BBC Hausa Labaran Duniya Da Dumi Duminsu
BBC Hausa Labaran Duniya Da Dumi Duminsu
Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta – INEC ta ayyana Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe.
Ƙananan hukumomi uku ne suka yi ragowa ba a bayyana sakamakonsu ba a jihar Adamawa, waɗanda suka haɗa da Michika da Song da kuma Fufore.
KARANTA CIKAKKUN LABARAN DUNIYA BBC
Fafatawa ta fi zafi tsakanin ‘yan takara biyu, gwamnan jihar mai ci da ke neman tazarce Ahmadu Umaru Fintiri na PDP da kuma Sanata Aisha Dahiru Binani da ke takara a jam’iyyar APC.
An tafi hutun cin abinci kuma an amince za a dawo da misalin karfe 10 na dare.
Hankula na ci gaba da karkata kan jihohin da ba a bayyana sakamakon zaɓen gwamna da na ‘yan majalisa da aka gudanar a jiha Asabar, wanda kuma Adamawa na cikinsu.
Alƙaluman da hukumar zaben Najeriya INEC ta tattara sun nuna cewa Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya kama hanyar samun nasarar zama gwamnan Kano.
Ƙaramar hukuma ta ƙarshe da aka bayyana ita ce Dala, wacce sai da aka tura jami’an tsaro na musamman domin taho da sakamakon, saboda matsalar tashin hankali.
Ga yadda sakamakon na baya-bayannan nan ya kasance
Ƙaramar hukumar Dala
ADP 607
APC 28,880
NNPP 54794
PDP 239
Ƙaramar hukumar Nasarawa
ADP 505
APC 38,952
NNPP 53,434
PDP 480
Ƙaramar hukumar Birni da kewaya (Municipal)
ADP 1,297
APC 30,264
NNPP 47,351
PDP 359
Ƙaramar hukumar Gwarzo
ADP 78
APC 26,881
NNPP 25,419
PDP 377
Ƙaramar hukumar Bebeji
APC 14,782
NNPP21.001
PDP 254
Ƙaramar hukumar Fagge
ADP 235
APC 17,452
NNPP 23,015
PDP 540
Ƙaramar hukumar Ungoggo
ADP 378
APC 24,644
NNPP 33,111
PDP 819
Ƙaramar hukumar Tarauni
ADP 417
APC 21,276
NNPP 31,333
PDP 321
Ƙaramar hukumar Gwale
ADP 448
APC 21,548
NNPP 39,460
PDP 638
Hukumar zabe a jihar Kwara ta sanar da Abdulrahman Abdulrazaq na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Hukumar zabe a jihar Gombe ta sanar da Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Hukumar zabe a jihar Jigawa ta sanar da Umar Namadi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Hukumar zaɓen Najeriya na shirye-shiryen fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnoni a wasu jihohin Najeriya da aka gudanar ranar Asabar.
A jihohin Adamawa da Bauchi hukumar zaɓen ta shirya tsaf domin fara karɓar sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomin.
A yau lahadi an ci gaba da kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisaun dokokin jihohi a mazaɓar VGC a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Hukumar zaɓen ƙasar ce ta ce za a gudanar da zaɓen ne a yau kasancewar ba a samu gudanar da zaɓen a irin waɗannan mazaɓu ba.
A sanarwar da hukumar INEC ta fitar ta ce ba a samu gudanar da zaɓen a wannan mazaɓa ba kasancewar masu kaɗa ƙuri’a sun turje wa ma’aikatan da aka tura.
Sai karfe 2 na rana za a soma sanar da sakamakon zabe a jihohin Kano da Kaduna
Hukumar zaben Najeriya a jihohin Kano da Kaduna sun bayyana cewa sai karfe biyu na rana za su soma sanar da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jiya Asabar.
Sakamakon zabbukan gwamnonin jihohi
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an harbe wani tsohon kansila a bisa zarginsa da sace akwatin kaɗa ƙuri’a.
Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar ɗin nan.
Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.
Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.
Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa a Getso.
Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara.
Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.
Ita ma a na ta ɓangaren, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.
- Zaben Jahar Kano Abunda Ke Faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Zamfara abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Sokoto abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Adamawa abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Gombe abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Lagos abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Borno abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Katsina abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Kebbi abunda ke faruwa halin yanzu
- Zaben Jahar Yobe abunda ke faruwa halin yanzu
Wannan shafi yana kawo muku sakamakon zaben Nigeria.
Rumfar zaɓe mai lamba PU 47 da ke Hausawa a Kano na da yawan masu rajista zaɓe 22.
Ya zuwa ƙarfe 9 na safe mai kaɗa ƙuri’a ɗaya ce kawai ta bayyana a rumfar.
Ita ma ta ce sai da ta taka sayyada tsawon kilomita huɗu kafin isa rumfar zaɓen kasancewar babu abin hawa.
Sakamakon Zaben Jahar Sokoto na 2023
Jami’an INEC na wucin gadi sun ja tunga a mazabar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, suna masu cewa ba za su karɓi kayan aiki ba har sai an biya su hakkokinsu na aikin da suka yi a baya.
Add Comment