Littafan Hausa Novels

Renonta Zanyi Complete Hausa Novel

Renonta Zanyi Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Renonta Zanyi Complete Hausa Novel
Bismillahir Rahmanir Rahim,in The Name of Allah,The Most Beneficent,the most mercifull praise be to Allah Lord of The Words,…Assalamu Alaikum Our Follow Fans,We are Starting our New Book,We Ask Allah Subhanahu wata’ala to guide Us Throught And Make it Succussful Till The End Ameen ya Allah*

“` Wannan lbrin Is a Fiction Story Kirkirarre ne Daga Fasaharmu,Juyamana lbri ko Sarrafashi ta Wata Siga,Bada Izininmu ba Toh Hukuma ce Zata Rabamu Insha Allahu“`

*BABI NA D’AYA*

*KADUNA*

_Area:Anguwan Rimi Gra_

Misalin karfe 9:30pm Daidai na Daran Ranar Asabar,ya baro Office dinsa,Direbansa Garzali ne ke Jansa Cikin Bakar Motarsa Bugatti.

Hon ya Zuba akofar Tamkamemen Get din gidan nashi Mai kama da Aljannar Duniya,Megadinsa Habu ya Rugo da Gudu yazo ya Wangalemusu get Domin yasan Yallabai ne ya Dawo Adaidai Wannan Lokacin.

Bintoto Hausa Novel Complete

Lokacin da Motar Ta Sulala parking Space kafin Tagama Daidaita Zama Sai ga Wasu kyakyawan Yara Guda Biyu mace Da Namiji Wadanda Ashekaru bazasu Haura Shekara goma ba Tsawonsu Daya Kuma kamaninsu Daya,sai dai mace Tafi Jiki da Kuma Tsukakkiyar Fuska yayinda Namiji yake Siriri Ammh Fuskarsa nada Fadi,Farare Tas kamar Ka Taba Jini ya Fito akallon Farko zaka musu ka Fahimci yaran yan gayu ne na Karshe Kodaga ganin yanayin Kayan Kantin Dake Jikinsu Riga da Wando da Kuma yanayin Fatarasu na Jin Dadi ne.

Da gudu suka isa jikin Motar Suka Bude Bangaren Baya Suna Fadin”Wlcm Daddy…”Atare na Kallesu na sake sai alokacin Naga Dimple dinsu ya Lotsa Agefen Kumatunsu Lokaci Daya Yaran masu kama da Juna Sosai Inaga ma yan”biyu ne,Bangama Mamaki ba Sai da Naga Wani Cute and Handsome Ya Fito Daga cikin Motar yana Sanye da American Suit masu Ruwan Toka ya Matse Wuyansa Da Tie,Fuskarsa Tana bayyana Tsantsan Farincikin Dayake Ciki Naganin Kyakyawan Yaransa dayake Alfahari dasu

Rumgumesu yayi yana Shafa kansu yana Fadin”Thank u my Childreen…”Yake Fada Shima Duka Kumatunsa na Lotsawa,aShe anan yaran Suka Dibe Tsantsan kyau da Kuma Kyan Jiki,Dogone kakkarfan Namiji ne mai Tsawo da jiki da Fadin Kirji,Dan Kimanin Shekara 43 aduniya ammh kuma Bazaka iya Kiramasa Wadanan Shekarun ba Saboda Yadda ya Mori Jiki da kyan Fuska Ba Fari bane Tas,Ammh Kuma Bazamu Sanyashi alayin Bakake ba,Fatarsa Tafi Kama da yan Maroco,Saboda Murjewa da jin Dadi,doguwar Fuska gareshi mai Dauke da dogon Hancinsa da Kuma Zagayayyen Bakinsa wanda Wani Bakin Saje yama Wajen Kwanya gwanin Bam Sha”awa yana da Daradaran ido masu Dauke da Wasu Sirrika,ya mallaki Zara zara Gashin Ido Tamkar yana kari,sai Giras sa Dake Cike da gashi Kamar Wani Mace.

*ALHAJI TAHIR MANSUR DA’N BATTA* Kenan babban Manaja ne Dake kula da kamfanin *IBRAHIMĀ  KWATANO AND SONS LIMITED* Kuma Babban D”a Awajen Hakimin Dambatta Wato Alhaji Mansur Danbatta,Kuma miji ga *FARIDA IBRAHIM KWATANO* Kuma Uba ga *BASSAM,BASMA,NAILA…* Cikakken Jarumin Namiji mai Hakuri Hade Da Zati Da Haiba Miskilin Namiji Wanda bai maida Rayuwar Duniya da Abunda Ke Cikinta ado ba,wanda ake Alfahari dashi bayan iyayenshi Harta da Garinsa Danbatta Suna Alfahari da samu D”a Irin Tahir daya Fito Daga Ahalinsu

Zumbura baki Basma Tayi Tana Fadin”Daddy ina Mami…? hararanta Bassam yayi kafin yace”Eh ina Mami..? Kin manta dazu Munkirata da wayar *ANTY MUFEEDA* Tace mana ba yau Zata Dawo ba..”Tura baki Basma Tayi kamar Zatayi Kuka Tahir Dake Tsaye yana kallonsu Wani Takaichi yacikamai Ciki Jin Farida yau ma bazata Dawo ba,Hannun Basma yakama yana Fadin”Bassam Karbomin briefcase Dina Hannun garzali muje ciki..”da Hanzari Bassam yakarba Jakar Hannun Garzali yabi bayan Daddy Wanda ke Rike da Hannun Basma yana lallashinta don Ita Haka Allah yayi ta akwai Kulafacin Uwa ammh ba domin Haka ba yadda Farida ke Banzatar da Mijinta da ya”yanta yaci Ace Basma Tadaina damuwa da Rashinta don ba yau Ake ba.

Suna Shiga Cikin Kayatattacen Falon Kukan Naila yafara Musu Maraba Inda Take goye bayan Mufeeda wacce Ke Ta Faman Zagaye Falon Da Ita tana Faman Jijjigata ammh Taki yin Shuru,Cike da Tsausayi da Takaichi Tahir ke Bin Mufeeda da kallo Wacce Tajige da Zufa Duk da Sanyin Ac dake Falon Sakamon Naila Irin yaran nan Masu Kiba kamar Kajin Agric,ayayinda Ita Kuma Mufeeda Take Doguwa Siriirya kamar Ta karye saboda Rashin Nama,yarinyar sai Rinjayarta Take kamar zasu Fadi,daga gani Tafi karfinta, gata yarinya karama Domin Ashekaru bazata Haura Shekara 16 ba,Doguwar Fuska gareta mai Hade da Hancinta Shiba gajere ba,Kuma ba Dogo ba,Mufeeda baza ka Sakata Cikin Jerin kyakyawan Mata ba sai dai Tsaka tsaki.

Tana ganin Sun Shigo Tayi Azaman Dukawa Tana Fadin”Sannu da Zuwa Daddy…”Cikin Siririyar Muryanta Mai Cike da Yarinta,Amsawa yayi yana karisawa gareta bayan ya saki Hannun basma yana Fadin”Mufee,Meya samu Naila ne Take Ta Kuka Haka..? Yafada yana Mika mata Hannu Alamar Ta Kwantomai Naila din.

Batayi gaddama ba Ta Kwantota tana Mikamai ita Wacce Fuskarta Ta Hade da Majina da Hawaye,Ya karbeta yana Kallon Mufeeda dake Fadin”Wlh bansani ba Daddy,Tundazu ta Fara Kuka,na zata yunwa ne,sai na Hadamata Madara na bata taki sha,sai kuka take ganin Haka sai iya ta amasheta nan ma Taki yin Shuru Sai Kuka take tana Kiran Sunan Mamanita…”Tafada itama kamar Tayi kukan.

Mirmishi Tahir yayi yana Rimgume Naila wacce ke ajiyar Zuciya ta Kwanta Luf akan Kafadarshi,Kallonsu Bassam yayi kafin yace”Kunci Abinci..? Suka gyada kai alamun Eh,bai kara mgana ba ya Wuce ya Fara Haura Steps yana Dauke Da Naila kafin ya tsaya ya waigo yana Fadin”Oya kuje ku kwanta sai da safe..”Yafada yana Tamke Fuska Sum Sum Bassam da Basma kowanne ya Nufi Dakinsa yana Bata Fuska yayinda Da Mufeeda Tayi Tsaye tana kallonshi Ido ya sakarmata Fuska ba Walwala yace”Tsayuwar me kikeyi ke kuma..? Jikin Mufeeda na Rawa Tace”Ba…bakomai Dama dama…”Tafada tana Sosa kai Ware idonshi yayi kafin yace”menene..? Akwai Matsala ne..?

Kanta na kasa tace”Dama zanceĀ  ne Daddy baka ci Abinci ba gashi chan iya taga jera maka akan Dinning…”Mirmishi ya saki kafin yace”Karki Damu bana jin yunwa,ki koma daki ki kwanta..”Kallonsa Tayi kamar Zatayi mgana sai ta Fasa ganin yadda ya Sakamata ido,jiki asanyaye ta juya tana Fadin”Sai da Safe Daddy…”Alebensa ya Karba da Fadin”Allah tashemu lafiya.,yafada yana kallonta Tana Tafiya kamar Zata Fadi Cikin Sanyinta ta Shige dakinta,.

Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya juya yana Dauke da Naila,Ya Karisa Haura Step ya Bude Kofar Farko Mai Dauke da Kayattacen Royal bed Wanda yaji Shimfidun Alfarma gwanin ban Sha’awa Dakin bashi da Yawan Tarkace sai Wani Cafet Wanda ya mamaye Dakin gabadaya mai Taushi yana Fitar da Kyalli Gwanin Ban Sha”awa sai Makeken Wardrope maiĀ  Cinye Rabin Dakin,sai Dreesing Mirror kusa da Kofar Tiolet.

Kai Tsaye ya Karisa gaban Gadon sai da ya Haura Tsakiyar gadon Kana ya Kwantar da Nihal Wacce Barci ya Kwasheta Tana Sauke Ajiyar Zuciya Jin ya Sauketa,Hannu ya saka yana Shafa Goshinta Ahankali alamar lallashi nan da nan Ta Koma barci Saukowa Yayi Daga Kan gadon yana Sauke Ajiyar Zuciya kafin ya Cire Coat din Dake Jikinsa,Ya Rataye Kan Wani Dogon Abu Alamar na Rataye kayane,Towel ya Dauka ya Bude Kofar Tiolet ya Fada da Addu”a Dauke Cikin Abakinsa

Akallah ya Ashafe Tsawon Minti Talatin Kafin ya Fito Daga Tiolet,kugunsa Daure da Wani Babban Towel sai Kansa yana Rike da Karami yana Goge Ruwan Dake Diga asaman kanshi kai Tsaye Wardrope din Dake dakin ya Nufa ya sanya Hannu ya Bude Kayane Jere Bisa Hanger Iya Kallanka Mallam,gefen American SuitĀ  bakake da masu Ruwan Toka,Dabam gasunan Ajere na Kowani Kamfani sai Wanda ya Zaba zai saka kama daga DKNY,Tommy,hilfiger,Armani,louls,button,Doke,and Gabbana,Bersace,hakama bangaren Manyan kaya Tazarce Kama daga Shaddodi,gezner,yadika Masu Kyau da Tsada Suma bangarensu Dabam Haka bangaren Shirt da Jeans Suma Waje Gudane,bangaren Kayan Shan Iska Irinsu Short Niker Da Riga mai Gajeren Hannu Suma Suna Waje na Dabam sai Daga Kasa bangaren Kayan barci ne gasunan kala kala masu Taushi Da Tsari.

Cikin kayan Barci nashi Pjm ya Dauko Riga da Wando Masu Ruwan Toka Ruwa Na Diga Daga jikinsa ya Zura Kayan,Ammh Rabin Hankalinsa na kan Naila dake Barci,Baro Gaban Wardrope din yayi ya isa gaban Madubi ya Dauki Wani Turare Spry ya Fesa kafin ya Mtsa Chan Gefe Inda Wata Katuwar Darduma Ke Shimfide ya Tsaya Shuru kafin ya Daidaita Natsuwarsa ya Tada Sallah,

Tsawon Wasu Mintina ya idar da Sallar Shafa”i da Wuturi ya Dade yana Addu”a Kafin Ya mike Wata Yunwa na Kwakulan Cikinsa In Har Bazai Manta ba,Rabonsa da Abinci Mai lafiya da Kwari Tun Jiya Da Daddare kafin ya Dawo Gida Ishaq ya matsa masa Suka biya ta gidansa Sukaci Abinci Toh bayan Shi banda Ruwan Coffea bai kara saka Wani Abu mai Nauyi abakinsa ba,Cikinsa ya Shafa yana Tuna Kalaman Mufeeda yarinyar Tana bashi Mamaki gata Karama da Ita ammh Tafi Farida sanin Halayyarshi Ta Kuma Fita Karantar yanayinsa..,wata Zuciya tace Toh Ita Ke Zaune dakai Farida Yawon Biki da Suna da Zuwa Gidan Kawaye Bai barta ta Zauna dakai ba Balle ta Karanci Waye kai Tahir

Kansa ya Shafa yana Sauke Numfashi kafin ya Nufi Karamin Fridge dinsa Dake gefen Gado yazauna kafin ya Bude ya Ciro Madarar Hollandia Hade da Kofi Silba wani Karami mai kyau ya Bude ya Tsiyaya,Ya Shanye Duka Kafin ya sake Cikawa ya Kafa kai ya Shanye yana Ajiyar Zuciya mai da Komai yayi Cikin Karamin Fridge din Kafin ya Dora Kafafunsa Duka biyu kan Gadon Yana Kuma Jingina bayansa da Gado,ganin kamar Sanyin Dakin yama Naila Yawa ne yasa ya Dauki Remote din Ac ya Rageta yana Kuma Kokarin gyarama Naila Kwanciya Aranshi yana Tunanin Farida Wata Irin Uwa ce.

Haushin Hakane yasa Ya Mika Hannu ya Dauki Wayarsa Wacce Da Zai Shiga Wanka ya Ijiyeta akan Side Drower,Cikin Lokaci Kadan ya Lulubo Nombarta Wacce Yayi Sarving dinta da *WIFEY*, yayi Shuru yana Bin Wayar da kallo kafin ya cije baki ya Latsa mata Kira yana kallon Agogon Bangon Dakin 10 ta Wuce,wayar ta Shiga Haka Ta Dinga Ringing har Ta Katse Bata Daga ba,bai Hakura ba ya sake Kiranta Nan Ma har ta Karishi Ringing ta Katse bata Daga ba,Tsaki yaja ya kife wayar Gefensa Kafin ya Dauko Karamin Qur’anin Dake kan Side din Drower din gadon ya Bude Suratul Maryam Inda ya Tsaya Jiya Da Daddare Kafin ya Kwanta Domin ya Riga ya Zamemai Jiki baya iya Barci sai ya Karanta al”qur”ani Shiyaasa baya Taba Kwana da Bacin Rai.

Yafara Karatun Kenan Ahankali Cikin Zazzakar Muryansa mai Cike da Amo da Sauti mai Dadin Sauraro Wayarsa ta Fara Kara Tana Neman Dauki sai da yakai Karshen Ayar Kana ya Dago da Kanshi ya Dauko Wayar ganin Sunan Wanda Ke Kirane yasa Yayi Mirmishin Dayafi Kuka Ciwo ya Daga Kiran Yana Fadin”Yanzu Farida Rayuwar da kika Daukanma Kanki mai Bullewa ce..?

Dagachan Bangaren Farida Dake Gefe Cikin Wani Kayataccen Hal Ana ta Dinner Wajen ya Kaure da Hayaniya Tare da Kidan Dj,Sanye Take da Doguwar Rigar Wani Ubansu Fefe les Wanda yaci Dinki mai kyau da Tsari kalan blue Head din kanta Kuma pick Fuska Taci Uban Makeup kamar Wata Amarya Doguwar mace ce Ammh ba Sosai ba,Fara ce, sosai sai Kuma Akwai Kyau da Dirin Mata gaba da baya Masha Allah,Baki ta Bude Zatayi mgana tana Yatsina Fuska Wanda Fararen Hakoranta Suka bayyana Tare da Hakorin Makkanta Yana Daukan Ido Wanda yake Karamata kyau.

Cikin Kosawa Tace”Toh Uban Korafi Ai ina ganin kiran ka Nasan Abun da Kakirani ka Fadamin kenan,Haba Tahir wai Yaushe ne Zaka Daina Kunyatani ne Gaban Kawayena..? Tafada Tana Hararan Gefen Wayar Kamar Tana kallonshi,Shuru yayi yna Kokariin Danne Bacin Ranshi kafin yace”Au kinfison Kada Ki Kunyata gaban Kaawayenki Ammh Kin Manta da Lahirarki da Abunda Kikeyi zai iya Kaiki Wuta Farida…? Baki ta Tura Kafin Tace”Na Shiga Uku Wai Don Allah Tahir me nakeyi Ne..koda yaushe mganar ka kenan Zan Shiga Wuta..”ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace”Yanzu Fisabillah Kwananki nawa bakinan Kin Saka Kafa Kin Fita kin Zubar da ya”yanki Da Mijinki da Gidanki Abun Takaichi Wai Da Sunan Bikin Kanwar Kawarki Farida Anya Kina Son Gamawa Da Duniya lafiya..?

Daure Fuska Tayi Kafin Tace”Ikon Allah,duk mai ya Jawo Wannan mganar..? Inace Su Bassam Sun Girma Suna da Wayon da Zasu Kula da kansu,…”Ya katseta da Fadin”Naila fa..? Kin ijiye mai Bata Nono ne..? Yamutsa Fuska Tayi kafin Tace”Ina Mufeeda..? Miye Amfaninta dama Don Ta Kula da Ita na Amince nama goggo Mgana Anemin ita,Mganar Abinci Kuma I know iya bata Wasa Komai Kuke Bukata Zata Girka Ta Baku ,Toh kuma Wht Else Tahir..?

Cikin Kulufuwa da Bakin Ciki yace”Nifa..Nace Ni Mijinki fa Farida Hakkina na Aure Wa kika Rataye ya bani,Iyan ko Kuwa Ita Mufeedan…? Yafada Cikin Son Kwantar da Fushinsa Duk da yakasance mai Hakuri.

Yar Dariya ta Saki kafin tace”ai dama na sani Duk Wannan Kumfar bakin naka Saboda Ban Dawo na sakarma Jiki kayi yarda kaga dama bako..? Wai Tahir na Tambayeka..? Bata bashi Ikon Mgana ba Ta Cigaba da Fadin”Kai baka gajiya da Sex ne,Narasa Wani Irin Miji Allah ya Hadani Dashi Haba Abu kamar Bambaran Masara Kaga Mallam Nifa ba Sex machine bane balle Ka Ringa Hawata Duk sanda Kaga Dama Ina laifin Sau Daya Asati,ga Kawaye nan Su Binta su Zeenat Su Smarty Ba Wacce Mijinta ya Kirata balle ya Takura mata sai ni Dayake Allah ya Hadani da Ustaz dan Jaraba Sai na Koma na Nanike a gindinka Tahir Duk Shekara kana Min Ciki ina Haihuwa Kamar Waata Akuya ko..? Toh Wlh Baka isa ba,Hakan bazata Taba Faruwa ba Don Allah kar ka sake Kirana Zan Dawo Tunda ba dauwama Zanyi Achan ba,Muna Wajen Dinner so gobe zamu kai Amarya Kano Dagachan Zan biya na kwana Awajensu Abba may be Sai Jibi zan Dawo…”

Daga Haka ta yanke Kiran Tana Hararan Wayar Kafin Ta saki Tsaki Tana Fadin”Fitinanne…”Wayar ta kashe Gabadaya Ta Wurgata Jaka kafin Takoma Wajen Kawayenta Wadanda Keta Kallonta Tundaga Nesa Suna Dariya

Tahir yaji Wani Abu na Tasomai Daga Kasan Ransa mai kama da Fushi Da Bacin Rai ammh yana Dannewa Wayar yabi da Kallo kafin ya Sauketa yana Sakin Ajiyar Zuciya,yana Kokarin bama kanshi Hakuri,Ammh Dole ne gobe yayi sammako yaje Kauye wajen Goggo ya sanar da Ita an Kawo Limit din Daya Gaji da Zama da Farida Saboda Haka In bata Amince ya Saketa ba Toh Dole Ta Yarjemai ya Kara Aure,Domin Shi ba Dutse bane lafiyayyan Namiji ne mai Bukatar Kulawar Mace Wanda Keson Ya”yan sa Fiye Da Kansa,yana Bukatar Wacce Zata Kula da Duka bukatunsa dana ya”yansa Wacce Take Daraja Aure ba Sakarya Irin Farida ba,wacce In Har ya Lissafa Daidai Wlh Tafi Wata biyar Rabon Data Hada shimfida Dashi,ko bayan Haihuwan Naila bai Wuce Sau Uku Suka Hadu ba.

Ijiye Qur”anin yayi yana gyara Kwanciyarsa Hannu ya saka ya Kashe Hasken Dakin Kafin ya Kunna Dumlight,blanket yaja Ya Rufe kafafunsa Zuwa Kugunsa Inda ya Hada da Naila ya Rufe Mata Rabin Jiki kafin ya maida Kanshi Bisa Filo yana Nanata Dalilin Goggo na Banza Data Dogara dashi Ta Hanashi Kara Aure,Wai da Cewa yana Aiki karkashim Mahaifinta Shi ya Rikeshi Kome ya Zama Shine Sila,Shi kuma Wannam bai Dameshi ba Tunda Son da Iyayen ke mata yasa Suka kasa Tsawarta mata ,Shikan Wannan Karon ba Gudu baja da baya Koda Kuwa hakan zai saka Alhaji Ibrahim Mahaifim Farida ya Yanke Harkan Nemanshi yaji ya yarda Arziki na Allah ammh In yafada Halaka fa..? Ba wanda Zai Zargi Farida Illah Shi da Zai Shiga Cikin Duniyar Nadama na Har Abada.

Da wannan Tunanin yayi Addu”ar Barci ya Shafa Kafin ya Shafama Naila,Hannuwansa ya Tallafa akirjinsa kafin ya Runtse Ido Yana Fatan Barci ya Kwasheshi bayason Tuna Wata Aba Farida..

2 Comments

Click here to post a comment