Littafan Hausa Novels

Mutunta Kai Hausa Novel Complete

Mutunta Kai Hausa Novel Complete

*✨MUTUNTA KAI* 1✨

✍🏿Rashida bature

TABBAS KEDIN TA DABAN CE, MUTUM NAGARTACCE KO A INA YAKE ZAKA GANSHI DABAN YAKE, KE DIN DAWISU CE INA MATUKAR GODIYA A GAREKI *HAJIYA RAMLAT(MAI DAMBU)* HALINKI NA GARI YA BIKI HAR KUSHEWAR KI.

BISIMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.

KHUBRA! KHUBRA !! KE KHUBRA !!!

“Wai ni khubra bakya gidan nan ne naketa faman Kiran ki kina Jina kin yi banza da ni ?

Wata dattijuwace tayi maganar da alamun jikarta ta ke kira don matar ta manyan ta.

Saurayina Hausa Novel Complete

Wata kyakkyawan yarinya na hango zaune akan gado wacce shekarun ta ba zasu wuce shekaru sha bakwai ba (17 years), farace sosai farin ta irin mai yellow din nan ne,round face take dashi se manyan idanuwan da take dashi suka Kara ma fuskar nata kyau,ga dan karamin bakin ta wanda yayi pink irin me turawan nan gwanin burgewa.

mommtsa karamin bakin ta naga takeyi da alamun lissafi takeyi amma jin Kiran ta da akayi ne yasa ta turo karamin bakin ta gaba tare da sakko da qafafuwar ta qasa daga kan gadon katakon da take.

tana daga cikin dakin ba tare data daina abunda ta keyi ba kuma bata motsa daga gurin ba,ta bude dan micilin bakin ta tace.

” Allah Hajiya Diddy kin cika Kira kamar wata tsohuwar makauniya.

seki jira na kammala abunda nakeyi nazo,duk da nasan yanzu haka wani abun zan miqo miki shiyasa kike ta kwalamin kira,yanzu haka ma abun yana kusa dake amma sabida son jiki irin naki bazaki tashi ki dauka bam,ke dai kullum kinfi son kiga mutum ya kare rayuwan shi a wahale”.

Gyara zaman ta tayi tare da cigaba da abunda takeyi ba tare da ta tashi taje taji Kiran da tsohuwar take mata ba.

“shin Khubra zaki fito a cikin d’akin nan kuwa ko sena shigo na gamu dake?

rai bace kyakkyawan matashiyar da aka kira da khubra ta bar abun da takeyi ta nufi kofar futa falo fuskarta Sam babu annuri,harta Kai bakin k’ofa zata futa se kuma ta juyo tare da dawowa da sauri ta tattare duk kudin da ta baza akan gadon,ta nemi guri mai kyau ta boye.

Seda ta tabbatar sun samu gurin boyo me kyau sannan tafito falo don jin Kiran da tsohuwar take mata.

“Hajiya Diddy gani nafito seki fadi abun da zan miki don sauri na keyi ”

Da ido dattijuwar ta bi Khubra da shi tana duban ta.

kauda kanta gefe Khubra tayi tare da hade fuskar ta.

kama baki Diddy tayi tace.

“Oh ni Abu! yanzu khubra akan Kiran da nake miki ne shine kike ta faman wannan 6ata fuskar haka?

duk da ba’a cikin dakin nan nake ba na tabbata babu abunda kike tsina nawa acikin dakin in banda lissafin karya d……

karyafa kikace Diddy?

kubra tayi saurin katse hajiya Diddy daga maganar da take fada sannan batare data jirata ta karasa maganar da take shirin karasa wa bama.

ran khubra ne ya Kuma baci kamar zatayi kuka tace.

” yanzu tsakani da Allah Diddy lissafin kudaden da zanyi sarin da sune zakice kudin karya?

Gyada Kai Khubra tayi tace.

” Ehhhh lallai! tabbas ba laifin ki bane hajiya Diddy,laifi nane amma babu komai da Sannu zamu gauraya ni dake.

kuma kadan ya rage miki na dakatar da duk wata hidimar da nakeyi a gidan nan.

” in banda ma abunki Hajiya Diddy hala so kikeyi na dauki kudin nawa na kaima masu abincin kaji ba tare dana kirga ba,salon na basu kudin yayi yawa.

sororo Diddy tayi daga kan kujeran da take zaune a Kai tana kallon Kbubra,sannan ta mele baki tace.

“yanzu Khubra inba son bata ma Kai lokaci ba har kya dauki dogon lokaci kina qirga naira dubu uku? tun sanyin safiya fa kiketa wannan lissafin qirge qirge da yaqi Karewa, kin bata tsawon awanni kina abu daya.

“ Hmm Diddy kenan !

kefa bazaki taba ganewa ba,Wai kin manta cewar marashi idan ya samu naira dari (100naira)tofa jin kansa yakeyi kamar Wanda ya samu dubu dari ne?

To Ina gani nida nake da naira har dubu uku?

Khubra tayi tambayar tana kallon Diddy,ganin Diddy ta kasa cewa komai se binta da ido takeyi hakan ne yasa Khubra cewa.

“No Diddy bama se kince komai ba ni barin baki amsa.

” Wallahi Diddy a yanzu Jina nake yi kamar wacce nake da Naira million uku, shiyasa ma kikaga na kasa daina lissafin kudin nan.

Kuma kin san dole na nutsu nayi lissafin abunda zai fissheni,don idan take ne da nayi da Kar nayi lissafi duk daya suke agurin ki tunda bake kike sayan komai na gidan nan ba shiyasa bakisan Yaya duniyar take cikiba na tsadar rayuwa da muka tsinci kan mu aciki ba.

Please Diddy barin miki yar Karamar tambaya.

” shin kin kuwa San nawane kudin mudun shinkafa a kasuwa yanzu kuwa?

To wallahi tun wuri gara ki farka daga nannauyan barcin da kikeyi don yanzu shekaran yin tattali ne ya kama.

da kike maganar cewa ina ta qirga kudi na kasa gamawa.

ai ni naga amfanin kirgawan da nayi, don gashi dana sake qirgawan nasamu naira talatin ya haukan kudin.

don Allah Diddy in kinga Ina lissafi kiringa barina nagama Kar ki ringa kira na kina rudani.

“Yanzu dai gayamin Kiran me kike min don nabar kudi na acikin daki gara naje na zauna kusa da abuna.

” mtssss in kin gama fitsarar naki seki futa Kofar gida ki basu kwai(egg),in kuma sun gaji da jiran ki sun tafi to kinyima kanki,don kamar muryan isiya me shago naj…..

A dari Khubra ta nufi kofar falon su ba tare da ta jira Diddy ta qarasa maganar taba tana cewa.

“a gaskiya Diddy kibar yin haka wllh, yanzu daman arziki ne yazomin har gida amma fisabilillahi seki zauna timmm akan kujera ki rikeni da maganar da bazai amfaneni  da komai ba fisabilillahi.

tana maganar tana karasa futowa tsakar gidan, hakan yayi dai-dai da sake sallamar isiya me shago.

“wa’alaikassalam! dan Allah isiya yi hakuri dan jirani gani nan zuwa.

da sauri ta juya cikin falon su bata tsaya jin maganar da Diddy takeyi ba ta nufi cikin dakinta ta dauko hijab dinta daga cikin wardrobe, hijab din yasha guga se qamshin turaren Kaya wanda ta Sanya a cikin wardrobe dinta yakeyi, da sauri ta Sanya ta fito ta nufi kofar gidan su.

Isiya me shago yana ganin futowar Khubra ya washe bakin sa don Yana tsananin son Khubra duk da yasan a bune me wahala Khubra ta kulashi da sunan soyayya duba da yanda bata kula duk wani saurayin da zaizo mata da suna soyayya, takance anata Kai wake wani soyayya kana nan kana fama da talauci amma kana batun wani soyayya to wallahi gara mutum ya koma yaje yayi Sana’a shi ya nemi kudin sa, idan ka samu kudin ka ko mata hudu kakeso a rana daya zaka samu.

“Allah yataimaki hajiya Khubra qamshin Duniya, kina tafe qamshi na binki.

Dan yamutsa fuska khubra tayi tare da dan murmusa wa tana wani dan basarwa murmushin da tayi mishin ma don ya ambaci qamshi ne, don ita arayuwan ta tanason qamshi,tana kumason intasa tatawo guri asan lallai taci sunanta khubra qamshin Duniya.

A yangan ce kamar yanda ya zamo kamar dabi’ar ta ne hakan tace.

“Isiya kiret nawa zan baka?

tayi maganar tana duban isiya daya zuba mata ido se washe baki yakeyi.

“Kiret uku ma zaki bani, da yake Ina da sauran kwai din a shago.

” OK,yanzu dai zan baka kiret biyu da rabi don kwai din bazai kai kiret ukun da kakeso ba,maybe ko zuwa anjima idan kajin sunyi kwai din Sena turo maka da ragowar sauran.

Jiki na rawa Isiya ya miko ma Khubra kiret din hannun shi wanda zata zuba mishi kwai (egg)din aciki yace.

“ah haba ai wannan ba matsala bane ,ni da Kaina ma zanzo na karba basekin aiko min dashi ba qamshin duniya.

amsar roban zuba egg din Qamshi tayi da muryan ta me sanyi tace.

” ammafa Isiya yanzu kudin yakaru ba kamar yanda aka Saba bayar wa bane don komai an Kara mishi kudi,abincin kajin ne aka samu Karin kudi ko mai sun kara kudi.

” ikon Allah to allah yasa mudace akawo min haka ai ko nawa kikace haka zan saya allah dai yakaro yawan qamshi.

” ameen tafurta tare da shiga gida domin kawo masa kwai din.

“Aikin banza a haka dai za’a kare kullum a bulbula qamshi babu mashin shini.

mama Tabawa tayi maganar tare da tsayuwa daga shanyar kayan ta da takeyi a igiya.

Hakan kuma yayi dai-dai da futowar Maam Saratu daga sashen ta tana neman Yaron da zaije mata aika.

Kallon Maam Tabawa tayi tare da yamutsa fuska tace.

“kekuma dawa kike surutu haka kamar wacce sanyi ya taba ta?

mele baki Maam Tabawa tayi tare da juyowa tana kallon Maam Saratun tace.

” in banda abun ki dawa kika ga magana ta tayi kama?

inba wancan me kama da Karan raken ba.

qan qance ido Maam Saratu tayi da alama itama tana da haushin wacce ake maganar a kanta ne tace.

” hmmm kedai bari kawai Tabawa, samun waje tayi shiyasa bata ganin kowa da mutumci a gidan nan,ita game Sana’a tafi kowa kudi gidan nan ko? da sannu zanyi maganin ta, ina me tabbatar miki da cewar matukar Ina numfashi to a haka Khubra zata yita zama ita da sana’ar ta babu cigaba fitsararriya kawai.

murmushi Maam Tabawa tayi najin wannan zance daya futo daga bakin mama Saratu.

da harara dukan su biyun suka bi bayan Khubra wanda bata masan sunayi ba,don gaba daya hankalin ta yayi nisa a jera kwai din ta se nishadin ta takeyi, ita Inka ga tana nishadi to anzo sayan kayan sana’ar tane,sam bata da lokacin su mama saratu takance basuda abun yi ne shiyasa suke wahal da kansu a tunanin wani.

***********

yau take juma’atu babbar rana.

Baba me zuma baya futa ko Ina a wannan rana na juma’a inba masallacin juma’a ba, se kuma in wani muhimmin abu idan ya taso.

kowa nagidan mu yana kasan cewa a sashin su tare da yin wankan juma’a aci ado da sabbin kaya don har sabon abinci akeyi sabida wannan aranar kamar dai ranar sallah.

Kuma kowa zai nutsu a gida babu batun futa gurin Sana’a a ranar se dai kowa yayi hidomominsa a cikin gida.

ranar yazo a girkin mama Saratu don ita ta karbi girki a yammacin alhamis ta kwana a d’akin Baba me zuma.

futowa mama Saratu tayi haraban gidan don takira  yaro ya siyo mata kwai (egg) futowar ta kenan ta hangi Yaron ta yana tawowa zai shiga sashin su tace.

“yauwa Rabe zo kaje min gurin wancan Yar gadaran ka karbomin  kwai rabin kiret,kace idan Baban ku ya tashi za’a kawo kudin.

da murnar sa ya juya ya nufi sashen Hajiya Diddy don yasan yau zasu dan maida miyau.

Seda yazo dab shiga sashin hajiya Diddy sannan ya dai-dai ta tafiyar sa sannan ya shiga sashin bakin shi dauke da sallama.

da yake ni agurin Diddy na nake da zama tun rasuwar mahaifiyata.

amsa sallamar nayi ba tare dana dago daga abun da nake yi ba.

karasowa yayi kusa dani ya rusuna yace.

“Adda khubra barka da safiya da fatan kin tashi lpia.

” Lafiya Lau na tashi.

“Adda Khubra daman wai inji mama nane ki bata kwai rabin kiret in baba ya tashi daga barci zata karba miki kudin k……

hannu Khubra ta daga mishi ba tare da ta bari ya qarasa ba, ta kada yatsar ta manuniya tace.

” ba wannan maganar.

“wa kake da suna! Rabi’u kake ko Rabe?

“kul ka yarda ka karasa wannan batu mara b’ullewa don kasan bana bada kwai dina bashi.

dama mama Saratu tace maka na bata bashin khumra ne,da senayi shahadar quda nabata shima don nasan in ta shafa ubana ne zaiji qamshin,amma batun na bada kwai bashi sam hakan ma be tasoba, na gama magana zaka iya tafiya kayi hidimar gabanka nima kaga aiki nakeyi.

juyawa nayi na cigaba da zuba ruwa a robobin kaji don zan shigar musu dashi dakinsu ne daman.

tunda Maam Saratu ta hango hannun rabe Babu kwai, kuma taga yanayin fuskarsa tun daga nan tasan yau ma khubra tayi halin nata,Rabe ne ya karaso gun mama Saratu yana me cewa.

“ni wallahi mama ki daina turani gurin Adda khubra domin lamarin ta Sam babu sanayya, ya kwashe kaf yanda sukayi da khubra ya gaya ma mama Saratu.

batace komai ba ta juya cikin sashen ta rai a bace.

Kwafa mama Saratu tayi tana tafiya tana surutu tana cewa.

” Yarin ya dani kike maganar,yau tunda na sa a raina se naci kwai tabbas se naci, ai yau uban ki yana gida dole yafuto yaje shida kansa ya karbo min kwai na soya naci.

” malam!malam !!

miqa baba me zuma yayi tareda yin salati ya bude idonsa me Cike da barci ya zuba ma mama saratu, yana jin wani irin takaicin abunda tayi mishi yanzu, jinjina wannan rashin hankali na Saratu yayi, tsabar rashin hankali yana cikin barci me dadi ta katse mashi da wani irin mahaukacin tashi.

Kwafa yayi yace.

“Dan Allah Saratu yaushe zaki waye ne ke kam?

Wari irin tashin mijine haka Saratu ?

a mai makon da kikazo tashi na a barci ai kyamin tashin yan gayu,amma fisabilillahi ki dubi irin yanda kike ta dani daga barci.

Shin nace se yaushe ne zaki waye ne ke kam ?

ace Ina mijin ki kidubi yanda kike tashina abarci kamar wanda kike tashin kwarto.

Baki bude mama Saratu take kallon Baba me zuma tace.

“ahhh ! Kai kajimin malam, yo inban tasheka hakaba yaya kakeso na maka ?

kai kullum in anyi abu se kace mutum be iya tashin ka a barci ba.

” mtssss daman ai baki iyan ba,ke ko kunya bakiji kullum kizo kina cewa malam malam, to Allah yasa malum malum ne ba malam ba,mata fa yanda aka sanku an sanku da lallashin miji ne bawai zabura miji ba.

Barin baki shawara ko zai miki amfani,in zaki tashe mutum a barci kamar ni mijin ki,Kamata yayi kizo kusa dani kiringa shafani kina mannamin kiss agoshi ko akan bakina ,amma ku matan yanxu sekace matan zamanin da Sam baku iya lallashin miji ba se tsagoron rashin kunya kuka iya.

mtssss to waima tsaya! Shin me zan miki yanzun da kika zo kika min qerere akai.

yayi maganar yana me kallon Maam saratu da take sake da baki tana kallon shi.

cikin gajiya da halin mijin nata Wanda shi kullum yana jin kanshi kamar yaro.

kullum shi burin shi a zauna a kusa dashi a ringa shafashi sekace wani mage(cat).

mtssss mama Saratu taja karamar tsaki aranta tare da kumbura fuskarta tace.

nidai duk ba wannan bane a gaba na don na riga da na hardacce wadan nan zantukan naka, yanzu dai tashi zaka yi kaje kama fitsararriyan yarka magana tabani kwai,na aika a siyomin amma da yake taga bani na haifeta ba shiyasa ta raina ni ta hanani kwai din, wata qila idan Kai tagan ka ta bayar, kuma wallahi bazan lamunci rashin kunyarta ba.

Da mamaki baba me zuma ya Kalle ta yace.

“wace yar tawa ne kam kike magana ban gane ba ?

” kaji Malam da wani Magana.

“waye kuwa kaga duk fadin gidan nan zatayi min rashin mutumci batare da tayi shakkaba inba khubra ba, ita kasan ta samu goyon baya a gidan nan shiyasa takeyin yanda taso.

fuska hade Baba me zuma yace.

Ke kuma meya hadaki da Khubra da farar safiyan nan?

Baki mama Saratu ta mele tace.

“ni kuwa malam me zai hadani da ita? kasan a kullum nakan gujema shiga harkan ta saboda gudun rashin kunyan ta shiyasa inba ta kamaba bani shiga damuwar ta,yanzu ma na aiki Rabe ne na bashi kudi nace yaje gurinta ya sayomin kwai domin insamu in soya maka kafin katashi daga barci don bana son ka tashi ban gama abun karya wa ba, sannan ga hajiya Diddy be kamata ace abun Kari yana kaiwa rana ba bata karya ba, amma budar bakin yarinyar nan setace ita Sam bazata bayarba duk salon mu karya mata Jari,ita ma ta dawo ta tsugunna kamar yaran mu wanda se abun da aka basu Sannan zasu samu .

Shiru baba me zuma yayi sannan ya sauko daga Saman gadon ya nufi sashin mahaifiyar nashi.

Tunda ga bakin sashin mu Baba me zuma ya fara sallama.

Dajin sallamarsa hajiya Diddy tace yau kuma mu’azu ne nakeji haka da sassaafe?

“Assalamu alaikum.

baba me zuma ya sake sallama tareda shiga cikin falon yana me zama kan daya daga cikin kujerun falon.

“Hajiya barka da safiya.

barni kawai Kai dai mu’azu,ka fito fili kawai ka gayamin shin wanene Allah yayi masa cikawa da farar safiyan nan?

daga ganima mutuwar keso yayi aka kaishi yanzu.

” mutuwa kuma Hajiya?

Baba me zuma yayi tambayar yana kallon hajiya Diddy da mamaki .

“to Mu’azu inba mutuwa akayi ba Ina kafito da farar safiyar nan haka?

naga baka saba shigowa nan sashin da sanyi safiya bane shiyasa nace hala mutuwa akayi.

dukar dakai Baba me zuma yayi qasa yana me sake gaishe da hajiya kaka.

” antashi lpia hajiya yaya sanyi da gajiyar ayyuka ?

” Alhamdulillah ayyuka kam wannan sedai atambayi yar albarka na.

tayi maganar tana nuna khubra lokacin da ta fito daga kitchen din da yake cikin falon, hannun ta yana dauke da babban ture wanda ta sanya tea flas akai,gefe kuma plate din soyayyar dankali ne a ciki se gefen sa kuma soyayyar kwai ne.

karasowa cikin falon tayi anutse ta ajiye tiren agaban hajiya Diddy sannan ta rusuna tace.

“Alhaji Baba barka da safiya antashi lpia.

murmushi baba me zuma yayi sannan ya amsa mata gaisuwar da take mishi.

” lpia lw khubra Yaya hidiman kaji?

Caraf Hajiya Diddy tayi tace.

“ai ba kaji kadai take hidimaba harda ni tsohuwar ka take hidimtawa.

murmushi nayi wanda har Seda gefen fuskata ta lotsa nace.

” Baba alhaji barin kawo maka abun karyawa.

Kitchen din na koma na fasa kwai (egg) guda uku na soya mishi sena juyo sauran dankalin dana bari a kula na zuba black tea a flas na kawo na ajiye a kasa na tsiyaya masa tea a cup tareda mika masa,ya karba ya ajiye akan tebur din dayake gabansa Wanda na daura plate din chips da kwai akai ,yaduben cikin nutsuwa yace.

“hajiya khubra me kaji da kwai ,wato dadinku  kawai kukeji keda hajiyar ki shi yasa kuka yi jazur daku.

murmushi nayi Ina me sunkuyar da kaina,don nasan zolaya ta alhajinmu yakeyi .

” to Amma khubra meye ya hadaki da mamar taku ?

na dago kaina da alamar mamaki Ina girgizawa alamar a’a.

” to idan bake ba akwai wata bayan ke dakike gabana ne me suna Khubra ?

“Aa’uzzuki bikalimatullahi,aniyar kowa ya bishi, da ikon lillahi babu wanda ya isa yayi miki komai.

dukan mu Hajiya Diddy muke Kallo don jin abunda take cewa.

” eyy Kalleni da kyau Mu’azu!

” saratu dai ta gyara halinta,menene abun juya magana anan inbason shiga tsakanin ya da uban ta ba?

barin mayar maka da yanda akayi tinda abunda ta turoka kaji kenan idan yaso in na gama baka labarin daga baya seka hada dani da khubran karufe mu da duka.

“inace cewa tayi abata bashin kwai inta samu kudi zata biya daga baya,dake ita qamshi Yar albarka ne tace wa rabi’u.

“rabe kaga wannan kwai din duk dama su shi nariga da karbi kudin su akan zan tara musu,a hakan ma ban gama tarawaba saboda kajin basu dayawa guda 20 ne,kaga bazai yiyu na sayarba bayan nakarbi kudin mutane alqawari baice haka ba,ko zakaje mata shagon isiya ko zaka samo mata?

Kallon Baba me zuma Hajiya Diddy tayi bayan ta gama bama baba me zuma labarin tace.

“duk Ina zaune agefe sukayi haka *(oh kaji tsohuwa da tsari)*

shikuma rabe da kake gani,da yake yaron zamani ne shi,da yaje gurin maman nashi seya gayama uwarsa karya da gaskiya,don su aikinsu kenan zaman gulma .

Shiru baba me zuma yayi tare da gyada Kai kawai yana mamakin hali irin na saratu don abunda ta gaya mishi daban da abunda yanzu yazo ya tarar.

cigaba da karyawan su sukayi tare da hira Jefi Jefi har ya kammala karyawa ,sannan ya mike yashiga toilet din dayake cikin falon ,ya wanke hannunsa ya futo yana mai duban mahaifiyar tashi da mama ki akan fuskar shi yace.

“Hajiya me nake gani acikin bayan gidan ki haka kamar abun tafasa ruwa na zamani ?(water heater).

” yi maza Mu’azu ka cire Wai din da kasa a maganar ka.

don kuwa ba kama bane abun tafasa ruwanne da gaske.

“aini babu abunda zance ma wannan jika tawa sedai nace Allah yakara tsaremin ita ga mugun baki da duk wani abun ki, Allah yama rayuwar ta albarka, qamshi nikam ta zamomin qamshin alkhairi,dubi falona dubi jikina yanda na dawo kullum bakina acin mai dadi mai maiko yake.

ni dama zan gaya maka kayima matan ka bayani daga yau na sauke musu kwanona a gidan ka sedai in sunyi abun dadi sesu kawomin,don qamshi tanamin komai nidai Babu abunda zance sedai alhamdulillah duk yayan ka babu Wanda yayi koyin halin ka da kwazonka kamarta.

“amiin hajiya.

cewar alhaji Baba me zuma yana dan nazarin maganar da Diddy tayi yanzu.

Hajiya Diddy kallon baba me zuma tayi Wanda yake sake gyara zaman sa akan kujera tana sauraron jin abunda zaice.

” Hajiya tunda naga kajin sun karbeta zan bata wasu kudin seta Kara kaji yanda kasuwar zai dan dada bunkasa tunda dakin da kajin nata suke ciki naga yanada girma,kuma naga tana kula da kasuwancin ta babu shiririta aciki.

Baki Hajiya Diddy ta washe tace.

” in kayi hakan ma ka kyauta Allah yama albarka ya Kara arzuki da daukaka,amma wani hanzari ba guduba nidai bazance komaiba bazan ma yar albarka na shishshigi a harkan kasuwan cinta ba gara tazo kaji daga bakinta ,don bata cika son karban kudin mutane tana hadawa dana kasuwancin ta ba *(kaji wani batu agun tsohuwar nan sekace kudin ruwa)*

“kina Ina jikar hajiya!?

Hajiya Diddy ta bude murya tana Kiran Khubra.

” yi maza ki fito mahaifinki nason magana dake.

futowa nayi na durkusa daga gefe nace.

” gani Baba.

gyaran murya baba me zuma yayi yace.

” khubra tunda naga kiwon kajin ya karbe ki to inaso zan karamiki wasu Yan kudi ki Kara siyo kajin don abun yadan fadada inaga zaki fijin dadin ana kiran ki da hajiya khubra qamshi me kaji da kwai.

dariya nayi na rufe fuskata nace.

” Baba alhaji nagode sosai Allah yakara budi yajikan mahaifa.

” amiin khubra Allah yamuku albarka.

Yanzu karfi da yaji nima kin makalamin sunan Alhaji,gashi suna ya bini har kasuwa da gurin aikina haka ake kira na dashi.

baba me zuma ya fada yana murmushi .

Murmushi Hajiya Diddy tayi tace.

” Nima ba gani ba, ni ko kano ban taba zuwa ba amma qamshi na ta samin suna Hajiya Diddy, gashi kuma suna ya bini har mutuwa allah dai yasa yanda kika samin sunan Hajiyar nan allah yasa ki biyamin kudin kujeran maka naje nasauke farali.

murmushi nayi nace.

” amiin hajiya ta.

namike nakoma daki don na karasa shirya wa.

Hajiya Diddy ne ta dubi Baba me zuma tace.

” to tunda allah yasa yar hajiya ta amsa zata karbi kudin to fa dole se ankaro mata ma’aikata don aiki zai mata yawa ,ni dama zaka yarda daka tura Rabe yaje neman aiki anan gidan gonar Yar hajiya ko za’a dace,

kaga shikenan ma ya huta da wannan yawon tazubar din da yakeyi agari .

murmusa wa alhaji yayi yana mai jinjina yanda hajiya da jikanta suka daukaki wannan sana’ar nasu,kwata kwata kaji guda 20 nefa amma har ake kiransa da gidan gona.

Baba me zuma Jan numfashinsa yayi yace.

“yanda kikace Hajiya hakan za’ayi,babu damuwa zan turo mata shi ko za’a dace yasamu gurbin aiki agunta.

sun dan jima suna tattaunawa kafin yayi mata sallama ya fita.

Mama saratu me jiran a kawo mata kwai ta soya ta cika tayi fam.

Lokacin da Baba me zuma ya shigo sashin ta ta dubeshi tayi mishi kallon shekeke kamar bazata tanka mishi ba se kuma wani qullutin baqin ciki ya taso mata adan hasale tace.

” yanzu malam

fisabilillahi tuntuni Ina zaune Ina jiranka ka kawomin kwai na soya amma se yanzu ka dawo daga sashin su, kuma daka dawo din ma seka dawo babu kwai.

shin ko kaima tafi karfinka ne?.

Kuma zaman me Kake yi a sashin nasu har tsawan wannan lokacin?

07052100719 only chat.

[20/02, 6:00 pm] +234 806 366 8063: *✨MUTUNTA KAI✨* 2

✍️Rashida Bature.

MUTUM NAGAR TACCE KO A INA YAKE TABBAS ZAKA SAMESHI YA FUTA DABAN WATO INA NUFIN *HAJIYA RAMLAT(MAI DAMBU)* BAZAN GAJI DA MIKI GODIYA BA DOMIN GIRMAN KI DABAN NE.

Wani irin kallo Baba me zuma yabi mama saratu dashi irin kallon baki da hankalin nan,sannan ya kad’a kanshi yayi wucewar sa cikin dakin shi ba tare daya tsaya sauraran shirmen taba.

sororo mama saratu ta tsaya tana bin bayan Baba me zuma da kallon mamaki.

tafa hannun ta tayi tace.

“oh ni saratu! Tabbas malam yau zama bai ganka ba, don futowa zakayi ka sayomin kwai a duk inda ake siyarwa don tunda nasa rai na akan zanci kwai tofa yau senaci tukun na hankali na zai kwanta.

Rabe dake tsaye a gaban rijiya zai dibi ruwa a ciki ne ya ajiye gugar hannun shi ya matso kusa da mama Saratu yace.

“Mama tunda adda khubra bata bayar da kwan ba,to ke me zai hana kikawo kudin ki kawai nasiyo Miki a gun Isiya me shago.

Wani irin muguwar Kallo mama Saratu tayi ma Rabe tana jin kamar ta Kai mishi bugu a bakin daya ambaci ta bada kudin.

a fadace mama Saratu ta watsa mishi harara tace.

” Nabi kudin da gudu na takeshi babu takalmi.

lallai Rabe yau ka dad’a tabbatar min da cewar sunana saratu sarkin asara.

Yo inba hakaba Kai har kace na bada kudi na sayama kartin banza kwai suci su lashe baki,to wllh kowama ya hakura inbe karbo kwan agun yar gadaran ba to nima bazan cire sisi na na siyaba don ko Ina da kudin to Ina da abun yin da zanyi da kudin .

A fusace ta juya zuwa d’akin ta tana cigaba da surutai.

Shigowar kamal kenan daga sashin mama Tabawa ya tarar da mahaifiyar shi tana wannan jidalin ya kalli kanin shi Rabe yace.

“Rabe wai yau waya tabo mana mamar mu ne da sanyin safiyar nan haka ?

Seda Rabe yaja numfashi sannan yace.

” wallahi ya Kamal yau mama ce ta dage wai setaci kwai,kuma bata da ko kwandala,kasan halin Adda khubra bata bada bashin kwai din ta, shine fa mama taji haushin hana tan da Adda khubra tayi taketa fada.

” Allah ya kyauta to.

Cewar Kamal yana me qarasa shigowa cikin sashin nasu,shikuma Rabe ya cigaba da dubar ruwan shi.

*****************

Numfasawa Alhaji Mansur yayi tare da kallon babban danshi yace.

“tun dazu fa nake maka magana *HATIM*, amma Kayi shiru ka barni se zuba nakeyi ni kad’ai na.

Wata irin qaya tacciyar murmushi kyakkyawan matashin da aka kira da suna Hatim yayi har Seda kyawawan hakoran shi wanda suke Jere reras a bakin shi suka bayyana,wannan irin murmushin bama kowa yake yima irin taba se wa mutum biyu ko zuwa uku, idan tayi tsananin kamawa ne hakan kafun kaga yayi murmushin da hakoran shi zasu bayyana gaba daya, su din ma iya ma alhalin shi ne wato Ammee da Aby se kuma Jiddy wato kakar shi mahaifiyar baban shi wacce suke zaune gida daya da ita se dai kowa da sashin sa.

Numfasawa Hatim yayi ya dago narkakken idon shi wanda akoda yaushe zaka ganshi kamar me jin barci ya kalli Alhaji Mansur koshe akuyam, Seda ya dan dauki lokaci kafun ya bude bakin shi da kyar kamar Wanda aka mishi dole yace.

“Aby yanzu ni me Kake so nace anan?..

Baki na bude na gyara tsayuwa kawai Ina Kallon ikon god,sabida tsananin dadin muryan Hatim, muryan nashi tana dauke da izza da kuma qasaita ga wani irin kwarjinin da take qara mishi idan yana maganar.

gyara zama Aby yayi yana fuskan Hatim yace.

“wani irin magana ne haka Hatim zaka ce ba kasan me zaka ceba.?

” Please mana Aby! tun fa last zaman da mukayi da Kai na baka shawarar ku canza manajojin ma’aikatan ku kaida Jiddy amma kukayi buruss da magana ta tun abun bai Kai haka jagulewa ba.

Sosai Aby yake kallon Hatim wanda yake sauke numfashi da kyar da kyar, dan yayi Yar wannan maganar kamar Wanda yayi gudu.

“yanzu Hatim kana ganin sauya manager kowani kamfani na shine samun maslaha na lalacewar da kamfanin nan tayi? Kuma hakan kana ga kamfanonin zasu samu cigaban da aka rasa?

Kai Hatim ya gyada ma Aby tare da lumshe idon shi ya furta.

” In sha Allahu hakan muke fata da kuma sa rai.

Girgiza kai Aby yayi sannan yace.

” har yanzu dai Hatim kana nan akan bakan ka naqin amsar kamfanonin nan a hannun ka kaja ragamar su ko?

ka tattare a naka kamfanin abun ka?

Murmushi Hatim yayi yace.

“Aby bazan iya hada aiyuka dayawa a kaina ba, wannan ma da kyar nakeyi, Jina nakeyi kamar aiyukan sun min yawa.

Murmushi Aby yayi tare da daga kafada ya mike yace.

” ni zan tafi, zanyi kokari zuwa gobe naga mun zauna da ma’aikatan kamfanin duka semu ga abunda zai yiyu.

Ya mika ma Hatim dake zaune akan kujeranshi hannu su kayi musabuha kafun Hatim din ya taso suka futo yana ma Aby rakiya har bakin motar shi,Seda Aby ya shiga motar da aka kawo shi direba ya shiga yaja motar suka bar haraban ma’aikatan abincin kaji dasu kifi da duk dai wata dabba, wannan kamfanin ba kamfanin kowa bane illah na Hatim,bama wannan ne ka dai kamfanin Shiba yana da Kamfanoni da dama a qasar waje.a hankali Hatim ya sauke numfashi tare da juyawa ya nufi sama yanda office d’inshi yake.

Bai Cika zama a Nigeria ba, amma duk lokacin da yake Nigeria to yakan zauna a office d’inshi na nan Nigeria yayi aiki sosai.

Hadaddiyar agogon diamond din dake daure a hannun shi ya kalla ya sauke numfashi sannan ya tattare wayoyin shi ya danna wani abu dake ajiye asaman tabur din dake gaban shi kamar bell haka abun yake, zuwa can Sega wani matashi ya tawo yana zuwa bakin kofar office din yaci burki tare da Sanya hannu a jikin kofar office din yayi nokin,bai shigo ba har Seda Hatim ya bashi izinin shigowa sannan ya shigo, bai tsaya tambayar komai ba ya fara tattare Kayayyakin da yake kan tubur wanda Hatim din yazo dasu yayi amfani dasu irin laptop da wasu takardu, Seda ya tattare duk abunda ya kamata sannan ya dan risina yace.

“ranka shi dade angama hada komai.

Ido Hatim ya lumshe tare da sake jingina jikin shi da kujeran da yake Kai.

Seda ya dauki tsawon minti goma a haka sannan ya mike suka futo daga office din wannan matashin shine ya rufe office din sannan ya biyo bayan Hatim din da sauri suka Jera har zuwa wajen elevator suka shiga ya saukar dasu zuwa kasa yanda motacin sa suke.

***********

Tunda naji fucewar Baba Alhaji daga sashin mu na dawo falon na zauna kusa da hajiya Diddy wacce take ta santin dankali da kwai d’in dana soya mata.

Kallon ta nayi na kada Kai na nace.

“hajiya ta irin wannan Santin dankali haka ?

Ko daga Kai Hajiya Diddy ba tayi ba bare ta kulani har sanda tagama santin ta tas sannan ta dubeni tace.

” daman so nakeyi nagama nakira ki don haka zauna da kyau inason muyi magana.

gyara zama na nayi a qasa kamar yanda tace.

“me kike ganin zakiyi da kudin da mahaifin ki yace zai baki?

Baki na bude Ina Kallon Diddy har Seda ta Kai karshen maganar ta nace.

” kai hajiya! wllh harkin razana ni, nafa zaci wani magana me girma ne zaki gayamin ni har kinsa gabana yana ta faduwa.

Ware hannu Diddy tayi ta nuna min tace.

” kinci gidan ku, yanzu wannan ba magana me girma bane kike nufi a wajen ki?

Kai amma dai kekam khubura Allah ya gyara min ke.

Baki na turo gaba nace.

” to inbanda abunki Hajiyata Ina kikaga an taba lissafin kudi mutum besan yawan kudin da za’a bashin ba?

ai kamata yayi mu jira muga idan yakawo kud’in se muga nawa ne idan yaso sena zauna na tsara abunda nakeso nayi dasu,daga baya idan nayi lissafi sena gaya miki abunda na tsara don jin shawarar ki a game da tsarin nawa, kedai yanzu kawai mu zuba mashi ido muga nawa zai bayar.

kanne ido kakus tayi tare da cewa.

“wai yaya naji kina cewan mujira mu zuba mishi ido mugani?

Ai ni na zaci yanzu zai tafi sashin sa ya dauko kudin ya bayar?

Diddy tayi maganar tana me qarasa mikewa tsaye daga kan kujeran da take zaune akai.

Binta da Kallo nayi nace.

” Ni dai a fahimta na gaskiya inaga ba yau yake nufiba amma bari dai mu jira mu gani.

“muga wa”?

Diddy tayi maganar tana gyara daurin zanin ta daya kunce tana wani zaro ido waje.

“cab din ai nikam zama bata ganni ba,ai bakin daya furta zai bada kudi tofa bakin shi zaisa ya bamu kudin nan a yau, don bazan tsaya sanya har matan sa suji labarin nan ba, kinfa San mutum da kudi,mu muna nan zaune muna jiran zai kawo kudi shikuma suna can suna juya masa lissafi yazo ya hana kudin nan,don gaba daya na fahimci hidimar gidan nan kamar akwai has aciki,don nasan hakan ba k’aramar aikin su bane, nikam kinga fucewa ta a gidan nan gara na taro kudin nan da zafin ta.

hanyar futa a falon ta nufa,se kuma naga ta tsaya cak tare da juyowa tace.

“khubra yi maza ki shiga d’akina a durowan dake kusa da gado na zaki ga wani durowa ki Jawo, aciki zakiga laida viva bag maza ki dauko min.

Da sauri na shiga dakin na duba yanda tace na dauko na kawo mata.

Seda Diddy ta Kade ledar ta leka sannan tayi ajiyar zuciya tace.

“Alhamdulillah Kinga wannan laidar aciki zan zubo kudin idan ya bani, kinga laidar baqace maganin masu rufa ido kenan Allah dai ya dauramu akan duk wani me nufin mu da sharri, duk wanda kuma yake son ganin gazawar mu to Rabbi kasa seya biyo ta qasar takalmin mu kafun ya wuce,ni dai na tafi seki bini da addu’ar dacewa.

tsabar mamakin Diddy ne ya hanani cewa komai harta bar sashin namu.

“Assalamu alaikum!

yaaa Mu’azu gani nan tafe.

Hajiya Diddy kenan wacce ta wage muryan ta tana rafka sallama a kofar sashin Baba me zuma.

Mama tabawa dake kishin gide a d’akin ta tajiyo muryan hajiya Diddy.

wuffff Maam Tabawa tayi ta futo daga dakin nata murmushi dauke asaman fuskar ta.

“Hajiya Diddy kene tafe”? maraba maraba

“Ina kwana Hajiya Diddy”

wani kallo Hajiya Diddy tabi mama Tabawa da dashi, sannan ta kauda kanta gefe tana kare ma gidan Kallo tana yatsina fuska kamar me jin warin wani abun kafun ta maida kallon ta zuwa kan Tabawa da take rusune daga gefe tace.

“Amma dai Tabawa ku Kam kun yi haddar gulma wallahi,tsabar haddan da kukayi kwararo kwararo an San da zaman ku,in banda jin tsegumi daga jin na kira sunan dana Mu’azu ke se kiyi wuff ki fito kamar wacce ki kaji nace ina Tabawa take?

waini tsayama tukum na tambaye ki, shin ko kin canza sunan ki ne kika Koma Mu’azatu ban sani ba?

kanta mama Tabawa ta girgiza alamar a’a.

” ai na zaci kin sauya sunane ban saniba?”

sadda Kai qasa Maam Tabawa ta kuma yi ta rasa abun cewa.

Ina tambayar ki nayi,.

nace kokin saki tabawa ne kika riqi Mu’azatu wato takwarar sunan Mu’azu kenan?

Kai mama Tabawa ta sake girgiza wa don babu bakin magana.

“inba gulmaba daga jin nace Mu’azu seke kiyi futt ki fito Salam Salam dake kamar wacce akayi ma kiranye.

dama sunan ki Mu’azatu ne sekice yayi kusan kamar sunan na ki, to senaga Ina had’in tabawa da Mu’azu fisabilillahi in ba son gulma ba,yanzu nasan cewa zakiyi gaisheni kika futo kiyi.

Tayi maganar tana kwaikwayon muryan Tabawa tana binta da harara tace.

” to billahillazi karrr nake kallon mutum ehe, ai da In da gaske kina son ki gayar dani dinne ai kin San hanyar sashina,da tun asuba kinje can kin gaisheni, to bazan amsa gaisuwar ki anan ba tunda nan ba gida na bane kuma nina tako takanas nazo har inda kike,maza tashi ki juya kiyi sashin ki hala bakya rasa abun yi ba don ni banson iyayi, kuma ki bude kunne kiji da Kyau gurin Mu’azu d’ana nazo bagun Tabawa ba.

dukan ku kuma kusani duk abunda kukayi ma uwar wata tofa kushirya karb’an saka mako au badade au bajima,don kun haifi mace kun haifi namiji wataran duk abunda kuka yimin tasss se anrama min abunda kakumin akan ku,kuma tunda babu abunda na muku na cusgunawa se aikin alkhairi dana muku na haifa muku d’ana danayi a cikina harya auro ku kuke rufa ma juna asiri kuda shi.

sim sim Mama Tabawa ta tashi tayi cikin sashin ta.

Maam saratu dake labe daga bakin kofar da zai hada sune ta kunshe bakin ta se Zabga dariya ta keyi tana Allah shi Kara.

Seda tayi me isar ta kafun tayi futttt tafito ta d’aya kofar da zai hadasu a tsakar gidan su,fuskarta a sake kamar ba taji komai ba ta dubi Maam Tabawa tace.

“Tabawa Ina zakije ne haka?”

Maam Tabawa bata kula Maam Saratu ba domin ta shaqa dayawa taji haushin kwafsa mata da Diddy tayi don taso jin dame hajiya Diddyn tazo don tasan bata xuwa sashin su haka kurin seda dalili.

wucewarta tayi tabar Maam saratu tana mata dariyar mugun ta a ranta.

**************

futar hajiya Diddy na mike na cigaba da gyaran sashin mu,nagama goge ko Ina se kyalli yakeyi na sauke labulaye tare da rufe kofar falon nashiga cikin gidan na dibo gaushin wuta nazo na kunna turaren wuta d’an borno me dad’in qamshi nan take dakin ya dau qamshi me sanyi ,sannan na nufi bayi (toilet) don nayi wanka .

***************

Qamshi ! Ke qamshi!!

Nifa tsiyana dake kenan ata kiranki kina nan kina wannan wahalallan lissafin naki,to yi maza ki fito ga babban lissafi ya samu.

Cak na ajiye biro da takardan da yake hannu na nafito daga cikin dakina Wanda yake acikin falon sashin Diddy,Ina ware ido na don naga wani lissafin ne hajiya Diddy take fadin yafi wanda nakeyi.

bakar laidan dake hannun ta ta mikomin,kallon miye wannan na mata Ina me bin laidar da kallo.

“ke banson iya shege mana, miye hakan Ina baki abu kamar Ina baki Kashi bazaki sa hannu ki karba ba.

” to kidai tsaya kiyi ma kanki don kudin da alhajin ku yace zai baki ne naje nayi yaqe-yaqe na karbo miki kinsan ni banison jir……….

ai ban tsaya naji ka rashin maganar Diddy ba na wafce laidar har sanda hajiya Diddy ta furgita ta kurma salati.

” innalillahi! khubra kinada lafiya kuwa zaki karamin hannu na?

yanzu khubra sakayyar da zaki min kenan?

Takanas na tashi naje na titsiye dan marayan allah nan na karbo miki kudin wai don karki rasa shine zaki zubar dani agefe?

to kidai gyara halinki nikam bazan iya miki ba inkin isheni tsaf zaki barmin sashi na ki koma can gun matan ubanki suyi yanda sukeso dake.

dariya nayi Ina me rungume Diddy nace.

“Afwan sweet Diddy na wllh babu me rabani dake se Allah,kuma in banda abunki Diddy ai kinsan murna ne tamin yawa har na rasa yanda zanyi.

Da sauri na sake Diddy na shige cikin daki na, hannu na yana dauke da jakar kudin da Diddy ta bani.

ban wani dauki lokaci ba nafito nasake fadawa jikinta Ina murna don Sam murmushi yakasa barin fuskata.

Kallo na Diddy tayi da mamaki tace.

“ina kuma kika Kai kudin.

” shiiiiiii kiyi shiru ki Diddy ki daina ambatar kudin nan da qarfi, kinsan ance kudi al’aura to don haka kiyi qasa qasa da muryar ki.

Diddy ke in banda abun ki taya zamu bude kud’i irin wannan da rana tsaka?

salon kiga manyan garada akan mu,to nikam ba dani za’ayi haka ba, dole mu jira se dare ya raba shine lokacin da naji a kace ana lissafin kudi irin wannan,shin Diddy bakiji mutane suna cewa masu kudi basu barcin dare ba? .

don haka kema ki jira se zuwa jibi ko cikin dare zamu bude mu k’irga.

au bama daren yau za’a bude kudin ba?

Diddy tayi tambayar tana bud’e baki.

“A’a ba haka nake aikina ba Diddy,dole ne kibi tsari na zuwa gobe na tara yara na musu sadaka, sannan nayi istihara mu roki alkhairi game da abunda zamu fara da kudin ..

Allah ya jikan iyayen mu.

07052100719 chat me if you want.

[20/02, 6:01 pm] +234 806 366 8063: *✨MUTUNTA KAI✨* 3

✍️Rashida Bature.

tun k’arfe uku na dare na farka nayi istihara kamar yanda na sama raina zanyi,najima Ina sallah har asuba tayi, tashi nayi na gabatar nafula wato salatul Fajr,sannan na zauna a gurin nayi lazumi har aka kira assalamu.

mikewa nayi na gabatar da sallah asuba.

na jima Ina kai kuka na ma Allah buyi gagara misali,bayan na idar nayi azkar din safiya don bani wasa da azkar domin shine takobin mumini,Seda na shafa addu’ar sannan na mike na ninke abun sallan na miyar dashi yanda nake adanawa sannan na durkusa a agaban gado na nadaga bakin katifar da take kan gado,hannu nasa a karkashin katifar na dauko wannan bakin laida da Hajiya Diddy ta karbomin agun alhajin mu.

mayar da katifar nayi kamar yanda yake sena zauna a bakin gadon na kunce daurin da nayi ma bakin laidar sekuwa ga tulin kudi sun bayyana.

idona na zaro waje don kuwa tunda nazo duniya bantab’a ganin kud’i masu yawa tsiraran su hakaba,wani irin yawu na hadiye baki bude.

gyara zama na nayi da kyau sannan na mik’e da sauri naje na kulle kofar d’akina sannan na dawo na zauna na zazzage kud’in akan gado,da wani irin Kallo na kebin kudin.

Seda na gama bin kud’in da Kallo sannan na fara rabasu Kashi Kashi,na cire yan dubu dubu da ban, se yan d’ari biyar biyar ma daban,sannan na fara aikin k’irgasu dalla dalla don banison asamu matsala.

bani nagama kirga kud’in nan ba har saida naga rana ta b’ullo ta jikin labulen window na sannan na sarara musu, a hakan ma da naso nasake tisa k’irgawa kar wani ya mak’ale ajikin d’an uwansa .

cikin hanzari na futo na nufi cikin kitchen dake cikin falon mu,na kunna gas wanda na dan tara riban da nake samu nasiyo mana don amfanin mu duk da d’an karami ne, daura ruwan bak’in tea nayi na mishi hadin komai sanna na futa daga kitchen din na nufi d’akin da kaji na suke don na kwashe Kwan da sukayi karsu fasa su shanye,Se da na basu abinci da ruwa sannan na futo daga d’akin kajin.

bayan na gama bama kaji ruwa da abinci na dibo kwai din da sukayi naje na a dana shi acikin gurin da na ware domin adana d’anyar kwai, gurin na mayar dashi kamar store don Yana da kofa harda makullum da nasa akayi min shi.

kwai (egg) na kulla a cikin laida baka,na nufi cikin gidan mu wato sashin da matan alhaji mu suke.

Sashin Mami Zulay amaryan alhaji mu na fara shiga, a haraban sashin nata na hango ta a duke da amalar wani abun takeyi a tsakar gidan na duk’a na gaishe ta da girmamawa don muna shiri sosai da ita, don ita tafi sauran matan baba na kirki ga hakuri, tana da Yar ta guda daya ta mace.

“Mami na ashe kin   tashi “?

Murmushi Maam Zulai tayi tace.

“na tashi khubra, yau dai ban bari maganin nan ya rinjaye niba.

murmushin nima na mayar mata tare da sake gaishe ta.

“Antashi lafiya Mamin mu yaya karfin jikin?”

“lapiya law khubra jiki yayi sauki sosai ,yaya hajiya ta tashi dafatan komai lpia.

nayi murmushi nace komai lafiya Mami,amma Mami ina Zahra take ta barki kike tsaye anan ke kadai?

Nayi tambayar Ina Kallon aikin da Mami takeyi na Shirya musu abun karyawa da takeyi.

Dafa kaina tayi tace.

“karki damu diyar arzik’i zahra suna ciki nima abu nafuto zan dauka kika ganni anan.

Kaina na daga mata sannan na mike nace.

“Mami na allah yakara miki lpia.

” amiin Khubra nagode da gaisuwa.

Ajiye mata laidar dake hannu na nayi a kasa kusa da ita nace.

” Mami na ga kwai ba yawa a soyama Zahra, Mami na acigaba da mana addu’a ma wannan sana’ar nawa.

murmushi Mami Zulai tayi tana me cewa.

“in banda abunki khubra yaya za’ayi ki debo kayan jauran ki haka,ai semu karya jarin,dakin bari har sekin dad’a bunqasa tukunna seki bamu alakoron.

tayi maganar da sigar zolaya tana dariya.

dariyan nima nayi nace.

kai Mami na yanzu kwai guda goma ne dayawa ?

ai addu’ar ku na cigaba da kuke mana akoda yaushe bazai taba bari kasuwar mu tayi qasa ba, don haka Mami na Kimin addu’a da bakin ki me albarka.

Murmushi Mami ta sake yi tace.

“to shikenan khubra mun gode Allah yasa nan gaba abud’e mana k’aton gidan gona Allah kuma ya kauda idon makiya arzik’i yata bunkasa.

” amiin Mami na, maybe hajjin bad’in bad’ad’a dake za’aje irin wannan addu’a haka.

nafada Ina dariya.

“kajimin yarinya.

wato bama na bad’in nan ba har sekin karamin da bad’ad’a ko.?

Dariya nayi Ina tafiya nace.

” to inna banda abunki har yau she na bunkasar da zan miki alkawarin zan biya Miki kujeran makka shekara me zuwa? kinsan ni bani karya don asoni.

kai Mami ta daga tace.

” hakane kuma.

“to muna matukar godiya da wannan kyautar .

Futa nayi a sashin Maam Zulay na nufi sashin Maam Saratu, daga bakin komar falon ta na tsaya nayi sallama yaran ta ne suka amsa min,shiga cikin falon nayi na samu guri daga kan kujerun da suke falon na zauna kamar yanda naga yaran ta guda biyu sunyi,yaa Kamal dana gani a falon na fara gayarwa Rabe kuma ya gaisheni tunda shidin na girme shi duk da ba wani girma na can bane.

duk rashin jituwar da mukeyi da matan Alhajin mu bashi ya hana mu yaran gidan girmama junan mu ba.

Maam Saratu tafito daga cikin dakin ta tana cewa.

” a’a Yaya nakejin kamar muryan yar gadara a dakin nan?

tana me k’arasa futowa cikin falon.

basarwa nayi kamar banji taba,zama tayi a daya daga rub’abb’un kujerun ta da suke falon, duk da bawani Yara ne da Maam Saratu ba amma kayan dakin ta yafi na kowa lalace wa agidan.

sanda ta yi kusan minti uku da zama sannan na dubeta nace.

“Maam barka da safi da fatan antashi lafiya.

” lafiya law alhamdulillah na tashi.

” ai na d’auka maganar ma bazaki iya bane kin wani hakimce akujera sekace fulanin gidan sarki.

murmushi nayi wanda ya zamemin jiki in bason magana shi nakeyi ma mutum don hakan ma ya wadatar basai nace komai ba,hakan kuma yakan qular da wanda nayi domin shi, don sukance raini ne hakan.

ba tare dana ce mata komai ba na mike na isa kusa da kafarta na ajiye baqar laidar dake hannu na nace.

“Maam ga kwai a soya masu rabe amma sadaka ne.

mikewa nayi na nufi kofa domin futa a sashin……

” keee dawo ki d’auki Kwan ki, kamar ke har nice zaki kalla don bakida kunya kicemin sadaka kika bamu kwai, da yake ance miki mu mabara tane ko.?

bance mata komai ba na juyo da nufin na d’auki laidar kwai din caraff Rabe ya d’auke laidar Kwan kamar walqiya yana cewa.

“dan Allah Adda khubra kiyi hakuri ki barmana wallahi mu muna son kwai din,zamu soya mun gode Allah ya qara budi tunda mama tace bata so kinga shikenan semu had’a da nata mu soya sema yafi auki, mun gode my Adda.

Dafa kafadar shi nayi Ina sake murmushin da Maam ta tsana nace.

“cewa zakayi allah shikarb’a don sadaka na bayar d’an kanina.

murmushin na kuma yi na juya nace.

Byee yaa Kamal.

Nayi tafiya ta cikin isa da izza kamar yanda suke cewa shiyasa suke kirana da qamshin gadara.

Ina jiyo muryan Rabe yana murna suna tafawa da Yaa Kamal.

b’angaren Maam Tabawa na shiga da sallama na iske surayya abakin murhu tana wura wuta.

“Adda khubra Ina kwana?

harara na galla mata.

bakinta tayi sauri rikewa tace.

” au sorry Adda khubra antashi lpia.

murmushi me dauke da harara nayi mata nace.

“lafiya law,yarin ya duk ranar da kika sake cemin ina kwana Sena zubar miki da rub’abb’un hakoranki kaf a qasa.

Ina me wucewa na nufi cikin falon Maam Tabawa, Seda nayi sallama tareda d’aga labulen falon na shiga ciki.

k’afata na sanya acikin falon amma Jina nayi kamar wacce na sanya fata a cikin yashi.

haka na daure na shiga na sameta a baje itada sauran yaranta  guda biyu, guri na samu a Saman kujeran falon na zauna,duk yaran suka hada bakin su gurin cewa.

“Adda khubra antashi lafiya .

murmushi nayi musu nace.

” lafiya law Alhamdulillah,dafatan kuntashi lafiya kum?

na amsa musu tare da kallon fuskar Maam Tabawa wacce ta mele baki tareda kauda kanta gefe don tafi sauran matan baba na din rashin wayewa.

” Maam Tabawa barka da safiya antashi lafiya .

“law.

tace min atakaice don duk cikin matan alhajimu tafi nuna min rashin kauna don dai kawai Diddy tafi nuna soyayyar ta a kaina.

hakan dana gani ne nima yasanu na mike na ajiye mata qullin laidar dake hannu na a gaban ta nace.

” Maam ga kwai asoya ma kanne na sadaka.

naki guda biyune aciki sauran duk nasu ne.

banjira cewar taba nayi fucewata yaran ne ma naji suna cewa.

” Adda allah ya amfana .

komawa sashin mu nayi na sauke ruwan black tea din dana daura akan gass,juye wa nayi a tea flas guda biyu,sannan na fasa kwai da dan yawa na yanka albasa, na Sa danyar tumatur nad’an bubbuga tafarnuwa kad’an bame yawaba na sanya maggi Sena dauko dafaffen zogalen dana tsinka a tsakar gidan mu na wanke na dafa na ajiye agefe shine yanzu na dauko na zuba ahadin kwan na barbad’a Curry kad’an sannan na daura pan din akan gass na kunna na soya mana na jera namu akan tebur din dayake falon, sena sauran ragowar flas din akan tire na nufi sashinsan Alhajin mu.

A bakin kofar falon na tsaya nayi sallama.

daga ciki naji ya amsa min tare da bani izinin shiga.

Seda na ajiye turen hannuna akan tebur na sannan na durkusa nace.

“Baba Alhaji Barka da safiya da fatan ka tashi lpia.

Kallo na baba me zuma yi tare da ajiye jaridan hannun shi yace.

” lafiya law na tashi khubra Yaya kika tashi keda hajiyar taki?

murmushi nayi Ina tsiya ya mishi black tea a cup nace.

“duk lafiya law muka tashi Baba.

Na bashi amsa Ina mika mishi cup din tea.

Karban cup din yayi yana cewa.

” mashà Allah yau kuma wani abun dad’in nasamu haka ne Yar hajiya?

Karamar dariya nayi nace.

“kai alhaji kwai nefa da ruwan shayi ba wani abu ba.

na bashi amsa Ina me dad’a gyara zama na a qasa kusa dashi.

” Kai amma nagode sosai qamshin Hajiyar ta kamar kinsan Ina neman black tea dinan don inason na futa yanzu sabida muna da wani taron gaggawa daya taso min,Allah yayi miki albarka Allah ya baki masu miki kema,Allah ya jikan mahaifiyar ki.

” Amin nace idona yana me dan tara qwalla na tunawa da mahaifiya ta da nayi.

shiru falon yayi ganin hakan da Alhajin mu yayi ne yayi gyaran murya don kauda shiru ya dubeni yace.

akwai abun da kike sone Khubra ?

Naga yanayin ki kamar da akwai abunda kike so ki gaya min.

girgiza kaina nayi Ina wasa da yatsun hannu na nace.

“a’a Baba, daman godiya nazo zanyi na aikan da Hajiya Diddy tabani jiya,daka bata ta bani shine nazo godiya.

Bude baki Baba me zuma yayi yace.

” oho! kice dai toshiyar baki kika kawomin da kwai.

yayi maganar da raha don ya mantar dani damuwar dana shiga na tunawa da mahaifiya ta danayi.

yana maganar yana dariya, nima dariyan nayi nace.

” a’a Baba Alhaji nidai godiya nazoyi zalla.

Ina me dariyan nima.” Baba Alhaji nagode sosai allah yakara rufa asiri yasa kafi haka Allah kuma yajikan mahaifa yabamu ikon jin qanku.

“amiin khubra shiyasa nake me alfahari dake a Koda yaushe saboda kwazonki dakuma sanin ya kamatan ki da hangen nesa,duk da kasan cewar ki mace nasan halinki na kuma San zaki iya, amma zan dan dada rokonki daki nutsu ki bada himma ga kasuwancin ki tunda angama karatun sakandiren sekuma muta addu’a har Allah yafuto da mijin aure kafun nan zanso ki cigaba har lokacin da zaki samu mijin.

Kaina na duqar a qasa nace.

“nagode sosai Baba alhaji.

amma baba alhaji ashe daman kana da kudi dayawa dayawa haka ?

Kama baki Baba me zuma yayi yace.

” oh khubra kincika bin kwaf,inada kudi daidai gwargwado,nuna wane bansonyi don nasan halin matana, kema don na auna hankalinki ne, naga a kaji guda a shirin har kinsan kin gyarama hajiya Diddy sashinta kin sanya mata tayals a dakin ta,kin saya muku gass na girki kin gyara daki daya daga cikin d’akunan dayake cikin falon kin mayar dashi kitchen, ga abun tafasa ruwan zafi kin sanya mata a bayin ta kin don Kar tayi alwala da ruwan sanyi a lokacin sanyin na, duk kin dauke nauyin da ya dace ace nine yakamata nayi mata don neman albarka, amma se gazawa ta fado kaina ke kuma da kike diyata kika dauki wannan babban ladar,Sam baki barinta da yunwa kafin matana su tashi su girka su Kai mata ke harkin gama kin bata taci ta koshi,ga kuma kulawa da ita da kikeyi wanda ko ita ta haifeki iyakan biyayyar da zaki mata kenan,kinga kuwa kin cancanci na baki sama da miliyan dubu ma idan Ina dashi,ba Wai kuma don nafi sonki bane a cikin yara na bane, sedai kinsan ance rai yana son mai kyautata mata, kuma nima a shirye nake na bada gudun mawana ga duk wanda ya maida hankalin shi ga neman na kanshi don banison mutuwar zuciyar da yaran nan sukeyi,duk wanda ya maida hankali ya nemi abun yi to yazo nikuma nayi alqawari zan bashi Jari,amma bazan taba bada kwandala na don a salwantar da ita ta hanyar da bai kamata ba,ki duba kiga yayun ki babu abunda sukasa a gaban su sedai su shiga su fita se gantalin bin abokai da suka sanya agaba, yanzu har kananun ma sun dauki halin manyan.

Yayi maganar muryan shi tana rawa, alamun abun ya dade yana damun shi acikin ranshi.

Seda ya dauki tsawan mintuna Sannan yace.

” wannan kud’in da kika ga na bayar a baki, kud’in filina ne dayake garin dungal shine na sayar wancan satin akan zan dad’a a kasuwancin siyar da shanun da nakeyi,se kuma ganin da nayi kin mai da hankali ga kiwon kajin da kikeyi ne kuma Allah yasa ma abun albarka shine nace barin baki mugani ko za’a dace,don naga nauyin da kika daura a kanki yayi miki yawa gashi har naji Hajiya Diddy tace ta saukemin abincin gidana Wai naki ma ya wadatar, naga kajin naki kuma sun kasa ma wannan d’awainiyar.

Dakatawa yayi da maganar shi kamar me nazari sannan yace.

“da fatan bazaki bani kunyaba Khubra, zakiyi abunda ya dace dama wanda nake hasasowa anan gaba.

Kaina na daga idona yana me cikowa da kwalla muryata a sanyaye nace.

“in sha Allah Baba zan maida hankali naga nayi abunda kud’in bazai lalace ba,sedai Baba Alhaji Ina neman Karin addu’ar ka domin ganin haske ma lamari.

Murmushi Baba Alhaji yayi sannan yace.

” addu’a kullum acikin yimuku mukeyi Khubra, sedai zamu dad’a akan Wanda mukeyi in sha Allah, allah yamuku albarka gaba d’ayanku.

“Amin nace nayi masa sallama nadawo sashin Hajiya Diddy.

😘 07052100719 only chat.

Add Comment

Click here to post a comment