Littafan Hausa Novels

Inno a filin Zabe Hausa Novel Complete

Inno a filin Zabe Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

INNO A FILIN ZAƁE

 

 

©AMEERA ADAM

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*

 

Ƙirƙirarran Labari.

 

1&2

 

A zabure ya miƙe sakamakon jin ƙarar faɗuwar murfin tukunyar da ke barazabar tarwatsa kwanyarsa, a hankali ya zura kansa yana leƙen windo a tunaninsa ‘yan bangar siyasar da ke kai kawo a layinsu ne suka fara farmakar gidajen mutane. Domin ba zai manta ranar da abokinsa yana kwance bai yi aune ba ya ji sara a gefen cinyarsa. A duƙe ya hange ta gaban ƙaton murhu ta babula wuta tana ci sai kiciniyar ɗora tukunya take, sai dai da alama murhun ya yi wa tukunyar yawa wannan ya ƙara mata jinkirin ɗorawa, saboda yadda wuta ke lasar hannuwanta da ta kai tukunyar za ta ɗora. Guntun tsaki ya yi ya koma ya kwanta, yana daga kwance ya ji Inno na mita.

A Makabarta Ne Hausa Novel Complete

“Wannan wacce irin jarrabar rayuwa ce a ce tukunya ta gagari murhu, kai Allah wadaran naka ya lalace raƙumin dawa ya ga na gida. Wallahi duk Sammani ne ya ja mini da bai sako mini gas ba, saboda yana baƙincikin kar na fita zaɓe. Kai Allah ka raba mu da baƙin hali irin na Sammani, a ce kai ba ka samu bangon lasar zuma ba kai ka na baƙincikin wani ya samu. To ka je don kanka Sammani ba zan ga komai ba sai alheri.” Da ƙyar Inno ta samu ta jogana tukuyar da duwatsu ta ɗora ruwa ta koma gefe tana jiran tafasarsa.

 

Cikin ɗaki ta shiga ta ɗauko sabuwar atamfarta da gallelen hijabinta ta ajiye a gefe, ƙarar zubar ruwan ta ji da sauri ta ƙarasa bakin murhun ta ga tukunyar ta karkace ta jiƙa murhun gabaɗaya. Cike da takaici ta juye ruwan ta faɗa banɗaki, bayan ta fito ta yi alwala ta shiga ɗaki tana shiryawa.

 

Agogon wayarta ta duba a lokacin huɗu saura don haka kai tsaye ɗakin sammani ta leƙa ta fara tashinsa, “Sammani ka tashi asuba ta ƙarato ka rungumi alfirjir a kan sallayya!” A ƙagauce Sammani ya furta, “Don Allah Inno ki bar ni ko biyar fa ba ta yi ba, wannan zaɓen ko Baba Inuwa ne ya fito takara sai haka.” Sammani ya ƙarasa maganar yana juyawa haɗe da jan bargo, a hassale Inno ta furta. “Ba dole masifa ta addabe mu ba, a ce yara ba su san su rungumi alfijir a farkon bayyanarsa ba sai an yi assalatu, wannan wacce irin jarrabar rayuwa ce haka? Mu tashi mu roƙi Allah shugaban da zai sassauta mana a fara zuwa Hajji kyauta sai ku kwanta ku saki saleɓa, kai ni dai Allah ya jarrabce ni da Sammani wa ya sani ko har da irinsu a ‘yan hana ruwa gudu.” Da ƙarfi ta ja ƙofar ta wuce ɗakinta ta fara gabatar da nafilfilu.

 

BAYAN SALLAR ASUBA.

 

“Sammani ni dai na yi sallah yanzu haka zuwa zan yi na kama layi.” Sammani da shigowarsa daga masallaci ya ce, “To Inno Allah bada sa’a.” Inno ta karkace tana kallon katin zaɓenta ta ce, “Sammani tuna mini wacce jam’iya ce ta farar aniyar wannan yaron mai nagarta?” Sammani ya ce, “Inno wai don Allah ba ki ji maganar Baba Inuwa ba?” Inno ta haɗe fuska tana faɗin, “Sammani wace ce ni?” Murya a ciki Sammani ya ce, “Wace ce kuwa ban da kakata.”

 

“To daga Allah sai ni sai ƙanin Ubanka muka rage maka, ba zan saka dangin uwarka ba don babu tsiyar da suke tsinana maka, don haka wallahi ko tsine maka na yi sai ta hau kanka tun da ni na haifi ubanka. Wallahi ka ji na yi rantsuwa idan ba ka fita zaɓen nan ba ban yafe maka ba.” Sammani ya sake ɓata fuska ya ce, “Wallahi da rantsuwarki da ta Bala mai nama duk ɗaya ne, zaɓe ne na ce miki ba zan yi ba. Kuma kar ki ƙara aibanta mini dangin Mahaifiyata, wai ma kin ci abinci kuwa duk wannan baloƙoƙon da kike yi?”

 

Inno ta riƙe haɓa tana faɗin, “Yanzu sammani har lokacin cin abinci gare ni? Na zauna cin abinci layi ya wuce ni a gaba zaɓe? Na rantse da Allah zaɓen shugaban ƙasan nan ba zai wuce ni ba da ikon Allah, yanzu kai za ka kaini shekara huɗu masu zuwa, na san ina da sauran rayuwa a gaba Sammani? A’a ba zan ga wannan jarrabar rayuwar ba ni da filin zaɓe sai na ga abin da ya ture wa buzu naɗi.” Ɗaga kafaɗa ya yi cike da rashin damuwa ya ce, “Allah raka taki gona. Ga fili ga mai doki nan. Ki tabbatar da dai kin sha maganin gudawarki tun da na ji kwana kika yi kina zaryar banɗaki.”

 

 

Ummou Aslam Bint Adam

INNO A FILIN ZAƁE*

 

 

©AMEERA ADAM

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*

 

Ƙirƙirarran Labari.

 

3&4

 

Inno ta washe baki cike da jin daɗi ta ce, “Tuni ta tsaya Ɗan’sammani tun farkon dare gudawar ta tsaya, yanzu dai zan tafi na san sai ka tashi daga baccin nan na ka na jaraba za ka fito ko?” Sammani ya gyaɗa mata kai don ba ya son sokibututsun Inno, tana gama magana ta yi gaba har ta kusa fita ta dawo ta ce.”Saura idan ƙanin Ubanka ya bugo maka waya ka ce masa na fita zaɓe, ni ma wayata zan kashe don kar ma ya dame ni da kira. Haka kawai mutum da ‘yancinsa a hana shi zaɓe yo ina dalili? Zaɓe tun lokacin su Namadi Azukuwe nake yi…” Zaro idanun da Sammani ya yi ya katse Inno, ya wuce cikin gida yana jinjina kai don zancen Inno bai gama ratsa shi ba, Inno na ganin haka ta maƙale jakarta a hammata ta fice.

 

FILIN ZAƁE

 

Lokacin da Inno ta karasa filin zaɓe cike yake da mutane wasu sun yi layi wasu kuma na tsaye carko-carko, cutsawa ta fara yi cikin mutane daga bayanta ta ji ana kiranta tana waigawa ta hangi Aminiyarta Goggo. Takaici ne ya cika ta don sai da ta ci tafiya mai nisa ta biya wa Goggo su taho tare aka ce ba ta nan, cike da jin haushi Inno ta ƙarasa ta ce.

 

“Me za ki ce mini Goggoje? Wallahi kin ci amanar aminci da yarda kuma an yi ɗaya ɗayau ba ƙari. Idan kin san tafiya za ki yi ba sai ki gaya mini kada na biyo miki ba? Kai ni ban san jarrabar rayuwar da ta samu amintarmu ba, kuma ni da gidanki a gidan duniya dai an gama idan kin ganni a ɗakinki to a Aljanna ne.” Goggoje da ke tsakiyar wasu mata ta ce, “Haba Inno wallahi ban ga amfanin wayarki ba, tun farar asuba nake kiranki a kashe, shi ya sa na ce ko bacci ya sha kanki baki tashi ba. Ina za mu yi biyu-babu taho ga layi na kama miki can.” Goggo ta yi maganar tana nuna wa Inno wani layi da ke gefenta, da sauri Inno ta ci gaba da kutsawa tana zuwa za ta shiga wata inyamura ta taso mata tana faɗin. “A’a Mama wannan ba kyau yanzu kin zo.” Goggo na jin haka ta hayayyako tana cewa, “A’a Maman Shediren kar mu yi haka da ke wannan ce me wurin da na gaya miki tun ɗazu.”

 

Ba don ta so ba Inyamurar ta matsa Inno ta shiga ciki, suna nan tsaye mutane suka ci gaba da taruwa ana ci gaba da kaɗa ƙuri’a cikin kwanciyar hankali.

 

Suna na nan tsaye wasu manyan mata suka shiga cikin filin da manyan motoci, waɗansu matasa ne suka fara sauko da manyan buhunbuna da alama kayan rabo ne a ciki waɗanda ake siyan ƙuri’un talakawa. Ta kan layinsu Inno aka fara, tun da suka fara rabon biredin mai ɗauke da hotunan jam’iyyar hamayya Inno ke wurga musu mugun kallo. Wata kakkaurar mace ce mara tsayi ta ƙaraso wurin su Inno ta miƙa mata biredin haɗe da sabbin kuɗin naira dubu biyu, sunkuyowa matar ta yi saitin kunnen Inno ta ce.

 

“Baba wa kika yi niyyar zaɓa? Ga tallafi daga ɗan takararmu ki zaɓi *Son kowa* na tabbata…” Ba ta ƙarasa magana ba Inno ta katse ta da cewar, “Tsohonki zan zaɓa, ja’ira fitsararriya.” Ta saka hannu ta shaƙo wuyan ‘yar kakkaurar matar tana ci gaba da cewa, “Kuma wallahi ba za ki bar gabana ba sai kin cinye biredin cikin buhun nan, na yi niyyar zaɓar *Mai farar aniya* amma ki nemi ki saye ni da biredi, biredin me?” Duk yadda matar nan ta so ƙwatar kanta ta kasa, Goggo na daga cikin layinta tana ganin ta fara niyyar yin galaba a kan Inno ta fito da sauri ta fisgi takalminta ɗan madina tana tafka wa matar a faffaɗan bayanta.

 

Cike da azaba matar ta ware ƙatuwar murya tana neman taimako, daga can gefe wani matashi ne ya ƙaraso yana faɗin. “Butar uban nan Human Leader me yake faruwa? Kayyasa ba wani shege wallahi.” Ya ƙarasa maganar yana zaro ƙaramar wuƙarsa.

 

 

Ummou Aslam Bint Adam

Add Comment

Click here to post a comment