Littafan Hausa Novels

Matar Lameer Hausa Novel Complete

Matar Lameer Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MATAR LAMEER*

 

Miqewa tayi da sauri ta daga kanta tana kallon me shigowar ya tafa hannu tare da tuntsirewa da dariya yace “kin dauka wannan raggon mijin nakine ko? Nifa ina mamakin yanda mace kamarki zaki tsaya kina auren wannan sullutun mutumin da baya iya biya miki buqatarki itafa mace tafi kowa yanci kuma tanada zabin daya dace da ita namiji dai har namiji a riga Amma a gado babu fuss sai jinkai da izza a waje, koda yake hakanma ni yayimin ya auromin mata babu ko sisina nayi mata ban ruwa kuma ta cikamin aljihuna da kudi hhhhhhhh!”
Suka kwashe da dariya ita kuma ta tsuke fuska tace “amma kasan nace maka kada kazo gdannan yau yayanka zai dawo kuma kasan cewa banason ya fahimci akwai alaqa tsakaninmu mu zauna a matsayin abokan gaba haka nakeso shirin ya kasance.

Muwaddat Hausa Novel Complete

Dara² idanunsa ya sauke akan me tallan furar da ya tsayar ta dago da hardaddiyar hausarta tace “Kado ka hiya niman magana wallah in zaka shiya jaka hudu ka shiya in bakka shiya kuma ka bareshi dama kai ka cika son araha toni komi nawa mi tsadane kajima in hwadi maka”
Yanda take mgnr ne yayi bala’in bawa pillot Lameer dariya yayi murmushi yace “komanki me tsadane nikuwa idan babu damuwa mu buga wani wasa mana ki fadamin komai kikeso zanyi miki zan aureki kawai dan ki rinqa bani dariya ko sau daya kika bari nazo gurinki baki bani dariya ba zan sanya karnukan gdana su cijeki idanfa kin yarda”
Wani murguda baki Jiddoh tayi tace “hohoho aura kado mi akai akayika da har zan kasa baka dariya yo ko innarka da baffanka ai nabawa dariya kai bura ma kaji wani abu kwanaki da naje burni har wani me qaton ciki nabawa dariya bare kai dan tatsitsi dakai amma fah tsaya kaji ni bani auren kado kado bashi riqon aure saki a jininku shike yawwa kuma jauro Madi ma ya fika kyau gashi dan gayu har agogo fah yake sawa

 

_Somin tabi_

 

*UMMUH HAIRAN CE.

*MATAR LAMEER*

*2*

 

Sake gyara zaman hularsa yayi ya zuba mata maganadisun idanunsa yana qare mata kallo sama da qasa yace “nononki baiyi tsami ba ko?” Turo baki gaba tayi ta qara tura cokalelen dankwalinta gaba tace “yo nonon shanuwa idan yayi tsami ai saidai akai juji” dariya yayi da ganin bata fahimci me yake cewa ba yace “amma akwai ranar da nonon naki zaiyi tsami fah” wani tsalle tayi tace “ariyyy hege Kaɗo da muguwar alkaba’i kake idan nonona yayi tsami ai goggo kasheni takayi kai barima kaji ranar nan da mukaje dandali ana ajon auren me yar butta da tsalha da nashiga ina rawa kowa saida ya liqamin takarda”

Ɗan ƙaramin bakinta ya zubawa ido yana kallonta yarinyar kyakkyawa sai bambadanci daya dami rayuwarta miqewa yayi tare dayin miqa yace “kisamu leda ki juyemin a ciki zan baki jaka uku da rabi” miƙewa tayi ta zari qwaryarta zata tafi ya riqo hnnunta da sauri yace “tsaya mana Hauwa” sakin ƙwayar tayi jikinta ya dauki rawa ta zube a gurin ta fasa uban ihu ya saki bottle ɗin hannunsa yayo kanta yayi saurin rufe mata baki yace “ke kinada hsnkali kuwa JIDDAH uwar me nayi miki da zaki zunduma wannan uban ihun salon kisa yan uwanki su bugeni”

sake rintse idonta tayi ta zunduma ihu tana fadin “shikenan na mutu na lalace jiyannan goggo ta gama hwaɗi mami cewa idan kaɗo ya tabaka mutuwa kakeyi yanzu nima shikenan mutuwata tazo zan tafi inda Allah wayyoh ni goggo wayyoh ni baffa wayyoh ni Madi dan burni kaɗo ya cutamin shikenan walakiri zaya kasheni…”

 

Tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido haushi baƙin ciki da takaici kamar su kasheshi baisan sanda ya fincikota ya hadata da jikinsa yace “badai tabaki nayi kike haukannan ba to na rungumeki na tsotsi bakinki ma yarinya sai ki jira mutuwarki kowanne lkc daga yanzu”

 

Bai damu da yanda ta bata jikinta da nono ba ya sake mannata da jikin motar ya matseta yanda ko hangenta baayi ya manna mata kiss a goshinta da lebenta ya sauke numfashi ya saketa ta kuwa zube a gurin shikuma ya zaro dubu biyu ya ɗora mata a cinyarta ya shige motarsa yaja yabar gurin itakam jiddah sake neman guri tayi ta kwanta bayan ta soke kudinta tana jiran mutuwarta don tayi imanin a yau kaɗó ya cusheta babu abinda zai hanata mutuwa.

 

Numfashinta ma ɗaukewa takeyi wai ta mutu idan ta bude idonta saita sunsuna rigar jikinta sai taji ƙamshin jikin kaɗo a jikin rigarta sai ta sake mutuwa taji ko zata dainajin ƙamshin turaren kaɗonta

 

*UMMUH HAIRAN CE..

*Free*3*
Tananan kwance har masu kiwon shanun rugarsu suka fara dawowa idan taji tafiyar mutane sai ta qara kwanciya tayi luf ita a dole ta mutu idan suka wucce sai ta bude idonta tayi ajiyar zuciya tace “hege walakiri ya wucce baiganni ba”
Kai harfa dare ya fara shiga Jiddoh ana kwance jikin ta qaura yayi la’asar qarshe dai ta tashi zaune ta takure a jikin wata bishiya tanata dan kukanta.

 

Baffanta ne yazo wuccewa yaci karo da qwarya yayi saurin ja da baya tare da ciro touch light dinsa ya fara haske haske can ya hangota a takure ya matsa da sanda gabanta yana ware Mata kallo Saida ya tabbatar itace sannan ya matsa kusa da ita ya hasketa tayi saurin dagowa tare da qanqame jikinta tana karkarwa tace “na tuba azara’ilu mazarin rai alqur’an bansan ya taba hannuna ba kuma ma har rungumeni yayi sumbaceni nidai yau mutuwa kala uku zanyi wayyohh Baffa zan tafi nabar ko harda Madi dan burni aradun Allah kado ka cuceni…”

 

Naushin da taji taji an sakar Mata a bakinta shine ya dawo da ita hayyacinta ta bude idonta ta saukeshi akan baffanta aisai ta zabura ta miqe da sabuwar rawar jiki tace “kaima Baffa ka mutu ne ashe zanci gaba da ganinka a lahira amma baffa ance a lahira baa zalumci meye yasa ka bugemin baki” fincikarta yayi yace “dama Yadammu ta hwadi mani cewa akwai wani kado da yake zuwa yake siye nononki kullum har yana qara miki kudi yanzu har takai ya hwara rungumarki yana sumbarki to alqur’an baki jamin abin hwadi a duniya ba a rinqa nunani da lebe muje wuro nijiyya ubanda yace ki rinqa hutta kina neman maza mazanma asararru irin kadawa su shusheki su tai su barki”

 

Figarta yakeyi da dukkan qarfinsu suna shiga ya watsata tsakar gdan fadi yake “Laure Ladi ku fito kuji abunda almurar diyar nan take aikatawa nan fa duk gida aka fito akayi cirko² ita kuma ta qara bajewa a dole itafa mutuwa take jira.
Gyaran murya Baffa wuro yayi yace “wato Laure kene kika lalata yarki da kanki yanzu gatanan ta hwadi miki abinda suke aikatawa da kado” salati aka hau yi ana tafa hannuwa fadi suke sun banu sun lalace wani uwar maqura da goggo tayi Mata ne yasata sake shiga hayyacinta tace “qur’anin ubangiji bani nace yayimin shine yayimin kuma nima har mutuwa nayi walakiri yaqi zuwa ya tafi dani da tuni na huta”

 

Buge bakinta goggo tayi tace zakici uwariyonki yar qaniya” Baffa ne ya daga murya yace “Tani kaje kace da Jauro mudi anjima inason ganeshi aradun Allah aure zanyi miki tunda ke bakyajin magana yau ki tsokano masunta gone ki tsokano manoma yanzu kin fara biyewa shiriritar kado to gara kowa ma da kado donni ko gaisuwa banso ta hadani da kado shashashan kawai”

___________Qarfe tara na dare ya shiga cikin garin Kano saboda tsakanin Kano da qauyen Alqalawa da nisa sosai don’t qallah yakai kilometer 94.

 

Gdan iyayensa dake cikin unguwar Tarauni ya fara zuwa yayi parking ya fito ya qwanqwasa bayan yan mintina yaji ana zare saqatar gdan suka gaisa da maigadin yace “Alh kuwa yananan?” Shafa kansa yayi yace “Sai Hajiya dama tace idan kazo ince tanason ganinka”
Saida gabansa ya fadi don yasan Kiran mahaifiyar tasu ba alkhairi bane, hakanan yasa aka budensa get din ya shiga da motarsa yayi parking ya fita ya dauki ledojin da yasa aka yanko masa zabbi manya guda ashirin ya raba biyu zaikai gidansa daya daya kuma ya taho dashi gdan iyayen nasa ya shiga.

 

Da sallama aka amsa masa ya miqawa me aikin da take yankan apple ledojin guda biyu days zabbi daya qwansu ta tafi shikuma ya zauna tare da rusunawa yace “hajiya barka da hutawa”……….

 

Add Comment

Click here to post a comment