Littafan Hausa Novels

Sune Suka Janyo Min Hausa Novel Complete

Sune Suka Janyo Min Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SUNE SUKA JANYO MIN

By Hafsat Hisham

 

 

Page 1 and 2

Free page

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayii min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

 

 

 

Katon mansion ne babba wanda yake dauke da katon part guda daya sai kuma k’aramin part daga gefe, motoci ne birjik a parking spot, wani saurayi na hango jingine da mota yana kallon wristwatch dake daure akan tsintsiyar hannunsa, black beauty mai gemu yana sanye da kaptain ya murza hula tangaram, he looks neat and breathtaking, daga ganinsa ba ya damuwa, he have such an innocent face…..

A hankali take taking steps tana tunkarar inda yake fuskarta a murtuke, she looks stubborn, tana sanye ne da atamfa dinkin riga da skirt wadanda sukayi suiting dinta, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, tana da matuk’ar kyau, she’s brown skin, tall, slim, gorgeous and breaktaking, tana tafiya baki daya jikinta yana girgiza, yana hangota ya washe baki yana murmushi, saida tayi mashi wani mugun kallo idanunta a tsaitsaye cike da tsiwa sannan tace,

Gwauro Hausa Novel Complete

“Osman… How dare you… Na fad’a maka kadda in k’ara ganinka a gidan nan amma saboda na ci shine ka dawo… Na fad’a maka na daina soyayyar ana dole ne…”.

Osman yayi murmushi sannan yace,

“Calm down Arfaat… Ki kwantar da hankalinki… Calm down…”.

Arfaat ta watsa hannuwa a iska saying,

“Calm down my f**t…”.

Osman fuskarsa dauke da damuwa yace,

“I didn’t mean to upset you… Idan nayi maki laifi ne ki fad’a min sai in baki hakuri…”.

Arfaat tace, “Babu laifin da kayi min soyayyar ce na fasa yi, ana dole ne…”.

Osman ya soma girgiza while saying,

“Lailaturrahman kadda kiyi min haka, duk tsayin lokacin nan da muka dauka muna gima soyayyarmu mai cike da tsafta sai yanzu da na gama nitsu a kogin sonki sannan kice mu rabu… Ba zan iya rabuwa dake ba…”.

Arfaat tace, “Ni kuma zan iya rabuwa da kai… Hey, this is annoying, I feel like throwing up… I don’t want to see your face ever again, get the hel! out of my sight…”.

Osman yace, “No… Arfaat don’t do this…”.

Arfaat ta juyo gefe tana kwalawa security kira, daya daga cikinsu ya k’araso, kamar sauran yana sanye da suit ne bakake, kato ne majiyi karfi, yace,

“Yes…”.

Arfaat tace, “Ka tabbata ya janye motarsa daga gidan nan kuma daga yau kadda a k’ara barinsa ya shigo gidan nan otherwise you know what I’m capable of doing…”.

Yace, “Yes Ma’am…”.

Osman yace, “Please Arfaat don’t do this, I can’t take it, I can’t lose you…”.

Arfaat tace, “If you ever love me truly in your heart then respect my decision and get the hel! out my life… Your are annoying….”.

Ta juya ta soma walking toward kofar shiga parlor tana jin yana kiran sunanta amma bata juyawa ba, ta shiga bedroom ta durkushe kasa tareda fashewa da kuka saying,

“I’m sorry Osman, idan na cigaba da kasancewa tare da kai zasu illataka ne shiyasa na rabu da kai… I’m really sorry…”.

Motsi taji ta ruga bathroom ta kunna tap tana wanke fuskarta wasu hawaye suna zubowa, ta jima sannan ta sakarwa kanta shower ta fito, ta saka gown ta rufe kanta da veil, ta kwanta akan gado tayi lamo tana tunani akan yadda rayuwa take wasan kura da ita akan abun da babu laifinta a ciki….

Ta janyo wayarta ta shiga yanar gizo, baki daya history dinta tana bincike ne akan jinnul ashirk, call ne ya shigo wayar tayi jim tana kallon sunan dake akan majigin wayar _Oum Salmerh_ saida aka jera mata misscalls biyar ba tayi picking ba, text message aka tura mata….

_A sanadinki yayi accident_

Da sauri ta dannawa numbar kira har jikinta yana rawa, daga daya bangaren muryar mace ne tana kuka tace,

“Arfaat kin cucemu a rayuwa, kin tarwatsa mamu farin ciki, amma babu komai kije mun barki da Allah…”.

Arfaat ta fashe da kuka saying,

“Na boni… Kuna wani asibiti ne?”.

Daga daya bangaren aka ce,

“As if you care bayan kece sanadin komai… Allah baya barin zalunci ki jira ranar sakamako…”.

Arfaat tana magana taji shiru tana dubawa taga tayi hanging call din ne, ta fad’a akan gado ta zafe kai sai kuma ta maida akalar kiranta zuwa wata number tayi jim sannan tace,

“Zanyi maka message yanzu and I want you to look into it and get back to me immediately, it’s urgent…”.

Tayi hanging call din ta tura text message, ta zura long hijab a saman kayan da suke jikinta ta suri makullin motarta ta fice, ta danna horn mai guard ya wangame mata get ta danna motar waje, text message ne ya shigo wayar tana dubawa ta sauya akalar motar zuwa wata hanyar, cikin mintuna kadan ta k’arasa asibitin tayi parking motarta, da gudunta ta shiga emergency, tayi turus ganinsu a tsatstsaye kowanne fuskarsa dauke da damuwa, a hankali ta soma ja da baya tana girgiza kai while saying,

“Why? Why? Why me? Afterall bani bace nayi amfani daku…”.

Oum Salmerh ce ta hangota cike da b’acin rai ta nufo inda take ta kama hannunta ta jata ta wurgar da ita waje, tana hawaye at the same time fuskarta dauke da b’acin rai tace,

“Meyyy kikeyi a nan bayan kece sanadin komai? Duk abun da ya faru dashi kece kika janyo… Duk abun da ya faru dashi kece sanadi… Don haka ki wuce ki barmu da bakin cikin da muke ciki… Please don’t make it hard for us, just leave… You don’t have to play the innocent… We are the victims here… Kin rabamu da farin cikinmu…”.

Arfaat ta fashe da kuka while saying,

“Oum Salmerh… Ba ni da laifi… Ba laifina bane…”.

Oum Salmerh ta had’e hannayenta waje guda tace,

“Please I beg of you, please leave, ki barmu da bakin cikin da muke ciki…”.

Arfaat ta soma tafiya a hankali tana girgiza kai yayinda hawaye suke zubowa daga idanunta, ta zauna akan bench tareda dafe kai tana zubar da hawaye, cikin ranta tace,

“Mi yasa ba zaku fahimci ni ba… Ku fahimceni sun ce idan ban rabu dashi ba zasu cutar dashi… Sun ce idan ban rabu dashi ba zasu b’atar dashi… Ba ni da wani zabin da ya wuce in rabu dashi domin kubutar da rayuwarsa… Shin yaushe ne zasu rabu dani? Shin yaushe ne zasu bari inyi aure? Tun yanzu da nike da kananan shekaru sunce ba zasu bari inyi aure ba? Shin hakanan zan zauna inyi shekaru har inkai lokacin aure in zarce ba tareda nayi shi ba… Sun cuceni, *SUNE SUKA JANYO MIN* saboda son abun duniya da kuma son zuciya irin nasu…”.

Ta jima a haka kafin ta kanga waya a kunnanta tayi jim sannan tace,

“Abba ban iya driving da kaina, a aiko wani yazo ya daukeni…”.

Sai kuma tayi hanging call din, tayi kasa da kanta fuskarta dauke da damuwa, bayan mintuna ashirin taji muryar namiji a saman kanta saying,

“Arfaat… Makullin…”.

Arfaat ba tareda ta d’ago ba ta mik’a mashi makullin, tareda mashi pointing inda motar take, foot step taji alamar yana tafiya ne, ta d’ago jin har lokacin kamshinsa yana manne da wajen, mik’ewa tayi tai taking steps ta b’alle murfin backseat ta shiga ta rufe tayi relaxing tareda rufe idanunta ba tareda ta damu da ganin ko waye ba, yana parking motar ta b’alle murfin motar ta fice ta wuce ciki….

Saida ta goge hawayen da suke akan fuskarta sannan ta shiga parlorn, Abba, Ummy, Sultan da Nabila ta tarar, Nabila ta ruga da gudu ta rungumeta, Arfaat ta kirkiro murmushi saying,

“Hi…”.

Abba yace, “Arfaat mi ya kaiki asibiti?”.

Saida tayi sama da fuskarta ta maida hawayen da suke shirin zubo mata sannan tace,

“Na baku labari akan mafarken marfaken da nakeyi da kuma barazana da sukeyi min akan idan ban rabu da Omar ba zasu b’atar dashi, nace ya rabu dani shine yayi accident…”.

Bata jira abun da zasu ce ba ta wuce staircase ta fad’a bedroom dinta saida ta watsa ruwa sannan ta kwanta bacci ne yayi awon gaba da ita wanda yake tareda mafarkai masu cike da tsoratarwa da razanarwa….

Washegari tun da safe ta shiga kitchen ta had’a breakfast ta saka a basket tayi wanka ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skirt, ta zura long hijab ta sauko kasa, tana tafiya ne a hankali da sand’a, Ummy ta dubeta da mamaki tace,

“Ina zakije?”.

Arfaat tayi turus tareda ware idanu, tace,

“Zanje asibiti ne ganinsa…”.

Ummy tayi pointing staircase tace,

“Go back to your room, babu inda zakije…”.

Arfaat tace, “Amma Ummy…”.

Ummy ta daka mata tsawa saying,

“Lailah get the hel! out of my site…”.

Hafsat ta juya da gudu ta koma bedroom dinta ta fad’a akan gado tareda fashewa da kuka, Ummy ce ta shigo zama tayi a bakin gado ta dafata tace,

“Lailerh, zuwanki wajenshi bashi da amfani, it will only complicate thing, there’s nothing you can do, kiyi mashi addu’a Allah ya bashi…”.

Arfaat ta rungumeta tareda fashewa da kuka, tace,

“Why? Why me?”.

Ummy tace, “Allah zai kawo maki mafita… Ki saki ranki ki cigaba da yi mashi addu’a…”.

Arfaat ta kirkiro murmushin karfin hali tace,

“In shaa Allah…”.

“Allah yayi maki albarka…”.

“Amin…”.

Umma tace, “And I almost forget Aisha ta kira, jibi zata aiko Baby tareda direba kije da ita telanta zai aunata and zaki amso mata dinkunanta dake a wajenshi…”.

Hafsat tace, “Alright… Allah ya kaimu…”.

Umma tace, “Amin…”.

Sannan ta mik’e ta fita….

***************

Two Days Later,

Arfaat ce ta fito harabar gidan tana rik’e da hannun wata cute yarinya er kimanin shekaru tara, tana sanye ne da long hijab har kasa yayinda ta rufe fuskarta da niqab, looking lovely, decent and neat, direct suka nufi wata sabuwar mota ash kirar Mercedes Benz, ta danna horn mai guard ya wangame mata get ta danna motar waje, a daidai wani bene tayi parking ta kalli rubutun dake akan shagon dinkin sannan ta b’alle murfin motar ta fito tana rik’e da hannun Baby suka nufi shagon dinkin, tana tafiya long hijab dinta yana sharar kasa, saida tayi salaam sannan ta shiga, samarin dake cikin shagon dinkin suka amsa sallamarta, tace,

“Najeeb fa?”.

“Najeeb yanzu aka kirashi ya tafi gida…”.

“Okay dama zan amshi dinkunan Auntynerh ne a wajenshi… Ga wayata ku saka min digits dinsa…”.

“Ga wayar nan ya bari akan charge…”.

Arfaat ta dafe kai sai kuma tace,

“Okay bara na jirashi a mota, idan ya dawo kuce yayi min magana ga motar can wancen ash din…”.

“Sure…”.

Ta juya ta koma cikin mota, Baby tace,

“Angel… Game…”.

Arfaat ta mik’a mata iPad dinta tareda biscuits, tayi relaxing tareda lumshe idanu sai kuma ta bud’e murfin motar ta zuro kafafunta tana kallon wajen, ji tayi bugun zuciyarta ya k’aru, ta dafe saitin zuciyarta tana mamakin dalilin faruwar wannan al’amari, hangoshi tayi zaune akan mota tareda wasu samari, saida gabanta ya yanke ya fad’i, the more take kallonshi the more take jin yana k’ara mata kyau, the more take kallonshi the more take jin yana k’ara shiga ranta, the way he talk, his smile, anything about him is unique and perfect, fari ne sosai har yellow skin dinsa take saboda haske, he’s damn cute, good looking saurayi, kyakykyawan buzu, yana sanye da brown shadda ya murza hula zanna bukar, da sauri ta kawar da kanta ganin zai juyo, a hankali ta juya da kanta ta cigaba da kallonsa, kallonshi kawai yana saka bugun zuciyarta ya k’aru, kallonshi kawai yana sakawa ta jita a cikin kwanciyar hankali, ta shagala da kallonshi har bata san lokacin da Baby ta fita daga motar ba, juyowa yayi, da sauri ta kawar da kanta pretending as tana danna waya duk da bazai lura da ita ba….

“Salaam alaiki…”.

Ta jiyo muryar namiji, ta d’ago ta ware idanu ganinsa a tsaye a kanta, yana murmushi….

 

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan naira dari biyar kacal 500, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

*For those of you asking yadda zasu biya kudin, zaku biya ne ta hanyar tura hoton Katin MTN via WhatsApp 09169472057, ko kuma VTU/Transfer ta 09169472057, sai kuyi screenshot ku tura via WhatsApp 09169472057*

 

Hafsat Hisham ce 🥰😘🥰

[17/02, 4:46 pm] +234 916 947 2057: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN* 💨

By Hafsat Hisham

 

 

Page 3 and 4

Free page

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayii min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

 

 

Arfaat ta d’ago ta ware idanu ganinsa a tsaye a kanta yana murmushi, da mamaki take kallonsa, gyara yanayin fuskarta tayi a sanadin ganin Baby da tayi rik’e da hannunsa, tace,

“Wa alaikassalaam… Sorry she most have disturb you…”.

Baby yace, “I didn’t disturb him… He’s my new friend…”.

Arfaat ta kama hannunta tace,

“Na gode… Sorry, I was carried away ta fita ban lura ba…”.

Yace, “Alright…”.

Sai kuma ya juya ya soma tafiya ta bishi da kallo bata koda blinking, the way he walk is unique, yana juyowa tayi sauri ta kawar da kanta, yayi wa baby waving hand, itama tayi mashi waving hand, ya koma ya zauna akan motar, Baby tace,

“Angel…”.

Arfaat tayi firgigit daga kallonsa tace,

“Meyyy?”.

Baby tace, “Kinyi shiru baki hira, it is annoying, zanje wajen Uncle yayi min hira…”.

Arfaat ta ware idanu tareda rik’e hannunta tace,

“A’a, babu inda zakje…”.

Baby ta fizge hannunta ta gudu wajensu, saida ya kalli inda Arfaat take sannan ya d’aura baby a bayan motar, Arfaat tayi jim tana kallonshi, she can’t take her eyes from him, ji take kamar an saka magnet a tsakanin idanunta dashi, sau biyu yana kamata tana kallonshi, tayi kasa da kanta saying,

“Na boni, what will he think of me, koda yake dole ne in kalli inda yake tunda baby tana wajenshi…”.

Sai kuma ta mik’e tareda nufar inda yake, tayi masu salaam….

“Salaam alaikum…”.

“Wa alaikassalaam…”.

Arfaat tayi jim sannan tace,

“Kuyi hakuri na rik’eta amma ta gudo…”.

Daya daga cikinsu yace,

“Kadda ki damu…”.

Baby tace, “Ba zan biki ba…”.

Arfaat tace, “Hey you, wuto muje…”.

Sai a lokacin yayi magana saying,

“Zaku wuce ne…”.

Arfaat tace, “A’a, tukunna dai, dinki nazo amsa wajen Najeeb kuma ba ya nan, an kirashi gida, wayarshi tana shagon…”.

Daya daga cikinsu yace,

“Ina da numbar k’anwarshi, let me call her…”.

Arfaat tace, “Na gode, Baby let go…”.

Baby ta turo baki tace,

“I’m going no where…”.

Yace, “Kadda ki damu idan kin tashi tafiya zan kawota…”.

Tace, “Alright then, thank you and sorry for disturbing you…”.

Ta juya ta koma cikin motarta tana satar kallonshi daga lokaci zuwa lokaci, babu jimawa Najeeb ya dawo akan bike, yayi mata salaam, ta d’ago saying,

“Wa alaikassalaam… Najeeb… Right?”.

Najeeb yace, “Ehhh shine, kiyi hakuri an kirani gida ne kuma na manta wayar a shago…”.

Arfaat tace, “Don’t worry, Hajiya Aysha ta aikoni zan amsar mata dinkunanta a wajenka kuma tace zaka auna Baby…”.

Najeeb yace, “Ehhh munyi haka da ita, na gama dinkunan suna ciki, bari na kawo maki, Ina babyn take…”.

Arfaat tace, “Gata can wajen mutumin can bara in shigo da ita shagon sai ka aunata…”.

Najeeb yace, “Alright…”.

Arfaat ta fito daga motar tareda rufeta ta nufi inda suke, tace,

“Na gode, yazo, baby muje ya aunaki mu wuce gida…”.

Baby ta kalleshi tace,

“Uncle let go…”.

Yace, “Okay then…”.

Ya duro daga saman motar ya kama hannunta, a tare suka shiga shagon, Arfaat tace,

“Najeeb gata nan, itace zaka dauki measurement dinta…”.

Najeeb yace, “Abdurrahman…”.

Arfaat cikin ranta tace,

“Ohhh ashe sunanshi Abdurrahman…”.

Abdurrahman yace, “Yane guys… How far…”.

Saida Najeeb ya auna Baby sannan ya fiddo leather da dinkunan suke ciki, Abdurrahman yace,

“No… Ka bari, zan daukar mata…”.

Arfaat tayi murmushi tana kallonshi, the more take tare dashi the more take jin bata son su rabu, har mota ya rakasu ta amshi leather ta saka a backseat, Baby tace,

“Bye Uncle…”.

Abdurrahman yace, “Bye baby…”.

Arfaat tace, “Thanks so much… Na gode…”.

Abdurrahman yace, “You are welcome…”.

Ji take bata son rabuwa dashi amma bata da wani zabi da ya wuce shi, ta dannawa motar key na nausata akan kwalta, tana driving a nutse tana murmushi yayinda take tuno fuskarsa, yadda yake magana da kuma murmushinsa, tafiyarsa….

Arfaat ta fad’a akan kujera saying,

“Wash…”.

Ummy tace, “Ina kuka tsaya…”.

Arfaat tace, “Lokacin da mukaje ba ya nan kuma ya bar wayarsa a shagon saida muka jira ya dawo…”.

Ummy tace, “You should have call and inform me, har hankalina ya soma tashi, ina tunanin in kira wayarki…”.

Arfaat tayi murmushi sannan tace,

“In shaa Allah…”.

Ummy ta zuba mata idanu kamar mai nazari, Arfaat tace,

“Ummy?”.

Ummy tace, “Angel you look happy, kina ta murmushi, da alama kina cikin farin ciki…”.

Arfaat ta mik’e tareda yin juyi while saying,

“In shaa Allah daga yau kin cigaba da ganin murmushina kenan…”.

Ta wuce staircase, saida ta watsa ruwa sannan ta kwanta akan gado tayi lamo tana tuna fuskarsa yayinda murmushi yake sub’uce mata, she is wondering mi yake yi a wannan lokacin….

Sultan ne yayi knocking tareda salaam, tayi firgigit tareda amsa sallamar da yayi, ya shigo, ya dubeta da mamaki yace,

“Mi ya faru kike ta murmushi?”.

Arfaat tace, “Nothing, I’m happy because I deserve to be happy…”.

Sultan ya tab’e baki sannan yace,

“Ummy tace ki sauko kici abinci…”.

Arfaat ta koma ta kwanta akan gadon saying,

“Kace mata na koshi…”.

Sultan yace, “Not me… Ki tashi kije ki fad’a mata da kanki cox maidoni zatayi…”.

Arfaat ta duro daga saman gadon tabi bayanshi, a parlor ta tarar da Ummy, Ummy tace,

“Ga abincinki can akan dinning table…”.

Arfaat tace, “I’m full…”.

Ummy ta dubeta da mamaki tace,

“Amma baby tace tunda kuka fita ba kuci komai ba…”.

Arfaat tace, “Hakane…”.

Ummy tace, “Then ki b’ace min daga gani, ki zuba abinci kici…”.

Arfaat ta wuce dinning table, ta janyo plate tayi serving sakwara da miya wacce taji busasshen kifi, ta soma ci tana lumshe idanu yayinda take tuna fuskarsa, she’s wondering mi yaci, she’s busy enjoying the food, tana dagowa taci karo dasu tsaye a kanta suna kallonta fuskokinsu cike da mamaki, they’re totally speechless, tace,

“What?”.

Nabila tace, “But Angel you hate sakwara…”.

Sultan yace, “Tun da na tashi nasan baki cin sakwara, da kici sakwara gwara ki kwana da yunwa, duk ranar da za’ayi sakwara saidai Ummy ta dafa maki wani abun…”.

Ummy tace, “I’m totally speechless…”.

Arfaat tayi murmushi saying,

“Indai sakwara ce daga yau ta koma one of my fav food, daga yau zan rink’a cin sakwara…”.

Sultan yace, “Are you alright, anya baki buge kai ba…”.

Arfaat ta harareshi saying,

“Cikina ne and now I decide zan rink’a ci shine har zaka ce min na buge kai, buge kai manya…”.

Ummy tace, “Shi kuma shinkafa da na dafa maki fa sai inyi ya dashi?”.

Arfaat tace, “Ummy sai ayi sadaka dashi, sadaka maganin bala’i…”.

Ummy ta juya ta koma parlor fuskarta dauke da mamaki, Nabila tace,

“Angel you are weird…”.

Sultan yace, “Gwara ki fad’a mata gaskiya, weirdo…”.

Arfaat ta d’age shoulder saying,

“Ba weirdo ba, komai zakace bazan biye maka ba domin a yau ina cikin farin ciki…”.

Sultan ya tab’e baki ya wuce balcony, Nabila ta koma parlor wajen Ummy, Baby har tayi bacci….

Kira ne ya shigo wayarta tayi firgigit tana imagine ace shine ya kirata, tana dubawa taga Aunty Aysha, tayi picking tareda kanga wayar a kunne tayi jim sannan tace,

“Wa alaikissalaam… Ehh mun amso kuma ya dauki measurement dinta… Hakane mun samu ba ya nan saida muka jira… Har tayi bacci… Okay then, zasuji… You are welcome… Ahhh… Tuba nike… Ahhh…”.

Sai kuma ta cire wayar daga kunnanta ta mik’e ta wuce parlor, ta kunna light wakar soyayya tana sauraro tana tuna fuskarsa tana murmushi, throughout da rest of the day ta b’ata shi ne wajen tunaninsa wondering mi yake yi a wadannan lokuttan….

Washegari tana farkawa daga bacci shine abu na farko da ya fara fado mata a rai, ji tayi shi kadai take son ta gani, idan ta ganshi baki daya damuwarta b’acewa takeyi sai zallar farin ciki, suna breakfast tayi zuru tana juya spoon, Abba yace,

“Arfaat what wrong with you?”.

Arfaat tayi firgigit tace,

“A’a babu komai…”.

Abba yace, “Kin tabbata ba waccen damuwar bace…”.

Arfaat ta girgiza kai tace,

“A’a…”.

“Tun da kun gama jarabawar gama sekondire wani gift kike son in baki?”.

Arfaat cikin ranta tace,

“Abdurrahman…”.

Amma a zahiri sai tace,

“Ko miye ka bani ina so…”.

Sultan ne yace, “Angel ke da kika ce kullum zaki rink’a farin ciki, amma yau you look different, tun yanzu… Arfaat you are weird…”.

Arfaat ta taso mashi saying,

“Sultan ka fita daga harkata… Abba ka rabani da wannan yaron…”.

Sultan yace, “Waye yaron?”.

Abba yace, “Kai Sultan ka daina takular Mamana, ke kuwa Arfaat bazan rabaki dashi ba amma nace ya daina b’ata maki rai…”.

A tare sukayi dariya, Nabila tace,

“Abba really she is weird, jiya taci sakwara and she said that it’s yummy…”.

Abba ya ware idanu saying,

“Are serious…”.

Nabila tace, “Yes…”.

Sultan yace, “Hakane…”.

Abba ya maida kallonshi a kanta yace,

“Wai hakane…”.

Arfaat tace, “Daga na yanke shawarar zan rink’a ci shine suke fassarani…”.

Abba yace, “I’m surprise, anyway finish up your food… We will talk about it later…”.

Suna gamawa ta tattara abubuwan da aka b’ata ta wuce dashi kitchen, ta wankesu ta gyara kitchen din ta fito ta tadda Ummy a parlor tace,

“Abba fa?”.

Ummy tace, “Ya fita…”.

Arfaat ta gyad’a kai ta juya ta soma taking steps, Ummy tace,

“Arfaat…”.

Arfaat ta tsaya cak tareda juyowa tace,

“Na’am…”.

Ummy tace, “About you eating sakwara, are you sure nothing is wrong…”.

Arfaat tace, “No… Nothing’s wrong…”.

Ummy tace, “About your medicine…”.

Arfaat tayi shiru tana raba idanu, Ummy tace,

“I guess bakiyi amfani dashi ba sai ki wuce kije kiyi yanzu…”.

Arfaat ta juya ta wuce sama, ta zauna a balcony tayi tagumi tana tunanin yadda za’ayi ta koma wajen ko zata sake ganinsa, dubara ce tazo mata sai kuma ta turo baki tace,

“Ummy ba zata bari ba…”.

 

 

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan naira dari biyar kacal 500, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

*For those of you asking yadda zasu biya kudin, zaku biya ne ta hanyar tura hoton Katin MTN via WhatsApp 09169472057, ko kuma VTU/Transfer ta 09169472057, sai kuyi screenshot ku tura via WhatsApp 09169472057*

 

Hafsat Hisham ce 🥰😘🥰

[17/02, 4:46 pm] +234 916 947 2057: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN* 💨

By Hafsat Hisham

 

 

Page 5 and 6

Free page

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayii min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

 

 

Arfaat tayi jim, kira tayi a wayarta, daga daya bangaren Abba yayi picking call din, tace,

“Salaam alaikum…”.

“Wa alaikissalaam….”.

“Abba about leshen da ka siya min wanda Ummy tace dole sai nayi mashi riga da zani…”.

“Ehhh…”.

“Ina son ne in kaiwa mai dinkin Aunty ne yayi min express in amso a yau, ban iya barinshi a can, it’s expensive…”.

“Okay amma ki tabbata riga da zani kikayi, otherwise…”.

“Ummy will scold me…”.

A tare sukayi dariya, yace,

“Sai kin dawo ki kula ban da gudu… And about your car key lamido ya bani shi yana a bedroom dina…”.

“Lamido?”.

“Wanda ya daukoki daga asibiti…”.

“Da yake da sauran nike amfani shiyasa ban lura ba, idan ka dawo sai in amsa…”.

“Alright, bye…”.

“Bye…”.

Ta sauke ajiyar zuciya tareda mik’ewa ta soma taka rawa fuskarta dauke da murmushi tana hasashen yadda zata ganshi, cikin mintuna kadan ta gama shiri ta zura long hijab har kasa ta sauko kasa, Ummy ta dubeta da mamaki tace,

“Ina zakije?”.

Arfaat tace, “Wannan leshen ne zan kaiwa tailan Aunty yayi min, nayi wa Abba magana…”.

Ummy tace, “Ita kuma Rumaiserh fa, naga ita takeyi maki dinki…”.

Arfaat tace, “Idan naje zatayi min yawo da hankali ne kuma bazan barshi a can ba, it’s expensive…”.

Ummy kallonta take da mamaki tace,

“Expensive ko kuma kina son ne ki bada a maki bubu kamar yadda kika ce ba…”.

Arfaat tace, “It’s not that…”.

Ummy tace, “Anyway you can go, idan kikaje kikayi abun da kike so ina zaune zaki sameshi inci maki mutunci… Allah ya kiyaye hanya kai…”.

Arfaat tace, “Amin…”.

Tun akan hanya tana driving tana fatan idan taje kadda ta samu tailan saboda ta samu lokacin kallon Abdurrahman, tana shawo titin ta baza idanu tana fatan hangoshi saidai har tayi parking bata ganshi ba, inda suke a jiya wayam babu kowa, ta turo baki tana fatan kadda ta samu Najeeb, ta dauki leather ta kutsa kai cikin katon shagon da salaam akan lips dinta, tace,

“Najeeb fa?”.

Najeeb yace, “Barka da zuwa, hajiya…”.

Arfaat tace, “Dama dinki na ne na kawo amma express nike so, zan tsaya ka gama in tafi dashi, kadda ka damu zan biya ko nawa ne…”.

Najeeb yace, “Okay…”.

Arfaat ta mik’a mashi leather din tace,

“Here you go, ka saka min digit dinka, zan tura maka style din da zakayi min via WhatsApp…”.

Najeeb ya amsa ya saka numbarsa sannan ya maida mata yace,

“About the measurement?”.

Arfaat tace, “Zan had’a maka dashi… Riga da zani ne… And please take your time kayi min dinkin yayi kyau, zan jira a mota ne, idan ka gama sai kayi min magana gata can bakar Jeep din can… About the payment, bani da cashi saidai inyi maka transfer sai ka tura min aza…”.

Najeeb yace, “Sure…”.

Arfaat ta fita tana tafiya tana kallon wajen tana fatan ta ganshi, ta bud’e motar ta shiga ta zubawa wajen idanu, saida ta jima sannan tayi sending wa Najeeb abun, ta jima sosai a wajen amma babu Abdurrahman babu alamarsa, ganin Najeeb ya kusa gama dinkin kuma idan ya ba ta bata da dalilin k’ara dawowa, ta murza key ta danna motar akan titi ta dauki hanyar gida, tayi parking motar a parking spot ta fito ta wuce ciki tayi salaam taji shiru, ta shiga ciki ta tadda babu kowa a parlor, ta kutsa kai kitchen inda ta samu Ummy, Ummy ta dubeta da mamaki tace,

“Ina dinkin?”.

Arfaat tace, “Gobe in shaa Allah zanje in amso…”.

Ummy ta tab’e baki tace,

“Idan ma bubun kika saka aka yi maki kike b’oyo zaki hadu dani, you will see the other side of me…”.

Arfaat tace, “Ba haka bane…”.

Ta juya ta haye sama, ta fad’a akan gado tayi lamo tana jin babu dadi da bata ganshi, she’s wondering where he is and what he is doing, throughout the rest of the day tayi ne kamar marar lafiya….

Washegari wajen karfe goma, Ummy ta tusata a gaba, tace,

“Ki tashi kije ki amso dinkin…”.

Arfaat tace, “Da saida anjima zanje…”.

Ummy tayi mata wani mugun kallo tace,

“Ni kuma yanzu nace kije ki amso…”.

Saida Arfaat ta tura baki sannan ta mik’e ta wuce sama jim kadan ta sauko tana sanye arebian gown purple tayi rolling veil, ta janyoshi ta rufe daga bakinta zuwa saman hancinta, tana driving tana fatan idan taje ta ganshi amma wayam ta hango wajen babu shi babu alamarsa, wucewa tayi da motar ta zagayo amma still ba ya nan, saida tayi zagaye sau ukku sannan tayi parking motar ta d’aura kanta akan sterry fuskarta dauke da damuwa, cikin ranta tace,

“I’m love with you Abdurrahman… Where are you… What are you doing… Na rok’eka kazo gareni…”.

Wani abu ne ya fado mata a rai, ta ware idanu tace,

“Na boni, what idan suka cutar dashi, koda yake ba soyayya muke ba, I’m just crushing, one side love and they have nothing to do with it…”.

Saida ta shafe mintuna ashirin a mota ba tareda ta fita ba, Ummy ce ta ajiye mata call, daga daya bangaren tace,

“Arfaat… Meyy kike jirane har yanzu baki dawo ba…”.

Arfaat ta ware idanu, da sauri tace,

“Gani nan akan hanya…”.

Ta kira numbar Najeeb yana picking tace,

“Arfaat ce, ka kawo min dinkin gani nan a bakin shagonku, zakaga motata fara…”.

Babu jimawa Najeeb ya kawo mata dinkin, yace,

“Jiya lokacin da naga gama har kin tafi…”.

Arfaat tace, “Something came up shiyasa na wuce…”.

Ta zaro dinkin tana dubawa tace,

“Wow, sunyi kyau…”.

Najeeb yace, “Amma…”.

Arfaat tace, “Kadda ka damu ka dauka ina sane…”.

Najeeb yace, “Na gode sosai, Allah ya k’ara arziki, sai kin kawo wani…”.

Arfaat tace, “Sure…”.

Saida ta kalli wajen sannan ta dannawa motar key ta dauki hanyar gida, tana barin wajen, Abdurrahman ya k’araso yana tafiya a kafa ya shiga wani shagon aski, ta ajiye leather din tace,

“Gashi na amso…”.

Ummy ta warware dinkin tana gani tace,

“Allah ya soki… Meyy yasa kika dade?”.

Arfaat tace, “Na b’ata lokaci ne akan hanya, Abba yace kadda inyi gudu…”.

Ummy tace, “Ohhh really?”.

Arfaat tace, “Haka yace…”.

Ta mik’e ta wuce sama, karfe ukku na rana, Sultan da Nabila suka dawo daga makaranta, karfe hudu ta gama shiri cikin kayan Islamiyya ta sauko kasa, Sultan da Nabila suna jiranta a mota, ta bud’e backseat ta shiga, direba yaja motar yana saukesu ya juyo da motar, karfe shidda yaje ya daukosu, Ita da besties dinta Rufaida da Aseeyerh sun jero suna tafiya suna hira, tayi masu bankwana ta nufi inda motar take ta bud’e backseat ta shiga direba yaja motar….

The following day tunda ta tashi take tunanin abun da zata fad’awa Ummy ta barta ta fita, saida ta gama rehearsal sannan ta nufi bedroom dinta, ta kutsa kai da salaam akan lips dinta, Ummy ta d’ago saying,

“Wa alaikissalaam…”.

Arfaat tayi shiru tana raba idanu, saida Ummy ta k’are mata kallo sannan tace,

“Miye?”.

Arfaat tace, “Dama ina so ne inje gidansu Fadila tunda yau alhamis babu Islamiyya, bayan mun gama exam tazo amma ni banje ba…”.

Ummy tace, “Some other day, yau zan aikeku kasuwa tareda su Sultan…”.

Arfaat ta juya ta koma bedroom dinta tana murmushi, dama burinta shine ta fita ko zata ganshi, Sultan da Nabila suna dawowa daga school suka ci abinci sukayi wanka suka shirya, Ummy ta basu aiken, a Mercedes dinta suka tafi, ita da Sultan suna a frontseat yayinda Nabila take a backseat, hanyar inda aka aikesu da kuma shagon dinkin are totally opposite, ba hanya daya suke ba amma saida tayi zagaye dasu….

Sultan ya dubeta da mamaki yace,

“Angel ba hanyar bace…”.

Arfaat ta harareshi saying,

“Naga dai motata ce, duk hanyar da naga dama ita zan bi…”.

Saida tayi zagaye tabi ta wajen shagon amma wajen wayam yake babu shi babu alamarsa, da zasu dawo saida ta k’ara zagaye amma still bata ganshi ba, kuma a lokacin yana a shagon dinkinsu Najeeb….

Arfaat ta turo baki fuskarta dauke da damuwa, Sultan yace,

“Angel na fad’a maki you are weird…”.

Nabila tace, “Yes she’s weird…”.

Arfaat tayi banza dasu ta kyale tana driving motar, suna komawa gida ta wuce bedroom dinta tayi tagumi, a hankali tace,

“Yaushe zan k’ara ganinshi… A Ina zan samu koda hotonshi ne?”.

Da sauri tace, “Bla*ck box…”.

Ta ware idanu tace,

“Gosh… Na cika kallace-kallace… Tabbas I’m weird…”.

Throughout washegari jumuah bata fita, the following day tunda safe suka shirya direba yayi dropping dinsu a Islamiyya, bayan an tadosu, direba yace,

“Ma’am zan amshi sako bayan Atc zanbi ta can…”.

Arfaat tace, “Okay…”.

Yana shawo titin shararrar pipe ta juya tana kallon waje, kamar ance ta d’ago tana dagowa ta hangoshi zaune akan bench yana motsi da lips dinsa da murmushi akan fuskarsa, da sauri tace,

“Ka tsaida motar…”.

Da sauri direba ya gangara da motar yayi parking a gefen titi, da mamaki suke kallonta, Sultan yace,

“What?”.

Arfaat tayi firgigit tace,

“Kabeer kaje ka siyo min biscuits a wancen shagon…”.

Ta zaro kudi daga jikkarta ta mik’a mashi ya amsa ya b’alle murfin motar ya fita, ta maida kallonta inda Abdurrahman yake tana kallonshi tana murmushi, babu jimawa direba ya dawo ya mik’a biscuits din yace,

“Ga shi…”.

Arfaat ta juyo da sauri tace,

“What?”.

Direba yace, “Na siyo…”.

Arfaat tace, “Amma kamar nace maka biscuits din guda ukku zaka siyo tareda bottle water…”.

Direba yace, “An gama ranki ya d’ad’e…”.

Ya juya ya koma shagon cikin ranta tace,

“Why did he return so quickly? He don’t have to walk so fast…”.

Sultan yace, “But Arfaat you didn’t mention that?”.

Arfaat ba tareda ta juya ba tace,

“Na manta ne…”.

Sultan yace, “Why do I feel that da gangan kikayi?”.

Arfaat tace, “That’s your own cup of tea…”.

Babu jimawa direba ya dawo ya mik’a mata leather din ta amsa tareda dafe kai tace,

“Gosh sorry zan k’ara maidaka ga dubu biyu kaje ka amsho min lemo…”.

Direba ya amsa ya juya ya koma, Sultan kallonta yake cike da mamaki baki bud’e idanu waje, yace,

“Sis Arfaat you are weird…”.

Arfaat tace, “And that does not concern you… Naga tsakanina dashi ne…”.

Sultan yace, “Amma kina bashi wahala ne…”.

Arfaat yace, “I don’t have time for you…”.

Ta juya ta cigaba da kallonsa tana murmushi, her heart went blank, ji take babu abun da yake damunta, the more take kallonsa the more take kara jinta a cikin farin ciki, she loves him indefinitely….

Direba ne ya dawo ya mik’a mata leather tareda change din, yace,

“Ga shi…”.

Ta amsa tace,

“A’a, ka rik’e canjin…”.

Direba yace, “Na gode…”.

Arfaat tace, “Don’t worry and kayi hakuri na wahalar da kai…”.

Direba yace, “Babu komai hajiya ai girmanki ne…”.

Tace, “Godiya nike ina k’anwarka wannan wadda muka tab’a dropping…”.

“Tana nan…”.

“Ai bata da zumunci, idan na manta ka tuna min zan baka sako kakai mata…”.

” Godiya take…”.

Tana ji tana gani yaja motar, tun tana juyowa tana hangoshi har suka b’ace mashi….

 

 

 

Littafin SUNE SUKA JANYO MIN na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan naira dari biyar kacal 500, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana

*For those of you asking yadda zasu biya kudin, zaku biya ne ta hanyar tura hoton Katin MTN via WhatsApp 09169472057, ko kuma VTU/Transfer ta 09169472057, sai kuyi screenshot ku tura via WhatsApp 09169472057*

 

Hafsat Hisham ce 🥰😘🥰

Add Comment

Click here to post a comment