Hadin Kaddara Hausa Novel Complete
HAƊIN ƘADDARA
By
*AyshaNalado*
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUƘAYYATU* son so fisabilillah🙏
📖1⃣
Page 7
Bayan tafiyar su Suraj ɗaki Eshart ta nufa dan gabatar da nata sallan la’asar ɗin, a kwance ta samu Salmah rigingine riƙe da waya a hannunta, tana karatun littafin gaba da gabanta na Ayshercool, saboda yadda labarin ya dau hankalinta ko ɗagowa ta kalli Eshart ta kasa, idon ta akan waya ta amsa mata sallama, A’ishatu ta ce “master a nan anata Sana’a.” Still bata ɗago ba ta ce “umm.” Taɓe baki Eshart tayi ta rasa daɗin me Salmah keji a karatun novel,kullum sai tayi shi kamar farilla, ta ce “to sai ki tashi ki haka kiyi sallah gashi nan anata kira.” Kicin ƙosawa da katse mata karatu da take yi ta ce “tohhhh.” Riƙe haɓa tayi tace “Allah ga kayanka, Allah ka shirya.”
Yan Boarding Hausa Novel Complete
Wannan karon kam bata samu amsa ba, ganin haka yasa ta shige toilet don yin alwala, tana fitowa , ta tarad da Salmah ta kife wayar tana miƙa sai murmushi take saki ita ɗaya, hararar ta A’ishatu tayi tace “ai na ɗauka baza kiyi sallar bane.” Ta ce “Eshart baza ki gane bane novel ɗin ya haɗu ne over wlh, duk fushin da na kwaso da takwaicin wancen yaron ina hawa online naga tayi posting, baki ji daɗin dana ji ba, ji nayi kamar an wanke min zuciya da ruwan sanyi.” A’ishatu data gama shimfiɗa pray mat ta saka hijab ta ce ” To madallah ina zuwa ki ga.” Tana gama faɗin haka ta kabbara sallar ta, ganin haka yasa ita ma ta mike tayi toilet don dauro nata alwalan, bayan sun idar kasancewar ranar alhamis ne babu islamiyya yasa suka zauna a ɗaki suna ƴar taɓa hira,Salmah na bata labarin abin da Suraj ya mata yau a school, sai dariya A’ishatu ke mata, ita ko sai masifa take tana tsigale shi kwace yana gurin, Cikin da dabara A’ishatu ta sa ko maganar kangiwa Cikin hirar tasu, aiko nan Salmah ta shiga yabon shi tana kuzuzuta shi, tare da faɗin irin nagartar shi, gyada kai tayi tace “lallai mutumin nan karshe ne har na matsu naji cikakken sunan shi.” Salmah tace “cikakken sunan shi, Ahmad Idris Ahmad kangiwa.” Ji tayi zuciyarta ya shiga luguɗen daka daga jin sunan, Murmushin yaƙe tayi tace “umm kaji special name sunan manya.” Salmah ta ce “mahaifin shi, shi ne General Idris Ahmad kangiwa. Tsohon soja ne mai matakin general, mutum ne nagartacce wanda yake da tsananin tausayi da taimakon talakawa da son tallafawa rayuwar su, hakan yasa ya kasance mai farin jina a cikin al’umma, bayan yayi ritaya Kawai sai na kusa da shi suka bashi shawarar ya faɗa harkar siyasa ta nan ne Kawai zai samu ya taimaki talakawa wanda wannan ne babban muraɗin shi, Allah ya saka mishi kishi da tausayin talakawa a ranshi tun bai san kanshi ba, baiyi kasa a gwuiwa ya tsunduma harkar siyasa. Shigar shi siyasa ya girgiza zukatan magauta, don mutum ne shi na mutane yana da wani irin farin jini mai ban mamaki, fitowa ta farko jam’iyar shi ta TBA ta tsaida shi a matsayin dan takaran gwamna, kasancewar shima mai arziki ne sosai da sosai, wannan abu ya matukar ja mishi bakin jini a gurin daɗɗaɗun jam’iyar wanda suke ta harin wannan damar ba’a basu ba, shi karan kanshi bai so ba don shi da yaso ne ya fara daga ƙasa ƙasa kamar senate haka, amma tunda sunga cancantar shi sun daura shi dole ya karba, tun kan a kai ga yin zaɓe ma wasu daga Cikin jamiyoyin adawa suka shiga zame wa, suna janyewa, don sun tabbatar baza su iya karawa da shi ba, ranar kuwa da akayi zabe tun kan akai ga yin announcing kowa ya tabbatar da cewa shine ya lashe zaɓe, yayi mulkin garin nan a shekara ta dubu biyu , lokacin da yayi mulki bani da wayau, amma a labari ance har yau ba’a taba samun managarcin mulki kamar lokacin mulkin shi ba, duk da yasha gwagwarmaya sosai da sosai da mutane mabanbanta, yayi yaƙi sosai da mabarnatan garin nan, bai bari anyi wasa da dukiyar talakawa ba, aiki tukuru yayi, gaskiya a lokacin shi talakawa sunji daɗi,a haka yayi mulki shi har na tsawon shekara takwas a garin nan kafin ya sauka,inda a zabe na gaba aka sake tsaida shi dan takaran senate, shima alhmdllh yayi nasarar lashewa inda ya sake wasu shekaru 8 din akan mulki, bayan wannan matakin ance ya rike matakai da yawa masu karfi a mukamin gwammati.” Gyada kai A’ishatu da ta buɗe dukkan kunnuwanta tana shan labari tayi, jin salmah ta dasa aya, Cikin mamaki tace “duk a ina kika samo wannan labarin haka.” Murmushi tayi ta ce “a gurin Abie kinsan Abie yana ɗaya daga Cikin manyan lowyoyin shi a halin yanzu, kuma suna tare tun da daɗewa don shima Abie dan siyasa ne, tun yana matashi kuma koda ya gama karatu ya samu aiki bai bar siyasa ba, to a haka suka haɗu da general Idris kangiwa har ya zama ɗaya daga Cikin lauyoyin shi.” A’ishatu tace “masha Allah, kuma har yanzu yana siyasa?” Ta jehowa Salmah tambaya, Salmah ta ce “tun shekaru shidda da suka wace ya ajiye siyasa, sai dai har yanzu yana daya daga Cikin masu fada aji na kasar nan A halin yanzu babban ɗanshi ne ke siyasa, gwamnan mu na gobe da yardar Allah, Mr Ahmed I Ahmad kangiwa.” Ta kàrashe maganar cike da shauki, cikin da tsagwaron mamaki A’ishatu ta ce “kina nufin Mr AA kangiwa.” Salmah ta ce “kwarai kuwa shi nake nufi fari mai farar aniya.” So take ta jeho ma Salmah wata tambaya amma kuma tana tunanin ta yaya, kafin takai ga ƙara cewa wani abu, Ammi tayi sallaman ta shigo ɗakin, hannunta rike da wayarta, ko sannun da suke mata bata samu amsawa ba ta ce “ku shirya yanzu pls na aike ku, gidan hajiya turai ku kai mata saƙo, gobe da safe za’ayi tafiya dashi wlh na sha’afa sai yanzu ta ke kirana, na tuna, na nemi salman ban ganshi ba na ta kiran shi a waya ma bai dauka ba.” Da to Ammi suka amsa,ta juya ta fice tana cewa “ina jiran ku a ɗakina.” Sharp sharp suka shirya Salmah ta saka wando falazo da riga mai dan kauri ta dauki hijab din ta mai hannu irin na zamani dogo har kasa ta saka, ta saka takalmin ta hill, ita kam A’ishatu, dogon rigar atamfa ta zura ta yafa gyale medium, wanda ya shiga da kayanta, bata daura dan kwali a kanta ba saboda ita ba ma’abociyar daurawar bace, Salmah ce ta shafa hoda da dan jambaki,ita kam A’ishatu lip gloss fari ta shafa a pink lips ɗinga, ta zura plat a kafarta suka fito sai kamshi suke bazawa, a tsaye a falo suka samu Ammi riƙe da wani babban leda mika musu tayi tace “oya kuyi sauri, kuje ku dawo, kar ku zauna kuna kaiwa ku juyo kunji ko.” Har suna hada bani wurin cewa “to Ammi.” 2k ta mika musu ta ce “gashi ku dauki drop din napep ya sauke ya jira ku ya dauko ku, bazan ba ku mota ku tuka da yamma ba, dama salman na nan ne sai ya tuka ku, kuyi maza da kun kai mata ku dawo kuce ina gaishe ta.” suka amsa mata da to, tare da saukar saƙon suka fito, basu sha wani wahala ba, wurin samun adaidaita,ko ciniki basu yi ba suka shiga tare gaya musu inda zai kai su, da kwatance ya kaisu har kofar gidan , sai da suka sauka salma kemai bayanin ya jirasu ya maidasu sai su bashi kuɗin gaba ɗaya, hakuri ya basu kan cewa yana da uzuri, mai karfi su sallame shi Kawai, ai da sun gaya mai haka tun farko da bazai zo ba, Salmah tace “Oh ohh yanzu ya zamuyi gashi ko daga nan zuwa fita titi baban aiki ne, ga yamma Mallam ka mana hakuri mana ko titi ka fidda mu.” Ya ce “malama nima kumin hakuri uzirin gaggawa gareni ku sallame ni dan Allah, kudin ku Dari shidda.”Salmah zata kara magana A’ishatu ta dakatar sa ita tare da mika mishi dubu daya ya basu canji ya juya abinshi.
Shiga get ɗin tamfatsetsen gidan sukayi, kasancewar me gadi yasan da zuwan su yasa basu wani tsaya dogon bayani ba ya buɗe musu.
A falo suka tarad da ita zaune, hamshakiyar macece yar gayu, tana ganin su ta shiga sakar musu fara’a suma murmushi suka shiga yi har suka isa gabanta, suka ɗuka har ƙasa suka gaishe ta a tare, amsa wa tayi tana ɗago su , ta ce “oh ikon Allah ni turai girman ƴa mace babu wuya yanzu Salman da A’isha kune haka kuka kara zama zankaɗa zankaɗan yan mata, a lallai bari na fara shiri a Kwai gagarumin biki a gabana.” Duk dariya suka saka cike da kunyar maganar ta, macece mai fara,a da yawan barkwanci hajiya turai akwai kirki kawar Ammi ce tun ta kuruciya, miƙa mata saƙon A’ishatu ta yi,karba tayi tace ” yawwa dama yanzu nake son na sake kiran ta Ashe ma kuna cikin gidan, ya kuke yarana ya karatu.” Suka amsa da alhmdllh, tace to ku zauna bari nasa a kawo muku ruwa, har suna haɗa baki gurin cewa “A’a hajiya mungode.” Hararar su tayi daga inda take zaune ta shiga kwala kiran sunan yar aikin ta, da sauri ta iso tana cewa “gani hajiya.” Ta ce “ki kawawo yarana abi taɓawa.” Kan kace kwabo ta cika musu gaban su da kayan maƙulashe, ba yadda suka iya haka dole hajiya turai ta saka suka tsatstsakura, tana tare dasu tana musu fira cikin barkwancin ta suko sai dariya suke yi idan ta fali abin dariya, wani masifeffen ƴamshi ine ya turnike hancinsu, kafin su gama tunanin daga ina kamshin nan ke tasowa ya bayyana a falon Cikin gayun shi, matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, da haihuwa kyakkyawan gaske wankan tarwaɗa dan gaye na nunawa sa’a, tunda ya shigo falon idanunshi ke kan su, yana binsu da wani irin mayen kallo musamman A’ishatu data fi daukar hankalin shi, zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun falon, idanunshi a kansu ya ce, “hajiya baƙi kikayi ne?” Ta ce “baƙi kuma ƴan gida,baka gane su bane.”kafin yace komai suka shiga gaishe shi, don su, sun gane shi sarai ɗan ta ne, Ammar abokin yaya Anas, amsa su yayi yana kare musu kallo don son lallai gano ko su waye, hajiya turai tace “da gaske baka gane su ba.” Ya girgiza kai, ta ce “Aiko dai anji kunya ƙannen Anas ne fa, Salmah da A’ishatu.” Zaro ido yayi cike da mamakin girman yaran, yaran daya Sani a yan kwailaye sune suka zama haka, cike da mamaki yace “ikon Allah, yanzu salmah ce ta girman haka.” , Shi sai yanzu ma yake gane ta, hajiya turai ta ce “ba kun watsar da zumunci ba, ai ga irinta nan, yanzu da a hanya kuka haɗu sai dai ka wuce su wace ko? Ni bana ma jin tunda ranar da Anas ya bar ƙasar nan kaje gidan nan.” Sose keya yayi cikin rashin gaskiya, ta ce “naga kamar fita zakayi pls ka biya ka sauke min su daga nan ma ka shiga ka gaisar da hajiya Rabin.” Da sauri ya ce “OK ba damuwa muje bari na kaisu.” A ranshi yaji dadin wannan lamarin don shi faduwa ce tazo mishi daidai da zama……
Oum Ummeetarh ce😍
09116099486
[…] Hadin Kaddara Hausa Novel Complete […]