Mahaseem Hausa Novel Complete
[05/11/2022, 6:50 pm] +234 902 983 1068: *_MAHASEEM_*
{ “`Heart“` “`Touching“` “`Story“` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
“`HASKE“` “`WRITER’S“` “`ASSOCIATION“` …💡
*Alhamdulillah I’m back my Fan’s,Ina ma Allah godiya daya bani ikon fara rubuta muku Wannan labarin mai suna MAHASEEM, Sannan ina Mik’a sak’on gaisuwa ta gare ku massoya na,aduk inda kuke.*
*Bamu Dace Da Juna Ba*
*Akan* *Kanwata*
*Zuri’a* *D’aya*
*Ke* *Haske* *Ce*
*Mahaifiya* *Ta*
“`Wa’inan littafan nawa duk zaku same su a Arewabook, kuyi searching sunan akwai su complete, pls kuyi Following na
“`
*Page 01*
_Wata_ Kyakyawar yarinya ce wacce ba zata wuce Shekaru goma sha bakwai ba na gani ta shigo cikin gidan a guje kamar wacce aka biyo, wata mata dake zaune kan turmi ita ma naga ta tashi ta shige daki a guje, Yarinyar naga ta d’au buta ta shige bayi, Can naga matar nan ta leko ta window ganin ba komi sai ta fito dakin daidai nan yarinyar ta fito bayi tana dariya matar cikin bacin rai tace”Wannan yarinyar akwai fitinaniya inace biyo ki akayi ashe tsabar rashin nutsuwa ne kika shigo a guje”
Dariya ta k’yal k’yale dashi sai ga wata mata ta fito daga dayan dakin tana cewa” _Mahaseem_ meke faruwa ne”
Wacce aka kira da Mahaseem ta fashe da dariya harda rik’e ciki tana nuna dayan matar dake hararar ta”Inna Jummai wai daga shigowa ta kawai naga Inna ladi ta shige daki a guje, aradu ta ban dariya”
Wacce aka kira Inna ladi tace”shegiyar yarinya mai kama da Aljanu kinyi ma kanki”tana fad’in hakan ta shige d’aki.
Inna Jummai ta kalle Mahaseem”A ko yaushe ina fad’a miki ki dinga nutsuwa ke yanzu ba yarinya bace”
Turo baki Mahaseem tayi”Ni wai mene nayi,kawai Inna ladi matsoraciya ce”
“Yanzu dai shiga daki ki canza kayan makarantar”
Mahaseem dariya tayi tare da shigewa cikin daki, ta canza kaya ta fito da sauri inna Jummai tace”ina kuma za kije ko abinci ba zaki ci ba, baki ganin yamma tayi ne”
“Aradu gidan su laure zanje, ina binta bashi yau sai ta biya ni ko inyi mata na jaki” ta fad’i tana tafa hannaye.
Ko kafin Inna jummai tayi magana har Mahaseem ta fita a waje taci karo da Wata yarinya kawai naga ta d’aka mata duka ta ruga a guje, yarinya kara tasa ta shige cikin gidan a guje, Inna ladi ce ta fito hankali tace”Bibalo waye ya dake ki ne”
Bibalo na kuka tace”Mahaseem ce kawai banyi mata komi ba ta d’aka min duka”
Cikin massifa Inna ladi ta shiga surfa massifa”Wannan yarinya ta fitini kowa, shegiya irin mayu zat dawo ta same nine ai”taja yarinyar zuwa d’aki.
Mahaseem tana tafe tana yar wak’ar ta taje gidan su laure a kofar gida ta tsaya ta aiki wani yaro tace yace ana kiran laure inji Habu, nan yaron ya shiga ya fad’a ma laure ai ko da sauri ta tashi ta yab’a gyalen ta saboda Habu saurayin tane,sai dai mai, tana fita tai karo da Mahaseem cikin tsoro zata juya, Mahaseem ta shak’o wuyar ta”Ai yau ba zaki gudu ba, nasan dama ba fitowa zakiyi ba idan bance Habu bane, aradun Allah yau sai kin biyani kud’i na”
Laure gaba daya a tsorace take”sake ni toh in kawo miki ai naira hamsin ce”
Sakin ta tayi ta rik’e mata hannu”toh mu shiga gidan naku ki dauko min kar ma ayi tunanin wani ai mu k’awaye ne koh?”ta fad’a tana daga mata gira
Sanin halin Mahaseem yasa Laurr ta d’aga kai, a haka suka shiga gidan ta shiga d’aki ta dauko naira hamsin ta bata, murmushi Mahaseem tayi tace”Kawata laure sai anjima” ko kulata ba tayi b ta fita,daga nan wucewa tayi wani guri inda ake saida dussa ta siya ta nufa gida tana zuwa ta nufa gurin wata akuya tana cewa”Yar Akuya ta zo kici dussa”ta zuba mata a wani kwano tana shafa jikin akuyar, da bala’i Inna ladi ta fito jin muryar Mahaseem”uban mai Bibalo tayi miki kika dake ta”?ta nufe ta ganin hakan yasa Mahaseem ta shige d’aki a guje ta rufe kofa Inna Jummai na tambayar ta meya faru bata kulata ba ta nufi window tana tsalle tana cewa”ba dai Ubana ba wallahi, Bibalo kuma sai na dake ta tunda ta raina ni”cike da tsiwa take fad’a yayin da Inna ladi ke massifa sosai. Kin bude kofar tayi haka Inna ladi ta gaji ta bar gurin, Inna Jummai ce ta kalle ta”wai ke meke had’a ki da Bibalo ne? ”
Tsalle tayi ta haye gado tace”Wallahi ta rainani, nace dazu taba akuya ta ruwa, shine Dan tana gaban Innar ta wai tak’i din dama nace kwarankwatsi sai na dake ta”
Inna Jummai girgiza kai tayi kawai domin tasan Mahaseem da shegen tsokana ga tsiwa.
Wace ce Mahaseem?
Asalin ta y’ar wani k’auye ne Mai suna Rahaama dake Jihar Kaduna,iyayen ta fulani ne Mahaifinta Malam Habibu su biyo iyayen su suka haifa daga shi sai kanin shi Malam Ayuba, iyayen su suna da arzik’i irin na kauyen nan domin baban shi manomi ne,ba’a Dade ba ya rasu inda aka raba musu gado shi Malam Habibu yayi ta tatala gadon shi, a haka ya had’u da wata bafulatana soyaya ya shiga tsakanin su, zance ya kai gaban manya aka daura musu aure, sunan ta Na’ima rugar su tana da Dan nisa daga kauyen nan, tallar nono take kawowa nan, bayan auren su ba’a Dade ba shima Ayuba yayi aure anan kauyen ya samu mata Jummai, a gidan su duk suke zaune, Ayuba shagalin shi kawai yakeyi da kudi duk ya cinye gadon nashi, Malam Habibu yana yawan mai fad’a akan ya dinga tatali sai yace aa shifa gara yaci kudin shi, ana haka Na’ima ta samu ciki,ita da Jummai suna shiri sosai kasancewar gida daya suke,wata rana aka wayi gari mahaifiyar su Malam Habibu ta rasu, sosai suka ji mutuwar ta, bayan wasu watani Na’ima ta haihu ta samu y’a mace aka sa mata suna Mahaseem, Sosai sukayi farin ciki, nan fa malam Ayuba ya fara damuwa ganin jummai ita ko b’atan wata bata taba yi ba, a haka Mahaseem ta shekaru biyu, lokacin Malam Ayuba ya had’u da wata ladidi ta, sosai take son shi amma shi baya sonta, da asiri da kissa tasa ya aureta, tunda akayi auren babu zaman lafiya tsakanin ta da Na’ima da Jummai domin ta tsane su, sai dai ita ma shiru ba haihuwa har tsawon shekaru biyu, lokacin Mahaseem shekarar ta hud’u a duniya, mahaifiyar ta na dauke da wani cikin wata rana suka shirya tafiya rugar su, Jummai ta dauki Mahaseem tace Dan Allah su bar mata ita tunda Mahaseem din ta dage ba zata bisu ba, nan suka tafi suka barta tunda aranar zasu juyo, Allahu Akbar ashe wannan tafiya bata dawowa bace domin a hanyar su ta dawowa sukayi hatsari ba wanda ya rayu a motar, Malam Ayuba ya shiga tashin hankali na rasa dan’uwan shi, Mahaseem bata da wayau amma ko yaushe sai tace yaushe iyayen nata zasu dawo, sosai Jummai ke kuka idan tace hakan saboda akwai shak’uwa sosai a tsakanin ta da Na’ima, Malam Ayuba yace shi zai rik’e Mahaseem saboda gadon da aka bar mata, sannan ladidi bayan ta gama takaba yazo ya nema auren ta Dan kawai ya samu dukiya tunda ita ma an bata nata gadon, Ladidi ganin dagaske sonta yake kawai sai ta amince ta aure shi, amma ta tsani Jummai da Mahaseem, ana yin auren kuma sai ta samu ciki ai nan fa ta fara ma Jummai gorin haihuwa ita dai bata kulata domin ita mace ce mai kirki da hakuri, a haka ta haihu ta samu ya mace aka sa mata Habiba ana cemata Bibalo, Malam Ayuba haka yaketa had’ame dukiyar marainiya Mahaseem kuma ba sonta yake b yafi son y’ar shi kawai baya son nunawa ne a gari kar ace gadon Mahaseem yake so shiyasa yake nuna yana sonta, Ladidi ko ba karamin haushin hakan yake ba, shi ko cemata yake kawai saboda mutane yake yin hakan ai shima ba sonta yake ba, ita ma ladidin duk ya cinye mata nata gadon.
A yanzu shekarar Mahaseem Goma sha bakwai, kyakyawa ce ajin farko, doguwa ce mai kyan diri gata fara sol, tana da dogon hanci da bakin ta Dan daidai, hakoranta a jere farare kal ga dimples idan tana magana yana lotsawa, ga gashin ta baki ne sosai mai santsi domin bata ma kitso sai dai Inna Jummai ta dinga gyara mata shi, tana da cikar gira da gashin ido, Mahaseem duk kauyen nan ba wanda ya kaita kyau da tsafta ga ta da son kwaliya, mussaman Kawu Ayuba ya siyan mata kayan kwaliyar, Mahaseem tayi Primariya yanzu tana secondary SSS 1 take akwai ta da kokari, ga son zuwa makaranta, tana zuwa Islamiyya, nan ma Jummai na kokari tana bata tarbiya tunda ita ma tana da ilimin ta, Malam Ayuba yayi kokari ne yasa Mahaseem a makaranta kar yan kauyen su zage shi akan rashin kula yar marainiyar, Mahaseem akwai shegen surutu, ga rawar kai da shegen tsokana amma sai tsoro, kawayen ta biyu laure da Indo amma tafi shiri da Indo, duk sa’oin juna ne,ita da Indo ajin su a makaranta, Inna Ladi ta tsani Mahaseem baran ma yanda taga ta cika tana zama budurwa, tun tana karama take sa Mahaseem aiki, lokacin tana tsoron ta haka za tayi ta bata wahala, amma tunda ta fara girma sai tana k’i, idan Aiken ta tayi sai ta gudu taki zuwa, aikin gidan ko idan ba dukan ta tayi ba ba tayi, Inna Jummai idan tayi magana sai Inna Ladi ta hauta da massifa, shiyasa ma bata shiga harkar ta, Mahaseem ta tsani Inna Ladi, shiyasa idan tayi mata wani abin sai ta huce akan yarta Bibalo, habawa ai nan za tayi ta bala’i an taba mata y’a dan tunda ga kanta bata sake haihuwa ba, yanzu Bibalo shekarar ta sha biyu, Mahaseem duk Wanda ya tab’o ta bata hakura sai ta rama, Malam Ayuba yayi fad’an har ya gaji domin ana yawan kawo mai karar ta, Inna ladi ma har abin na bata haushi sai tace yafi son Mahaseem akan y’arshi, toh amma fah shima idan ta bashi haushi kulle ta a daki yake ya nakad’a mata dukan tsiya.
~Wannan kenan~
*_TAKU CE UMMU_ _BASHEER_*
[05/11/2022, 6:50 pm] +234 902 983 1068: *_MAHASEEM_*
{ “`Heart“` “`Touching“` “`Story“` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
“`HASKE“` “`WRITER’S“` “`ASSOCIATION“` …💡
*Page 02*
“`Maitama Abuja“`
_Kyakyawan_ Saurayi ne ya fito daga cikin wata had’adiyar mota fara mercedes wato Wanda akafi sani da benz (C300), dogo ne mai fafad’ar kirji, jikin shi na mazaje ne masu k’arfi, fari ne, yana da manyan ido, dogon hanci tare da pink lips kamar wanda ya shafa lipstick saboda yanda yayi pink sosai, sanye yake cikin navy blue suit, hannun shi rik’e da labcoat, dayan hannun kuma briefcase ne, cikin takun kasaita haka yake tafiya zuwa Cikin gidan wanda ya had’u iya haduwa Mansion ne domin bangare daban daban na gani, nan ya bud’e wani kofa mai kyau ya shiga, wata matace fara na gani tana saukowa daga stairs, Murmushi ta saki tana cewa”Habibi nah ka dawo”
Ramin Mugunta Hausa Novel Complete
Murmushi yayi mata wanda ya kara mai kyau tare da zama a kujera ita ma zama tayi, yace”Mom Barka da warhaka”
“Yauwa Habibi ya aikin?”
Zai bata amsa sai ga wata Kyakyawar budurwa ta shigo da gudu sanye cikin Uniform ta fad’o kan Mom, wani irin tsawa ya daka mata da sai da ta mik’e”Nawwal kina hauka ne zaki shigo haka”
Mom ce tace”Aa kyalen min Auta nah, kinji je kiyi shower kizo kiyi lunch Dan nasan ba kiyi ba a school ”
Kallon shi tayi tace”Sorry Broh _NIBRAS_ ya aiki”
Ko amsa ta baiyi ba ya dauki wayar shi yana dannawa ganin haka ta nufi upstairs jiki a sanyaye.
Mik’ewa yayi domin tafiya side dinshi Mom tace ya tsaya yaci abinci yace Nawwal ta kai mai zaije ya huta, nan ya fita,wani bangare naga ya nufa Dan karamin flat mai kyau ya shiga masha Allah nace ganin haduwar sky blue and white komi na parlour, straight bedroom ya shiga nan ma fa ya hadu domin komi white ne zallah, ya dad’e yana wanka sannan ya fito ya shirin cikin wasu kananan kaya, jin knocking yasa ya nufa kofar yana budewa yaga Nawwal rik’e da basket na abinci matsawa kawai yayi taje ta ajiye a dining ta Fita,bayan yaci abinci yaje massalaci sai da yayi isha’i ya shigo gidan, wani side naga ya nufa, yana shiga naga wata tsohuwa a zaune kan kujera ta tasa TV a gaba, idanun ta sanye da medical glass, murmushi yayi ganin gaba daya hankalin ta na kan TV din, zama yayi kusa da ita hannu tasa a baki alamar yayi shiru, hannu yasa ya fara matsa mata kafafu, kallon shi tayi”ai koh kamar kasan ina neman mai matsa min kafa duk sunyi tsami”
“Kina shan magungunan ki kuwa?”
Tsaki taja”kai raba ni da wannan magungunan sai dacin bala’i”
Mik’ewa yayi yana cewa”Still dai ya kamata ki dinga sha saboda lafiyar ki”
Hararan shi tayi”toh likita bokan turai”
Murmushi yayi tare da mata sai da safe daidai zai fita sai ga wata matashiyar budurwa ta shigo cikin matsatsen doguwar riga bako gyale, tana ganin shi tayi wani fari da ido”Ya Nibras two days ban ganka ba”
Tsaki kawai yayi ya bar gurin, haushi taji ta kalli Granny tace”tsohuwa kinga abinda Yayi min koh?”
Dak’uwa tayi mata”Amshi nan uwar kice tsohuwa, wallahi Naila ki kiyaye ni”
Tsaki tayi ta juya tana cewa”Dan ma kin samu nazo gaishe ki shine zaki wani wani mttsssss….” Ta fita tana guna guni.
Ita ma tsakin taja ta cigaba da kallon ta.
Familyn Kabeer Yero sanane ne, Alhaji Kabeer babban mutum ne Dan kasuwa ba Wanda bai San Family Yero ba, d’an Kaduna ne anan yayi aure matar shi daya ce Safiya, ta haifa mai yara maza uku daga nan bata sake haihuwa ba, Akwai Sultan, Aliyu sai Lawal, Sultan yayi karatun likitanci ne a kasar Sudan acan ya had’u da wata balarabiya Sunan ta Nimrah soyayya suke sosai amma iyayen ta sunk’i yarda ta auri Dan Nigeria haka ya koma Nigeria amma gaba daya yana cikin damuwa, lokacin daya koma kanin shi Aliyu yayi aure yana aiki a kamfanin baban su, lokacin da Sultan ya dawo mahaifin su ya bude mai hospital, nan ya fara aiki ya had’a harda kasuwanci ai nan fah ya fara kud’i, sosai ya damu da Nimrah har ya sanar da mahaifiyar su nan ta fad’a ma Baban mussaman ko Baban ya shirya shida wani yayan shi da aminin shi da Sultan din su kaje har Sudan suka nemar mai auren Nimrah ganin iyayen Sultan sai suka amince bayan wasu yan bincike aka sa ranar aure acan akayi auren aka kawo ta Nigeria, ba’a Dade ba da auren mahaifin su Sultan ya rasu inda ya bar musu tarin dukiya, bayan wasu kwanaki da rasuwan shi aikin kasuwancin ya maida Sultan Abuja acan ya ya gina wani baban Hospital, Ba’a dauki lokaci ba lawal Shima yayi aure, Nimrah duk ta damu da rashin samun haihuwa saboda two years kenan da auren su amma shiru ga matar Aliyu ta haifi namiji, Sultan ganin kowa da gidan shi a kaduna ga mahafiyar su ita kadai a gida sai mai aiki yayi tunanin gina musu gida a Abuja, gadan gadan aka fara aiki, lokacin Nimrah ta samu ciki, ai koh ba karamin farin ciki su kayi ba, bayan wata tara ta haifa kyakyawan d’ant ranar suna yaci suna Nibras ba’a Dade ba matar Lawal ma ta haifi danta Hibban, bayan wasu shekaru Alhaji Sultan ya kammala gini, gida ne na gani na fad’a babban gida ne mai dauke da side daban daban akwai side dinshi sai na Lawal da Aliyu, sai na mahaifiyar su, sai kuma wani flat da yayi guda uku masu kyaua jere na y’ayan su Maza, tare da taimakon kannen shi suka had’a kai aka kamala komi hatt da furnitures komi sabo, amma Alhaji lawal yace ba zai iya barin aikin shiba amma zasu dinga zuwa Hutu, Alhaji Sultan baiji dadin hakan ba, haka suka tare a gidan su dake Maitama Abuja,
Bayan wasu Shekaru, Alhaji Sultan ya zama babban attajiri, karshe ma kanin shi Aliyu ya daura a company shi, Yaran su biyu yanzu Nibras sai kanwar shi Nawwal, sai Alhaji Aliyu yaran shi uku akwai Salman, Naila,sai Hibban wanda yake sa’an Nawwal, shekara d’aya ne tsakanin Naila da Hibban,sak’o ne kullum cikin fad’a suke, sai Alhaji Lawal danshi Fawwaz sa’an Nibras sai kannen shi uku mata, Sa’adat, Nihla sai Safina, Ummie(mahaifiyar Nibras)tana son yaran ta sosai tana ji da Nibras ba kadan ba take sonshi, haka Nawwal ta shagwab’a ta dayawa, Ummie bata da wata matsala akwai kirki sai dai bata son talauci ko kadan tana da high taste, Matar Aliyu wato Mom bata da mutunci akwai ta da son abin duniya ga hassada da bakin ciki ko kadan bata shiri da Ummie dama tunda aka auro ta basu shiri tana bakin cikin ta fita kyau, gashi kuma mijinta yafi nata mijin kud’i, bare kuma yanzu da mijin nata ke aiki karkashin Abie(Alhaji Sultan) sosai take bakin ciki, gashi duk ta bata yaran ta bata tsayawa ta basu tarbiyya, baban Dan nata Shaye shaye yake ga neman mata kuma ta sani,bata damu ba, Naila kuwa bata da nutsuwa akwai shigar banza ita dai bata bin maza amma fah bata da kunya ko kadan, tana da kyanta daidai, tana bala’in son Nibras amma shi baya son ta, kowa a gidan yasan yanda take son shi, Hibban ba ruwan shi domin yanzu yake da 24yrs,yanzu ya gama ABU Zaria inda ya karanci Law,Hibban yana da kyau,yana da haske domin duk yafi su Naila haske duk da ba fari ne sosai ba, shida Nawwal suna shiri sosai, Mom tana jin haushin yanda suke shiri kusan ko yaushe Yana side dinsu Nawwal, sau dayawa shine yake koya mata Karatu, tsakanin Naila da Hibban ba nisa shekara d’aya ne tsakanin su,Mom ba karamin haushin Naila take ji ba yanda take son Nibras, Kullum sai ta zauna tana musu hud’ubar tsiya, Salman ne kawai yake daukan hud’uban ta sauran koh anan zasu watsar dashi, Salman yana jin haushin yanda baba shi ke aiki kasan Abie gani yake kamar su ba’a son sune.
Nibras kyakyawa ne saurayi Dan kimanin shekaru ashirin da tara, yayi karatun likitanci inda yanzu ya zama cikaken Doctor mahaifin shi ya daura shi matsayin shine Babba a hospital dinshi, inda mahaifin ya koma harkar kasuwanci lokaci zuwa lokaci kuma yana Dan duba hospital din, Nibras mutum ne mai son tsafta, miskili ne baya son hayaniya, yana da aboki guda daya Sahal shima doctor ne tare suke aiki, Nibras mata basa gaban shi domin bai tab’a yin soyayya ba cewa yake waste of time ne, yana son aikin shi domin taimakon Al’uma, Suna shiri shida Fawwaz, lokaci zuwa lokaci shida iyayen shi sukan je Sudan domin gaida yan’uwan mahaifiyar su suma kuma sukan zo wani lokacin.
“`Please ina son a dinga comments sosai, more comments more Typing“`
“`TAKU CE UMMU BASHEER“`
[05/11/2022, 6:50 pm] +234 902 983 1068: *_MAHASEEM_*
{ “`Heart“` “`Touching“` “`Story“` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
“`HASKE“` “`WRITER’S“` “`ASSOCIATION“` …💡
*Page 03*
Zaku iya samun Litafin MAHASEEM a Arewabook,da zarar kun danna wanna Link din yana nan a Arewapick
MAHASEEM:: https://arewabooks.com/book?id=635465711677b95a648a4741
“`Mahaseem“`Ce zaune kayan kwaliyya ne a gaban ta, Ta shafa wannan ta goga wannan, Ta dauki kwali ta damb’ara shi kan girar ta mai cika sai ya wani dankare, aka diga kwali a goshi da hanci, sai kumatu da kasan bakin ta duk tayi d’ige d’ige, ta dauki jambaki ja ta shafa a lips din shima yaji sosai gashi dama ta shafa powder yayi ranbad’au, madubi ta kalla tana murmushi tace”Ho ni, Ho ni aradu na hadu, nayi shegen kyau fah”
Inna Jummai dake lazimi ta kalle ta tace”Wai lafiyar ki qalau kuwa kike kwaliya da daren nan?”
Ajiye madubin tayi tace”Dandali zanje fah, kin manta dazu n fad’a miki”
“Dandali kuma Mahaseem, kinsan cewa na hana ki zuwa , kina y’a mace ace zaki fita da daddare, ke ko tsoron duhu da aljanu ba kya yi”
Turo baki tayi ta b’ata rai”kai Inna yanzu fah akayi isha’i, kuma ni banjin tsoro”
“Aiko ba inda zaki, kinyi kwaliya sai kace Aljana”
Kamar za tayi kuka tace”Nidai ba Aljana bace, kuma duk yan matan kauyen nan na fisu kyau”
Banza da ita Inna Jummai tayi can Mahaseem ta mik’e wai zata je bayi,tana fita kuwa tayi murmushi ta fara sand’a zata fita, tana kallon bayan ta, tazo gurin k’ofa taji taci karo da mutum arazane ta dago kai, wa zata gani, kawun tane a tsaye shigowar shi kenan sukayi karo, Tsawa ya daka mata”gidan Uban was zaki kike sand’a?”
Sosa keya ta fara”ehm…da..wai..zan..rufe kofa ne fah kawu”
Tsaki yaja Dan yasan karya take ai ko ya fatatake ta, ta wuce d’aki ta shiga tana ta guna guni, Inna Jummai tace”Ke Kuma lafiya, kika shigo kina magana ke kad’ai?”,
Fashewa tayi da kuka tsabar takaici domin tayi zasu had’u da Indo a dandali, Inna Jummai tayi magana juyin duniyar nan taki kula ta a haka bacci ya dauke ta.
Washegari da safe bayan tayi sallar asubah ne Inna ladi ta tasa ta a gaba wai sai ta jawo mata ruwa a rijiya haushi duk ya ishe ta, ta tsani Jan ruwa da sanyin safiya, haka tana Jan ruwan tana guna guni, Sai data cika wata robar, tana gani Bibalo ta fito d’aki tana hamma ita sai lokacin ma ta tashi, kwafa Mahaseem tayi tace”yarinya zaki ci na jaki, a kanki zan rama, wato ke da ake so ba kya aiki koh”
Bibalo bata ji ta ba saboda suna da Dan nisa tsakani, bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin kayan makaranta dark blue wando sai farar riga da hijab fari iyakar gwiwa ta dauki jakan makarantar zata fita dakin Inna Jummai tace”ah ina zaki baki karya ba”
Tsaki tayi tana sa sandal tace”Kawai da sasafe a ishi mutum da massifa ga aikin tsiya sai kace wata jaka”
Inna Jummai tasan akan mai take mawa nan tace”hakuri za kiyi komi na rayuwar nan lokaci ne wata rana sai labari, ki bar ma Allah komi”
Mikewa tayi tace”Inna ki bari kawai nasan mai zanyi…yanzu bani kudin break”
Mika mata naira hamsin tayi tana mata addu’ar a dawo lafiya, har ta fita k’ofa ta dawo tace”Inna y’ar Akuya ta Dan Allah ki kular min da ita kinji”
Murmushi tayi tace”Mahaseem mai akuya karki damu maza yi sauri kar ki makara”
Wucewa tayi daidai zata fita taga kokon da Inna ladi ta dama shi kenan yana gaban murhu taje dauko sugar, kawai Mahaseem tasa k’afa ta kifar dashi ta fita da sauri tana dariya ai ko banza dai ta rama.
Bayan sun fito break ne Mahaseem ta kalli Indo da wata yar ajin su Lami tace “kai kuzo muje gidan headmaster mu samo gwaiba”
Da sauri Lami tace”Kutt aradun Allah ban zuwa, headmaster idan ya kama mu buga zamu sha”
Dungure mata kai Mahaseem tayi”Banza matsoraciya kawai, Indo zo muje kuma saura idan kin gani kice zaki sha , nasan ki da shegen kwad’ayi”ta kare tana jan hannun Indo, ita kanta Indo tsoro take amma tasan halin k’awarta yanzu sai ta daina kula ta akan hakan.
Sad’af sad’af haka suka shiga gidan da yake gidan cikin makaranta ne,Mahaseem ta kalli Indo”Ke Indo maza haye ki tsinko”
Zaro ido tayi”Tsoron hawa bishiya nake Allah kuwan”
B’ata fuska tayi”dallah can ki hau ki tsinko ko sai yazo ya ganmu ne”
Jiki na rawa Indo ta fara k’okarin hawa kwatsam sai ga Headmaster”Dama kune masu zuwa satar gwaiba koh?Allah ya kama Ku yau”
Indo da sauri ta tsaya tana rawar sanyi tsabar tsoro domin ta tsani duka, Mahaseem ma ta tsorata amma cikin tsiwa tace”Headmaster kaji tsoron Allah yaushe muke zuwa, yau nefa, kuma ma ai cikin makaranta ne nan duk cikin PTA dinmu za’a cire Idan ma munsha”
Takaici ne kama shi aiko ya tasa su a gaba har makarantar baiyi magana ba, Suna zuwa ya sasu Kneel down, ya samu bulala yayi musu biyar biyar masu kyau, Indo sai kuka take Mahaseem ko idon nan yayi Ja amma ko hawaye, aranta ko tunanin ya za’ayi ta rama take, haka suka koma aji ko karatun ma bata nutsu taji ba.
Bayan an tashi tana hanyar zuwa gida ita da Indo ta hango Bibalo rik’e da bokitin nik’a, dariya tayi tana zuwa daidai Bibalo ta kifar mata da nik’ar gaba daya kayan miyan ya zube a jikin Bibalo, ta fashe da kuka ta zauna a gurin.
Mahaseem ko jan Indo tayi suka bar gurin, Tana zuwa ta shiga gida da d’an wak’en ta, Inna Jummai dake tuk’a tuwo a tsakar gida tace”Mahaseem ke dai ba zaki dinga jin magana ba koh, sallamar fah”
Lokaci daya annurin fuskar ta ya dauke ganin tuwo”kai Inna meye haka kuma ya nake ganin Tuwo, gaskiya ba’ayi min adalci ba idan na zama shugaban k’asa zan hana yin tuwo a Nigeria ”
Dariya Inna tayi”Allah dai ya shirye ki, idan ba kici ai sai ki siyo wannan taliyar yaran kici”
Da murna tace”yauwa innata shiyasa nake sonki, amma fah ba taliyar yara bace Indomie ake cewa”
“Oho dai tunda kin gane”
Bibalo ce ta shigo gidan da kuka wuff Mahaseem ta shige d’aki ta kulle, da sauri Inna Ladi ta fito jin kukan shalelen ta, nan Bibalo ta fad’a mata abinda ya faru rai a b’ace ta nufi bakin kofar tana cewa”Shegiyar yarinya, irin jaraba, yanzu ni kin raina ni a gidan nan koh, wato ana goya miki baya, fitinaniya”
Mahaseem ta window ta lek’o tayi gwalo tace”Ga fitinaniya nan Bibalo, mai kan kwakwa”
Habawa ai nan ranta ya kara b’aci tayi window harda daukar mucciya, da sauri Inna Jummai ta tare ta tana bata hakuri cewa karta biye ma kuruciyar Mahaseem ita ko massifa take tana cewa ai Inna Jummai ce take koya mata iskanci iri iri a gidan, ita dai aiki ta koma tana yi, tunda taga mahaseem tayi shiru, ita koh Uniform take cirewa tana dariya domin ta maida Inna ladi mahaukaciya.
Suna hanyar dawowa daga Islamiyya ita da Indo sunzo wucewa ta wani lungu suka hango Headmaster ya duk’una yana bayan gida, Da sauri Mahaseem ta rad’a ma Indo Wani abu a kunne Indo zaro ido tayi tana girgiza kai, Mahaseem ta harare ta, waigawa tayi taga wani katon kadangare, ai ko tayi lamo ta cafko shi Dan bata tsoron kadangare, a hankali ta isa bayan headmaster ai ko ta wurga mai kadangaren, da sauri taja hannun Indo suka ruga a guje, jin kamar wani abu ya fad’o mai yasa ya mik’e sai baiga komi ba, ya cigaba da abinda yake kawai sai jin waiwayi yayi a wuya yana tab’awa yaji kadangare, ai wani ihu yasa saboda a rayuwar shi baya son kadangare bare wannan kutu mai jan kai ne,Headmaster a guje ya ruga ko wandon bai gama sawa ba, yana rike da ita a hannu………….
Sannu a hankali yake tafiya zuwa Side din granny, sanye yake cikin white shaddah, kanshi ba hula gashin shi ya kwanta luf luf gwanin sha’awa irin na larabawa, Nibras kenan, tafe yake cike da kasaita yana danna wayar shi, Wani kyakyawan saurayi na hango fari amma ba sosai ba, yana sanye da sky blue Yadi, kanshi hula ne colour kayan, Fawwaz kenan fuskar shi dauke da murmushi ya mik’a ma Nibras hannu suka gaisa, a tare suka nufa side din granny, Wanda Fawwaz ne ke Dan jan Nibras da hira shidai Uhm ko hmm yake cewa, Fawwaz bayan gama karatun shine Abbie ya samar mishi aiki a Abuja shine yake zaune dasu.
Around 4pm ne kowa ya hallara a parlour granny domin duk Friday suna haduwa dukan su, ayi hira har zuwa magrib,Granny ce ta kawo shawaran hakan domin kara kusanta da juna, Dan tasan Mom da Ummi ba shiri suke ba, bata son su raba mata kan y’aya da jikoki, Shigowar su a tare yasa kowa ya kalle su, Kawu Ne yayi saurin cewa”Ku kuma sai yanzu ne zaku shigo biyar saura”
Nibras ko kallon shi baiyi ba ya nufa gurin Granny, Fawwaz ne yayi murmushi yana cewa”Kawu ayi hakuri Dan Allah, sannun Ku da gida”
Kawu yaji haushin yanda Nibras yayi mai, ciki ciki ya amsa ma Fawwaz, nan suka gaida kowa, dai ana ta hira cikin anashuwa idan aka cire Mom da Ummi wacce basu wani sa baki a maganar, Salman ko ganin Nibras ya shigo bakin ciki ya kama shi kawai sai ya tashi ya bar gurin, Nibras ko wayar shi kawai ya cigaba da dannawa, Naila wacce taci uban ado saboda shi ta dawo kusa da jujerar da yake tana magana k’asa k’asa”Ya Nibras kayi kyau, gaskiya ina kishin ka Allah yasa ba wacce ta ganka da shigar nan”
Banza yayi da ita, haka tayi ta zuba ba tare data damu ya kulata ba, Mom dake kallon ta sai signal take mata da ido akan ta bar kusa dashi, ita koh yar duniya ko a jikinta, Ummi tana lura dasu amma bata damu ba Dan tasan d’an nata mata basa gaban shi bare kuma Naila tasan ba sonta yake ba. Haka akayi ta hira ana wasa tsakanin Granny da jikokinta,
Sai gurin magrib aka watse aka bar granny, tana jin d’adin yanda take kasancewa tare da familyn nata, damuwar ta daya Lawal baya nan, amma kuma ai ga Fawwaz da sauki.
Mom tana suna shiga side dinsu taja hannun Naila zuwa bedroom”ashe ke wawuya ce, bance ki fita harkar miskilin yaron can ba?”
Turo baki Naila tayi ta d’aga hannu”Abeg pls mom ki barni da wanda nake so, nidai ina son shi kuma aure za muyi”
Cike da takaici Mom tace”Dan Ubanki ba sai ki auren shi in gani ba, kullum ina fahimtar dake gaskiya amma kink’i ganewa…..”
“Brain dinta na kifi ne, ai , Stupid Mara zuciya, meye amafanin son wanda baya sonka baya son iyayen ka?” Salman ne ya katse maganar Mom lokacin da yake shigowa dakin.
Naila cikin rashin kunya tace”No Ya Salman kar fa ka takura min, kowa fah abinda yake so yakeyi a gidan nan, kai waye ya takura ma” wani irin duka yazo kai mata ta zille ta fita brdroom din a guje, zai bita Mom ta jawo hannun shi”wai kai meye hakane, yanxu sai ka bita kuna tsere shiyasa ta raina ka ai, Respect ur self pls”
Yana huci ya zauna kan bed yana cewa”da kin barni nayi maganin rashin kunyar ta ai”
Zama tayi tana mai nuna mai bak’in cikin ta akan Ummi da yaran ta, shi kanshi bakin ciki kishi da hassada ya rufe mai ido.
~Kauye~
“Kam bala’i, yau sai kinci Ubanki yarinyar nan” Inna Ladi ta fad’a lokacin da Mahaseem tayi mata wurgi da bokiti wai ba zata sha ruwan ba.
Ganin tayo kanta rai b’ace tana bala’i yasa ta fasa k’ara tace”Wayyo Inna zata kashe ni,zo ki ceci rai”
Kafin Inna Jummai ta fito Inna ladi ta cafke Mahaseem dake shirin guduwa, wani ice ta jawo ta shiga dukan Mahaseem dashi, Inna Jummai ce ta k’wace ta da k’yar amma bakin Mahaseem yak’i mutuwa cewa take”Wayyo Allah zata kashe marainiya, jama’a za’ayi kisan kai, wayyo Allah ya isana”
Inna Jummai ne ta jata gurin dakin ta yayin da Inna ladi me cewa”Massifafiyar yarinya duk kin ishe mu agidan nan toh bari malam ya dawo, dole asan abinyi, shegiya irin mayu mai kama da Aljanu”
Mahaseem na kuka tace”Ban yafe ba wuta balbal, kuma sai na rama gurin Bibalo”
Za tayo kanta ta shige d’aki tasa sakata.
“`Nidai nace Mahaseem ga tsoro ga tsiwa“`
_TAKU CE UMMU BASHEER_
[…] Â Mahaseem Hausa Novel Complete […]