Littafan Hausa Novels

Saurayina Hausa Novel Complete

Saurayina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

*SAURAYINA💫*

_FREE BOOK_

 

 

 

*JANUARY’S 2023 (1)*

 

 

 

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱…_

 

 

 

“`MARUBUCIYAR… (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d’a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak’in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d’aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA….. And Other’s BUT NOW (18) SAURAYINA FREE BOOK….. loading….. Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱“`

 

 

Maman Teddy Oum Aphnan Sun Ce Sun Tuba

 

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad’aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had’ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *SAURAYINA* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d’aya Allah ka k’ara shiryamu dukanmu_

 

 

 

*INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D’AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD’AKAR DA AL’UMMA BAKI D’AYA……. AKODA YAUSHE ALK’ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL’UMMA SAIDAI INA K’OKARIN WAYAR DA KAN AL’UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID’IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR *

 

 

 

 

 

“`13/1/2023/ January Friday“`

 

 

 

_ 1 to 5_

 

 

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

 

 

 

 

 

………Hairat mutuniyar kirki ce kamilalliyar macce Mai natsuwa had’ida da Addini, y’ace ga Malam bukar sani sai mahaifiyarta maryam,. Bazaka kirasu talakawa ba Kuma bazaka kirasu masu kud’i ba, Amma dik da hakan shi mutum ne Mai matik’ar tawakkali da ilmi Sosai, yara 2 kawai ya mallaka A duniya jafar shine sai Hairat, jafar ya kammala University d’insa Yanzu haka Yana Aikin banki, inda hairat Kuma ta kammala secondry d’inta yanzu haka tana jiran fitar saka makonta,….

 

 

 

 

 

Hiddah yarinya tagari saidai kanta Yana d’an rawa saka makon rashin mahaifiyar ta tana hannun kishiyar mahaifiyarta ne tinbayan rasa mahaifiyar ta tadawo hannun kishiyar mamanta, Bata tsangwamata Saidai Kuma Bata d’aura ta Akan daidai ko Rashin sa, hakan yasa take Abunda taga dama Domin mahifin ta ba mazauni garin bane…. …..

 

 

 

 

Umar matashin yaro wanda sunada Arziki daidai k’ima, tin Umar yana k’arami iyayensa Suka Sami matsala Suka rabu, sai mahaifiyarsa ta d’auke Abunta tacigaba da kula dashi, yanada yayu da dama d’ayan yayansa Tahir yanada Mata Kuma yanada Arzikinsa iya k’ima, sai ya d’auko umar ya maidashi gurinsa da zama, dayake shi mutum ne Mai Adalci haka yabari matarsa ta d’auko k’annenta 2 d’aya Namiji d’aya Macce Kuma dika lalurarsu tana hannunsa harta karatunsu, duka ya had’asu yasasu Amakaranta gaba da secondry yanzu haka dika sunkammala sai jiran saka makonsu suke……………..

 

 

 

Amar, yaro matshi maiji da kyan fuska, yanada yayu maza dama Mata harzuwa k’annensa, shikansa yayansa Yana tsaye kansa Dan ya gyara rayuwarsa……,……

 

 

 

 

…….. Tare suka jero bayan sundawo daga islamiyya dama Hairat da Hiddah k’awayene Sosai, suna tafiya suna D’an tab’a fira Akan hadda d’inda Aka basu,.

 

 

 

 

Umar da Amar ne Suka jero manyan Abokai Suma sun shak’u Sosai Dan har mutane sunsansu tare,

 

 

Had’uwa sukayi dasu hiddah Kan hanyar,

 

 

Tagansu Amar ya tsaya Yana fad’in”Ga y’an makaranta sundawo”

 

 

 

“Wallahi kuwa kaidai Bari Amar dik mungaji yau trekking mukayi” cewar Hiddah, dama sunsaba Sosai Dan dik unguwar su d’aya gidansu Hairat ne Kawai keda nisa,

 

 

 

“Gaskiya Kam islamiyyar ku da nisa ai Kuna k’okari, Wai ita Wannan k’awar taki Bata magana ne Kullum Saidai ta daure fuska tak’ara gaba idan muna magana dake halan wai batasan Ni *SAURAYIN KI* bane, ko tsoron mutane take,” ya k’arasa maganar yad’an zuba idansa ga Hairat d’in

 

 

 

Jin Abunda yace yasa tad’an murmusa tareda cewa “laifin tane saboda Bata bani labarin kaba Kuma Ni banwani sanku ba shiyasa Amma kuyi hak’uri”

 

 

 

“Ah bakomai ai dagani nasan bakida saurin sabo gaskiya, to Yanzu dai kirik’e Aranki kinsanmu Ni sunana Amar kuma in sha Allah nine zankasance mijin k’awarki nangaba k’ad’an, saiwanan Abokina ne sunansa Umar,”

 

 

 

 

“Hunmmmm to Allah ya nufa malam Amar kuma Allah yasa mudace”

 

 

Dik maganganunnan dasuke Umar baice Komai ba Amma kuma yakasa d’auke idansa Kan Hairat haka kawai yaji Allah yadasa masa sonta A zuciyar sa,

 

 

“Ah Wai yau An d’aure bakin Besty Umar ne Naga tind’azu baiyi magana ba” cewar Hiddah tana zubamasa ido, ganin Hairat yake kallo Aiko ta tintsire da dariya had’ida cewa”yeee nagane yaudai Umar ya kamu wallahi, umar kanason k’awata ko? Wallahi ga mata nabaka Umar sunan ta Hairat dama batada *SAURAYI* to haushina yau kinyi kaima kayi budurwa” tana dariya tafad’e haka had’ida janyo hannun Hairat

 

 

 

Wani irin takaici Hairat taji, “tinda Angayamiki bamai Sona ba ai dole kiyi tallata wallahi banason walak’anci Hiddah” tana gama maganar ta warce hannunta tawuce fuuuu tana masifa

 

 

 

 

Dariya kawai Hiddat take tana fad’in”bazaki jirani ba? Yau ba fira Kenan”? Dik cikin dariya take maganar

 

 

Hairat batako juyoba Balantana tabata Ansa,

 

 

 

Murmushi kawai Umar yayi tareda shafa sajen fuskarsa yace”kinga kunsa tayi fushi harta wuce”

 

 

 

“Barta Kawai zata huce nasan halin kayata muje ko,”

 

 

Wucewa sukayi Still Umar Yana murmushinsa Mai kyau.

 

 

 

Hairat kuwa da fushin ta taje gida, mama dake tsakar gidan tace”ke lafiya Hairat Wannan fushin fa,”?

 

 

 

Tana tura Baki tace”ba..ba..ba.. Hiddah bace ta b’atamun Raina,”

 

Dariya mama tayi had’ida cewa”kunfi kusa fad’anku bamai Shiga Balantana yayi kunya, Abincinki nanan Kan drowar madubi”

 

 

 

“To” Kawai tace tashige ciki………

 

 

 

Umar kuwa bayan rabuwar su Hairat ce tadawo Aransa Yana tuna maganar Hiddah inda take cewa ga *Matanan nabaka Umar* Afili ya furta “Allah yanufe hakan”………………………•••••••••••••••

 

 

 

 

 

 

_Afffff nagaji wallahi Kuma idona naciwo kusani Addu’a Allah yaban lafiya idona, AMEEN_

 

 

 

 

 

*Please kumun comment d sharing Dan Allah 🙏 nagode*

 

 

 

 

 

 

 

_BASEERATA ITACE ARZIKINA _

 

 

 

 

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

Add Comment

Click here to post a comment