Littafan Hausa Novels

Amfanin Kanunfari

Amfanin Kanunfari Ga Mata da Maza

 

 

 

 

 

 

Amfanin KANUMFARI

In zaki jiƙa kanunfari at least ki bari yayi 2-3 days kafin ki sha. Kuma ki

zuba shine yanda in ya jiƙa ruwan zai koma brown. Babban goran faro

ki sa masa cokali uku na kanunfari.

Ni da Yaya Rafeeq Hausa Novel Complete

1. Kanunfari Yana taimakawa wurin rage ciwon mara ga mai ciki da

kawo haihuwa da wuri.

 

Amfanin Kanunfari

Wata ƴar’uwa bayan waccen rubutun ta faɗi cewa: “Kanunfari yana

hana me ciki ciwon mara kuma yana taimakawa wajen haihuwa da

sauri. Ga wani haɗin da nake amfani da shi “Ki samu dabino, ki ciccire

ƙwollon ki sa shi a rana idan ya bushe ki daka tare da kanumfari ki

rinƙa sha da madara.” Tace “Na yi amfani da shi kuma ya mun sosai

wallahi.”

Wata itama tace: “Nima na gwada especially idan kika hada kanumfari

da minannas, ki samu empty roban swan ki jiƙa da ruwan sanyi ki bar

shi ya kwana, sai ki rinƙa sha da peak milk (madarar ruwa). Ki yi ta

refilling (sake cikawa) har ƙamshin da color brown ya tsane sai ki

zubar ki jiƙa wani.”

“Tace har tsayin labour (naƙudan) ta ya ragu, nan da nan sai ta ga ta

haihu sanadiyyar amfani da kanumfari. Wato kenan duk mai ciki in tana

amfani da shi zata samu sauƙin ciwon mara da rage tsahon naƙuda.

Domin ƙarin ruwan ni’ima da daɗi. In dai mace ta riƙe waɗannan in

Allah Ya yarda bata da matsalar ni’ima.

2. Ki samu kanumfari, rake, ginger/ginseng in so samu ne, sai zuma.

Ki dafa rake da sauran kayayyakin amma ban da zuma, na kamar minti

30. In kika sauke ya huce sai ki murje ruwan raken ya fita jikin shi, ki

zuba zuma a ciki, ki rinƙa shansa. Yana mutuƙar saukar da ni’ima

kuma yana ƙara sha’awa da daɗi. Wasu ma suna saka mazarkwaila a

cikin dahuwan.

3. Ki rinƙa nika kankana da kanumfari, ki zuba riɗi in kina da shi sai ki

niƙa shi sosai. In kin juye sai ki zuba isashen madara ki rinƙa sha.

4. Ƴaƴan goji/kabewa (pumpkin seeds) suna ƙara wa mace sha’awa

da daɗi. Akan busar da shi a daka a rinƙa sha da madara ko a dafa a

sha da madara. Wasu kuma suna daka shi tare da busashen ƴaƴan

kankana su sha da madara. Yana wanke duk wani dattin jiki. Sannan ki

dafa goji dai-dai wanda zaki iya shanyewa. Sai ki sauke, ki zuba

dakakken kanunfari, zuma da madara isashe ki sha da yawa. Wasu

kuma tace ruwan suke su sha wato ki dafa shi da kanumfari sai ki tace

ki sha akai akai, duk wanda dai kika ga zaki iya. Yana gyara jiki da fata,

yana ƙara ƙarfin sha’awa da ni’ima da daɗi ga mace da na namiji duka.

5. Kankana (watermelon), yana ƙara sha’awa, ni’ima da daɗi. Ki rinƙa

yanketa har da wurin farin domin akwai sinadarin da jiki ke buƙata a

ciki. Zaki iya haɗa kankana, kanumfari da cocumber ki niƙe ki rinƙa

sha.

6. Cin kifi da shan farfesun sa yana kara sha’awa. Ki sanya kayan

ƙamshi sosai a cikinsa (nutmeg, tafarnuwa, kanunfari, ginger, girfa

dss) ki ci ki sha romon isashe. Cin nama mai romo-romo amma wanda

yaji haɗin kaya kamar riɗi, kafi malam da nonon rakumi.

7. Tafarnuwa yana sanya mace juriya yayin saduwa. Yana kashe

infection da cututtuka marasa adadi ciki da waje. Yana cleansing

cututtukan ciki. Zaki iya sashi a cikin abinci ko ki rinƙa haɗiye shi da

yoghurt bayan kin yanka ruwan jikinsa ya ɗan fito. Zaki iya hadiye

babba guda ɗaya da yoghurt mara sugar duk bayan sati biyu ki sha,

sau biyu a wata kenan ko sau uku. In baki so akwai capsule na

tafarnuwa kuma akwai oil nashi. Yana wanke duk cutukan ciki da mara.

Don haka kada kiyi sake da shi.

8. Yawan cin ayaba da yin juice dinsa da madara shima yana sanya

mace juriya, kuzari da daɗi. Abarba yana gyara ƙamshin sperm da ƙara

lafiya.

9. Ginseng kamar citta yake ana siyar da tea nashi a kasuwa wurin

masu siyar da tea na kanti kala-kala, kuma ban san sunansa da hausa

ba. Yana ƙara sha’awa, juriya, yawan sperm da daɗi. Zaki iya dafa shi

da kanumfari. Haka nan in babu shi za a iya amfani da ginger.

10. Nutmeg (gyaɗar miya) ana samun shi wurin masu siyar da kayan

ƙamshi (su kanunfari da citta) A rinƙa daka shi ana sashi a farfesun da

zaki sha. Waɗanda suka ji su tafarnuwa, kanunfari da citta. Ki ci naman

ki sha romon.

11. Ki siya busashshen dabino, kanunfari, aya, zaki iya hadawa da

busashen kwakwa. Ki daka su ko ki kai a niƙa miki gari kenan. Ki rinƙa

sha da zuma ko madara. Wannan yana dadewa bai lalace ba. Sannan

zaki iya niƙa su ki sha kamar kunu. Haɗin nan yana mutuƙar wanke

ƙoda da ƙara wa mace daɗi da ni’ima. Sannan zaki iya haɗa aya,

dabino, gyadar mata da mazarkwaila ki yi garin shi kina sha da zuma ko

madara.

12. Ki rinƙa shan zuma kada ya rinƙa yanke miki, haka nan yoghurt/

nono. Ki rinƙa soya kwai amma kada ya soyu sosai da man zaitun da

safe. Ki rinƙa cin zogale da shan ruwansa, ki rinƙa yin miyar ugwu

leaves ko alayyaho. Ki rinƙa dafa wake tare da kifi, isashen albasa/

tafarnuwa da ganyayyaki. Ki rinƙa yawan yin salad Ko kwaɗon duk

ganyen da kika samu.

13. Ki rinƙa yawan shan lemu ko matse ruwansa. Ki rinƙa yawan cin

cocumber yana gyara fata, ƙara ni’ima da daɗi. Ki rinƙa shan rake mai

yawa kada ya yanke miki ko bashi da zaƙi sosai.

14. Kada ki manta da shan shayin kanunfari, cinnamon (girfa),

cardamom (Habhan ko Habbahan), ginseng ko citta, a sa na’a na’a

(mint), tafarnuwa dss. In kina yawan sha ni’ima ba zai yanke miki ba,

infection ba zai zauna a jikinki ba, ba zaki rinƙa warin gaba ba, ba zaki

rinƙa jin kasala ba.

15. Ki rinƙa shan garin zogale da yoghurt da safe kafin ki ci komai.

Yana maganin ulcer yana da kuma sinadarai mai yawa a cikinsa. Ki

rinƙa yawan cin aya kada ya yanke miki. Da cin kwakwa da dabino ga

daɗi ga karin ni’ima. Ki rinƙa shan isashen ruwa da rana, ki rage cin

abinci mai nauyi sosai yayin zuwa turaka zai sa miki kasala. Waɗannan

kaɗan daga cikin abubuwan da nake ganin zai amfani mata ne da na

rubuta yau. Ki rinƙa ƙoƙarin jure amfani da abubuwa har jikinki yayi

adopting ya saba. Akwai abubuwan da aikinsu ba na yanzu yanzu bane.

Bana bada maganin mata, don Allah a daina tambayata ana kawo mun

matsaloli. Kuma bani da whats app group na mata sai Markazus

Sunnah. Nagode sai mun sake haɗ

Daga Sadeeya Lawal Abubakar.

 

amfanin kanunfari,amfanin kanunfari ga budurwa,amfanin kanunfari ga maza,amfanin kanunfari da madara,amfanin kanunfari da zuma,amfanin kanunfari a fuska,amfanin kanunfari ga mata,amfanin kanunfari ga mace,amfanin kanunfari a gashi,amfanin kanunfari da ganyen magarya

Add Comment

Click here to post a comment