Littafan Hausa Novels

Kishi da Aljana Hausa Novel Complete

Kishi da Aljana Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

 

[05/11/2022, 10:09 am] +234 814 777 1250: DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN ƘAI.

 

 

 

FREE BOOK NE.

 

PAGE 1

 

 

 

 

KISHI DA ALJANA👹

 

 

 

 

NA MRS SULAIMAN( ZAINAB FALALU)

 

 

 

 

MARUBUCIYAR

 

 

 

 

ƘADDARAR MU

 

WANI HANIN GA ALLAH.

 

KISHI DA ALJANA.

 

 

 

 

 

 

 

Misalin ƙarfe uku saura na dare, Abdul ya farka a firgice daga baccin da yake,

 

Gaba ɗaya babu inda baya rawa a jikin shi, ga zufa da ta jiƙe shi sharkaf tun daga kan shi har zuwa ƙafar shi,

 

 Mahaseem Hausa Novel Complete

 

Shiru yayi ya dafe kan shi da ke sara mishi da hannun shi na dama yana ta ƙoƙarin ya tuna abinda ya gani a cikin mafarkin shi, amma ikon Allah kamar wanda aka shafe wa tunani tas ya manta abunda ya wakana a cikin mafarkin.

 

 

 

 

Ban da ƙarar bugawar agogon bangon ɗakin, da kuma kukan tsanya baka jin motsin komi se na zuciyar shi dake bugu ɗai-ɗai.

 

 

 

 

 

 

 

yafi awa ɗaya a zaune, yana ta so ya tuna mafarkin shi, amma ina, se ma kan shi da yaji yana juya mishi kamar wanda ake hajijiya da shi.

 

 

 

 

Salin alin Abdul ya gyara pillon shi ya takure waje ɗaya ya rumtse idanun shi ko Allah ze sa baccin na shi ya dawo

 

Se wajajen asuba tukun baccin yai gaba da shi.

 

 

 

 

 

 

 

duk da rashin baccin da Abdul be samu ba hakan be hana shi farkawa a dai-dai lokacin da ake kiran sallar asuba ba, saboda sabo

 

 

 

 

Jiki a mace ya farka bayan yayi addu’ar tashi daga bacci

 

(ALHAMDULILLAHILLAZI AHAYANA BA’ADA MA AMATANA WA’ILAIHINNUSHUR)

 

 

 

 

seda ya zauna kusan seconds, kafin ya yunƙura ya shiga toilet ɗin dake manne a bangon ɗan madedecin ɗakin na shi

 

 

 

 

Bayan ya kama ruwa, sannan yayi alwala ya fice zuwa masallacin dake nan ƙasan layin su.

 

 

 

 

 

 

 

Bayan an idar da salla tare da Abbah suka jero suna tafe Abban ke tambayan Abdul

 

 

 

 

“Anya kuwa idanun nan naka sun samu isashshen bacci kuwa?”

 

 

 

 

Murmushi Abdul ya yi yana shafa ƙeyar shi, kan shi a ƙasa yace

 

 

 

 

“Nayi sosai Abbah, kawai dai be isheni bane”

 

 

 

 

Abbah ya ƙara jefa ma Abdul tambaya

 

 

 

 

“me ka tsaya yi baka kwanta da wuri ba to?

 

 

 

 

“na kwanta da wuri, ina jin gajiyar da na kwaso ce yasa nake jin baccin be isheni ba”

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abbah yace

 

 

 

 

“in ka shiga ciki se ka ɗan ƙara baccin ko ka samu idanun ka sun sauka daga fushin da sukai”

 

 

 

 

Murmushi kawai yayi, Abbah ya wuce can main cikin gidan, shi kuma Abdul yai hanyar inda nashi ɗakin yake can ta bayan main building ɗin gidan.

 

 

 

 

Tunda ya doshi lungun da ze sada shi da ɗakin shi yake jin masifaffen ƙamshi na tashi,

 

Da ɗan mamaki ya ƙara fito da idanun shi da bacci ya ɗan ƙara musu girma, yana nazarin daga inda ƙamshin ke fitowa da sanyin asubar nan.

 

 

 

 

Buɗe hanci sosai Abdul yayi yana shaƙar ƙamshin da yai masifar tafiya da tunanin shi, har wani ɗan nishaɗi-nishaɗi yake ji.

 

 

 

 

Mutum ne shi da Allah ya sa mishi masifar son ƙamshi,

 

Sam baya son ƙazan ta, basa shiri kwata-kwata, in dai kaji faɗan Abdul ko ƙorafin shi, to tabbas akan rashin tsafta ne.

 

 

 

 

 

 

 

Buɗe ɗakin shi yai ya shiga, tsayawa yayi sororo yana kallon ɗakin, ya kalli can ya kalli nan, a fili yace

 

 

 

 

“dama na gyara ɗakin ne kafin na fita?”

 

 

 

 

Can ƙasan zuciyar shi yaji ta bashi amsa da “eh mana”

 

 

 

 

Ajiyar zuciya ya sauƙe ya fara ƙoƙarin cire jallabiyar dake jikin shi, ji yake idanun shi har wani rufewa suke tsabar baccin da ke cin shi.

 

 

 

 

Sanyin na’urar ɗakin ya ƙara, sannan yabi lafiyar gadon shi da ke gyare tsaf,

 

Ɗora kan shi da yai akan pillow yaji same ƙamshin ɗazu a jikin pillown, ƙara kai hancin shi yai yana shinshinawa, har wani lumshe idanu yake, can yace

 

 

 

 

“to ƙamshin nan fa, shi kuma daga ina?”

 

 

 

 

Yarda baccin ke cin shi da kyau yasa kawai ya watsar da batun ƙamshin turaren, ya shige bargo, kan kace me bacci yai awon gaba da shi, a hankali aka kashe wutar ɗakin ta ɗauke.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Bacci sosai Abdul ya sha,

 

se wajen ƙarfe sha ɗaya na safe yaji kamar ana raɗa mishi magana a kunne ana cewa

 

 

 

 

“Tashi, kar ciwon yunwa ta kama min kai”

 

 

 

 

Cikin raɗa-raɗa aka rinƙa rada mishi ya tashi

 

 

 

 

Tarwai Abdul ya buɗe idanuwan shi yana wai-waigawa gefe da gefen shi, ɗan ƙaramin tsaki ya yi, a hankali yace

 

 

 

 

“mafarki ne ma ashe”

 

 

 

 

Toilet ɗin shi dake manne a cikin ɗakin ya nufa,

 

idon shi ya kai kan tiles ɗin bangon toilet ɗin, tun daga sama har ƙasa yake kallon yarda yake ɗaukan idanu, ga ko’ina na cikin bayin ƙal kamar ka zuba abinci kaci, bayan ƙamshi me daɗi dake tashi a ciki.

 

 

 

 

Cikin nishaɗi Abdul yai uzirin shi, yana cikin uzirin shi a yaji motsin kamar an fita daga ɗakin,

 

Be kawo komi a ranshi ba tunda ya san ƙannen shi sukan shigo in tasu ta kawo su ko ma dai wani abun daban.

 

 

 

 

Be wani jima can sosai ba ya kammala abinda yake tukun ya fito

 

 

 

 

Lafiyayyen abinci ya ci karo da shi a jere kusa da gefen gadon shi, abunka ga wanda ke jin yunwa dama,

 

Remote ɗin Tv ya ɗauka ya kunna, sannan ya jawo tray ɗin da aka jero abincin a ciki ya bubbuɗe kulolin dake kai.

 

 

 

 

Soyayyen chips da ƙwai ne a ɗaya, ɗayar kuma farfesun naman kan akuya ne da ya dahu yai luguf yana zuba ƙamshi.

 

 

 

 

Ƙwat, haka Abdul ya haɗiye yawu, miyan shi har tsinkewa yake

 

 

 

 

Kakkauran tea ya haɗa a ɗan madedecin kofi sanann ya zuzzuba komi a plate ya hau ci, har wani lumshe idanu yake tsabar yarda abincin ke ratsa shi

 

Sosan gaske Abdul ya kwashi sanwa ya cika cikin shi taf sannan ya ture gefe yana hamdala.

 

 

 

 

 

 

 

Be wuce zaman awa ɗaya da rabi Abdul yai ba aka kira sallar azahar

 

 

 

 

Seda ya haɗa kwanukan tsaf a kan tray ɗin da aka kawo su tukun ya shiga toilet ya ɗauro alwala, sauri-sauri ya saka kaya, ya fesa turare tukun ya ɗauki wayar shi dake ajiye gefen gado ya saka a aljihun blue jeans ɗin jikin sa sannan ya fice daga ɗakin bayan yasa key ya kulle ƙofar ya wuce masallaci.

 

 

 

 

 

 

 

Ko da Abdul ya dawo daga masallaci be tsaya ko ina ba yai hanyar gida

 

 

 

 

Tura ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin gidan nasu ya yi sannan ya shiga,

 

wucewar fauza ya hango zuwa ɗakin shi ɗauke da flask a hannun ta

 

Tsayawa Abdul yai daga nufar cikin gidan da yai niya, ya ƙwala mata kira

 

 

 

 

“Fauza, gani nan, ya akayi?”

 

 

 

 

Jiyowa Fauza tai tace

 

 

 

 

“Ya Abdul breakfast Ummie tace a kawo maka, taga har rana tayi baka fito ba”

 

 

 

 

Galala Abdul ya tsaya yana kallon ƙanwar tashi, mamaki fal ranshi, yace

 

 

 

 

“Waye a cikin ku ya kawo na ɗazu?”

 

 

 

 

Fauza tace

 

 

 

 

“gaskiya ba wanda ya kawo, nice ma nazo ɗazun naga ƙofar ka a rufe se na juya da shi”

 

 

 

 

Wucewa cikin gidan Abdul yayi bayan yace ma Fauza “muje”

 

 

 

 

 

 

 

Ummie ce zaune a palour ita da ƴan matasan yaran ta, Amal, Ruƙayya, Se ƴan biyun ta Hishma da Hisham suna kallon wani series film da suka nace ma kallo ko gajiya basa yi.

 

 

 

 

Kusan a tare Fauza da Abdul suka shigo palourn,

 

Hanyar kitchen Fauza ta yi, Abdul kuma ya ƙarasa shiga palourn bakin shi ɗauke da sallama, yace

 

 

 

 

“Sannu da hutawa ummie”

 

 

 

 

Idon Ummie na kan Fauza da tai hanyar kitchen ɗauke da abincin da ta haɗa a kai ma Abdul ɗin

 

 

 

 

Fuskar ta a ɗaure tace

 

 

 

 

“Kawo min abincin nan fauza”

 

 

 

 

 

 

 

Bayan Fauza ta kawo abincin gaban ummie, hannu ummie tasa ta buɗe taga a yarda ta zuba shi a haka aka dawo mata da shi

 

 

 

 

Kallon Abdul tai da ya miƙe a kan doguwar kujera idon shi a rufe, tace

 

 

 

 

“ka dawo da wannan ɗabi’ar taka na rashin son cin abinci ko?

 

 

 

 

Shiru Abdul bece komi ba, kamar me bacci

 

 

 

 

Ummie ta ɗaga murya kaɗan tace

 

 

 

 

“ina tunanin ba da kurma nake magana ba”

 

 

 

 

Kaɗan Abdul ya buɗe idanun shi ya kalli ummie, yace

 

 

 

 

“Wallahi ban san dani kike magana ba ummie,

 

Ya ƙara da

 

“me kuma na ƙara yi?”

 

 

 

 

Balla mishi harara ummie tayi,

 

sannan ta maida Idon ta kan Ruƙayya da tafi kusa da abincin tace

 

 

 

 

“Kai mi shi abincin can kan dinning”

 

 

 

 

Abdul ɗin ta ƙara kallo tace

 

 

 

 

“Kafin raina ya ɓaci ka wuce kaje kaci abincin can,

 

wallahi minti kaɗan na baka ina son inga empty plate”

 

 

 

 

Ta ƙara da “mutum ko kuzarin kirki be da shi”

 

 

 

 

Ta shi zaune Abdul yai yana ɗan sosa ƙeyar shi, yace

 

 

 

 

“wai ummie breakfast kike nufi ko lunch, ni fa bangane ba?

 

 

 

 

Zuba mishi idanu ummie tayi tana nazarin Abdul ɗin da maganar shi,

 

Can ta ja tsaki tace

 

 

 

 

“Kar ka rainan hankali mana, ai ba yau ka saba faɗin hakan ba, kiri-kiri da girman ka kazauna kana girba ƙarya akan abinda ba shi ne ba”

 

 

 

 

Abdul da maganar ummien ta fara hawar mishi kai ya numfasa yace

 

 

 

 

“wallahi Allah naci breakfast ɗazu da safe ummie”

 

 

 

 

Shiru ummie tai, ta zuba mishi idanu, can tace

 

 

 

 

“naji, ai yanzu lokacin lunch yayi, kaje kaci wancan ɗin”

 

 

 

 

Badan ran Abdul yaso ba, ba yarda ya iya haka ya nufi dining ɗin inda Ruƙayya ta kai mishi abincin ya ja kujera ya zauna yana kallon uban abincin dake gaban shi,

 

dan har ga Allah a cike yake jin cikin shi, dan ba ƙaramin kwasa yai ma abincin ɗazun ba

 

 

 

 

A hankali ya jawo kular abincin ya zuba ba dan ze iya cinyewa ba, se dan baze iya saɓa umarnin ummie ba

 

 

 

 

lomar shi ɗaya, kawai ya fara jin wata busa me daɗi a cikin kunnen shi,

 

a hankali Abdul ya lumshe idanun shi ya ture abincin yana sauraren busar da ke ratsa shi tun daga kanshi har zuwa ƴan yatsun ƙafar shi

 

 

 

 

Plate ɗin abincin da ya ture gefe na kalla, a hankali a hankali naga an cinye abincin tas se plate ɗin,

 

 

 

 

Dai-dai sanda abincin ya ƙare, a dai-dai nan kuma busar ta tsaya, se wata iska me ɗan ƙaran daɗi dake ratsa Abdul, duk da na’urar sanyi dake aiki a palourn hakan be hana iskar tasiri a jikin Abdul ba.

 

 

 

 

kallon Abdul Ruƙayya tai,

 

da mamaki take kallon plate ɗin gaban shi, a ranta tace “mugun dama a yunwace yake amma ze cuci kan shi yaƙi ci”

 

 

 

 

Taɓo ummie tai da hankalin ta kacokan na kan Tv, ta nuna mata Abdul dake zaune idon shi still a rufe

 

 

 

 

Ita kanta ummie da mamaki ta kalli Abdul tace

 

 

 

 

“Allah dai ya kyauta maka, dama kana jin yunwa amma kake cutar kanka ka zauna da ita”

 

 

 

 

A hankali Abdul ya buɗe idanun shi ya sauke akan plate ɗin gaban shi da ya bari danƙam da abinci a ciki,

 

Mamaki abun ya bashi sosan gaske, amma lokaci ɗaya yaji a cikin ranshi abun ya dena bashi mamakin, sema murmushi da yayi jin ƙorafin da ummie ke ta zuba mishi na yana so amma yana kaiwa kasuwa.

 

 

 

 

Abdul yace yana ƙoƙarin barin dining ɗin

 

 

 

 

“Ni kam tunda na samu an shigar da abincin ai shikenan”

 

 

 

 

 

 

 

Ummie ta galla mi shi harara tace

 

 

 

 

“kai dai ka sani da borin kunyar ka, mutum ya isa ya aje iyali amma ana fama da shi kusan kullum akan cin abinci, Allah ya kyauta maka dai wallahi”

 

 

 

 

Murmushi Abdul ya yi, amma can ƙasan ranshi yana jin tabbas akwai wani abu.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

COMMENTS AND SHARE SABODA ALLAH❤️

 

 

 

 

MASU BUƘATAR A TALLATA MUSU HAJAR SU, ZASU IYA TUNTUƁATA TA WANNAN NUMBER

 

08145225540

 

 

 

 

MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU).

[05/11/2022, 10:09 am] +234 814 777 1250: KISHI DA ALJANA👹

 

NA MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU)

 

MARUBUCIYAR

 

ƘADDARAR MU

WANI HANIN GA ALLAH

KISHI DA ALJANA👹

 

PAGE2

 

Kusa da kujerar da ke kallon ummie Abdul ya zauna, yana ƙorafin nace ma film ɗaya da sukai kullum

 

Ba wanda ya tanka a cikin ƙannen, se ummie kawai data ce

 

“ni da palour na ba wanda ya isa ya hana ni kallon abinda nai niya”

 

Sosa ƙeyar shi yai, yana miƙewa tsaye hannun shi dafe da hannun kujerar da ummie ke zaune yace

 

“Allah ya huci zuciyar ki ummie, ni bari in leƙa wajen muslim, tun safe naga call ɗin shi”

 

Ummie tace ba yabo ba fallasa

 

“A dawo lafia”

 

Ƴan biyun umma suka haɗa baki wajen faɗin “adawo lafia ya Abdul, ka kawo mana wannan sweet ɗin me daɗin nan”

 

Murmushi Abdul yai ya dungure kan Hishma data fi kusa da shi yace

 

“kwaɗayayyu kawai”

 

Bayan Abdul ya fice daga palourn, Ruƙayya ta matso kusa da ummie murya can ƙasa tace

 

“Ummie kin lura da yanayin yaya Abdul kuwa?, wallahi se in ga in yana wani abun kamar ba kan shi ɗaya ba”

 

 

Taɓe baki ummie tayi tana amsa call ɗin da ya shigo wayar ta

 

Bayan ta gama amsa call ɗin ummie ta kalli Ruƙayya da ta maida hankalin ta ga TV tace

 

“ehm, me ki ke cewa ma?”

 

Rukky da hankalin ta yai gaba tace “ba komai fa ummie”

 

Ba wanda ya ƙara cewa komi, suka ci gaba da kallon su,

 

kiran sallar la’asar ya tashe su dukan su, kowa yai hanyar inda ze yi alwala

 

Tarbiyar ummie kenan ga ƴaƴan ta, ba ka isa ko kaɗan kayi wasa da sallah ba, lokacin ta nayi duk wani abu da kake zaka aje shi in ka fara gabatar da sallar se kaci gaba.

 

 

A ƙasa Abdul ya taka har zuwa gidan su muslim da layi ɗaya ne ya raba su,

 

Har ya kai gidan be haɗu da wasu mutane ba se ɗai-ɗaiku,

 

Bayan sun gaisa da megadin gidan su muslim, Abdul yace

“mutumin na ciki kuwa?

 

Megadin yace “yana ciki, shima be jima da shigowa ba”

 

Ƙarasa shiga gidan Abdul yayi, Can cikin gidan ya wuce in da ze sada ka da ahalin gidan

 

Har cikin palourn maman muslim ɗin Abdul ya shiga ya gaishe ta sannan ya fito

Fuskar nan ta shi ɗaure kamar ba shi ne ya shiga da fara’ar shi ba

 

Haka ya ƙarasa ɗakin muslim fuska ɗaure.

 

Kafaɗar shi muslim ya daka yace “wannan ciccin maganin fa?, kai da wa?”

 

Tsaki Abdul yai yana zama a gefen gado yace

 

“na shiga ciki gaishe da mama wata mayyar yarinya ta kafeni da idanu kamar zata cinye ni”

 

Kwashewa da daria muslim yai yana nuna Abdul da ya haɗe girar sama data ƙasa yace “matsala ta dakai kenan guru(haka abokan su ke kiran Abdul tun suna yara) daga an kalle ka shikenan kai an maka laifi, na rasa kai da wasu idanu ka ke gane cewa an kalle kan”

 

Tsaki Abdul ya ƙara ja, yana jin ba daɗi sam a cikin ranshi,

a duniya ba wani abu da ya tsana irin mata su kalle shi, abun na mishi ciwo matuƙa

 

Ganin ƙulewar da Abdul ya yi yasa muslim dena dariyar shaƙiyancin da yake mi shi yace

 

“Nasan yaran gidan nan duk sun tafi islamiya, Nasma ce kaɗai a gidan se mama

 

Kafin muslim ya rufe bakin shi Abdul yace

 

“ai Nasmar nake nufi, shegen kallon tsoya ne da ita kamar mayya”

 

Shiru muslim yai yana kallon Abdul dake ta jero tsaki akai-akai, can dai yace

 

“Ba zaka taɓa canzawa ba guru,”

 

Abdul yace

 

“naji, bazan canza ba ɗin malam, ina ruwan ka?”

 

Banza muslim yai da shi yana ɗaukan towel dake sagale a ƙofar toilet ɗin ɗakin shi ya shige ciki ya bar Abdul dake ta ɗacin rai zaune a gefen gadon shi.

 

 

Be wani jima sosai a toilet ɗin ba ya fito daga shi se boxers,

 

kallon Abdul yai da har bacci ya kwashe shi daga ɗan kishingiɗar da ya yi, be tashe shi ba sema mai da ya shafa ya saka kaya sannan muslim ya ɗan bubbuga ƙafar Abdul ɗin.

 

Buɗe ido Abdul yai yana kallon muslim dake shirye cikin manyan kaya yana zuba ƙamshi, cikin murya ta wanda ya fara bacci yace

 

“Daga kwanciya bacci yai gaba da ni, muje masallaci daga can nai gida, tunda lokacin magrib ya gabato”

 

muslim yace “Ba wani gida da zaka tafi malam, ka manta munyi da kai zamu je gidan su juwairiya?

 

Sosa kai Abdul ya yi, ya kalli muslim da ya ɓata rai yace

 

“guy, nifa ba inda zan raka ka, kawai ka je”

 

Muslim yace “wallahi se ka je, kai fa ɗan rainin hankali ne wallahi,

mun gama shirya magana da kai tiryan-tiryan shine zaka wani doje yanzu bayan na riga da na gama gaya mata cewa tare zamu zo, salan ka maida ni maƙaryaci a wajen ta?

 

Banza da shi Abdul yayi, dan yanzu kam be da ta cewa, tunda shi yai mishi alƙawarin ze raka shin, kuma saɓa alƙawari ba ɗabi’ar Abdul bace.

 

Can dai da ƙorafin muslim ya ishe shi yace

 

“To ƙorafin ya isa haka mlm, ai dai ba zanje gidan mutane da ƙananan kaya ba ko? ka barni naje gida na canza tukun”

 

 

Mukullin mota muslim ya ɗauka yace “muje gidan ka sauya kayan se mu wuce daga can”

 

Ba yarda Abdul ya iya, ba kuma dan ranshi ya so ba ya tashi bayan ya ɗauki wayar shi dake aje a gefen gadon da yake kwance ya yi gaba ya bar Muslim ɗin a baya.

 

A hankali Abdul ke takawa zuwa wajen da Muslim ke aje motar shi,

Kanshi a ƙasa yana replying msg ɗin wani friend ɗin su, kamar ance ya ɗaga kan shi, yana ɗaga kan nashi kuwa sukai ido biyu da wata kyakkyawar mujiya ta zubo mishi idanun nan nata.

 

Ido cikin ido suke kallon juna, fitowar muslim ya dai-dai da tashin mujiyar tai gaba abun ta.

 

muslim da ya ƙaraso yanzu yace “ya ka tsaya anan guru? motar a buɗe take fa”

 

Abdul be ce komi ba, se shafa kan shi da yai yana ƙara waigen inda mujiyar nan ta bi da kallo.

 

 

Seda suka gabatar da sallar isha anan masallacin dake ƙasan layin su Abdul tukun suka tafi gidan su juwairiya

 

Muslim kaɗai ke ta surutun shi, se Abdul yaga dama ya amsa mishi eh ko a’a har suka ƙarasa unguwar su juwairiya

 

Parcking muslim yai a bakin ɗan madedecin gate ɗin gidan ya danna mata kira a waya

 

Ringing biyu juwairiya ta ɗaga, be jira cewar ta ba yace “gamu a waje”

 

 

Basu wuce minti biyar ba a zaune, a ka buɗe mu su gate ɗin gidan suka shige

Daga ɗan gefe muslim yai parcking sannan ya fito

Kallon Abdul yayi ganin ya gyara seat ɗin kujerar motar yai kwanciyar shi hada janyo hula gaban goshi,

Muslim yace “bana son iskanci guru, meye haka? dan Allah ka fito muje mana”

 

Ko uffan Abdul be ce mishi ba, sema rufe idon shi da yayi yana maida kanshi ɗaya ɓangaren.

 

Da ƙyar muslim ya samu Abdul ya fito bayan magiyar da yai ta mishi.

 

A hankali suka taka zuwa inda juwairiyar ta saba sauke muslim ɗin in yazo

 

Zaman su ke da wiya ta shigo ita da wata cousin ɗin ta, fuskar ta ɗauke da murmushi.

 

 

cikin nutsuwa Juwairiya da cousin ɗin ta suka aje tray ɗin hannun su sannan ta zauna a kujerar dake kusa da muslim tana mishi barka da zuwa

 

A hankali Abdul ya ɗaga kan shi daga danne-dannen wayar da yake ya kalli juwairiya ba yabo ba fallasa suka gaisa, tun daga gaisuwar nan be ƙara cewa uffan ba se ma ci gaba da yayi da danna wayar shi.

 

A fakaice muslim ya yi ma wannan cousin ɗin juwairiya signal da ido,

 

Da yake sun san me suka shirya dukan su,

 

a yangance taja kujerar kusa da Abdul itama ta zauna tana kafe shi da idanu

 

 

Tabbas Abdul yaji idon ta a jikin shi, amma kurar da ta ɗebota ma be kalla ba,

ci gaba ya yi da abinda ke gaban shi a lokaci ɗaya kuma yana sauraren firar abokin na shi da budurwar sa.

 

Cikin zolaya juwairiya tace ma cousin din tata “Nihal ki zuba ma Abdul ruwa mana”

 

Kamar jira take kuwa, da ɗokin ta tajawo gora ɗaya ta buɗe sannan ta miƙa mishi

 

Hannun ya sa ya karɓa ba tare da ya kalle ta ba,

Yana ƙarba ya aje robar a gefen shi yaci gaba da danne-dannen shi.

 

Da mamaki nihal ke kallon Abdul, ta ƙura mishi ido ba ko ƙyaftawa

 

Kamar da wasa taji ansa wani abu kamar yatsa an tsokane mata idanu.

 

Kan kace me idanun baiwar Allah na ta zubda ruwa, wasa-wasa har wani dishi-dishi take gani

 

Muslim ne ya lura da yarda nihal ɗin ke ta murza idanu, yace “lafia dai ko?

 

Murya na rawa kamar zatai kuka tace “wani abu ne ya faɗa min a ido”

 

juwairiya ta taso daga inda take ta matso kusa da nihal tace “bari in hure miki”

 

ido dai yaƙi, ba musu juwairiya ta kama hannun nihal tace “bari in rakata cikin gida”

 

 

Muslim yace “eh gara ki rakata, ta samu ta wanke fuskar ƙila ko miye ya fita”

 

Abdul be ce komi ba, se ma a zuciyar shi da yace “maganin me shegen kallo kenan ai”

 

Wasa-wasa tun da nihal ta samu idon ta ya buɗe tace bazata koma ba,

mutumin da ko kallo bata ishe shi ba

 

Ba yarda juwairiya ta iya, haka ta koma wajen su

Sanda ta koma har sun fito daga inda ta barsu sun tsaya a inda sukai parcking

 

Ba su wani ƙara daɗewa ba sukai mata sallama suka tafi.

 

A hanya muslim ke ta zabga mishi tsiya yace

“ba kyau abinda kake yi guru, yarinyar a gaban ka abu ya same ta amma ka nuna ko ajin ka alhali saboda kai take zaune a wajen, gaskiya baka kyauta ba kuma ka sauya hali”

 

Ta tafasa Abdul be ce ba, har muslim ya sauke shi a bakin gate ɗin gidan su ya juya ya tafi.

 

har yasa ƙafa ze shiga gida ya tuna su Hishma sun bashi saƙon sweets, ya manta shaf be siya ba kuma,

 

Memakon ya ƙarasa ciki ya ɗauki mota, juyawa kawai yayi acewar shi zuwa shagon ba nisa,

 

Tinƙis-tinƙis yake tafia,

can ƙasan kunnen shi yake jin takun tafia a ta bayan shi

 

cak ya tsaya daga tafiyar da yake, yana tsayawa yaji an tsaya, a razane Abdul ya juya amma bega kowa ba, a fili ya ja a’uziya sannan yaci gaba da tafiyar shi

 

Duk da hakan be dena jin takun tafiyar ba, a bayan shi da yake jin tafiyar,

yanzu kuma a gefen shi na dama ya koma ji

 

Haka nan ya dake yasa ma ranshi cewa sahun nashi tafiyar yake ji

 

Abdul na zuwa shagon ya iske shagon a rufe, har cikin ranshi be ji daɗi ba,

 

Haka nan ba dan ya so ba ya juya zuwa gida

 

Yayi nisa gaf da ze shiga gida nepa suka ɗauke wuta, dumɗum layin yayi baka ganin komi se hasken taurari da suma ba wani haske can

 

Laluba aljihun shi Abdul yayi ya ciro wayar shi dan ya haska

 

Kamar da wasa yaga haske tarwai ya haske gaban shi,

cikin zuciyar shi yaji ance mishi “muje”

 

Kamar raƙumi da akala haka Abdul ya ci gaba da tafiya cikin hasken nan har ya shiga cikin gida hasken na biye da shi

 

Seda hasken nan ya raka shi har gaban palourn ummie tukun ya ɓace ɓatt dai-dai nan yaji baƙar leda me ƙayau-ƙayau a hannun shi from no where, yana dubawa yaga sweets ɗin da su Hishma suka bashi sautu ce a ciki.

 

COMMENTS AND SHARE SABODA ALLAH

 

MASU SO A TALLATA MUSU HAJAR SU, ZAKU IYA TUNTUƁATA TA WANNAN NUMBER 08145225540

 

 

Add Comment

Click here to post a comment