Littafan Hausa Novels

Sadauki Omar Hausa Novel Complete

Sadauki Omar Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SADAUKI OMAR

 

 

*MALLAKAR:*

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

 

Bisimillahir rahamanir rahim.

 

 

*ARASHI*

 

‘kirkirarran labari ne daga ni marubuciyar banyi don inci zarfin wani ko wata ba Wanda yaga yayi dai-dai da yanayin na rayuwarsa to a rashin sani ne.

 

 

*GARGADI DA JAN KUNNE!*

 

Ban yarda wani ko wata ya juya min yanayin labari na ta ko wace siga ba ba tare da izina ne ba ban yarda ka/ ki siyar min da littafi ba duk Wanda yayi d’aya daga cikin biyu na barshi da Allah!

 

 

 

*SADAUKI! OMAR*

 

Kai daga jin sunan littafin kasan ya tsaru zai kuma bada ma’ana Ina ma’abota karatun littafan Hausa kuyi maza Ku garzayo ku samu naku littafin SADAUKI OMAR yazo muku da sabon salo mai sanya Ku nishadi ilimantar wa fadakarwa nishadantarwa duk a cikin wannan littafin babu shakka! Wannan daban yake da sauran!! *SADAUKI OMAR🏹* Iya sarauta iya mulki tsantsar soyayya muskilanci bakin kishi! Bak’ar gaba! Tsananin jarumta!!! Duk a cikin wannan littafin kar ku sake abaku labari!!!!

Fuska Uku Complete Hausa Novel

*Ga masu bukatar biyan kudin karatu zasu tura #300 ta wannan accont din…..0542382124…Binta Umar GT bank idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars 08089965176 _07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya…… Mutanan Nijar Idan kuna so Ku biya zaku tura dala Dari ta wannan numbars….90899076 88137740 Katin airtal ko Orange.*

 

 

 

 

Free Pege

 

 

 

 

Masarautar *KANO*

Cikin wata ‘kwaleliyar rana na hangoshi tsakiyar filin motsa jiki ya na sanye da ‘bakar vest had’e da wani bugujejen wando mao dogon madauri vest din ta matse jikinsa sosai kamar ma taso yi masa kadan saboda yanayin halittar jikinsa mutum ne murd’adde ‘kakkarfa! Wanda ko daga nesa ka hangoshi zaka shaida hakan wani ‘katon ‘karfe me mugun nauyi yake d’agawa yana saukewa gumi sai yanko masa yake daga ko wace ga’ba ta jikinsa. Duk girman gurin shi kadai ne tsaye daga can sama kuma ko wace baranda ka kalla mutane ne keyawe da ita suna kallonsa kana kallon fuskokinsu zaka fahimci jarumtar *Omar* din na burge su.

 

Cikin isa da kasaita take tafiya tun kafin ta ‘karaso jama’ar da sukayi dafifi gurin le’kensa suka fara kaucewa suna zubewa ‘kasa hade da sunkuyar da Kansu suna mik’a gaisuwa gare ta, ko kallonsu bata yi ba ta wuce tana ya mutsa fuska wata baiwa na biye da bayanta. Can karshen barandar ta ‘karasa ta d’ora hannayen ta akan ‘karfen tare da rankwafawa jikin ‘karfen tana ‘kare masa kallo. Minti biyu ta d’ago kanta tana jan siririn tsaki! Ikilima dake tsaye kusa da ita tace”Allah ya taimaki Uwar dakina ko a dauko abun zama ne.”? Girgiza kanta tayi da kyar tace”Kira min Tafida.” Da sauri Ikilima tace”Angama ranki shi dad’e.”

 

Can ‘bangaran maza ta nufa minti uku sai gasu tare da Tafida ya zube kasan gurin yana kwasar gaisuwa ba tare da ta amsa ba tace”Je ka kira min wancan Wawan.”! Tafida ya kasa fahimta Wanda take nufi cike da ladabi yace.” Ranki shi Dade ban fahimci Wanda kike nufi ba.” Filin gurin ta kalla har yanzu yana nan yana abunda yake ta ‘kara Jan tsaki a karo na biyu Cikin ‘yar tsawa tace”Ina na kalla yanzu. “!? Tafida yace.” Filin Hazo! Kauda kanta tayi ba tare da ta sake cewa komai ba. Tafida ya mike jikinsa a sanyaye ya bar gurin.

 

Akwai tafiya sosai kafin ya isa inda yake Yana ganin zuwan Tafida yasan akwai matsala saboda ‘ka’ida ne idan yana wannan abun ba’a zuwa gurin har sai lokacin da aka d’iba ya ciki don mai Martaba ba ma har yanzu bai futo ba. Tafida ya ‘karasa gurin jin babu ‘kwari yace.” Ran SADAUKI! Ya Dade yana ‘karko.”!! Yana cigaba da sama da ‘kasa da dotsen yace.” Ya akayi ne Tafida ka karya doka fa kayi maza ka bar gurin nan kafin mai Martaba ya futo shi.” Yace.” Gimbiya Aysha! Ke kiran ka.” Da d’an mamaki! Yake kallonsa kafin yace.” Ka bar gurin nan kafin ranka ya ‘baci! Tafida yace.” Allah huci zuciyar jarumin maza!! Murmushi yayi yace.” Kaje kace mata ‘naki zuwa idan ta cika Mara kunya ita tazo gurinan.” Tafida yace.” Ayi min afuwa bazan iya fad’ar haka ba zan shirya wata k’aryar dai.” Murmushi yake yana kallon Tafidan lokacin da yake barin gurin motsa jikinsa yake yana mamakin Yarinyar bai San me yasa ba take shiga harkasa Sam! Baya shiga sabgarta saboda yanayin halayen ta tunda tunda yake da sai ya irga iya adadin maganar su amma ya lura a ‘yan kwanakin nan tana nema ta dunga shiga gonarsa kwata-kwata baya so take kula shi! Amma ta kasa fahimta shi mutum ne Wanda baya daukar raini ko wulakanci dalili kenan da ya killace kansa daga hurumin ta ya lura sai ya taka mata burki sannan zata daina damunsa, mamaki ma yake ko kiran me take masa oho! Shi dai na farko baya daya daga ciki n hadimanta ballanta tace Tsaki kawai yake yaja yana cigaba da aikinsa gefe guda kuma yana tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya yanke alakarsa da ita.

 

“Gyara kintsi dai! Takawar ka lafiya dan toron giwa.” Muryoyin fadawan sarki ke tashi gurin wannan ya tabbatar min da cewar sarki ya futo filin *Hazo* filin nuna bajinta kenan. Guri ya nutsu duk wata hayaniya da ake gurin kamar anyi ruwa an dauke busa da sarewa ne kawai ke tashi a gurin daf da sarki zai zauna fadawa kusan su goma masu jajayen kaya suka baza manya-manyan rigunan su suka kare sarki sai da suka tabbatar ya zauna kan kujerar shi sannan ko wanne ya koma gurin tsayuwar sa, daya bayan daya masu rawani suka dunga futowa irinsu galadima Waziri Wambai ko wanne ya zauna gurun zaman shi saman k’atuwar barandar inda suke hango Omar tsakiyar filin cikin kwaleliyar rana yana gwada jarumata shi . Wani irin murmushi sarki yake yana Yana kallon Omar jarumatar yaron na mutukar burgeshi da bashi sha’awa yaso ace ‘Daya daga cikin ‘yayan sa na da kwatankwacin irin jarumatar Omar din sai dai kash! Allah ya bashi ‘Yaya lusarai marasa jin magana da gangarewa….. Yarima Faisal yana kallon mahaifin nasa yana sakin murmushi ya lura bajintar Omar din na mutukar burgeshi take yaji wata irin tsanar Omar din cikin zuciyar sa ya lura Sarki na mutukar sonsa duk cikin bayin dake cike da gidan ya fifitashi fiye da sauran Dole ne su dauki kwakkwaran mataki kansa don yana gani sarkin zai iya bashi wata sarautar ko kuma ya ‘yan tashi cikin bayi babban abunda ya tsana kenan a rayuwarsa ya fiso kullum Omar din ya dauwama cikin kaskanci da aikin bauta.!

 

 

Wani irin tsalle yake kafad’arshi dauke da ‘katon dutsen kwanjinsa sai sake murd’ewa yake saboda tsabar jin karfi ya kai ya kawo tsakiyar rana gumi na yanko masa daga ko wacce kusurwa ta jikinsa OMAR kenan SADAUKI JARUMIJ NAMIJI. wannan abun da yake ya dauki hankalin duk Wanda yake gurin Sarki ya mike daga kujerar sa yaje ya dafa barandar gurin yana kallonsa fuskarsa dauke da murmushi na ya bawa bajintarsa, Muryarsa mai cike da kamala da nutsuwa Yace.” SADAUKI! JARUMIN NAMIJI! Kafin kice kwabo duk wanda ke gurin ya amsa da fadin kalmar SADAUKI! JARUMIN NAMIJI!! Zuciyoyin mutum uku a gurin kamar su babbake don bakin ciki da takaici Yarima Faisal ya kalli Galadima dake hakimce kan kujerar sa ya sha kunu tamkar Wanda aka aikowa da mala’kan mutuwa tunda ya zauna a gurin ko motsi yaki yi kawai ya futo ne ma Don yana gudun b’acin ran Sarkin amma da babu abunda zai sanya ya futo ganin ma kaskancin bawa irin wannan. Yarima Faisal yayi ‘kwafa tare da mi’kewa a fusace! Alkyabbar jikinsa ya buge da karfi yana wani irin huci! Ya sauka daga gurin. Gimbiya Aysha kuwa Wani irin takaici ne ya kamata ganin yanda ake wani murna da ihu! Duk akan bawan da ta tsana a rayuwarta tayi alk’awarin sai ta ‘kaskantar dashi gaban bayi da wad’anda suke bashi girma domin ta lura da yanda yake wani isa gami da ji da kai da miskilanci yana a matsayin bawa! In dai tana raye cikin masarautar su babu Wanda ya isa ya bashi girma sai ya ‘kaskanta. Rai a bace itama ta buge alkyabar jikinta da sauri Bayin ta suka take mata baya.

 

 

Kimanin awa guda Omar ya dauka yana wannan Abu kafin Sarki da kansa ya sauka! A nutse yake ratsa gurin har ya isa inda yake tsaye wani farin karamin towel ya dauko ajihunsa ya shiga tsane masa gumin jikinsa Kafin ya kamo hannunsa suka bar gurin…. Take yanayin busar da ake a gurin ta sauya Sarki sai da ya shigar da Omar b’angaran su fadawa na binsu a baya suna Fad’in”Mai Martaba ya Yaba da jarumatar ta SADAUKI JARUMIN NAMIJI kayi godiya guri Sarkinmu Mai adalci. Suna isa k’atuwar kofar da zata sadaka da dakunanan bayan masarautar Sarki ya saki hannunsa Omar ya zube kasan gurin yana jinjina hannunsa guda da fad’in Godiya nake Mai Martaba Allah ya ‘kara maka nasara da lafiya mai amfani.” Sarki ya Dora hannunsa a kansa har yanzu fuskarsa da murmushi Yace.”Omar Jarumin Namiji ina alfahari da kai duk cikin bayi na.” Sarki! Na gama maganar shi ya juya da niyyar tafiya manya-manyan rigunansu suka baza suna Fad’in “Gyara kintsi toran gwiwa gaba salamu baya salamun Mai farar Aniya!! Omar kansa a kasa sai da ya tabbatar da wuce war Mai martabar sannan ya dago kansa, a nutse ya mike daga gurin ya nufi d’akinsa domin wanke jikinsa Omar ya kasance mutum mai tsananin tsafta da tsantsani.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

2/3/2020

 

*BINTA UMAR ABBALE*

SADAUKI OMAR

 

 

 

*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din……0542382124… Binta Umar GT bank…. Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin….. Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137749 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*

 

 

 

Free pege

 

 

 

 

Ma dai dai cin daki ne Wanda yake dauke da karamin gado mai dauke da k’aramar katifa k’arama sai kafet dake shimfid’e a dakin kalar Kore labulayen dake kewaye da dakin ma koraye ne sai k’aramar sif mai murfi biyu jingina jikin bangon dakin gefe da gefen gadon kananun drowars ne mai dai dai ta akwai band’aki cikin dakin mai daidaici nan naga ya nufa bayan ya dauki towel mai Dan fadi dake sa’kale jikin hanga Minti goma ya futo daga bandakin jikinsa daure da towel din sai da na tsorata ganin zahirin hallitar jikinsa wani irin kakkarfan mutum ne murdadde kai da ganinsa a ido kasan zaiyi karfi fuskarsa na kalla na ganta a had’e kamar bai taba dariya ba ya nufi bakin karamin gadon coco butter naga ya bude yana shafawa a jikinsa ya rufe naga ya dauko karamin Abu sai da na kura ido tukkuna na gane kwalli ne naga ya bude ya zaro tsinken yana dadurawa a idonsa kwayar idonsa ya bude nayi saurin matsawa baya ganin wasu irin idananu lafiyayyu masu dauke da wani irin kwarjini da haiba sun sha kwalli rabad’au! Na sake kallonsa lokacin da yake sake dadura tsinke kwallin cikin idonsa ya bude idonsa tar! Nan na gane Allah yayi masa baiwar kyawu Wanda sai ka tsira masa ido tukkuna kake ganin tsantsar baiwar sa karamin bakinsa kewaye yake da wani irin bakin kashi gazarzar! Da alama yana yawan gyaran fuska ya wani yadi mai laushi naga ya dauko ruwan Zuma dinki ‘Yar shara ya dauko wata hula irin ta Fulani mai kunnuwa ya sanya kansa wani k’aramar kwalba naga ya dauko cikin drwar ya bude nan na gane turare ne cikin kwalbar ya goggoga a jikinsa ya maida kwalbar ya aje kofa ya nufo da alamun futa nayi saurin kaucewa. Sai naga ya tsaya wuyansa ya shafa naga ya nufi toilet minti biyu ya futo naga yana d’aura Abu a wuyansa nan na fahimci irin abunda yake daure a damtsan sa ne so nake na tabbatar shin menene gani nake kamar laya Oho na kasa gane menene na dai fi ganin masu mulki na d’aura irin shi, ko me ya hada shi da kayan masu sarauta shi da yake ma’kaskancin bawa inji Gimbiya Aysha. Kofar futa ya nufo a karo na biyu nayi saurin matsawa ya wuce na juya da sauri ina kallon yanda yake tafiya kamar zai tsaga ‘kasa.

 

***

 

“Allah ya ‘kara mik lafiya da nasara Uwargijiya ta Allah yaja Zamann ki Gimbiya Aysha d’aya tamkar da dubu sarauniya kyakyawa kike tamkar zinare farar mace alkyabar mata cike kike kin cika da ‘kasaita ba’ayi ba kuma baza’ayi ba insha Allah babu wacce zata kamo ki a fagen kyau da Iya kasanta.”!! Ikilima kenan dake gurfa ne gaban Aysha take faman banbad’anci ga yabo ga Uwar d’akinta saboda ta lura da yanayin da take ciki na b’acin rai duk lokacin da ta shiga yanayin b’acin rai sai tayi mata irin wannan kirarin take sauraran su.

 

 

Ajiyar Zuciya ta sauke ta Dan gyara kishingidar da tayi a nutse tace” Ikilima yau raina yayi masifar b’aci wallahi.” Ikilima ta sake sadda kanta kasa kafin tace”Allah ya huci zuciyar gimbiya.” Shiru gurin yayi na minti biyar ta mik’o hannu zata dauki apple din dake Jere cikin wani irin ture na silver Ikilima tayi saurin mik’a mata a nutse ta karba ta Dan gutsira tana ya mutsa fuska k’wafa tayi a fili tace”Ikilima wai da me wancan bawan yafi sauran bayin dake masarautar nan ne naga Sarki naji dashi sosai shi kuma na lura yana alfahari da hakan babban abunda ya ‘bata min rai shine bai wuce ganin Sarki da kansa ya sauka filin Hazo har ya goge masa gumin jikinsa Gaskiya raina ya baci da wannan lamarin Ina mutukar jin haushi inga kuna girmama shi kar Ku manta daku da shi duka d’aya ne a cikin gidanan, daga yau sai yau na fad’a miki duk sanda na sake ganin kina bashi girma sai nayi mugun bata miki rai da kaina zan kai ki gaban Sarkin Horo! Ya Zane miki jikin ki shine hukuncin ki.”!

 

 

Ikilima tayi ‘kasa da kanta cike da tsoro da fargaba tace”Allah yaja zamanin ki insha Allah zan kiyaye.”! Tsaki taja ta gutsri apple kadan tana taunawa kamar bata so tace”Dallah tashi kije kice ina kiransa yanzu-yanzu.”! Ikilima ta mike da sauri tana fad’in”Angama ranki shi dad’e.” Da sauri ta futa daga Palo ita kuma ta cigaba da gutsirar tufar tana ya mutse fuska da alama ta saba da hakan tunanin irin kaskancin rashin mutumci da zatayi masa take.

 

 

 

Ikilima na futa ta tsaya tana cizon ya tsaya ya ma za’ayi ta iya tunkarar Sadauki da wannan sa’kon, duk da yake bawa a masarautar amma yafi su yanci ta ko wane fanni kuma a tsakaninsu suna mutukar Shakkar sa gami da girmama shi tana jin nauyi taje tace Wai yazo inji Gimbiya, tunda gaban idonta dazu da Tafida ya kirashi yaki zuwa wannan karon ma tana gani ba zuwa zaiyi ba…….Atika CE ta karaso gurin hannunta rike da wata irin k’atuwar tsintsiyar kwakwa tace.” Ke kuma me kike tsaye a gurin nan tun d’azu.”

 

 

Da sauri Ikilima taja hannunta suka matsa gefe rad’a-rad’a take fad’a Atika tace”Zo muje in rakaki wallahi dama INA so in sake ganinsa ke nifa wallahi da zai aure ni sonsa nake kamar in kashe kaina.”!

 

 

Ikilima tace”Lallai Atika wallahi ki iya bakin ki dube ki don Allah ‘yar gajera dake ina zaki kai ingarman namiji irin wannan ai sai ya kashe ki.””” Cikin jin haushi Atika tace”Aikin banza meye abun ba’a a ciki kin San dai na fiki kyau sai dai ki nuna min tsayi kuma waye yace miki girman namiji na kashe mace ke har yanzu baki san kome ba.”

 

Ikilima tace”Ni kiyi shiru muje mu tsoron masifar gimbiya nake kin San dai halinta.” Tafiya suke suna hirar Omar Atika na sake fad’awa Ikilima yanda take bala’in kaunar Omar din.

 

 

 

Dake ko da yaushe gate din gurin a bude yake yasa suna isa suka hango shi can gurin dokuna tsugune a tsakiyar su da alama abinci yake basu….. Yunusa ya hango su ya karaso gurin tare da fadin”Wai kuke nema ne? Kun San dai dokar cikin gidanan mata basa shiga b’angaran maza hakanan maza basa shiga b’angaran mata.”! Ikilima tayi saurin cewa”Dama Gimbiya ce ta aiko mu gurin SADAUKI! Yunusa ya kalli can gefen da yake yace.” Bari in fad’a masa.”

 

Can ya nufa ya na isa yace.” Omar Gimbiya tayi aike.”! Idanunsa ya d’ago yana kallon Yunusa da sauri naja baya ganin yanda idanun NASA sukayi wani irin jaza kwayar idon ta kara baki sai shek’i take….. Babu walwala tare dashi yace.” Wacece Gimbiya. “!? Yunusa yace.” Gimbiya Aysha mana ga can bayin ta kofar shigowa don na hanasu shigowa gudun samun matsala.” Kansa ya sunkuyar ya cigaba da abunda yake….. Yunusa yace.” Dad’i na da kai Kenan ka mayar da kanka kayi shiru baka bani amsa ba….. Yana mik’awa doki ruwa yace.” Kace musu nace su ce mata baza’a zo ba.”!! Yanda ya fad’i maganar zaka fahimci a cikin b’acin rai yake. Yunusa yayi jimm! Kafin ya bar gurin ya iske su inda suke tsaye rana na bugun Kansu yace.” Ku fada mata yace.” Yana da uziri.” Suka amsa da “To” duka suka juya domun tafiya.

 

 

 

 

 

 

 

3/3/2020

 

*BINTA UMAR ABBALE*

SADAUKI OMAR

 

 

 

 

*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din……0542382124… Binta Umar GT bank…. Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin….. Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137749 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*

 

 

 

Free pege

 

3

 

 

 

 

 

Jiki a sa’bule Ikilima tayi sallama ta zube gabanta cikin sanyi murya tace”Allah yaja zamanin ki yace.” Yana Dan wani uziri yanzu kiyi hakuri……”Saurara min.”! Ta katse ta tun kafin ta ‘karasa maganar tata mik’ewa tayi zaune tana wani irin huci! Tace”Kamar ni na kirashi yace.” Yana da uzuri ko wane uziri yake dashi nasan nawa uzirun yafi nashi tunda yana a matsayin mai bauta ne bashi da uzirin kansa sai uzirin iyayen d’akinsa yau zai gaya mun Wanda yake d’aure masa gindi a cikin masarautar nan.” Mik’ewa tayi Ikilima tayi saurin gyara mata rufaffafun takalmanta masu wani irin gashi a jiki tare suka futa ikilima na take mata baya gabanta sai fad’uwa yake! Ganin ta nufi sashen su Omar din……… Omar na gama bawa dokuna abincin su ya futo daga tsakanin su can wata rumfa ya nufa kafin ya karasa yaji alamun taku an shigo gurin da sauri ya juya suka had’a ido kallon kallo suke wa junansu Ikilima taja gefe ta tsaya kanta a kasa.

 

 

Tsayuwarsa ya gyara yana watsa mata wani irin kallo kai da ganinsa kasan na kaskanci ne. Wani irin b’acin rai ya sake kamata ita yake wa kallon raini irin haka. A fusace! Ta nufe shi ta d’aga hannu da niyar kwad’a masa mari! Hannun ya rike yana murd’ewa! Ba tayi tsammanin zai dauki matakin haka ba. Cikin dauriya gami da tsananin azabar da take ji ta buga masa tsawa tare da fadin”Sakar min hannuna ma kaskancin bawa Wanda takalmin kafana ma yafi ka daraja a gurina.”!! Omar ya murd’e! Hannuna da karfi har sai da ya bada sautin ‘kas-‘kas! Ta cije baki cikin dauriya don saura kadan hawayen azaba ta kufce mata abunda saboda kar yaga gazawar ta yasa take kokarin dannewa duk da haka dai kana ganin kwayar idonta zaka gane tana kar’bar gashi.!

 

Hannun ya yarfar yana kallonta a ya mutse yace.” Ne man me kike min.!? Aysha ta rasa me zata ce saboda takaici Kuka tasa tana nuna shi da hannunta da yake karkarwa tace”Wallahi sai kayi nadamar murd’e min hannuna da kayi bakin mugu azzalimi sai na kaskantar da kai cikin gidan nan wallahi!

 

Zagin da take masa bai dame shi ba don haka gyara tsayuwarsa yayi fuska a kirne! Ya sake maimata mata tambayar sa ta farko “Nai man me kike min.”!?

 

Hannu ta sake d’agawa cikin shammata zata sake kai masa mari a karo na biyu taji ya damk’i hannun da iya karfin sa! ‘Kara ta saki! Tana kokarin zubewa a gurin! Saura kadan futsari ya kufce mata. Saurin sakin hannun yayi yana kara daure fuska hade da kafe ta da jajayen idanunsa masu girma.”!!!

 

” Allah ya isa na.”!! Abunda take iya fad’a kenan tana matse hannunta hawaye na silalowa a kumatun ta. Ko alamar tausayin ta babu a tare dashi ya sake gyara tsayuwarsa a karo na uku ya sake maimata mata tambayar sa ta farko ” Ne man me kike min. “!?? Aysha yanzu ta fara dawo wa hayyacin ta kwata-kwata sai ta manta Neman ma me take masa ta diriri ce….. Nashi b’angaran so yake kawai yaji Neman me take masa da zata dunga aiko masa ‘yan aike….. Ganin tayi shiru yasa ja tsaki ya juya da niyyar barin gurin…..” Wawa Bakin azalimi Makaskanci Mara Iyaye kawai sai kayi nadamar zaman ka cikin masarautar mu Dan iska sai ka San ni kayi wa haka ni zaka ta’bawa jiki ko? Sai kayi nadamar abunda ka aikata a gare ni.”!!! Kalamanta sunyi masifar bata masa rai har ya tsaya sai kuma wata zuciyar tace”K’yaleta kawai kar ka kulata.” Ci gaba da tafiya yayi ya jiyo ta tana fad’in”Shashasha mai siffar Askarawa kawai.”! Murmushi kawai yayi ya bude d’akinsa ya shige

 

 

Ta juyo a fusace! Ikilima tayi saurin sunkuyar da kanta Don duk abunda ya faru a kan idonta ya faru…”Allah ya taimake ki.”! Ta fada tana sake dankwafar da kanta kasa, Cikin mutuwar jiki tayi gaba ba tare da ta cewa Ikilimar komai ba, da saurin ta rufa mata baya tana mamakin karfin halin Omar da jarumatar sa tunda take bata ta’ba ganin kukan gimbiya Aysha ba sai yau lallai Omar ya cika namijin da za’a jinjina masa.

 

 

 

Jikinta ta zube tana kuka harda shassheka Hajiya Kulu mai dakin kusurwa ta d’ago kanta tana cike da mamakin Wanda ya sanya ‘yar gaban goshin ta kuka irin haka tabbas abunda ya faru Babban lamari ne….. Sai da taci kukan ta ta koshi kafin ta fad’a mata abunda ya faru.

 

 

‘Kwafa kawai Kulu take tace”Wannan ta’kadirin yaro wannan annamimin yaro! Wannan Dan iskan yaro! Ya addabe mu na tsane shi na tsani na bude ido in ganshi cikin masarautar nan har kullum Idan ka zauna da mai martaba bashi da aiki sai na kwarzanta bajintar yaron gami da kwarzanta jarumatar sa wato d’aurin gidin da ya samu gurin mai martaba yasa yake ganin kamar yana ra wata fawa a cikin masarautar nan lallai yau tunda ya sanya ki kuka sai ya raina kansa tabbas zai gane shi din ba kowan kowa bane. Face makaskancin bawa.”

 

 

Aysha ta sauke ajiyar zuciya tana fadin”Mammah duba ki gani fa yanda ya mummurd’e min hannuna duba ki ga saura kadan ya kwashe min fata.”

 

 

Tace”Rabu da d’an banza Idan ma maye ne shi to sai dai yaci kansa domin dai ke Kin fi karfin sa shin wai ma me ya kaiki har inda yake.”? Aysha ta soma inda inda “Nifa ba zuwa nayi ba aike nayi yazo yaki zuwa shine na futo domin zuwa nan kawai naganshi nake masa magana shine kawai ya kamani ya mummurde min hannu.”

 

 

” Yanzu na fahimce ki, Wane irin mataki kike so a dauka a kansa.”? Kawai ki aika a kirashi ni nasan matakin da zan dauka a kansa.”

 

 

“Baiyo.”!!!!! Wacce aka kira da wannan suna futo daga wani karamin daki dake cikin palon gabanta ta zube tana fadin” A gafarce ni Uwar d’akina ina kimtsa miki gado ne.”!

 

 

Tace.” Maza je ki kira min Tafida.”! Ta mike da sauri ta futa… Mintuna uku sai gasu sun shigo tare Tafida ya zube yana kwasar gaisuwa. Tace”Na amsa maka Tafida maza je ka kira min Makaskancin bawan nan.”! Tafida ya gane ko wa take nufi da sauri ya mike ya futa.

 

“Baiyo kije ki cigaba da aikin ki.”!

Da sauri ta mike tana godiya.

 

 

Suna tare da Yunusa Sakon Mai dakin kusurwa wato Kulu ya same shi kwata-kwata ya manta abunda ya faru tsakaninsa da Aysha don shi mutum ne Wanda baya barin Abu jikin ransa jin Kuli ce take Neman sa da kanta yasa ya amsa suka jera tare da Tafida har suka isa shashen nasu Tafida yaja ya tsaya kofar shiga daya daga cikin masu tsaron kofar ne yayi masa ido har katafaran palon Uwargin sarki Wato kulu mai dakin kusurwa!! Bai ji wani d’ar! Ba don ganin Ayshar hakimce cikin kujera ba ya dai yi saurin kauda kansa saboda ganin yanayin suturar dake jikinta dama haka take k’ananun kaya matsatstsu take sanyawa a jikinta kafin ta d’ora alkyaba gata ita tubarkallah macece mai zati a cike take ko ina mussaman a kirinta tana da manya manyan nonowa masu fadi da tsine. Ga uban ships dake bata da tsayi sosai yasa suka futo sosai ko cikin alkyabbata take motsi suke Idan babu alkyabba a jikinta ko ke mace kika kalleta sau daya sai kinyi marmarin sake kallonta saboda yanda take da tsarin jiki mai kyau.

 

 

Omar ya rankwafa tare da fadin”Barka da yamma Ranki shi Dade sakon ki ya isa gare ni wai kina nema na.”

 

 

Tace.” Wato wai ne ma ko? Omar yayi shiru tace”Kai wawa Wanda bai San hallaci ba ina mai tabbatar maka da cewar karshen ka yazo wato baka sanni ba har yanzu ko!? Omar yayi shiru yana sauraron hayaniyar da take masa ta cigaba da cewa”Nice nan Kulu Mai dakin kusurwa Kulu mai magana da aljanu idan baka San labarina ba to kaje ka tambaya kaji wacece Kulu Uwar gidan mai martaba nasan kafin ka futa wajen gari cikin gidanan za’a fada maka wacece ni.”

 

 

Omar dai shiru yayi yana sauraran ta tace”Takad’iri kana ganin kana da girma da kwanji na daukar dutse da k’arfe to duk wannan karfin naka da jarumatar taka basa bani tsoro kawai naso zaman ka cikin masarautar nan Idan da ban so ba da tuni na fatattake ka domin ni nan da ka ganni sharrina yafi dubu naci dubu sai ceto.”!!!!! Takaici da b’acin rai ya kamashi! Ya lura matar kamar bugaggiya take a nutse yace.” Ne man me kike min ko da wani taimako da za’ayi miki.” A fusace! Ta mike tsaye tana nuna shi da hannu “Kai baka isa ka taimake ni ba don ubanka! Waye kai me kake takama dashi!? Duk sanda wannan Kalmar ta sake futowa daga bakina sai ka kwana bakwai a daure.”! Omar yayi shiru yana jinta a fusace! Tace”Me Aysha tayi maka kake kokarin karya mata hannu.”? Gefen da take zaune ya Dan kalla yayi saurin dauke kansa.

 

Cikin tsawa tace” Ba magana nake da kai ba ka sunkuyar da kai kamar munafiki.”

 

“Mammah! Kyaleshi.”! Tafad’a lokacin da take mik’ewa inda yake tsaye ta nufa kansa dake sunkuye ta dago da hannunta ta ware karfinta ta kwashe shi da mari!!! Ko gezau baiyi ba…… ” Baiyo.”!!!! Ta kwala mata kira ta futo da sauri tana amsawa tace”Je ki taro min bayin dake sashen nan su kuzo tare.” Baiyo ta futa da sauri domin cika Umarnin da aka bata.

 

 

Add Comment

Click here to post a comment