Littafan Hausa Novels

Sadaka Yalla Hausa Novel Complete

Sadaka Yalla Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

️SADAKA YALLA

_(Baraa ko karuwanci! Love, Funny, romantic and sympathy story)_

 

 

*Idan kashiga Damuwa da kunchi ka tuna Allah…*

 

 

Free page

001

 

 

 

*AUNTY AISHA MMN TEDDY*

 

 

_Bismillahir rahmanur raheem_

***

 

_LONDON_

 

 

Tafiya yake yi tare da hayewa stairs ɗin dake tsakiyar falon ,wanda hannun sa ɗaya na a kunnen sa da ya dafe wayar sa ƙirar iPhone x Wanda ko ba’a ce ba kasan kira yake mai muhimmanci ,tun daga yanda ya natsu yana sauraren mai maganan …ɓangare guda kuma na ɗayan hannun sa handkerchief ne mai ɗan girma ,wanda yakai girman madaidaicin Towel yana sa hannun sa tare da tsane zufan dake sauko masa ba ƙaƙƙautawa…kallon sa nayi ina ɗan ƙare masa kallo ,namiji ne wanda yafi kama da sura da ƴan dambe don gamɓan sa ka kalla yanayin girman su sai kaji tamkar ka sa gudu kabar inda yake ,ga fuskar sa ɗaure babu alamun rahama . Hannun shi yakai yana shafa sajen da ya bari a fuskar ,yana hura iska tare da furxar dashi ….Abdul Ahaad shine kalmar da ya kuma katse sa ,wanda ta kira shi murya babu wasa. Lumshe lulun daƙwa daƙwan idanun sa yayi kamin ya amsa ɗayan ɓangaren kirar da Na’am Ammie”. I say you should come Back”. Wannan itace magana ta ta ƙarshe . Ni nasa ka, kuma nayi maka tilas ka taho London a lokacin da baka buƙata! And now all is gone , is past so what next? Ka dawo gida nageria. Shekara ɗaya kenan aka shugaban ƙasar Nigeria yace ” Ƙasa ta yafe maku zunuban ku , don haka ka dawo gida ,shekara kusan goma kana London…sai dai mu ƴan uwa idan mun matsu muna Son ganin ka muna aiki da saukar jirgi? Na gaji bakai kaɗai ba duk wani soja ma tuni ƙasa ta yafe maku akan guduwar da kuka yi a aikin soja! Nasan Ni na saka ka kayi hakan ba’a Son ran ka ba,amma ka sani Ni uwace kuma Ni na haifeka ,bazan bari na yarda ina gani da idanu na na rufe a turaka daji halaka ba…baka rasa gatan uwa da uwa ba. Wannan shine dalilin faruwar komai don haka Pls Abdul come back Nigeria now. Ta ƙare maganan tana yin shiru tare da sauraren jin na bakin sa…wanda kusan mintuna biyu bai ce mata komai ba ,sanin waye shi da baƙin ma miskilancin sa yasata yin shiru ba tare da tayi fushi ta sauke wayar a layi ba.

 

My Uncle Hausa Novel Complete

“Ɓangaren Abdul Ahad kuwa nisawa yayi yana ware idanun sa da suka sauya daga fari zuwa jah a lokaci ɗaya Ammie”. Ya kira sunan ta cikin wani irin murya na Son fahimtar da ita…kana yace ” Wai yanxu Har Nigeria abun yarda ne, da don sun faɗi abu since ya wuce shikenan ya wuce? Wallahi ƙarya sukeyi , kuma duk wani wanda yabar Nigeria ya gudu daga shekarar mu akan Boko Haram sai yanzu zuwan kidnappers Ace mu dawo mu yi yaki mu koresu ,wani yayi kuskurar dawowa to wallahi kashe shi za’a yi har lahira Ammie,kar Fah ki manta rantsuwa mukayi kan zamu tsaya mawa gida Nigeria koda zamu rasa rayukan mu .an kashe da yawa daga cikin mu ,wanda mu saboda mun shiga soja da kuɗaɗen mu wannan yasa da muka ga baxamu iya ba muka bar Nigeria , and now na riga na zama cikakken ɗan ƙasar London there is now more Ammie ,na fi jin daɗin rayuwar nan a yanzu.

 

 

Abdul Ahaad! Ta kira sunan sa cikin convenient voice Kamin tace ” Yanzu Fah su wa ke mulkin Nigeria? Abie ne fa! Mahaifin ka! Pls pls Ahaad ka natsu shekarun ka Fah yanzu yaci ace kana da iyali 34 ba wasa ba… Ammie! Ya kira sunan ta yana katse ta ba tare da yajira jin me zata faɗi ba…Ammie yanxu suruka kike buƙata ,so I have many girlfriends here , Wanda Ni suke jira a ko wani lokaci…there’s Shirley and angeleka so… Ya Isa wannan shashancin banzan ya ishe ni haka! Ba angeleka ba , Allah yasa Angel ne Mala’iku n zare rai ban yarda ba ,ban kuma amince ba…kai nake so ka dawo! Kuma bana sha’awar yin surukuwa da wata ƙabila da ba ta Hausa Fulani ba finale.

 

No Ammie shikenan na fahimta yanzu Ni dai duk wacce kuke so ku aura mun ita , akawota London shikenan ,amma Ammie ko mutuwa nayi ina roƙon ku kar a dawo da gawata Nigeria”. Kasa basa amsa Ammien tasa tayi kawai saboda takaici sai datse kirar tayi tana cilla wayar gyefe tare da dafe kai. Yau ta gama nadama akan abubuwa da yawa da itace sila yanzu ya tayi…nisawa tayi tana miƙewa tare da fara takawa tana kai kawo a tsakiyar ƙayataccen falon nata ,kamin kaman zauwatacciya ta fara magana da cewa ” Abdul Ahaad nasan ka jarumi ne ƙwarai , Ni nasaka maka komai dake maka shakku , lokacin da kayi soja da kanka ka kai kan ka saboda jarumta. A lokacin da mutuwa ke maku ƙwanƙwaso tunkarar ta kayi kai tsaye ,wanda Ni na tare ka…nasan komai Abdul , ka saba da shashanci ne na ƙasar waje wannan yasa ka kake ƙin dawowa ƙasar ka ta haihuwa . Har kake tunanin Auren baturiya….kaiii Yah Allah! Tayi furucin tare da ɗaga hannayen ta sama. Kamin tace ” ko nawa ne zamu biya mu fansa diyar ka Abdul ,kai ke nan mana ɗa ɗaya tilo,idan bamu kareka ba meye amfanin arxiƙina ? Dana mahaifin ka da yake ministan kuɗi a Nigeria a yau? . Huuuuu nisawa tayi tana nufar window side ɗin ta tare da sa hannu tana matsar da cotton ɗin windown tare da kallon ilahirin farfajiyar gidan da girman sa da tsaruwan sa ya wuce misali.

 

 

***

 

Wani irin gudu shanayen keyi garke guda…ƙananu da manya , sun tarwatse sun banzama suna shiga cikin gari ,da wannan dare wanda yasa mutane n cikin garin gwargwaje dake nan zaria kowa faɗin na bakin shi ,don ko ba’a faɗi ba kasan wanda suka koro wa’annan shanayen ɓarayi ne garke garke don sun fi dubu …mahmuda ne me napep yajah ya tsaya yana Furta innalilahi waina ilaihir rajiun…kai Allah ka iya mana! Bai ƙare maganan tasa ba , yaji wata murya na faɗin Sadaka yallah bawan Allah! Cikin ɗan sauri ya juyo yana kunna hasken kekensa ,wanda yasa shi ƙare mata kallo ,irin buzayen fulanin nan ne na daji , wanda suka baro ƙasar su suka zo cirani don ɗan matsololi n su .

 

Mahmuda ne ya fiddo da ido yana cewa ” Au Wai Dama ku mutanen SADAKA YALLAH har yanzu kuna nan? Eie . Ta basa amsa cikin gurɓatacciyar hausan ta , wanda kai tsaye mahmuda yace ” To jeki gaba nima almajiri ne,baki ga ƙarfe goman dare ina aiki ba?”. Amaimakon tayi gaba sai gani yayi ta ƙwashe yalolon mayafin dake jikin ta tana banƙaro masa nonuwa gaba tare da cewa” Sadaka ko Karuwa! Ƙurrr Mahmuda yayi ma na shanun ta ,don wani abu yaji yana masa yawo sam ya manta da mutanen da ya ɗauko…sai dai Muryar wata mata a kujerar bayan napep ɗin nasa yaji tana doka Salati da salallami tare da faɗin ” Aiko kuwa dai kunyi asara… Malam zaka kaini inda zani ko na sauka na hau wani???.

 

 

Cike da borin kunya mahmuda yajah napep ɗin cikin sauri, wanda itako wannan sadaka yallah idon ta a tsatstsaye babu alamun kunya ko nadama…gaba naga tayi tana nufar wani rumfar mai sayar da lemu inda mazan mutane irin drivovi da sauran su sukayi cin cirodo…..

 

 

***

 

 

Shatu Fulfulbe!! Sunan dana ji ana kira kenan cikin wani arrogancy voice wanda yasa Shatu sakin Ƙwaryar nonon tana matsawa da jikin ta sosai jikin bukkan , tare da ƙanƙame jikin ta….Gaba ɗaya fulanin kidandan ne tsugunne masu fitsari nayi masu mutuwar zaune nayi. Yayin da ɓarayin shanun suka ƙwantar da mazan Fulani shida suka kashe nan take da bindiga. Wannan yasa Shatu tsorota duk jin ta da take kaman namiji ba tsoro yau ta firgita. Gashi babu sunan wanda suka riƙe ya kama bakin su sai na Shatu FULFULBE. Ɗaya daga cikin su ne ya kalli Baban Shatu wanda take kaka ga Shatu yana cewa ” Baaba dama mana furar da nono. Wanda sai a yanxu na duba ga Baaba dake ta murxa hannun ta da luddayi ƙasa , tana aikin damu a tunanin ta a ƙwaryan dake gaban ta ne ,bata san tsoro yasa ludayin aƙasa take turbitsa shiiiii….ƙara magana yayi mutumin yana dariyar mugunta tare da faɗin Baaba dama mana furar da nono. Jiki na rawa tana kaɗa kai cikin gwarancin ake hausan ta wanda bai fita take faɗin ” Mi addama maka nakeyi ɗan nan . Dariya suka sheƙe dashi da sai da kaf ilahirin dajin rugar ya amsa kana su kuma cewa ” Baaba ki dama mana furar da nono mu sha! Itako ƙara faɗin ” Mi addama maka nakeyi!

 

 

 

 

 

#Symphaty

#Romantic

#Love

#Comedian

#story

 

 

 

_Hahaha ko nima Fah na dara , Baba taga mutuwa dole tace mi addama maka nakeyi .

 

_Ban ga lefin Abdul Ahaad ba ko kun gani? Nigeria wanda yabarta waxai so dawowa dole yace ko gawarsa kar a dawo dashi Nigeria

 

 

 

_Littafin na kuɗi ne kamar yanda kuka sani Regular payment₦300 VIP membership ₦₦500 spc 1k…Zaki iya turo da kuɗin ki ta wannan asusun bank account 6037312299 ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi nawa 08081202932 ƴan Niger zaku biya 600f katin airtel._

 

*Masoya na nasan kunfi billions kumun share iya iyawanku*

 

*Mmn teddy*

ANTY AISHA MMN TEDDY:

*SADAKA YALLA!

_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)

 

 

*Idan kashiga Damuwa da kunchi ka tuna Allah…*

 

 

Free page

002

 

 

 

*AUNTY AISHA MMN TEDDY*

 

 

_Littafin na kuɗi ne kamar yanda kuka sani Regular payment₦300 VIP membership ₦600 Spc 1k…Zaki iya turo da kuɗin ki ta wannan asusun bank account 6037312299 Mohammed A’isha Keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi nawa 08081202932 ƴan Niger zaku biya 600f katin airtel…_

 

***

 

Mi addamawa kike Baaba?? Ɗaya daga cikin su yayi maganan yana kallon Baaban Shatu dake ta murza liddayi a ƙasa tana damun fura ,kan ta a sama tana kallon kidnappers ɗin tsoro yagama dirar mata ita duk a tunanin ta Aƙwaryar nono take damun, bata san a ƙasa ta sanya liddayin ba…ohk yayi Baaban fulfulbe dama mana furar musha ya ƙare maganan tare da miƙa hannun sa yana matsar mata da ƙwaryar nonon ,wanda sai a sannan ta farga da ludayin ba a cikin ƙwaryar yake ba! Yi haƙuri ɗan nan tayi maganan firgit ,ganin ludayin hannun ta a ƙasa. Dariya suka sheƙe dashi suna miƙa bindigansu sama babu imani suka saito inda Ɗan Fulani ke tsaye da mashin ƙarfe ƙarfe a hannun sa …duk wannan masifan da akeyi kuma suke ciki shi bai saki mashin ɗin nashi ba. Abun ka ga fillo da shegen Son Abun Duniya. Kai bafullo kawo mana duk abun da ka mallaka mu bar ka da ranka!

 

 

Muryar ɗaya daga cikin su mai amsa kuwa ya daki dodon kunnuwan su ,wanda yasa Ɗan Fulani kallon Shatu dake tsuma tana masa alamun ya miƙa mashin ɗin ,amma sai ɗan Fulani ya zube yana cewa ” Aradu Bani da koshishi…ban aje ba,ban da komi sai wannan ƙarfen. Kuma daga binni Baba ta ta aiko muni dashi. Buɗe baki ƴan kidnp ɗin sukayi ,kamin wani mai kai sol sol yace ” Shakumdu sauke bindigar ka maza! Ashe ma har ƴan uwa suke dashi masu kuɗi ? To yanxu ku ɗauko mana shi , kamin nan a tattara kowa na wannan ruga ki tasa ƙyeyar su muyi cikin daji.

 

Inalallahi wai’ina ilaihir rajiun shine abun da Ɗan fulanin ya faɗi cikin dasasheshiyar hausan sa …kamin ya juya ga ƴan uwan sa Fulani yana sauya harshe zuwa fulatance ,su dai ƴan kidnping sun ga fulanin ne duk sun miƙe tsaye , kawai sai kika ga kowa ya fashe ciki harda Ɗan Fulani wanda ya ɗauki mashin ɗin cak ko nauyin ta baiji don shi bata shanayen sa yake ba…cilawa yake da wannan mashin a dajin rugar kowa yasan shi ga faharin yana da ƴan uwa a binni. Takaici ne yasa ƴan kidnping ɗin buɗe masu huta kashe bayin Allah kawai suke ,masu darewa nayi a wannan dajin Allah duk sun watse sun bar rugar su ,da ko man su. Ɗan Fulani kuwa dirawa yayi ta wani katanga tare da hayewa mashin ɗin wannan shine dalilin da Allah ya ƙaddara ƙwanan sa a gaba .

 

 

Gudu suke yi a haka suka fito titin farara , a wannan tsakiyar dare . Wanda suka mace a hanya sun mace ,wanda aka kashe an kashe ,haka wanda ɓarayin suka kama sun kama. A gyefen titi Shatu ta zauna tare da lafewa jikin Baaban fulfulbe ,kowa ka ganshi a cikin tashin hankali ,amma abun haushi mutane kowa yana zuwa wucewa yana yin ido biyu da fulanin nan me yakon su tsaya a masu agaji ,sai kaga abun hawa ya wuce da wani irin matsiyacin gudu fiiiiiiiiiii ,kowa na tsoron rayuwar sa ,don sun san kidnpers ne kaɗai zasu koro su a wannan tsakiyar dare n.

 

 

Allah sarki bayin Allah Fulani namu , duk wani juyayin iska , bugun abu ko wani irin sauro dama wannan sun saba da cizon shi haka ma yau sukayi kwanan ido biyu a titi , suna jirar wayewar gari su koma rugar su ,a cewan su basu da inda zasu je da ya wuce nan.

 

***

 

Ƙwance yake ƙarfe 10:03am ya miƙe ƙafafun sa a kujerar mai kama da restchair , idanun sa na akan wayar hannun sa da yake IG hankalin sa ƙwance don ya manta da faɗan da Ammie ta kirashi a jiya tayi masa na ya dawo Nigeria. Post ɗin hoton sa yayi a page nashi , cikin shigar sport Wanda ko ba’a faɗa maka ba kasan hutu da ƙwanciyar hankali sun zauna a wurin nan… AHAAD JAGABAN! da haka kowa kebin sa da comments wanda fellowers ɗin shi shi kan sa bai san iyakan su ba…daga celebrati ya koma soja don haka dole ya samu masoya ga ƙyau ga miskilanci ga aji shi yasa kowa ke kirar sa da JAGABAN! Sam ya manta da Shirley dake zaune tana masa surutan ta , da bai sauraren ta sam. A hankali ta matso jikin shi tare da kai hannun ta tana ɗago da fuskar sa dake a kan screen …lulun idanun sa ya zuba mata masu firgita marar kunya kamin tace ” Pls Abdul Ahaad ! Kauda kansa yayi daga kallon ta yana ƙoƙarin cigaba da latsa wayar sa. Nan yaji takai bakin ta tana ɗaurawa bisa laɓɓan sa tare da fara sgueezing nashi tana tsotsan laɓɓan nashi in a romantically . Kusan minti uku suka ɗauka a haka ba tare da ya dakatar da ita ba… Wanda babu abun da kake ji na tashi a wurin sai ƙarar AC dana tsotse tsotse ka ɗauka alawa ta samu mai ɗan karar daɗi. Ganin bata da alaman zame bakin ta daga nasa yasa shi sa hannu yana kauda kan sa tare da zare bakin sa .

 

 

Wani irin gauron numfashi ta sauke , kana takai hannun ta tana riƙe nashi kaman zata sa masa kuka , don ta lura baya jin biye ma iskancin ta na yau! IG ta ɗauke masa hankali . Shafa gyefen fuskar sa tayi tana shafa sajen fuskar sa a hankali tare da faɗin ” Pls My lab.. No shirley Shine kalmar da yayi mata ,tare da haɗe girar sama da ƙasa yana kallon ta tare da ɗan lasar laɓɓan sa na ƙasa kana ya buɗe bakin sa nan take hushiryar sa suka bayyana na sama kamin yace ” I have alot to do now ok?.

 

Shiru ta masa , wanda ganin ya cigaba da aikin sa yasata kai hannun ta tana kama nasa hannun tare da cewa ” lemme do massage for you! Ɗan ɗaga mata kafaɗa yayi na she can do”. Wanda ganin haka yasa shirley fara matsa masa fingers ɗin sa a hankali tana masa tausar hannun don tasan daga nan ne tafiyar zata miƙaaa.

 

Yanda take bin jikin sa da wani irin salo wai adole wannan shine tausar? Niko nace ta ƴan iska dai. Jawota yayi jikin sa kai tsaye yana haɗata da ƙirjin sa….kallon ido cikin ido suke wa juna kamin ya sakar mata ɗan murmushi yana ƙoƙarin haɗa bakin shi da nata wayar sa ta fara ruriii yanayin ringing tone ɗin da yakeyi na Ammie hayaty yasa shi saurin dakatawa da duk wani abu da yake yi …yana ɗaukar wayar tare da saurin karata a kunnen sa…Ammie brk da sfy. Bata amsa sa ba ,sai cewa tayi ‘ Abdul inaso yanxu ka hau tashar labaran arewaci kaga mai ke faruwa a ƙasar ka ta Afrika. Kamin yayi magana ta katse kirar . Wanda lokaci ɗaya shirley taga sauyi daga garesa. Hannun sa yakai yana rabata da jikin shi tare da miƙewa zaune yana gyara zaman sa.

 

 

***

 

 

Mutane basu fara taruwa ba sai wuraren tara ,wanda kamin jami’ai su taho tuni ƴan jarida sun hallara don watsa labarai. Magana duka ake mawa fulanin akan meke faruwa? Amma sai dai kashh basu da ƙwaƙwƙwarar Hausa a tongue ɗin su , wanda wasun su masu rauni kuka kawai suke…suna miƙewa tare da Nufar dajin da suka fito. Wani ɗan jarida ne yabi bayan su cikin sauri yana haɗa su da Allah su tsaya suyi masa magana ,tare da Tambayar idan sun koma cikin dajin basa tunanin halaka?. Wannan ne yasa Shatu fulfulbe juyowa a zafafe tana kallon ɗan jaridan kamin ta fara magana da gurɓatacciyar hausan ta tana cewa ” Idan ba koma rugar mu ba ,ina zamuje…shin ku da muka fito kun bamu ma sauki? Ina manyar ƙasan suke? Meye amfanin su na shuwagabani a gare mu ,bayan sun kasa mana komai. Sun kasa mana taimako da mahalli bare abun da zamu ci muyi rayuwa! Gomma mu koma mu mutu a dagi yafi mu mutu a titi mutuwar wulaƙanci. Kawai sai ta fashe da kuka tana cigaba da cewa ” Sun kashe wasun mu! Sun mawa wasun mu illah da rauni! Sun kwashe dukiyar mu! Meyayi saura shikenan rayuwar mu! Zamu kai masu shima su amsa idan su Allah ne! Tana faɗin haka ta juya tana nufar inda sauran ƴan uwan ta sukayi …wannan lbrn shike yawo gari gari ƙasa ƙasa ana yamaɗiɗi ga halin da Nigeria ke ciki. Duk abun da ya faru a idon Abdul Ahaad da shirley wanda ita dai bata jin komai sai Ahaad da ya miƙe tsaye.

 

 

A hankali ya fara takawa tare da kaiwa da komowa a tsakiyar falon “Abdul Whats wrong?”. Kamin ta ƙarika maganan ne taga ya nufi inner room ɗin shi ,wanda cikin sauri tayo bayan sa…..A tsaye ta gansa yana haɗa kayan sa …wanda cike da fargaba da tsoro take tambayar ina zashi? Wanda kai tsaye ya bata amsa da Gida Nigeria! Fiddo ido waje tayi tana kallon shi kamin tasa rigimar bai isa ya tafi shi kaɗai ba tare zasu tafi ayi masu aure a can. Bazai tafi ya barta ba”. Nidai ganin haka farin ciki yasani saurin fichewa daga wurin ina nufo gida Nigeria kai tsaye don nayi mawa Ammie busharar dawowan sa , don addu’ar ta yau Allah ya amsa.

 

 

***

 

 

Major general naji samarin falon na faɗi suna dariya….wanda Abdul Ahaad dake zaune yana ganin komai sabo a gareshi yau kwanan sa biyu kenan da dawowa . Labari ya gama waɗe dangi ƴan uwa ,kullum gida mutane ,wannan kuma shike damun sa ,don ya rabu da jin hayaniya irin haka. Wannan yasa shi kullum ka ganshi hankalin sa na akan wayar sa ,don shugaban sojojin arewaci ya umarta yana Son ganin su nan da ƙwana uku . Duka falon abokanan sa ne duk sojoji kuma manya kowa da yaran sa ,kuma babba ne …dariya Samir ya bushe dashi irin na manyan sojojin nan marasa imani yana ɗaukar lattr tare da kunna sigari yana kaiwa bakin sa , sai da ya zuga sannan yace” Yanzu Jagaban no more going back kenan? . Dariya Abdul yayi wanda tun da ya dawo sai yanxu yayi dariyar,tuno masa da takensu na soja da Samir yayi….kai kashe karar sigarin nan Kar Ammie ta shigo da baƙin ta. Rabu da ɗan iska ƙila ance masa a daji muje . Yahya yayi maganan yana dunkula hannu tare da dokan Samir . Suna a haka kuwa sai ga Ammie da gayyar ƙawayen ta sun zo ganin Abdul Ahaad da har ya gaji da gaisuwa. Kowa sai dai ya tafi da cewa ” Wannan wulaƙantaccen dama da soja ya dace ba da wani abun ba.

 

***

 

Ƙarfe tara da rabi na dare Ammien Ahaad ta shigo Bedroom ɗin sa ,don sanar masa da kirar iyayen sa yayyun sa ƙanin sa da suke falon Grandma ana jirar isowar shi suyi meeting… Fitowan da kenan daga bathroom da rigar wanka .yana comb ɗin suman kanshi . Ammie brk da dare! Brkn Son ya ƙwanan gida Nigeria? Tayi maganan tana murmushi tare da nufar waldrop ɗin sa …don fiddo masa da kaya. Mirror ya nufa yana fara shafa jikin sa da mayuka masu ƙamshi da turaren sa da ya zama masa ɗabi’a ,don shi mutum ne ma’abocin Son ƙamshi…

 

 

Ammie ne ta Kai hannu tana fiddo da wani yadi da ta ganta fara ƙal. Cike da rashin fahimtar meye ? Ta fiddo shi waje tana kallon side ɗin da yake kamin tace ” Abdul wannan yadin Fah ? Na meye?. Ɗan kallon inda Ammie take yayi kamin cike da nuna ko a jikin sa yace ” Ammie likkafani ne na siya ,koda na mutu kun huta sai kumin sittira dashi………………

 

 

 

 

Abdul Ahaad likkafani babban magana tofa!

 

 

_Littafin na kuɗi ne kamar yanda kuka sani Regular payment₦300 VIP membership ₦600 Spc 1k…Zaki iya turo da kuɗin ki ta wannan asusun bank account 6037312299 Mohammed A’isha Keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi nawa 08081202932 ƴan Niger zaku biya 600f katin airtel…_

 

 

 

*Masoya irin billions kumin share zuwa grps naku

 

Add Comment

Click here to post a comment