Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023
Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023
MomIslam
_True life story_
*Arewabook@momislam11*
🆓 Page 7
“Dan girman Allah karki bari ta dawo gida, Indo muguwar mata ce zata iya yin komai akan taga Hanan tayi aure a gidan duhu”
A inda yayi maganar ya ba Hajiya Indo tausayi, tace “insha Allah Junaidu hakan ma bazata faru ba, gobe zan mayar da ita kokuma in kaita Kano tunda tsakaninmu akawai nisa, da garaje bazata ji marmarin dawowa ba”
Sakamakon zaben gwamna jihar Kano
“Yauwa Indo nagode Allah yayi miki albarka”
Cewar malam Junaidu da har yanzu yana durk’ushe jikinsa na karkarwa,
Hanan da yanzu ta farfad’o ta kalli Indo sai Kuma ta fashe da kuka,
“Hanan meya faru ko kinason komawa gida ne?”
Hajiya Indo ta fad’a tana kallon yanayin Hanan d’in,
Cikin muryar kuka Hanan tace “nidai inason zuwa gurin Inna Meramu har ji nakeyi kamar in rufe ido idan na bud’e in ganni a gurinta”
Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023
Gaban Hajiya Indo ya buga rass ta fara tunanin inhar Inna meramu taji labarin Hanan tana gurinta to Babu makawa sai ta tozartata ko tayi mata asiri tabi duniya tunda Babu tsoron Allah a tare da ita,
A fili tace “ki kwantar da hankalinki nifa banasan inga kinje gidan duhu saboda wlhi inhar kika shiga wannan gidan kinyi sallama da shak’ar iskar waje sai mutuwa, saboda ba’a fita a gidan”
“Eh naji inaso”
Sosai Hajiya Indo ta sake tabbatarwa da maganar Hanan da takeyi ba yin kanta bane, saboda duk da yarintarta idan akace mata zatayi aure a gidan duhu har zagin mutane takeyi yau ita da kanta take cewa tanaso?,
Acan 6angaren Alhji Munir kuwa yanzu ya dawo da k’atuwar leda bak’a mai d’auke da soyayyan k’wai da dankalin turawa sai tea a sabon cup da bread Mai yanka-yanka,
Da sallama ya k’araso d’akin ya sameta ta haye saman gadon tana ta tsalle kamar ba itace mai jinyar ba, ga kanta nad’e da bandeji, ya ajiye ledar tare da kamo hannunta yace “zo kici abinci”
Da sauri Hinde ta nutsu,
Alhji Munir ya fito da soyayyan k’wai da dankalin harda shayin da bredi ya ajiye a saman ledar kafin yace “bismillah”
Jikinta na rawa ta d’auki kofin shayin a tunaninta kunu ne, tana Sha ta fesar tare da d’aukar wainar k’awai takai bakinta, lomar farko shima ta fito dashi tare da fashewa da kuka tace “fate nakeso ko tuwo ni bazanci wannan ba, saboda tunda nake ban ta6a ganinsu ba”
Alhji Munir ya zuba mata ido kafin yace “to kici dankali”
Cikin sa’a taci shima d’in ba sosai ba ta ture gefe tana jin zuciyarta na tashi, abinka da ba saba ci tayi ba.
Wayarsa ta fara Ring, a hankali yasa hannunsa a aljihu ya ciro wayar, Hinde ta k’ura masa ido tanason taga abinda zeyi da wayar, sai taga ya kara a kunnensa yana cewa “wlhi na bige yarinya ce gashi na rasa iyayenta inaga zamu koma k’auyennne ayi cigiyar danginta”
Hinde ta duro a gado tare da fincikar wayar hannunsa, tana ta kallo tana dariya tace “wannan abin magana yakeyi?”
“Eh mana yanzu aka kirani”
Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023
Ta Kuma kwashewa da dariya tace “Naga har haske yake kawowa sake kunnawa in gani”.
Alhji Munir ya kunna mata kallon yaran larabawa da suke spelling din ABCD suna wak’a, yana fita ta ajiye wayar a k’asa tayi tsalle ta fad’a kan wayar tana cewa “kodai mayu ne, ga wasu fararen Abu sai kace aljanun k’arshen duniya”
Alhji Munir ya shigo da saurinsa ya ganta ta mimmik’e k’afafuwa a k’asa, cikin fara’a yace “tashi muje”
Tana mik’ewa yaga screen d’in wayarsa ya tsatsage gashi ko haske Babu, jikinsa na rawa yakai hannu ya d’auko wayar, ya danna ta kawo Amma ciki yayi Zane”
Ya kalli Hinde dake dariya a tunaninta tayi abin arzik’i tace “Baba na gyara maka zaman mutanen dake son tsotse jininka”
Alhji Munir ya zaro ido, yana son yi mata fad’a ya kasa saboda wani kwarjini da tayi masa, Kuma yana gudun kar tak’i sanar dashi komai akan rayuwarta, yaga kamar Babu abinda ta sani na game da jin dad’i, dalilin da yasa ya gano hakan shine, ya kawo mata abincin da yara suke murna idan suka ganshi Amma ita ta ture, ga waya da duk wani yaro ya Santa Amma tana neman lalata masa, ya kamo hannunta tare da tura gashin kanta wanda yake tashin tsami cikin d’ankwali, ya kalli k’afarta da ta kasance duk faso, yace “muje in siya miki silifas”
“Meye wannan?”
Hinde ta tambaya tana zuba masa idanuwa”
Alhji Munir yace “takalmi” ya nuna kafarsa yace mata “Amma ba irin nawa ba”
Kasancewar an sallamesu suka wuce hannunshi ana Hinde, d’ayan hannun Kuma ya rik’e magani.
Tana hango motarsa ta zame hannunta a nashi kafin ta k’arasa da gudu ta ture motar da k’afa, a tunaninta motar zata fad’i sai taga ko motsi batayi ba,
Alhj Munir ya girgiza Kai yana dariya.
Hannunta ya rik’e yasa ta a gaban mota shima ya shiga, ya had’e fuska alamar Babu Wasa yace “idan kika sake ta6a wani abu anan wlhi zan dakeki”
Batasan duka dole ta nutsu.
Alhj Munir yace “inane gidanku waye sunan mahaifinki?”
Duk da yarintarta wayonta yana nan saboda a zurfin tunani sai tafi wani Mai yawan shekarun ma,
Hinde ta fashe da kuka sakamakon tunowa da idan ta koma gidannan mahaifinta zai kasheta, Kuma burinta na fitar da mahaifiyarta bazai ta6a cika ba muddin ta koma wannan gidan, a tak’aice ma batasan halin da mahaifinta yake ciki ba.
Alhj Munir yace “kibani amsa in samu in mayar dake gida lokaci ya k’uremin kinga ana kiran sallahr la’asar”
Hinde ta share hawaye kafin tace “ni bani da iyaye, kawai tsintar kaina nayi a inda ka ajiyeni dan Allah ka taimaka min ko gidan masu aiki ka kaini in dinga samun kudi ina cin abinci”
Alhj Munir ya tsorata, shima ya fara tunanin anya ba aljana bace, duba da yawan gashin kanta gashi bak’i kamar na doki Kuma Babu alamar k’arashi akayi, farcenta kuwa dogo kamar ba’a a ta6a yankewa ba, Alhj Munir yace “y’an mata sauka ko nawa ne zan baki dan Allah ki saukarmin a mota karki cutar dani”
Abin ya bawa Hinde dariya, tunda taga yana jin tsoronta Kuma yake ganin kamar ita ba mutum bace , ta lank’washe hannayenta kamar kuturuwa ta zame hular kanta, cikin wata iriyar murya tace “dama inrinku muke nema, tun wuri ka kaini gidanku idan ba haka ba wlhi sai na juyar damu a cikin wannan motar, kuma kai zaka mutu ba niba”
Alhji Munir ya fara fitsari a wando cikin tsananin tsoro yace “dan…dan Allah kiyi hak’uri duk inda kikeso zan kaiki amman Banda gidana”
Hinde ta turje ita dole sai gidansa,
Alhj Munir shima ya dinga yi mata magiya amma Sam tak’i amincewa da ya kaita gidan iyayenta,
KD
K’arfe 9:pm na dare, Abu Uzaifa yayi parking motarshi a gurin ajiye motoci, Rashida na jinsa ta fara murmishi tana cewa “Munipa dadynki ya dawo”
Munipa tayi tsalle tana dariya, abin mamaki, Abu Uzaifa ya shigo da murmishi ya rungume Hajiya Rashida bai nuna mata komai ba, sai wani shauk’i ma da yakeji, yace “Munipa yau banzo d’aukarki ba ko?”
Munipa ta shagwa6a fuska tare da cewa “dady ai driver ya d’aukoni”
Hajiya Rashida tayi masa sannu da dawowa tare da tayashi rage kayan jikinsa suka wuce dinning dukkansu a tare sukaci abinci, Munipa tana kan k’afar Abu Uzaifa, bayan sun kammala an d’an jima abu Uzaifa yace “Amma wannan k’awar taki mahaukaciya ce ko?”
“Meya faru wani abun tayi maka?”
Rashida ta watsa masa tambayoyi,
“Babu komai amma last kar in sake ganinki da ita wlhi idan ta sake shigowa gidannan a bakin auranki”
Abu Uzaifa ya fad’a ranshi a 6ace,
Hajiya Rashida tayi dana sanin tambayarsa da tayi saboda wad’annan kakkausan kalaman daya gaya mata sun jefata cikin rud’u.
Washe gari, sam bayajin fita aiki, kiran ma’aikatan gurin aikin nasu yayi yace “su gudanar da komai yau yana gida”
Kasancewar yau Monday driver ne yakai Munipa makaranta shikuma yana nan gurin Rashida,
Kwance suke a kyakkyawan bed Wanda ya dad’a K’awata d’akin, Rashida na kwance a k’irjinsa tace “uhm meyasa kake cewa idan har ta sake zuwa sai dai ka sakeni, tunda nake dakai kalamar saki bata ta6a shiga tsakaninmu ba sai yau?”
Tana rufe baki Kiran Hajiya Indo ya shigo, Abu Uzaifa yasa k’arar magana,
Hajiya Indo ta mak’ale murya kafin tace “Mosoyina ya ake ciki?”
Cikin tsananin kishi Hajiya Rashida ta fizge wayar tace “wawuya dak’ik’iya girman kyauye mara hankali butulu, mijina kika koma bi iyee?”
“Ke Kuma wacece da zaki yimin magana da wayar saurayina?”
Da sauri Rashida ta mik’a masa wayar tare da fashewa da kuka tana cewa “wlhi Allah sai naje har k’auyen nasu nayi mata illa batasan tayi gangancin shiga gonata ba, batasan waye Rashida ba?”
Abu Uzaifa ya rungumeta yana cewa “haba komai ya wuce mana, tunda dai ban amsa ba”
Cikin zafin rai ta dawo kansa, “wane irin baka amsa ba, wayasani ma ko ankusa auran naku kanaso ka zamo munafiki?”
Kalmar daya tsana a rayuwarsa kenan, cikin zafin zuciya ya wanka mata mari yana huci kamar wani zaki.
K’AUYE
Biki ya rage saura kwana uku, hankalin Inna meramu inyayi dubu ya tashi ta rasa inda zatasa kanta, tayi tsubbace-tsubbacen abin har yanzu tana ganin kamar bata samu galaba akai ba, tana zaune a tsakar gida kan dakalin k’ofar d’akinta Hajara k’awarta ta shigo, jikinta har kyarma yake saboda tsabar munafurci, Inna meramu na ganinta tace “Allah yasa da abin alkairi kikazo, tunda naga kin kwaso sauri nasan akwai magana a bakinki”
Hajara tacire mayafin dake rataye a kafad’ar ta kafin tace “can naga Y’arki Mai mashin ya wuce da ita su biyu harda Hajiya Indo me k’afar yawo”
Inna meramu ta mik’e cike da ruwan masifa tace “da gaske kikeyi ko wasa?”
“Zanyi miki karya ne? ki tambayi mijinki shine ya samo musu Mai mashin”
Inna meramu ta rangad’a salati tare da d’aukar mayafi tabar Hajara a gurin ta fice ko takalmi babu,
Tayi neman duniya Allah besa zata had’u da malam Junaidu ba, kowa ta tambaya sai yace mata rabonshi da ganin malam Junaidu tun safe, hankalinta ya tashi lissafi ya kwance mata ta rasa makama ta rasa inda zatasa kanta, babban tashin hankalinta idan Usaini ya dawo zai iya nakasata duk da tsufanta bazai duba komai ba.
Ganin Inna meramu ta fice yasa Hajara fitowa itama ta dawo gida tana cashewa da rawa, tace “saura muga inda Usaini zai ladabtar da Inna Meramu saboda mugun San kud’i inake ina had’a zuri’a da gidan duhu, acan gonar bayan gari ta hango malam Junaidu ya rafka tagumi yana kuka cikin masifa ta tafi da gudu tana ta tsallake kinyar masara saura biyu ta isa gareshi ya….
Saboda Allah da Kuma masoyana nace..
Littafin WAKE ÆŠAYA is not free paid book ne,
Akwai wad’anda suka fara tura 500 d’insu da farko zan saku a Vip.
Nayi rangwame da nace 500 yanzu duk meso zai iya bin wad’annan tsarukan saboda masu maganar yayi musu tsada.
Normal 300
VIP 600
Special 1k
Ga matakan da za’abi domin biyan kud’in
Account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Katin mtn da Vtu ta wannan number 08163626370
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Y’an Niger zaku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
Mom Islam
[…] Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023 […]
[…] Sakamakon Zaben Jahar Borno 2023 […]