Littafan Hausa Novels

BBC Hausa Sakamakon Zaben Gwamna Adamawa

Sakamakon Zaben Gwamna Adamawa

 

 

 

 

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna da aka bayyana a jihar Adamawa, tana mai bayyana shi a matsayin ba karbabbe ba.

INEC din ta kuma dakatar da aikin tattara sakamakon zaben cike gurbi da aka yi, wanda kwamishinan zaben ya ayyana Sanata Aisha Ahmed Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe shi. Tuni ma ta umurci kwamshinan zaben Jihar ta Adamawa da sauran baturan zaben da su hallara a shelkwatarta da ke Abuja babban birnin Najeriyar.

Bayan dogon jira da aka shafe awanni ana yi na kawo sakamakon ƙaramar hukumar Fufore wadda aka ce rikici ya hana a bayyana ta, yanzu dai an bayyana sakamakon, kuma Binani ce ke kan gaba.

Ga Sakamakon Zaben Jahar Adamawa na kananan hukumomi 21 kamar haka

1. Karamar hukumar Guyuk APC: 14,172 PDP: 18,427 

2. Karamar hukumar Lamurde APC: 9,376 PDP: 19,102 

3. Karamar hukumar Jada APC – 20,899 PDP – 22,933 

4. Karamar hukumar Gombi APC – 19, 665 PDP – 19,866 

5. Ƙaramar hukumar Shelleng APC – 12,589 PDP – 14,867 

6. Karamar hukumar Ganye APC: 21,605 PDP: 17, 883 

7. Karamar hukumar Demsa APC: 11,798 PDP: 22,958 

8. Karamar hukumar Mubi ta kudu APC: 32,342 PDP: 17,469 

9. Karamar hukumar Mayo-Belwa APC: 23, 576 PDP: 20,239 10. Karamar hukumar Maiha APC: 13, 242 PDP: 12, 792 

11. Karamar hukumar Gerei APC – 16, 140 PDP -17, 298 

12. Karamar hukumar Hong APC 18,639 PDP 31,443 

13. Karamar hukumar Madagali APC – 9.650 PDP – 27, 351 

14. Karamar hukumar Numan APC – 10,626 PDP – 17,026 

15. Karamar hukumar Mubi ta kudu APC – 18,149 PDP – 12,686 16. Karamar hukumar Yola ta kudu APC – 32, 255 PDP – 21, 006 17. Karamar hukumar Toungo APC – 7,161 PDP – 7,884 

18. Karamar hukumar Yola Ta Arewa APC – 37,885 PDP – 24,877 

19. Karamar hukumar Song APC – 19,935 PDP – 24,744 

20. Karamar hukumar Michika APC – 15,793 PDP – 30,262 

21. Ƙaramar hukumar Fufore APC -24,777 PDP – 20,409 

Za’a gudanar da zaben gwamnan jihar Adamawa a shekarar 2023 a ranar 18 ga watan Maris, 2023, domin zaben gwamnan jihar Adamawa, a daidai lokacin da zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Adamawa da sauran zabukan gwamnoni ashirin da bakwai da zabukan sauran majalisun dokokin jihohi.

Adamawa

An shirya gudanar da zaben ne makonni biyu bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya to sai dai anyi karin sati daya a bisa wasu dalilai daga hukumar zabe wato INEC. An sake tsaida gwamnan jihar mai ci na jam’iyyar PDP, Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin dan takarar gwamnan jihar.

Sakamakon Zaben Gwamnoni Jahar Sokoto 

Zaben fidda gwani da aka gudanar a tsakanin ranakun 4 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Yunin 2022, ya sa Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party a ranar 26 ga watan Mayu, yayin da jam’iyyar All Progressives Congress ta tsayar da Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Aishatu Dahiru Ahmed a ranar 25 ga watan Mayu.

 

Duk da cewa hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke ya soke zaben fidda gwani na APC a ranar 14 ga watan Oktoba, hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya soke soke zaben tare da mayar da Ahmed ranar 24 ga watan Nuwamba.

Add Comment

Click here to post a comment