Littafan Hausa Novels

Mafari Hausa Novel Complete

Mafari Hausa Novel Complet

 

 

 

 

 

Mafari Hausa Novel Complete

*LABARI/RUBUTAWA*

*KHADIJA S.SAMINU*

*(ƳAR GATAN MAMA)*

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR…*

 

Rayuwar mu.

A Wani Gida.

Maganin kar ayi..!

Rana dubu…

Wata Duniya.

Mace-Macen Aure.

Lumbu-Lumbu.

Huza’iyya.

 

SHAFI NA FARKO

*11/Mar./23*

 

•••

*GODIYA*

 

*Dukkan Godiya da Yabo sun tabbata ga Ubangijin taliƙai wanda bai haifa ba ba’a haifeshi ba,mamallakin kowa da komai mai bada iko a sanda yaso ga wanda yaso.Allah ina roƙonka ka yarje mini da na Rubuta abinda nai nufi na alkairi ka sanya ya amfanin al’umma Annabi mai girma.*

 

•••

*Allah kayi salati ga Rasulullahi adadin dukkan abinda ka halitta sannan ka nunkashi sau adadin abinda ka halitta.Allah kaita ninkashi har zuwa ranar sakamako.Allah a cikin arziƙin da kakewa bayinka Allah ina roƙon arziƙin Soyayyar Rasulullahi har ƙarshen rayuwa.*

 

Matsalar Gidan Miji Hausa Novel Complete

•••

*Wannan Labari ba na kpwa bane,na yishi saboda ni da al’umma mu amfana,duk wanda yai dai-dai da rayuwarshi akasi ne,sannan ina roƙonsa da idan mai kyan ciki ne yai kala da rayuwarsa to ya ƙara ƙaimi wajan aikatashi,idan kuma saɓanin haka yai ƙoƙari wajan yaƙi da zuciyarsa domin mu gudu tare mu tsira tare.*

 

•••

*Tun kafin na shiga duniyar Marubuta na daɗe ina Gajeren-Rubutu akan 🧕🏻RAYUWAR BUDURWA🧕🏻 Wanda ake gabatar da shirin a wani ƙasaitaccen tsohon group me suna ✨ROYAL LADIES✨ Da yawa daga cikin ƴan group sun sha ban shawara akan na maidashi Littafi mai zaman kanshi Ubangiji bai amince ba sai yau.Ina miƙo gaisuwata gareku tsofaffin Iyayena,yayyena,ƙawayena irinsu👉🏻Amina Khabir(Ummu Khdeejah), Aunty Maryam(Ashmar Luv💞) ,Humairaty,Zainab A.Sharif,Aunty Aisha (AU ALMARKAZY),Queen Zeey,Garzeey,Mmn Khdeejah,Sailuba Isiya,Humairah Fillo,Babyn baby….DS.Dama waɗanda ban ambata ba duka ina muku fatan alkairi.*

 

•••

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.*

 

 

 

••••

 

MAFARIN kowa ce Rayuwa mai inganci ita ce *MACE!* Idan aka ce Mace,ana nufin *MAFARIN TARBIYYA*.Domin Tarbiyya ba ta samuwa se da Mace,ita kuma Mace ba ta zama Mace se idan ta samu *MAFARI* na ƙwarai.

 

*Wace iriyar Mace ce zata iya samar da Mafarin ƙwarai?*

 

Lallai wannan ita ce muhimmiyar tambayar da ya kamata ace ta shiga cikin zuƙatanmu,to! A zahirin gaskiya ba kowace iriyar Mace ce zata iya samar da Mafarin ƙwarai ba illa…*BUDURWA!*.

 

Nasan zuwa yanzu da yawa munji a zuciyarmu ya za’ai *BUDURWA* ta zama ita ce wadda zata zama *MAFARIN TARBIYYA?*.

 

To! Kafin na ɗauki alƙalamina se da nai dogon nazari akan *BUDURWA MAI TARBIYYA* Sannan na ɗauki babban matsayi a ɓangaren Tarbiyya na miƙa mata shi dan naga da ita kaɗai yafi cancanta,idan aka ce *UWA* ita ce Mafarin Tarbiyya anan abin tambayar shi ne ya akai ta zama Uwa? Kuma daga wane mataki ne ta zama Uwar?. Amsar anan ita ce,ta zama Uwa ne saboda lokaci ya kaita,sannan daga matakin Budurtaka ta zama Uwar.

 

 

*WACE IRIYAR BUDURWA CE TA KE ZAMA MAFARIN TARBIYYA?*

 

Budurwar da ta ke zama Mafarin Tarbiyya ita ce Budurwa mai👉🏻Ilimi,mutunci,kauda kai,haƙuri,ladabi,biyayya,juriya,gaskiya,ruƙon amana,uwa uba aiki da ilimin da ta ke samu,sai kuma Tsoron Allah wanda shi ke gaba da komai.ds.

 

 

*ILIMI* Kina Budurwa,ki dage ki maida hankalinki wajan tsayawa ki nemi ilimi,sannan kafin ki fara neman ilimi sai kinsan matakan neman ilimin wanda su ne zasu temaka miki wajan samun ingantaccen ilimin da ke da al’umma zakui alfahari da shi.Da farko idan zaki shiga neman ilimi ya wajaba a kanki da ki fara sanin MUHIMMANCIN ILIMI,DA FIƘHU,DA FALALARSA. Sannan kiyi NIYYAR NEMAN NENAN ILIMIN Haka kuma kafin ki fara neman ilimi se kin ZAƁI shi kanshi ilimin da kikeson samu,da shi kanshi Malamin da zai koyar da ke karatun,da kuma Aboki/Ƙawar da zaku ringa ɗaukar karatu sannan kuma ki tabbata iya tsawon rayuwarki kina neman ilimi har zuwa sanda Ubangiji zai kawo miki mijin da zaki aura…

 

Sannan idan zaki nemi ilimi ya zama kina da Ƙoƙari da Himma,kuma kafin ki fara nema sekin zauna kin tsara iya yanda kike tunanin idan kullum za’ai miki kamar shi za ki riƙe ba tare da kin manta ba,haka kuma se kin ringa bibiya dan idan kina biya shi ki ajje ba abinda zaije lokaci ƙanƙani zaki neme shi kiji ya gudu.Sannan a yayin neman ilimi ki zama me dogaro ga Allah tare da neman yardarsa a farkon karatun da ƙarshenshi,amma duk da waɗannan matakai da kika bi wajan neman ilimi baza sui miki amfani yadda kike buƙata ba har sai kin haɗa da Ladabi da Ƙasƙantar da kai wajan neman karatun.

 

A taƙaice dai Budurwa tana ɗauke da ƙishirwar da babu me kawar mata da ita sai Ilimi,haka kuma farilla ne a kanta ta nemi shi domin kuwa Annabi sallallahu alaihi wasallama yana cewa *’Neman Ilimi wajibi ne akan kowane Musulmi Namiji da Musulma Mace’* Dan haka ya wajaba a kanki ki nemi Ilimi na Arabi da Boko,daɗin daɗawa kuma babu ilimin da yafi ki nemeshi kamar ilimin halin da kike ciki.Ilimi yana da matuƙar muhimmanci dan haka wani shehin malami mai suna *IMAMU BURHANUL’ISLAM* ya zauna ya ringa rerawa Ilimi baitittika saboda matsayinshi har a cikin wani baiti yake cewa…

 

*Ku nemi Ilimi dan shi Ilimi ado ne ga masu shi,haka falala ne da ɗaukaka wadda ta ke sanya godiya.Kuyi sammako wajan neman Ilimi,kuma kada wani canji yasa ku dena neman Ilimi ko ya yake.Ku nemi Ilimin Fiƙhu domin shi ne Ilimin da yafi kowane Ilimi tsada da falala mai girma,haka kuma yana sanya tsoron Allah da adalci ga kowa.*

 

Kinga kuwa Ilimi babban makami ne wanda idan kina da shi zaki iya shiga kowa ne waje kuma komai haɗarinsa,ba tare da kin lura ba zaki ga Iliminan ya tseratar da ke.Ya ke Budurwa! Ina kira a gareki da ki farka daga nannauyan baccin da kike ki watsar da kowa da komai ki tsaya ki nemi Ilimi wanda zaki alfahari da shi ƴaƴanki suyi alfahari da shi nan gaba.Ka da ki ƙarar da zuwa makarantarki wajan fira da ƙawaye ko mu’amala da waɗanda ba karatu ne ya kawo su ba,ki ƙarar da lokacinki akan abinda zai amfanar da ke ya amfanar da ƙawayenki da ƴaƴanki da al’umma ba ki ɗaya.Ina kira gareki da ki ajje yawon bikin ƙawa da bin kango-kango idan kinji kiɗa yana ta shi,ki zama wadda idan kinzo wucewa kinji kiɗan sheɗan kikejin ba daɗi a ranki saboda tuna da yawa cikin mutanen da ke wajan ba zasu tafi ba se da zunubi..

 

 

 

 

*Sai kuma gobe in Allah ya kaimu,nagode*

 

 

 

*Allahumma arzuƙni bi Hubbi Rasulullah

 

 

 

 

 

 

 

*ƳAR GATAN MAMA MAFARI

 

 

 

 

 

 

*LABARI/RUBUTAWA*

*KHADIJA S.SAMINU*

*(ƳAR GATAN MAMA)*

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR…*

 

Rayuwar mu.

A Wani Gida.

Maganin kar ayi..!

Rana dubu…

Wata Duniya.

Mace-Macen Aure.

Lumbu-Lumbu.

Huza’iyya.

 

nd now…

 

MAFARI

 

 

 

 

*SADAUKARWA GA MAHAIFIY

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

 

 

*SHAFI NA BIYU*

*12/Mar./23*

 

 

•••

 

Ki bawa kanki dukkan gudummawar da ki ke buƙata ta hanyar ajje son zuciyarki da ajje mu’amala da mutanen da ra’ayinku baizo ɗaya ba.Malaman Addini dana Boko masu yawa suna kuka da wasu daga cikin *ƳAN MATA* yadda suke nuna halin ko’inkula da yadda karatunsu ke tafiya,a cikin makarantun Boko ne zaka samu Ƴan mata da yawa waɗanda basa zuwa makaranta lokuta da dama wanda hakan ya ke jawo musu cizon yatsa daga baya,ba’a fahimtar rashin zuwan nasu har sai wani dalili yazo wanda makaranta zata buƙaci ganin iyayensu wanda a wannan lokacin idan *IYAYE* sun zo za’aji suna faɗin ai kullum sai sun turo ta makaranta basu da masaniyar dalilin da yasa bata zuwa,idan mamaki ya kama Malami/Malama suna neman ƙarin bayani sai dai kaji Uwa/Uba ya ce/ta ce *”Wallahi yarinyar nan ta fi ƙarfinmu sam batajin maganar kowa dan Allah Malam a temaka mana”*. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! To dan Allah duba,Mahaifi ko Mahaifiya fa ke faɗin haka ga Yarinyar da ake sa ran zuwan wani ɗan lokaci ƙanƙani a aurar da ita ta haihu ta baiwa yara tarbiyya…

 

To dan girman Allah *Ta ya ya wannan BUDURWAR zata iya baiwa Yaro/Yarinya TARBIYYA?*

 

Wannan tambayar duk inda aka je aka dawo dai guda ɗaya ce ba canji a tattare da ita,domin kowa yasan ba zata taɓa iya bada *MAFARIN ƘWARAI* ba,sedai ta bata *TUN RAN GINI,,TUN RAN ZA NE.* Domin ita kanta babu Mafarin a tare da ita.

 

Dan haka nake kira gareki yake *BUDURWA* da ki nutsu ki tsaida hankalinki waje ɗaya,ki kori dukkan wata ɗabi’a mara kyau dake tattare da ke ki tausayawa Iyayenki,ƴan uwanki,ƙawayenki da ƴaƴanki dama al’umma baki ɗaya.

 

A duk sanda kika tsaya kika samu nagartaccen Ilimi ko wane iri to kin wuce kallon banza,hantara da sauransu.Kuma Iyayenki zasui alfahari da ke da duk wanda kike mu’amala da su tun suna raye,domin duk sanda aka ta shi kwatancenki se an ambaci Mahaifiya ko Mahaifinki domin sune farkon waɗanda suke karɓar sakamakon abinda kika aikata kairan ko sharran, *”Abokina wai jiya ina ka ke ta sauri zaka je ne,naga jiya Liman na shafawa ka fice har kana tuntuɓe fatan dai lafiya?”*

 

*”Hhhh! Abokina kenan,ai sam farin ciki ne ya lulluɓe ni har na gaza furtama abinda ke zuciyata,kwana uku kenan jiyan da haɗuwata da wata Yarinya kyakkyawa kawai naji nan duniya ita nake so.”*

 

*”Iko sai Allah! Yau na ji maɗaukakin mamaki da kace kanason wata yarinya,kai da kace ƳAN MATAN YANZU duka ba na gari sai fatan shiriya?”*

 

*” ASTAGFIRULLAH.! Wato Abokina zuwa yanzu na fuskanci duk inda ya zama da ɓatacce to tabbas za’a samu na gari,kuma ni Allah ya amsa addu’ata yarinyar nutsattsiya baka ganta ba kamilar mace kowa ya shedeta a unguwarsu da makarantarsu kuma yarinya ce mai ƙoƙari wajan neman Ilimi,kuma kaima na tabbata za ka sheda hakan idan ka rakani taɗi Hhh”*

 

*”ALHAMDU LILLAH! Na tayaka murna Abokina daka samu MACE ta gari mai addini da aiki da Ilimi,nima ina roƙon kaci gaba da tayani da addu’ar samun irinta koma wadda ta fita,kai ni ko a ƙawayenta ka binkitamin dan ina da tabbacin dukkanin waɗanda ta ke mu’amala dasu daga gidajen arziƙi suka fito rainon IYAYEN ƘWARAI!.”*

 

Duba👆🏻Yana neman Mace ta gari mai Ilimi ko da a ƙawayen *BUDURWAR ABOKINSHI NE* To kenan idan ke ta gari ce bayan anyi kwatance da ke harda ƙawayenki ma yi ake,wannan kaɗai ya isa ya zamo miki hujjar da zaki zamo Mace ta gari kodan a dinga jinginaki cikin Matayenn da ake addu’a domin a mallake su,shin kin taɓa jin wanda ya zauna yana roƙon Allah ya mallakamai Macen da ta ke bata gari ba?

 

Nidai ban taɓa ji ba,ko da kuwa a labaran da nake karantawa na Marubutanmu ban taɓa karantawa ba,haka kuma ban taɓa haɗuwa da wanda ya karanta ba,abinda na sani shi ne dukkan wani *NAMIJIN ARZIƘI* idan ya ta shi *MACEN ARZIƘI* yake fatan Allah ya haɗashi da ita.Dan a yanzuma zamanin da muka shigo su kansu *LALATATTUN MAZA* idan suka ta shi lalacewarsu basa neman *LALATACCIYAR MACE* irinsu,kintsattsiya suke nema saboda suna gudun kamuwa da wata muguwar cuta da ba’a rasa lalatattu da ita,sun san gun kamilalliyar mace ne kaɗai zasu cika mummunan nufinsu kuma su tsira daga kamuwa daga mugayen cututtuka…

 

*👆🏻WANNAN SHI NE BABBAN DALILIN DA YASA MAZAN BANZA KE BIBIYAR KAMAMMUN MATA WANDA HAKAN A YANZU YAKE CIWA KAMAMMUN MATAN TUWO A ƘWARYA.Ko da ke sannu a hankali zamu zo wannan gaɓar yanzu maganar Ilimi ake.*

 

Dan haka kiyi amfani da damar da kike da ita ki nemi Ilimi tun ƙwaƙwalwarki bata cunkushe da al’amuran rayuwa ba,damar da kike da ita a yanzu idan kika bari ta wuce haka zaki gama girmanki ba Ilimi,yayin da kika tsufa kuwa sedai kawai a biki ta lallami dan ansan in ba’a lallaɓaki ba rashin Iliminki bazai haifar da ɗa mai ido ba.Ya ke BUDURWA! Bazan gajiya wajan ba ki shawara akan ki jajirce ki nemi makaɓin da zaki kare dukkan wani farmaki da aka kawo miki ba,wannan makamin kuma shi ne *ILIMI.*

 

Ya ke *UWA* Ina daɗa shawartarki da ki tsaya tsayin daka wajan ganin ƴarki *BUDURWA* ta samu *INGANTACCEN ILIMI* Wanda zai zame mata *MAFARI..!* A cikin al’amuranta.

 

 

••••

*MUTUNCI!!!*

 

 

*BUDURWA MAI MUTUNCI* Ita ce wadda al’umma ke da burin ganin ta mamayeta ta kowane ɓangare,kuma ita ce wadda Iyaye suke raba dare suna addu’ar Allah ya tsare mata mutuncinta,haka Mazaje ita suke addu’a da burin mallaka a matsayin matar auresu,suma Ƴaƴaye ita suke farin cikin shaidawa ƙawayensu a matsayin Mahaifiya,haka kuma ƙawaye ita suke alfahari da kasancewarsu tare da ita.

 

Duba,kowa da kowa farin cikin kasancewa tare da ke yake yi,dan haka ki bakin ƙoƙarinki wajan ganin kin zama ɗaya daga cikin Mata masu Mutunciii.Budurwa mai Mutunci ba ta raina manya,bata ƙarya,ba ta Hassada,ba ta da ganin ido,haka kuma ba ta bada wata ƙofa da Mutuncinta zai zube.Ƙoƙarinta kullum *TA YA YA ZATA KARE MARTABA DA MUTUNCIN IYAYENTA DA MA ITA KANTA?*

 

Ya ke Budurwa a duk sanda wata Mu’amala ta haɗaki da haɗaki da wata ko wani,yi ƙoƙari ki bayyanar masa da Mutunci da ƙimar gidanku,duk sanda ki ka ji ko ki ka ga wata ɗabi’a wadda batai miki ba a tattare da shi ko ita kada kiji kunya kuma kada kiji tsoro,cire fargaba da tunanin yadda zai karɓi maganarki ki faɗa masa ko ki faɗa mata gaskiya cikin daddaɗan lafazi wanda bamai furtashi sai *BUDURWA MAI MUTUNCI*.

 

Ya ke Budurwa mai Mutunci,ina ƙara ƙarfafamiki gwiwa wajan cigaba da baiwa manya girma ta kowace siga,manya bawai ana nufin iya tsofaffin unguwa ba A’a! Hatta waɗanda suka girmeki duka manyane kuma suna buƙatar ki girmamasu,matan maƙota ne,ƙawayen yayyenki ne,ke a tsarin Mutunci ma bawai dole se wanda ya girmeki ba za ki girmama ba harma wanda kika girma da ƙannenki ababen girmamawa ne,domin se kina ganin mutuncinsu zasu ga naki mutuncin,kuma ki gwada kiga aduk lokacin da kika haɗu da wata wadda a girme da komai kin fita kika bata girma se kinga itama bata da buri se ta girmamaki saboda kunya ta ke ji aduk sanda kika haɗu da ita kika ce mata “A’ah! Aunty Khadijah” Tasan kin girmeta amma hakan baisa kina kiranta da gadara ko nuna isa ba,wannan girman da kike bata shi zaisa mata kunyarki taji kina da wani matsayi a wajanta fiye da na girme mata da kika yi.

 

Abu na gaba indai har kina son kici gaba wanzuwa cikin Mata masu Mutunci sai kinyi yaƙi da ƙarya kin mata fata-fata,dan inhar kina ƙarya to tabbas wata rana sekin nemi Mutuncin Mutuncin da ke tare da ke kin rasa dan ita *ƘARYA* duk sa’ilin da kika yi ta sai wani kaso daga Mutuncinki ya zube daga idon wanda kika yiwa,dan haka idan har kinason tsira da Mutuncinki sai kin raba da hanya da ƙarya dan duk Mace mai ƙarya babu kallon da ake binta da shi sai na banza.

 

Duba ke da kanki cikin ƙawayenki se kiga wata a makaranta ko a layinku ita ba ta da burin da ya wuce a haɗu ta fara zuba se kace kanya,ƙarshe kuma idan aka ɗauki zancen nata aka sa a miizani se aga mafi yawa daga cikinshi ƙarya ne ba gaskiya ba.Kuma in sha Allahu tafi-tafi se wata rana an dinga buga misali da ita a cikin Maƙaryata! Haka kuma ba ta da damar zuwa waje sedai kiji ana gatanan gatananku👌🏻

 

Ya ke *BUDURWA MAFARIN TARBIYYA* Babban makami guda ɗaya ne wanda za ki yaƙi ƙarya da shi kuyi hannun riga wato *BARIN SURUTU/TAƘAITA MAGANA👌🏻*.Dan babban Jigon ƙarya shi ne Surutu,dan da zarar mutun ya fiye surutu sai an sa me shi da ƙarya a cikin zantukanshi,dan tun yana faɗin gaskiya se ya koma faɗin ƙarya ba tare da shi kanshi ya farga ba se hakan ya zame masa al’ada mai wuyar bari.

 

Dan haka ina kira gareki yake Budurwa da *ki guji yawan zance,domin shi yawan zance yana kawo ƙarya,ita kuma ƙarya tana zubar da Mutunci,idan kuma ba ki da Mutunci ba zaki iya bada tarbiyya ba.*

 

Dan haka mu kula da harsunanmu matuƙa mu rage surutan duniya da labarai mu yawaita Salatin Annabi sallallahu alaihi wasallama da Tasbihi dan mu tsira daga faɗawa halaka ta kowace fuska.

 

 

*HASSADA.*

 

Ƙiyayyarka ga wane ba zata hanashi arziƙi ba,haka soyayyarka ga wane ba zata sanyashi arziƙi ba.Ka da ki yarda Hassada ta shiga ƙoƙon ranki,domin ita idan ta shigeka maganinta na da matuƙar wahala haka zalika kuɗi ba sa iya siyenshi ballantana ka siya ka warke.

 

Ki guji Hassada,tsakaninki da ƙawayenki ne,yayyenki ne,ƙannenki ne,maƙotanku ne dama kowa da kowa.Dukkan abinda kika ga wani ya samu sanyawa ranki Allah ne ya bashi kuma kema zai ba ki,idan kuma kinga bai ba ki irin nashi ba,,,tabbas in kika duba zaki ga ya ba ki ta wani ɓangare daban wanda shi bai bashi ba…….✍🏻

 

 

 

 

 

 

 

 

*Ku daure ku bibiyeni sannu a hankali zan iso inda nakeson isowa,sann kuyi sharhi tare da tambayar abinda baku gane ba ta hakanne zan gane kuna biye da ni,na gode.*

 

 

 

*Allahumma arzuƙni bi Hubbi Rasulullah!✨🥰*

 

 

 

 

*ƳAR GATAN MAMA✍🏻💞💞*

Add Comment

Click here to post a comment