Nata Matar Aljan Hausa Novel Complete
*NATA…*
Matar Aljan🤡
Gajeren labari
MRS SADAUKI 💫✍️
FCWA ☀️
Masu jiran complete na *SEEYA* ku garzayo na kammala duk wacce ta shirya saya ta tuntuɓe Ni ta WhatsApp +22795045822
1
A duduƙe yake tafiya ya na sakin layi tamkar tsohuwar mota mai maras burki.Kayan jikinsa duk sun tamiƙe saboda tsufa haɗi da datti.
Bakinsa sai zubar da yawu yake,yayin da idonsa suka shige can ciki tsabar tsufansa.Tsoho ne tuguf,zai haura shekaru ɗari da talatin.Ya tsufa sosai har ta kai shi da riƙe sanda don taimaka masa wajen tafiya.
Alkama Bisa Dutse Hausa Novel Complete
Bakin titi ya tsaya ya na kallon kwalta,yadda ababen hawa ke zirga-zirga ya saka ya ji wani abu ya tsarga masa a rai.
Nutsatsin idonsa ya juya wani baƙin hayaƙi ya fito ya daki kwalta,ko minti ɗaya ba ayi ba aka yi hatsari tsakanin mai babbar mota da wani mai mashin.
Abun babu kyawun gani yadda jini ke malala kan kwalta.
Tsohon nan na tsaye ya na dariyar ƙeta wacce kusan a cikin jininsu yake.A hankali ya fara takawa don ƙarasawa wajen da aka yi hatsarin kamar yadda duban jama’a ke tururuwa zuwa.
Kutsa kansa yake cikin mutane,”kai jarababen tsoho ina kuma za ka je? Mutane na gudun yin baƙin gani kai sai wani kutsa kai ka ke.Tsofi ire-iren ka su na can gida su na hutawa domin jiran mutuwarsu amma kai ka fito da wannan tamiƙaƙen jikin naka mtsw” wani ɗan sanda ne ya faɗa cikin masifa ya na mai ture tsohon har sai da ya faɗi ƙasa.
ACP Khalil kenan,matashin police mai jini a jiki in ka na son ganin karkashinsa to a samu case inda za a zuba rashin mutumci.
Mutum ne maras tausayi,baƙin ciki da hassada su ne manyan-manyan jigon rayuwar shi.
“Kowa ya watse mu fara aikin mu” Khalil ya faɗa cikin tsawa,nan kowa ya dare aka basu gu.
Tsohon nan na kwance tunda Khalil ya ture shi,ganin za su fara aiki yasa shi buɗe baki cikin muryar tsoffi “ku taimaka ku miƙar da ni tsaye ban iya tashi,yarona ka tayar da ni” ya faɗa ya na mai miƙa ma Khalil hannu.
Cikin hassala Khalil ya ce “ku ɗauke shi ku saka mini shi a mota”
“Yalaɓai mota kuma?” Wani daga cikin ƴan sandan ya tambaya,mugun kallon da Khalil ya watsa masa ne ya sa shi yin shiru ya je suka cika umarninsa.
Bayan sun gama Coster ya bada umarnin a ɗauke gawar da kuma mashin ɗin,har za su tafi Khalil ya lura kamar jinin da ya zuba a kwalta ya ƙafe alhalin ba a wanke gun ba.
Bai wani damu ba ya shiga mota suka wuce,cikin ɗaki mai zarnin fitsari ya ce a saka tsoho.
Zaune ya yi kan kujera ya kunna sauti ya na saurare sai wani gyaɗa kai yake kamar ƙadangare.
Wayarsa ce ta ɗau ruri,”hello Sweety” daga can ɓangaren aka ce “Khalil ka zo gida please”
“Mine ne? ”
“Kai dai kawai ka zo za ka ga ko ma mine ne”
“Hum! Linda ban san lokacin da za ki girma ba,ok gani nan zuwa” ya na gama faɗa ya kashe kiran.
Daga inda yake zaune ya na iya hango tsoho wanda tun ɗazu shi yake kallo duk wani tarihi na dangane da Khalil ya karance shi kaf.
“Ka ci sa’a zan tafi gida ne da wlh sai na koya ma hankali ta yadda gobe ko an ce ka fito ba za ka fito ba ” Khalil ya faɗa ya na hararen tsoho bisanin yasa a buɗe shi.
Ya na daf da shiga motar shi ya ji muryar tsoho “Khalil???” Cak ya tsaya tare da juyowa,cikin sauri tsoho ya tako izuwa gare shi ya ce “ka ci sa’a da ban kwana a celle ba da wlh sai na koya ma hankali ta yadda ko gobe aka ce ka kama tsoffi irina ba za ka kama ba”
Khalil sake da baki yake kallon tsoho,ya kasa cewa komi har sai da tsoho ya fice.
Ya ja ajiyar zuciya,ta ya aka yi ya san sunan shi? Bai damu da ya yi ma kansa wannan tambayar ba ya shige motar shi.
Kamar wanda aka yi ma doli haka Khalil ke ware ido ko Allah zai sa ya ƙara ganin tsoho sai dai wayam babu ko da sawun shi.
Nan ma ya kamata ace ya yi lura da hakan,don da fitowar shi bai kai ace ya yi nisa ba amma Khalil ya share ya isa gida.
Horne ya yi ya na jiran mai gadi ya buɗe masa,ta cikin mirror ɗinsa ya tsinkayi tsoho can bayansa kaɗan.Wannan karon kuwa Khalil sai da ya ɗan farga domin sai da ya fito daga mota amma fa bai gansa ba.
Ya yi tsuki ya koma motar shi tuni mai gadi ya buɗe get,Khalil ya cinna hancin motar ciki.Kamar an ce ya duba mirror idonsa ya kai nan kuma ya ƙara yin tozali da tsoho ya tafiya.Ko parking mai kyau bai yi ba ya fito,ƙofar gida ya je ya duba bai ga tsohon ba da har yanzu.
Khalil ya dafe goshi,ya shirin shiga cikin gida ya ji wani iska mai ƙarfi ya gifta ta gaban shi.
A ɗan dame ya shiga ɗaki ko sallama babu, Linda wacce ke cikin rigar da wando na jeans ta rugo da gudu ta rungume shi.
“Welcome Sweety” ta furta haɗi da sumbatar shi,duk wata damuwa da Khalil yake ciki ta na gushewa wane a duk lokacin da yake tare da Linda saboda yadda yake mugun sonta.
“Sweetyna mi ki ka shirya mini ne haka?” Ya tambaye ta ya na ɗan juyi da ita.
Ta yi dariya ta na mai cewa “zo ka gani”direta ya yi a ƙasa ita kuma ta ja hannunsa izuwa bedroom ɗin su.
“Waooo! ” Ya furta ganin yadda ta yi ma ɗakin ado sosai,hatta bed ɗin an zuba masa jajayen furanni.
Khalil ya ware idonsa da kyau ya na kallon surprise ɗin da matar shi ta masa.Ya juyo ya kalleta sai ya ga ta na hawaye,”kuka kuma Sweety?” Ya tambaye ta,sai ta saki murmushi ta ce “na murna ne mu je mu yanka cake”ta jawo hannunsa suka dawo falo kafin ta buɗe frigo ta ɗauko cake wanda aka yi ma zanen love.
“Barkar da zagayowar shekarar aurenmu” ta furta ta na murmushi har dimple ɗinta ya lotsa.
Khalil ya ɗora hannunsa kan Linda suka yanka cake ɗin cike da farin ciki suka shiga baiwa junansu.
Tsoho wanda ya biyo bayan Khalil ya na daga bakin ƙofa ya na kallon komi.Wani baƙin ciki ya turniƙe shi,a duniyar bil’adama babu abin da ya fi tsana kamar ya ga masoya na cikin farin ciki.
Ya yi murmushin mugunta kafin ya matsa izuwa gare su.Yawunsa ya zuba cikin cake ɗin,su kuwa sai ci suke ba tare da sun sani ba.Cike da shauƙin so Khalil ya ɗauki Linda cak,toilet ya kai su ya masu wanka.Duk inda suka shiga tsoho na take masu baya,Khalil ya dire Linda kan bed su ka shiga raya sunnah babu Bismillah balle zancen addu’a.
Tsoho ya yi tsaye ya na kallonsu,yau ne karon farkonsa da ya taɓa ganin yadda bil’adama ke kasancewa da junansu.
Cike da mugunta ya yi surkulen shi domin zafafa sha’awar Linda.
“Sweety” ta furta kafin ta ƙara jawo hankalin Khalil su ƙara tsunduma kogin ma’aurata sai fa dai ita sam ba ta ji ta wani gamsu ba.
“Na gaji Sweety ki bari har gobe ko zuwa dare” Khalil ya faɗa,”ban gane ka gaji ba? Khalil!” A zafafe ya ce “ke dallah nace miki na gaji haba!”
Linda ta waro ido don yau ne karon farko da Khalil ya taɓa ɗaga mata murya.
Tsoho ya bushe da dariya kafin ya zuga Linda,kawai samun kanta ta yi da jefa ma Khalil wani cadre ɗin hoto.Ya dafe ƙirjinsa,sai kuma ya duba hannunsa wanda tuni ya ɓace da jini.A hassale ya fara jibgarta kamar wanda Allah ya aiko sai da ya yi mata liƙis sannan ya farga da aika-aika da ya yi.
“Innalillahi ! Mi ya shiga kaina ni Khalil ? Sweety ? Sweetyna?” Khalil ya faɗa ya na mai jijiga Linda….
[06/03, 7:40 am] +234 803 496 8241: *NATA…*Matar Aljan🤡
Gajeren labari
MRS SADAUKI 💫✍️
FCWA ☀️
2
Linda ta ture shi cikin kuka kafin ta shiga toilet,cikin bawon wanka ta zauna tare da fashewa da wani matsanancin kuka.
Tsoho ya biyo bayanta,daga bakin ƙofa yake kallonta .Daga inda yake a tsaye ya ƙare ma surar jikinta kallo sai ya ji wani abu ya tsarga masa amma kuma sai ya yi saurin fita kansa ganin wani tambari a damtsenta.
‘Masarautar Kikidemi tabbas wannan tambarinta ne in ban manta,kenan ita ƴar sarki ce? To mi ya kawota Cameru?’ tsoho ya yi kansa tambaya bisanin ya ƙare waro ido domin karanto duk wani tarihinta.
Linda Ƴa ga Sarkin Kikidemi,wani yanki da ke cikin côte d’ivoire.Ƙauye ne mai tarihi sosai,domin yankin ne mai ɗauke da jinsi biyu.Mutane da kuma Aljan-mutum.Ana kiransu ne da Aljan-mutum saboda siffar mutane gare su amma su na ɗauke da manyan fukafukai domin har tashi suke sama.
Garin kaf ɗinsu mashurukai ne babu musulmi,duk yawancinsu bautar gumakai suke da aljannu.Ɓangaren tsafi da asiri su ne lamba ɗaya,don har hira da mutanen da suka mutu suke yi.
Linda ita ɗaya ce Ƴa tilo ga sarki Bahar, azzalumi gwani wajen yin siddabaru don aljannu su ne fadawansa wannan ya saka ya yi zarra sosai.
Wata dariyar mugunta tsoho ya fashe da ita da ya fahimci wani mugun ƙulli wanda kusan Linda da shi kansa mahaifinta ba su san da shi ba.
Jin an taɓa ƙofa tsoho ya ɗan ja da baya,Khalil ne ya shigo toilet ɗin.
Wani tunani ya faɗo masa a rai,da sauri ya bugi kan Khalil shi kuwa kamar wanda aka tsikara ya ce “kin wani zo nan ki shige cikin bawo,kullum ki na toilet ke ga uwar tsafta amma jariri ma kin kasa haifa mini saboda tsabar mugunta”
Linda ta ɗago ta kalle shi cike da mamaki,wato yau Khalil ke yi mata gorin haihuwa? Da ta so yin shiru amma baƙin hayaƙin da tsoho ya busa mata yasa ta yin magana a zafafe “to kai mi ya hana ka yin cikin ka haihu? Wa ya sani ma kai ne juyan”
Kamar wasu kaji nan suka shiga cacar baki bisanin Khalil ya ce “na gaji da wannan lamari doli ki shirya mu tafi asibiti yanzu ba sai gobe ba”
Linda ta ja tsuki bisanin ta fara wankanta,shi ma wankan ya yi.
Kamar wasu maƙiyan juna haka suka shirya suka tafi asibiti.
Khalil ya yi ma likita bayani bisanin a ɗebi jininsu domin gwaji.
Su na nan zaune Dr ya fito “dukkan ku babu wanda ke da wata matsala lafiyar ku lau,sai dai jiran lokaci”
“Amma Dr tsawon shekaru uku kenan da mu ka yi aure fa”
“Eh lafiyar ku lau don ba ma sai an baku magani ba”
Godiya suka yi suka fito,Linda ta shiga mota ta zauna ta na jin kanta na mugun ciwo.
“Hum!” Khalil ya yi bisanin ya yi ma mota key.
Linda ta dube shi ta ce “ya aka yi?”
“Komi!”
Daga nan babu wanda ya sake yi ma kowa magana har suka isa gida.
Linda ta toshe hancinta saboda wani irin wari da ta shaƙa,da sauri ta yi baya ta na duduba ko ina na ɗakin.
Cake ɗin da suka gama yankawa ko awa ɗaya ba ayi ba shi ta hanga ƙuda na bi yayin da kuma duk ya ruruɓe ya yi baƙi.
“Warin mi nake ji?” Khalil ya tambaya lokacin da ya shigo ɗakin shi ma.
Da hannu Linda ta yi masa nuni da cake, Khalil ya ɗan waro ido ya ce “mi ya samu cake ɗin? ”
“Ni ma ban sani ba” ta bashi amsa.
Mai gadi Khalil ya kira ya fitar da tray ɗin da ke da cake.Duk da an fitar da shi ɗakin wani wari yake har yanzu,labule ta ɗage sannan ta fesa turare.
“Ƙila fulawar ce ba mai kyau ba” cewar Linda ,ba ta rufe bakinta ba Khalil ya nufi toilet da gudu .
Daga inda take ta iya jiyo kukan zawon da yake ketawa,Linda ta tuntsire da dariya sai dai da sauri ta gintseta jin cikinta na juyawa kamar ana kiɗa.
Toilet ɗin waje ta nufa,ita ma zawon ta yi.
A gajiye duk suka zube kan kujerun tsakar falo.Duk sun yi wani zuru-zuru musamman Linda ita da ba ta da jumurin ciwo.
Khalil ya kira likitansu ya zo har gida ya yi masu allura,ita kuwa Linda har da ƙarin ruwa.
Ba a jima ba bacci ya ɗauke ta ,ganin ta fara bacci baba tsoho da ke rakuɓe tun ɗazu ya na kallonsu su na saffa da marwa ya matsa kusanta.
Daidai kanta ya zauna tare da ɗora hannunsa kan goshinta.
Cikin bacci Linda ta ganta a wata duniya,wata ƙatuwar masarauta ce gabanta mai ababen tsoro.
Ta na shirin shiga ta ji wata murya a bayanta ta kira ta “Ammy!” Ta juyo da sauri sai ta ga wata Baby wacce ba za ta wuce wata biyu ba a duniya amma ta na tsaye kan ƙafafunta.
Linda ta ware ido da kyau sai ta ga kamanin Babyn sak irin nata.Kafin ta yi magana ta ji Babyn na mai ci gaba da cewa “ta dalilina kawai za ki shiga wannan masarautar,ke ce sarauniya mai jiran gado.Ke ɗin ƴar sarki ce”
Linda ta girgiza kai ta ce “a’a ni marainiya ce banda iyaye”
Baby ta yi murmushi ta ce “ki duba damtsen ki za ki ga tambarin sarauta”
Daidai nan Linda ta farka a furgice , Khalil ya ce “lafiyar ki kuwa?”
Ba ta bashi amsa ba,mafarkin da ta yi ne ya dawo mata da sauri ta janye hannun rigarta nan ta yi tozali da tambarin sarauta.
Dama ta san da zaman shi amma ba ta san dalilin da yasa yake nan ba.
“Khalil ina son zuwa gida”
“Wane gida?”
“Orphelinat mana ”
“Wajen mi?”
“Akwai abin da nake son sani ne” Khalil bai kai ga bata amsa ba ta yi luuu ta sake komawa bacci.
Tamkar wani caset a inda ta tsaya daga mafarkin nan ta dasa wani.Baby na tsaye a inda ta barta,”kin duba tambarin ko? Hum! To kar ki faɗa ma kowa in ba haka nan ba kurma za ki koma” Baby ta faɗa .
Linda ta waro ido ta ce “ke wace ce?”
“Ƴar ki mana Ammy ba ki gane ni ba ne?”
“Ai ni ban taɓa haihuwa ba”
“Sai nan gaba za ki haifo ni dama” Baby ta bata amsa.
Kamar wata sakara haka take kallon jaririya bisanin ta tambaye ta “yaushe zan haife ki to?” Dariya Babyn ta yi bisanin ta ruga da gudu can kuma sai ta tashi sama.
Linda na nan tsaye sai garin ya ɗau duhu,can sai ga wani haske ya bayyana gare ta.
Ƙarrr ya haske idonta,kamar wani mutum sai ya fara tafiya ita kuma ta na take masa baya.Sun yi tafiya sosai mai tsayi bisanin ya tsaya,ita ma ta ja ta tsaya.
“Barka da zuwa duniyar tunani sarauniya Linda,abun bauta ya karɓi roƙon ki zai baki haihu buɗe tafin hannun ki na hagu” wata murya ta faɗa mata haka,Linda ta buɗe hannun hagunta a nan take wata ƴar ƙaramar kwalba ja ta bayyana cikin tafin hannunta da sauri ta jimƙeta “wannan shi ne maganin haihuwa!” Murya ta kuma faɗa,bisanin hasken ya ɓace sai garin ya dawo normal.
Dube-dube ta fara yi ta rasa ta wace hanya za ta bi ta je gida,ta yi taku ɗaya kenan ta ji wani ya caki tafin ƙafarta ta yi ihu da ƙarfi daidai nan ta farka.
“Linda lafiya ki ke ihu?” Khalil ya tambaya,Linda ta ce “Khalil ƙafat…” Saurar maganar ce ta tsaya mata jin wani abu a cikin tafin hannunta,zuciyarta na bugun tara-tara ta buɗe sa mi za ta gani? Kwalbar da aka bata cikin mafarki……
[…] Nata Matar Aljan Hausa Novel Complete […]