Littafan Hausa Novels

Auren Gado Hausa Novel Complete

Auren Gado Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AUREN GADO*

 

 

 

 

*Matar soja ce*

 

 

 

Daga marubuciyar

KUKURE NA

BARIKI AUREN SOJA

MUK’ADDARI

WANAKE AURE

ZANYI BIYAYYA

And now AUREN GADO,

 

 

 

*ASLM MAKARANTA, INA YIWA KOWA FATAN ALKHAIRI, GODIYA MARA IYAKA ZUWA GA MASOYA RUBUTU NA A DUK INDA KUKE, JINJINA TA BANGIRMA GAREKU, SOYAYYAR KU ABIN ALFAHARI CE AGARENI, GOYON BAYANKU SHINE SILAR CIGABA NA ALLAH YA BARMIN KU A DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI, TUNDAGA MASOYANA NA NIGERIA DA KUMA NA KETARE INA WA KOWA FATAN ALKHAIRI, NAFA DAWO BATAREDA NA SHIRYA BA DOMIN KU MASU BIYONI SUNA ROKONA, MATAR SOJA KIFARA MANA AUREN GADO MUN MATSU, TOH GASHI NAN SAI NEMAN GOYON BAYAN KU KAMAR KODA YAUSHE,*

 

*with ur help wnn lbrn zaitafi AUNTY deeja domin bantaba tsallaka koda airport ba don haka keep guiding me akan komai, and please make sure kin turomin na jirgi nasameki a bangkok din nan just once please, tunda corona ta hanani zuwa makka bana, but don’t worry kudin na gona just pray muyi harvesting buhu dari na soya beans, bana zamuje vocation a duk fadin bangkok, ayi kokari a biya don Allah zansiya takin gona 😉*

 

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM

 

 

 

 

🆓 page

 

 

 

1⃣&2⃣

 

A kwance yake abakin wani tafkeken beach , yana kallon duk matan dake kaida kawowa a wurin cikin fitinannun bikini da kuma lafta laftan sun glasses, wani irin ya mutse fuskar shi yakeyi domin kamar kashi haka yake ganin su, ba Abinda ya dameshi, bayajin mace zata iya burgeshi just like that saboda shigar banza,

Kallon shi nayi dakyau, gayen ba laifi chocolate ne shi duk da banga idanun shi ba saboda suna boye a cikin sun glass, Amma nasan zasu kasance masu kyau da tsari, lips dinshi kuwa I can clearly see them suna sheki very soft and shinny, he is behaving like jinin sarauta Amma I don’t know yet who is he? Gefen shi system dinshi ne tareda wayoyin shi guda biyu, daya tayi kara ya dauka cikin sauri domin ganin sunan dake jikin screen din wayar, “heartbeat, Hmmm no wonder mata basa burgeshi duk da yawon da sukeyi a gabanshi necked, sai dai me, yanda yake zuba shagwaba tareda maganar da yakeyi yasa mamaki ya cikani domin daga gani bada mace yake magana ba, is he a gay???

 

“Yaya please, wai kai are you really serious you are getting married??,

Banajin maganar dayan side d’in saidai Amsar shi, “of cos yaya dole inzo Auren ka nine fa best friend best brother and ur best partner in life, am coming insha Allahu, but kasan halin momy kuma I don’t want problem shiyasa nake zama na a bangkok, is alright am on my way don’t worry heartbeat, just for you.

Datse call din yayi ya mike, a lokacin na kalleshi da tsarin jikinshi daba riga sai guntun wando kawai ga six packs dinshi da suka fito gwanin burgewa alamar yana gyming, tareda kulada lafiyar jikinshi sosai, zare sunglass din yayi, na kalle sexy eyes da lashes dinshi kamar na mace zaro zaro, he is really handsome, one look zakiyi mai ki afka soyayyar shi indai zaki kalli wa’innan killer eyes dinshi, gashi ya iya juyasu, kamar wani karuwar namiji, cikin takun kasaita ya zura beautiful sleepers dinshi na maza ya kwashi kayanshi tareda key ya nufi can gefe inda ya parker open jeep dinshi, ya zube su tareda zama yajata a guje yabar wurin,.

 

Wani D’an madai daicin gidane a cikin jerin gidajen dake cikin unguwannin dake shahararriyar Unguwar ta

Phetchaburi Road, Makkasan,

Ratchathevi, Bangkok 10400 Thailand. unguwa ce ta wanda ya tada Kafada da Abubuwan duniya, duk da gidan da ya shiga ba wani kato bane amma kana ganin shi kasan ya gaji da haduwa, maid dinshi ne yayi saurin taron shi da gorar ruwa tareda towel, karba kawai yayi ya nufi bathroom, ya dauki Kusan hour guda kafin yafito kamar zai canjo fata,

Yana fitowa daure da guntun towel ya tsaya Turus tareda zubawa dakin ido yana mamakin ta, tayi mai dai dai tareda kashe shi da idanu, he just hate that character a wurin mace, shi so yake rana daya Allah ya hadashi da mace mai kunya, that is, tagama siyemai zuciya, but this kind of girls dake rayuwa a irin wannan garin wai in the name of study, Ahh he really hate them, karuwai kawai,

Ganin kallon rainin wayau Dayake watsa mata yasa ta zaburo tareda matsowa cikin rangwada, doguwar riga ce har kasa she cover all her body but akwai gyara a al’ amarin ta, duk da kyakykyawa ce gata a dire, kuma fara tas bai hana kagano idanun ta sun bude,.

“Hey dear tafada cikin kashe murya, wani irin kallon don’t touch me ya mata tayi saurin daga hannun ta sama tareda cewa “is ok I won’t dear, but please just once give me chance to prove myself.

“Dont even try to suffer ur self, nafada miki fauzy am not interested, just back up. ” am ready to follow you I promise zanyi duk y’anda kakeso am ready to change for you, nafada ma dady na kai nakeso zamu koma kano tare dakai please na horu ka soni don Allah, “Look don’t even try, bazan Auri sauran wasu ba infact am not ready for marriage now shiyasa dana gama school naki komawa gida saboda nasan Abinda zai faru, don haka kifita a rayuwa ta banason naci. Kuka tasa mai tareda dukawa kasa, “I swear bantaba bari wani yasanni ba kawai romance ne kuma kasan is a normal thing ai, kana ganin saboda kai nakasa komawa gida kullum cikin karya nake musu please karka tarwatsa min Rayuwa kaine cikon numfashi na, tausayin ta yaji sosai domin ta dade tana wahala a kanshi tun baya kulata har yafara D’an sauraran ta, “Oh come on, kinsan natsani kuka ko, ki shirya am going tomorrow mutafi nija am going for good, if you are ready….. “Of cos dear am ready, tafada tana dariya mai hade da tausayin kanta, goge hawaye tayi tafita cikin sauri domin ganin ta tattara duk Abinda zata bukata.

“Ahhh yafada tareda dafe kai, this girl is headache I swear,

Shiryawa yayi cikin guntun wando da black singlet yafito gwanin burgewa sai tsadadden agogon shi da kuma dankwalelen zoben dake karawa hannun shi tsari da kyau wa’inda baya taba rabuwa dasu, infact ko shopping zaiyi agogo ne first a tsarin shi he just love watches saboda suna karamai tsari da kwarjini,

 

Abincin shi ya zauna yafaraci wa’inda duk ganye ne sai crabs roasted ones, saida ya dauki lokaci kafin ya kammala ya sanya tissue ya goge bakinshi ya mike, duk al’adar Chinese ta gama ratsa shi abincin su harshen su al adunsu, wainda zasuyi matukar wahalar dashi a nija,.

Saida yayi clearing komai a daren, about visa da sauransu, karfe uku na Asuba jirgin su ya daga wanda zai kasance long journey duk da a jirgine, tafiyace ta Kusan awoyi, tana zaune a gefen shi ta zuba mai ido sai faman danna system dinshi yakeyi like ba wata halittar dake existing a kusa dashi,

 

She don’t bloody care tunda yace su koma nija tasan komai zaizo cikin sauki,

Saida ya dauki lokaci kafin ya rufe ya saka headphones ya rufe idanun shi yana farin cikin zaije wurin yayan shi wanda yafi kowa daraja a duniya a wurin shi yana mashi so mai girma yana kaunar shi fiyeda kanshi,

Duk da su marayu ne ubansu ya mutu tun yana D’an karami, baiyi lacking komai ba, domin baban su gawurtaccen D’an siyasa ne kuma D’an kasuwa wanda yanada share a manyan campanonin dake ciki da wajen kasar mu harma da ketare, subiyu ne kacal wurin mahaifiyar su, yayan shi Ahmed sai shi Ibrahim khalel wanda khalel din ne yafi amfani dashi,

Gatan da yake dashi baya faduwa haka kudi ba matsala bane a rayuwar su domin mahaifiyar su itama ba azaune takeba tana aiki da first bank tareda matsayi mai girma,

Akwai banbancin hali a tareda shi da d’an uwanshi, domin shi mai zuciya ne, shikuma Ahmed yanada sanyin hali da hakuri, shakuwa ce mai girma da tausayi a tsakanin Y’an Uwan biyu sukan iyawa juna sadaukarwa ta kowacce hanya, tun suna yara balle kuma yanzu, kowa yasan how they love each other, don haka ko ginin su a hade yake basu taba raba gida ba duk da sunfi karfin hakan, katoton gidan mahaifin su suka kara fadadawa tareda buga plat biyu nasu tangama tangama sai na mahaifiyar su wanda a ciki ma akwai part part dinsu, domin bataso suyi mata nisa, mace ce mai tsananin zafi da kuma rashin hakuri gashi bata son sunan talaka bare kuma talauci batason rashin Aji a rayuwar ta don haka kullum burinta ta fantama, bakaramin shiri takeyi a Auren ya’yan taba tunkafin su tashiyi ma, saidai kash ansamu akasi domin Ahmed ya kaucewa tsarin ta ta hanyar dakko Y’ar talaka tulus, wanda bakaramin daga akasha ba kafin ta Amince da zancen Auren bayan dogayen sharuddan data gindaya bayan Amincewar ta. To muje dai zuwa yanzu zamu fara,.

 

 

 

Karfe goma jirgin nasu ya sauka a babban filin jirgin na Aminu kano, wanda sukaci karo da motoci birjik a jere na taron su, tuni fauzy ta matso “you see kamar jira akeyi indawo kaga irin motocin da sukazo daukana please ka yarda muje gidanku after two days sai intafi gida. “Hmm yafada tareda watsa mata kallon you lost ur mind, kafin ya ce “al adar Chinese ce wannan ba ta bahaushe ba don haka go home zanyi inviting dinki to my brother wedding ok,. “Ok tafada cikin farin ciki, ta nufi masu taron ta wainda kana ganin motocin kasan itama Y’ar gidan wani kwallon barawon kasar muce,.

 

Hango yayan shi da yayi yasa ya tafi da sauri cikin farin ciki ya rungume shi, Ahmed din ma kyakkywa ne suna matukar Kama saidai shi fari ne while Khaleel chocolate ne, “my yaya kai kadai kazo were is mommy?

“Long story muje ko, yafada yana karbar jakarshi karama tareda bawa driver umarnin kwaso kayan da yazo dasu yakai boot, saida suka zauna yace “Am sorry yaya sai jiya nayi placing odar na kayan matar ka zasuzo tunda by air ne kafin bikin insha Allahu nasan zakaso su.

Rungume shi yayi cikeda farin ciki tareda cewa “tank you my kani, but please karka bari momy tasani kawai zamu Ajiye mata ne a dakina har akawo ta. “Why? Cos momy batason ta infact bakaramin yaki akayi ba kafin ta Amince ayi komai. “Mommy mommy bazata canja ba, so why she hate her? “Because she is poor. Saurin kallon shi yayi “so brother is your foult kasan momy tunfarko ai why ka dakko poor girl uhm?

“Because I love her so much I love Naziya a lot khaleel, she is innocent and young she is very cute I can’t help it, bazan iya Auren wata ba in har aka hanani zama da ita. Rungume shi yayi cikeda so da kuma tausayin D’an Uwan nashi yace “is ok am here you know I will support you, don’t mind mommy, but her name is unique. “Yeah she is also unique brother, yafada yana lumshe idanun shi tareda jin soyayyar ta mai zafi har wasu irin madarar ruwan hawaye ne suka taru a idanun shi,.

 

A cikin fitacciyar unguwar ta sulaiman crescent suka yada Zango cikin wani tafkeken gini na kece raini, tsarin gidan kamar a turai, ya fito tareda shakar iskar kayan marmarin dake zagaye da ginin gidan,

Harabar gidan shake yake da motoci different product da kuma runfuna na Alfarma dake karkashin bishiyoyin kwakwa ta ko ina irin na gargajiya da masu kudi keyi,.

 

Kallon shi Ahmed yayi tundaga kasa har sama “bazaka canja character dinka bako yawo daguntayen kaya imagine tundaga bangkok kazo da three quarter da t shirt baka ko jin sanyi? “Kamar ka mantani ko yaya nifa I hate heat wallahi shiyasa nake wuni a beach., zaka hadu da momy muje ciki,.

 

 

A tafkeken katon falon an tsara shi fiyeda tunanin mai karatu kujeru Kusan set uku ya mamaye amma da sauran fili kowane set da center carpet dinshi masu laushi da nutse kafafu, standing art tangama tangama ta koina bayan na jikin gini wainda suka zama kamar decoration a falon,

A tsaye take tanata kai da kawo kamar Y’ar sintiri tana jiran fevourite son d’inta, ya iso, ta hana masu aiki sukuni sun kalkale but parts dinshi yafi sau uku da safen nan, dishes kuwa kamar a hotel saboda d’oki,

Macece hakima kamar Aisha D’an kano margayiya taci Abuja style cikin tsadadden leshin ta wanda yafi karfin dari a jikin ta, da glashin ta na kara karfin idanu, wanda yakara fito da haiba da hutun ta harma da masu gidan ranar data tada Kafada a ciki,

 

Sallamar su yasa tamike cikeda fara’a tana “Oyoyo my happiness welcome back dear tafada tana rungume shi tareda bubbuga bayan shi, “tank you mommy munsame ku lafiya? “Alhmdulillah tafada tareda dagowa tana “ai dai tunda kadawo yanzu zanji saukin lamura na at least inada inda zancika burina, ka huta ka dage ka dakko min Y’ar gidan bayero ko buhari, ka huce min takaici. Tafada tana watsawa Ahmed harara, dukar da kanshi yayi tareda daukar Karamar jakar D’an Uwan nashi yayi ciki da ita, zama tayi a set daya tareda janyoshi tana faman korafi tun bai hutaba, ” hope zaka dakko Y’ar gidan mutanen arziki kai ba Y’ar matsiyata ba? “Mommy mommy mommy please meyasa kike hakane? Nifa am here because of my brother, kinsan banason korafi kibarshi ya Auri choice dinshi koda cripple ce tunda shi zai zauna da ita please allow him to be happy I beg of you. “Shikenan tunda kaima kabi bayan shi, amma promise me zaka share min hawaye kaji? “Ok I promise bari inje in huta am tired, fresh up akawo maka abinci a ciki ko? “Yes please kinsan me nakeso ai ko? “Sosai karka damu na shirya maka komai.

A zaune yasamu brother dinshi yana dafe da kanshi ya zauna tareda dafashi cikeda tausayi “relaxed bro am here komai zaiyi normal kaji, Aunty what ma sunan ta? “Naziya, yafada fuskar shi na washewa domin sunan ta kawai nabashi farin ciki, “get ready zamuje unguwar su anjima kaganta kaji. “Ok my heartbeat. “Stop that name kafin my Naziya taji tayi kishi fa. “Oh no yaya zata shiga tsakanin mu ne, to nima zanbi bayan mommy fa. Rungume shi yayi tareda cewa “no no no tasan da zaman ka, tundaga lokacin da muka fara haduwa, da ita, ka huta zanfada maka komai game da ita kafin muje gidan,.

Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

 

Karfe biyu ya farka daga baccin gajiyar da yayi yaga Ahmed zaune ya na baza kamshi cikin D’an datsesiyar getzner tana maiko, tashi yayi “yaya har kayi wanka? What is the time now? Agogon shi ya nuna mai ya zabura yana holy shit, ya diro a lumtsumemiyar katifar shi, yayi bathroom domin baiyi Azahar ba, cikin sauri sauri ya zura jallabiya ya tada sallah, domin duk abinda yake yi baya son wasa da ibadar shi amma idan ka kalleshi zaka dauka rayuwar duniya tafi komai ratsa shi amma yarone mai riko da Addini bisa ga goyon yayan kwarai da yazamo mai tamkar uba.

Saida ya idar ya bude jakar shi tareda ciro kananan kaya.

“Wait gidan kawu zamuje a mandawari kasan halin shi ka sa manyan kaya nasa an shirya maka new ones a wardrp dinka na nan dana can side d’in.

“What? Kasan nifa banason zafi ga garin nan da zafin tsiya kuma insa kayan da zasu hanani sakewa, “wait yaya ba an gama zuba komai ba a part dinmu why muke nan har yanzu? “Bisaga umarni na khaleel bazan yarda a saka Y’ar talakawa cikin ginin da na narkarda dukiyar mijina datawa ba, a kawo min gayyar k’uma da kudin cizoba ta zo nan ya isheta zama tunda bazata iya zama a katon giniba, domin ko dakin generator dinmu yafi gidan ubanta girma,. Saurin kaucewa khaleel yayi domin inda sabo sun saba, ya nufi katon wardrp din yaga kaya shake saida yayi murmushi saboda yasan aikin yayan nashi ne,

Fito da Kala daya yayi irin na jikin shi ya nufi hanyar bathroom domin ya canja saboda mommy dake dakin,

Tana zazzaga complain, fitowa yayi tareda rungume ta yana baza kamshi shima kanshi da yasha askin matasan zamani ya na sheki ya sha gyara ya ce” mommy please enough of your complains kibar yayana yasamu farin cikin shi mana,. “Oh wato kuna tunanin bansan what is best for him ba ko? Bayan na kawo mai yammata Kala Kala Yaran kawaye na masu ilimi amma ya nace sai Y’ar talakawa mtsww, ka kara Abinci kafin kutafi gidan kawun naku kafin yazo yana baza min fitinar shi shima yace na hanaku zuwa ku gaidashi, ta fita tana kasaita, “Hmmmm Sorry brother kariga kasan halin momy. “Is ok eat muje ko?

 

Hour guda ta kaisu gidan na kawun nasu Alhaji modu mai gwal wanda D’an kasuwa ne sosai a harkar gwalagwalai, mutum ne a tsaye akan zumuncin shi domin baida wasa yanada mata biyu da yara sunkai goma, shikadai Hajiya balkisu ke shakka domin yafita fitina kuma shima yanada kudi shiyasa take ragamishi domin sau tari yakan yimata Abu tace yaci Arzikin Aljihun shi.

Sunada kanni biyu mata bayan mahaifin su khaleel shine babba sai Alhaji modu din, su Y’an Asalin garin maiduguri ne iyayen su ne suka kawosu babban birnin na kano, sunginu suma duka domin ba talaka a cikin su har matan ma domin suna gidajen kusoshin kasar mu,

 

 

Y’an mata ne birjik a gidan wainda kowaccen su nada burin samun daya daga cikin wa’innan zaratan mazan saidai sam su Hankalin su baya kan kannin nasu infact basa burin Auren zumunci ma, itama Hajiya balkisu bata ra’ayi domin batason ya’yan ta suyi Aure inda bazata iya juya Suruka ba,,

Domin tasan Y’an Uwan mijinta duk ba wai mutunci sukeda shiba wanketa zasuyi akan ya’yan su,

Sun samu tar bar bangirma daga uwar gidan Kawu modun kafin ya dawo,

Sundauki lokaci a gidan har kawun nasu yazo, wanda yayi farin ciki sosai ya musu nasiha tareda basu shawarori, “yanzu tunda kadawo khaleel saika tallafawa D’an Uwan ka domin yayi matukar kokari wajen tafiya da campanoni da kuma masana’antun ku, sai kuci gaba da tafiyar da kasuwancin ku cikin tsari, Sannan naje munyi magana da uban Naziya, Auren naku nan da sati biyu aka tsayar don haka ka je ka karasa shirin ka “na kammala komai kawu ni ta wajena. “Toh masha Allah, sai mu jira lokaci Allah ya tabbatar da Alkhairi, Amma dattijon nata mutumin Arziki ne baidamu da Abin duniya ba gaskiya karka damu da shirmen mata wannan gidan irin shi ya kamaci namiji ya nemi Aure. Wani irin dad’i yaji tareda sauke Ajiyar zuciya, saida suka yi magrib kafin su bar gidan, suna hanya yana bashi labarin Naziya,…….. 🖊

 

 

*watch out, domin salon zai tafiyar daku masoya muje zuwa*

 

 

 

*Matar Soja*

[16/08, 11:51] : *AUREN GADO*

 

 

 

 

*Matar soja ce*

 

 

 

Daga marubuciyar

KUSKURE NA

BARIKI AUREN SOJA

MUK’ADDARI

WANAKE AURE

ZANYI BIYAYYA

And now AUREN GADO,

 

 

🆓 page

 

 

3⃣&4⃣

 

 

………….. D’an karamin gidane mai zaure a cikin tsohuwar unguwar ta jakara, almajirai ne birjik a zauren da Alama malami ne a gidan mai Y’ar Karamar tsangayar Almajirai, ko tsakar gidan ma akwai wasu dakuna dake dauke da Almajirai, rayuwar gidan sun dauki Almajiran kamar Yaran gida ba kyama ba wulakanci, matar gidan inna kulu mace mai hakuri, tanada ya’ya mata guda hudu manya biyu sunyi Aure sai Naziya da kanwar ta Shukrah, Yanzu Naziya nada shekara goma shatakwas sai shukrah mai shabiyar, ta kammala secondary dinta Bana a makarantar gwamnati, a tsugune take tana wanke kwanonin da suka bata Y’ar Karamar wayarta ce a kunne a gefen ta tana sauraron karatun Al’qur’ani mai girma tana bi a hankali cikin kwarewa,

Kare mata kallo nayi domin yarinyar batayi Kama da kalar talaka ba domin dai dai da duddugen kafarta farare ne tas kyakkywa ce sosai kamar wata Y’ar larabawa tana sanye da guntun hijabi akan al adar ta da kuma koyarwar inna kulu domin gidan su akwai mazajen Almajirai akoda yaushe, fitowa dattijuwar tsohuwar tayi tareda cewa “inkin kammala ki dora mana Abincin rana Naziya, shukrah ta kai mana markade tunda duk babu Almijirai yau, “toh Inna. Tafada tana wanke wurin data bata, she is really cool and beautiful ga tarbiya dake tattare da ita jikinta ba rama kuma bakiba duk da tana cikin hijabin ta nagano hakan jikinta D’an dai dai bazaka taba yimata kallon talauci ba duk da Abinci baifi karfin tukunyar suba, mahaifin su yana koyarwa yana sana’oin shi wanda yake daukar gidanshi da kuma hidimomin iyalin shi,

Haduwar ta da Ahmed wata rana ce tadawo makaranta a gajiye shikuma yazo unguwar su gidan wani yaron shi dabaida lafiya, tafiya takeyi cikin gajiya a kuma natse ta gefen titi, y’anda ya kwaso motar tashi yasa ya watsa mata ruwan datti kasancewar gari ne na damuna ga kuma yanayin unguwar da yatara guraben ruwa ta ko Ina, saurin jatayi ta tsaya domin gaba daya uniform d’inta ya baci Har fuskar ta ma ruwan ya fallatso mata, saurin fakawa yayi ya fito da sauri yana so yabata hakuri,

Dago kyawawan idanun ta tayi tareda goge fuskar ta da gefen hijabin ta inda jan ruwan bai bata ba, ta kuma kallon y’anda ya saki baki yana kare mata kallo batareda ya iya cewa komai ba, yarinyar ta gama tafiya dashi, juyawa tayi ganin baida niyyar cewa komai tayi gaba, saurin shan gaban ta yayi “Am sorry please ki tsaya muyi magana, ya zaki wuce batareda kince komai ba bayan nayi miki laifi?

Saurin Tsayawa tayi tareda dago idanun ta masu narkar da zuciya tace “nice zanbaka hakuri domin hanyar bata Y’ar talaka bace Nazo kuma na tsaya, sannan don Allah ka matsa in wuce kafin ayi wani tunani akaina a cikin unguwa ba mutuncin gidan mu bane tsayuwa da bako a kan titi. Tafada tana rabewa tayi gaba.

“Wow wow wow what a magic voice, yafada yana binta a hankali tana sauri har ta fada gidan su da gudu domin tana jin takun shi a bayan ta a mugun tsorace take dashi domin yayi Kama da Aljani a wurinta domin he is very handsome kana ganin shi kaga D’an hutu,.

 

Gefen Ahmed tunda yasa Naziya a ido yakasa sukuni saida yabi ta gefen yaron shi yaji komai akanta, tuni yagano Y’ar babban gidace wato gidan dattijan kwarai, baiyi kasa a guiwa ba ya dawo yasamu mahaifinta tareda neman izinin neman ta, Malam garba yaso ya hana domin ganin D’an gidan wani ne Bayason ya saka Y’ar shi cikin matsala, ya nuna mai mahaifin shi ya rasu kuma shike rikeda kanshi ba wata matsala, bai Amince ba saida ya turo kawun shi yazo suka tattauna ya Amince yabada izinin neman ta,.

 

Allah yagani bawai Ahmed baiyi mata bane, ita batada burin shiga gidan da yafi karfin ta wanda bata ma riga taga dukiyar ba tukun kawai shitake gani kudin su na bata tsoro, ganin irin k’a’i dar mahaifin ta, baya ko sake mata kudi infact tuni ya daina zuwa da shigar da zata hanata sakewa dashi domin ya lura da yanayin ta dana gidan su tsab, yasamu kanta ta hanyar nuna mata akarkashin wani yake shima yana hustling ne,. Shiyasa yasamu kanta har ta Amince suka Gina soyayya mai karfi a tsakanin su she really loves him domin he is very simple baida fushi baida girman kai saurayi ne mai natsuwa wanda ko yatsanta bai taba kokarin kamawa ba soyayya yake mata mai tsafta, har kawo yanzu da Al amarin yakai ga zancen Aure, zaman ta dashi tagano Abu biyu sune masu matukar muhimmanci a rayuwar shi, mommy and khaleel wanda basa hira sutashi bai kira sunan shi ba tagano irin tsantsar soyayyar da yakewa kanin nashi ta hanyar bata labarin shi a kullum zaice “in munyi Aure zaki rika dafa mai Abincin da yakeso baya son irin namu na nija zansa akoya miki irin dishes din da yakeso. Abun na bata mamaki ace mutum Abincin mu na nija mai shegen test baya burgeshi sai mara magi? she almost know everything about him by now saboda labarin shi, tasan yana karatu a waje kamar yadda Ahmed yafada mata kawun su ya kaishi waje karatu, Ita kanta so take taga wannan khaleel din da labarin shi baya karewa a bakin Ahmed,. Tana son Ahmed sosai halin shi, yanayin natsuwar shi ya banbanta da na samarin zamani masu burin cakumar mace da sunfara soyayya……..

Wannan shine D’an takaitaccen labarin Naziya da Ahmed.

 

 

A hanyar su ta dawo wa daga sabon titi yake bashi labarin komai na su Naziya tareda fadamai boye mata kudin da yayi saboda batason mai kudi y’anda ta nuna mai. Khaleel yasamu kanshi da yin dariya, ” she is funny wace mace ce batason hutu da kudi in this era? ” my Naziya wants a simple life ba a ginata akan greedness ba, all this kyale kyalen duniya basa burgeta do you know nasha siya mata gifts in ajiye domin gudun matsala ko fushin ta, do you know tun zaman mu bata taba demanding tana bukatar wani Abu a wurina ba, “she is such a diamond in the rocks, she is different khaleel my Naziya is perfect I told you. “Hmmm Allah yasa tana sonka like you love her? “She do Insha Allahu, koda baikai wanda nake mata ba nasan tana sona,

Karar wayar khaleel yasa yace “my God this witch. Yafada yana cutting call din. “Fauzy right? “Yes yaya ta cika naci bana son mace mai naci. “Hhhhh you are lucky khaleel fauzy batada laifi and secondly irinta mommy keso Y’ar gidan wasu kaga babanta ne minister na kudi, don haka bakada matsalar mommy kabada kai musha biki bayan nawa. “Yaya why ake Aure? “Hhhh khaleel saboda Aure sunnah ce mai karfi, sannan ba Abinda ke karawa namiji mutunci irin Aure, ga kuma samun natsuwa da soyayya idan kayi dace. “Yaya I don’t need any natsuwa a wurin mace ni. “Ah bakada lafiya ne? “Kalau nake kawai bana jin akwai macen da zatasa inji ni a namiji sai kawai in lafiyata ta motsa,. “You are wrong khaleel, kana samun macen da kakeso manhood dinka yadaina kwanciya cikin sauki, domin the moment you fall in love, zaka ji duk duniya ba Abinda kakeso sai kasamu kwanciyar hankali da farin cikin zuciyar ka, you are my younger brother but bazan boye maka ba na matsu ba a daura min Aure da Naziya ba am eager to have her ban taba jin lafiya ta tana aiki ba saida na hadu da ita, don haka kaima duk ranarda ka afka soyayyar wata zaka gano komai. Dariya kawai yayi domin shi yasan lokacin da kawai yake samun erection sai inya tashi a bacci yake sanin he is healthy ba wata Y’ar macen dake daga mai hankali domin bai sawa ranshi ba ma bare Abun duniya ya dame shi.

 

Cikin unguwar suka nufa wadda tuni yaji wani iri musamman irin kofar gidan dayaga sun tsaya Almajirai birjik sunata karatu ga hasken farin wata daya dallare KO Ina fiyeda hasken lantarkin dake wurin, wayar shi ya daga tareda danna number ta, ba bata lokaci ta daga hade da yin sallama, “Gimbiya kifito ku gaisa da heartbeat tare muke dashi.

Cikin murna ta mike tace “gani nan zuwa yanzu inga wannan kanin namu.

Yana kishingide ko motsi baiyi ba impact bayajin zai iya fitoda takalmin shi wajen wannan unguwar, dole momy tayi spark ai, don ma batazo tagani ba ma da in sama da kasa zata hade ba Yarda zatayi ba yasani.

Fitowa tayi cikin natsuwar ta sanye da hijabin ta, ta karaso jikin motar dayake tsaye nad’e da hannu, ya zubawa kofar gidan idanu har ta karaso kusa ta d’an tsaya nesa kadan kanta akasa ta gaida shi, “Ina wuni. “Lafiya kalau gimbiya ya kike? “Alhamdulillah, cikin muryar ta mai cikeda natsuwa, kwankwasa glass din motar yayi, ya sauke a natse tareda gyara zaman da yayi kamar wani sarki, kamshin shi mai matukar tsada ya huro tareda muryar shi mai cikeda wasu irin sirrika suka sakata dago kai cikin sauri,

A cikin kyawawan idanun shi nata yasauka domin hasken motar na haskashi dakyau, wani irin sanyi jikin ta yayi Mata domin Sam baiyi Kama da sunan kanin Ahmed ba a wurin ta saidai Yaya, irin cika motar da yayi da kwarjinin shi tareda kamshi da cikar haibar shi, kallo daya ta sauke idanun ta akanshi Wanda tsab da ita gwanace ya isa ta Zane hoton shi, daga ganin shi bazaiyi yawan magana ba, kuma zaiyi miskilanci sosai. Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji saukar muryar shi a cikin kunnen ta “Yayana naga Auntyn zamu iya tafiya ko? Shine kalmar data fito kawai batareda gaisuwa ko wani dogon zance ba. Ta shirya sakewa dashi domin karo dankon soyayyar ta a zuciyar Ahmed, amma is impossible yanzu don taki jinin girman kai da nuna isa just because yaje waje karatu, tuni taji yafita a ranta takuma daura damarar Kama kanta da Al amarin shi koda ta shiga gidan nasu,. Saida Ahmed ya leka kanshi tareda zuba mai ido “come on brother kafito mana ku gaisa da kyau, “no mungaisa daga nan ka sallameta mutafi nagaji kasan bangama hutawa ba, yafada a mugun kagare yake subar wurin yanajin warin Almajirai daga inda yake Idan yakara more minutes a wurin he will surely vomit,. Ya lura da yanayin shi don haka a gurguje ya sallameta ta tafi tana mai jin takaicin wannan khaleel din,.

Yana tada motar yace “Yaya wannan Y’ar yarinyar zaka Aura? Why?? she is too young for you please, fuskar shi a kwabe, “hhhhh she is perfect banason Auren katuwar mace ko over twenty nafison irinta mutum ya mori kuruciyar ta yafi Amma Idan ka Auri wayayyun mata bazaka mori komai ba, nafison innocent girl da zankoya wa komai,. “Hmmm zakasha aiki wallahi ai wahala zakayi kafin wannan ta iya daukar ka, kuma Yaya iyayen ta suka yarda suyi mata Aure? “Yes saboda mu anan takai Aure tunda ta kammala secondary,.

“What? Yaya this is too much, da Ina nan bazan bari kafara sonta sosai ba gaskiya. “You are too late now, domin inaji a jikina Idan ban Auri Naziya ba zaku iya rasani so ku tayani Addu’a kawai Ina son ta fiyeda tunanin ka nasan you will always support my back. “Of cos brother Insha Allah.

 

 

Karfe goma suka isa unguwar su, Wanda mommy Saida taci gaba da fada “kunje ghetto Area ko nasani saiya jamun kai, ka wuce kayi wanka kazo kuci Abinci kaima wuce ka watsa wainnan kayan dustbin kafin ka dawo falon nan kajini ko? Wucewa yayi cikin sanyin jiki ya tafi dakin shi Yana mai jin bakin cikin halin na momyn shi, kasa fitowa yayi saboda rashin jin dadin Abun, shima khaleel kasa cin komai yayi ya kalli momyn dake kan korafi “mommy why please? Ki yi hakuri Ki daina fada akan abunda dole za ayi. “Yes za ayi Amma ni Balkisu bazan bari ya cakuda min iri da na talakawa ba mu zuba tunda dangin ubanku sun nuna sunfini iko akan shi ni kuma zan nuna musu sai naso komai ketafiya mu zuba nida su.

“Momy ji nake kamar in koma bangkok kawai domin bazan iya tsayawa inga d’an uwa na a damuwa ba, please Ki barshi ya samu natsuwa mana. “Khaleel, kana ganin uwa zataki d’an tane? Ina son Ahmed kamar yanda nake sonka saidai bazan iya kawar da idona akan kwashi kwaram din da zai debo min ba.

Mikewa yayi kawai cikin fushi yabar mata Abincin yayi dakin yayan nashi, a kwance yake Yana tunani, dafashi yayi, dagowa yayi tareda rungume Khaleel din, “brother am worried, bansan irin zaman da zamuyi da Naziya a gidan nan ba, bana so injefa Y’ar mutane a damuwa bayan an bani amanar ta. Bubbuga bayan shi yayi “karka damu Ina nan zan taimaka maka ba Abunda zai samu baby doll dinka. Yafada cikeda dariyar tsokana domin ya kwantar da hankalin d’an uwan nashi,

Shigowa tayi dauke da tray tana fara’a domin taga Alamar Idan tayi sake yaran nata zasu juya mata baya akan zancen Auren nan, Wanda bazata taba Yarda da hakan ba,

 

 

“Toh yaran momy ga Abincin nakawo muku ni na damu kuci, kashin awaki, ta ajiye a tsakiyar gadon tareda jansu da hira kamar zata mayarda su ciki, tuni suka ware suka kwashi deshes din, tana cewa “bayan rasuwar mahaifin ku nayi iya bakin kokari na ganin bakuyi maraici ba, Alhamdulillahi yau dukan ku kunkai matasa Abun Alfahari a wurina, forgive your mother Ahmed na dauki buri mai girma akan ku naso nice zanyi maku zabin matan da suka dace daku Amma ka watsa mun duk shirina Ahmed. “Am sorry momy, kuma nayi miki Alkwarin zaki samu Naziya a duk yanda kikeso bazakiyi dakin sani ba yarinyace mai tarbiya da kin Amince da tuni nakawo miki ita ma kingan ta. “Aa tunda ansa rana ai lokacin zaizo don haka basai ka kawo taba, bakomai zan cika burina akan khaleel. “No mommy khaleel ma yanada tashi zabin ai, yafada Yana kashe mai ido, “no no no bana sonta Yaya please meye haka she is my mate fa tare muka kammala karatu why zaka ce Ina sonta ita keso na ni banga Y’ar da zanso ba har yanzu’

Wani irin dadi mommy taji ganin khaleel bazai juyuba a wurin mace tunda ita keso shi bayaso ai irinta takeso, “wow Auta na wacece wannan yarinyar? “Mommy Y’ar gidan minister kudin Nigeria ce, “what? Tafada tana dafe kirji, “Y’ar gidan mai nasara kake fada? Oh my god khaleel, ta rungume shi, that’s my son, ka kawomin ita kaji kace tazo inganta Amma ka gama wanke min zuciya d’an nan. Tafada tana mikewa bari inkira Auntyn ku infada mata tafara shirya mana babbar harka ta Fita tana danna kiran kanwar tata mai ra’ayi irin nata. Binta sukayi da kallo suna mugun mamakin halin na mommy, sai kace wadda bata jiku da kudi ba, kullum she is hungry for more, kallon Ahmed yayi da fuskar tausayi yace “why zaka fada mata Yaya kasan am not ready, kuma yanzu tunda taji bazata taba bari insha ruwa in Ajiye cup ba. “Is OK fauzy love you a lot kuma meye laifinta nasan tun lokacin da kuke tare, ya isa haka ka Amince bayan nawa kawai a daure min kai, do you know, Ina mafarkin ganin Auren ka? Ina so inyi witnessing Auren ka inga jinin ka. “Hhh oh come on Yaya kamar wani tsoho na barin wasiyya please tare zamu cika gidan nan da yara, “who know Khaleel? Allah kadai yasan me zai faru gobe, kasan cewa nan gaba kaine zaka rike gidan nan? “Why Yaya? Indai har kana nan bazan taba daukar girma ba saidai in tafiya zakayi dole in rike kana dawowa zanbaka komai domin ka shagwaba ni tuntasowa ta Abu daya nasani shine in saka master card dina inciri duk Abunda nake so ba tareda antanbaye ni me nayi dasu ba, Yaya nasan kudin da daddy yabari bawai haihuwa sukeyi da kansu ba kaine kakara habaka su har suka kai haka kaine jigon gidan nan bazan taba iya Abinda kakeyi ba…… “Shhhhhh zakayi Idan bana nan fiye ma da Wanda zanyi saboda I believe kai jarumi ne kafini iya tafiyar da Rayuwa. “Enough of this discussion kana sani a damuwa. “OK now kakira fauzy kafara bata kulawa domin tunda zancen yaje kunnen mommy ba fashi, yafada Yana dariya,.

 

Fita yayi daga dakin yayan nashi yanajin wani iri “Aure? Gaskiya bai shirya ba infact zaiyi ne saboda yayanshi ya insisting kuma koda baison Abu Idan yayan shi na sonshi dole shima ya soshi, Allah kadai yasan iyakar soyayyar da yake wa d’an uwan nashi, kwanciya yayi a kujera a dakin nashi Yana mai runtse idanun shi, so yake ya tuna komai na fauzy da quality’s dinta just for Ahmed, Amma first thing da yafado mai a rai yasa ya zabura tareda girgiza kai, “no no no why her?

Cikin Sauri ya dauki wayar shi domin ya k’aryata tunanin shi, fauzy ya Kira, kamar mai gadin wayar ta ta dauka jikin ta na rawa “oh my goodness darling you call me? Tafada tareda Sanya kukan farin ciki, tundazu take kiranshi yaki dagawa har wani zazzabi takeji saboda damuwa tana yimai wani irin so mara misali. Tun isowar ta ake tarairayar ta Amma duk natsuwar ta bata tare da ita,

“Yes I call. Yafada Yana gyara zaman shi domin baisan ma mai zaice ba kuma. “Tank you darling for calling, please Ina so inganka kasan is hard for me kwana daya bansaka a idoba I can’t. “Is OK zaki iya zuwa gidan mu gobe yanzu dare yayi. “OK am coming tomorrow tank you darling. Tafada tana buga tsalle tareda rungume filo, tasan yafara damuwa da ita tunda har yake so taje gidan su yanzu, hakurin ta ya fara aiki yanzu. Kwanciya tayi tareda Addu’ar gari yawaye ta ganta agidan su.

 

 

 

Gefen Naziya ta shiga gida da takaicin khaleel, domin yaron mugun d’an wulakanci ne, inba wai gizo idanun ta ke mata ba kamar kallon kyama yake mata, bayan duk unguwar su an shaida tsabtar su, duk da suna fama da Almajirai Inna kulu nada kokarin ganin ta tsabtace gidanta sosai,. Kwance take tana juyi shukrah ta matso gefen ta akan Y’ar madai daiciyar katifar tasu, tace “Aunty lafiya? “Hmm bakomai. “Aa Ina kallon yanda kike ta juyi tundazu kinkasa bacci, meke faruwa ne? “Kawai Ina tunanin yanda zan zauna da Ahmed ne tareda kanin shi shukrah dazu sunzo, baida k’irki irin Ahmed ya cika girman kai da nuna shiyayi karatu a kasar waje. “Ni kuwa Aunty kallon Arziki sosai nakeyiwa Yaya Ahmed fa. “No yafada min Yana da ubangida mai kirkine watarana motocin yake zuwa dasu, “nidai Aunty Ina tantama domin ko tsarin jikinshi ya isa ya nuna Yana cikin hutu. “Ni kuma me zakice dani? Tunda kowa kallon Y’ar masu kudi yakemin a school ko in munfita, halitta ce kawai. “Hmm tom kiyi bacci Ki kyale wani kanin shi Bashi zaki Aura ba.

 

 

 

Washe gari Karfe goma tayi mata a gidan su khaleel cikin tangamemiyar motar ta ta yayi, da kanta ta tuko kanta, da taimakon shi ta zo gidan domin unguwar su ba boyayya bace, momy ta zage sai rawar kafa takeyi an shirya mata tarba Kala Kala, cikin adon jan material doguwar Riga dinkin yayi na yayan masu daula, taci gwala gwalai wuya da hannayen ta tana zabga sheki da kamshi. Ta hadu ba sauki domin ta iya caba ado. Tasamu tarba gefen momy, Wanda koda tazo gidan bai tashi baccin safe ba,

Momy sai Ina ta saka Ina ta Ajiye takeyi da ita, sai zare idanun ta takeyi taga inda zai bullo. “Huh khaleel na bacci haryanzu bai tashi ba, kinsan da gajiya a jikin shi.

Shigowar Ahmed ne yasa Momy tace “ka duba d’an uwan ka ko ya tashi ga bakuwar ta iso. Gaisawa sukayi Yana Kara ganin wayewar ta da kudi Wanda yasan ba yanda za ayi Naziya tazo gidan nan saboda shi, banbancin yayan talaka kuma y’an gidan mutunci kenan da kuma ya’yan masu kudi. Yanzu meye Abun burgewa a nan mace ta nuna rawar kafa akan namiji, idanun fauzy ya gama budewa gaskiya and zasuyi kusan sa’a da Khaleel like he said, wucewa yayi Yana daya sanin bashi goyon baya akanta,.

A kwance ya sameshi Yana kallon saman pop, “oh you wake up? So kazo fauzy is here. “You see tunda Asuba mayyar ta tanbayeni address nafada mata don uwar ta a gidan mu zata karya? Dariya Ahmed yayi, “Auzubillahi yada zagi? “That’s why Yaya bana sonta wallahi batada kamun kai Sam ace Karfe goma ta zo wurin saurayi saikace ba iyayen ta a gidan. “Yanzu dai katashi kayi fresh up kafito tana jira mother in law dinta ta bata big welcome. Tashi yayi ya shige bathroom, like Always Saida ya kwashe hour guda kafin ya fito Wanda shirin nashi ma Saida ya kwashi rabin hour cikin guntayen kayan nashi kamar yanda ya saba.

Cikin takun kasaita da shan kamshi ya fito falon, fuskar shi Sam ba fara’a, “ga shinan yaron kirki ya fito. Mommy Tafada tana mikewa tareda taroshi kamar wani kwai jitake kamar ta goyashi saboda so, jikin fauzy na rawa tace “hy darling kamar ta ruga ta rungume shi takeji. “Tashi kuje dakin shi zakufi sakewa bari insa a hado muku breakfast akawo ciki. Cikin sakewa tace “Saidai baby ni ai mommy kin cika min ciki tun zuwana kike duramin ciye ciye, Tafada tana Dariya, “Allah Y’ar nan, to bakomai ai gidan kune nan.

Zama yayi a falon fuskar shi a cakude yace “ke iyayen Ki basa gidane kika fito early morning? Kallon fuskar shi tayi tareda yin murmushi duk da tasan maganar banza yafada mata ranta bai baci ba, “mommy na nan dady na nan kuma sun san inda naje. “Really? Kuma basuyi kokarin hanaki ba? “Why zasu Hanani? Bayan su masu goyon baya na ne akan duk Abinda nakeso kasan cewa sun san komai akan ka dady na a shirye yake da katuro neman Aure na, please khaleel ka cika mun burina I promise zaka sameni yanda kakeso zan share maka damuwar ka duka zanbaka gatan da mata basa iya bawa mazajen su just give me chance.

“OK zanturo tunda mommy ta Amince dake and my brother too yanzu kije gida zanturo. Tsalle ta buga tareda Dane shi ta rungume shi kam” don Allah da gaske zaka tura? Oh my god khaleel zanyi suman dadi yau. Tafada tana share hawaye, ban bare ta yayi a jikin shi ya ce “oh come on a gidan surukai kike fa behave yourself.

“Farin ciki ne yamun yawa baby muje mota indakko wa momy tsarabar ta please, Tafada tana riko hannun shi, jinta takeyi kamar anyi mata bushara da gidan Aljannah……. 🖊

 

 

 

 

 

*Matar Soja* *AUREN GADO*

 

 

 

 

*Matar soja ce*

 

 

 

Daga marubuciyar

KUSKURE NA

BARIKI AUREN SOJA

MUK’ADDARI

WANAKE AURE

ZANYI BIYAYYA

And now AUREN GADO,

 

 

🆓 page

 

 

 

5⃣&6⃣

 

 

..,………. Kaya na kece raini ta kawowa momy tsaraba Wanda tayi ta godiya kamar zata goyata, bayan tafiyar ta bata da wani zance sai na “Ibrahim khaleel bikin ka zamu gwan gwaje ba karya kaga Abun Arzikin da ta kawomin tun ba ayi Aure ba? Wucewa yayi cikin dakin shi domin shi yanzu daya sani yake mara iyaka daya Amince mata tazo gidan su har Mommy ta ganta, yanzu ya boni shikam………

Wasa wasa Saida aka kwashe kusan sati daya bai kuma daukar wayar taba ta Kira ta turo msg yafi hamsin Yana shareta, momy tayi nacin zancen turawa gaisuwa Yana ja baya, domin shidai bai shirya ba infact baya ra’ayin zama da fauzy she is not his choice zai cutar da itane kawai, bazata taba samun kanshi yanda take soba. Bikin Ahmed da Naziya ya matso gefen gidan su shikadai ke shirin shi da Abokan shi Yana cikin tsananin farin ciki, momy tace bazata wahala akan Y’ar talaka ba, yan uwan tane dai suka fara cika gidan, musamman Aunty zarah, Wanda itace kanwar ta da sukazo hali daya, komai na Aunty zarah sai a hankali tana son gayu da babbar harka.

Duk akwatunan da Ahmed ya hada momy ta sa anrage duk wani gold tasa ancire ansa passion wai basu san darajar su ba talakawa ne. Baida yanda zaiyi saidai farin cikin shi daya Khaleel ya hadomai Nagani na fada a bangkok, don haka sunkai sun boye sai in ta tare, duk wani event mommy ta soke wai yarinyar da ba wayayya ba yaja musu Abun fada bada itaba, don haka ya hakura domin Albarkar Aure yake nema in Allah ya mallaka mai ita burin shi ya gama cika, sannan farin cikin shi daya itama tace bata son wani bidi’a walima ta isheta da za ayi a gidan su,.

Khaleel yana gefe baya cewa komai he just feel boring baiga Abun burgewa a yin Auren ba ba wani Abu da ya bashi sha’awa da har zaiji yanason yayi Auren ma, fauzy sarkin naci tazo tun Ana jibi Bikin ta tare duk inda Aunty zarah ta shiga suna tare gaba daya yabi d’an uwan nashi sun kauracewa gidan suna part din Ahmed saboda jama’ar da suka cika na momy, yaki ko Yarda su hadu da ita, ta d’an ji sanyi ganin tana cikin gidan su kuma no matter what sai sun hadu kafin ta koma gida, ita da ta samu daurin gindi a wurin uwar miji ma, ita kanta tasan mommy batason Auren Ahmed domin ta gama bata labarin ta tas.

 

Rana bata karya inji bahaushe, Alkawari ya cika, inda Aka daura Auren Ahmed da Naziya akan sadaki mafi daraja, sai muyi fatan Allah ya kade fitina, tunda aka daura Auren ya baro taron ya dawo gidan tareda kulle kanshi cikin dakin su, zazzabi yakeji mara dalili tareda jin wani irin bakon Al amari a tattare dashi, Ahmed nata neman shi, Saida ya kirashi ya dauka yafada mai cewa yana gida, dawowa yayi shima tareda barin Abokan shi ya same shi a dukun kune cikin bargo,

 

Cire babbar rigar shi yayi ya zauna gefen gadon tareda cewa “bakada lafiya ne? “Fever ke son kamani, “sorry namiji, kasan me? Yafada yana gyara zama, tashi Khaleel yayi ya jingina a jikin gadon yace what my brother? “Burina yacika khaleel, today Naziya is legally mine, but am worried me zata fuskanta a cikin gidan nan, how is she going to react after she find out about everything? “Like what brother? Like our wealth, this big mansion, and mommy. Yafada yana rage murya cikeda tausaya wa kanshi, kamar yarone yaga alawa Ana mai kwalelenta haka yakeji yanzu, yasamu farin cikin shi Amma baya cikin farin ciki.

 

Matsowa yayi sosai kusa da d’an uwan shi yace “Yaya this is the time da zakayi fighting back, ka tsaya akan ra’ayin ka, you have to talk brother, fight for your love, and Aunty Naziya will be happy bazaka samu Matsala da itaba, in tace zata sama yayana hawan jini bazan raga mata ba cos batasan irin fighting da kakeyi akan soyayyar taba. “Hmmm you known, nafison momy ta barni in zauna a gefen mu, bana son Naziya ta shiga cikin damuwa nasan zata sha wahala Idan akace zata zauna cikin gidan, she can’t handle it, bata saba da irin wannan rayuwar ba. And mommy is our mother dole mubi Abinda takeso Auren Naziya da A hannu na yake Dana hakura for mommy happiness, but Allah kadai yasan mai ya boye a cikin Al’ amarin,

Yafada cikeda damuwa, Dariya khaleel yayi mai d’an sauti wadda ta Kara bayyana kyanshi sosai, “Yaya this my Aunty is very lucky, tasamu miji mai sonta sosai Anya zaka kuma Aure nan gaba like the way mommy is planning? ” no Khaleel bana son Naziyata ta zauna da kishiya Ina so tayi rayuwar y’anci ne, Ina son inganta cikin hutu da walwala, khaleel na gama tsara irin yanda nakeso rayuwar Naziya ta kasance, I love her beyond your imagination, ka tayani son Naziya kaima kamar yanda nake sonta.

Sundauki dogon lokaci yana daukewa yayan nashi damuwa ta hanyar k’arfa famai guiwa, Saida friends suka fara kiranshi ya Fita tareda barin khaleel cikin damuwa, Alwashi ya dauka mai girma akan zai taya yayan shi fighting akan duk Abinda zai daga mai hankali bazai so yaganshi cikin damuwa ba,.

 

Bai kuma Fita a gidan ba ko sallah a part din yakeyi ya koma ya kwanta, yarasa abunda duk ya Cire mai walwala da natsuwa bayajin dadin jiki da zuciyar shi baki daya, he just fee like going back to bangkok, baisan mai ke hana shi sukuni ba. Sai Karfe Tara Ahmed ya kuma shigowa dakin ya tsaya a kan shi tareda cewa “brother what is wrong? You look very dull. “I don’t know Yaya kawai bana jina cikin natsuwa. “relax nima haka nakeji tundazu but now am fine, your Aunty is here khaleel, finally Naziya is here. Zama yayi tareda rungume Khaleel din yana fitarda hawayen da yarasa na menene ke fitowa daga idanun shi.

Saida ya d’an natsu yace let go and welcome your sister in law. Mikewa yayi ba musu, ya bishi sanye cikin kana nan guntayen kayan da ya canja tundazu.

 

Gefen Naziya kuwa tunda suka sako kai cikin wannan tafkeken gidan gaban ta ke faduwa gashi gwaggonnin tane suka rakota su uku bisa ga umarnin malam domin baison gayyar tsegumi, kanta a duke yake tunda motar da ta dakko su ta shigo, cikin Y’ar rakiyar ta daya tace “t’irk’ashi wannan gidan mutum daya ne ko dai gidan y’an yankan kai? Sauran suka fara salati, shikenan malam saida Y’ar nan yayi, irin wannan gidan saikace wata unguwar? Saurin daga kanta tayi ta saki baki tareda dafe kirjin ta tana karanto Addu’ar tsari a cikin zuciyar ta, jikin ta shegen rawa yafarayi. Har motar ta tsaya Abokin da ya dakko su yace “Hajiya kufito mu shiga ciki ko? Kamar way’enda kwai ya fashewa a ciki haka suka fito ji sukeyi kamar ace ar su ruga, shi ya musu jagora kowaccen su Addu’ar da duk tazo bakin ta takeyi, rike take da tsintsiyar hannu irin wainda ake rikewa na share dattin daki a wurin sabuwar Amarya bisa ga Al Ada, nasan wasu sun san wannan Al Ada akan ce ta share duk fitinar d’akin kafin ta zauna cikin dakin ta.

 

Daya cikin gwaggon nin nata tace “kawo Abar nan inrike da ita zankoma Y’ar nan domin ko takarda bazaki shara ba a gidan nan, “Toh ai gidan da waje ma babu ko Alamar d’aud’a bare ciki, ai wajen ma ni yafi dakina tsafta, haka suketa sambatu tsakanin su. Ita kuwa jitakeyi kamar ta ruga da gudu saboda tsoro, wasu irin zafafan hawaye ne ke zubowa akan kyakkyawar innocent face dinta. She is regretting today, wayace ta Amince mai? wayace ta yarda da Auren shi? gashi yayi mata karya yakawo ta gidan da bata taba zuwa kusa da irin shiba.

 

 

A falon mommy ce hakimce itada y’an uwan ta, Zarah ce ke gefen ta da kuma uwar y’an kanzagi fauzy, sunayin Sallama mommy tace Zarah kusa katuwar tabar mar nan akan carpet din Idan sun tafi a fita a Y’ar da ita a waje kar k’uma ta shigo mana gida.

Sunji komai a kunnen su jikin su na rawa suka karaso akan tabarmar suka zauna tareda gaida su cikin girma mawa, cikin su daya tayi karfin hali tace “Hajiya toh ga Amanar Y’ar ki nan Allah ya tayaki riko.

“Ni Amanar me zaku bani saikace wata kishiya ta, to kuji infada muku tun mijina nada rai ko zance bai taba zuwa ba bare ayi zancen yimin kishiya, don haka karma ku fara ku jira Wanda ya Auro ta yazo kubashi…… Yauwa ga shi nan ma, Tafada tana nuna shi domin yana fitowa yaji zancen momyn wani irin zafi tareda damuwa zuciyar shi ta shiga. Khaleel ma yaji komai kuma he is not happy da irin yanda mommy takeyi ga su fauzy dake musu wata irin Dariya kamar sunga kashi itada zarah, wani irin baci ran khaleel yayi da Sauri ya matso tareda kallon Fauzy, ” ke wace iri ce uban me kikeyi a gidan mu haryanzu baki tafi ba?

 

“Aa banson shirme Ibrahim, ya yarinya tazo maka k’ara zaka hauta da fada? “Mommy angama Bikin tazo ta wuce gidan ubanta tom. Jikin ta na rawa ta zabura ta nufoshi kamar zata fada jikin shi “no please na dauki permission wurin mommy na ta yarda inyi kwana biyu baby just for you….. “Oh come on, ke meyasa bakisan….. Saurin dafashi Ahmed yayi domin bayason more humiliation agaban y’an uwan Matar shi Dama ita kanta, yanzu yana tunanin how he is going to face her ne ma.

Shiru yayi tareda juyawa da Sauri ya yi cikin dakin shi dake part din momy, ranshi yayi mugun baci dole ya koyawa wannan fauziyar hankali gobe.

Fadin zuciyar Naziya da tunanin ta bata lokacine ma, daya daga cikin y’an uwan mommy ne tace “ku muje in nuna muku part d’in ta, Tafada tana mikewa kafin ya yar ta ta kuma kwab’a, sanyi Ahmed yaji domin yama d’askare yakasa ko motsi.

Suna shiga suka ware idanu domin basuga ko tsinken da sukasa aka kawoba, wadda ta rakosu ce tace “wannan dakin mijinta ne gidan su na waje a can akasa da kayan ta, kamar tasan me suke tunani,

Domin sunga gadajene na kasar waje ba irin nasu d’an wambai ba.

 

Cikin sauri sukace “tunda munrako ki Naziya mu zamu koma dare nayi, Allah yabada zaman lafiya da hakuri kinji ki rike tarbiya da mutuncin malam Dana kulu domin kinsamu tarbiya dai dai gwargwado kinsha nonon hakuri da kuma mutunci, Allah ya kade fitina. Suka juya cikeda sanyin jiki, riko daya daga cikin su tayi tasa kuka “Don Allah gwaggo karku tafi kubarni ni kumayar dani gida wurin Inna bana son nan gidan. Tafada tana kuka mai cikeda tausayin kanta da Rayuwar ta, daga shigowar ta harta karanto irin Rayuwar da zatayi a cikin wannan gidan.

Shigowar Ahmed ne yasa takara rike ta gam tana gunji. “Ahmed ka rike Amana ga Matar ka mu zamu tafi kaji. Babbar Tafada cikeda tausayin Y’ar tasu, hannu yasa zai rikota tayi tsalle ta koma gefe tareda sakin su tana gyara hijabin ta dogo.

Fita sukayi ta koma gefen dakin ta zauna tareda saka kuka mai zafi da kuma k’ara,

Rakasu yayi a gurguje yadawo domin kukan da takeyi bakaramin daga mai hankali yakeyi ba.

A zaune take ta hada kai da guiwa tana kuka mai ciwo. Zama yayi dabas a gaban ta cikin sanyin jiki, tanajin kamshin jikinshi daya cika ko Ina, takasa dagowa. Hannun shi ya dora saman kanta, da yasa tayi Saurin dagowa tareda ja baya tana Kara hade jikinta wuri daya,

“Am sorry bazan kuma tabaki ba tunda bakyaso, Amma please kiyi shiru haka kukan ki na tabamin zuciya sosai.

Yafada yana kallon yatsun Hannun ta farare tas da sukasha jan lalle Hannun ya mugun burgeshi, ji yake kamar ya riko ya tsotsa, bai taba ganin lalle ya burgeshi ba sai a Hannun ta. Jin shirun shi yasa ta dago tareda zubamai lashes d’in ta masu kyau da kuma fararen idanun ta da suka cabe da ruwan hawaye, taga Inda yake kallo da ya shagalar dashi sosai. Saurin cusa Hannun ta tati cikin hijabin ta da yabashi damar kallon na fararen kafafun ta, wani irin gauron numfashi yaja tareda d’an matsawa kusa da ita, ta kuma ja baya again. “Why Naziya? Please karki horani a haka zuciya ta zata buga, ki horani ta kowacce hanya but karkiyi min iyaka da zuwa gareki, am dreaming about it always, nasan ni mai laifine a wurinki, Amma kisani ni mai sonki ne shiyasa na boye miki gaskiyar rayuwata Naziya banason in rasaki I love you so much my wife. Yafada yanajin wani irin shauk’i da yanayi mara misali, kallon shi takeyi wani iri kamar zataga wani Abu daban, batajin zata iya Rayuwa a cikin wannan gidan tareda kuma mahaifiyar shi da itace farkon matsalar data Kara girgiza ta.

 

“Am sorry Naziya, nasan i’m wrong domin bakiyi planing zama a irin gidan nan ba, yafada yana murmurshi, domin itace mace ta farko dayaga wai batason daula. How silly? Maganar mommy tasa yayi Saurin ja baya tareda tashi tsaye ya kalleta “kazo ka zauna gaban jaririyar yarinya a daren farko to kazo ka wuce dakin d’an uwan ka kowa yasan ango baya shiga dakin Amarya sai anyi budar kai don haka wuce kabani wuri tun ban sab’amaka ba.

Daukar babbar rigarshi yayi yafita jikinshi a sanyaye. “Ke kuma ki tashi kidaina wannan kukan munafuncin kije kisha Ac anzo inda yafi gidan tsoho ga katifa mai numfashi aje a more, kin zo kina kukan munafurci. Tafada tana fita dakin cikin fada. Zubewa tayi nan kasan dakin tasa kuka, “Ahmed yasa ankawo ta inda bazata taba yin mutunci ba,har wani irin ciwo taji gefen kanta nayi saboda kukan da takeyi.

 

A kwance ya samu khaleel idanun shi a bude yana kallon saman dakin wani irin zazzabi yakeji har yanzu Wanda yarasa dalilin faruwar shi, jin takun d’an uwan nashi yasa yayi Saurin juyawa ya kalle shi, “Yaya ango me kakeyi a nan yau? Yanda yaga hawaye tareda ganin damuwa kwance a fuskar d’an uwan nashi yasa yaji tuni zazzabin shi ya tafi, tashi yayi cikeda damuwa yace “Yaya taki kulaka ne? Zan bata mata rai Idan ta nemi jefamin kai cikin cikin damuwa. Yafada jikinshi na rawa domin yaune karo na farko dayaga hawaye a idanun jarumin yayan nashi mai hakuri.

“Mommy. Yafada yana Rungume d’an kanin nashi domin yasamu sauki. “Me tayi kuma? Fadamai yayi yana jan numfashi, “oh Mommy, Bari inje inyi mata magana. Yafada yana kokarin tashi tsaye, rikeshi yayi tareda girgiza kai, “karkaje tace Al Ada ce sai gobe zan shiga wurin Matata.

“What kind of Al Ada? “Budar kai. Zabura yayi cikin haushi “let me talk to her. “No leave it, just do one thing please go and check on her please she was crying.

 

“No kabarta zatayi shiru ka kwanta yau ne kawai tunda ka hanani inyi mata magana.

“Please go Ina so inji ko tadaina kuka, inaji a jikina tana can tana kuka.

Bayason musu, especially da yayan nashi don haka mikewa yayi kawai ya fita.

Ba kowa a falon yanzu duk Suna cikin part din mommy Suna hira da shewa, girgiza kai yayi yana tunanin Abinda zai aikata gobe a gidan halin shi dasuka sani bai canja ba bayason rubbish. Tundaga falon yakejin kukan ta kasa kasa. Wani irin zafi yaji a zuciyar shi, da sauri ya shiga dakin, a kwance take a kasan kamar yanda take tundazu saidai yanzu Ana iya ganin kayan jikinta domin duk hijabin ya tattare ya koma wurin cikinta, zaka iya ganin perfect figure dinta, Wanda ko Ahmed bai taba samun damar ganin ta haka ba, kullum tana cikin hijabi, akan kafarta idanun shi yafara sauka.

Wanda wani irin attraction ya rika jansa ya kasa Cire idanun shi, “first time da henna designs ya Bashi sha’awa, ga kafafun ta kamar na turawa a mulmule farare tas dasu, “Wow she is Unique, zuciyar shi ta furta. Domin tsarin jikinta da yake gani, bai taba ganin small body with a perfect shape ba like her.

Motsinta yasa yadawo hayyacin shi cikin Saurin tareda tsorata ta zuba mai ido, tana zarewa, domin ita bata taba ganin katon namiji irin shi da guntun wando da singlet a gaban ta hakaba, wane irin gida Ahmed ya kawota, da Sam ba tsari ba wani sanin ya kamata. Saurin jan hijabin ta tayi kasa tana mikewa kukan nata ya dauke dif, fuskar shi mai natsar da yaro mai kukan banza, tuni ta hadiyi wani irin miyau, she knows he’s khaleel domin ganin farkon da tayimai bazai taba bacewa a idanun taba. Gaba daya jitakeyi ya cika mata dakin da girman shi, ga fuskar shi mara walwala, idanun shi masu dauke da wani irin sinadari Wanda batasan ma ma’anar shiba. Juyawa tayi ta Bashi baya ganin ya dauke kanshi batareda ya iya cewa komai ba. Saida ya dauki lokaci kafin yagama tunanin yanda zaifara yimata magana, cikin karfin hali yace “good tunda ba kuka kikeyi ba, Yaya na is worried sosai shiyace inzo in dubaki, tunda kinyi shiru shikenan, yafada yana tafiya batareda ya kuma kallon gefen taba, a falon yaci karo da ledar da yayan shi ya Ajiye Wanda kowane ango ke shigarwa Amarya da ita, dauka yayi ya koma, dai dai ta kuma juyowa, idanun ta suka kuma cin karo dashi, wani irin Saurin juyawa ta kumayi ledar ya Ajiye “you have to eat karki kwanta da yunwa Yaya na zai damu. Yafada yana fita Hannun shi cikin pocket din guntun wandon nashi.

Cikin sauri bayan ya fita ta dannawa kofar key domin Allah yagani batason ganin shi again,

 

Add Comment

Click here to post a comment