Littafan Hausa Novels

Diyam Hausa Novel Complete

Diyam Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

DIYAM
By
Maman Maama
To my daughter Haleema, May you forever be blessed.
Bismillahir Rahmanir Rahim
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannan rubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubuta sharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikon karantawa.

Littafin DIYAM kyauta ne, ina fatan ya zamanto min sadakatujjariya har bayan raina. Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana, na fili dana boye.
Diyam is a total work of fiction, in yayi dai dai da labarin ki/ka to coincidence ne ba wai da niyya ba ne.

Mairo Yar Kauye Hausa Novel Complete

Diyam littafi nane, mallaka ta ce, duk wanda ya juya min littafi ko ya siyar min ba tare da sani na ba shi da Allah.
Just follow my pen for I assure you, you are going to fall in love with DIYAM.
Episode One
Madaidaicin dakin karatun mai dauke da dalibai 36 yayi shiru bakajin motsin komai sai na takardu, sai kuma very clear voice din lecturer da take gabatar da lecture ga dalibai masu karantar ilimin law a makarantar Blavatnik school a cikin Oxford University. Darasi ne suke yi akan marital laws, inda malamar take yi musu bayani dalla dalla game da dokokin da suka shafi auratayya. Saboda kasancewa daliban sunzo ne daga mabanbanta kasashe, wannan yasa malamar take daukan kasashe daya bayan daya take musu bitar dokokin kasashen da niyyar in sun gama sai su hadu suyi comparing aga wadanne ne sukafi kyau kuma wadanne chanji ya kamata a samar.
A yau ne kuma malamar tashigo kasashen nahiyar Afrika. Ta fara da Nigeria, the giant of Africa. A nutse ta fara karanto wa daliban dokokin da kasar Nijeriya take dasu wadanda suka shafi auratayya. Suna tsaka da daukar darasin ne suka ji snicker, malamar ta dakatar da karatun da take yi ta dago kanta a tare da duk sauran daliban suka kalli sashen da dariyar ta fito.
A extreme end of the class room, sitting alone like an abandoned island, wata kyakkyawar budurwa ce wadda kallon farko in kayi mata daga nesa zaka ce kyakykyawa ce, in ka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi yadda kake tunani kyau, as kana cigaba da kallon ta kyawunta yana cigaba da bayyana a gare ka. Da yawa a makarantar ana yi mata kallon balarabiyya amma nigerians suna ganin ta suke fahimtar cewa tasu ce, kabilar fulani ce, kabila mai dangantaka da larabawa. Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa tayi dariyar ba. Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa ana kallonta ya saka ta dago kanta da sauri, dara daran idanuwanta a bude kuma ta saka su a cikin na malamar da take tsaye a gaban desk dinta. Suka tsaya suna kallon kallo sannan malamar tace mata “why do you laugh? Are you finding this funny?” Ta girgiza kanta da murmushi a gefen kumatunta. Malamar ta koma kusa da podium ta tsaya tana kallonta sannan tace “where are you from?” Still kanta a kasa tace “Nigeria” malamar tace “menene ra’ayinki game da wadannan dokokin na auratayya a Nigeria. Kina ganin sunyi dai dai ko kina da gyara?” Shiru ta sake yi na wani lokaci, sannan tayi karamar dariya tana girgiza kanta, fuskarta na nuna cewa akwai abinda yake damunta, suddenly kuma sai tayi magana “bani da gyara ma’am. Saboda all those laws da kike lissafawa a rubuce kawai suke, maybe for the sake of the likes of you da zasu nema for educational purposes, amma ba wai amfani ake yi dasu ba” malamar looked interested, tace “so, can you tell us the situation of marriage in Nigeria?” Nan take murmushin fuskar budurwar ya dauke, ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana kallon rubutun da yake gabanta. “You have a very beautiful handwriting kanwata” taji muryarsa a kunnenta as clear as if yanzu yake gaya mata.
Ta dago kanta tace “in Nigeria ma’am, northern Nigeria to be precise, marriage is just like a form of legal slavery” gabadaya hankalin yan ajin ya koma kanta, har wadanda ada suke yan rubutun su yanzu sun juyo suna kallonta. Ta cigaba cikin yaren turanci mai dauke da nigerian accent “tabbas kafin aure akwai kalmomin i love You, amma yawanci a baki suke tsayawa basa karasawa zuciya, daga zarar anyi aure miji will have a feeling similar to feeling din da master yake ji a lokacin daya sayi slave. Like since I pay your dawry it means like I own you, you belong to me. Sai ya manta da cewa shi da matar belong to each other. Wadansu mazan ko first year ba zata wuce ba zasu juye su zamarwa matar like total stranger, like bata taba sanin sa ba a rayuwarta.
“Na sani cewa kusan more than 80% na mutanen mu na arewa musulmai ne, kuma na sani cewa a Alqur’ani ance ‘alrijali qawwamuna alan nisa’i’ miji shine sama akan mace, amma kuma da ubangiji yayi gaba kadan a Alqur’ani sai yace ya sakawa maza wannan qawwamar ne saboda su ya dorawa nauyin ci da sha da sutura da muhalli. Amma a halin yanzu more than rabin mazan mu basa iya daukan wannan nauyin da Allah ya dora musu. Mata da yawa su suke ciyar su shayar su kuma tufatar da kansu da yayansu wani lokacin ma harda mazajen na su. Mace zata fita ta je office neman kudi ko kuma ta fita saro kayan sana’arta sannan ta dawo ta girka abincin data siyo da kudinta ta, tayi shara da wanke wanke da wankin kayanta dana yaranta da na mijin, kayan kuma da ita ta siya da kudinta, ta taya yaranta yin homework din da aka basu a makarantar da ita take biya musu kudin makaranta, sannan kuma mijin yayi expecting zata kai masa ruwan wanka tayi masa ta shirya shi tayi masa tausa sannan ta biya masa bukatarsa a shimfidar auren su”.
“Mace ce zata yi ciki, ta haihu, wata ma hatta ragon suna da kayan fitar suna ita zata siya, ta shayar da dan ta ciyar dashi da komai amma idan rabuwar aure tazo sai mijin yace ‘ajjiye min yayana’. Tana ji tana gani, tana kuka yayanta suna kuka, haka za’a raba su mijin ya dauka ko daya ba za’a bata ba, kuma a karshe shi din daya dauka sai yaje ya kaiwa matarsa ita kuma ta azabtar dasu ta bautar dasu saboda ba ita ta haife su ba. Yara da yawa sun rasa ransu saboda irin haka, wadansu sun salwanta, wadansu sun koma almajirai, wadansu yan daba saboda babu tarbiyya, babu soyayyar iyaye”. Ta goge hawayen da ya taru a idonta ta cigaba
“That’s why am here in Oxford, that’s why am studying law. Saboda in tabbatar cewa babu wata mace a Nigeria da zata sake shan wahala a hannun namiji”
“Ohh shut up please”
Duk class din suka juya suna kallon wanda yayi magana. Ta san shi, tana ganin sa a ajin amma basu taba magana ba dan haka ko sunansa bata sani ba kuma bata da interest din sani. Ya juyo yana kallonta yace “just because kin zauna a kusa da wadanda basu ji dadin aure ba bai kamata ki zauna a nan kina fadin maganganu marasa dadi akan kasar mu ba” ta daga gira daya sama tana kallonsa tace “wacce kasa kenan?” Yace “wacce kike magana akanta” tace “you don’t look like Nigerian, and definitely not a northerner” yace “ohh but I am” tace “which part?” Yace “Abuja” ta dan rufe bakinta tana dariya tace “but Abuja is not in the northern Nigeria, so you shut up”.
Ya kara bata rai musamman ganin dariya a fuskar daukacin yan ajin. Shi dai yasan duk da shi ba dan arewa bane ba amma ba zai bari a zauna a yaga arewa har haka ba, for his mother is from the north, his only sister now lives in the north, his uncle too, dan haka ya san hakkinsa ne ayanzu ya gayawa mutane cewa karyace kawai yarinyar ta shirya musu, maybe dan tayi suna.
Yace “I may not be born in the north, but my mother is a northerner, kuma….” Tace “was she born and raised in the north?” Dan shiru din da yayi yasa ta fahimci no ce amsar sa, ta daga kafada tace “then she too is not a northerner” da sauri yace “her father was” ta sake cewa “born and raised?” Ya mike tsaye, frustrated, yace “what does it matter?” Tace “everything. In kana son sanin halin da al’umma suke ciki you need to live with and study them”. Ya sake yunkurowa da niyyar sake kokarin kare mutuncin kasarsa kamar yadda yake tunani amma sai ya zamanto period din ta kare. Yayi kwafa sanda malamar take bayanin cewa zasu dakata anan sai next class zasu cigaba.
DIYAM……….writing
In anyi comments da yawa zanji dadi, kuma zan fahimci ana son in cigaba.
❤DIYAM❤
By
Maman Maama
Episode Two
Washegari basu da madam Sally, malamar da tayi musu lecture din jiya, a takaice ma lecture din safe kawai suke da ita shikenan sun gama. Wannan yasa suna fitowa kowa ya fara kokarin tafiya gida dan gabatar da al’amuran sa na yau da kullum. Yarinyar jiya ce ta fito a karshe, tana rungume takardu a kirjinta da hannu daya daya hannun kuma tana rike da wayarta, tana ta waige waige kamar me neman wani sai kuma ta fara tafiya a hankali tamkar mai jin tsoron taka kasa.
Daga inda yake tsaye yana hango yadda daliban suke fitowa daya bayan daya. Ya dauko pack din cigarette a aljihunsa da lighter ya kunna yayi mata dogon zuka ya lumshe ido. Deliberately ya riga kowa fitowa saboda yana son ya ga fitowarta, yana son su cigaba da maganar jiya, yana so kuma ya ja mata kunne akan tasan maganar da zata fada tasan kuma a inda zata fada. Ya danyi karamin tsaki. Haka kawai tana neman ta zubar masa da class a cikin mutane dan duk friends dinsa sunsan shi ɗan Nigeria ne kuma zasu dauka abinda ta fada gaskiya ne.
Yana kallonta ta fito, ta danyi dube dube sannan ta taho direct zuwa side din da yake, tana tafiya a hankali tamkar mai kirga takunta wanda hakan ya bashi damar karewa siffarta kallo, ‘too beautiful’ yayi deciding, ‘too beautiful for my taste’. Har tazo ta wuce shi bata ko lura dashi a gurin ba, ya bata dama ta danyi nisa sannan ya yar da cigarette din hannunsa ya bita da dan sauri yace “hey” ta dan tsorata kadan sannan kuma ta kalle shi ta dauke kai ta cigaba da tafiya, ya daidaita takun shi da nata ya sake cewa “hi” ta dakata tana kwallonsa cikin ido ba tare da ko alamar tsoro ba tace masa “Assalamu alaikum” ya dan shafa kansa yana jin duk confidence din da ya ke dashi yana draining. Her eyes makes him uncomfortable. Jin bai amsa ba yasa ta sauke idonta kasa ta cigaba da tafiya. Ya bita a baya yana cewa “my name is Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq” ya sake shafa kansa yace “my God, this is so awkward, I always feel like this duk sanda nake introducing kaina. I hate my name. Na rasa dalilin da yasa iyayen mu suke son lallai sai sun saka wa yayansu sunan iyayen su. I mean, it make the name only circles and remains in the family. I always wish I can change my name” ta daka ta ta tsare shi da ido, ya dauko handkerchief a aljihunsa ya goge fuskarsa duk kuwa da cewa ba gumi yake ba, he obviously looked nervous, duk planning din da yayi na irin maganganun da zai gaya mata ya gudu ya barshi. A zuciyarsa ya gode wa Allah da ya zamanto su kadai ne a gurin. Yayi ajjiyar zuciya yace “I am talking too much, aren’t I?” Ta girgiza kai kawai sannan a nutse tace “in my religion, Islam, an bawa mutum damar chanza sunansa in baya so, what you only need to do is ka sayi rago ka yanka da niyyar ka chanza suna, sai ka kira mutane su shaida, shikenan. But I don’t know ko naka addinin ya yarda da haka” he was stunned, wato kallon wanda ba musulmi ba take masa, how can she even think that? Ya bude baki zaiyi magana amma ya kasa cewa komai, sai daya hadiye wani abu mai daci a makogwaronsa sannan a karshe yace “I am a Muslim also” ta dauke kanta tace “sorry, my bad” cikin jin zafin maganar ta yace “me yasa kika yi tunanin ni ba musulmi ba ne ba?”
Ta kalle shi tun daga kan brown wind tossed hair dinsa, his cigarette stained lips, katuwar head phone din dake kunnuwansa, shirt dinsa da take dauke da katoton hoton Lady Gaga, wandon sa da yake tsatstsage daga guiwa, zuwa takalminsa da yafi kama dana sojoji, sannan ta daga gira daya sama tace “na farko you don’t dress like a Muslim, na biyu nayi maka sallama baka amsa ba, na uku muslims don’t complain about their parent’s choice of name, Abubakar Sadiq suna ne mai dadi kuma mai daraja” he was speechless, tunda yake ba’a taba yaga shi irin yau ba, me wannan yarinyar take tunani? Wacece ita? Babu abinda yake so a lokacin irin ya hada wa kyakkyawar fuskanta jini da majina. Ya dunkule hannu amma sai jikinsa yayi betraying dinsa har ta juya ta barshi a tsaye, instead, sai yaji bakinsa yana furta “baki gaya min sunanki ba” ta juyo tace “why?” Ya maimaita “why? I just told you my name that’s why” tace “I didn’t ask you for it” daga haka bata kuma cewa komai ba sai ma kara sauri da tayi.
Ya dunkule hannunsa ya naushi iska, ya rankwashi kansa yana jin haushin kansa sai kuma ya shafa gurin daya rankwasa alamar yaji zafi, gaskiya ya fara sanyi da yawa, har shi mace zata yiwa haka? Who is she?
Daga bayanshi yaga wata yarinya tazo ta wuce shi da sauri tana kira “Diyam!! Wait for me” yaga ta tsaya ta jirata ta karaso sannan suka cigaba da tafiya tare. “Diyam” ya maimaita, how can someone name his child water? Me parents dinta suke tunani? sai kuma ya koma gefe ya samu guri ya zauna, ya dauko sigari ya kunna, ya gyara zaman headphone dinsa ya zuki tabarsa ya lumshe ido yana lissafa hanyoyin da zai rama abinda Diyam tayi masa.
*****. *****. *****
Diyam taji kiran da akayi mata, ta juya suka hada ido da kawarta Judith, kawarta ce tun a Nigeria suka hadu lokacin suna shirye shiryen tahowa UK, a lokacin da suka yi registration ne Diyam ta fahimci cewa Judith tana neman gidan zama sai kawai ta jata suka zauna tare a nata gidan, tare da Murjanatu. Tayi mata murmushi lokacin da Judith ta karaso suka jera suka cigaba da tafiya a tare. Judith tace “if you don’t mind me asking, were you talking to that guy?” Diyam tace “yes I was, what about it?” Judith ta danyi dariya tace “it is just that you never talk to anybody” Diyam ma tayi dariya tace “believe me, it wasn’t such a good talk. Am sure that guy is never going to talk to me again” suka yi dariya baki daya, Diyam ta dafa goshin ta tace “God, am so boring, how do you guys manage living with me?” Judith tace “it is never easy” haka suka cigaba da tafiya suna hira akan halayen Diyam.
A kafa suka tafi estate ɗin da gidan su yake, suka je block E suka hau lift zuwa fifth floor inda apartment dinsu yake. Judith ta fito da key din hannunta ta bude kofa. Suna shiga a parlor duk suka zube a kasa saboda gajiya. Murjanatu ta fito daga kitchen da spatula a hannunta tana kallonsu, black beauty ce, mai dan karamin jiki, manyan idanuwa da cikar gashin gira. Kana ganinta zata yi maka kama da irin shagwababbun yaran nan wadanda suka taso cikin naira, tace “shi yasa naki zuwa yau. Haka kawai akan lecture daya bazan sha wannan wahalar ba” diyam ta kalleta tace “kinyi missing, alot” Murjanatu ta karkata kai gefe tace “at least ai nayi muku girki ko? So what you should be saying is ‘thank you'” Judith ta mike tayi pecking Murjanatu a cheek dinta tace “thank you”.
Suna cikin cin abincin, wanda Diyam chakula kawai take kamar mai cin magani tana ta complain din how much she misses abincin gida. Tace “I can give anything, I mean anything, dan in samu tuwo in ci” Murjanatu ta tabe baki tace “niko ko missing tuwo banyi ba, sam dama ni ba sonshi nake yi ba” Wayar Diyam tayi kara ta kalleta kawai ta dauke kai. Judith ta dauka tana kallon sunan mai kiran har ta katse sannan ta ajiye tace “ban taba ganin marar zuciya irin mutumin nan ba, wulakancin da kike masa Diyam ya isa haka” Murjanatu ta daga hannu tace “hey, yayan nawa kike cewa marar zuciya?” Tana yin shiru wayar ta tana yin kara, ta langwabar da kai tace “Please Diyam, kinga ya kira a wayata. Please just for today” Diyam ta harare ta bata ce komai ba, Murjanatu ta daga wayar ta gaishe da wanda ya kira tana kallon Diyam tace “lfy lau take, yanzu muka dawo daga lecture wallahi duk mun gaji yaya. Eh bata zuwa da motar wai exercise ne zuwa school din. Eh shikenan for today. Gata nan tana cin abinci. Bata ci da yawa wallahi yaya, wai tuwo take so. Ah ah ni ban sani ba wallahi. Yaya ni Wallahi ban iya tuwo ba. Okay, sai anjima” ta ajiye wayar tana turo baki fuskarta kamar zata yi kuka tace “wai inyi miki tuwo yau da daddare ince with love from him” duk suka yi dariya, Diyam ta tashi tana rawa tana yiwa Murjanatu gwalo ita kuma ta dauki pillow ta bita da gudu suka shige corridorn da bedrooms dinsu suke.
Diyam………. writing
❤DIYAM❤
By
Maman Maama
Episode Three
Bayan tafiyar su Diyam, ya jima zaune shi kadai, yana ta sakawa yana kwancewa yana kuma zukar hayaki zuwa hunhun sa. Sai da ya ga kwalin ya kare sannan ya jefar da shi ya duba agogon hannunsa yayi tsaki ya mike. Cab ya tare zuwa hotel din da ya ke. Yana shiga dakin ya zauna akan gado yana kare wa dakin kallo kamar yau ya fara ganinsa, idonsa ya sauka akan hoton wata yar kyakkyawar budurwa akan study table dinsa tana murmushi. Ya lumshe idonsa ya bude. She have been the reason for everything daya ke ciki a yanzu, for all his pain and his agony. Ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta for the hundredth time amma yanzu ma kamar ko yaushe bata dauka ba. He wandered me yasa ba tayi blocking dinsa ba dan gwara ya kira bata shiga ba akan ya kira ba’a dauka ba, meaning ta gani kenan, meaning tasan all what he is going through but she just doesn’t care.
Fatima sunanta, Khausar suke kiranta, he had been in love with her for as long as he can remember, maybe tun da yasan menene love din but he failed to tell her. Daga baya kawai sai yaji labarin wai zata auri brother dinsa, that has been the beginning of his agony, wannan ne asalin dalilin fara shan sigarin sa. Yayi iyakacin kokarinsa tun a lokacin dan ganin cewa ya cire ta a ransa and he succeeded a little, but then sai auren baiyi da brother din nasa ba and his brother ended up marrying another. Wannan turn of events din ba karamin faranta masa rai yayi ba, he saw it as another chance na auren wadda yake so.
Shekara guda kenan da faruwar hakan. A cikin shekarar ne kuma yayi failing terribly in his course of study a Abuja, amma sai ya alakanta hakan da cewa dan baya son course din ne, yace yafi son yabi footprints din maternal grandmother dinsa wadda ta kasance lawyer, da kyar yayi iyakacin kokarinsa har ya samu aka barshi ya taho UK karatu duk da cewa iyayensa basu so hakan ba sunfi son ya zauna tare dasu amma saida ya taho tare da daurin gindin kakar tasa, yayi hakane saboda ita, saboda Khausar, for she now lives in UK tare da auntyn su. But sai me kuma? He realized bayan zuwansa cewa ai she is already dating his cousin kuma, wannan yasa ya daura damarar ganin ko sama da kasa zasu hadu sai ya raba wannan relationship din, wannan ya jawo rigima ba yar kadan ba tsakanin sa da cousin dinsa Ayan and he failed miserably. A karshe Khausar looked into his eyes and said “I will never marry you ko mazan duniya sun kare”, and that made him mad, so mad that when his aunty tries to resolve the issue he looked into her eyes and said “go to hell”.
Sati biyu kenan da faruwar hakan. Tun daga ranar ya hado kayansa ya dawo wannan hotel din da zama shi kadai. Kuma tun daga ranar babu wanda ya neme shi kaf family dinsu not even his Mami.
But wannan duk ba shine babban problem dinsa ba. Problem dinsa shine satin sa daya da barin gidan auntyn sa parents dinsa sukayi blocking dinsa out of their family bank account. Tun tashinsa da wannan account din suke amfani gaba daya gidan, kowa yana da access da shi sai dai kawai a karshen wata kayi bayanin abinda kayi da kudin daka dauka, yanzu babu. Shi kuma ba aikin yi ba, dan haka blocking dinsa daga family account ya mayar dashi almost koboless. Bashi da komai, hatta kayan abinci bashi dasu kuma kudin siyan abincin nasa has almost run out, zuwa karshen satin nan yasan ko na abinci bashi dashi.
Yasan wannan duk hikimar Mami ce, they want to fish him out ya kawo kansa ya karbi laifinsa, shi kuma yana jin tsoron yadda hukuncin sa zai zama, ba zaiji da dadi a gurin daddyn sa ba. Kuma yasan he have lost Khausar for good. Yayi biyu babu. Abinda yake bukata a yanzu shine karfin gwuiwar facing family dinsa, accepting mistake dinsa da kuma repenting, but to do that yana bukatar courage, yana bukatar wani yayi masa magana at least ko fada ne ayi masa a gaya masa yayi ba dai dai ba.
Bai san mai yasa yarinyar dazu ta fado masa a rai ba, Diyam. Ya kwanta ya rufe ido yana tunano fuskarta, tabbas tana da courage. From her looks, yadda take ware kanta daga cikin mutane zuwa yadda turancinta bai gama nuna ba yasan cewa she is from a poor background, maybe irin yayan talakawan nan ne da gwamnati take dauka take basu scholarship suke tahowa kasashen waje suyi karatu. But she really does have courage, daga yadda tayi magana rannan a class da kuma yadda tayi facing dinsa straight in the eyes ta gaya masa maganganu. Har dare yarinyar tana cikin ransa, amma kuma ya kasa yanke mata hukunci a ransa.
Washegari kamar kullum Diyam ta riga kowa tashi. Tayi wanka tayi alwala tazo ta bude al’qurani tana bita har akayi assalatu sannan ta je dakin Murjanatu ta tashe ta tazo ta tayar da sallah. By seven har ta gama komai, ta dumama sauran tuwon jiya ta zauna tana ci Judith ta fito tayi joining dinta sannan Murjanatu ta fito itama, but sai taki cin tuwon ta hada tea da bread ta sha. Suna yi suna hirar abubuwan da suka shafi karatun su, Murjanatu tana ta mitar takura musu da Diyam take yi suke zuwa school a kafa bayan ga mota an ajiye musu musamman saboda zirga zirgar su.
Suna shiga makaranta Murjanatu tana haki ta kalli Diyam tace “you and yaya na deserve each other. Kafiya ce daku da naci akan abinda kuka sa kanku. At the end kuma ku wahalar da wanda yake tare daku. Ni dai daga yau na daina turturing kaina wallahi, motar zanke shigowa koda ni kadai ce” Diyam ta daga gira daya tace “ba sai ki shiga ba, in kin iya driving din” suka yi dariya tare da Judith, ita kuma Murjanatu ta tura baki tayi gaba tana kunkuni ta barsu tunda ba department dinsu daya ba, suna dan yin gaba kadan suka rabu da Judith itama sannan Diyam ta karasa department dinsu ita kadai.
Tun daga nesa ta gane shi. Yana tsaye kamar kullum da headphone a kunnensa da kuma sigari a hannunsa. Ta duba agogon hannun ta taga it is not 8:00 yet amma har ya fara zuke zuke, maybe ko breakfast baiyi ba. Ta dauke kai ganin cewa bai ganta ba dan kamar yayi zurfi cikin tunani.
Har suka yi nisa da lecture din tana ta saka ran ganin ya shigo amma shiru bai shigo ba, sai da aka fara concluding sannan ya shigo dan haka ko zama bai gama ba malamin ya fita, and she felt sorry for him. Suna nan wani malamin ya sake shiga ya gama ya fita daga nan kuma zasuyi one hour break sai su sake wata shikenan. Ta fita ta nemi coffee shop ta zauna aka kawo mata coffee da cake taci duk da dai ba yunwa take ji ba but she just need to eat something saboda suna da wata two hours lecture din, Madam Sally. Tana zaune ta hango wucewarsa yayi hanyar gate. She wonders ina zaije tunda suna da wata lecture din? Sai kuma ta daga kafada tana mamakin me yasa ta damu da business dinsa.
Har suka tashi a ranar bata kara ganin sa ba. Da daddare suna cin abinci ta bawa su Murjanatu labarin encounter dinta da guy din tace “I am just feeling sorry for him. He obviously is distracted, confused maybe” Murjanatu ta harare ta tace “ni dai babu ruwana. Daga tausayi kuma sai muji wata magana ta daban. Kinsan in yaya yaji wannan maganar zai iya harbo nuclear bomb ya tarwatsa Oxford gaba-daya” Diyam ta daga kafada tace “Allah yasa uranium zai harbo ba nuclear bomb ba. I will talk to whoever I want to talk to” Murjanatu tace “you are not going to give my brother a break are you?” Diyam ta mike tsaye tace “no i am not, har sai yayi abinda nace masa” Murjanatu tayi murmushi tace “maybe baki san shi ba kamar yadda kike tunani” Diyam ta wuce daki da sauri tana jin zafi yana taso wa a zuciyarta.
Da safe basu da lecture da wuri dan haka suka yi baccin su sosai. Sai after ten Diyam ta tashi ta fita parlor ta tarar Judith tana kitchen tana hada musu breakfast. Ta dawo dakin ta ta shiga wanka. Tana fitowa wayar ta tana ringing amma ko kallonta bata yi ba ta dauke kanta ta cigaba da shiryawa amma a zuciyarta tana mamakin yadda yake keeping track din komai nata, yasan sanda take da lectures yasan kuma sanda take free. Wayar tana katsewa taji text ya shigo, ta dauka takaranta, sakon barka da safiya ne mai hade da tsadaddun kalaman da sai da suka huda zuciyarta amma sai kawai ta tabe baki ta ajiye wayar. Ita dashi a ga wanda yafi taurin kai.
Diyam……… writing
❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Four

Tana saka kaya Murjanatu ta shigo dakin, daga ganin fuskarta Diyam tasan akwai problem, ta ajiye skirt din hannunta tana bawa Murjanatu data zauna a kan gado dukkan attention dinta. Ta daga gira daya sama tace “me yace kuma?” Murjanatu tace “he asked me about Judith” Diyam ta hade rai tace “what about her” Murjanatu tace “he asked wai bata kawo mana maza gida? Na gaya masa bata kawo wa but he didn’t sound convinced.” Ta sunkuyar da kanta kasa tace “am afraid he is going to send her away” Diyam ta dafe kanta tana zagaye dakin da bacin rai a fuskarta sannan tace “tell him nace Judith is my friend, if he wants to get to her he will have to go through me. Ni na kawo ta gidan nan, in yana son ya kore ta sai ya fara kora ta tukunna” Murjanatu ta saka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tace “ba dani ba, bani Murjanatu ba. Uwata ta daina haihuwa ballantana ta sake haifo ni” Judith ta bude dakin ta leko kanta tace “hey girls, food is ready” sai kuma ta tsaya tana kallon yadda suke kokarin kakaro murmushi.

A bayan lecture hall dinsu ta hango Sadiq. Shi kadai kamar kullum, da sigari a hannunsa kamar kullum, tayi saurin dauke kanta ganin yana kokarin juyowa. Amma sai ta tsaya a kofar hall din bata shiga ba tana so taga yau zai shiga ko yauma zamansa zaiyi a waje. Sai da aka kusan fara lecture din sannan ya taho, a gabanta a jefar da sigarin hannunsa ya saka kafa a murje ta, zai wuce Diyam tace ” you know smokers tend to die young ko?” Ya kalleta for some seconds, ya busa mata hayakin bakinsa yace cikin husky voice “says who? I can’t believe malama kamar ki ta yarda da wannan saying din. Kin manta kaddara? Ina islamiyyar taki ta tafi?” Ta sa hannu ta kade hayakin daya huro mata tace “maybe ni da kai munyi understanding kaddara differently. Tell me why do we pray? Why do we struggle? Me yasa muke neman duniya kuma muke neman lahira in dai har an riga an rubuta komai, me yasa ba zamu kwanciyar mu ba mu jira abinda aka rubuta mana yazo ya same mu. Yes kaddara rubuyacciya ce, major abubuwan da zasu faru a rayuwar mu a rubuce suke but what is in between depend on choices din da muke making. Wannan shine fahimtata. Yes, kamar yadda ka fada shekarun da aka rubuta maka ba zasu chanza ba amma how you are going to spend them depend on you, ko dai kayi spending dinsu healthy and happy in ka daina shan sigari ko kuma kayi spending dinsu with lung cancer in ka cigaba da smoking” ya kalle ta daga sama har kasa yace “go to hell, both you and your preaching” ya shige class din ya barta a tsaye. Taji zafin maganar sa amma sai ta hadiye ta bishi a baya.

Suna shiga class din wani guy ya kalli Sadiq yace “the Nigerian guy. Why do you skip madam Sally’s class yesterday, don’t you want to depend your country anymore?” Sadiq yayi banza dashi ya shige ya samu guri ya zauna. Sannan yan ajin suka juyo gabaki daya suka zubawa Diyam ido, ta yi gyaran murya tace cikin harshen turanci “abinda na fada rannan gaskiya ne, gaskiya ne based on sani na. Shima kuma musa min din da yayi gaskiya ne based on sanin sa. We may have come from the same country but we live in different worlds. Muna zama cikin different mutane, muna kallon rayuwa from different perspectives. My being right doesn’t makes him wrong. You as potential lawyers should know that” duk yan ajin suka kada mata kai cike da gamsuwa sannan ta wuce ta shige seat din karshe ta zauna.

Madam na shigowa ta fara tambayar Diyam “will you like to continue with that day’s argument?” Diyam ta girgiza kai tace “no ma’am, it’s okay” ta juya gurin Sadiq tace “what about you, are you satisfied as well?” ya gyada kai yace “am okay ma’am. We now understand each other” sai ya juya a hankali ya kalli Diyam, itama ta dago kai suka hada ido and she smiled at him, a take ya fahimci cewa she have the brightest smile he have ever seen.

Bayan sun gama dukkan lectures dinsu, ta fito tana tsaye tana jiran Murjanatu sai gashi ya taho, ya tsaya dan nesa da ita kadan yace “waiting for a friend?” Ta daga murya tace “yeah” sai kuma taga ya zo zai wuce ta, tace “my name is Haleema. Haleema Usman Kollere. But people call me Diyam” ya gyada kai yace “I am Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq. Most people call me Bassam. You can call me that as well”.

Tayi murmushin ta mai kyau tace “nice to meet you Bassam” ya danyi dariya yana jujjuya kai yace “You have a beautiful smile, very beautiful. Ban san me yasa ba kya yawan yinsa ba. Ta daga gira daya sama tace “if it is beautiful than it is precious kenan. Abu mai tsada kuma kasan ba’a ko ina ake ajjiye shi ba” ya sake dariya, his eyes twinkling, amma bai ce komai ba, tace “and you. Ban dauka ka iya dariya ba” ya gyara fuskarsa yace “believe me, I do laugh alot. Yanzu ne dai I am in kind of not laughing situation. But na miki alkawari in na fita daga ciki we will laugh more” daga haka ya juya da sauri ya bar gurin.

Yana tafiya Murjanatu tana karasowa. Tana kallon bayansa tace “who is that guy? Amma ya hadu fa” Diyam tayi murmushi bata ce komai ba, Murjanatu ta sake cewa “ko shine rannan kuke maganar sa da Judith?” Suka jera suna tafiya da Diyam tace “yeah shine” Murjanatu ta bata rai tace “then it is official, gaskiya ina taya yayana kishi. Lallai ma Diyam din nan” ta turo baki, Diyam tace “oh ashe baku hadu ba daga ke har yayan naki tunda insecurity yana damunku. Ashe kujerar taku bata kafu ba, ai hausawa sunce fargaba asarar namiji” Murjanatu ta harari bayan Bassam da har yanzu suna iya hango shi tace “ohh dama wancan namiji ne? Ai na dauka macece ta aske kanta ta saka wando. Ai wannan yana ganin yayana zai narke a gurin dan tsoro. Wannan daga ganin sa rainon madara da cerelac ne, yayana kuwa tuwon biski yaci da kunu dan haka ba sa’an sa bane wallahi” Diyam da take ta dariya tace “naga alama kam. Tuwon biskin ne yasa kansa yayi tauri da yawa” ta fada tana lakucewa Murjanatu hanci, Murjanatu tace “ouch, sai kin nane min hancin kinsa na rasa mashinshini?” suka yi dariya baki daya, sannan Murjanatu ta fara rokon Diyam akan ta fita dasu yawo yau da yamma “Please, Please Diyam, this routine is killing me slowly, ai ance taba kida taba karatu ko?” Diyam tace “sai jibi weekend sai muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu a gida”

Washegari Friday, Diyam tana zaune a seat dinta tana rubutu taji ance “hi Diyam” ta dago tana kallonsa bata ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa yace “Assalamu alaikum” tace “ameen wa alaikas salam Bassam” ya kalli seat din kusa da ita yace “can I?” Ta gyada kai ba tare data dago ba. Ya zauna ya fito da book dinsa pretending to be reading amma ita tasan ba karatun yake ba. Can ya ajiye littafin yayi tagumi yana kallonta yace “can I ask you something?” Ba tare da ta kalleshi ba tace “sure” yana taping hannunsa akan desk yace “me yasa ake ce miki Diyam? It means water right? Me yasa ake ce miki water?” Ta daina rubutun ta na kallonsa tace “maybe I am as important as water is to some people” yayi dariya yace “your boyfriend maybe” tayi murmushi kawai. A lokacin lecturer din su ya shigo, ya gyara zamansa yace “boring, boring, boring” ta sake murmushi kawai tana wandering me yake yi a makarantar in bashi da interest a karatun.

Add Comment

Click here to post a comment