Littafan Hausa Novels

Hakkokin Aure Da Ya Kamata Ku Sani

Hakkokin Aure Da Ya Kamata Ku Sani

 

 

 

 

 

 

HAKKOKIN AURE ABISA ALQUR’ANI DA SUNNAH

DARASI NA 33

MAZA DA YAWA ZASUYI DANA SANI AGABAN ALLAH

Da yawan maza a wannan zamanin sukanyi aure ne badan ibadah ba sai kawai domin biyan buƙatar kansu, hakan yasa mata suke fuskanta matsaloli iri-iri acikin zaman aurensu a wannan zamanin.

Zaizo yayita lallaɓaki kafin ya aureki amma da zarar kin zama matarsa ya samu ya kusanceki, tofa shikenan saiya fara canja miki, ya fara watsi da duk wata soyayya da yake nuna miki a lokacin baya kafin aure,

kuma bazaga gane auren biyan buƙata bane sai lokacin da suka gama jima’i yana samun biyan buƙatarsa saiya juya mata baya, babu ruwan da ita, bai damu ba ta sami gamsuwa ko bata samuba, inda zatayi masa magana akan cewa itafa bata sami gamsuwa ba a wannan lokacin da sai ya gaya mata magana mara daɗi lallai maza kuji tsoron ALLAH ku sani ALLAH bazai bar wannan hakki ba dole za’a tambayeku akansa.

Yadda Amarya Zatayi A Daren Farko

Wani kuma daga lokacin daya santa a mace, to shikenan batada wata daraja a gurinsa saiya fara tunanin ƙaro aure, koda kuwa baida halin ƙaro auren, kuma ita kanta matarsa ta gida bata samun cikakkar kulawa daga gareshi amma a haka yake hangen ya auro wata a waje kuma fa baya iya gamsar da ita a kwance kuma baya wadatar da ita da duk wani da take buƙata na hidimomin gida.

Amma a haka zakaga ita wacce zai ƙaro saboda rashin tunani bazatayi bincike ba akansa tasan yaya yake rayuwa data gidan, amma a haka zata aureshi babu bincike saboda kwaɗayin abin duniya ko kuma yazo ya banka mata ƙarya, sai bayan ta shigo kuma a fara yawo gurin Bokaye ana nemi sihiri.

Sannan daga ranar daya ƙaro aure to ita wannan uwar gidan ta zama mara amfani zai maida ita kamar shara, domin ita shara duk dattin da aka kwaso ita ake kaiwa, to itama idan aka ɓata masa rai akanta zaizo ya sauke bazai iya zuwa wajen amaryasa ba yayi mata haka ba.

To itama amaryar data kwana biyu zai fara hangen wata saiya fara wulaƙantata itama, wannan shine auren biyan buƙata, irin wannan auren ALLAH yana cire albarka acikinsa.

Sannan wasu mazan kuwa da zarar uwar gida ta nemi hakkinta sai yayi ƙoƙarin zaginta wanima harda duka wani kuma saiya saketa to ku sani ALLAH yana kallon duk abinda kuke aikatawa ALLAH yace na haramta zalunci akan kaina kuma na haramtashi a tsakaninku.

Sannan kuma babu wani miji ko maca da wani zai zalunci wani a tsakaninsu face sai sun tsaya agaban ALLAH a ranar alƙiyama an karɓawa mai hakki hakkinsa kuma a wannan rana ana biyan hakkokine da ayyukan ƙwarai, kuma sai a kwashi salloli da azumi da wasu ayyuka na mutum na shekara ɗaya basu gama biyan hakkin matarka daka tauye na kwana ɗaya ba.

Lallai mazan wannan zamanin mun rasa wasu abubuwa wanda duk wanda bai kiyayesu ba zai iya samun kansa acikin azabar ALLAH wato sune kamar haka:

• Hakkin ciyarwa gwargwadon iko.
• Tufatarwa gwargwadon iko.
• Baiwa matarka lokacinka domin ɗebe kewa.
• Maganganu masu daɗi da rarrashi.
• Gamsar da ita a yayin kwanciyar aure.
• Girmama iyayenta da ƴan uwanta.
• Nisantar kule-kulen mata a waje.
• Son kanka da nuna isa da iko ga matarka.

Wato abubuwan nada yawa lallai mu sani akan rashin kiyaye waɗannan abubuwa da muka lissafo a sama da yawan maza zasu iya faɗawa cikin azabar ALLAH a dalilin rashin kiyayesu.

Da yawan mata suna afkawa zina ne a dalilin mazansu basa iya gamsar dasu a yayin jima’i.

Da yawan mata suna fara yiwa mazansu sata ne a dalilin mazan basa iya basu abinda zai wadatar dasu na harkokin gida kuma bawai babu bane akwai dukiyar kaeai mugunta ce.

Sai kaga abincin da za’a dafa kowa yaci dashi da ‘ƴa’ƴansa amma yana baƙin cikin ya bada kuɗin cefanen dazai wadatar ayi komai yayi kyau, idan kuwa tayi iya ƙokarinta da abinda ya bata, sai yazo yana faɗa yana masifa, ya manta shine ya bai bada abinda zai wadatarba.

Don haka lallai maza muji tsoron ALLAH mu gyara tsakaninmu da matanmu sai tsakaninmu da ALLAH yayi kyau.

ALLAH ka bamu ikon yin adalci a tsakaninmu da matanmu.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.

Add Comment

Click here to post a comment