Takun Saka Hausa Novel Complete
TAKUN SAAƘA
*_Bilyn Abdull ce
_ZAFAFA BIYAR 2K22_
*_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al’umma. Ka haneni rubuta abinda zai cutar da wanina da ni kaina. ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan bayin ALLAH da suka bar duniya
_Masoya abokan tafiya ga ZAFAFANKU BIYAR sun sake dawowa a karo na biyar insha ALLAH
*Chapter one*
…………Sosai motocin ƴan sandan guda uku na farin kaya ke zuga uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai jiniya mai tsanani da zata iya tada hankalin duk wani mai tsoro. Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauka suke gefen hanya domin basu fili, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Sai dai kowa mamakinsa da tambayarsa shine (Mike faruwa haka?).
Basu da mai basu amsa, kamar yanda nima bani da amsar. Sai dai mu cigaba da binsu domin sanin mike faruwar? Baki ɗaya.
Renonta Zanyi Complete Hausa Novel
A lokacin da waɗancan motocin ke tsere-tseren gudu mai kama dana kai agaji ko ceton rayuwaka anan headquarters na ƴan sandan jihar a kusan hargitse take a wani yanki na cikinta, hargitsin nata kuma yanada tabbacin alaƙa da waɗan can motocin.
Kusan gaba ɗayan ma’aikatan department ɗin tsaye suke cirko-cirko a ɗakin na’urorin bincike cikin matuƙar taraddadi da ƙaulanin fargabar abinda ke faruwa. Yayinda kusan ma’aikata bakwai ke zaune sun duƙufa wajen sarrafa Computers ɗin cike da ƙwarewa da nuna matuƙar ƙwazo. Bakajin sautin komai sai na keyboards da ajiyar zuciyoyi.
“Sir mutumin nan yana da matuƙar wayo, bana tunanin zamu iya dakatar da shi da ga zuƙar kuɗaɗen nan fa a wannan karon ma”.
Ɗaya daga cikin masu sarrafa computers ɗin ya faɗa yana yarce uwar zufar daketa faman tsatstsafo masa a goshi, duk da ac dake aiki a ɗakin. Dafe kai wanda yake ma maganar yayi cikin matuƙar dagulewar tunani. Sai kuma ya ɗago a fusace yana kallonsa. Cikin tsawa ya daki desk ɗin gabansa yana kallonsu da idanunsa da ke jajur na ɓacin rai.
“Idan har kuka bari ya cimma burinsa a wannan karon kuma bazan yafe muku ba. Har sai yaushe ne zamu iya daƙile wannan tsageran ɗan ta’addan yaron dake ganin a kullum yafi ƙarfin hukuma?!!”.
Yanda yay maganar da bugar desk ɗin a tsawace ya saka da yawansu zabura. Wanda yay maganar yay saurin maida hankalinsa ga computer ɗin gabansa jikinsa na ɓari ya cigaba da sarrafata da sauri-sauri. Shima ɗayan dake gefensa tsawar ta rikitashi matuƙa, dan haka ya ƙara ƙaimi wajen sarrafa na’urar gabansa.
Ogan nasu ya cigaba da masifar data sake hargitsa sauran harma suka rasa nutsuwarsu wajen sarrafa na’urorin. Ɗif komai dake wajen ya tsaya, hakan ya jawo yin tsitt ɗin ɗakin lokaci guda. Gaba ɗayansu suka zubawa Computers ɗin ido a hargitse, dan sun san aikin gama ya gama kawai. kamar yanda ya saba cin nasara a kansu yauma ya sake ci……..
★
A ɓangaren motoci masu rera gudu bisa titi kuwa sun isa banki ne, inda suka iske mutane da duk ma’aikatan bank ɗin hankalinsu a tashe. Musamman ma shugaban bankin da yafi kowa birkicewa. Dan kuɗin da guy ɗin ya ɗiba ya tatsesune cikin asusun matar gwamna. Duk da dakatar da shi da aka samu nasarar yi ya zuƙi biliyoyin kuɗin da su kansu tsoron bayyanama duniya sukeyi saboda gudun abinda zaije ya dawo kuma.
Cikin ƙanƙanin lokaci jami’an nan na hukumar farin kaya da ƴan sanda sun gama zagaye bankin dan ana ƙyautata zaton wanda ya aikata laifin ko wani nashi yana cikin bankin har yanzun basuyi nisa ba.
An garƙame ko’ina da ina, duk wanda ke a ciki baida damar fita sai an bincikesa ciki da bai ɗinsa, musamman ma wayoyin hannu da bags.
Al’amarin tamkar rufa ido har aka gama bincike mutane aka koma kan ma’aikatan banki babu mai ko alamar aikata laifin. Zuwa yanzu kuma babban ɗa ga gwamna ya iso wajen tare da mahaifiyarsa matar gwamna ɗin da securitys ɗinta. Hakanne yasa wajen ƙarayin tsamari dan ta nuna tsananin ɓacin ranta na ƙarancin tsaro da bankunan ƙasarmu ke fama da shi. Inda kake tunanin ka ajiye kuɗinka ka koma kai barci mai daɗi a gidanka shine kuma ya zama gidauniyar wawaso na salon ɓarayi masu aiki da ilimi, ta tabbatar musu bazata yardaba, kodai kuɗinta su dawo cikin asusunta kokuma ta ɗauki tsatstsauran mataki akan bankin da ma’aikatan cikinsa. Wannan shine ya ƙara ɗaga hankalin duk wani ma’aikaci dake a reshen wannan banki.
Abu ya ƙara tsamari dan har C.P da kansa ya iso wajen tare da mataimakin gwamna da wasu manya-manyan ƙusoshin gwamnatin dan ɓarnace ta ɗunbin kuɗi wannan ɓarawo ya aikata wadda a ƙiyasi bama ya taɓa aikata kwatankwacin irinta ba a duk hatsabibancin da ya aikata, dan babu hukumar tsaron da babu sunansa a ƙasar matsayin mai-laifi saboda tsagerancinsa.
Takaici da baƙin cikin halin da ake ciki ne ya saka wani ɗan sanda yima mabaratan dake zaune a ɗan gefen bankin korar kare, dan yanda suka zauna zuru-zuru suna kallon duk wainar da ake toyawa ne yasa takaicinsu kamashi. Ya fatattakesu tare da bada umarnin idan sunƙi barin wajen a saka musu barkonon tsohuwa maisa hawaye.
Tuni suka fara haɗa kayansu suna barin wajen da sauri-sauri. Wani gurgu dake a tsohon kekensa (Wheelchair) ya murzata da ƙyar yana barin wajen, keken sai wani irin mugun ƙara yake saboda tsabar tsufan da yayi.
Cikin layi na uku dake akan titin da bankin yake ya shiga, sai da ya iso saitin wani kango makahon dake biye da shi a baya yana raira ƴar waƙarsa da laluben hanya da sanda yace, “Boss mun iso point”.
Wani irin ƙuuu! Yaja birki da keken, ya waiga bayansa ya kalli makahon da ya buɗe idanunsa ras yanzu, ɗauke kansa yay ya maida idanunsa ga ko’ina na layin babu kowa sai jefi-jefin yara dake wasa. Cak ya miƙe daka saman keke yana jan wani uban tsuki dasa hannu ya yaga daddauɗar rigir malun-malun ɗin shaddar jikinsa data fita hayyacinta saboda tsufa. Ya fincike rawanin daya aza akai da hular suma duk ya jefa saman keken.
Ba ƙaramin ɗunbin al’ajab da mamaki bane suka lulluɓe ni saboda ganin lafiyayyen mutum ƙyaƙyƙyawa tsaye akan ƙafafunsa, a yanayin jiki dai daka gansa kaga matashin mai tashen ƙuruciya da cikakkiyar lafiya, amma abin mamaki fuskarsa ta tsoffi ce, hasalima harda tarin furfura a saman kansa da sajensa zuwa gemu. Sosai raina ke cike da ɗunbin mamakin hakan, dan nidai ban taɓa gani ba tunda nake. Ace matashin saurayi da fuskar tsoffi…
Takun Saka Hausa Novel Complete
.Chapter two*
………Idanu sosai na ware domin ƙare masa kallo, sai dai isowar mashinan power bike guda biyar cikin layin ya rabamin hankali biyu, tuni makaho shima ya yaye kayan dattin jikinsa ya fito a lafiyayyensa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin wanda suke a saman mashinan ya faka nasa gabansa, ya sakko tare da sauke jakkar bayansa dake goye ya ciro takalma masu azabar ƙyau da sauran kayan bada kariya daga haɗari na mashin ɗin.
Cikin sauri wani ma ya sakko a nasa mashin ɗin ya warware kujera ya ajiye masa sai kace wani sarki.
cikin wani salo na isa da ƙasaita yakai zaune tamkar wanda ya samu kujerar falonsa, yanda yake abu cikin izza da isa ya sani yin zuru ina kallonsu.
Wanda yake riƙe da takalmin ya kai tsuggunne gabansa ya fara zare masa takalman robar dake ƙafar tasa irin na masu kiwo ɗin nan duk sun fashe saboda wahala. Takalman ya shiga saka masa, shi kuma ya amshi hular kwanon ya ɗaura a kansa tare da sauran kayan. Miƙe yay cike da ƙwarewar ƙasaita ya ɗare bisa mashin ɗin.
Makaho da wanda ya kawo masa mashin ɗin suma duk suka haye sauran mashinan da ƴan uwansu suke..
Kasancewar nashi mashin ɗinne a gaba ya sake daidaitashi. Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama, ƙaramin yatsansa ya fara miƙarwa alamar (ɗaya), ya ɗaga na kusa da shi (biyu), yana ɗaga na ƙarshe alamar (uku) suka saki wata irin sautin ƙara data gigita kusan mafi yawan jama’ar layin. Tuni mata suka shiga gudun afkawa cikin ɗakuna, masu ƙarfin hali naɗan leƙowa suga mike faruwa?.
Kasancewar layin da suke yana gab da bankin tuni saƙonsu ya isa kunnuwan jami’an tsaron dake zagaye da wajen. Har rige-rige jami’an tsaron keyi wajen hawa ababen hawansu, dan sunsan wannan singing ne na tabbatar da shiɗin na kusa da bankin.
Daga ɓangarensu kuwa a wani irin mugun gudu suka harbo mashinan suka fito daga cikin layin, hakan yayi dai-dai da gabatowar motocin jami’an tsaron kwanar layin suma. Isowar jami’an tsaron ya sakasu danna wani abu a jikin mashinan nasu tuni hayaƙi ya gauraye titin baki ɗaya suka harba mashinansu tamkar walƙiya.
ALLAH yaso a ƙaramin titi suke, da tabbas babu abinda zai hana haddasuwar gagarumin haɗari saboda yanda gaba ɗaya titin ya lulluɓe da hayaƙi, mai tahowa baya ganin mai tafiya.
Sai dai duk da wannan hayaƙi hakan bai hana mota ɗaya cikin motocin jami’an tsaron bin bayansu ba a guje suma. Kusan mintuna uku cikakku hayaƙin ya ɗauka kafin ya baje, zuwa lokacin tuni mashinan nan sun ɓace ɓat daga yankin ma baki ɗaya tamkar na aljanu.
Rai a ɓace sauran jami’an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. Masu ƙarfin hali ne ke ƙoƙarin tsintar ƙananun takardun dake yashe a ƙasa alamar masu power bike ne suka sakesu tare da hayaƙin. Abinda ke a jiki ya ƙara harzuƙasu, dan kamar yanda ya saba barin sunansa idan ya aikata laifi a wannan karonma hakane. Sunan nasa ne a jikin takardar tare da zanen fuskarsa ta tsoffi raɗam.
A zabure ɗaya daga cikin jami’an yace, “Kai! Wannan ai yana cikin al’amajiran dake a ƙofar bankin suna bara”.
“What!!?”
C.P ya faɗa a matuƙar zabure.
Manager da shima ɗaya daga cikin takardar ke hannunsa muryarsa a hargitse ya ce, “Tabbas wannan al’amajirin sati biyu da suka wuce na fara ganinsa a wajen nan. Amma dai wannan ya cika matsiyaci”.
Zafi da ƙunar da zukatansu suke musu ya hana kowa ƙara magana. A kuma dai-dai lokacin matar gwamna da yaronta suka iso wajen suma. Dan sun gaji da jiran tsammani a cikin banki. Jin cewar basu kamashiba yasa ɗanta ya fara masifa tamkar zai haɗiye harshensa. Hakama mataimakin gwamna ya tabbatar musu karsu wuce awanni ashirin da huɗu basu kamo hegen ba.
Daga haka kowa yabar wajen rai ɓace. Jami’an tsaron ma kowa ya koma inda ya fito domin ƙulla mai yuwuwa.
Jami’an farin kaya harsun kama hanyar barin wajen suma suka dawo, sakamakon kiran wayar oga kwata-kwata na hukumar tasu da ɗaya daga ciki yayi domin sanar masa halin da ake ciki. Shine ya basu umarnin komawa su duba inda wannan gagarumin ɓarawo ya fito bayan barinsa banki.
Sun shigo layin, inda suka iske mata da yara cike suna kallon kujera da kayayyakin da gurgu da makaho suka cire. Cikin mamaki suma suke duban kayayyakin, tare da ɗanyin tambayoyi ga mutanen wajen kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
Ɗaya daga cikin jami’an yakai duƙe yana ɗaga kayan dake bisa keken guragun. A mamakinsu sai ga facemask exactly da wadda ke jikin fuskar guy ɗin, kuma itace zane a jikin takardar da ya bar musu a titi.
Komai basuce ba, saboda basusan da mutanen da suke tare a wajenba dan ya zama shu’umi kuma. Suka tattare kayan kaf har sandar makaho suka bar wajen..
A lokacin da mashinan power bike ɗin can ke reren gudun tserewa wasu daga cikin ɗaliban babbar jami’ar jihar ke tururuwar fitowa domin neman ababen hawa da zasu maidasu gidajansu dan sun ƙare darasin karatu na wannan rana.
Matasan ƴammata uku dake ƙoƙarin tsalla titi cikin matuƙar gajiya da yunwa suka daka uban tsale domin komawa baya sakamakon gabatowar waɗanan mashina dake gudu tamkar su kaɗai ne a titin.
Ɗaya a cikinsu takai ƙasa sakamakon tuzguɗewa da takalmin ƙafarta yayi, ƙarar data ƙwalla ne ya maido mafi yawan hankalin mutane da idanunsu ke akan power bikes ɗin kansu. Ɗayar budurwar tai saurin kamo wadda ta faɗin tana ambaton kalmar “Subahanallahi Hafsat!”.
Ɗayar kuwa a wani irin harzuƙe ta wurga musu wani abu dake hannunta, cikin sa’a kuwa sai gashi ya manne saman jikkar ɗaya daga cikin masu power bike ɗin. Cikin zafin rai da tsiwa tai alamar harba bindiga da yatsunta biyu tana faɗin, “Ku tafi duk iya inda kuke buƙata a tafin hannuna kuke, ko ƴaƴan ubanwaye ku a ƙasar nan zakusha mamaki, dan sai nayi sanadin da hawa power bike zai gagareku insha ALLAH”.
Karaf wannan furuci na ƙyaƙyƙyawar matashiyar budurwa da shekarunta bazasu gaza sha takwas ba a kunnen ɗaya daga cikin jami’an ƴan sanda nan da suka biyo bayansu, sai dai dandazon ɗaliban daya rufe kusan rabin titin ya rage musu ƙaimin gudun da sukeyi suma domin son cimmasu. Sassauta gudun nasu ya basu damar jin furucin wannan matashiyar budurwa da tuni ta maida hankalinta ga ƴar uwarta data faɗi suna ƙoƙarin ɗagata tsaye dan da alama taji ciwo a ƙafarta ne.
Cikin sauri jami’in nan da yaji furicin budurwar ya dirgo a motarsu ya nufi wani mai taxi, magana sukai da babu mai jinsu, mai taxi ɗin ya miƙa masa key ɗin motar.
Sauran ɗalibai na ƙoƙarin tsaidama ƴammatan nan napep da basu shawarar su kai wadda ta faɗin asibiti dan da alama taji ciwo babba jami’in nan yazo gabansu ya faka taxi ɗin nan, batare da yin wani tunani ba suka taimakawa ƴar uwarsu ta shiga suma suka shiga.
Sai da suka fara tafiya ɗayar budurwar tace, “Kai gaskiya kosu waye akan mashinan nan sun cika tantirai, dole ne a dinga cewa ƴaƴan manyan ƙasarnan sai sun sha kayan haukansu suke hawa power bike sunama mutane hauka da shi a tituna kamar nasune su kaɗai. Yanzu dan ALLAH bayan ALLAH ya taƙaita wahala ai za’a iya rasa rai ta dalilinsu ko?”.
Wani banzan tsaki budurwar nan data jefa musu abu taja tana cije lip. A tsiwace tace, “Aiko a wannan karon ko duniya suka sha sun sako kansu a tarkon da iyayen nasu da suka saya musu mashinan sai sunyi dana sani insha ALLAHU. Dan wlhy har gidan ubanninsu sai nayi sanadin da za’a bisu ɗai-ɗai a kamo koda iyayensu zasu ɗauki mataki ne sai sunayensu ya ɓacin da bazasu sake gigin hawa power bike a cikin jama’a ba”.
.
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*TAKUN SAAƘA!!
*_Bilyn Abdull ce
_ZAFAFA BIYAR 2K22_
Chapter Three
………..Hafsat tai azamar ɗago kanta tana dubanta, duk da hawayen da ke sharara a kumatunta na azabar da take ji a ƙafarta, cikin ƙarfin halin ta ce, *_“Muhibbat!_* dan ALLAH karki sakamu a wahala da hatsabibancinki. Kwana huɗu kenan kacal da gama kashe wata wutar da kika kunno, indai dan nice karki damu, dama ALLAH ya ƙaddara sai naji ciwon nan koda bata sanadinsu ba, ina roƙonki kibarsu Ya Abubakar su huta da shegen tsokanarnan taki”.
Harara Muhibbat ta zubama Hafsat da murguɗa baki tana juya idanu, harta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi shiru saboda isowarsu cikin harabar asibitin.
Ko kaɗan jami’in nan baiso Muhibbat tayi shiru ba, amma kasancewar yasan aikinsa sai bai nuna hakanba, sai ma ƙoƙarin taimaka musu da yayi domin ganin an shiga da Hafsat taga likita akan lokaci.
Da taimakon jami’in aka duba ƙafar Hafsat da ta samu tsagewar ƙashi, Zahidah sai godiya take masa saboda ƙoƙarin da yaketa musu, dan sunso su kira gida ya hanasu. Hanawar tasa kuma ta bama Muhibbat haushi, dan a ganinta ya cika shishshigin tsiyane kawai, musamman daya kasance duk wani motsinta sai ta ritsa idanunsa akanta.
Tun tana hararsa a ƙasan ido da masa ƙunƙuni har takai ta fito fili tana dalla masa harara. Ganin dai ba daina kallon nata zaiyi ba a tsiwace ta ce, “Wai malam kallon fa? Dan ALLAH karka cinyeni a tsaye mana”.
Sosai yanda tai maganar ya bashi dariya, dan tsaf ya gama fahimtar itaɗin matsiwaciyace ta gaske. Sannan babu tsoro sam a cikin idanunta kona sisin kwabo. Komai baice mata ba, sai ma ɗauke kansa da yayi kawai gefe tamkar bai jita ba. Taja tsoki tana murguɗa baki da miƙewa tabar wajen.
Can gefe ta koma tana ƙoƙarin sarrafa wayarta cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci kiran da tayi ya shiga, sai da aka ɗaga sannan takai kunne tana faɗin, “Assalamu alaika Yaya”.
Amsa mata akai da ga can, kafinma ya gama rufe baki cikin shagwaɓa taci gaba da magana. “Yah Uthman muna hospital ne”.
A tsananin tsorace muryarsa ta bayyana, “Hospital Auta?! Waye bai da lafiya?”.
“Oh Yaya calm dawn, Hafsat ce taji ciwo a ƙafa amma da sauƙi, dan yanzu haka ma an gama mata gyaran sunce tsagewan ƙashine”.
“Ya ALLAH! Auta wai sai yaushe ne zakuyi hankali ku kam? Yanzu haka a wajen shegen rawan kan nan naku hakan ta faru?”.
“Na rantse Yaya bafa da gangan bane, wasu marasa kirki ne suka kusan turemu a power bike”.
“What?!. Power bike fa? Ku miya kaiku kan titin da masu power bike kebi!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace ne ya sata zabura, duk cikin yayun nata yafi kowa sauƙin hali bayan Yah Abubakar. Sai dai kuma idan ya rikice tafi tsoronsa fiye da kowa a cikinsu….. Cikin katse mata tunani yace, “Zan turo muku Ammar yanzun nan danni naje katsina ne..”
Yana gama faɗan hakan ya yanke wayar. Kasaƙe Muhibbat tayi tana kallon wayar, yayinda gefen zuciyarta ke ayyana mata neman mafita. A fili tace, “Tab Yah Ammar! Wlhy bazan bari ya samemu a asibitin nan ba wannan ɗan matsalar”. Da sauri tabar wajen zuwa inda jami’in nan mai amsa sunan driver-n taxi yake da Zahidah.
“Zahidah tunda sunce zasu iya sallamarmu gara mu wuce gida, dan na haɗa gurmi wlhy”.
Zahidah dake mata kallon mamaki tace, “Gurmi kuma! Nami to?”.
“Humm daga kiran Yah Uthman fa na faɗa masa shine wai zai turo mana Yah Ammar shi yana katsina. Ni kuma wlhy banason Yah Ammar yazo asibitin nan ya samemu saboda yafi gidan haya matsala kema kin sani”.
Kafin Zahidah dake dariya tace wani abu jami’in nan yay saurin cewa, “Ai sunma sallemu daman, inaga ku shiga ku fito da ita kawai mana”.
Harararsa Muhibbat tayi tana ɗaure fuska. “Ikon ALLAH sai kallo, wai ni kam bawan ALLAH ca’akai ka kula damu ne kokuwa? Taxi ɗinka muka hau ka kawomu inda muke buƙata, to sai mi kuma ya rage?”.
Murmushi yayi idanunsa a kanta, “Sai ku bani kuɗina ya rage ƙanwata”.
“Ya salam! Dan ALLAH kayi haƙuri bawan ALLAH. Wlhy gaba ɗaya mun shafa’a ne”. Zahidah ta faɗa tana laluben bag ɗinta.
“Karki damu ƴammata babu damuwa. Nasan kuna a rikicene ai. Amma ƙawar nan taki ya kamata ta rage tsiwa”.
Zahidah dake miƙa masa ɗari biyar tai dariya, “Kaga fita batunta ga kuɗinka mun gode sosai”.
“Ai karki damu riƙe kawai sai na kaiku inda zaku yanzu sai na amsa”.
“Malam gara dai ka amshi kudinka kai gaba, dan bazamu sake shiga motarkaba ɗan sarkin shiga sharo ba shanu”. Muhibbat ta faɗa tana hararsa.
Saurin toshe bakinta Zahidah tayi itama tana hararta, “Wai nikam Hibbat kodai wadda tai miki wankan jego bata gasa bakin nan bane da baya barin kowa. Ina laifin bawan ALLAHn nan, kigafa ƙoƙarin da yay mana akan Hafsat”.
Hibbat ta buge hannun Zahidah da haushi, “To dan kuma ya taimakemu sai ya ishemu da shishshigin jaraba. ALLAH ni banason shishshigi da ƙwala kai a faranti irin na wasu mazan”.
Tana gama faɗa tai shigewarta ɗakin da Hafsat take. Duk binta sukai da kallo, kafin Zahidah ta maido kallonta ga jami’in. “Ayya dan ALLAH kai haƙuri. Ita haka take sam ba’a gane kanta tamkar mai aljanu”.
Ƙaramar dariya yayi yana sosa tsakkiyar kansa da key ɗin taxi ɗin. Yace, “Kinga karki damu ni salon natama birgeni yakeyi, irin waɗanan sam ba’a cutarsu a duk inda suka shiga. Je kawai ki fito dasu na kaiku kafin a sake kirana ɗan shishshigi”.
A yanda ya ƙare maganar cikin langaɓe kai kalar tausayi yasa Zahidah ƙyalƙyalewa da dariya tana shiga ɗakin domin su fiddo da Hafsat..
Da ƙyar Muhibbat ta amince jami’in nan mai taxi ya ɗaukesu zai maida gida. Dan ko sai kumbura take a motar tana ƙananun ƙunƙuni alamar bataso hakan ba. Shi dai yakanyi murmushi lokaci-lokaci idan ya ɗago ya dubeta ta mirror yaga yanda take cika baki da iska tana harare-harare……..
Kamar yanda aka saba yau ɗinma tuni media ta ɗauka. Gidajen redio dana televisions harma da yanar gizo mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke. Dan lamarin wannan gagarumin ɓarawo ya daina bama mutane tsoro sai al’ajabi da mamaki. Kullum ji suke jami’an tsaro na farautarsa, mai makon ya tsorata ya ɓuya sai ƙarama gawurta yake a al’amuransa. Gashi babban abinda zai baka mamaki manya-manyan ƙusoshin ƙasar masu lasisin iya ɗaukar mataki yake bi yana yashewa da saka rayuwansu cikin tarkuna. Dan da wahala ya kafa maka ƙahon zuƙa daga ƙarshe baka koma ƙarƙashin binciken hukumar *EFCC🐦* ba, ko ka ƙare rayuwarka da ciwon paralysis saboda barazanarsa idan yay dirar mikiya aka kaddarorinka da kuɗaɗenka. Yanzu dai yanda ya yashe asusun matar gwamna bawai ya barta bane kenan. Duk da neman da ake masa ruwa a jallo cikin kwanaki ƙanƙani zai sake silalowa ya danƙara mata wani harbin mai zafi har sai ya kai rayuwarta ƙasa kwance zai barta.
Duk yanda ƴan jarida sukaso jin ta bakin jami’an tsaro da gidan gwamnati akan wannan al’amari abin ya gagara. Sun haƙura dole suna bada labarin iya abinda idanunsu suka gani da ɓarnar da wannan mutumi ya tafka a baya kafin wannan ɗin.
Yayinda a gefe kuma jama’ar gari suketa tofa nasu. Wasu najin daɗin abinda yakeyi ɗin dan bawai a satar kuɗin manyan ƙasar kawai ya tsaya ba, har ƴan fashi da suka addabi mutane da ƴan ta’adda yakan kama waɗanda har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda yake kaisu ya ɓoye. duk da kuwa shima ɗin mai laifi ne a bayyane, wasu ko na jifansa da ALLAH wadai saboda suna ganin bashi da maraba da ƴan ta’addar da yake kamawa ai. Yayinda ƴan kanzagi ke zaman rubuta shaci faɗi su yaɗa a kafafen yanar gizo game da shi da ayyukansa.
[…] Takun Saka Hausa Novel Complete […]