Waye ya lashe zaben shugaban kasa 2023
Waye ya lashe zaben shugaban kasa 2023
ZABEN SHUGABAN NAJERIYA, INA MAFITA?
Kasancewar Najeria kasa mai kabilu da yawa (polyethnic country) yasa samun dan takara guda daya wadda dukkan mutane kasar zasu goya masa baya zai zamo abu mai tsananin wahala.
Amma idan mukayi duba na tsanaki zamu gane dalilan da yasa kowane mabiyi yake kwadayin nasa dan takarar ya lashe zaben. Lashe zaben dukkan ‘yan takarar kuwa, tabbas, abune maras yiwuwa.
To kenan me ya kamata mu yan kasa mu lura dashi game da kowane dan takara domin ganin an share mana hawayen jinin dake kwaranya daga idanuwan mu?
Amsa zata iya samuwa idan muka duba potentiality da kuma past record na ‘yan takarkaru, musamman guda biyar dinnan.
Ku biyoni domin ganin mahangata gameda su.
Sakamakon Zaben Sokoto 2023
• A yadda nake gani indai kishin kasar nan da kuma TUNANIN kawo karshen halin rashin tsaro da muke fama dashi a kasar nan ne a gaban ka, ba tareda tunanin fifita kabila kaza a kan kaza ba, to tabbas zaben HAMZA ALMUSTAPHA shine yafi chanchanta, domin shine yafi kama da wadda zaiyi haka a cikin yan takarar nan.
• Idan har burin ka shine a kawo cigaba a Arewa, dan Arewa yaji kamar dan gidan su keyin wannan mulki, kai wataqila ma a dawo da Kano FCT , to tabbas ka zabi RABI’U MUSA KWANKWASO.
• Idan kuwa burin ka kawai shine dan Arewa yayi mulki – ma’ana a hana dan kudu koda kakani-kayi, hakan na muffin koda kuwa mu yan Arewar baza muga komai a kasa ba, to ka zabi ATIKU ABUBAKAR.
• Har wayau, idan kai burin ka shine a kaskantar da Hausa-Fulani, (watakila ma har da Bayerabe), sannan kuma a daukaka Inyamuri da abokan su, Kai harma Inyamurai su fitar da kasar nan da suka dade suna burin fitar wa – wato Bayafara, to tabbas kada kayi kasa a guiwa wajen zaben PETER OBI.
Kai kuma mai burin a daura daga inda Baba Buhari ya tsaya, a kuma cigaba da daukaka Yarbawa dakuma kaisu matsayin da Allah bai kaisu, sannan a manta da cewa Arewa a Najeriya take, ma’ana ayi mata halin ko-in-kula, to maza ka garzaya ka zabi BOLA AHMED TINUBU
Daga karshe, zan tuna mana maganar Malam Bahaushe cewa: SO SO NE, AMMA SON KAI YAFI.
Saboda haka a ranar Asabar, zamu fito domin mu zabi wadda yake son mu, kuma yake kishin mu, tareda yi masa fatan Allah ya yi riko da hannayen sa, Ameen.
Thursday, February 23, 2023.
Moustapha Misau.Atiku ya lashe mazabun Shema, Majigiri, Uli a Katsina
Zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Hakazalika, dan takarar Sanatan Katsina ta tsakiya a jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 83 inda ya lashe zaben Shema. Sai dan takarar jam’iyyar APC mai kuri’u 79 sai kuma NNPP da kuri’u 26.
Sai dai dan takarar majalisar wakilai ta APC ya lashe zaben Shema, inda ya samu kuri’u 76. PDP ta biye mata da kuri’u 57 yayin da NNPP ta samu kuri’u 52.
Takaitaccen sakamakon Rukunin Zabe na Shema:
Zaben Shugaban Kasa:
PDP 84, APC 72, NNPP 25
Zaben Sanata:
PDP 83, APC 79, NNPP 26
Zaben majalisar wakilai
APC 76, PDP 57, NNPP 52
Salisu Majigiri, shugaban jam’iyyar PDP na Katsina, wanda kuma ya zama dan takarar majalisar wakilai a mazabar Mashi/Dutsi, shi ma ya lashe zaben sa da jam’iyyar sa ta PDP.
Sakamakon kuri’un da aka kada a mazabar sa mai lamba 006, Danmalka Majigiri II Sabuwar Rijiya Ward, Mashi LGA, Katsina Stat kamar haka.
Shugaban kasa:
PDP 182, APC 83, NNPP 06
Majalisar Dattawa
PDP 197, APC 82, NNPP 06
Yan Takarar Mashi/Kurfi:
PDP 195, APC 69, NNPP 08
Hakazalika, Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Katsina, ya lashe ward dinsa na dukkan dan takarar jam’iyyarsa a zaben ranar Asabar.
Sakamakon zabe daga Uli’s Polling Unit, Muntari Tela 001, Kudu III, Katsina LGA.
Shugaban kasa
PDP 127, NNPP 38 da APC 33
Katsina Central
PDP 110, APC 73, NNPP 16
Add Comment