Hirar Soyayya Masu Dadi
“Ba Zan Yi Miki Kishiya Ba”, Wannan Ita Ce Kalmar Da Samari Da Yawa Suke Gayawa ‘Yan Matansu Kafin A Yi Aure
Daga S-bin Abdallah Sokoto
Akwai wani kuskure da samarin mu su ke tafkawa a wajen hira da ‘yan matan da zasu aura kafin ayi aure. Kashi 80% na samarin mu da alkawarin cewa yarinya su ke baza su kara aure ba, daga gareta an rufe kofa. Su kuma mata dama duk duniya babu wata kalma su ke son ji daga bakunann mazajensu kamar su ji sunce baza su karo aure ba. Wannan na daga cikin dalilinda yasa ake samun wasu matsaloli a zamantakewar aure a wannan zamani. Domin kai ne kayi rantsuwa da Allah cewa baza ka karo aure ba, amman akazo cikin shekara daya da auren ku sai ka fara tunanin karo, kaga kenan doli a samu hayaniya a gidan ka, domin kasancewar macce mutun ce mai rauni.
Yaron Gidana Hausa Novel Complete
Wanda yake akwai bukatar ko bakada niyyar kara aure ka gayawa yarinyarda kake son aure cewa lallai kai idan Allah ya baka dama mata 4 zuwa 3 ko 2 kake son aurren a rayuwarka, ko da kuwa ba ka da niyyar yin haka a rayuwar ka. Domin fadar wannan shi zai sa ta sanya a ranta cewa lallai komai daren dadewa ba ita kadai kake da burin zama da ita ba, don haka duk sanda ka tashi aure insha Allah bazai zo da wata fitina ba, domin tun tuni ta san cewa wannan rana za ta zo, domin ka fada mata zuwan wannan rana tun kafin kuyi aure.
Sannan bayan haka, za ta fi kyautata maka da kuma baka kulawa, domin ganin ta dauke hankalin ka daga maganar karo aure, saboda dama ba wani abu bane ke sa mafi yawancin maza karo aure ba illa rashin samun cikakkiyar kulawa daga matansu ba. Akwai maza dayawa da su ke da burin auren macce daya a rayuwarsu, matukar su ka samu dacen maccen ta farko mai kulawa da su da kuma ya’yansu, amman rashin samun ta ke sa doli ya nemi karo aure.
Saboda haka samari ku daina barin dadin hirar soyayya na daukarku kuna daukar alkawarin da ku ka san baza ku iya cikawa ba bayan aure.
Ubangiji Allah ya ka bamu mata nagari, mata kuma Allah ya baku maza nagari.
[…] Hirar Soyayya Masu Dadi […]