Bakar Rana Hausa Novel Complete
Bakar Rana Hausa Novel Complete
DON ALLAH KAR KA DAUKA SHIRME NE KA WUCE BAƘA ƘANRANTA BA
Story and written
BY FIRDAUSI SALISU BALA ( FEEDOR MANAGER)
MASOYIYYAR ROYAL STAR CE
A short story
Editing by Sahibar Royal Star
Sunana Amina Aminu, ina zaune ne a garin Gusau Zamfara State, U/Zabarma, Ku Kasance da rayuwata, domin inganta taku rayuwar, da ta iyalanku.
Daure a matsayin ki/ka na Uwa ko Uba ki/ka karanta tare da watsama duniya in har ya riske ka, domin in ganta rayuwar wasun ka/ki, amasayin ka/ki na wanda take amfani da yanar gizo kai/ke ma kasamu ladan hakan tare da aiki da shi.
Burin Rai Hausa Novel Complete
Wanna ba Litafin kudi bane, Amma a matsayinki na Mahaifiya, ko na ce mace ko Uwar d’iya mace, ko mai shirin zama Uwa, zaki iya tallafama wa’in da wannan ab’un ya riska, ta hanyar bada taki g’udunmuwa. Haka kai ma amasayin ka na mahaifi ko Yaya ko kane komai shirin zama Uba nan kusa.
Zaka iya bada gudunmuwarka ta hanyar katin waya, ta wannan number
09033356045
A account number Kuma
3090221082
Salisu Firdausi Bala
Eco Bank.
Kadara tausayi bacewar rana cikin kya-kyawar rayuwar wata matashiyar budurwa yarinya mai suna Amina Aminu.
ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Bismillahirrahmanirraheem.
Part 1
Pages
One to End
_______Cikin kukana nak’e k’wala wa Mamata da Babana kira, amma ina babu yanda suka iya wurin ceton rayuwata, Babu wanda ban kira ba a cikin gidan mu, amma ko sauro bai zo cetona ba, haka ya cigaba da ya gamin rigar mutuncina Tare da sauka akaina.
Kalon yaransa yayi tare da m’asu allamun su baza, Ahankali nake bud’e idanuwana akan Likitan da yake k’okarin sake dau ramin ruwa na a Jesu, tare da kwada kaina gefe gadon inda naƙe kuka a cikin zuciyata tamƙar raina sai fita inda kuwa ji nake kamar ana min suyar naman kaza a cikinta, kasa jurewa nayi kawai sai na fizge alurar da bai Dade da sakamin ita ba, tare da nufar kofar f’ita dakin da gudu duk da ba wani g’udun nake iyawa ba sanadiyar mugun ciwon da na ke ji a kasana. Wata matashiyar mata ce tai saurin rikeni tare da ƙara riƙeni da kya don kar na kuf’ce mata har inda Mamata ta karaso ta damka mata ni, cikin kukana nak’e fadin “don Allah ku barni! ku barni naje”, “kije ki kashe kanki a titi ki ke son mu barki?” Cewar Baba, hannuna ya ja tare da nufin mayar dani dakin da aka kwantar dani tsawon kwana biyar kinan inda ban san ma inda k’aina yake ba sai yau, kasancewar faiɗan da aka min.
Kalonsa nayi tare da ce wa “don Allah Baba ku taimakamin ku mayar dani gida wallahi ba zan iya jure zamana a Hospital din nan ba” Babu yanda za su yi dole ne suka mayar dani gida.
Daga isarmu direct d’akin Yayana na wuce tare da kulewa, inda Mamata zata fara min magana ne Baba ya yi saurin katse ta tare da ce mata ta barni na gama saukowa tukuna don yanzu duk abunda za su gayamin ba zan sauko ba”. Bayan shiga ta ne na nufi toilet din masak’aicin dakin tare da yin wanka na dauro al’walata, shinfida sallaya nayi tare da fuskantar alkibla na fara jero salolin da ake biyata na rankasu na ranar, tare da daukar al-qur’ani mai girma da daukaka na fara karantawa cikin luggar haf’su tare da zaƙakiyar muryata mai dadin sauraro cikin kuka tare da roqon mahalicina da ya bi min hakkina akan wannan azzalumin bawan nasa wanda yai sanadiyar bacewar rayuwata da rushemin duk wani buri da nagarta ko nace mafalki a duniyata, hakan na kasance na tsawon sati daya inda Mamata kuwa kullum Safe da Rana da Dare takan aikomin abincina kuma nakan dauka naci wani sa’i`lim ko nace wani lokacin don yunwa ba bakuwar kowa bace
Babana ne ya taramin kannena da yayena tare da min nasiha a kan na yarda da kaddarar Ubangijina tabbas nasihar su gareni ta yi babban tasiri inda yasa na bude dakin da nai tsawon ƙwana biyar a cikinsa tare da rungumar yan uwana da mahaifana daya bayan daya tare da daukar m’asu al’kawarin cewa zan koma kamar yanda nake a can baya.
Yau kam ta kama’min Monday morning inda kuma ina da test a safiyar nan ta Human leaning, na Mallan Abdul-Hakkim Dan Higagge ta bakin student cikin atamfata nake marun da milk din Hijab d’ina inda Mamata tai tsaye tana kalona tare da share dan guntun hawayenta da yake gan-ganro mata duk don kar na gani, zuciyata ‘ta’ k’araya, foda na dan murza ma fuskata tare da dan shafa ma labbana mai dan kwalli da idona, Salma ce ta dubeni inda ita ma tana shirinta na zuwa school dinsu cikin black din wando da sikai bulu din Hijab da riga mai dogon hannu, duk da ta kasance a secondary section take a SS two, sai Fad’imatu da Anty Hidayatullah ke faman shirya mata cikin black seket da orange tishet da yake basa sa komai akansu ‘yan Nursery ne. Wada take a Nursery Three inda tana karatu ne a makarantar da Anty Hidayatullah ke koyarwa, sai dai ita tana koyarda ‘yan Primary section ne a Peeland International College Gusau, Nursery Primary and Secondary School.
Kallona suke cikin tsan-tsar farin ciki jikkata na dauka mai dauke da takkadun makaranta ta tare da binsu dai b’ayan daya na mana m’asu peck a goshin su tare da ce wa bye-bye suma suka cemin. Duban Mamata nayi tare da ce mata “ni na tafi”, “adawo lafiya” tace min tare da zura romin addu’o’ daga baƙin ta mai albarka.
Dakin Hajiya na nufa wadda ta kasance Mata ta farko ga Babanmu da Fa’iza na fara karo wadda take matsayin sa’ata kuma komai namu guda da ita kuma tare muke karatu sai dai Department din kowa daban, ita tana karatu ne a Biology Computer inda ni kuma nake karatuna ne a Home Economics ne kuma muna shekarar k’arshe ne a Federal College Of Education (Technical) Gusau Zamfara state. Cikin murnarta take kiran Hajiya fito kuga ab’un mamaki, “na mai fa?” Cewar Hajiya “na y’ar ki cikin shirinta na zuwa College” da ko saurinta suka fito, gaishe ta nayi cikin ladabi da biyyaya kamar yarda ka’idar gidan namu take ko nace tarbiyar iyayen mu da suka koya muna ko nace suka bamu, taso da niya tayi tare da rungume ni tana ce wa “Alhamdulillahi ala kulli halin, tsalki ya tabbata ga Ubangijin talik’an bayinsa Mumunai kuma tsalki ya tabbata agaresa hakan na dan gaisa sama-sama da y’an uwan nawa tare da nufar shiyar Babanmu a rufe na sameta don hakan sai na kwan-kwatsa masa tare da kwala masa kira kamar mai binsa bashi ina ce wa “Babanmu ka bude kaban kud’in zuwa Makaranta kar na makara, ai ko cikin hanzarinsa ya taso tare da zare kubar d’akin nasa da hanzarinta kara zowa yayi gabana tare da rumgumeni yana faman manna min peck akan fuskata tare da fadin “Alhamdulillahi” lallai Allah abun godiya ne kallonsa nayi tare da fadin “kar na makara fa Babanmu” k’udin ya miko min tare da cewa “Allah ya dawamar maki da farin ciki a zuciyarki Aminatu, “Amin” nace masa tare da nufar kofar waje duk da ina jin Fa’iza na faman kirana da don Allah na tsaya mata, tsayawa nayi tare da yin addu’a f’ita daga gida, daga jefa kafar tawa kuwa waje na fara had’uwa da mutanena don dai ba dai fara’a ba kuma son mutane ma ba a ko magana, haka na gaidasu inda akwai wani mai shago yana kusa da gidanmu muna kiransa da Ella Zaru kamar taubasai hakan muke dashi, “kai jama’a gawa fa ta mike fa” Ai ko kamar jiransa nake ya fara nima na fara mayar masa da lafazina har Fa’iza ta fito muka kama hanyar da zata sadamu da Box din makarantarmu don muna k’u’sa da wurin Bus-stop dinmu, kasa muke zuwa mu dawo kasa daga wurin, Ya Qasim ne daya ke shirin fitowa da mashin dinsa ne daga gidansu ya kalle ni tare da fadin “la! la!! la!!! wa nake shirin gani? kamar k’anwaty na ko?” “Eh Yayana ni ce”, na amsa masa “Masha Allah, to ya jikin naki? ” Cikin yar jin kunyata nace masa “da sauki” “to Allah kawo sauki tare da bi miki hakkin ki wurin wan can wawan azalumin nasa” “Ameen” nace masa kallon Fa’iza yayi tare da cewa “ja’irar yarinya tunda ba za ki iya gaidani ba to ni bari na gaidaki”, “ai to ko ka gaidani bazan gaida kai ba gwara ma ka rufa ma kanka asiri ka hankura da daukar da ka’ke wa kanka da kake a matsayin Yayana”, ke nidai kudai na wanna shirman naku don zai iya sawa mu tarar da Box din ta tashi, tare da wacewarmu, sai dai ban taba risken wani abun ƙaima ga rawuya ta na tsongwama ga Yan Uwa da abokan arziki ba sai sanda na tsince kaina a cikin k’addarata ta biyu.
Bayan wata U’ku ne da kwana shida, awata ranar Litanin ina tare da kawayena a School muna cin Dankalin da muka tsaya tare da zob’o, duk dama tsawon kwanana hudu ina fama da zazzabi mai matuka’r zafi ga kuma wani kwadayi da yake da wainiya dani. Ai kuwa ban karasa cin dankalin nan ba na fara kwararo da amai kafin dai na bar School sai da nayi har so biyar, ganin yaki tsayamin ne ya sa course mate dina daukar wayata tare da kiran Fa’iza, a wayata suka sanar da ita abunda yake faruwa, babu dadewa ta iso tare da d’auka ta muka nufi gida, inda ko kamar an turo ko Ammanan gaba hakan na cigaba da kwarasa kamar raina zai fice, ta shi Hajiyarmu tayi ta taimakamin domin mikewa daga duken da nike a wurin bakin makwararan gidan mu, b’ayan mikewata ne na sulale kasa tsummamiya, ban far’fado ba sai b’ayan awa daya idanuwana na fara warewa akan diyan gidanmu da i’danunsu ya bi ya rine kamar garwashi, inda na sai da kalona ga Babanmu. kallon su nayi tare da fadin “Babana mai ke faruwa? me ke damuna?” “babu komai” yace min in da Doctor ya shigo dakin ya fara dubani ya ce “asamu abata abinci tasamu taci koba daɗi” sannan ya fice abun shi, Mama ta dubeni tare da cewa “mai zaki ci?” Ban ma san sanda nake fadin “ina son cin ɗatun bula mai daddawar basto da kuma Danbu Mai zogale tare da mangoro danye” hakan nake ta jero su, Yaya Hashim ne ya dubeni tare da cewa “duka zaki iya can ye su?” “Eh wallahi Bro fiye ma da hakan” yau ne aka sallamemu muka dawo gida, kuma har yanzu ban san abunda ke damuna ba har yanzu fita nayi domin sayan gala don na gaji da zaman gidan kuma wani ƙwadan ta nake faman yi, sai dai hakan duk lungun da na shiga ko wurin da nabi zan ga ana faman nune na da d’an ya’sa wasu kuma suna nuna ni da bakinsu, da Babbar kawata Firdausi na haɗu amma ab’un mamakin kuwa shi ne mun saba da mun haɗu za mu yi hoggin din juna sai kawai ta kauda k’anta kamar bata ganni ba, “ke mallama miye hakan kamar baki ganni ba? Zaki wa’ni kauda kanki gareni” “Don Allah ki rufamin asiri ki rabu dani, kuma daga yau babu ke babu ni don gaskiya bazan iya abota da uwar shege ba kuma ma mazina ciya, nima ta batamin suna” tana gama fadin haka ta wucewarta nima wuce wata nayi don ban fahimce inda maganarta ta ta dosa ba b’ayan isata ne wurin mai suyar awara da hanzarinta ta mike tare da ce wa “da Allah mallama mai ki ke min anan wajen?” Cikin murmushina na ce “awara nazo saya don ni bani da rikici kuma ma ban cika daukar abu da zafi ba, ”to bazan sayar ba kuma ki wuce ki bani wuri tun kafin na miki rashin kunya”, wani ne da yazo saya shi ma ya fisge k’udinsa ta tare da ce wa “ni kam Allah ya tsareni na saya abunda Uwar shege zata saya” tureni kawai naji tayi tare da fadin wallahi “k’ibar min nan ko na halaka ki bakar munafuka kawai daman kun san abunda kuka shirya shi yasa kuka gayyato barayi a cikin gidan ku don su zo su miki fyade b’ayan wasu watanni ace kina da ciki don a raina muna da wayo ko? to ai duk mun gane don hakan k’i bar min waje”, yaran unguwarmu ne suka biyoni suna fadin “tayi cikin shege kuma ba za’a haifa muna mugun iri a shiyarmu ba” tare da jifata wasu na jamin Hijab d’ina cikin g’uduna nake har na kai gida inda na fara tuntube da Babanmu, kalonsa nayi tare da zubewa kasa nace “Don girman Allah Baba ka fadamin da gaske ne ina dauke da cikin shege a cikin jikina?” “Eh bazan iya cigaba da boye miki ba domin kuwa kin riga da kin sani” nasiha ya karamin tare da fadin babu yanda bawa ya iya da ƙadarar ubangijin sa kowace irice indai har tana cikin babin kadararsa dolene ya dau k’addarar Ubangijina a gare sa.
Ɓangaren mahaifiyata kuwa.
Zaune take cikin tagumi tare da kalon Babanmu tace “Alhaji yanzu haka zamu cigaba da ganin wannan bakin ciki a cikin gidan nan?, duba fa ka gani hatta ‘yan uwanta ya shafesu ka gama m’asu neman yannan ta duk sun zo sun amshe sadakinsu, kana ganin Hajiya ab’un baya mata ciyo ne? duba fa ka gani yanda Na’ima ta dade Bata samu Miji ba anata addu’a kuma Allah ya amsa tare da kawowa amma sanadiyar wannan yazo ya karbe komai nasa tare da jifarmu da munanan kalamai ba zai had’a Zuri’a da ta shegu ba ko kofar gida gagarar diyan gidan nan yake ballemu ga ka kuma kai da ko sallah ka daina yinta a masallacin unguwar nan in dai har kana nan sai dai kayi a gida”. “To ya za mu yi tunda kaddarar muce tazo ahakan”, kuma nace ka bari mu tura ta a kauye ka hana wurin gwa-gwanta Maryam wato Mairo amma ka kiya to don Allah ina rokonka da ka bari na zubar da cikin nan… Ai ko bata ida zancen taba Baba ya wanke ta da mari tare da fad’in “lallai Suwaibatul Aslamiya yau kin ban kunya matuka, tare da ban mamaki tare da ce wa dama kina cikin Uwaye mata m’asu jefa rayuwar diyansu cikin halakar duniya da ta lahira , shin kin san yanda yake da illa kuwa a duniya? to bari ma kiji ba lallai bane in kin je zubar da cikin tayi rai ba domin azabtar zuba da ciki tafi ta nakuda ni a ganina, in kuma kika yi sanadiyar zubar da cikin ya fara zama mutum to ki san cewa kamar kinyi k’isan kai ne kum allah baya yafe lefun bawansa dana wani bawan nasa sai dai in tsakanin vawa da allah ne to wanna ba zamu iya yankee rahamar Ubangiji ga bayinsa ba domin shi mai yafiya ne akan bayinsa. sanna kuma kin aikata zulubi ,don haka a matsayin ki na Uwa ban ga dalilin da zai sa ki dukufa wurin gani kin kara tozarta rayuwar yarki ta lahira ba, domin saki iyah jamata wani laifin a wurin ma halicin ta. don hakan ina mai haninki da ki hanu akan wannan mummuna tunanin naki marar amfani, domin kuwa banga fa’idar subar da cikiba koda kuwa ya kasan ce da gan-gan aka same sa bale na ‘Yar ki da ya kasan ce kadarane.
“Tabbas nayi nadaman hakan Alhaji kuma duk rashin sani ne ahakan ma nayi alkawarin taimaka wa mata ta hanyar wayance m’asu kai da su guje taimaka ma y’ay’ansu ta wannan hanyar idan har k’addara ta riske su ko makamanciyar wannan ko kuma a’kasinta, na godewa Allah da ka kasance miji agareni kuma Uban diyana”.
Ɓangaren gidanmu kuma duk da mun k’asance m’asu matuka’r son junanmu da zaman lafiya mu goma sha uku ne acikin gidan mu Hajiya Rabi’atu ita ce mata ta farko ga mahaifinmu kuma tanada yara gudabaƙwai u’ku Maza hudu Mata daga ciki akwai Yaya Qasim sai Bro Buhari sannan sister Na’ima sai Bro Hashim sai Fa’iza sanna Haruna tare da autar’su Asiya, inda kuma duk sanadiyar wannan ya’sa aka fasa auren Yaya Na’ima da kuma Fa’iza wada duk tafi bani tausay don dai tana matuka’r kaunar Fauzan wanda suke buga soyayya a tsakanin su
Sai dakinmu wanda muke mu shida ne kuma Mamata ce amarya Bro Yahaya sai Anty Hidayatullah sannan ni Aminatu sai Salma da Kamal sanna autarmu Fad’imatu Zahra inda muma an fasa auren Anty Hidayatullah.
Wannan ya jawo sanadiyar watsewar zuri’ata ba karamin fada akayi ba tsakani yan da’kinmu da na Hajiyarmu duk ta sanadin wannan.
A ɓangaren Ana’s ko Wanda ya k’asance Masoyi a gareni kuma Wanda akwai al’kawarin aura a tsakanin mu shi ma ya gujeni duk da soyayarmu da ke tsakanin mu amma bai duba ba yabi ta son zuciyarsa tare da gudun maganar mutane ya fasa tare da karbar k’udin sadakinsa da ya biya da naki hakura na masa magana sai cewa yayi shi kam ba zai iya haɗa makwancin diyansa da inda aka kwantar da cikin shegeba yayi rayuwa, nima tawa zuri’a tazo ta lalace su zame min tantirai aduniya”.
Ba’yan haɗa duka wannan ne na yanke shawarar kashe kaina domin samama abunda ke cikin cikina sallama da rayuwata tare da ta ahalina duk ganin cewa ta haka ne k’awai zan cece k’aina da zuri’ata.
inda na kashe kaina tare da abunda ke cikin cikina
Ku kasance da
Royal Star Writing domin Jin sauran darrusan guda hud’u masu zuwa nan bada dadewa ba ga mai son turo muna comment dinsa ko shiga cikin muhawara zai iya tuntub’ar wannan Number kamar hakan
09033356045
Domin bada taka g’udunmuwa amatsayin mu na al’umar daya ma taurin mu daya
Muhawarar tamu zata kasance ne kamar hakan
~Shin suwaye sannadin rasa rayuwar Amina Aminu tare da cikin ta?
~ Miye hukuncin da ya kamata ayiwa maƙwaftan su dan gane da halin da suka nuna game da halin da suka nuna na rashin mutun ci da rashin ƙar bar kadara yare da rungu meta gabaki dayan su a masayin su na maƙwaf ta, tare da duk da sun san gaskiya kuma suka take ta?.
~sannan mai zamu iya cema dangin Mazajen da suka nuna kin daukar k’addarar Ubangiji akan dangin Amina suka fasa auren wa’in nan matan tare da jifar su da munanan kalamu, shin ya dace daga baya idan syka dawo a basu auren yaran kokuma a hana masu auren?
~Sannan amatsayin ka/ki na Uwa ko Uba wace shawara ce za ka/ki iya b’ayarwa domin bada taku gudunmuwar, wada tazaman maki/ka wajibi, in dai idan ka/kina son kasancewa a Cikin Group din nan dole ne kibi doka, bumu haɗa Maza da Mata ba don kawo wani rikici ba ko la!la!! cewar al adarmu ba
~sanna muna son kadau ƙanka amasayin iyayen su Aminatu tare da fadin ra’ayinka
MU HAƊU DAKU A KASHI NA BIYU
D’ANA NE SANADI
Taku har kullum Feedo manager
MASOYIYYAR ROYAL STAR CE
Add Comment