Ramadan Day 1 To 30 Quotes
Ramadan Day 1 To 30 Quotes
Ramadan Day 1 Qoate
“duk wanda ya kirkiro muna wani abu a cikin al’amarinmu wannan wanda baya cikinsa, to an mayar masa”.
Ramadan Day 2 Qoate
“an gina addinin musulunci akan abubuwa guda biyar; ka shaida babu wani abinda ya cancanta a bautawa in banda Allah, kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, ka tsaida sallah, kuma ka bayar da zakka, kuma ka ziyarci dakin Alllah, kuma ka azumci watan ramadana”.
Ramadan Day 3 Qoate
“Addinni tunatarwa ce ga Allah, da kuma littafinsa, da kuma mazonsa, da kuma shuwagabannin musulmi, da kuma al-ummarsu baki daya”
Ramadan Day 4 Qoate
“Abinda na hanaku ankansa, to ku nisanceshi, abinda kuma na umarceku dashi, to kuzo man dashi gwargwadon iko, domin wannan shine ya halakarda wadanda suke kafin ku, yawan tambayar da sukeyi da kuma sabawar da suke yiwa Annabawansu”
Ramadan Day 5 Qoate
“Kabar abin da kake kokwanto zuwa ga abinda ba ya saka kokwanto.”
Ramadan Day 6 Qoate
“Manzon Allah S.A.W ya ce Yana daga cikin kyawun musuluncin mutum ya bar abin da bai dameshi ba”
Ramadan Day 7 Qoate
“Imanin dayanku bazai cika ba har sai yaso ma dan uwansa abinda yake so ma kansa”
Ramadan Day 8 Qoate
“Manzon Allah S.A.W yace Jinin Mutum musulmi ba ya halatta sai da dayan abu uku. Bazawari mazinaci, da ran da ya kashe rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama’a”
Ramadan Day 9 Qoate
“Manzon Allah S.A.W yace Wanda duk ya kasance yayi Imani da Allah, da ranar Lahira, to ya fadi alhairi, ko kuma yayi shiru.”
Ramadan Day 10 Qoate
“Manzon Allah yace hakika Allah ya hukunta a kyautata akan dukkan komai, idan zaku yi kisa, to ku kyautata abin kisan, Idan za ku yi yanka, to ku kyautata abin yankan, kuma lalle dayanku ya wasa wukarsa, kuma lalle ya hutar da abin yankansa.”
Ramadan Day 11 Qoate
“Manzon Allah S.A.W yace kaji tsoron Allah duk inda kake, kuma ka biyar da kyakkyawan aiki a kan mummuna, domin ya shafe shi, kuma kayi hulda da mutane, da hulda kyakkyawa”.
Ramadan Day 12 Qoate
“Lalle hakika yana daga cikin abinda mutane suka riska na daga cikin maganganun (zantuka) Annabawan farko cewa: idan ba ka da kunya, to ka yi abin da ka ga dama”.
Ramadan Day 13 Qoate
“Ko wacce yine da rana take fitowa, idan ka sasanta tsakanin mutane biyu kanada ladar sadaka, haka kuma taimakon mutum a kan dabbarsa, ko ka dauka masa kayansa akanta, ko ka dora masa kayansa akan ta, kanada ladar sadaka, kuma ga kowane taki da ka taka shi zuwa Masallaci, kanada ladar sadaka, haka kuma kau da wani abu dake iya cutar wani akan hanya shima kanada ladar sadaka.”
Ramadan Day 14 Qoate
Ina yi muku wasiyya da tsoron Allah Mai Girma da Daukaka da kuma ji da kuma da-a, koda za-a shugabantar muku da bawa. To hakika duk wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Na umarce ku da bin sunnata, da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa, ku riketa da kyau. Ina horonku da kirkirarrun al-amura, domin kowacce bidi-a bata ce.
Ramadan Day 15 Qoate
“Hakika Allah Madaukakin Sarki ya wajabta farillai, kada ku wulakanta, kuma ya sanya iyakoki kada ku Ketare su kuma ya haramta wadansu abubuwa, kada ku ketara su, kuma ya kyale wadansu abubuwa don rahama a gare ku, ba don mantuwa ba, to kada kuyi bincike akansu.”
Ramadan Day 16 Qoate
“Ka guji abinda a cikin duniya sai Allah ya soka, kuma ka guji abinda a hannun mutane, sai mutane su so ka.”
Ramadan Day 17 Qoate
“Da ana baiwa mutane abinda duk suke roko, da wadansu mutane sun yi da’awar dukiyar wadansu da jininsu. Sai dai mai Kara ya kawo shaidu, ita kuma rantsuwa tana akan wanda ya musu.”
Ramadan Day 18 Qoate
“Duk wanda ya ga abin ki a cikinku, to ya canza shi da hannayensa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, idan ba zai iya ba, ya ki abin a zuciyarsa. wannan shi ne mafi raunin imani.”
Ramadan Day 19 Qoate
hakika Allah Madaukakin Sarki ya ce: Wanda ya yi gaba da masoyina, to hakika na yi masa izinin yaki da ni. Kuma bawana bai gushe ba yana neman kusanci a gare ni, da nafilfilu, har sai na so shi. Idan kuwa na so shi, to, sai na kasance ni ne jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da kuma hannunsa da yake jimka(taba wani abu) dashi, da kuma kafafuwansa da yake tafiya dasu. Kuma wallahi idan ya rokeni, wallahi sai na bashi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina, wallahi sai na tsareshi”.
Ramadan Day 20 Qoate
“hakika Allah ya yafe wa al,ummata abin da suka aikata shi bisa kuskure Ko mantuwa, ko abin da aka tilasta su akansa.
Ramadan Day 21 Qoate
” Idan ka yi yammaci, to kar ka jiraci safiya, kuma idan ka wayi gari, to kada ka jiraci yamma. Nemi ribar lafiyarka kafin ciwonka, da kuma rayuwarka domin mutuwarka.”
Ramadan Day 22 Qoate
“Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya kasance yana son abinda nazo dashi”
Ramadan Day 23 Qoate
“Ya kai dan adam, hakika muddin ka roke ni, kuma ka Kaunace ni, zan gafarta maka abin da yake kanka, kuma ban damu ba.’
Ramadan Day 24 Qoate
” Ya kai dan adam da dai zunubinka ya kai tsattsakin sama sannan ka nemi na gafarata maka, zan gafarta maka.”
Ramadan Day 25 Qoate
” Ya kai dan Adam hakika da za ka zo min da zunubi cike da Kasa sannan ka hadu da ni, bakayi shirka dani da kowa ba, to da na zo maka da gafara cike da ita.”
Ramadan Day 26 Qoate
“Wanda hijirarsa ta kasance domin Allah da manzonsa to ladar hijirarsa tana ga Allah da kuma manzonsa.”
Ramadan Day 27 Qoate
“Wanda hijirarsa ta kasance domin duniya don ya sameta ko kuma wata mata da yake son ya aura, to ladar hijirarsa tana akan abinda yayiwa hijira.”
Ramadan Day 28 Qoate
“Addinin musulnci shine; ka shaida cewa babu wani abin da ya cancanta a bautawa in banda Allah, kuma ka shaida cewa Muhammad manzon Allah ne, ka tsaida Sallah, ka bada zakka, ka azumci watan ramadana, ka ziyarci dakin Allah, idan hanya ta sauwaka gareka”
Ramadan Day 29 Qoate
“ka bautawa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to Shi Allah yana ganinka”
Ramadan Day 30 Qoate
“lalle hakika halal a bayyane yake kuma hakika haram a bayyane yake”
Ramadan 2023 Dates, Images, Pictures and Quotes
“Yaku wadanda kukayi Imani kuci daga abu mai tsabta cikin abinda muka azurtaku”
[…] Ramadan Day 1 To 30 Quotes […]
[…] Ramadan Day 1 To 30 Quotes […]