Littafan Hausa Novels

Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammad (SAW)

Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammad (SAW)

 

 

 

 

 

 

 

 

Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammad (SAW)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

Tarihin Annabi Muhammadu (ﷺ)

 

 

 

bismillah

 

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai

 

ﻭَﺻَﻠَﻰ ﺍَﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﻦْ ﻵ ﻧَﺒِﻲِّ ﺑَﻌْﺪَﻩُ

 

Tsira da amincin ALLAH sutabbata ga ANNABIN dababu wani bayanshi

 

Salati da tsira da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (ﷺ)tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Maɗukaka.

 

TARIHIN MANZON ALLAH (ﷺ).

 

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan Abdullahi (Sallallahu alaihi wa sallam).

Tarihin Annabi Yusuf AS

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan qusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam,

 

 

(Harshen Larabci: Abūl-Qāsim

Muḥammad ibn AbdAllāh ibn Abd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

 

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Aminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdul-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi yAllahu anhuma).

 

Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

 

Laqabinsa: Almusɗafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.

 

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka.

Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in.

 

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah (swt) su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.

 

Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa maɗauwamiya ita ce Kur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

 

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.

 

Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

 

Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi ɗauki ba daɗi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.

 

Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu ‘yar Zami’a da A’isha ‘yar Abubakar da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab ‘yar Huzaima da Maimuna ‘yar Al-Haris da Juwairiyya ‘yar Al-Haris da Safiyya ‘yar Huyayyi ɗan Akhdabl.

 

‘Ya’yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faɗima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.

 

Ammominsa: su Tara (9) ne, su ‘ya’yan AbdulMuɗallib ne: Al-haris da Zubair da Abu ɗalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.

 

Ammominsa mata: Su shida (6) ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali ɗan Abi ɗalib (a.s) da Hasan ɗan Ali da Husain ɗan Ali da Aliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan Ali da Ja’afar ɗan Muhammad da Musa ɗan Ja’afar da Ali ɗan Musa da Muhammad ɗan Ali da Ali ɗan Muhammad da Alhasan ɗan Ali da Muhammad ɗan Hasan Mahadi (a.s).

 

Mai tsaron qofarsa: Anas ɗan Malik.

 

Mawaqinsa: Hassan ɗan Sabit, da Abdullahi ɗan Rawahata, da Ka’abu ɗan Malik.

 

Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi ɗan Ummu Maktum da Sa’ad Al-kirdi.

 

Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!

 

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

 

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H. Wajan da ya yi wafati: Madina. Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Maɗaukaki Mai alfarma. Ka sani cewa Muhammad (ﷺ) shi ne qarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa qarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (ﷺ) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (ﷺ): Shi ne Muhammad ɗan Abdullah (ﷺ) kuma babarsa ita ce Aminatu ‘yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul awwal bayan ɓullolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa). Aiko Annabi Mai Daraja (ﷺ)

An aiko Annabi Muhammad (ﷺ) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaqi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saqon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah ku rabauta” .

 

A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riqa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa’adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni” . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane qalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).

 

Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari’arsa mai sauqi mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaqoqi masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maqiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowane lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaqoqinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba.

Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saqo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur’ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (ﷺ) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (ﷺ) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

 

Bayan cikar addini da kafa Ali ɗan Abu ɗalib (A.S) shugaba na al’umma kuma halifa bayan Annabi (ﷺ) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: “A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni’imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini” . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauqi, sai dai ya yi tsanani har sai da ya haɗu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H.

Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (A.S) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a ɗakinsa a Madina inda qabarinsa yake yanzu. Ya kansace abin koyi ne shi a riqon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alqawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawan ɗabi’u, da baiwa, da ilmi, da haquri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da taqawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da qasqan da kai, da jihadi. Jikinsa ya kasance qololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuqa wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da ɗabi’a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.

 

Ataqaice, ya tattara dukkan wata ɗabi’a mai kyau da girma da ɗaukaka da kuma ilimi da adalci da taqawa da kuma iya tafiyar da al’amuran duniya da na lahira, waɗanda babu wani mahaluqi da yake da irinsu. Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: “ɓarna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo” . Allahu

 

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻛَﻤَﺎ ﺻَﻠَّﻴْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻛَﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ

ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﺁﺗِﻨَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﺣَﺴَﻨَﺔً ﻭَﻓِﻲ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﺣَﺴَﻨَﺔً ﻭَﻗِﻨَﺎ ﻋَﺬَﺍﺏَ ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ

 

Add Comment

Click here to post a comment