Hunayda Love and Romantic Love Story

Hunayda Love and Romantic Love Story

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*

 

(Home Of Qualities And Trusted Writers Of The Nation)

 

 

Bismillahi-rahmanir-rahim.

 

*GODIYA*

 

Dukkan yabo da godiya su tabbata agareka ubangijin talikai mamallakin ranar sakamako. Agareka kad’ai muke neman taimako kashiryar damu kan hanya madaidaiciya.

Tsira da Amincin Allah su k’ara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad s a w da alayensa da sahabbansa har izuwa ranar tashin k’iyama.

 

 

*GARGAD’I*

 

Wannan labarin mallakar marubuciyar ce ban yarda wani ko wata ya juyan labari ba tare da izinina ba.

 

 

 

*TSOKACI*

 

Wannan labarin k’irk’irarren labari ne banyi shi dan wani ko wata ba basira ta ce idan yayi karo da labarin wata ko wani yayi hak’uri arashi ne.

 

 

*DEDICATED TO FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION*

 

*GAISUWA AGAREKI*

 

Mamana Allah ya ja daranki Mamata ya biya miki buk’atunki na akhairi ya raba ki da sharrin masu sharri, alfarmar Annabi Muhammad s a w.

Allah ya jik’anka Babana Allah ya gafarta maka Allah ya kyautata makwancinka Allah yasa can tafi maka nan tare da dukkan musulmi baki d’aya.

 

Auren Wata Tara Hausa Novel

*Y’AN AMANA*

 

 

*Bestyna Teemah Sabo*

 

Kirkin ki da karamcin ki na daban ne agareni, ina miki k’auna Fisabilllah .

 

 

*Aisha Aliyu kebbi*

 

Sisterna ina matuk’ar yabawa da k’ok’arinki agareni ina miki son so fisabilillah Allah ya bar k’auna.

 

*UMMASSALMA A ABDULLAHI*

 

Masoyiyata ina k’aunarki Aminiyar k’warai.

 

 

*❣️HUNAYDAH❣️*

*LOVE AND ROMANTIC STORY*

 

🅿️ 1️⃣to2️⃣

 

 

Bisimillahirrrahamanirrahim.

 

 

“Hunaydah muryar wata dattijuwar mata ke tashi, daga cikin d’aki ga dukkan Alamu wadda take faman kiran bata kusa da ita,

zuwa can kamar wajan minti biyar wata y’ar matashiyar budurwa wadda bata haura shekara sha shidda zuwa sha bakwai ba, ta bud’e wata k’ofa ga dukkan Alamu toilet ne da Alamun alwala tayi labulen d’akin ta bud’e had’e da “cewa” Annah ina toilet shiyasa ban amsa ba.

 

Matar da aka kira da Anna ce ta tura mata kwanon dake gaban ta, Hunaydah maza d’auki Abin karin nan ki karya zan aike ki gidan Innarki Rabi keje kiji ya zancen zuwan mu dubiyar,

 

Turo baki nayi had’i da “cewa”to Annah wai kedai bakya gajiya da fita. Badan komai na fad’i haka ba sai dan bana son zuwa Gidan Inna rabi bana k’aunar zuwa na tadda Yaya Ammar agidan musamman da nasan cewar yazo hutu yana gida haka badan raina ya so ba na gama karyawa nayi sallar walaha kasancewar k’arfe goma tayi bayan na idar shiryawa nayi zan tafi,

 

Anna ce ta sake rafkan kira da baya nadawo yawwa Hunaydah idan kinje ki cewa Ammaru yazo gidannan Ina nemansa da to na amsa na fita.

 

Ahankali nake tafiya kasancewar haka nake tafiya ta da yawan mutane gani suke kamar yanga nake amma nikam haka Allah ya halicce ni daga unguwar gwale zuwa gadon k’aya bamu da nisa naira Talatin zaka hau adaidaita haka na fito nasamu adaidaita cikin minti biyar na isa. Unguwar Gadon k’aya dayake gidan abakin titi yake gida ne me girman gaske wanda kallo d’aya zaka yiwa ginin gidan kasan ankashe mak’udan kud’ad’e wani tangamemen gini ne wanda iya tsaruwarsa ma Abin kallo ne tun kafin ashiga gidan K’wankwasa get d’in gidan nayi wani soja ne ya Lek’o ganina da yayi atsaye yasa shi bud’e min k’aramar k’ofa na shiga.

 

 

*Writing by Ammieyn Amatullah*

 

 

*Please Comment and Share*

Post a Comment

Previous Post Next Post