Littafan Hausa Novels

Yazdad Hausa Novel Complete

Yazdad Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

YAZDAD

 

 

FREE BOOK

 

STORY AND WRITTEN

BY

FATEEMAH RABI’U

 

( GAJERAN LABARI)

 

 

BISSIMILLAHI RAHMANUN RAHIM

 

 

 

 

PAGE1️⃣➡️2️⃣

 

……………….. Filin jirgin aminu kano cike yake da mutane tako ina kowa yana jiran jirgin dazai sauka qarfe biyu daidae wasu ahali na hanga wow masha Allah daga alama suma tarbar wani nasu suka zo wata macece mai cikar zati kyakkyawa ta dan manyanta sai mata biyu maza biyu daga alama ita ta haife su, dan irin tsantsar kamar da suke da ita, wata daga cikin y’an matan ta d’ago tace ummahh qarfe biyun fa ta kusa mu matsa wllhy harna qagara inga Ya YAZDAD munyi miss d’inshi da yawa wadda aka kira da ummahh ta sakar mata murmushi tace SALIMA ai dole kuyi kewarshi tunda ya tafi karatu zuwanshi bai wuce biyu ba, sai yau daya gama gaba d’aya, wacce take bi mata ta amsa da hakane ummahh ita kuma mai suna HAFSAT cikin sauri mazan guda biyu suka katse su da cewa dan Allah ummahh ku tasu jirgin fa ya sauka,

Kishiya a yau Hausa Novels Complete

 

Cikin sauri hafsat tace ya AL’AMIN da ya JAFAR dan Allah ku farayin gaba, cikin sauri suka wuce suma ummahh dasu hafsat suka take masu baya,

 

Fasun joji keta sakkowa saida mutane suka rage sana wani matashin saurayi mai jini a jika ya fara sakkowa cike da tafiyar qasaita, WOW😱 kyakkyawa ne kamar mahaifiyarsa har yasu ya d’arata dogone but ba sosai ba, yana da dogon hanji har baka ga wani irin saje daya zagaye fuskarsa mai bala’in kyau da bakinsa madaidaici pink color mai matuqar kyau time guda inka kallesa saika sake kallonsa, Allah ya basa wani sahihin kyau mai kwantar da hankali, takowa yake cike da murmushi a fuskarsa ya nufi ahalinsa, kai tsaye wajan mahaifiyasa ya nufa rungumeta yayi cike da kewarta ummahh ya furta, da muryarsa mai matuqar dad’in sauraro Ohhh YAZDAD baka girma ne wai kai cewar ummahh murmushi ya sakar mata yace ummahh nayi kewarku ne, fah ya qarashe cike da y’ar shagwaba juyo yayi wajan qanan nashi cike da murna ya had’a su ya rumgume, suma cike da murna, suka d’oguma sai cikin muta guda biyu suka shiga suka d’au hanyar gida, cikin motar ma dai labari suke tayi cike da tsantsar shaqowa wadda zaka fahimce ta lokaci guda, yazdad yana da saurin sabo yana da shiga rai gashi da sakin fuska amma fa wani time din miskili ne na bugawa a jarida shi yasa inyana wannan yanayin na miskilance ba wadda ma ke shiga harkarsa cikin qanan nasa,

 

Wannan kenan

 

 

Kae tsaye wani gida mae bala’in kyau irin dae na masu kud’inan bana tashin hankali ba, kundae gane masu karatu, hon sukae mae gadi ya lek’o yana ganin masu gidanne da hanzalinsa ya bude masu git d’in kai tsaye parkin space suka aje motocin jikin gidan suka nufa kai tsaye cikin babban falon gidan gsky falon ya had’u sosai tsayawa ma qiyasta yadda falon yake ai za’a bata time ne, zubewa suke a kujerun falon dan sund’an gaji, ummahh tace yazdada kaje pat d’inka kad’an watsa ruwa saeka dawo ga abinci a dining, ook ummahh kawae yace tashi yayi ya nufi bangaransa shiga yayi ko ina fas d’an murmushi ya saki danshi a duniya yana son tsafta shima dai pat d’in nasa akwai d’an madaidaicin falo sai bathroom kai saye bathroom d’in ya shiga rage kayan jikinsa yayi ya shiga tolet,

 

 

Bayan ya fito ya shirya fitowa yayi babban falon gidan duk suna zaune shi kawai suke jira dukansu dining suka nufa hafsat ce ta tashi ta seving d’in kowa, bayan sun gama ci falon suka dawo aka d’ora firar yaushe gamo,

 

ASALINSU

 

Alhaji Muhammad shine asalin sunan baban su yazdad ya rasu tun suna y’an yara garama shi yazdad tunda shine babba ya sanshi sosae, yana da wayo ya rasu Muhammad ya had’u da Hajiya BINTA auran soyayya sukae suna rayuwarsune a cikin garin KANO basu da wasu dangi sosae gsky suna da kud’i na rufin asiri bana azu a gani ba, tun bayan rasuwar mahaifinsu dama ummahh tana aiki ita ta cigaba da kula da yaran nata har ta samu yazdad ya tafi karatu SUDAN koma cikin ikon rabbee ya gama karatunsa cikin nasara har gashi ya dawo.

 

Wannan kenan

 

 

 

************************ KATSINA

 

Zaune nake uwar d’aki ina aykin tunan dana saba dana d’orawa kae na kaena mn na… Ina cikin tunani naji an dafa ni haba RAMLA wae wannan wacce irin soyayya ce haka Allah ya d’ora miki ta wannan bawan Allah nan USMAN cewar qanwa ta fad’awa nayi jikinta na fashe da wani irin kuka mae cin rae cike da tsanar usman d’in tace wannan bawan Allah fa ramla ba sanki yakeyi ba Allah ya gani ke ke wahalar da kanki cike da tausayi na ta idasa maganar d’agowa nayi da idanuwa na masu kamar inajin bacci na share hawayen da suke zubo min nace khadeeja bazaki gane yadda nake ji a cikin raina bane wllhy da ina da dama dana dad’e da ciresa a raena, hakane ramla amma nidae a matsayina na qanwarki ina baki shawara ki dage da addu’a da zabin Allah insha Allahu indae ba alkhairi bane gareki Allah zae canza miki wani wadda ma ya fisa, kumah gsky ki rage tunani but kar mama ta gane kinga zata shiga wani hali kinga tun rasuwar baba itama ba wani cikakkiyar lpy ne da ita ba, gashi ba wani yan uwa gareta na azo a gani garemu ba sae Aunty baheeja kawae itama tana kano so dan Allah karki bari harta gane kuma kinga karatu zamu fara a kano kumah ance B.U.K KANO school d’in basa wasa kinga tasha wahala kamin ta samu zamu fara karatun nan so please Ya ramla karki sama kanki soyayyar wannan mutanan wadda bae san darajar mace ba, ace saeki kirasa kusan sau nawa bazae d’auka ba sana kuma bazae kira ba, wllhy aunty ramla kina bani tausai kedai taki qaddarar a soyayya take mae wuyar sha’ani cewar khadeeja, ramla tace insha Allah zan dage da addu’a kamar yadda kika ce kumah insha Allah zan maeda hankali ga karatu kuma kinga a hostel zamu zauna sae minfi karatun amma khadeeja wllhy yarda nake ji a raina kamar bazan so wani d’a namiji kamar usman ba, kumah duk abinda yake min bana jin haushin sa wllhy khadeeja har bana fatan wata ta fad’a soyayyar da ba’a sonta koh baqiyi nane kuwa, ta idasa maganar cike da shashshekar kuka, cike da tausayinta khadeeja ta gara rungume yayar tata suna da fahimtar juna a tsakaninsu saba iya boye damuwar junansu suna qaunar junansu wani time d’inma mamarsu bata taba jin wata damuwarsun,

 

 

Asalinsu yan garin katsina ne a nan sukae rayuwarsu har izuwa ranar da mahaifinsu ya rasu mae suna mlm MUSTAFA mutunan kirki, mahaifiyar su mae suna Ameenatu macece mae hakuri da kirki tana son yaran tana sosai su kad’ai Allah ya bata,

 

Sauke numfashi tayi bayan ta gama tunanin tace aunty ramla ki dae dage da rok’on Allah insha Allahu Allah zae cire miki soyayyar usman dan inaji a jikina ba alkhari bane tare dake, khadeeja ta qarashe maganar cike da tsantsar tsanar usman d’in dan itafa tunda ta lura baya son yayar tata yana wahalar da ita taji bae kwanta mataba kwata-kwata,

 

 

Insha Allah khadeeja zanyi duk yadda kikace kumah kemah ki tayani da addu’a amma Allah ya gani bana fatan in qara fad’awa wata soyayyar irin wannan, insha Allah zan taya ki da addu’a karki damu,

 

 

Ramla ramla khadeeja……. Muryar mama ce ke kiranmu koh cewar khadeeja eh muje tashi nayi nabi bayan khadeeja d’an madaidaecin falonmu muka iske mama tace ahh kuna can d’aki kudai zaman d’aki ku fito muyi fira mn ta qarashe maganar cikin kulawa ni kuwa matsawa nayi kusa da mahaifiyar tawa nad’an jingina da kafad’arta na d’an lumshe ido cike da kulawa ta shafa fuskata tace ramla lpy kuwa murshin yake nayi nace a’a mama ba komai kawai har mun fara kewarki tafiya karatun nan, khadeeja kuwa sauke ajiyar zuciya tayi tace eh wllhy mama kinga mun kusa tafiya shi yasa, mama d’an murmushi tayi itama zatayi kewar yaran nata d’aurewa kawai take cikin kwantarwa da yaran nata hankali tace inbanda abinku

ai koba karatu akwai aure fah, ai ita rayuwar mace haka take,

 

 

Nidai abinda nake so daku shine dan Allah a duk inda kuka tsinci kanku ku kare mutuncinku koh y’ay’a matane duk abinda kuka aikata Allah yana ganinku ku kiyaye dan Allah, insha Allahu mama muka amsa gaba d’aya…………..✍️

 

 

 

 

 

 

Comment And Share

 

 

Fateemah rabi’u ce

Add Comment

Click here to post a comment