A Makabarta Ne Hausa Novel Complete
A MAƘABARTA NE
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Yadda na fara lafiya Ubangiji kasa na gama lafiya. Gaisuwa a gareka dukkan masoya
0️⃣1️⃣
Misalin ƙarfe 3:am na dare gudu take yi a kan titi sai waigen banyata take, wayar dake hannunta ta yi ringing, a hanzarce ta danna za ta yi magana ta ji an yi sama da ita shuu. Ihu take kurmawa ta na faɗin.
Inno a filin Zabe Hausa Novel Complete
“Waiyo Umma ku taimakeni za a saceni.”
Wani irin ɓakin duhu ne ya mamaye idanunta abin da ya ƙara kaɗa hantar cikinta, idanunta tamkar za su fito waje saboda firgici da tsananin tsoron da take ji.
Idanunta ta runtse bakinta na rawa zuwa wannan lokacin ta kasa furta koda kalma ɗaya, ji ta yi an dire ta a kan wani abu mai ɗan tudu ta yi saurin buɗe idanunta, ƙara ta ƙwalla ta na ƙanƙame jikinta sakamakon ganin wani zabgegen abu wanda ta kasa ganin tsayinsa, baƙi ne sosai ba ta iya ganin wani kalar abu ne, shi dai gashi nan kamar mutum kamar doguwar bishiyar giginya..
“Hahaha!
Ta ji wata dariya mai sa zuciya firgici ta ziyarci dodon kunnenta.
Sake ɗago kai ta yi ta juya gefenta ai da sauri ta zaro idanu ta na ja da baya sai ji ta yi ta bugi wani abu, jiki na rawa ta juyo cike da zullimin mai idanunta za su gane mata ta yi arba da ƴar ƙaramar yarinya wacce ba za ya wuce shekaru 7 ba. Bakin yarinyar jini ne ke fita haka zalika kanta yana ɗauke da ƙahuna guda uku, hannayenta har jan ƙasa suke masu dauke da baƙaƙen faracuna masu tsayi da kaifi, kannuwanta tamkar na tunkiya jajaye sai juyawa suke kamar yadda dabbobi ke yi da nasu, ƙafarta sak irin ta biri.
Baki na rawa ta ce.
“Baiwar Allah ku su waye wai?”
Wata mahaukaciyar dariya yarinyar ta yi cikin muryarta irin na ƙananun yara ta soma magana.
“Karki sake tambayata mu su waye, idan ba haka ba “Ta ƙarashe maganar ta na zaro mata manya-manyan idanunta baƙaƙe tamkar gawayi ne a kwayar idanun.”
Muƙut! Ta haɗiye yawu ba shiri, dafata ta ji an yi ta baya ta zabura ta juyo, arba ta yi da wannan dogon ɓakin abin. Saboda tsananin tsoro futsari ta saki cikinta ya murda ta saki zawo ganin wannan shirgegiyar halitta. Runtse idanu ta yi ta ƙasa furta komai in banda futsari babu abin da take saki.
“Hahaha! Hahaha! Hahaha!”
Sautin dariyarsu suka shiga gigita ta, zuwa can ta ji tsit hakan yasa ta buɗe idanunta.
“Waiyo na shiga uku!
Ta faɗa ta na kallon ƙasan inda take. Tsalle ta yi ta koma gefe ta na kallon wajan a firgice ta soma magana.
“Waiyo ni! A MAƘABARTA NE nake kuma a kan kabari?”
“Kwarai kuwa a MAƘABARTA NE kike.”
Ta ji an ba ta amsa daga gefenta.
Juyowa ta yi cike da tsoro ta sake arba da yarinyar nan, baki na rawa ta kuma cewa.
“Wai me kuke nufi da ni ne? Me na muku kuke bibiyar rayuwata? Z..
Tsawa aka daka mata ta kasa ƙarasa maganar.
“Mu ba’a tambayar mu.”
Shuru ta yi sai kallon ƙaburburan dake kusa da ita take.
Tim! Ta ji ƙaran faɗuwar wani abu, da sauri ta kalli inda abun ya faɗo, baki ta buɗe ta na son yi magana ta ji an manne mata bakin kawai ta zazzaro idanu ta na kallon mutumin da yake ɗan nesa da ita.
Kamar kiftawa da bismillah ta ga an fille kan wannan mutumin, zubewa ta yi a ƙasa ta na son yin magana ba hali ta rarrafa ta nufi gangar jikin mutumin idanunta waje. Jini kawai ke ta malala a jikinsa ta ɗaura hannu a ka ta kurma ihu ta ce.
“Uncleeeee!”
Firgigit ta farka daga baccin da take jikinta ya yi sharkaf kamar an zuba mata ruwa, numfashi take fitarwa ta na jinjina kai sai kuma ta fashe da kuka wiwi ta soma surutai.
“Allah ka tseratar da ni daga wannan mugayen mafarkan da nake, wannan abun biyu su waye su da kodayaushe suke kaini maƙabarta?”
Zabura ta yi jin ana shafa bayanta ta juyo, ihu ta sa ta na sauka daga kan gadon ganin jarirai guda biyu kwance a kan gadon, kallon fuskarsu ma abin firgita ne. Kafin ta yi ƙwaƙƙwaran motsi sai ganin ɗaya daga cikin jariran ta yi ta tashi tsaye ta na tafiya ta doso ta, ai a zabure ta nufi ƙofar fita ta na kiran sunan duk wanda ya zo bakinta, sai dai ta na zuwa bakin ƙofar ta kasa buɗewa ga wannan jaririyar na doso ta ta na zaro mata ido. Fuskar jaririyar ƙofa-kofa ce wani ɓakin ruwa mai yauki yana fitowa haɗi da wasu irin tsutsoyi suna fitowa suna shiga cikin idanunta.
“Waiyo Allah Inna lillahi wa inna ilaihin raju’un! Umma! Ku taimakeni aljana za ta kamani Umma, Abba! Abba! Ku ceceni kar ta ƙaraso gurina.”
Haka take faɗa ta na buga ƙofar da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar, juyowa ta yi taga jaririyar ta kusa isowa inda take ta taƙarkare ta kurma ihun da ya fito da dukkan ‘yan gidan suka yo ɗakinta.
“Suhaima! Suhaima! Buɗe ƙofar mana.
Ta jiyo muryar mahaifiyarta na kiran sunanta, sai yanzu ta tuna ƙofar a kulle take, cikin rawar jiki ta murda makullin ƙofar ta buɗe. Ƙoƙarin tareta suke ganin ta na neman gudu, mahaifinta ya kamo hannunta ya ce.
“Suhaima wai anya lafiya kike.”
Kasa magana ta yi sai cikin ɗakin da take nuna musu ta na ƙara ƙanƙame mamanta, mamaki ne ya kamasu suka kalli ɗakin ba su ga wani abu ba.. A tsorace ta ce. “Abba aljannu ne a ɗakin nan ni dai ba zan sake kwana a ɗakin nan ba, yanzu fa ja..
Ba ta ƙarasa maganar ba sakamakon arba da ta yi da wannan jaririyar ta na girgiza mata kai fushi ya baiyana a kan fuskarta. Sororo duk suka tsaya suna kallon Suhaima da zazzaro idanu ta na musu nuni da ɗakin, ƙanenta ya shiga ɗakin ya duba bai ga komai ba ya fito. Tsaki ya ja ya ce. “Dalla can Wallahi Anty kin soma samun ciwon hauka tsakanin jiya da yau” Ya faɗa yana wucewa.”.
Fama aka dunga yi da Suhaima ta shiga ɗakin amma ta ce ita fa ba za ta kwanta a ɗakin nan ba, Umma ta jata ta kaita ɗakin yayarta ta kwanta. Ganin ita ɗaya ce za ta kwanta ta ce. “Umma don Allah ki zo mu kwanta Wallahi sake ganinsu zan yi ki taimakeni.”
Ta faɗa ta na zare idanu tare da ƙanƙame hannun Umma. Ganin da gaske tsoro take ji Umma ta ja ta suka kwanta ta maƙale a jikin Umma ta na runtse idanunta. Sosai mamaki ya kama Umma jin yadda zuciyarta ke bugawa, addu’a ta dinga tofa mata ta na shafa kanta har bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita..
Washe gari bayan an fito daga Sallah Abba ya dawo gida, a palo ya yada zango ganin Suhaima a palon sai ƙifƙifta idanu take kamar barawon da dubunsa ta cika.
Ganin Abba yasa ta dan sunkuyar da kai ta ce. “Go..good morning Abba.” Tsuru ya mata da ido yana amsa gaisuwar da ta masa, wayarsa ce ta soma ruri ya fito da ita daga aljihu, ganin mai kiran sai abin ya bashi mamaki har sai da fuskarsa ta nuna. Yana ɗaga kiran da sallama cike da mamaki ya ce. “Sani ina shi Abdullah yake naji wayarsa a hannunka da safiyar nan?”
Kuka ya ji Sani yasa ya soma koro masa jawabi.
“Uncle Daddy ya mutu.”
What! Ban gane me kake nufi ba da gaske ya mutu?”
Amsa ya basa da.
“E muma sai da muka tashi muka gansa an masa yankan rago.”
“Inna lillahi wa inna ilaihin raju’un! Sai ya yi baya rajaf ya zube a kan kujera ya saki wayar ta faɗi ƙasa.
Umma da ta fito daga kitchen jin maganar Abba ta ce. “Lafiya dai? Me ya faru naji kana sallallami?”
Suhaima kuwa kwalalo idanu waje ta yi ta na jiran taji mai Abba zai faɗa, dafe kai Abba ya yi da ƙyar ya iya cewa.
“Abdullah ya wasu.”
Zabura Suhaima ta yi za ta fankaya da gudu Umma ta yi saurin kamo hannunta , a ruɗe ta kalli Abba ta ce. “Abba Wallahi sune suka kashe Uncle na gansu a gaban idona suka cire masa kai, Abba Wallahi n..
Ba ta ƙarasa ba ta zube a ƙasan carpet a sume…..
# comments
#share
#noting
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[…] A Makabarta Ne Hausa Novel Complete […]