Littafan Hausa Novels

Doctor Yusuf Hausa Novel Complete

Doctor Yusuf Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

DOCTOR YUSUF

Gajeran Labari

 

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS*

 

 

LABARI DA RUBUTAWA:

*Xayyeesherthul-humaerath*

Tare da

*Zeey ƴar Mutan Zazzau*

 

*SADAUKARWA GA, SIRRIN’YAMACE*

 

*MARUBUCIYAR:*

 

BABU RUWAN SO (FREE)

WASA DA SO (FREE)

AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE)

JAMEEL (200)

MATAR POLICE (200)

KUCHAKAR KISHIYA (FREE)

HAYATIY (FREE)

AMEENATOU (300)

KWADAYI (FREE)

ASHE HAKA SO YAKE (300)

SAI NA AURI MARUBUCI (FREE)

 

 

AND NOW

DOCTOR YUSUF

FREE

 

*TSOKACI: bamu fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka bamu yarda a juya mana labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zamu kara ko mu rage,bamu yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta*

 

PAGE-1

********Yau ne Rana ta Farkon Kasancewata a makarantar GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL BAUCHI (G.S.S.B) tun daga Wajen Makarantar Tsari da Yanayinta ya tafi dani, Dauke Da Murmushi a fuskata na karasa ga Ofishin Shugaban Makarantar nan take ba tare da mun tsaya wani zance ba bayan mun gaisa ya mun iso zuwa Ss3 domin kuwa mun gama komai tun ka fin in zo Makarantar.

 

Abotace Ko Kuma Soyayya Hausa Novel Fitattu Uku

Da shigana idanuna suka fara tozali da kyakkyawar budurwa da ta sake mun Murmushi nan take ba tare da na ankare ba nima na sake mata.

 

Kasancewar ta abancin gaba kuma ita ka dai hakan ya ba Shugaban Makarantar ba ni umarnin zama a bencin da take.

 

Ba Musu na karasa gareta.

 

Tare da yi mata sallama, cikin fara’a ta amsa mun tare da fadin, “Barkanmu Da Safiya Yayana.”

 

 

Saurin dagowa nai ina kallonta jin kalmar da ta furta, “Yayana.”

 

Murmushin nan dai ta kare sake mini wanda ya sanya Ni sunkuyar da kai na nan take.

 

 

Ba mu kara yiwa juna magana ba,har Malami ya shi go a ka fara yi mana Lesson.

 

 

Abun Mamaki lokacin da aka zo kiran Atendas Bayan an kira sunanta Fateema Isma’il sai ga shi an kira nawa Yusuf Isma’il.

 

Malamin ne ya dago yana fadin, “Fatima daman Kina da Yaya A makarantar nan?”

 

Maimakon jin Amsar Aa ji nai ta ce, “Eh Sir.”

 

 

Da Mamaki mu ka kalli juna amman a wannan lokacin ma, Murmushin dai ta sake mun ka fin ta ci gaba da rubutunta.

 

 

A raina ban da sake-sake ba abun da nake da farko ta furta mun kalman Yaya ga shi an tambayeta ma ta kara tabbatar da hakan.

 

Ban ji Mamaki ba sai da wata ta shigo tana kokarin zama a bencin da muke ka da bakin Fateema ta ce, “Surayya wannan desk Din mune da Yayana, Please ki duba na su Zainab su biyune.”

 

Ta karasa maganar tare da kawar da kan ta.

 

 

Karfe 12 dai dai muka fito daga Lesson, mota ce na ga anzo daukan Fateema ya yin da ni kuma daman da Kekena naje.

 

Ko da ta shiga motar lekowa tai muna hada ido ta a daga mun hannu alamar byee byee

 

 

 

🤤🤤Matan Sirri A ci gaba ko adaina??

 

Kar wata ta fadamun green magana wlh sai in hwada miki blue

 

In dai kuna so in sha Allah zan kokarta cikin sati daya mu kammala.

 

 

08103080717

 

Urs Xayyeesherthou

[2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️

Gajeran Labari

 

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS*

 

 

LABARI DA RUBUTAWA:

*Xayyeesherthul-humaerath*

 

*SADAUKARWA GA, SIRRIN’YAMACE*

 

*MARUBUCIYAR:*

 

BABU RUWAN SO (FREE)

WASA DA SO (FREE)

AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE)

JAMEEL (200)

MATAR POLICE (200)

KUCHAKAR KISHIYA (FREE)

HAYATIY (FREE)

AMEENATOU (300)

KWADAYI (FREE)

ASHE HAKA SO YAKE (300)

SAI NA AURI MARUBUCI (FREE)

 

 

AND NOW

DOCTOR YUSUF

FREE

 

*TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta*

 

 

KU GANE DUK DA KASANCEWAR LABARIN DA AKA BANI ZAN RUBUTA AMMAN NOVEL DOLE YANA BUKATAR AKARA MASA ARMASHI

 

SANNAN MASU CEWA DOCTOR MUTUM DAYANE😹WANNAN BA DAMUWATA BANE NI DAI YA BAN LABARI KUMA GA SHI ZAN RUBUTA MAKU AHTO.

 

PAGE-2

******

 

 

Washegari Misalin karfe 10 na shirya tsaf cikin manyan kayana, sanye da hula,kamshi kuwa ba sai an fada ba na san shi kadai ya isa bada sakon isata aduk in da zan kasance.

 

 

Ban san dalili ba amman zuciyata ta zaku da in isa ga makarantar hakan ya sa duk da kasancewar karfe 10:30 ake fara lecture na tafi 10:00 kawai ko dan zuciyata za ta samu sukuni.

 

 

 

Haka kuwa akai domin ko da naje ba kowa Makarantar Shiru,sai wajen 10minit ka fin mutane suka fara zuwa.

 

 

Ina zaune ina zura idanu ta yadda zan ga Fateema ta bullo kamar kuwa ance kalli nan.

 

Daga idanuna na ci karo da motarsu.

 

Murmushi ne ya bayyana a fuskata wanda a baɗini mamakin hakan nake.

 

 

Fitowa tai fuska dauke da fara’a kamar jiya,sai dai yau su biyune.

 

Hada idon da muka yi ne ya sani saurin sunkuyar da kaina kasa.

 

 

Ji nai anyi mun Sallama

 

Hakan ya sani dagowa.

 

Wata Yar budurwa ce kamar Fatima.

 

Bayan na amsa ta kara da, “Na ce ka zo mu shiga ciki mana.”

 

 

Kan in ba da amsa muryar Fatima na ji karaf tana fadin, “Yayana muje ciki ko.”

 

Tsintar kaina na yi da bin bayanta ba tare da na ce uffan ba.

 

Illa a yadda na lura wannan budurwa ta bi Fateema da kallon banza ya yin da ita kuma ta sake mata Murmushin ko in kula.

 

 

Muna shiga suka zauna ita da kawarta ka fin ni na zauna a karshe kusa da Fateema.

 

 

“Ina Kwana Yayana? Fatan mun tashi lafiya ya sanyi?” Cewar Fateema tana kallona.

 

 

Na amsa mata da , “Lafiya lau, Alhamdulillah fatan ke ma kina lafiya?”

 

 

Murmushi ta yi tare da juya kallonta ga kawarta ta tana, “Maryam Ga Yayana nan Yusuf da na baki labari jiya ba ki zo ba ya fara zuwa.”

 

 

Murmushi ita ma Maryam ta sake tare da fadin, “Barka dai Yayanmu ina kwana?”

 

Fateema ta harareta.

 

“Yayanku kuma? Yayana dai,Ya fi miki ki ce Yayan Fateema kawai.”

 

 

Dariya mu ka yi dukanmu har ni ta ce, “To Yayan Fateema.”

 

Daga nan Lesson Teachern mu ya shigo aka fara Lesson.

 

*****

 

Wace ce Fateema Isma’il?

 

Sannan Wane ne Yusuf Isma’il?

 

Ku biyo ni domin jin su waye Jaruman Littafinmu.

 

 

FATEEMA ISMA’IL ‘,Ya ce ga Alhaji Isma’il babban dan siyasa a jahar Bauchi, ta kasance ‘Ya ta Uku kuma ta karshe a gareshi Yayunta biyu Mace da Namiji, Yana Matukar Ji da Fateema Kasancewarta Auta kuma sunan Mahaifiyarsa, uwa uba ta kasance mara son hayaniya domin ko cikin mutane bata cika shiga ba.

 

 

Fateema ba za asata sahun farare ba kuma ba za asata sahun bakake ba,dagowa,mara jiki kyakkyawa ce dai dai gwargwado Mussamman da ta kasance mai fara’a a ko da yaushe.

 

A yanzu tana kokarin Xana Jarabarwarta ta Neco ne domin ci gaba da karatu kamar yadda ta da ra ayi haka ma iyayenta

 

Wannan kenan!

 

 

YUSUF ISMA’IL

‘Da ne ga Malam Isma’il Dan Kasuwa mai rufin asiri na shi daidai gwargwado, sannan shi kadai Allah ya ba su.

 

Isma’il ba fari bane haka kuma shima ba ace da shi baki wuluk ba, tare da matsakaicin tsayi daidai gwargwado.

 

Ya kammala karatun Secondary dinsa shekaru biyu baya kasancewar bai ci jarabawa ba ya sa shi kara zanawa awannan shekarar domin neman gurbi a jami’a tare da cika burin sa na kasancewa Likita.

 

Dalilin zuwan shi makarantar su Fateema kenan.

 

 

****Ci gaban labarin.

 

Duk da kasancewar Malami na aji amman hakan bai sa wannan yarinyar ta ci gaba da dallawa Fatema harara ba, Maryam ce ta ce, “Fateema wai kuwa ko kin lura da Zainab tun dazu ban da hararmu ba abun da take fa.”

 

 

Fateema ta ce, “Harara kuma? Ina ga ba da mu take ba,ki share kawai.”

 

Duk da cewa Fateema ta san da ita take amman ta zabi sharewan fiye da kulata.

 

 

Assignment aka ba mu Fateema take fadin, “Ni kam Wallahi ban gane ba fa sam ban san ya zan yi wannan assignment din ba.”

 

 

Yusuf ya ce, “ai kuwa yana da sauki da kin fahimta.”

 

 

“To Yayan Fateema ko zaka dan kara mana bayani don wallahi ko ni ban fahimta ba.” Cewar Maryam

 

 

Yusuf ya kalli agogon hannunsa kan ya ce, “Lokacin ta shi ya yi, amman mai zai hana kumin magana a Wtsp group kawai sai in kara maku bayani.”

 

 

Da sauri Fateema ta furta “to bani numberka.”

 

 

Nan ya bata numbersa ta yi saving dai dai da lokacin ta shi kuwa.

 

 

Tare muka fito daidai kofar ajin muka ci karo da Zainab tsaye ga dukkan alamu ta sa wani abu aranta.

 

 

Fateema ta ce, “Excuse Zainab za mu dan wuce.”

 

 

Tana dagowa ta dallawa Fateema mari

 

 

…..

 

 

Urs Xayyeesherthou

[2/13, 9:42 AM] Xayyeesherthul-humaerath: *DOCTOR YUSUF*👨‍⚕️

Gajeran Labari

 

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS*

 

 

LABARI DA RUBUTAWA:

*Xayyeesherthul-humaerath*

 

*SADAUKARWA GA, SIRRIN’YAMACE*

 

*MARUBUCIYAR:*

 

BABU RUWAN SO (FREE)

WASA DA SO (FREE)

AZZAWAJUL-MUKADDAR (FREE)

JAMEEL (200)

MATAR POLICE (200)

KUCHAKAR KISHIYA (FREE)

HAYATIY (FREE)

AMEENATOU (300)

KWADAYI (FREE)

ASHE HAKA SO YAKE (300)

SAI NA AURI MARUBUCI (FREE)

 

 

AND NOW

DOCTOR YUSUF

FREE

 

*TSOKACI: ban fara rubuta labarin nan ba sai da amincewar Dr. Don haka ban yarda a juya mun labari ta kowace siga ba,sannan labarin gaske ne illa wasu abubuwan da zan kara ko in rage,ban yi labarin nan da niyar tozarci ga kowa ba illa nishadantarwa mai cike da wa azantarwa ga wanda ya fahimta*

 

 

Page 3

 

Kuyi hakuri mantawa nake bana sa feji

 

 

 

______

Cikin Harzuka Maryam ta daga Hannu zata ramawa Fatima, da sauri Fateema ta dago tana, “Aa Maryam bar ta Don Allah.”

Ta karasa maganar tana rike mata hannu.

 

 

Har cikin Rana sam Isma’il bai ji dadin Marin da Zainab tai wa Fateema ba,domin a zahiri ma fuskar shi ta canja.

 

 

Tsaki Zainab ta yi tana ci gaba da Harar Fateema, “Wallahi da kin bari ta tabani, ba ruwana da matsayin Ubanki agarinnan in ya so karshen zance kusa a kasheni,tsinannu masu shan jini.”

 

 

Cikin tsawa Isma’il ya furta, “Enough na ce ya isa ko? Ka da ki kyetare iyakarki Malama.”

 

 

 

Fateema ce ta ja hannunsa da na Maryam su ka bar wajen.

 

 

Ita kuwa Zainab ta tsaya tsayuwar Mamaki,mai dauke da takaici.

 

 

Tun daga Ranar doctor da Fateema suka kara shakuwa,ya yin da a kullum ban da harara ba abun da ke hada Fateema da Zainab.

 

Kullum suna tare har ya kai ga Duk wanda ya riga wani zuwa sai ya jira dayan ya zo ashiga Lesson tare.

 

Gabadaya yan Class kowa ya san Fateema da Isma’il, in kana son bacin ran junansu to ka taba wani aciki.

 

Mussamman Fateema da ba ta kaunar Wata ‘ya mace ta raɓi Isma’il ko kadan,nan da nan za ta sauya yanayi.

 

 

Ko da sun koma gida, a weekend ko dare kullum ba sa da abun yi da ya wuce chatting da Kiran Waya.

 

Ya kasance har yan gidansu Fateema ba wan da bai san labarina ba,duk da kasancewar basu taba ganina ba,amman a kullum ban da hirata ba abuj da take.

_______Safiyar Monday da isa ta makaranta na tarar da Fateema na jirana kamar kullum.

Murmushi a fuskar tare da wata bakar leda,mika mun ta yi tana, “Yayana yau ka kusan makara sosai fa, na kusa yin fushi.”

 

 

Ba tare da na bata amsa ba na bude ledar mai zan gani?

 

Wani tsantsararen agogene da turare ido kadai ya isa baka amsar cewa ma su matukar tsada ne.

 

 

Na dago ina kallonta tare da bude baki.

 

Kan inyi magana ta ce, “Dadyne ya dawo daga tafiya ya kawo mana tsaraba, kuma Momy ta ce ka ki zuwa ku gaisa fa.”

 

Ta karasa maganar cikin salon shagwaba

 

Add Comment

Click here to post a comment