Littafan Hausa Novels

Minene Alaqar Mu Hausa Novel Complete

Minene Alaqar Mu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Minene Alaqar Mu Hausa Novel Complete

*MINENE ALAQAR MU*

 

Written by

*Bintu

 

3⃣2⃣

 

Da sauri Fauzy ta tashi ta nufi cikin gidan, ta d’auko mayafin ta ta saka bathroom slipper d’in ta, ta fito tana ta uban sauri kamar ba Fauziyya yar qwalisa ba.

Tana fitowa ta nufi parking lot d’in su ta tsaya…da sauri driver d’in ta ya qaraso yana bud’e mata motar ta, ta shiga shima ya shiga ya tada suka fita daga gidan..

Rayuwar Zamani Hausa Novel Complete

Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce mata “Ina zamu je Maa?”

Ba tare da ta kalle shi ba tace “Gidan Ummy”

Ya riga ya san tana nufin gidan mahaifiyar Suleiman za suje saboda haka ya qara ma motar shi gudu, cikin qanqanin lokaci suka iso gidan.

 

Da sauri securities d’in dake zagaye da gidan suka miqe mutum biyu daga ciki suka qaraso, driver ya bud’e window d’in side d’in shi suka gan shi sannan suka bar shi ya wuce..

 

Gidan Ummy gida ne mai tsaro sosai, kasancewar gaba d’aya yaran ta maza biyar jami’an tsaro ne,kuma ba qaramin muqami ke gare su ba..

 

Suna shiga ciki ko gama parking bai yi ba ta bud’e ta fito tana ta uban sauri ta shiga gidan..

Tana shiga ta iske Ummy zaune a parlor cikin shigar kamala, sallamar Fauzy ta sa Ummy d’agowa ta kalle ta tana amsa mata…

“Aa Fauziyya ce, shigo ciki mana”..

Fauzy ta shiga ta nemi wuri ta zauna, cikin wani ladabi da bata saba ba ta gaishe da Ummy..

Ummy dai nata bin ta da kallo tana ganin ikon Allah, can kuma ta ce ” Amma Fauziyya kamar ba dai dai kike ba,mike faruwa ne?”

Fauzy ta d’ago ta kalli Ummy muryan ta da alaman karaya ta ce “Toh Ummy wallahi Fatima ce har yanxu bata dawo daga school ba,kuma an kira gidan su yarinyar dake maido ta baban ta yace ita ma bata koma ba, shi ne nazo ko zaa samu mafita”

Ummy tayi salati tana tafa hannu, can kuma ta ce “Oh ni Fatime wannan wani irin labari ne, yanxu Fatimar ke baa gani ba kamar wani tsinke?”

 

Fauzy ta ce “Wallahi Ummy ba’a ganta ba”

Ta qarasa tana fashewa da kuka, ita bata ta’ba sanin tana son Teemah sosai irin haka ba sai yau da take jin kamar ta rasa ta,ji take ina ma zata iya maida hannun agogo baya,tabbas da da kanta zata na kai Teemah makaranta ta d’auko ta,ji take kamar zuciyar ta zata qone tsabar rad’ad’in da take mata…

Ummy ce tayi ta lallashin ta kafin ta d’auko wayar ta ta kira yaran ta gaba d’aya tace su same ta gida akwai matsala..

Ai kuwa in less than one hour sai gashi sun had’u gaba d’aya su hudu,ban da Suleiman dake can Sahara….

 

Bayan taruwar su ta fad’a masu abun da ke faruwa,dukkan su saida tashin hankali ya bayyana kan shi a fuskokin su…

Cikin jimami Jabeer ya ce “This is a very serious case, wake da number d’in principal d’in su please, shi ya kamata mu fara kira”

 

Imran ya ce”Yes, ta nan ya kamata, ko zuwa gobe in sha Allah sai muje gidan su yarinyar “..

Ummy ta ce ” Madallah da yaran albarka, Allah ya baiyana mana su cikin aminci, Allah kuma ya tona asirin barawo”..

 

 

_BATOOL And TEEMAH_

 

A hankali Batool ta bud’e idanun ta wanda take jin sun mata nauyi ga kan ta da taji ya sara mata, da sauri ta maida idon ta rufe sai kuma ta sake qoqarin bud’e shi karo na biyu..

Da Teemah ta fara cin karo wacece take kwance daga gefen ta saman buhu, da sauri ta fara bin inda suke da kallo, wani daki ne ginin bulo sai dai ko plaster ba’a yi mashi ba, nan fa ta fara qoqarin recalling abun da ya kawo su wurin kafin ta tuna mai napep d’in da suka hau..da sauri ta fara karanta innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ta yunqura ta tashi zaune sannan tayi qoqarin miqa hannun ta don ta jawo Teemah jikin ta, amma kuma sai taji an riqe hannu, da sauri ta kalli hannun nata sai taga ashe a d’aure take, ta maida kallon ta ga qafafun ta suma ta gan su a d’aure, ai kuwa ta fashe da kuka tana karanta innalillahi wa inna ilaihi rajiun this time a little bit louder..kukan ta me ya tada Teemah daga baccin da take da sauri itama ta miqe zaune sau kuma ta maida kallon ta ga hannun ta da taji shi a d’aure sai dai ita qafar ta a kunce take ba’a daure ta ba, ai kuwa da sauri ta qarasa wurin Batool ta fad’a jikin ta tana fashewa da kuka, Batool ta ce “shhshhh, daina kuka kinji daddy’s girl”

Teemah ta kalle ta tace ” Aunt an sace mu kuma kina cewa in daina kuka?shknn mu kuma,dama daddy baya nan bare ya gano mu”

Batool tace “Daddy baya nan,amma kuma Allah na nan, shi xai kare mu”

Teemah ta ce” Haka ne, Allah ya kare mu”

Batool ta amsa da “ameen”…

Suna cikin haka ne wani qaton gardi ya shigo d’akin, fuskar shi ba alamun sauqi kanar ya had’iyi kumurci, ya qarask wurin da suke yana aje plate d’in dake hannun shi, ya duqa ya kwance daurin dake hannun Batool sannan ya d’auki plate d’in ya miqa mata, ta saka hannun ta dake zugi saboda dad’ewar da yayi a d’aure ta karb’a, shi kuma ya juya zai fita, da sauri Teemah ta ce a tsorace ” Kajiii”

Ya juyo ya watsa mata jajayen idanun shi, ta qara matsawa jikin Batool sannan tace”Ka manta baka kwance ni ba,dan Allah ”

Ya mata kallon banza sannan ya dawo ya kwance ta sai kuma ta sake cewa “karfe nawa dan Allah”

Sai da ya dunqule hannun shi kamar zai naushe ta sannan yace “Biyun dare”..

Suka kalli juna ita da Batool sannan suka maida kan su qasa, ya ce ” Ku maida hankali ku ci abincin nan don rabin shi TUE ya ce a baku, idan yaga yawan shi to kun ja ma kanku,ba lallae a qara baku abinci ba sai nan da wasu kwanaki”..

 

Daga nan ya tashi ya bar d’akin, Batool ta share qwallar data zo mata tana bud’e plate d’in, shinkafa ce da mai sai dai kwata kwata man bai ji ba qamas take, maimakon a saka yaji sai aka sa gishiri,shikenan kuma…

A hankali ta motsa abinci tana ci tana ba Teemah, amma ko rabi basu yi ba suka ajiye saboda yanda suka ji kamar zasu maido shi kuma sun kashe yunwar dake damun su..

Sai wani ruwa da aka basu kalar ruwan brown ga wani gaushi kamar an jiqa kanwa a ciki, toh dai sun sha kadan don kada qishi ya halaka su……..

 

 

*©Bintu*

Add Comment

Click here to post a comment