Masarautar Jordan Hausa Novel Complete
_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*_Ban yarda wani ko wata ta sauya min ko maida min shi Audio yin haka shiga hakkin marubuciya ne jiki magayi_*
*Ina baku hakuri bazan samu typing ɗin Uwata tafi takowa ba Na maida masarautar Jordan cikin zafaffa sha ɗaya 11*
*BOOK ONE*
Not editing⛳
Page….١~•Tarihin *Daular MasarautarJordan*
A yau kasar Syria ta haɗa kan bayin da tasaya daga yankuna daban daban na africa da kuma wasu yankunar Asia. Daga cikin tawagar bayin da suka haɗa maza da mata, za’a kaisu Masarautar kasar Jordan ne, inda mashawartan fadar suka bukaci haka.
K’asar Jordan tana cikin yanki Gabarta tsakiya, kuma tana makwabtaka da kasashe biyar naduniya, Palestine, Israel, Syria, Saudia,Iran…
Daular Jordan tana cikin yanki jazziratul Arab, kuma yanki ne da Annabawa suƙayi gwagwarmayya a wajejjen, a ruwayyar wasu Malaman sun tabbatar Annabi Ibrahim kafin ya wucce falastinu yabi ta yanki Jordan haka Annabi Isah, ba iyasu ba annabawa dayawa sunyi rayuwarsu tatsakanin gurin domin Annabi ya wucce yankin Jordan kafin ya isa Sham, wato Yanki syria.
Bayan haka khalifofin Annabi Muhammad sun iso da da’awa yankin, har zuwa karni na uku bayan wafatin manzon Allah. Akwai kabilu guda uku dasuka kafa daular Masarautar Jordan.
Hashmiyya daga kabilar Banu Hashim, sai Husseiniyya daga cikin Banu Husein, sai Urdawa. Wanda suka haɗa kansu domin kafa kasar Jordan, tafiya tayi nisa sosai gashi kasar tana cikin kasashe masu ababen tarihi, musan red ocean. Matsalar da ta ɓullo daga cikin daular itace yadda kabilar Banu Hussein suke gallazawa yan kabilar Urd, musaman wanda suƙa kasance ba Musulmai ba, cutar dasu da Banu Hussein take yi bakaramin tunzura su yaƙe ba, karshe suka shiga suka fita tsakaninsu da Isra’ila suka kwace yanki, suka cigaba da gallazawa musulman yankin. Wanda ya janyo akayita fafatawa tsakanin Yahudawa da Larabawan yankin.
Ashekaran 1968 a wata mayu majalisar ɗinkin duniya tare da goyan bayan saudia cire kasar jordan daga yanki isra’ila, inda suka bawa kabilu guda uku na kasar shawaran su dai daita kansu, su bawa kansu damar mulkinsu.
Daga cikin kabilun guda uku, nan aka shiga muhawara me zafi, har yaja hankalin talakawar gari, suka ce abawa Kabilar Banu Hashim wato Hashmiyya. Sai dai tsakanin kabilu guda biyu basu so bawa Banu hashim sarauta ba, sabida su tsarinsu akan addinin musuluncine yayi yawa, kabilune da suke da nasaba da zuri’a Banu K’urash. Dan daga cikin macca suka zo inda suka same kabilar Banu Urd.
Lokacin da akazo zaɓar wanda za’a bawa sarki, a cikin zuri’a Banu hashim, sai aka samu cikin kabilar an sami rarrabuwar kai. A cikin banu Hashim sun kasu gida uku, gida Na farko sun kasance *YASIR ABDULLAH ALHASHMIYYA* shida Zuri’ashi ke jagorantar gidansu. Sai Gidan *ZAID BNI ABU ZARRI ALHASHMIYYA* shi yake jagorancin Zuri’arsu, HISHAM BNI UKSHE ALHASHMIYYA, shi yake jagorantar zuri’arshi, kuma dukkan zuri’ar ALHASHMIYYA, yan uwan juna ne, dan duk Y’aya’an baffanaine, Domin kakansu MUHAMMAD ASHRAF ALHASHMIYYA shi ya haifi iyayensu Maza, ABDULLAH shine Babba, ABU ZARRI ke binshi, sai UKSHE, shine karaminsu, da aka fara Maganar Yasir ya zame kanshi yace baya bukatar mulki, na familynsu ma da aka bashi ya ishe shi, sai ya zama tsakanin Abu Zarri da Ukshe ake takarda, karshe aka ajiye kuri’a, duk wanda yasame kuri’a mafi rinjaye shine zai zama sarki, a tsakaninsu biyu, kafin ranar Zaɓin.
Kafin Ranar zaɓe Ukshe da Abu Zarri sun fantsama bin bokaye dan daisu mallaki mulkin abu guda daya gigitasu dangane da mulkin, ba kome bane face ce musu da akayi dukkansu babu wanda zai mulki kasar amma a cikin kabilarsu za’a samu amma basu ba dan ko zuri’arsu babu wanda zaiyi mulkin. Haka ba karamin haushi ya suka ji ba, akan basune zasu ɗare mulkin garin ba. Dan haka suka zuba ido suga waye zai ɗare mulkin,
Ranar da za’ayi zaɓen Yaseer bni Abdullah ya tafi gun a matsayin me zaɓen Abu zarri sai ga abin mamaki dan gabaki ɗaya Emirate council shi suka zab’a.
Abin bakaramin girgiza Ukshe yayi ba, jinjina abin yayi a ranshi bayan an taya Yaseer Murna, dan suka rungume juna tare da farin ciki koda Ukshe yazo ya rungume Yaseer ya kai bakinshi kunnen Yaseer cikin jin zafi yace mishi.
“Wannan ba farin ciki ya dace kayi ba, kuka ya kamata kayi dan na rantse da karfin ikona sai kabar kujeran da karfin tsiya dama munafurtanmu kayi kace kai baka so nan kuwa kasan ranka ashe kanaso zaka sha Mamakina.”
Yana gama faɗar haka ya janye jikinshi, tare da sakar Yaseer.
Da idanu Yaseer ya raka Ukshe shi a duniyarshi ya tsani fitina, shi yasa har yau baida abokin faɗa. Sai ya shiga damuwa ak haka zuri’asu sukayita murna.
Bayan kwanaki da naɗashi sarkin Jordan na farko, abinda ya fara shine tabbatar da adalci akan kowani kabila, sannan da kuma karɓan haraji, daga attajirai da kuma yan kasuwa cikin tsarin da addin9 ya shar’anta.
Sai bautar da mutane bisa dole, da kuma shagali babu gaira babu dalili wani abun da mutane basu sani ba, Larabawa shagalalulun mutane ne, gashi a cikinsu alkur’ani ya sauka amma dan son more rayuwa sunkan buga tsiyarsu.
Sarki Yasir yana da mata daya da yara uku, Abdullah da Badi’at sai Raziya..
~_~
Zaune yake gaban Bokansa wanda yake gabashin Pakistan dab iyakar india ta kashmir,, cikin d’agawa da Izza yace.
“Ra’eez zan mallaka maka darhami milliyoyi mulkin Jordan kawai nake buƙata kota halin ƙaƙane kuwa.”
Wani irin ruwa boka Ra’eez yake watsawa a cikin wutar dake ci a gabanshi, tashi wutar tayi sama. Ta mutu baki ɗaya, kunna wutar yayi ta sake tashi sama, sannan ya juya ga Ukshe, yana girgiza mishi kai. Yace,
“Mulkin kasar Jordan banaka bane, ba kuma zakuyi shi ba. Sai dai naga zaka zama Uba ga Fadar zaka juya fadar amma bazaka taɓa xama haka ba, kuma ba zaka taɓa nasara akan Yasir ba, lokaci na zuwa da zaka mulke kasar kuskurenka shine barin kasar, da kayi kazo nan zaka ga abinda Yasir ya aikata ga masarautar baki ɗaya.”
Tashi yaƴi ya leƙa cikin wutar malamai ya hango ƙewaye a cikin fadar anata saukar alkur’ani. Ihu ya kwala yana zaro idanu,
“Meye mafita? Ya zanyi Ra’eez?”
A lokaci guda ya jefawa bokanshi ka koma masarautar kome zakayi ka tabbatar kayi amma mulkin ya haramtawa Kowani mugu da azzalumi, babu wanda ya isa hawa kujeran sai adali, karku nemi tsige shi da karfi domin masarautar zata fuskanci abubuwa.”
Haka ya tashi yabar kasar pakistan wato.
.~_~
Sannu tsarin mulkin Sarki Yasir ya gunduri munafuƙai da wasu daga cikin kabilunsa da kuma kabilun, Yahudawa da Urdawa.
Take aka cimma matsaya inda suka zarta da hukunci lokacin Ukshe ya bar kasar zuwa China niman yadda zai amshi mulki babu, tashin hankalin.
Ranar da yadawo ko gidanshi bai shiga ba, yasamu labarin kifarda Sarki Yasir, abinda yaja sanadin mutuwarsa, wanda ba’a fahimci taya ya mutu ba.
Abin mamaki ana sallar gawarsa, aka fara samun matsalar. Ambaliyar ruwa wanda yayi sanadin rayuka da dama. Ba’a dawo daga jimamin mutuwar ba da ambaliyar sai ga rikici ya kaure tsakanin urdawa da Yahudawa, ana cikin haka Zuri’a Yasir suka fara nasu da Zuri”ar Abu Zarri.
Take abinda boka ya gayawa Ukshe, ya dawo masa . Dan karshe shine aka samu da maganar, kallon kujeran fadar yaƴi firgita, abinda yafito daga bakinshi ya girgiza kowa a fadar mikewa yayi yace.
” Yaku Banu Hashim! Ni Ukshe na naɗa Abdullah Bni Yaseer bni Alhashmiyya, a matsayin sarki ki akwai me jane, Kabilarmune shi jininmune shi Kuma bakuraishe ne danmu kuma shine yafi dacewa da mulkin kasar Jordan.”
Dake larabawa nada kishin kabilarsu ba tare da wani ja ba, suka amince dan matukar suka ki amincewa, tabbas tsakanin Banu Nazir Ko Banu Hussein sune za ace subasu mulki, su kuma basaji zasu bawa maguzawa ko yahudawa mulki..
~_~
Bayan shekara ashirin da Hudu abubuwa sun faru. Wanda babu wadda yasan meye silarsu sai dai ancigaba da shimfiɗa mulkin zalinci da cutar da talakawa, ana ɓarnatar da dukiyar kasa, ba tare da sanin Mahakunta ba.
*Syria Damascus 2017*
Janye yake da wata budurwa bakar fata, har inda ake saida mutane fincikota yayi ya wurgata yana faɗin.
“Darhami dubu ɗari.”
Kallonshi kazab yayi tare da fashewa da dariya yace.
“Kai Malam muna sayansu a darhami dubi biyar kai har dubu ɗari.”
Wani kallon Banza yayiwa Kazab sannan yagyara tsayuwa yace.
“Baiwata da kake ganinta, tana da kwarewa a abubuwa irinsu girkinmu na larabawa, tana da kwarewa a gyaran ɗaki kai har dakunar dabobi zata gyarashi tsaf.”
Wani irin kallo suka mishi ya ɓata rai, dan asalin kallon tuhuma suka mishi, take ya dai daita nutsuwarshi. Tare da ɓata rai, tasowa ɗaya daga cikin asakar yaƴi yazo gabansu ya kallesu, kallonta yayi yadda take zaune akasa take mata kafa yayi ta fasa kara, tsaki yayi yana faɗin.
“Da tana da juriya da mun ɗauketa, ka maida ita ƙawai bazamu sayeta ba.”
“Toh nace kasaye tane? Gashi zaka nakasata kalan wani yazo yaganta a nakashe yace bazai sayeta ba, Ba lallai bane ka sami nasara akan burinka ba ama cimma burinka ta kowacce dama shima tankar shafe wasu tarihine, Tashi kinji ai maganin Yan mata irinku kenan, kin baro gatanki dan soyayya kinzo min daga haɗuwar face book, kinga rayuwa nama fasa sayar dake muje na cillaki a ruwa kimutu ma nima na huta.”
Janta ya shigayi ya nufi hanyar da zai maida shi cikin gari, musaman wanda zai kaishi gabbar ruwa.
Ganin dagaske mugun matashin nan yake yasa Kazab yace.
“Mun sayeta Darhami 80! Daga kanshi ba kari,”
Yatsina fuska yayi tare da tureta ta faɗi kasa, yace.
“Jeki suma su san yadda zasuyi sake ni sai Allah ya rabani ds k’aya.”
Kuɗinshi suka watsa masa sannan suka ja igiyar da ya ɗaureta da shi suka jata cikin wani mota kiran bus suka jefata ciki, tare da rufe motar.
Komawa gefe da jikin motar suka ɗanyi kus-kus, sannan suka dawo tare da tadda motar su uku a gaba, dan maza ne su.
Tafiya suka fara idan suka ji harbi sai su tsaya dakyar dai suka fita a yanki mafiya a hatsiri a cikin garin damascus yayinda suka dinga samun madakatai sabida, dubi da yanayin da kasar syria ke ciki, yasa suka samu tsaiko kafin ha na tsawon awowin arba’in da takwas, kafin suka fita zuwa bakin boda.
Koda suka isa bodan nan wani iftila’i ya afka musu, dan ina isa gun bom na tashi sakamakon harin da Kungiyar sakai ya Isis, wanda yaja rasa rayuƙar dinbun mutane dan dole aka buɗe bodar wasu suka fita daga ciki kuwa har da motar da Baiwar nan takeciki.
Abinda yasa aka bar motar sabida alamar tambarin Masarautar jordan da take dashi. Shi yasa suka wucce ba tare da wata matsala ba, a cikin motar kuwa zaune suke su kusan goma sha biyar har da kartin maza, a cikinsu kallonsu tayi tare da kauda kai, haka suka cigaba da tafiya duk da sunyi kwana biyu a cikin garin damascus amma basu samun yancin leka waje ba, sakamakon yanayin garin, tana kallon wata mata da kanta ke jikin wani mutum watar wacce take ɗauke da juna biyu sai juya kai take, alamun tana cikin wani yanayi. Kallon mijin matar tayi tace.
“Matarka bata da lafiya ne?”
Gyaɗa mata kai yayi, cikin damuwa yace.
“Eh!”
Ganin yadda matar take gumi lokaci ɗaya ta fahimci haihuwa ce, dukda bata tabbatar ba. Kallon matan cikin motar tayi tace.
“Ku baje mayafanku,”
Da sauri suka buɗe tare da bazawa, dake cikin motar kaman cikin j5 ne dan haka matan suƙa mike ita kuma ta gyara matar, wacce take nishi tare da kiran sunan Allah. Cikin ikon Allah sai ga jariri ya fasa kuka, ajiyar zuciya matar ta sauke, sannan ta koma ta lumshe idanunta alamun gajiya, dake Allah ya takaita mata wahala har da mabiyar wato Mahaifa suka faɗo da yaron, gyara matar tayi sannan ta duba jakarta yar karama irin ta gefen nan wadda ake ce masa side bag jakar gefe, ta ciro sabon audugar mata da kuma sabon pant tasawa matar, audugar matan sannan ita kuma tasa wndo. Sauke mayaffan sukayi lokacin wata matashiya ta naɗe babyn, tana murmushi tace.
“Yar uwa! Ke nurse ce?”
Kallon yarinyar tayi ta girgiza kai sannan tace.
“Kakata ce unguwar zoma a kauyenmu na taso tana karɓan haihuwa.”
Taka birki akayi suƙaƴo gaba motar kamar……..
Vote MJ# Follow Mai_Dambu…….
_Wallahi Vote ɗinku idan bai kai 300 ba Zan sayar da Book ɗina ba karya….Wannan shine Page ١_
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
🏰🏰🏰
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
🏰🏰🏰
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Not Editing❌
Page-٢
Salati suka saka baki ɗayansu, ba kome ihun mutane tare da dukan motar ana harbi asama yasasu curewa guri guda, tare raba idanunsu ganin ana ƙoƙarin buɗe, tsuru tsuru suka yi. Hankalin kowa a tashe, jin ba’a buɗe ba yasa dukkansu suka sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma a tare, sai kallon juna suƙe can aka tadda motar suka bar gun. Abinda ya bata mamaki a tafiyarsu ba kome bane sai yadda mutanen da suka sayesu basu damu dasu ba, dan suna jin kukan Jariri baisa sun tsaya ganin meye ya faru ba, tunda sun saye su babu ruwansu dasu.
A haka suka cigaba da tafiya basu kuma haɗuwa da kome ba, har suka isa garin jordan, inda aka tsaya a kofar shiga kasar aka fiddasu musaman da karnin jini ya ɗagawa kowa hankali, harsuma mutane, wani gida aka kaisu inda zasu zauna kafin zuwa gobe a shigar dasu cikin garin Amman capital city ɗin Jordan kenan.
Suna shiga gidan suka tadda mata a tsatsaye ga maza ma haka, suma sunata aiki ana tsulla musu bulala.
Kallon juna suka yi sannan aka nuna musu inda zasu zauna ɗaki ne babba sai ban ɗaki guda ɗaya,inda mata zasu zauna kenan sai kuma mazan suma haka.
Suna shiga dakin basu tsaya kome ba, ruwa suka tara me shegen sanyi suka wanke yaron dashi tare da uwarsa. Da sabulun baiwar nan, da take wanke yaron saida kwalla ya zubo mata, sabida kewar nata dangin gashi tarabu dasu.
Sai da tawanƙe shi tass sannan ta naɗe shi a gyaren uwarshi itama tashiga wanka.
Kallon yan matan suke gata bakar fata amma she have pure heart. D’aya daga cikinsu mika mata hannu tace.
“Zahrah sunana! Kefa?”
Murmushi tayi wanda zai nuna maka cewa dabi’arta ce murmushin ta mika mata hannu tana cewa.
“Nafisat! Amma Feener ake kirana?”
Yarinyar da ta ɗauki yaron lokacin da aka haifeshi tace mata.
“Ni kuma Zakiya” wata acan gefe tace mata.
“Mujahida” ta kusada Mujahida tace.
“Hinduh” haka sukayita gabatar da kansu, sannan me jegon tafito tana murmushi tace musu.
“Ni kuma Salmah, daga Afganistan”
Gyara zama Feener tayi tace..
“Ni kuma daga Senegal”
Zakiya tace” Oman daga can nake”
“Algeria daga can nake”
Hindu tace.
“Daga libya na fito” haka suka gabatar da kansu, cikin jimami Salma tace.
“Gashi zamu tafi masarautar Jordan, me cike da mugun hatsari dan matukar kayi kuskure toh sunanka gawa, don Allah kamar yadda muka hadu a nan karku bari arabamu ta hanyar rasa ɗayanmu, musaman ke Feener kece bakar fata, kuma zaki iya fuskarta k’alubale sabida nuna wariyar launim fatar da zasu nuna miki.”
Tsorone ya bayyana akan fuskarta, tabuɗe bakinta zatayi magana aka shigo musu wani bushashiyar gurasa tare da wani wani irin miya, haka suka zauna zasu ci dan tunda suƙa baro syria bushashen gurasa ake wurgo musu, haka zasu ɗauka ci ruwa kuwa a wani gora ake wurgo musu, dan haka suna ganin wannan suka rufa musu dan rabawa dai dai akayi, ta ɗauki nata ta bawa. Salma tace.
“Kece kike bukatar abinci, ni ban damu da abinci ba tun tasowata, bana cika damuwa da ciye ciye.”
Girgixa mata kai Salmah tayi cikin damuwa tace.
“Don Allah kici ni wannan ya ishe ni.”
“Karki damu, ni ba damuwata bace abinci nasaba da rashin cin abinci haka halitta ta take, kici kawai.”
Data ga zasu dameta mikewa tayi ta shiga ban ɗaki tayo alola, sannan ta shigo ta fara sallah, sai da ta sauke bashin kanta sannan ta sallaci na ranar da tarasa shi.
Haka ma duk sauran sukayi, kafin suka shimfiɗa hakarkarinsu a kasa suka kwanta.
~_~
Karfe uku na dare aka tashisu badan kome ba sai dan su fara ganin yadda bayi suke cin mugun wahala, har akayi sallah asuba, suma suƙayi sannan aka sake shigo musu da wata farar shigafa da madara a cikinsa, aka turo musu dake kamar kunu ne shi kan Feener tasha, tana lumshe idanunta. Amma ba sosai ba tabawa Salmah sauran sabida cikin jego. Suna cikin karyawa aka kawo wasu yan matan aka haɗa dasu, karfe takwas suka aka fito dasu, yan matan da akakawo biyu shekarunsu zai kai nasu zakiya, d’aya kuma zasu yi sa’anin da Salma sai wata yar karama wacce Feener na rike hannunta, har suka shiga motar. Babbar cikinsune ta kwace hannun yarinyar daga Feener tace.
“Baki ganinta baka ce zata goga miki bakinta kema ki zama munmuna irinta.”
Kallon Feener yarinyar tayi, cikin danuwa tace.
“Kaltu!!! Wai haka ne zaki goga min bakinki?”
Murmushi Feener tayi tare da girgiza mata kai tace.
“Bazan goga miki baki ba, amma tunda yayarki bata son muzauna tare zaki iya zama gunta kat tayi kartayi fushi dake.”
Haushine ya kamasu Hindu suka ja tsaki tare da cewa.
“Mukan bamu da wannan duhun kan domin itaƙanta alkur’ani da bakar tawada aka rubutata, sannan Babban Ladanin musulunci Bilal , bakin fata daga Ethopia dan haka mu bama cikin larabawan da suke kyamar launin fata.”
Riketa Feener ta ɓata rai dan duk cikinsu har Salmah, Feener ta girmata sosai balle kuma ita kanta yayar Yarinyar
A haka suka shiga motar, suna taɓa hira sama sama, har suka shiga garin Amman. Kafin suka nufi hanyar masarautar, tun kafin su isa masarautar suke kallon garin sannan aka mike hanyar masarautar, anan suka kara tabbatar da kansu sun iso wata nahiya ta daban.
Tafiya ce me nisa wanda ya ɗaukesu mintina arba’in sannan suka isa cikin masarautar wanda idan ka ganshi zaka ɗauka ginin akayi, a wani guri sannan aka ɗauka aka ajiyeshi da gindinsa.
Tsarin masarautar kawai abin burgewa ce, sabida ginshikan da aka gina masarautar, saman ginin inda aka ɗaura wani abu kamar tubali me zubin ruwan gwal, sai kyali yake anyi wani tsarin gini kamar masalaci, dukda masalacin yana bakin kofar masarautar. Wato faɗar yawan tsarin masarautar ɓata lokacine.(Zauren mai dambu sunga hoton masarautar.😹)
Suna shiga masarautan a tsakiyar fada aka tsayar da motar, mutane ne a cike a gun. Daidai an fito dasu, aka fito dasu ganin an janyo wata mata tana kuka tare da cewa.
“Wallahi bani na aikata ba, taya zan kashe sarki Ashraf adalin sarki don Allah ku min rai bani bace, sharri aka min wani katon badakare. Wanda kana ganinshi kaga (Kamal minna😹) tare da wani kato kamar (Jaheedu) suƙa ɗaure hannun matar sannan suka saka kanta akan wani katato, tana kuka tana kome, tace.
“Ya Allah ka kawowa Masarautar nan agaji da ceto, Ya Allah ka kawo wanda zai dakatar da abinda ke faruwa a cikin wannan masarautar.”
Saka takobi sukayi aka gintse kan matar, ya faɗi kasa ihu Mujahida tasaka tare da yankan jiki ta faɗi, a gun. Lumshe idanu Feener tayi dan tabbas wannan masarautar ba kanwan lasa bace, babu sauki a cikinta balle wajenta. Yunkurin kashe sarki kawai an gintsi kan ɗan adam ina kuma kayi wani abun da bai kai haka ba toh tabbas sai dai a cinye namarka ɗanye.
“Kowa ya kwan dasanin cewa, duk wanda yayi yunkurin kashe Sarkinmu, shine zai fara shekawa Lahira dan haka ƙuma bakin Bayi kushiga hankalinku dan ƙuna kuskure zaka buɗe idanunka a lahira ne, na rantse da Allah sarki takobina a washe yake domin cusge kayikan mutane.”
Korasu akayi kamar wasu dabobbi, inda aka nufi wani shashi daban daga masarautar aka kaisu, sunga bayi a cure guri guda suna ƙuka, wani yaro da aka barshi yana birgima yana kiran .
“Ammiih!!!”
Yabawa kowa tausayi dan ga duk alamu ya nuna cewa Uwarsa ce aka tsinke kanta, yadda yaron yake kuka saida yasasu duƙkansu kuka, a hankali Feener taje gunsa ta ɗagashi tare da rungume shi itama kwalla na zuba idanunta, tace.
“Ya isa ukty! Amminka tana cikin aljanna, kuma zata ji daɗi idan kayi mata addu’a.”
D’ago kanshi yayi gana sauke ajiyar zuciya, ya kwantar da kanshi a kirjinta yana ce mata.
“Ammina zata dawo?”
Sake rungume yaron taƴo a wannan karon takasa tsayar da kukanta, domin tsakaninta da Allah take shasheka, wannan wacce irin masarautarta ce haka da dan adam da ruhinsa basu da kima, a yau da tashigo kawai tabbatar da wani alkarya tashigo, a yau tasan duniyar da tashigo, me cike da tsantsar zalinci da mugunta.
Shigowan wasu karfaffan mata yasata ɗago kanta, kallonta suka tare da taɓe baki cikin izgilanci.
“Ke bakar mutum! Daga wata duniya kike?”
D’ago jajjayen idanunta tayi sannan tace.
“Daga Senegal!”
“Yayi kyau, toh ku gabatar mana da kanku dan ace a cikiku akwai wacce take da kwarewa a girki hatta girkin dabobbi ta iya, dan sarkinmu bayi dame girki.”
Mikewa tayi tana kallonsu tace.
“Nice!”
Dariya suka saka mata, sannan suka ce.
“A haka sarkinmu zaici a bincikin? Mutumin da baici na gogaggun turawa ba, amma muje a baki kayanki, mu kuma gabatar dake ga Gajin iko, kafin akai ki shashin da zaki zauna.”
Wani shashi na gidan suka nufa dani, wanda yake da tsari na daban da masarautar. Ginin kawai abin kallone a haka nayita binsu har cikin, wani tangamemmiyar falo muka shiga me cike da kayan more rayuwa, ta sarakuna. Katon hoton wani farin dattiji cikin shigar alfarma. Fuskarshi cike da farin gashi.
Ko cikin falon bamu shiga ba, muka tsaya wata baiwa ce ta fito sakamakon jin sallamar Naja’atu.
Murmushi tayi tace.
“Ina gaida uwar ɗakin bayin Jordan meke tafe dake?”
Gyara tsayuwa Matar tayi, sannan ta nuna mata Feener tace..
“Gata nan mun kawota Gajin iko ya gantane wannan karon har da bakaken wake a cikin masarautar.”
Zuɓa mata ido baiwar tayi kafin ta gyaɗa kanta tashige cikin wani falon, can sai gata tafito tace.
“Ku jira yanzun zai fito.”
“Toh madalla.”
Wasa-wasa sai da suka shafe awa ɗaya a gun kafin dattijon yafito rike da sandar dogarawarsa ta Azurfa kana ganinta sai wani irin shaiki take, zama yayk duk suka zuɓe tare da kai mishi gaisuwa. Jinjina kanshi yayi idanunshi kan Feener wacce kanta yake sunkuye bazato yace.
“Shekarunki nawa? Sunanki? Daga wani yankin duniya kike?”
D’ago kanta tayi taga yayi mata wani irin kwarjini da cika ido, sunkuyar da kanta tayi jikinta na karkarwa, bakinta na rawa har tana tauna harshenta tace.
“Safeenat Hadi! Daga senegal”
Bai kuma ce mata kome ba, ya maida hankalinshi kan agogon falon, sannan ya kalle Naja’atu yace.
“Ku kaita.”
Mikewa sukayi tare da ita suka fita a falon.
Shiru yayi zuciyarshi nakin amincewa da baiwar Sarkinsu, amma bai da hujja hanata.
Can gun bayi aka maida ita, tare da nuna mata ɗaki. Zuwa anjima za’a zo akaita, tare da jera mata dokokin zama a cikin gun girkin.
~_~
Bayan awa gudu sai gasu Naja’atu, kiransu Hindu akayi suka tafi wani bangare na gidan, aka sasu sukayi wanka, sannan aka basu wani riga iyakarshi ya rufe kirji,amma cibiyarsu a buɗe, yana sa guntun hannu, amma tawajen cikin kuwa wasu silala aka saka masu wani irin kara, sai wani wando me tsagu har cinyar gefe da gefe, ga wani jigidar karfen, sai wani awarwaro da aka basu suka saka. A kafarsu wanda yake bada wani kara cuuu.
Sai wani hula shima me karafun, wanda kana juya kai zai bada sautin.
Sakasu akayi a gaba, aka kaisu wani falo na daban gun cike yake da manyan mutane. Suna shiga gun aka sauke sauti dake akwai makaɗa, take aka umarce dasu fara rawa. Irinta larabawan zamanin Jahiliyya. Dake dukkaansu larabawane. Kuma sunsan kan rawan, ita rawan dai anayinta da k’ugune sannan anayi ana juya kowani kusurwa najikin……
VoteMj#Follow Mai_Dambu….
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page-٣
Wannan dabi’ar da ake a cikin masarautar iya emirater council ne suƙe wannan ɗabi’ar. Banda sarkin dan sam bai ciƙa shiga sabgar ba, kodan kasancewarsa shi ɗin matashine ko da yake baza ace haka ba, dan idan akayi dubi da yanayinsa ba mazaune bane a masarautar, kaisu wani ɗaki akayi nan wata baiwa ta nuna musu yadda zasuyi rawan sannan suka fita zuwa wannan falon.
Inda suka same su da manyan cikin fadar, nan aka sake musu sauti suka shiga rawan yayinda makaɗa suka shiga sake musu sauti, gefe guda manyan fadar suna watsa musu salala, tare da ruwan taccecen inabi…
Duk wannan abinda ke faruwa Sultan Ashraf bai san da haka ba, shigowar Amir Ukshe ne ya tsayar da kiɗan da rawan. Zama yayi a cikin tattausar shinfiɗinsa, yana karewa kowa kallo kafin yakishingiɗa aka cigaba da shagali.
***
Wani kitchen aka kaini mai girman gaske, kome na cikin kitchen ɗin royal colour ne, wato komi na na cikin kitchen ɗin ruwan golden ne hatta cokala da kofuna duk iri ɗaya ne. Bangaje ni da akayi ne ya dawo dani daga duniyar kauyanci, tsaki matar tayi cikin izgilanci tace.
“Matsalar akawo maka bayi daga africa kenan, gashi tazo ta buɗe baki tana kallo kamar wata doluwa, zaki wucce ko sai nasa guard sun zanemana ke”
Gaba nayi ina raba idanuna, bansan me zanyi musu ba dan haka na tsaya a gun ina kallon yadda suke haɗa girki kai kace taro ake. Kafin na ankara sai ji nayi an zabga min bulala a jikina, a razane na ɗago wani murɗeɗɗen mutum ne sanye da farin riga da bakin wando anyi masa tambarin masarautar a gefen kirjinshi ta dama, dariya duk masu girkin suka saka, nuna min aikin wata dattijuwa yayi, an ajiye min, kasancewa an faɗa musu na iya girkin larabawa su gwadani sannan akaini ɓangaren da zan zauna.
A sanyayye na karasa gun na tsaya buɗe panpo nayi na wanke hannuna, sannan na kalle abinda zanyi. Man zaitun da y’ay’anshi, zuma, da tafarnuwa sai kayan kamshi dangin curry masala, da kuma kaza katuwa, sai dankalin turawa da kayan miya tattasai ja da kore tumatir manya guda huɗu, sai wani maggi wanda yake da faɗi sai albasa, dafa kafaɗata tsuhuwar tayi sannan tace min.
“B’akuwa wannan shine irin abincin da Sultan Ashraf yafi so, da fata..”
“Kee! Tsuhuwa koma bakin aikinki ko kuma jikinki ya nusardake inda kike.” inji mutumin da ya zane ni, da sauri matar koma bakin aikinta.
Shiru kitchen ɗin ya ɗauka baka jin kome sai karan ajiye filet ko wani abu ko kuma cokali. Cikin sauri na fara aikina, ana wanke kazar ajiyeta a matsami ruwan ya gama ɗigewa, sai a koma kan irish ɗin shima a yanyankashi ba yankan chips ba. Yankar albasa akwance, za’ayishi sai a ajiye a cikin wani bowl akoma kan kayan miyar shima yanyankasu ke, a zuba akan dankalin, sai a zuba man zaitun da zuma a cikin kayan miyar tare da maggin da y’a’yan zaitun nan a cakuɗasu guri guda, sai a ɗauko kazar a zuba a cikinta, idan dama an raba kazar ta kirjine sai a saka zare da allura a ɗinketa, idan kuma ta kasa aka buɗeta sai a juye takasar, amma larabawa sunfi buɗeta ta kasa.
Sai a ɗinketa sannan a sake niman bowl azuba man zaitun, da maggi a haɗa ashafa a jikin kazar sai a saka an pan ɗin oven a saka a cikin.
Duk bayan mintuna goma zai ayita buɗewa ana zuka wuka a ciki, yadda za aji dahuwarsu.
…….. Bayan mintuna talatin da biyar aka ciro, matar da take da alhaki kula damu, itace zata fara dubawa. Tana gama dubawa ta kalleni tura min tayi gabana, cikin tsukewar fuska tace.
“Kici.”
Cikin sanyin jiki na yanki namar na kai bakina naci, suna ganin naci suma suƙa rufawa namar, tass suka cinye.
…… Daga nan suka sani dafa normal tea. Irin nasu na larabawa wasu ganyenma bansan su ba sai yau, ina gama suka sake bani aiki. Kai nasha azaba dan kafata har rawa yake. Dakƴar suƙa sallame ni daga kitchen ɗin.
***
Ina shigowa ɗakinmu nasami Yan matan nan, suna kuka cikin sauri na karasa gunsu na zauna a tsakiyarsu. Daura kansu suƙayi a jikina tare da fashewa da kuka, suna cewa.
“Feener! An wulakantamu anci zarafinmu, bayan munyi musu rawa sai da suka nemi yin lalata damu. Feener har da Sarkin ma.”
Karanta Littafin Yaro Ne Hausa Novel
Zaro idanu nayi waje, Zakiya tace.
“Feener Mujahida an mata fyaɗe tana bay..”
Turesu nayi na shiga ban ɗakin na sameta tsugune rungume da jikinta tana wani irin kuka, durkusawa nayi na rungumeta. Cikin kuka tace.
“Feener! Narasa darajata, dama haka bayi suke fuskanta? Na rasa iyaƴena a yakin syria ban taɓa kuka irin nayau ba gashi akan idona sarkin wannan masarautar yake tamin haddi bayan sun wulakantamu. Feener zan gudu.”
Girgiza mata kai nayi cikin kuka nace.
“Kiyi hakuri”
Narasa me zan gaya mata, dakyar nasata tayi wanka, sannan tafito a hankali abincinmu aka kawo mana, a wulakance aka ajiye mana, nice na cigaba da lallashinsu har suka taɓa abincin zan fara ci kenan aka buga kofar mikewa nayi na buɗe.
“Kizo mu kaiki shashin Sultan Ashraf yau zaki fara aikinki.”
Fitowa nayi na bi bayan mutumin. Fita mukayi daga shashin bayi sannan muka nufi cikin wani shashi wanda yafi kowani shashi kyau da haɗuwa,
Tazarar tafiyar da yake tsakanin get ɗin gidan da cikin tafiyace ta minti arba’in da biyar, amma cikin sauri muka isa gidan, bansan yadda zan kwatanta muku yanayin gidan, domin baka jin motsin kome a gidan sai takuna, kasancewa takalmina flat ne toh kuma yana bada sautin, tun da muka haura barandan. Masu tsaron gidan suke bina da kallo sabida sautin takalmina, falon farko da muka shiga, aka dakatar damu, wani bulalar me kama da itace aka zabga min a kafana, sai da nasake kara.
“Shiiiii!” shine abinda me tsaron kofar falon, ganin haka mutumin da ya kawo ni yasake murmushi can kasa makoshinsa ƴace.
“Ghaniyu muna godiya da tarɓan da tasamu,”
D’aga mishi hannu mutumin yayi, muka wucce, kwalla ne ya shiga saukowa a idanuna, tare da tarin dana sanin mara amfanin da nakeyi tun bamu isa cikin ba. Falon farko babba ne na fitar hankali, ga kaƴan alfarma a cikinsu. Sannan muka ratsa falon dan mun samu da mutane suna zaune babu wani hayaniya ko magana asalima zaman hutawa suke.
Haka muka wucce su babu wanda ya dago ya kallemu, balle kasa ran zasu mana magana, wani dogon korido mai tsayi shima tafiyar minti goma zakayi ya kaika kofar falo na biyu.
Muna zuwa aka buɗe mana kofa, muka shiga ciki mun sami mutane biyu a zaune kowannensu da abinda yake yi, sannan muka wucce, inda mukayi tafiyar minti ashirin da ɗaya, sannan muka nufi wani tafkeken falon me cike da abubuwan burgewa, irinta gidan sarauta. Babu kowa a falon sai tv da yake aiki. Tsayawa yayi a gun sannan ya kalle ni tare da mika min, takarda yace.
“Idan Allah ya nufa zamu sake saduwa toh sunana Sheik, zaki iya tsayuwan jira har lokacin da ya fito sai kisan yadda zaki bashi takardan domin yasan da cewa kece bakuwar da zaki fara girka mishi abinci sannan kiyi takan tsantsar da aikinki domin nan ba’a san kuskure ba kina yin abu kaɗan zaki ji a jikinki.”
Yana gama faɗar haka ya juya ya tafi, abinshi.
Jingina nayi da bango ina kallon Inda Allah ya kawo ni. Bayan wasu mintoti, na gaji da tsayuwa na zame na zauna, na cigaba da tsammanin fitowar sultan, shiru kake ji.
Awa ɗaya ya wucce wasu awowin suka wucce bai fito ba. Can da naga har lokacin sallah yayi bai fito ba, sai na juya na fita niman inda zanyi alola da sallah. Karshe dai sai da na dawo shashin bayi nayi sallah sannan na koma.
Ashe ina fita shima yana fitowa, ganin takarda asaman kujeran falon yasashi sanin an shigo falon yana ciki bai bi takai ba yayi ficcewarsa, zuwa masalaci. Koda ya dawo a falon farko ya tsaya sabida mutanen da suka zo masa dubayya, da kuma mishi Jajjen ya jiki. Suma dai matasane sa’aninshi kuma yan Kabilarsa na Banu Hashim, daga cikinsu kuwa har da Jikan Amir Ukshe.
A hankali nake takowa sabida ba’a son karar takalmina ko sautin da zai dame mazauna gidan.
Da sallama na tura kofar na shiga duk sunji sallamar amma babu wanda yayi yunkurin amsa min, asalima kamar basa gun kare musu kallo nayi anan na fahimci dukkansu yan bana bakwai ne.
Abinda yasani cewa haka kuwa ba kome bane sai dan luran da nayi dan akala bazasu wucce 28-29 ba, domin babu wanda ya haura talatin. Taɓe bakina nayi na wucce,
Har inda aka kaini, tsayuwa na cigaba dayi, wasa wasa banga idanun sarki ba sai bayan sallar la’asar, na gaji da zama na mike zan koma can shashin bayi, ina rike handle kofar zan fita shima ya rike zai shigo. Bazata muka buɗe kofar tare, har sai da kaina yayi karo da kirjinshi.
Da sauri nayi baya ina zare idanu, bai tsaya bin takaina ba yayi wuccewarshi, bin bayanshi nayi da ido tare da dafe goshina nace.
“Wayo ni Safinatu! Toh waye sarkin ne? Toh ko wannan ne? Amma ai lokacin zuwanmu baya falon mutane huɗu muka wuce a falon farko, na biyu kuma mutane biyu ne, ai ko shine Sultan Ashraf ɗin?”
Ni kaɗai nayita lissafin can nace.
“Toh kenan sarkinsu yarone, taɓ dole yayi abinda ya gadama,”
Tsaki nayi cike da takaici.
“Mugu azzalumi sai da ya ɓatawa Mujahida rayuwa dan sun ɗauki mulki sun bashi, Allah ya is….”
Ganin fitarshi nayi da sauri nabi bayanshi ina cewa.
“Ji mana! Don Allah zoka min iso da Sultan Ashraf.”
Nayi haka ne dan na cire tantamar dake raina, ko kallo ban ishe isheshi ba, sai ma masu tsaron lafiyarshi da suka tare ni suka kaini wani dakin duhu. Me kula da bakin kofar ɗakin ya shiga yayita zane ni. Har sai da nayi laushi, wanda yaja har na suma, sannan suka watsa min ruwan kankara, a firgice na farka sabida azaba ko kuka ban samu damar yi ba,, cikin kakkausar mutumin yace.
“Daga yau ko tsuntsu kika ga zaiyi kuka wanda zaisaka Sultan cikin damuwa ke zaki kora mishi,, sannan ki tashi kije kiyi aikin da aka kawo ki yi, Sannan sultan baya son hayaniya koda kuwa ta fashewar abune toh zaki ji a jikinki”
Jawo yayi ya watsa a waje tankar kayan wanki. Dakyar na mike zuciyata na min zafi, lura da nayi dare yayi sosai yasani niman hanyar can shashinmu.
Koda naje buɗe kofar falon na biyu najishi a rufe dole na dawo falon Sultan, abin bakin ciki koda na shima nasa a rufe karshe sulalewa nayi na zauna, na fashe da kuka.
“Wani tsautsayine ya raboni da gatana nazo nan ana wasan kura dani.” abinda nace knn ina kuka.
***
“Yallaɓai Alexandra mun mun sami labarin an sami wata Yar african da.”
“Benjem kaje kasan meye ya kawo Yar african masarautar jordan.”
Daga haka yayi shigewarsa ciki dan yayi imani da abinda bokanshi ya gaya mishi.
***
Fitowa yayi zai tafi masalaci ya ganni a zaune na cusa kaina cikin cinyoyina, kauda kanshi yayi ya bar gun. Saukar bulala naji yasani mikewa zubur ina sosawa ciki mutumin ya nuna min na shiga, yana bina har kitchen ya nuna min, sannan ya nuna min bango inda aka kafa wata yar allo da aka saka jerin sunayen abincin da za’a girka……