Maniyin Budurwa Banbancin sa da na Namiji
Maniyin Budurwa Banbancin sa da na Namiji
Maniyi kwayoyin halitta ne na da namiji wanda a wurin mu’amala ta aure yake haɗuwa da manyan ƙayaƙwan halitta na mace.
dabbobi sunada ƙwayar halitta wadda ake kira da maniyi kuma tanada jela wadda yakeyin motsi da ita.
Yadda Amarya Zatayi a Daren Farko
wasu daga cikin halittun ruwa suna halittar maniyi wanda be da jelar motsi wanda ake kira maniyia wadansu daga cikin tsirin sunada ƙwayoyin halitta marasa motsi wasu kuma sunada masu motsi.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Anan ZAUREN FIQHU Muna yawan samun tambayoyi akan wannan Mas’alar daga bangarorin Maza da mata. Amma in sha Allahu yanzu zanyi bayani daidai gwargwadon iko.
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Ina fatan zaku gafarceni. Zanyi bayani dalla dalla (duk da cewar akwai nauyi sosai) to amma abu ne wanda ya shafi addini. Kuma bangaren tsarki ne wanda sai dashi ibadah zata yiwu.
Maniyyi da Maziyyi suna da bambanci ta bangarori guda uku kamar haka:
1. Bambanci a yanayin Siffarsu.
2. Bambanci ayanayin da ake ji bayan fitarsu.
3. Bambanci a bangaren hukuncinsu.
1. SIFFOFINSU
Manzon Allah (saww) shi da kansa yayi bayanin yadda siffarsu take yayin da yake bada amsa bisa tambayar da Sayyidah Ummu Sulaym tayi masa.
Yace : “SHI DAI MANIYYIN NAMIJI, FARI NE KUMA YANA DA KAURI. SHI KUMA MANIYYIN MACE, FATSI FATSI NE, KUMA TSINKAKKE NE (BASHI DA KAURI).
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Akan wannan ne malamai sukayi Qarin bayani cewa Shi maniyyin Namiji yana Qamshin Furen dabino ne. Kuma yana fita ne tare da zunkudar junansa. (wato yana fita da Qarfi). Shima na macen haka yake.
Kuma in dai maniyyi ya fita daga Mace ko Namiji, acikin barci ko afarke, to yana Wajabta wanka.
Sai dai wadanda suke tare da Larura ko jinya, ko kuma ta dalilin faduwa daga sama, har maniyyi yakan fita daga garesu ba tare da motsuwar sha’awar komai ba, to wannan ba ya karya azumi kuma ba ya wajabta wanka.
Shi kuma MAZIYYI duk kala daya ne na mata da na Mazan. fari ne shi garai garai. Kuma yana fitowa ne bisa dalilin motsawar sha’awar Jima’i. Ta dalilin Kallo, ko shafa, da Tunanin Jima’i.
2. BAMBANCI YAYIN FITARSU:
Shi Maniyyi yana fita ne yayin da sha’awa ta kai Kololuwa, kuma akan samun mutuwar Jiki, har tsattsafowar gumi bayan fitarsa.
Shi kuma Maziyyi yana fita ne yayin motsawar sha’awa kadai. Kuma ba’a samun mutuwar jiki bayan fitarsa.
3. BAMBANCI A HUKUNCINSU:
Fitar Maniyi tana wajabta wanka, ita kuma fitar Maziyyi bata wajabta wanka. Sai dai Mutum zai je ya wanke al’aurarsa baki daya.
Malamai sunyi sabani akan Shin Maniyi Najasa ne, ko ba najasa bane. Amma shi Maziyyi kowa ya yarda cewa shi NAJASA ne.
MAGANAR QARSHE:
Maniyyin Maza: Fari ne yana da kauri da yauki.
MANIYYIN MATA: Fatsi ne, bashi da kauri, kuma yana da yauki yauki.
Ana yin wanka saboda fitarsa. Kuma Malaman Malikiyyah sunce Shi maniyi Najasa ne.
MAZIYYI : Na maza da Mata duk iri daya ne. Kuma fari ne tsinkakke. Garai garai yake kamar ruwan sha.
Yana karya alwala, kuma ana wanke al’aura baki dayanta sabosa fitarsa. Kuma za’a wanke tufafin da ya taba.
WADIYYI : Yana fita ne akarshen fitsari. hukuncinsu daya da fitsarin. Za’a wankeshi ne kawai…
[…] Maniyin Budurwa Banbancin sa da na Namiji […]