allah ya amsa addu’ar ki ya bar min ke har abada”. Ta faɗa all her teeths out ganin fara’a a fuskar Anna se kuma ta da yatsa a baki alamar tunani kana ta juya ta dube ta

 

“Ni fa ban ma san sunan sa ba Anna, me kike ganin sunan sa ze zama?”.

 

Fito da ido waje Anna tayi kafin ta saki dariyar jin shirme irin na Afiya, yanzu duk ma ikirarin son da take yi tana masa ashe ko sunan sa ba ta sani ba

 

“Yanzu duk wannan soyayyar ashe ko sunan masoyin ba’a sani ba, lallai my Afiya is a lover girl in her dream”.

 

Buga ƙafafu ta shiga yi a ƙasa

 

“Not only in my dream har da reality, ni ai ban san sunan sa bane amma naji wani yaron sa ya kira shi da oga, could it be his name is Oga Anna?”.

 

Dariya Anna ta shiga yi kamar zata shide, lallai yar ta ta ta cika auta, ji fa wani wauta, ko a ina ta taɓa jin sunan mutum oga oho.

Tashi tayi ta canja kujera tana juyawa Anna ƙeya ganin ta maida ita wata shashasha, seda tayi dariyar ta ta gama kafin ta koma kusa da Afiya ta zauna

 

“Kinga let’s be serious, tayaya za’a ce kina son mutum amma baki san sunan sa ba Afiya, ai wannan shirme ne, and again a ina kika taɓa jin real name na mutum wai Oga?, Hakan da kika ji an fada masa girmamawa ce being superior than Wanda ya fada ɗin, kar ki je wani wajen kiki ance oga kice sunan mutum ne wallahi dariya za’a yi miki”.

 

“Ai dai ban sani bane kuma shine kawai se kiyi ta min dariya?”.

 

Ganin yadda ta fara matso hawaye yasa Anna ta shiga lallashin ta dan kadan daga aikin ta ta fara kuka

 

“Anna is sorry, Amma dai ya kamata ki nemo sunan sa da, bakya tunanin papahn ki ya tambaya ko Ammar?”.

 

Shiru tayi cikin yadda da batun Anna, lallai ya kama ta ta san sunan sa amma ta yaya, shine bata sani ba, amma ai ga anna ta san she’ll find a way for her.

 

“Ya zanyi Anna?”.

 

Shiru Anna tayi cikin nazari kafin kuma ta sauke numfashi

 

“Forget about it, yanzu tashi kije ki hado custard din ki Sha, we’ll talk about it later”.

 

Bata fuska tayi dan ba haka taso ji ba sedai ganin yadda annar ta hade rai yasa ta mike zuwa kitchen Wanda see lokacin na lura da shi cikin falon.

 

Tana shige wa anna ta sauke numfashi cikin tausayin yarinyar, Allah ya gani ba’a son ranta ta ke hirar yaron ba sedai ganin da gaske Afiyan take yi a kan sa yasa ta biye mata, kamar yadda ta faɗa addu’a kaɗai zata mata dan a yanzu kam ba ta da yadda zata yi da Afiyan.

 

Ihun da ta fasa daga kitchen din yasa ta bita da sauri dan ganin lafiya, burki ta ja daga bakin kofa ganin yadda a mintuna kadan kitchen din ya koma upside down ba kamar yadda ta bar shi ba, da idanu ta shiga bin kayan kitchen din, tukunyar da take damun a ciki ta fadi can gefe komai ya zube.

Gefe ɗaya kuma gwangwanin madara ne shima a ƙasa kusan rabi ta zube, haka shima sugar da ta ɗebo a cup, cup din yayi gefe haka shima sugarn yayi nasa wuri, komai dai ya zauna da duwawun sa, dan hatta garin custard din ya watse.

 

Ɗago idanun ta tayi daga kallon kitchen din ta sauke kan Afiya, da fuskar ta d ruwan hawaye ke gudu ta fara cin karo se kuma hannun da ta riƙe tana jijjigawa, da sauri ta shiga tsallake kayan ta karasa gare ta tare da riko hannun Afiya bayan ta kashe gas ɗin da har lokacin ke ci a kawai.

 

Yadda hannun yayi jajir yasa ta san ƙonewa tayi shine ihun da take yi, jiki a sanyaye Anna ta ja hannun ta zuwa falo tare da zaunar da ita kan sofa it’s kuma ta wuce bedroom din ta dake Opposite dana Afiyan, ointment ta dauka ta koma ta shiga shafa mata a gurin da ta kone ita  kuma se faman shuuu take yi da baki hawaye kuwa kamar wadda aka bude fanfo sun ki daina zuba.

 

Ita kanta Anna hankalin ta a tashe yake internally dan bata san me zata fadawa Alaji Karami ba, a yadda ya tsani ko kuda ya taba masa jikin Afiya se kuma gashi ita ta mata sanadin ciwo a jiki, dana sani mara amfani ce ta rufe ta dan tasan faɗa kam se dai ta toshe kunne Amma ze yi shine har se ya gaji dan a kan Afiya idanun sa rufewa suke rufe.

 

Tagumi ta zuba cikin rashin mafita tana kallon yadda ta jingina jikin kujera idanun ta rufe tana sauke ajiyar zuciya

 

“Am sorry darling, ba na aika ki kitchen bane dan ina so ki kone, ina so ne ki zama responsible lady Kamar kowace budurwa sedai yanzu nadamar hakan nake dan da bance ba da baki kone ba, am sorry kinji, bari na faɗawa Alh ƙarami ko Ammar suzo muje hospital”.

 

Buɗe idanun ta da suka yi ja tayi tana kallon yadda gaba ɗaya anna tayi wani iri, ta sani ba komai ya dame ta ba kamar zafin da ta san zata ji da kuma fadan da papahn ta ze yi

 

“Meye laifin ki Anna?, So da kauna ta da kike yi kamar yar cikin ki ko kuwa don gyara rayuwa ta da kike ƙoƙarin yi?. Look Anna Baki da wani laifi, ko ƙanƙani dan kuwa abinda duk uwa zata yi wa yar ta kenan, You trying to cike gurbin rashin Nanah gare mu ne and I appreciate every bit of it, pls Anna Kar ki faɗawa papah kinji, you know se ya tashin hankalin sa da na kowa ma, har yanzu gani yake ni ɗin yarinya ce while am now grown up, gashi har na Fara soyayya ma kuma soon zan yi aure ko my Anna?”.

 

Ta ƙarashe teasingly duk dan ta sa Anna manta was da komai hankalin ta ya kwanta.

 

Dungure mata kai Anna tayi cikin tsananin so da kaunar da take wa Afiya, ita kan ta ta sani tana kaunar yarinyar irin yada take tunanin da Allah ya bata haihuwa to fa ba zata so abinda ta haifa ɗin ba kamar yadda take son Afiyan.

 

Yarinyan na da shiga rai, ga hankali da nutsuwa da hangen nesa batta dai da wauta da gabun ta sometimes Amma kam bata da wata matsala, in tana tare da ita har manta wa take bata da wani alaka na jini da su dan yarda take nuna mata basu da wani wanda ya fita.

 

“Come here let’s watch our series, it’s already five minute past five”.

 

Da sauri ta sauka kan rug kusa da Anna tare da kwanciya kan kafaɗar ta inda ita kuma ta maida hankali wajen canja musu channel zuwa zee  world da ake series ɗin sajnool hoob, yadda take son series din yasa Anna itama ta fara kalla se kuma taga tabbas akwai kyau, duk da jigon labarin akan soyayya ne amma kuma akwai gwagwarmaya sosai a ciki, kama daga cikin gida har zuwa waje.

 

Nan suka shantake wajen kallo kowane yayi shiru kamar baya wajen yayinda hankulan su gaba ɗaya ke kan Tv.

 

Seda aka gama sannan Anna ta tuna bata mayi dinner ba hakan yasa ta bar Afiya gaban Tvn ita kuma ta wuce kitchen sedai tana wucewa itama ta kashe kallon ta kwanta ringingine tare da jawo phone din ta ƙirar Samsung latest version, photon da ta buɗe wanda tayi masa batare da ya sani ba lokacin da yake kusa da ita yana magana da Salihu.

 

Kura wa screen ɗin ido tayi kamar shi ɗin take gani a zahiri, yadda tayi zooming photon kai kace za’a ambace shi ya amsa, a hankali ta kai hannu ta shiga shafa kyakkyawar fuskar sa, tun daga kan girar sa ta fara zanawa kamar me sketching, a haka a haka har ta gangaro kan dogon hancin sa da yake nan ba siriri sirit ba sedai kuma ba me fadi bane.

 

Pinkish brown lips din sa masu ɗan tudu kaɗan ta ƙurawa ido tana admiring shape din su, lokacin da ta sauke hannun ta kan low cut gemun sa kuwa seda ta lumshe idon ta saboda yadda ya mugun captivating mind din ta, ba komaki yasa ba se yadda gashin yake bakikirin kuma a gyare ya shiga har ta cikin haɓar sa da ta ɗan loɓa.

 

Fiye da minti hudu idanun ta na rufe kafin ta buɗe har sun ɗan canja kala saboda tsabar yadda take jin sa a ranta, ajiyar zuciya ta sauke tare da aje wayar batare da tayi exiting daga gallery din ba ta wuce toilet, gaban mirror ta tsaya tana ƙarewa kan ta kallo kamar wadda ke neman wani abu a jikin ta, kwata kwata hankalin ta baya kan kallon fuskar ta wadda tayi reflecting ta mirror din, tunanin ta kawai yadda za’a yi ta gan shi, so take kawai ta san sunan sa domin ba zata iya jurewa ba, sanar da papah da ya Ammar zata yi kawai asan abin yi dan zuciyar ta na gab da yin exploding, sedai bata san tayi maganar batare da ta san sunan shi ba dan kar su ɗauke ta wata mara hankali suyi mata dariya kamar yadda Anna tayi.

 

Ruwa ta watsawa fuskar ta tasa towel ta fito, kan bed din ta ta tadda Anna Zaune hannun ta riƙe da wayar Afiyan tana kallo, kusa da ita ta zauna hakan yasa Anna ɗagowa ta dube ta tana haska mata screen ɗin wayar

 

“Shine wannan ko?”.

 

A sanyaye ta daga mata kai tare da yin rau rau da idanun ta da suka cika da hawaye

 

“Dan Allah anna ki faɗa min taya zan san sunan sa, kinga bana so na fadawa papah maganar sa bayan ko sunan sa ban sani ba kuma Allah kullum ƙara son sa nake”.

 

Idanun anna na kan screen ɗin tana kallon sa, dan kyau yaron yana da kyau irin me fizgar hankali, ko daga cikin wayar nan tana iya hango tsantsar kwarjini da kamala a tare dashi, nutsuwar sa bata buya ba ko a cikin hoto, lallai baya ga laifin Afiya ba da ta kamu da son sa dan ta ko ina yakai a so a kaunace shi sedai matsalar ba daga nan bane.

 

“Kinji Anna kice wani abu mana”.

 

“Kafin ince komai se kin tashi munje kin ci abinci dan yau wuni guda baki ci abinci ba, na zuba miki ido inga iya gudun ruwan ki se naga ke ko damuwa baki yi ba, in kina son sanin sunan ki tashi muje”.

 

Ba dan taso ba sedan ba yadda zata yi ta mike zuwa falo, abincin ta zuba mata dan kadan sedai ita a hakan ma bata fuska take yi dan a cewar ta yayi yawa, haka dole ba dan taso ba ta tuttura shi gaba ɗaya dan yadda ta haɗe rai ta ga alamun da gaske take.

Add Comment

Click here to post a comment