Agolah Hausa Novel Complete
AGOLAH!!!nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABIU ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)
SADAUKARWA!!!
Zuwaga dukkanin yan uwa da abokan arziki, ina me nuna farincikina gareku, Allah yabar zumunci, ameen.
Bismillahir Rahmanirrahim.
Part 1…..5
Agarin kaduna, cikin unguwar Sarki. Awani katon gida, nashiga domin dauko maku labarin cikin gidan.
Alhaji Abba Bala, hamshakin me kudine, yanada mata daya da ya,ya biyu mata, Sunan matarshi Hajiya Zarah, takasance yar garin zariya, diyace agurin Malam Garba da matarshi Asabe, kishiyar mamanta, ce, tana kiranta da inna, Asabe takasance mace me kissa, hakan yasa take zaune da Zarah tamkar ita ta haifeta, babu wanda yasan dalilinta nayin haka, talakawa ne acikin danginsu kaf Zarah ce kadai tayi sa,ar auran me kudi, dalilin haduwarsu kuwa lokacin da Alhaji Abba yaje zariya acikin unguwarsu Zarah, yaziyarci wani abokinshi, ahanyarshi ta dawowa yahadu da Zarah tadawo daga aiken da Innarta tayi mata, lokaci guda yaji yakamu da sonta, ahaka. Bayan sungaisa yanemi data nuna mashi gidansu, yayi mata godiya yatafi.
Matan Asokoro Hausa Novel Complete
Tundaga ranar soyayya tashiga tsakaninsu, kai tsaye yanemi izinin aurenta agurin mahaifinta, babu bata lokaci ya amshi bukatarshi.
Zarah Allah yayi mata son kudi, babu abinda ta tsana irin talaka, duk da Allah yayita acikinsu amma bata son su, ko taron danginsu akeyi bata shiga, hatta da iyayenta hakuri sukeyi da ita, tasha yin mafarkin ta auri me kudi, segashi Allah ya amsa mata addu,arta tasamu me kudin,
Zarah bata damu da ilimin addini ba, ko sallah bata damu dayiba, amma tunda suka hadu da Alh, Abba taboye duk wani halinta marar kyau, shi kuma duk farin ciki ya isheshi yasamu diyar gidan mutunci, duk da azahiri iyayenta suna da mutunci amma bata gado suba.
Ahaka akayi aurensu, aka kaita kaduna cikin unguwar sarki akaton gidanta, haka suka cigaba da rayuwarsu cike da so da kauna, hankalinta ya kwanta, arzikin mijinta se karuwa yakeyi, hutu ya zauna mata tuni fatarta, ta murje tayi kyau sosai, tuni ta manta da iyayenta da danginta, tunda akayi bikin bata zuwa garinsu sosai, sede idan mijinta ya matsa mata, shima sede suje tare kuma bazata kwana ba, ko bikin dangine bata cika zuwa ba, idan ma yabata kudin gudummuwa ko kwatar abunda yabada bata basu, gashi Allah yayi mata rowa.
Ahaka ta haifa mashi diyarta ta farko me suna Hauwa,u sunan mahaifiyarshice yasa dan duk iyayenshi sunrasu, dama shi kadai suka haifa, sede danginshi, hakan yasa aka sama diyarshi sunan mamanshi, ana kiranta da JIDDAH.
Bayan sunanta ne Alhaji Abba yabama Zarah kudi masu yawa yace tafara bussiness, kuma shine yayi mata jagora zuwa dubai domin fara kasuwanci, daga haka harta fara zuwa ita kadai, ahaka ne tahadu da wata mata me suna Hajiya Karima, itama babbar yar kasuwace, halinsu ne yazo daya dan danan suka kulla kawance, itama anan kaduna take. Kawancensu sukeyi sosai, Karima takara nuna ma Zarah duniya anan idonta yakara budewa takara koyon duk wata kissa, sede ita karima bata bin bokaye sede duk wata kissa ta iyata, shiyasa Zarah take zaune da mijinta lafiya, tana yimashi biyayya, saboda yana sakar mata duniya, ita kuma babu abinda takeso kamar kudi, tun bayan haihuwar Jidda taso tayi planing amma Karima tahana ta, acewarta tabari tahaifi namiji.
Bayan shekara biyu da haihuwar Jidda takara haihuwar diyarta mace, har kuka seda tayi, saboda bata samu namiji ba. Ranar suna yarinya taci sunan maman Zarah Saratu, ana kiranta da JALILA.
Tun daga lokaci Karima tarakata aka tsaida haihuwar acewarta karta tsufa dawuri. Haka yara suka taso cike da kulawa, sudukansu suna da kyau, sede Jalila tafi Jidda kyau, Ahaka suka shiga makaranta, Jidda na P. 1 aka saka Jalila, haka suka cigaba da karatunsu, harsuka girma, alokacin Jidda tana da shekara 18 Jalila tanada 16, alokacin Jidda tana ss 3, Jalila tana ss 1. Halinsu kwata kwata bezo daya ba, Jidda gab daya irin halin Umminsu tadauko, Jalila kuwa irin Halin Dadynsu gareta, tunda suka gama Primary Jidda tafita daga islamiyya, Jalila ce kadai take zuwa, sede Dadynsu besan bata zuwa ba, kasan cewar aiyuka sun mashi yawa, ga tafiye tafiye dayakeyi. Ita kuma umminsu bata damu da ilimin addini ba. Tun Jidda tana ss 1 tafara kula samari, duk wanda zekirata yabata kudi to zata iya binshi duk inda yace, so dayawa Jalila tana kawo kararta amma Umminsu bata daukar maganarta abakin komai, karshema sede takoreta, ahaka harta shiga ss3 alokacin tahadu da kawaye yan duniya tuni suka maida bin maza aikinsu, sede kawarta. Ameera tafisu duniyanci, hakan yasa takaisu asibiti domin suma ayimasu planing. Tun daga lokacin suke sheke ayarsu, kudi suke samu sosai, dayake Jidda tana bama Umminsu kudi hakan yasa tarufe mata baki, takuma zama yar gaban goshinta. Kullum Jalila setayi kuka idan taga halin da yayarta tasa kanta, amma sanin kotayi magana babu wanda ze kulata yasa tayi shiru , saboda Zarah taja mata kunne akan idan har tafada ma Dadynsu wata magana akan Jidda seta tsine mata. Addu,a kawai takeyi mata, sannan ta maida hankalinta akan karatunta na boko dana islamiyya.
Alh. Abba ne yafito cikin shirinshi na tafiya sokkoto. Matarshi da yaranshi biyu, suka rakoshi har bakin mota. Alh, yace to Hajiya nizantafi akula da gida, insha Allah gobe zandawo, kallon yaranshi yayi yace ku kula da karatunku ina fatan babu wata matsala ko? Jidda tayi saurin fadin dady kayan kwalliyarmu sun kare, dariya yayi yace toga dubu 20 nan ai sun isa ko? Karba tayi tana dariya, Jalila tace dady mungode Allah yakara budi. Allah yatsare hanya, sosai yakejin dadin addu,ar da Jalila takeyi mashi aduk sanda yatashi yin tafiya, ita kuwa Jidda tuni tajuya tanufi gida tana murnar samun kudi, daga nesa take fadin dady seka dawo ayo mana tsaraba. Murmushi yayi ya girgiza kanshi yace toni zan wuce, Zarah ta rungumeshi tana fadin seka dawo mijina, Ganin haka yasa Jalila tayi mashi sallam itama ta juya, kiss yayi mata agoshinta yana kara rungumeta, anan yakara mata bandir guda na 1k yace kozata nemi wani abu kafin yadawo. Godiya tayi mashi sannan yashiga motarshi yawuce.
Dayake tafiyar batayi mashi sauri ba, kasancewar tsaye tsaye dayayi kuma dama befito gida dawuru ba, hakan yasa beshiga sokkoto dawuriba segurin karfe 8 na dare, kaitsaye yawuce gurin wadda yazo, dan agobe yakeso yakoma, shiyasa seda yaje yagama abinda yakawoshi sannan yawuce masaukinshi, misalin karfe 9: 30, dayake awajen gari masaukin nashi yake, yafito daga cikin gari tun daga nesa yaga kamar ana tsaidashi, sede beda niyar tsayawa, dan yasan halin yan, fashi babu abinda basayi inde suna son sutareka, haryawuce yaga kamar mata guda biyu ne abikin titin wadanda suke tsaidashi, gani yayi sunata waigen bayansu gashi daya daga cikinsu ta tsugunna kasa kamar tana kuka ganin yawucesu.
Cikin sauri ya taka burki yakoma baya, suna ganin ya tsaya da gudu daya takama hannun dayar suka nufi gurinshi, tambayarsu yafarayi, amma cike dasauri suka bude bayan motar suka shige. Dakyar take magana, dan Allah bawan Allah katemakemu kayi nisa damu daga gurin nan, wlh sunbiyo mu zasu kashemu…… Ai dajin haka yatada mota yafisgeta suka bar gurin, lokacin damasu binsu suka iso ko alamarsu basu gani ba, haka sukaita dube dubensu, ganin dare nayi suka juya domin komawa gurin Ogansu.
Urs
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
Nabeela lady:Â AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 5…..10
Parking yayi adede wani karamin gida, inda yakasance masauki agareshi aduk lokacin dayazo sakkoto, fita yayi suma suka, fito, tsayawa sukayi suna kallonshi, ahankali yace bansan ina zan kaiku ba, kuma gashi dare yayi, duk da kunce infitar daku wajen gari, agaskiya bazan iya kaiku ba, saboda dare yayi kuma gashi ku mata ne, idan harkun yarda dani kushigo ciki ku kwana idan Allah ya kaimu gobe semusan abinyi, domin nima ba,a garin nan nake ba, wani aiki yakawoni yau, kuma nagama gobe zankoma kaduna acan nake da iyalina.
Kallonshi babbar ciki tayi nawani lokaci sannan tace bakomai munyarda da kai. Bude masu gidan yayi bayan sunshiga yakoma yakwaso kayan cikin motar daya siyo, yashigo ya kulle gidan, zaune suke afalo, shima zama yayi sannan yace. Ga dukkan alamu kuna dauke da yunwa, sede abinci beda yawa kaza ce da lemu nasiyo se biredi, kucinye kawai gobe idan nafita nasamo mana abinda zamu karya dashi, matar tace mungode sosai, amma yanzu abinda kedamuna bamuyi sallar magriba da isha,i ba, murmushi yayi yajinjina irin addini na wannan matar, daganinsu kasan suna tare da yunwa, amma duk da haka take maganar sallah.
Dakinshi ya nuna masu yace akwai bandaki aciki idan sungama ga abin sallah nan, bayan sunshiga shi kuma yazauna afalo yana tunaninsu, yakosa sugama abinda sukeyi ya tambayesu labarinsu.
Babbar matar takalli yarinyar dasuke tare, da alama diyarta ce saboda tsanin kamar dasukeyi, tace kishiga ciki kiyi wanka sannan kiyo alwala, zama tayi tajirata, har tagama tafito sanye da kayan data cire, daukar hijabinta tayi ta kabbara sallah,ita kuma uwar tashiga domin yin wanka.
Motsi yaji yasashi saurin dagowa, ganinsu yayi sunfito tsaf dasu, anan take ya iya hango kyawun dake tare dasu, duk da akwai alamun walaha atare dasu hakan be hana kyawunsu fitowa ba, musamman dasukayi wanka suka fita daga cikin dattin dasuke, duk da basu canja kaya ba.
Abinci yadauko masu yamika masu lemu da ruwa harda biredin, murmushi babbar tayi tace da alama kaima bakaci komai ba, kuma gashi kabamu duka, kadebi kazar semu hada biredin, yace a,a kude kuci ku koshi tace Allah bazamu iya cinyewa ba, bata jira abinda zece ba, ta deba mashi kazar dan tana da girma ta mika mashi da biredin, amsa yayi yana mata godiya, murmushi kawai tayi takoma kusa da diyarta suka fara cin tasu, shide ci kawai yakeyi amma hankalinshi yana kan wannan matar, addu,a kawai yakeyi acikin ranshi Allah yasa bata da miji, dan tunda tafito yaji wani irin yanayi akanta.
Bayan sungama takwashe kayan tasa aleda ta kaisu cikin dustbin tasaka, kalon diyarta tayi taga tana gyangyadi, Alh, yace yan mata bacci kikeji kije ki kwanta, murmushi tayi tace to Dady, sosai yaji dadin yanda takirashi da dady, tashi tayi tamasu seda safe tashige daki, matar tace Alhaji kai kuma a ina zaka kwana? Murmushi yayi yace bakomai anan ma ya isheni, zama tayi akasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsunta.
Shima kasa yasauko dan nesa da ita kadan, yace duk da bansan sunanku ba, daga ke har diyarki kiyi hakuri kifadamun labarinku dan bazan iyayin bacci ba idan har banji dalilin dayasa akeso akasheku ba. Idan har babu damuwa inasonjin labarinku, dan Allah.
Hawayen dake idonta ta goge tace tabbas Alhaji ka cancanci kaji labarinmu, domin katemakemu kuma nayarda da kai.
Nide sunana HAJARA amma anfi kirana da HAJJO kasancewar mudin fulanine, Wannan kuma diyata ce sunanta FALAK, kuma ita kadai Allah yabani, mijina Allah yayi mashi rasuwa yau wata 5 kenan. Ajiyar zuciya yayi aranshi yana fadin Alhamdulillah.
Asalin labarin HAJJO……………
Ita kadai Allah yabama iyayenta, kuma su fulanin daji ne, basu da taka maiman garin zama, ako da yaushe suna. Canza gurin zama daga wannan guri zuwa wannan, tun bayan auren Baffanta da Innarta suka bar garinsu wanda yake acikin niger, dan sunkasance fulanin niger, haka suka rika yawo gari gari tare da Shanunsu, duk inda sukaje sukan kafa bukkarsu agurin suzauna har zuwa wani lokaci, idan sun gama sesu tashi zuwa wani gari, acikin haka har suka haifi Hajjo, wanda sunan innar Baffantane aka samata.
Lokacin da Hajjo tayi girma har takai sheakara 10 alokacin suka yada Zango acikin garin gusau, acan bayan gari suka kafa bukkarsu tare da wasu yan uwansu fulani dasuka hadu ahanya, koda sukaje gurin sunsami fulani dayawa agurin, anan Baffa yaji dadi, dan tunda suke yawo basu taba haduwa da fulani dayawa kamar wannan ba, anan suka zauna suka cigaba da kiwonsu, inda Inna yakeyin fura da nono tana dora ma Hajjo tana bin sauran sa,anninta zuwa cikin gari sukai talla.
Baffa dakanshi yayi sha,awar saka Hajjo makarantar boko kasancewar yaga wasu daga cikin yaran gurinsu suna zuwa, ahaka wani abokinshi jauro yayi mashi jagora zuwa makarantar da diyarshi take, shima yasaka Hajjo.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya gwanin dadi, su Hajjo suna zuwa makaranta, ranar da babu karatu kuma sutafi cikin gari talla.
Ahaka harsuka gama primary alokacin Hajjo tana da shekara 16, kyawunta yakara fitowa sosai, kowa sonta yakeyi, watarana suntafi kasuwa ita da kawayenta domin aranar kasuwa takeci, sunje kai talla
Tunda sukaje kasuwar ta lura dawani yanata kallonta, ahaka harsuka saida suka siyi abinda zasu siya suna shirin tafiya gida. Sallama taji anyi mata, amsawa tayi tare da juyawa domin ganin me mata sallama, wannan wanda tagani yana kallonta shine de tare da abokinshi.
Sannunku yanmata yace yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, bayan sun gaisa yake tambayarta sunanta, tace Hajjo, murmushi yayi yace Hajara kenan, amma sunan akwai dadi, ni sunana Bashir, kuma ni dan sakkoto ne, ina zuwa nan duk ranar kasuwa, amma Allah betaba jadamu ba, se yau, murmushi tayi tace zanwuce abokan tafiyana suna kirana kada dare yayi, kallon abokinshi yayi yace to abokina nima tafiya zanyi dan banason dare yayi saboda barayin hanya, dan Allah kabisu Hajjo kaganemun gidansu idan nadawo sati mezuwa kwana zanyi seka rakani. Godiya yayi masu sukayi sallama.
Tundaga wannan lokacin soyayya tashiga tsakanin Bashir da Hajjo, har iyayenta sun san dashi, Baffane yace ma Hajjo idan Bashir yazo yanason ganinshi.
Zaune suke abisa tabarma, anan Baffa yake tambayar Bashir asalinshi, Yace nide sunana Bashir, kuma ni dan asalin sakkoto ne, iyayena sun rasu tun ina dan shekara 20, banida kowa se kawuna, agurinshi nake kuma gida daya muke dashi, kasuwanci shine sana,ata ina zuwa garuruwa kasuwanci, kuma a sakkoto gidana yake wanda mahaifina ya mutu yabarmun.
Baffa yace Alhamdulillahi, anan shima yafadamashi alabarinsu, sannan yace tunda naganka naji hankalina ya kwanta da kai, kuma nabaka Hajjo, ko yaushe kake so adaura maku aure zaka iya zuwa, sede inaso dan Allah karike mana Hajjo bisa gaskiya da amana, ita kadai Allah yabamu, kuma kaga bamuda kowa anan, gashi ba gari daya zamu zauna ba, kasan mudin makiyaya ne, inaso karike mani ita, kuma dan Allah karika kawo mana ita duk sanda zaka zo kasuwa, kafin mutashi daga nan, duk da gaskiya bayanzu zamu tashi ba, dan naji dadin zaman gurin nan.
Bashir yace insha Allahu Baffa zaka sameni me riko da amanar daka bani, kuma insha Allah sati mezuwa tare da kawuna zamuzo se adaura mana aure, banaso ku wahalar da kanku, Hajjo kadai nake so, saboda haka kada kusiyi komai. Godiya Baffa yayi mashi sannan yatashi yakira mashi Hajjo.
Bayan sati guda Bashir yazo da kawunshi Wanda yake kanin mahaifinshi dasuke uba daya, sunanshi Lado, amma mutanan gari suna kiranshi da Figo. Kasancewarshi cikenken dan duniya, danshi haryanzu beyi aure ba,sede lalata yaran gari, beda wata sana,ar data wuce shaye shaye da sata, shine oga acikin group dinsu, dan har yara gareshi. Bashir hakuri kawai yake dashi, tunda agida daya suke, sede shi kawu Figo adayan part din yake.
Bayan andaura aure aka shirya Hajjo cikin dinkunan da Bashir yakawo mata, sosai tayi kyau ahaka sukayi sallama da iyayenta suna kuka tafito, kawayenta suka rakota, harbakin mota suka kaita, suma kukan sukeyi ahaka suka tafi, ita kada abaya Bashir da kawu agaba, Bashir ke tuka motar. Tunda Kawu yaganta yake hadiye miyau yana murmushi aranshi yana fadin tsuntsu daga sama gasashshe.
Bayan sunje gida ya aje kawu sukuma suka shige gidan, gidan yayi kyau sosai, komai yasaka aciki kayan more rayuwa masu kyau yasa mata.
Ahaka sukaji gaba da rayuwarsu cike da so da kauna, komai najin dadi Bashir yanayi mata, sosai yake taka tsan tsan da gidanshi, saboda kawu, dan yafikowa sanin halinshi, ko abincin da Hajjo take bashi be bari takai mashi shine yake bashi da kanshi, idan kuma tafiya takamashi sede yakai Hajjo gidan abokinshi Saddik ta kwana, duk yanda kawu yaso kebewa da Hajjo Bashir yahana, idan yashigo gidan sede idan Bashir yana nan. Duk sanda zeje gusau cin kasuwa tare da Hajjo yake zuwa, sosai Hajjo tayi kyau, takara girma.
Bayan shekara biyu da aurensu tahaifi diyarta me kama da ita sede Allah yayima yarinyar kyau sosai, tun tana jaririya, ranar suna Bashir yasa mata FALAK, dan yace yana son sunan sosai.
Tunda FALAK ta girma yasata a primary, ranar dazeje gusau tare suka tafi, kwnansu 2 sannan sukafara shirin dawowa, Inna tadauko wasu awarwaro masu kyau guda biyu ta bama Falak, kasancewar sun mata yawa yasa Hajjo ta amsa tasaka a hannunta, haka taji kamar karsu tafi, Baffa yakara tunama Bashir akan rikon amanar daya bashi, haka sukayi sallama suka tafi.
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
Nabeela lady:
AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 10…..15
Ahaka rayuwarsu taci gaba da tafiya, Falak tagama primary tashiga secondary school, kyawunta sekara fitowa yakeyi, Hajjo har tsoro takeyi idan Falak zata fita, shiyasa bata barinta zuwa ko ina daga makarantar boko seta islamiyya, haryanzu Kawu besamu damar biyan bukatarshi ba, sede ya matsa ma Bashir lamba akoda yaushe cikin karbar kudi yake, da Bashir yabashi jari zecinyesu, yakuma dawowa, tunda yaga Falak tafara girma kwadayinshi yakoma kanta, sede yakasa samun hanya.
Lokacin da Falak tagama Jss 3 suka shirya domin zuwa ganin gida, tare da Bashir suka tafi amotarshi.
Mamaki ne yakamsu lokacin dasuka isa bukkokinsu Baffa, babu komai agurin, yakoma fili, kasar gurin duk tayi baki. Kuka Hajjo tafarayi Bashir yanata lallashinta, haka yajuya yanufi cikin gari gurin abokinshi.
Bayan sungama gaisawa abokinshi yace ai wata rana ne da dare yan fashi suka sauka a bukkokinsu Baffa, suka kwashe masu Shanunsu da duk wasu dukiyarsu, sannan suka tarasu aguri guda suka samasu wuta, babu wanda ya tsira acikinsu.
Kuka sosai Hajjo da Falak sukeyi, Bashir ma duk dauriyar shi seda yayi kuka, sosai ya tausaya ma Hajjo, ahaka yayi ma abokinshi sallama suka juya, tunda sukaje gida yake aikin lallashin Hajjo, kuma yayi mata alkawarin bazatayi kuka dashi ba, da haka yasamu ta hakura.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya, arzikin Bashir se kara habaka yakeyi, dan yanzu yadena zuwa gusau Lagos kadai yake zuwa, tunda suka Haifi Falak basu kara samun haihuwa ba, Hajjo taso suje asibiti amma Bashir yace a,a haihuwa ta Allah ce tunda sun samu daya ma ai sungode.
Falak tana ss 2 ayanzu, bangaren islamiyya kuwa gab take da saukewa
Awannan lokaci tana da shekara 16, takara zama budurwa, komai natana yafito, hakan yasa iyayenta suka kara saka matakan tsaro akanta, dan kawu yace arika bata abincinshi tana kai mashi amma Bashir yahana.
Acikin yaranshi akwai babban yaronshi me suna Idi ana kiranshi da Jungle, shine yake bama Kawu shawarar yasa su sato mashi ita yabiya bukatarshi kawai. Kawu yayi murmushi yace kabari akwai tarkon danake dana ma Bashir saboda yanzu yaga yayi iyali shiyasa yamaidani abaya, duk wasu kadarorinshi yasaka sunan yarinyar nan ajiki, ka kyaleni dashi, yacemun zeje lagos, kuma nayi mashi magana akan inason wasu kudi masu yawa, inaso yabani su sannan in aikata mashi. Dariya suka sa gaba daya.
Zaune suke adaki Bashir yace Hajjo wlh kawu ya matsamun, gani yake kamar wasu kudade gareni, shiyasa yake tambayata kudi akai akai, mika mata wasu takaddu yayi da check na banki yace wannan takaddun gidan nan ne, wannan check din kuma na bankin Falak ne, domin aciki nake ajiye duka kuda dena,inaso kiyi masu boyo sosai, dan nayi alakawrin bazan kara bama kawu kudi masu yawa ba, koda yaje yaduba account dina baze samu komai ba, dan besan da wannan account din na Falak ba, tunjiya dana dawo daga Lagos yakeson ganina ni kuma boyewa nakeyi, se dazu yamun maganar kudi nace mashi banda kudi nayi asara sosai, yanzu mota ta ma zansa kasuwa insamu inbiya mutane kudinsu.
Haka yatashi yatafi yana bambami, tashi Hajjo tayi taboye. Abinda yabata sannan tadawo kusa dashi tazauna tace Dadyn Falak hakuri zamuyi da halin kawu, ni kaina ina tsoron shi wlh, kana ganin irin yanda yake sakama Falak ido, banaso wata rana yayi mata………. Bata karasa maganar datakeyi ba, sukaji an banko kofar dakin, wasu mutanene suka shigo , kuka Hajjo tafara tana fadin shikenan munshiga 3. Marin da,aka yimata ne yasata yin shiru, anan suka kama Bashir suka daureshi da Igiya, kukan Falak suka jiyo abakin kofa, dasuri tafada jikin ummanta tana kuka, abinda suka ganine yanasu mamaki, Kawu ne yashigo yana dariya.
Bashir yace kawu me muka yimaka arayuwa? Duk irin yanda nake yimaka biyayya amma baka gani, dariya Kawu yayi yace dama ai nafada maka, sbd haka yanzu zankashe ka kuma inmaida matarka da yarka dadirona, dan kasan tunda ka aurota nakejin kishinta, amma ka tare komai, ahaka har ta haifi yarinya me kyau, wadda naji bazan iya hakura da ita ba. Kuka sosai Bashir yakeyi sbd abinda yaji Kawu yana fada, ahankali yace kawu dan girman Allah kayi hakuri, wlh kome kakeso zanbaka kada kayimun haka, Kawu yace aikin gama ya gama, Bashir, yanzu da dukiyarka da iyalanka duk sun zama mallakina.
Zeyi magana kenan, Jungle yakwantar dashi, hanin yafiddo wuka yasa Hajjo da Falak suka matsa kusa,da kawu suka kama kafarshi suna kuka suna rokonshi, karar dasukaji ne yasasu juyawa. Kwance suka ga Bashir cikin jini Jungle yayi mashi yankan rago.
Anan take Hajjo tafadi kasa asume. Kanta Falak tayi tana kuka,
Anan kawu yasa su Jungle, suka dauki gawar Bashir yace suje can cikin daji su gina rami su rufeshi, bayaso subarshi batare da sunrufe shiba.
Bayan awa 2 su Jungle suka dawo, afalo suka iske Hajjo da Falak adaure se kuka sukeyi, anan kawu yace masu suje su kwaso mashi kayanshi su dawo mashi dasu nan, yace kasan yanzu nine megida, anan zan zauna har Hajjo tagama iddarta sannan na aureta, ita kuma Falak sa daka zanyi da ita. Dariya suka sa gaba daya, Jungle yace Oga tunda kadauki uwar dani kabama diyar ai.
Hade fuska kawu yayi yace banaso kana kawomun wasa acikin iyalina. Dariya suka kara sawa. Kawu yace jungle gobe kaje gurin malamin can katambayomunshi Shekara nawa macen da mijinta ya mutu takeyi kafin takara wani auren.
Dariya jungle yayi yace haba Oga ai sekasa ayi mana dariya kamata inje ina tambayar yanda ake idda, kasanfa nima nayi islamiya. Kawu yace yauwa, shikenan ma, fada mana muji, dan data gama zamuyi aure, kasan komai inaso inyishi yanda Allah yace kada inyi aure akan aure.
[…] Agolah Hausa Novel Complete […]