Littafan Hausa Novels

Kishiya a yau Hausa Novels Complete

Kishiya a yau Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

KISHIYA A YAU

 

 

 

*PART *

1

 

(TURE LIFE STORY)

 

 

Na

LUBABATU MAI CHANJI

 

 

hajiya Haneefah ce zaune adakinta dake saman bene tana karatun alkur’ani bayan ta idar da sallar walha kamar jiya yauma hayaniya takeji yau harda kuka daga makwaftanta ne take jiyowa kasancewar tagar bedroom dinta dake saman bene tana sauraren hayaniyar duk dake tashi agidan makwaftan nata saidai Bata fahimtar meke faruwa,Dan haka saitacigaba da

Kaddarata Ce Haka Hausa Novel Complete

karatunta,zuwa can Kuma sai ta runka jiyo sautin Yana kara karfi dole taruke alkur’ani bayan tayi sheda tamike da sauri tanufi kofa,hartagama saukowa daga matattakalar Bata lura da mutum a palour ba, saidai taji magana ummy lafiya? da sauri tawaiga saifudeen ne,zaune saman darning Yana break,tace masa inazuwa, malam iro ta kwalawa maigadinta kira, alokacin Yana bakin get Yana sauraren redio,dasauri ya iso yafara gaisheta tace mlm iro lafiya yau makwaftan mu? Yace eh to wallahi hajiya nima dai bangane Mike faruwa ba Amma dai komeye dai bamai dadibane domin kuwa tundaga jiya bayan magaruba nafara jin hayaniyar,yau Kuma akawayi gari da ita,ko adubo ne haj,,,,,,,,,,,,,,

 

maganars tamakale sakamakon bugun kofar da akayi da sauri ya waiwaya, sai yaga yarinya dagudu ta nufosu tana fadin ku taimaka mani,da sauri hajiyar tatarbota ganin tana layi kamar wadda Tasha kayan maye hijabinta jirkice fuska tayimata suntum kafar ta ba ko takalma,tana zuwa kusa da ita sai tayi kasa asome,cikin karaji hajiya ke ambaton sunan Allah,San nan tshiga Kiran Deeny,da sauri yanufo wajanta yqnafadin ummy lafiya meke faruwa?tace koma ciki kadauko kayan aikinka kafara Bata taimakon gaggawa dagudu shima yajuya ganin abinda ke faruwa,Koda yazo hajiya tadan gyara mata hijabinta San nan yashiga auna numfashin ta yace ummy Danshafa mata ruwa afuskarta ahankali ko taja ajiyar zuciya tafara motsa idanunta harta budesu ahankali duk da snyi mitsi mitsi alamar tadade tana kukan,hjy tace alhamdulillah tashi kinji mushiga cikin gida,tadan girgixa Kai ahankali murya Bata kofita sosai tace yace kada na kuskura nazauna ako ina naje nashiga duniya hajiya kibarni natafi kawai su Abba sundaina sona,,,,,

 

takara fashewa dawani sabon kukan hjy tace to shiya koreki nikuma nace kitaho gidana, gidana kuwa aiba gidan sabane, tashi muje kinji, ahankali takamata ta mikar da ita mlm iro da Deeny sai duban tausayi suke mata, Dan sunsan ba karamin abubane yafaru,da itaba Dan kuwa yaran gidansu suna da tarbiya sosai,ganin sunnufi cikin gida malam iro yakoma bakin aikinsa yanafadin Allah yakyauta, Deeny ma abinda yafada kenan Yana jinjina abin aransa,Koda suka shiga ciki dakin hjy dake sama cantawuce da ita takaita harbaki toilet tashiga da ita harciki domin kuwa taji jikinta haryanzu baidaina rawaba tashiga tahadamata ruwan gumi masu Dan zafi tace kishiga kigargasa jikin ki kinji tadan gyada kanta, tafuto tajamata kofar palour tanufo tashiga buda kayan break din dake zube darning tahada mata tea maikauri da kwai da dankali sai soyayyar agada,taloda atire ta nufi sama dashi,data shiga saita samu wani Dan table tadora tiren sama tabude wadurop dinta tazakulo wata doguwar riga marar nauhi mai yankakken hannu hade da dankwalinta ta aje ta bakin gado,San nan tadan zauna nadan mintoci,

 

hardai tamike tasake komawa tadan kwankwasa toilet din tace mekike ne?San nan taji alamun motsin ruwan San nan tadawo ta dauki wan nan rigar dakoma tadan kwankwasa tace anshi ga riganan kicanza ta jikinki ki Kuma dauro alwallah kafin kufito,tabude kyauren toilet din Tamika hannu ta anshi rigar harda godiya, tafuto bayan tagama, hajiya ta nuna mata waje tace zauna anan domin kuwa alamu sunnuna bayan damuwa harda yunwa kedawainiya dake,sallah kuwa natsuwa takeso Dan haka yi sauri kicinye plet din nan tas,tadago Kai tadubi hjyr tace eh hakanake nufi, ahankali ta dauki cup din tea din tafara kurba guminsa yafara ratsamata uwar hanji tadan dakata,San nan tacigaba da kurba hajiya tasake tura mata plet din dankalin tace hada da wan nan cikin yafiyi maki nauhi, ahankali tasa supoon tana Dan tsakura ahankali,hajiya tayi shiru tana kallan ta tana aiyyana abubuwa da yawa acikin zuciyarta,ganin tana ture plet yasa ta kalleta tace harkinyi mene? ahankali tace hjy nakoshi nagode Allah yasaka da alkhairi,daga nan hajiyar Bata tursasataba Dan tasan damuwa Bata barinma kaji yunwar hakanma tayi kokari,tace to RAHAMA tashi kigabatar da sallah ko raka’a biyu ce daniyar Allah yayi maki maganin damuwar da yajarabceki da ita domin kuwa ita kanta damuwar ibadace jarabawa ce Allah keyiwa bayinsa domin yagwada karfin imanin mummini,

 

ahankali ta Mike domin zuwa inda taga dardumar sallah alamun nanne wajan bautar hajiyar,daga nan hajiya tahada kayan tayo kasa dasu zuwa palour ba kowa sai tv daketa aiki ita kadai tasan tunda bataga Deeny ba yaje yayi sallar walha, Dan haka saita hada sauran kayan break din dama bawani dayawa takeyiba dai dai su take masu saiko maigadinta datake Mika mawa Koda yarage dai baida ywa batada son almubazaranci, palour tas yake sai kawai tadan kunna masa bouner kasancewar ta mace mai son kamshi,tajuya zuwa sama,Koda tashiga tatarar da ita hannu sama tana kaiwa Allah kukanta, hjy ta jinjina Kai,abin zuciyarta yafuto fili Bata saniba fadi take yah Allah kadauki Raina inhut,,,,,,,,,,,,

 

wata tsawa hajiyar tayi mata saida tarazanata Dan bataji shigo wartaba,tace inadalili idan yadauki rannaki mikika tanazar wacan din daharkike tunanin damuwar duniya tafi ta kiyama sauki ,ina iliminki yake na islama,ya ubangijin mu yace Mana (INNA MAAL USURIN YUSURAH)bayan tsanani akwai sauki aduniya ne kike fita da kunci alokacin da Allah yaye maki aduniyar nan Babu abinda ke tabbata walau dadi walau wuya,ashe kuwa idan Allah yajarabci bawansa yadace yadaina saurin yanke kauna domin kuwa sauki na nan tafe,alahira canne matabbata take,Dan haka maza kitubarwa Allah,kicigaba da neman daukinsa yanajinki Yana ganinki ki rufe dakaranta suratul yasin tana yaye damuwa, bayan kin idar Kuma inason ganin ki kisameni palour,tajuya zuwa kasa tana ta Al ajabin wan nan Lamari to mi yayi zafih?Kai Allah yakayauta ta fadi tana sauka zuwa palour saida ta canza tashar TV din San nan ta zauna tana jancarbin hannunta………

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Daga taskar Yar gidan Mai chanji

Add Comment

Click here to post a comment