Littafan Hausa Novels

Sakayya Hausa Novel Complete

Sakayya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SAKAYYA

 

( A touching heart story)

 

 

Written by gimbeeya

(Mss 1love

 

 

 

Page 1-5 !

 

 

 

 

 

 

Da sunan Allah me rahama me jin kai ,tsira d aminci su qara tabbata agun annabinmu Muhammad saw ,yacce na fara rubuta littafi nan Allah yabani ikon gamashi lapia Allah yasa mu amfana d saqon dayake ciki Ameen !!!!

 

 

 

————-tindaga inda yake zaune akan sallaya yake jiyo qamshin turarenta me dad’in qamshi da d’aukar hankali,riga d siket ne ajikinta na atamfa wanda yay matuqar amsar jikinta se d’an qaramin veil data yafa ,yayinda take qoqarin maqala jakarta tana cewa ” to nide na fita sena dawo ”

Kallon sama d qasa ISHAQ yamata yace “haba zahra’u shin kinmanta da cewa Ke matar aure ce ,yanzu da wannann shigar zaki fita,sannan inaso nasan ina zaki ???dannasan cewa ba inda kika sani a garinnan ,yau kwana nawa da Allah ya yayemiki jarabtar da ya d’oramiki ? Yanxu ….. aikafin ya rufe baki zahra ta dakatar dashi da cewa “Kaga ISHAQ dakatamin tsawon shekaru d’ai-d’ai har ashirin da uku bana ganin komi aduniyarnan se duhu,yanxu kuma d Allah ya yayemin se ahanani ganin duniya kafiso naita zama awannan gidan qasan!! Ina fama da murhu da ice wanda hayaqinsama kad’ai ya isa yamaidani gidan jiya,dan haka yanxu idona ya bud’e Kuma ba wanda ya isa ya hanani naga duniya ,duniya taganni,idan kaga dama ka zauna dani,inbakai niyyaba Kasan abunyi “daga haka tafice ji kake bammm taja qofa wacce takusa karyewa tinda dama qofar ta langa-langa ce .

Sadauki Omar Hausa Novel Complete

 

Wani irin hawayene me d’umi ya sauka a idon ishaq,zuciyarsane Ke masa wani irin suya,ahankali yadafe saitin zuciyarsa tare da rintse idanunsa,nan take kwakwalwarsa tafara tariyomasa rayuwar baya alokacin da ya Kyalla ido yaga Zahrau.

 

SHEKARU 8 DA SUKA WUCE…

 

Zaune suke ashagon d’inkinsu shida abokinsa sun duqufa akan aikinsu ganin sallah ta matso ga d’inkunan mutane ahannunsu,jin yatsaya da takun keken yasa faisal kallonsa inda yaga ya kurawa bakin shagonnasu ido juyowa yay domin yaga abunda ya d’aukemasa hankali,wannna makauniyar yarinyarce tareda qanwarta inda take riqe da hannunta yayinda d’aya hannun sandace take laluba hanya da ita,juyowa yay da kallonsa wajen ishaq yaga be d’auke idonsaba har seda suka wuce ,”kai abokina yanxu meye na qurawa makauniya ido haka ??”Faisal yafad’i yayinda yake kuma murzan kan keken d’inkinsa.

 

“Hmmm wlhy faisal bazaka ganeba yarinyarnan tana matuqar bani tausayi sosai,ba ilimi ba wata rayuwa me kyau ga makanta gata mashalllah kyakkyawa Amma ba idon gani ”

 

Batare da yad’ago yakallesaba yace “ishaq kenan duk yacce Kaga mutum kabarshi haka yacce Allah yaso yaganshi,komi Kaga mutum ya samu koya rasa ni’imace da Allah yamasa,Allah ne yasan manufar jaki dabe yishi da qahoba kai yacce take da kyannan daba makauniya bace Allah ne yasan…”aikafin ya qarasa ishaq yadakatar dashi “haba faisal kadinga kyautatawa d’an adam zato ni wallahi inaji ma nasamu matar aure ”

 

“Cafff !! Lalle ishaq bakada hankali makauniyar zaka aura,ai wallahi ko sarauniyar kyauce bazan aure taba wannan ai wahala zaka aura ana aure Dan ahuta taya mutum ze d’akkowa kansa wahala,yarinyarnan kuma tin da aka haifeta bata gani bare asa ran zata warke ”

 

Ishaq ne yace “koda haka zata mutu bata gani ni zan kula da ita har qarshen rayuwarta,faisal na dad’e ina tausayin zahra,seyanxu nagane cewa tausayin wani reshene daga cikin qaunarta,”

 

Faisal daya sandare saboda tsananin mamaki bayan makantarma qazamar yarinya wanda gidansuma bacin yau bare na gobe Amma ya lura abokinnasa yay nisa bayajin kira shiyasashi cewa “to Allah yabada sa ‘a”

 

Ranar wata asabar da yammaci sakaliya ,ruwan da akaine yasa unguwar sheshe dake cikin gari yin wani luffff,zaune inna hajara take tana tankad’en fulawa wacce sumayya qanwar zahra take wainar fulawa aqofar gida da magriba,sallama sukaji yaro yayi tare da cewa Wai ana sallama da zahra’u,inna hajara dake tankad’e d sauri ta d’ago kai dan maganar ta girgizata anyakwa gidannan aka turosa,dan koda wasa bawanda ya tab’a zuwa qofar gidan da niyyar yanason zahra kallon yaron tai tace “jeka cemasa wata zahran?,anyakwa nan gidanne?”

 

Jimmm kad’an yaron ya kuma dawowa yace “eh nan gidan ne yace zahra’u yayar sumayya ”

 

Ainan mamaki yakama kowa agidannan abunka da gidan cikin gari gidan yawa,da sauri inna hajara tashiga d’aki tace wa zahra’u ta tashi ana sallama da ita,seda gabanta yace rasss ahankali tace “inna waini ake sallama dani??”

 

Inna tace “eh,”maza kitashi nan danan inna tad’akkomata hijab tare da d’an shafamata powder da jambaki abinka da kyakkyawa seta qara wani haskawa ,innace tabata sandarta tare da mata jagora zuwa soro.

 

 

Har ta fito wajen ta tsaya batasan a inda yakeba d’aya gefen takalla tana “inayini?”ganin haka yasa ishaq saurin dawowa b’angaren yana “lapia lau,yake me hasken idaniya da kyan kallo ”

 

Murmushi tai dan tinda take arayuwarta ba atab’a yabontaba sedaima amata gori da itad’in makauniyace ,wani dad’i taji aranta tace “shin da gaske idanuwa sunada haske ?”

 

Yace “matuqar haskema ”

 

“Sedai bana gani dasu “tabashi amsa araunane

 

Wani abu yaji yadaki zuciyarsa yarda tai maganar amarairaice,had’iye abun yay yace “innace inasonki zaki amince ki aureni?”

 

Wani rass taji aranta,inna data lab’e asoro dan taji dame yazo kar acutarmata da ‘ya ganin bata gani aidataji ya ambaci kalmar aure nan take tai sujjada aqasa tana godiya ga Allah harda hawayen farinciki.

 

 

“Bawan Allah dan Allah inda wasa kake kagayamin,Taya mutum ze rayu da makauniya,nakasashiya Irina ,ba wanda ze iya d’aukan wannan nauyin se wanda suka kawoni duniya wato iyayena”

 

Ishaq gyara tsaiwa yay yace “zahra ba maganar wasa amaganarnan ked’in awajena tamkar kowa kike ,mutane Ke ganinki makauniya Amma aguna Ke rayuwatace amincewarki kawai nake nema ,kuma banso ad’au lokaci sosai ”

 

Nan danan zuciyarta tafara jeromata tambayoyi “Ashe dama za’asamu wanda ze sota??? Ashe dama ita d’in a idon wani tamkar kowa take ??? Ashe de itama zatai aure ?

 

Muryar sace takuma katsemata tinaninta inda yace “karki damu zanbaki lokaci ki tinani zuwa wnai satin zan dawo ”

 

Tace “tom badamuwa nagode ”

 

Murmushi yay duk d bata ganinsa yace “Nima nagode zahra se anjima ki kula da kanki ”

 

Harya juya zetafi tace “Amma meye sunanka?”

 

Ataqaice yace “ishaq mukhtar ”

 

Ahankali ta maimaita sunan ishaq yayinda take qoqarin shigewa gida,inda take ta maimaita sunan tana so ta tina ina taji sunan ,bade shine wanda rahila Ke mutuwar soba,rahilan datake wulaqantata take kyamarta tabbas inshine rahila zata gane cewa makauniya tafita tinda har takasa samun soyayyar shi Amma gashi yazo yana neman ta makauniyar datake kyama!!!!!

 

Share plx

SAKAYYA

( A touching heart story )

 

 

 

Written by gimbeeya

(Mss 1love

 

 

Page 5-10

 

 

 

Bayan shigar zahra’u gidane inna hajara ta tarb’eta da cewa “zahra’u Allah ya amsa addu’a ta Allah ya dubi marainiya,maza azo asiyomin alawa nai sadaka ”

 

“Wlhy inna haryanxu na kasa gasgata cewa ni akeso,kuma inna dagajin muryarsa me nutsuwane “zahra’u tafad’i yayinda take laluba kujera zata zauna.

 

Inna tace “nima wallahi na yaba da yaron ina yawan ganinsa ashagon d’inki yaro ne me zuciya ”

 

Sallamar sumayya ce takatse musu hirarsu tana “inna Wai  ishaq wajen wa yazo naganshi yanxu abakin lungu yana fita nikuma zanshigo ”

 

Murmushi inna tai tace “wajen ‘yar uwarki yazo cewa yana sonta kuma d maganar aure ”

 

Zaro ido sumayya tai tana “dan Allah “yacce tai maganar bazaka iya banbace farinciki bane ko kuma tsabar mamaki.

 

Inna tace “wallahi abun Allah kenan ”

 

“Lalle inna al’amarin Allah se shi,kinga ishaq ko bakiga yacce ‘yan mata Ke sonsaba saboda kwarjininsa da haibarsa,amma shikuma se Allah ya d’oramasa son yaya zahra “sumayya tafad’i tana murmushi

 

“Bade shine wanda zaliha Ke mutuwar soba??”muryar zahrace taji tamata wannan tambayar.

 

“Au kema kinsani wallahi shine waye besan yadda zahra ke sonshiba kullum setaje shagon d’inkinsu “sumayya tafad’i tana me jawo kwanon albasa zata fara yankawa.

 

Inna tace ” Allah kenan duk wulaqancin da zaliha kewa zahra segashi mutumin datake matuqar so shikuma ba wacce yake so kamar nakasashiyar data raina ”

 

Muryar kareematu suka jiyo tana “wace hirar ake ne??Wai waye yazo yana sallama da zahra’u mu abun ya d’auremana kai yau wace rana “kareematu ce tafito daga b’angaren su , wanda d’akinta yake jikin  katangar d’akin inna hajara abunka da gidan yawa.

 

Inna hajarace ta d’aga ido suka kalli juna itada kareematu tace “hmmm ai kareematu komi lokacine itama natane yazo ”

 

“Kice abun de da gaskene tasamu mijin aure “kareematu ta tambaya cike da mamaki.

 

Inna tace mata “Ehto abunde na Allah ne amma da alamun hakan ”

 

Ai nan kareematu ta tashi tashige cikin gida gayawa wannan gayawa wancen ,nan da nan magana ta yad’u cewa zahra makauniya ta samu mijin aure ,masu mamaki sunayi masu baqinciki sunayi masu farinciki sunayi….

 

 

—————————bayan wata biyu magana ta kankama Dan har yaturo manyansa,anyi magana tare da kawo kudi aka saka rana shekara guda,mijin kareematu shine qanin mahaifin su zahra da sumayya Dan haka shine waliyinta shiya amshi kudin,b’angare guda kullum soyayyar zahra qaruwa take aransa sau dayawa in suna hira yakan tambayeta yace “yanxu ace idonki ya bud’e me kike so kifara tozali dashi aduniya takan bashi amsa d cewa “inna ta sekuma qanwata sumayya da kuma mijina ishaq ,sune mutanen danake da burin ganin fuskarsu kafin nabar duniya duk da hakan ba lalle me yiwuba bane ” yakanyi murmushi yace “ba abinda yafi qarfin Allah ,kad’an daga ikon Allah ”

 

 

————kwanci tashi ba wuya shekara kwana,biki ya matso Dan yakasance yanxu saura sati uku,sedai ahalin da ake ciki ba maganar kayan d’aki ba labarinsa duk da ishaq yay qoqari wajen yimata akwatinta uku ,amma daga dangin mahafinta ba wanda yay qoqarin yimata kayan d’aki hatta sunusi mijn kareematu wanda shi akabawa kud’in auren be mata komiba,inna tayi kuka kamar ranta ze fita da jarin wainar fulawan da suke da wasu awakinta ta siyar ta iya semata katifa da filo.

 

 

Biki ya rage saura sati biyu sumayya ta fara rabon cingum,aikwa ranar dazata kai gidansu zaliha ,zahra tace sutafi tare, sumayya tamata jagora,sukaci sa’a kwa da zaliha suka fara cin karo tana d’iban ruwa arijiya,ganinsu kuma yasata saurin ajjiye gugan tana “yau kuma makafine suka zo gidannamu,koda yake aiba akirata makauniya ba tinda ta iya kwacen saurayi ”

 

Murmushi zahra tai wanda ya qara fito da kyaunta tace “gashi kuma kinbawa kanki amsa,se nake ganin kamar kin Gaza tinda makauniya ta iya kwacemiki saurayi ashema tafiki ”

 

Afusace tayo kanta tana ” Ke nakasashiyar banza karki gayamin ba dad’i acikin gidan ubana ”

 

“Hmmm maida wuqar alkhairi ne yakawoni cingum nakawomiki na bikina d ishaq sati na gaba “zahra tafad’i tana miqomata cingum.

 

Ai watsi tai da cingum d’in tana “Allah y sawwake ,inbanda aikin asiri meze dake ,kuma qarshen alewa qasa asirin naki ze karye ”

 

Zahra tace “to ashema asirin yayimin tinda har nayi yakamashi,wanima yayi asirin a aureshi “bata jira me zataceba suka fice sukabar gidan…..

 

 

 

————-ranar lahadi 20/3/2022 aka d’aura auren zahra’u hafizu da ishaq farouq akan sadaki duba ashirin tare da shedu yadda musulunci ya tsara,bayan kammala d’aurin aurene ishaq ya nemi abokinsa faisal daya rakashi wajen amaryarsa,aikwa yasha tsiya wajen faisal yay ta tsokanarshi zumud’in meyake yaude za akawomasa ita har suka qarasa be dena tsokanarsaba.

 

Mashalllah zahra’u tayi kyau qafarnan tasha jan lalle abunka da farar fata haka hannunta se d’aukan ido yake , amma fuskarta samm ba walwala,bayan sun gaisa da faisal nan yakoma gefe yabasu waje.

 

Kallonta ishaq yay yace “haba amarsu ta ango senaga uwa bakya farinciki da wannan ranar ?”

 

“Taya zakace bana farinciki Yayana ”

 

“Gashinan qarara afuskarki “ishaq ya fad’i yana me kuma kallonta.

 

Sunkuyar da fuska tai uwa zatai kuka bakinta na motsi alamun tana so tafurta wani abu takasa .

 

Cikin sanyin murya ishaq yace “haba matata karkiji shayin gayamin komi,nai alqawari bazan tab’a barinki kiyi hawaye arayuwarkiba meyafaru gayamin ”

 

Ahankali tace “Yayana Wai su baba sanusi basumin kayan gado ba se innace ta siyon katifa Wai da ita kad’ai za aka …. Se kuka yakwacemata ”

 

Murmushi yay yana “hajiya zahra da rigima kike yanxu wannan shine abun kuka kuma ,karki manta Ke nake so kuma naji nagani Wlhy zahra ko ke kad’ai aka kawomin ina so , Ke nakeso ba wnai abuba kuma wannan ba wani abubane ,ni akwai wasu kud’i aguna zan bawa faisal ya nemo mana madubi da siff ko sakanne,matuqar zaki farin ciki ”

 

Tini hawayen idonta ya d’auke ta rasa ma me zata cemasa ,wannan wane irin so yake mata afili kuwa cewa tai “Yayana bani da abinda zan sakamaka sedai Allah yabiyaka d aljanna,ina me  alfahari d samunka ”

 

“Nima haka matata ,sekije kishirya zuwa magriba zan aiko ad’akkomin gimbeeya ta ”

 

Sunkuyar dakai tai tana dariya shima dariyar yake ,yayinda faisal Ke gefe guda yana mamakin wannann abu ,yacce yaga abokinnashi yana soyewa da makauniya to qarewa ma ya aureta ikon Allah se kallo .

 

 

——to misalin qarfe bakwai da rabi na dare aka kai amarya d’akinta,gidane qarami Amma yasha fenti kuma ita kad’ai ce agidan, kowa yacika d mamaki ganin ammata kayan d’aki ita kanta seda tai mamaki duk da yagayamata Amma batai zaton da gaske yakeba ,wannan shi ake kira da mijin marauniya,zuwa tara kowa ya fashe anbar amarya ita kad’ai tana jiran angonta.

 

 

Share plx

SAKAYYA

 

 

Alqalamin gimbeeya

 

 

PAGE 3!!

 

 

 

Ganin’yan kai amarya sun watse hakan yabawa ishaq damar shiga wajen amaryarsa,bakinsa d sallama yashiga d’akin amaryartasa cike da farinciki tare da baqar leda ahannunsa “amarya bakya lefi koda kin kashe d’an masu gida “yafad’i yayinda yake qoqarin zaunawa akusa da ita.

 

Cikin d’an shesheqar kukan da ba arasa amare da yinsa ta amsa masa sallamar,kallonta yay ganin irin kyaun datai afili yace “mashalllah,yanxude ayi haquri da kukan dan bazan iya jurar hawayenkiba kinji tawan “yafad’i yana bud’e mata fuska lokaci guda kuma yana share hawayen fuskarta.

 

Ajiyar zuciya tai saboda wani irin abu daya shiga jikinta wannan ne karo na farko da hannunsa yafara tab’a jikinta,tashi yay ya zubamusu ruwa abuta sukai nafila raka’a biyu kana suka roqi Allah albarkar aurensu daganan yasamu yabata kazar da yoghurt taci duk da bawani da yawa taciba Amma de yasamu tad’anci dan dakyar ta yarda yabata,sifff ya bud’e ya d’akkomata kayan barci wanda yasamata a lefe marasa nauyi sannan ya dubeta yace “seki tashi in sauyamiki kayan ko ”

 

Ai zaro ido tai  tace”kai yaya ishaq ,bani kayan ahannuna zan iya sawa ”

 

“To mene ba mijinkibane “ishaq yafad’i yana qoqarin ciremata mayafin jikinta.

 

Ai kuka tasakamai tana “dan Allah yaya ishaq kabari zan saka kaji”

 

Yasan hakane zata faru shiyasaka be mata musuba yabata saboda dama tsokanarta yake,tinda yasan yanxu basu sababa kwatakwata ma ba abinda yashiga tsakaninsu yasan dole yanxu tanajin kunyarsa,”to kisamana ”

 

“To kad’an fita waje senasa ”

 

Wani guntun murmushi yasaki aransa yana “hmm yaro man kaza tare fa zamu kwana qarewartama “Amma azahiri fita yay yana “to Shikkenan ki sauri”

 

Agaggauce zahra ta cire kayan jikinta tasaka na bacci duk abinda take batasan ya lab’e yana kallontaba mamakine yakamashi ganin qirjin zahra duk aciccike duk da shekarunta be kai ace angama mata halittaba har sunkai haka kwatakwata shekarata sha shida fa,ganinsu kuma hakan ba qaramin d’aga masa hankali yay ba dama ya je yasha tsuminsa.

 

“Kingama saka kayan “ishaq yatambaya

 

Murya qasa-qasa tace “Eh”

 

Nan ishaq yakoma d’akin shima yasaka nasa kayan bacci sannan ya gyara musu filo suka kwanta daidai saitin kunnenta yake rad’amata irin farincikin dayake ciki awannan ranar,nan take itama tsigar jikinta tafara tashi saboda yacce muryarsa Ke shiga dodon kunnenta shiyasa duk jikinta ya mutu ,ganin haka kuma yasa ishaq saurin saka harshensa akunnenta yayinda numfashinsa Ke fita sama-sama,wani irin abu zahra taji ya tsirgamata tindaga kanta har qafafunta aitini ta qamqanmeshi jin hakan kuma yaqara fitar dashi daga hayyacinsa,cikin zalama yake mata wani kiss me tafiya da zuciya lokaci guda kuma yana murza kan boobs d’inta itama tini abar ta motso mata saboda ishaq yagama gigitata,ahankali yake kai kansa qasa daidai HQ d’inta yafara lasa ahankali aitini zahra taqara gigicewa har wani nishi take ,seda yatabbatar takai qoluluwa tukunna yafara karanto addu’ar saduwa da iyali jin hakan kuma yasa zahra saurin dawowa hayyacinta ai kan kace meye tini yafara aiki wani zafi da zugi taji yaziyarceta wata’yar qara tasaki tana “wayyo yayana dan Allah kabari da zafi sosaii ”

 

“Yi haquri zahra ibada kike “abinda ya iya cewa kenan cikin dakusashiyar murya,to hakade ishaq yaci amarcinsa adaren farkonsu wanda yakasance dare me matuqar muhimmaci da tarihi arayuwar kowanne ma’aurata.

 

 

———kwanci tashi ba wuya game yawan rai har sun shekara 3 da aurensu,acikin shekarunnan ba abinda ishaq baiwa zahra agidannan Dan kafin yafita nemo musu abinci seyay shara wanke-wake sannan ya girka musu abinci danma wani sa’in sumayya takanzo ta taya zahra hira da wasu ayyukan gida,harta wanki shiyake mata,uwa uba soyayya da kulawa ba wacce be bata Dan inde yana gida abaki yake bata abinci,abu na farko dayafara d’aga musu hankali shine jinkirin samun rabo domin ishaq ya qagu yaga d’ansa nacikinsa kodan gorin da abokansa Ke masa ya auri makauniya.

 

 

Rannnan suna zaune yana bata abinci abaki yace “tawan bakya ganin yakamata musamu mu dad’u agidannan?”

 

Bayan ta had’iye abincinne tace “Saurin me kake yayana shekaran mu uku fa da aure kuma du dudu shekarata nawa akamin auren ina 16 akamin yanxufa 19 nake inshallah yayana munkusa samu ”

 

Murmushi ishaq yay yace “to Allah ya amsa matata takaina Amma wane suna zamu saka masa ?”

 

Dariya tai tace “tin yanxu kuma Yayana har anfara zab’ar suna Amma de inda zakamin alfarma se asa sunan baba ,tinda Kaga yarasu ”

 

“Eh dama nima abinda nake so kenan ,asa sunan baba kinga kuma sunane me dad’i hafeezu ba ”

 

Kwab’e fuska tai tace “shine kafad’a to ”

 

“Ah kiyi haquri ainaga sunan babanane nima ko ”

 

Murmushi tai tace “hakane kam mijina ”

 

Gyara zama yay akan sallaya yace “nikwa zahra inaso mi wata magana,bakyajin kinason kidinga gani kamar yadda kowa yake gani ”

 

“To banda abinka yayana wazece be son gani??ko kamanni nafa bansaniba Kaga ko dole zanso naga yanake wataqila ma mummunace ni ”

 

“Kai matata aibaki gankiba,kinada matuqar kyau sosai,kinada haske, ga gashin idonki zara zara ,yayinda idanuwanki suka daidaita da karan hancinki siriri wanda yaqara fito da kyanki sannan gashin girarki baqace cunkus sede bakinki yafi komi kyau afuskarki qaramine wanda yake kamar kinsamai janbaki saboda ja ”

 

Zaro ido tai tana “kai yayana wannan kyaun ai yayi yawa da gaske ni nake dashi??

 

“Wallahi ba zance wasaba zaki mamaki kikaga kanki a madubi,gaskiya zuciyata tana bani nakaiki asibiti tinda ba atab’a zuwa anbincikaba inshallahu ko aiki za’amiki zanyi qoqari nabiya Dan kidinga gani kamar kowa “ishaq yafad’i yana me kallonta

 

Washe baki tai Dan tsananin farinciki tace “wallahi na dad’e ina cewa inna muje asibiti setace Wai ai kakana harya mutu makahone  tanaga nima gado nai Dan haka ba inda zata ”

 

Yace “tom ki kwantar da hankalinki inshallah zuwa jibi zan samu wasu kudi naiwa wani hakimi d’inkunansa na sallah yana biyana inshallah se muje ”

 

“To Allah yakaimu mijina..”

 

 

————-aikwa haka akai ranar da ya amshi kudinsa na gurin hakimi washe gari suka shirya sukatafi asibiti,da yake da wuri sukaje sun samu sunga likita “inda likitan ya bayyana musu cewa da tin lokacin da aka haifeta tana jaririya aka kawota asibiti da tini idonta ya bud’e,dan abun bawai lalura bace abune da yafaru sakamakon rashin samun qarfin gani na ido,amma da an d’orata akan wani sinadarai masu qara qarfin gani da tini idonta ya bud’e,wani magani ya rubutamata wanda kudinsa yakai dubu goma sha biyar yace matuqar zata juri sha ahankali ahankali zena qara mata qarfin gani watarana zata bud’i ido taga ganinta yadawo ”

 

Farinciki agurin zahra be misaltuwa taji dad’i sosai kana ta godewa mijinta Amma babban tashin hankalinta taya ishaq ze juri siyan maganinnan me tsada nawa yake samu?? Seyay wajen shekara be ajjiye dubu ashirin tasa takansaba to taya zai ajjiye dubu goma sha biyar duk wata tasan cewa sana’arsa ba wata me qarfi bace.

 

Cikin rarraunar murya tace “Yayana senaga uwa kudin magani yay yawa inbaze samuba karka matsawa kanka kaji ”

 

Hannunta ya riqe yace “matata takaina kinfi qarfin komi aguna inshallah baze gagaraba zan qara koda da dakone akasuwa ko jiran shago naga na samu na had’a kudin zuwa qarshen watan ”

 

 

” ai  wani hawayene ya gangaromata wanda tarasa kona meye aranta tana “wnanan wace irin soyayya ishaq yake mata aduniya,tayadda yanxu ze iya sadaukar da komi akanta.

 

 

 

Read and share

SAKAYYA

 

 

Alqalamin gimbeeya

 

 

Page 4

 

Tin daga lokacin da doctor yabawa ishaq katin maganinnan yake ta iya qoqarinsa domin yaga ya had’a kud’in maganin ba sana’ar dabeyi indai yasan ze samu kud’i ta hanyar halal harta dako inde za’abiyashi ishaq yi yake ,hakan yasa kuma be tab’a gazawa wajen siyamata maganintaba duk wata .

 

Hakade rayuwa tacigaba da dad’i ba dad’i,yayinda ishaq duk yafita daga hayyacinsa ,inka ganshi bazakace shine ishaq wannan d’an gayunba,duk yay baqi ya rame saboda ba qamar wahala yake sha ba wajen nemo musu abinda zasu ci tare da nemo kud’in magani ,to tun suna saka rai akan maganin harsun fara fidda ran bud’ewar idanunnata,hakana ko sun koma gun likitan abinda yake cewa kenan tade cigaba dashan maganin qarfin ganin na qaruwa,gashi yanxu wajen shekara uku da motsi duk wata ishaq seyay fafatukar nemo duba goma sha biyar d’innan har kawo yanxu wajen shekara uku ,zuwa yanxu kam yakashe kudi fiye da dubu d’ari biyar da saba’in ,duk da shan maganin datake Amma ba alamun sauqi hakan yasa suka fara cire tsammani akan samun sauqinta.

 

To kwanci tashi ba wuya yanxude sun nufo shekara bakwai da aurensu,hakana wajen shekara hud’u zahra tana shan magani,Allah buwayi gagara misali me iko akan komi me juya al’amarinsa alokacin da yaso mai yin yadda yaso kuma asanda yaso ,ranar litinin rana me d’unbin tarihi arayuwarsu da al’ajabi,wato aranar har qarfe 7 nasafe basu farkaba saboda ranar ammaka uban ruwa hakan yasasu makara,ishaq ne yafara farkawa inda yay ta qoqarin tashin zahra domin suyi sallah Amma ina magaginta yahanata tashi,ganin zata b’atamasa lokaci yasashi tashi yaje ya d’oro alwalarsa,tashin kabbarar haramarsa ne yakai kunnen zahra jin hakan yasata sanin cewa lalle sallah yake itama yakamata ta miqe,tashitai tana miqa tare da kiran sunan Allah mamaki tsoro razani ne suka kamata ganin cewa datai ta na iya ganin d’akin datake ,saurin juyar da idonta tai takalli inda ishaq Ke tsaye yana sallah siff d’in d’akin takalla kuma murza idonta tai dan taga shin mafarkine koda gaske itace take ganin komi haka tarrr a idonta,amma ina tagane azahiri ne wannan abun tabbas ita Ke gani,nan danan tai qasa tai sujjada ga ubangiji tarasa da wane irin yabo zata godewa Allah da yayemata wannan jarabawar da yay,bayan ishaq yayi sallamane yay saurin juyo da idonsa kan zahra’u wacce take asujjada cike da mamaki yake kallon irin farincikin datake da kuma dube-duben datake kafin ya ankara da gudu zahra tazo ta rungumeshi tana “Alhamdulillah yayana yanxu ina ganin komi,yayana ka dubi idona inaganinka ” shima qanqameta yay yana “da gaske kike,yanxu kina ganina da komi?”

 

“Ehwlhy ina ganin komi yayana nadena ganin duhu dama haka duniya take da haske “lokaci guda kuma tafashe da kuka wanda yanayin kukan ze tabbatar ma na farinciki ne wanda aka rasa me za’ai inba kuka ba.

 

“Allah da girma yake ,kad’an daga ikon Allah kenan dama ance me haquri shike dafa dutse yasha romansa kullum gani muke uwa addu’armu bata karb’uwa gani muke uwa lokaci baze zoba Amma se gashi Allah yakawomu tabbas al’amarin Allah da girma yake ,seki tashi ki asuba sannan muyi nafila raka’a biyu ta godiya da Allah ”

 

Ba musu cike da farinciki zahra ta tashi tana ” a ina kake ajjiye botar?”murmushi ishaq yay yana “wato yau base na zuba miki ba ,kiduba tana band’aki,itama murmushi tai tafice sedai tana fitowa tsakar gida gabanta yace rasssss “ganin yacce gidan yay duk y’a farfashe saboda yanayin damuna aranta take “wato a irin wannan gidan take rayuwa tsakar gida duk yafashe d’aki kwaya d’aya se band’aki da kitchen ga wani uban murhu azaure,muryar ishaq ce takatsemata tinanin ta “kina ina baki fara alwalar bane jiranki nake ”

 

“Ganinan yanxu zan fara “cike da kyankyamin band’akin ta d’akko botar tai alwala aranta tana godewa Allah dayasa idonta ya bud’e taga a irin qasqantacciyar rayuwar datake ciki,hakan yasa lokaci guda walwalarta ta d’auke.

 

Bayan ta idar da sallah ne ,nan suka tashi sukai nafila ta godiya da Allah ,sedai tinda suka idar da sallar ishaq ya lura da cewa walwalar fuskarta ta canja gaba d’aya “lapia naga gaba d’aya annushuwarki ta d’auke?”ishaq y tambaya

 

Batare data kallesaba tace “lapia lau,amma ishaq meyasaka kwata kwata gidannan ba agyarashi?”

 

Mamaki ne yacika ishaq anyakwa zahra tasan dawa take magana shekarar su bakwai da aure Amma bata tab’a bud’e baki takira sunan saba,sannan maganar gyaran gidan da take aqalla sau biyu yake sharewa yayi kafin yafita yayi bayan yadawo,danne abinda yakeji aransa yay yace “haba zahra kinmanta yacce nake share gidannan wataran har cewa kike nabar sharar haka ”

 

Wani kallo ta qara jefamai dan ita gaba d’aya tana ganin ishaq ta rainashi wani baqi dashi ga wata iriyar rama duk ya tsufe (Allah sarki abinda batasaniba shine neman kud’in maganintane ya maidashi haka wanda in akai lissafi dubu goma sha biyar sau wata 48 wato shekara hud’u zekai kimanin dubu d’ari bakwai da ashirin to amatsayinsa na talaka ba dole ya susuceba ”

 

“A’a ba shara nake nufiba ina nufin ramu kan dake tsakar gida dana band’aki “tafad’i ataqaice.

 

“Haba zahrah me neman kud’in abinci na yau da gobe dana magani ina yaga tagyaran gida ”

 

“Hmm to Allah y sawwake “abinda zahra tafad’i kenan kana ta miqe tana cewa “tom yakamata yanxu karakani gidanmu dan yanxu da inna ta kawai nake so nai tozali se ‘yar uwata sumayya ”

 

Kallonta yay yana “ai dama kobaki fad’i ba dole muje wajen inna kodan taga wannan abun Al ajabin dabata tab’a zato ba ,amma matata senaga uwa baki farinciki da ganina ba bayan Ke kike nunamin cewa in idonki yabud’e fuskata kikeso kifara tozali da ita ”

 

“Uhmmm nagankamana Amma banyi zaton hakan zanganka ba dakai da rayuwarka ”

 

“Zahra me kike nufi da hakan “ishaq ya tambaya cike d mamaki.

 

“Hmm zaka gane ne yanxu de tashi ka kaini wajen su inna dan Allah mayi magana daga baya “batare da ya qara cewa komiba yatashi yad’au hularsa dake saman siffff ,yana “taho muje to ”

 

Ai tunda suka fito waje mutane keta binsu da kallo itama kallonsu take kowa mamaki yake da bud’e war idon zahra sede bud’e war idonnata yasasu qara wani haske wanda yaqara fito da kyaunta,abinda zahra ta lura dashi shine lokacin da suka fito titi duk wani me motar daze wuce ta kusa da ita se ya qaremata kallo harya wuce ,itakam mamaki take tana duban jikinta shin wani abune da ita da yasa aketa kallonta.

 

 

—————— dayake basuda nisa basu jimaba suka qarasa gida,shigarsu yay daidai daya fitowar inna daga band’aki ai da gudu zahra tai kanta ta rungume ta tana “inna idona ya bud’e ina ganin komi yanxu ”

 

“Ke zahra’u Alhamdulillah ashe daman maganinann yanayi wlhy ni nacire rai,kai Allah shine abin godiya,wannan yaro ishaq Allah yasaka masa da aljanna ba abinda zamu biya shi dashi se fatan Alkhairi “inna tafad’i tana rungume da zahra

 

Sunkuyar da kansa ishaq yay yace “Ameen innah nagode ”

 

To abinka da gidan yawa ko wa ya firfito Anata al’ajabi idon zahra ya bud’e sashen inna yacika da mutane masu murna na yi masu mamaki nayi,itakam zahra taga baqin fuskoki da yawa wanda tasansu abaki Amma idonta be tab’a ganinsuba sedai duk wad’annan mutanen data gani ita kanta bataga kantaba bare tasan yakamaninta yake,bayan an watse ne tinda dama ishaq yatafi da niyyar da yamma ze dawo yad’auketa Yaude ta yini agida tinda ranace me muhimmaci agaresu baki d’aya.

 

Zahra ce takalli sumayya tace “qanwata kyakkyawa ce kefa “ni tinda na bud’e ido banga me kyaunkiba keda inna.

 

“Haba yaya zahra’u dan baki gankiba ne da se kinga kyannamu duk ya dishashe akan naki “sumayya tafad’i.

 

“Allah qanwata!??d’akkon madubi naganni ”

Sumayya tace “to “yayinda take qoqarin tashi ta d’akkomata madubi…..

 

 

Read and share

Add Comment

Click here to post a comment